Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
jinsa har yagama bashi labarin kaff,kana ganin fuskarsa kasan yana girmama girman al'amarin sosai.
"Wannan shine abinda ya faru,khaleel mai zanyi akai,abin ya ɗauremin kai sosai sanann yabani mamaki,bansan ta yanda zan fuskanceshi ba.
Dan haka na yanke shawarar ajiye wannan case ɗin na ɗauki wami daban,idan bincike yazowa mutum da alaƙa bashida daɗi ko kadan"
"Nasan da haka,sanann koni ma idan ina a matsayinka iya abinda zanyi kenan shiga zullumi,amma batun ajiye case inaga ya kamata kuwa"
"Kobai kamata ba dole zan aiwatar,inason zuwa gidansu amrah,duk da tana da laifi a cikin abinnan amma babu yanda zanyi,matata ce haƙƙinta yana kaina,musamman daya zamo ba ita kaɗai bace,amma kuma tunda fansa suka ɗauka nasan abin bazayyi muni ba sosai.
Kuma sannan wane bincike zan cigaba dayi tunda nasan wanda suke aiwatarwar,sannan ita kanta shugabar tasu bata garin ma ta tafi ƙarin karatu.
"Ƙarin karatu kuma,bayan anyi haka kuma ta tafi ƙarin karatu akan aikin,kuma tasan bazata cigaba da aikinba?.....mtsss akwai ayar tambaya a gameda karatun,kodai tasan za'a kamasu ta gudu ta barsu ko kuma wani abin take shiryawa. Domin ruwa baya tsami banza"
"To mai zata shiryah"
"Hmmm a yanda ka karanta labarin sabrah tace batada suna su suka bata,kuma a yanayin yanda take musu magana batayi kama da wanda hankalinta ya gusheba,yanayinta kuma yayi kama da na wanda tashiga wani hakin kunci na rayuwa.
Har yanzu baka zargi wani abu ba gameda itah"
Jijjiga kai sadeeq yayi cikin yanayin kiɗima,danshi bai gano komai ba,amma tunda khaleel ɗin yace akwai wani abu toh inaga tabbas akwai.
Ƴar dariyah khaleel ɗin yayi irinta ƙwararrun masu bincike har dimple ɗin sa yana lotsawa.
"Hmmm karka damu dan uwa,ka share hawayenka inaga zan karbi case dinnan nacigaba daga inda ka tsayah,yanda kake tunanin binciken ya tsaya ba haka bane,ni inada yaƙinin akwai wani abu kullalle kuma boyayye gameda makasan gudan biyu,wato MABARACIYAH da kuma KHAMRIYYAH,kaidai kabar komai a hannuna.. Daga ganin yanayinka nasan baka yarda dani ba,amma lokaci zai warware komai dakuma hujjoji"
Dafa kafaɗar sadeeq yayi tareda mikewa yayi hanyar waje.
Har yazo fita ya dawo tareda ɗaukar kundin tarihin sabriyyah.
"Idan bazaka damuba inason sake duba wanann littafin "
"Bakomai zaka iya tafiya dashi"
Sadeeq ya faɗa cikin kasalalliyar murya.
Washagari monday dec. Sadeeq ya shirya cikin kayansa ya fito daga ɗakinsa.
Da meenah suka haɗu zata tafi makaranta,sun fara jarabawa ranar shiyasa bata tafi da wuri ba.
A bakin dinning yaganta tana shan shayi da sauri sauri a tsaye,da alama mai kaita makarantane yake jiranta.
"Yah sadeeq ina kwana"
"Lafiyah,mai kike a gida har yanxu"
"Uhm dama mun fara jarabawa ne,yau aiki zakaje"
"Eh sarkin tambaya,ina ammi kuwa da khaleel"
"Ammi tashiga ɗaki,yah khaleel kuma yafita tunda safe"
Ina kuma yaje,ya faɗa aransa,amma ya basar tareda zama ya karyah sama sama shima ya fita zuwa headquater su.
Office ɗin shugaban su ya wuce domin kaiwa takardar ajiye case ɗin su khamriyyah.
Yana shiga office ɗin suka haɗa ido da khaleel wanda yake zaune suna magana da shugabannasu,har zayyi masa magana khaleel yayi saurin ɗauke kansa tamkar bai ganshi ba.
Shima sai a lokacin ya tuna ashe aikin su khaleel yafi nasu hatsari,su SSS ne shikuma secret interlligent security(SIS).
Ba'a son asan familynsu saboda hatsarin aikin.
Shima sadeeq ɗin kafsewa yayi tarefa miƙamasa hannu,suna gaisawa ya ɗauke kansa tareda sarawa shugabannsu.
"Dec. Sadeeq sai yau muka ga idonka a wajen aiki lafiya?"
"Uhm na ɗauki karamin hutune kawai,ayi haƙuri ogah"
"Okay ya wuce,ya batun mission ɗin dakake kanyi na wannan matan,inaso ka kawo min takardun case ɗin,Dec. Khaleel yace zai cigaba da binciken.
Bamuyi zaton daga karba rokonmu nayin aiki a wajenmu zai fara aiki yanzu ba,hakanma kuma a wanann tsohon case ɗin.
Duk da haka muneda da godiyah dec. Khaleel,inshaallah dec. Sadeeq zai baka dukkan bayanai akai,in kanaso ma zaka iya ɗaukarsa mataimakinka,don mataimakiyarsa ashe itace shugabar masu yin ta'asar"
"Duk naji wannan labarin,amma yanzu ba wanann mission ɗin zam faraba,inaso na fara dana MABARACIYAH,tunda itace ba'a gano wacece ba,kafinnan kuma ayimin afuwa zanyi wani uzuri na sati biyu tukunna."
"Ba komai muneda godiyah,idan kagama saika fara shikenan"
Daga haka sukayi sallama da shugaban securityn.
Yana fitowa daga office ɗin kira ya shigo wayarsa.
Ɗagawa yayi tareda amsa sallamar da'akayi masa.
"Naji mai kace,amma karka kuskura kace na dawo kasarnan,ban yadda naji labarin a wajen kowaba,ciki harda mahaifina,abinda na daɗe ina jira tsawon shekara goma sha biyar yau zan farashi,babu wanda zayyi idan ba ni ba,haƙƙine a kaina dole sai nine zanyi,dan haka zuciyata bazata taba yin sanyi ba idan ban biya abinda tayi ba.
Ka shirya min komai ina zuwa gobe "
Yana gama faɗan hakan ya jefa wayar a aljihu tareda furzar da isa mai zafi daga bakinsa ,kana ya nufi inda motarsa take,har sannan fuskarsa tamau take babu alamar fara'ah a kanta.
Toh dec. Khaleel kenan,ko menene a cikin ransa dayake boyewa allah ne kaɗai masani wannan labari.
____________
Deejah ce itada yadiko lami a tashar katsina dake garin daurah zasu tafi katsinan cikin gidan sarauta inda take aiki.
Basu dade da hawa motar ba tacika,dan dama sun samu mutane a ciki.
Dan murmushin gefen baki deejah tayi lokacin da motar ta fara haurawa kan titi da niyyar daukan hanya.
Kallon bishiyoyin da suke wucesu take tareda yimusu bye bye itama da hannunta.
Ba yaune shigarta na farko garin ba amma kuma wannan yana ɗayah daga shigarta zuwa aiki nata na kanta.
Dan haka dole tafiyar tasakata nishaɗi sosai.
Yadiko lami ce ta kalleta bayan ta gutsiri goro ta saka a bakinta,
"Yarinyah kekuwa akan kiyi aure shine zakije fara aiki a gidan sarauta,kinsan fah wanann wajen ba daidai yake da sauran waje ba.
Wajene da ake zuba mulki da kuma taƙama da nuna isa,dole kai talaka sai kayi haƙuri,duk da mu a bangaren Hajiya Saratu muke,ita babu ruwan Duniya Allahu masauƙi ce a wajenta.
Amma kinga Hajiya fulani ateeka,hmmm karki yadda ko kashinta ne wani abu ya haɗaki dashi,dan ba lallai ki kwana lafiya ba,dan haka ki kiyaye ko sashinta kada kije inkina son gamawa da arziƙi"
"Nikuma yadiko lami a sashenta nakeson nayi aiki,domin kuɗi nazo samu ba zaman lafiya ba,naji ance tafi biya da tsoka"
"Keeee ƴar nan,ranki ai yafi kuɗi koh,toh ki kiyayi kanki da wanann banzan tunanin"
"Babu abinda zai faru,ki kwantar da hankalinki,amma a wajenta nakeson aiki,kodah kuwa namana zata dunga yanka tana zubarwa da kaɗan kaɗan.................
Kunji fah,muje zuwa toh ...
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
29••30
Tundaga wannan maganar yadiko lami bata sake cewa deejah komai ba,dan taga abinnata azeemunne.
A tasha aka sauƙesu suka hau adaidaita zuwa gidan sarautar garin katsinan.
Tundaga bakin masarautar yanda ake zuba mulki kasan ba wajene na wasan yara ba.
A bakin kofar shiga gidan mai adaidaitan ya samu damar yin burki,dan yasan ko giyar wake yasha,bai isa tsallaka layin shigaba.
Kuɗinsa yadiko lami ta fitar ta bashi,tanayi yana gaisawa da fadawan da suke tsaye a bakin kofar,da alama akwai sanayya a tsakaninsu.
Itakuwa deejah amfani tayi da wannann damar wajen ƙarewa farfajiyar ƙofar kallo,duk da ba yau tafara shigaba amma kuma wanann zuwan na dabanne,dole ta lura kana ta maida hankali akan rayuwarta.
Yadiko lami ce ta jijjgata tareda yimata kallon alamar tambaya.
"Anyah kuwa deejah kalau kike,naga sai kalle kalle kike da kuma shiga tunani,saikace yau kika fara kallon fada,naga akwai a garinku daurah ma mai ɗumbin tarihi dayafi na nan"
......Masarautar daurah,masarautace data rayu a ɗumbin shekaru fiyeda da Dubu da suka gabata.
Garin ya ƙara samun suna ne da kuma kambun a tarihi a lokacin mulkin Sarauniya DAURAMA SHAWATA,ita ce sauraniyata tara a lokacin,wacce ta gaji mulkin daga wajen sauran matan dasuka gabaceta.
Sannan garin yana ɗauke da tarihin Abu yazeed wanda aka fi sani da Bayajiddah.
Shi mutum ne daya samu shiga hikayoyi da kuma tarihihi na ƙarasa hausa.
Wanda labari yazo cewa shine jarumin daya samu kashe macijiya SARKI da take cikin rijiyar ƙusugu ta har yanzu tana nan a garin dauran.
Uwa uba kuma riƙo da sarauta da kuma al'adu......sannan kuma ga.....
"Ya isa haka lami wannnan bayanin,haƙiƙa kin cancanci yabo da wanann bayanin naki,amma ki sani hattara,a gaban wata masarautar kike"
Wani bafadene ya amshe maganar yadiko lami ɗin,aikuwa ta kifta ido,da alama dama dashi take maganar
"Habadai,duk da tafita dadewa amma banda tarihi da daukaka,ko barta tayi kallo taga waje tamkar a kasashen larabawa"
Shima ɗayan dayake wajen ya fada.
Sunkuyar dakai deejah tayi taƙi bari su haɗa ido da bafaden,kanagani zaka dauka dan kunyah take yi badan tsaroba.
Jiransu tayi a gefe suka gama surutunsu kafin yasaka wasu yara ɗaukar musu kaya zuwa can bangaren hajiya saratun inda take aiki.
Bayan sun kutsa kai cikin gidan sarautar nan ma wani sabon kallon deejah ta kafa tareda na nazartar duk wani lungu da saƙo na gidan.
Sashen babu laifi yanada kyau sosai,amma bai kama na sarauniyar gidanba wato fulani ateekah,dan komai nata ma dabanne dana sauran gidan,shi kansa sarkin a wajene yake sarki,amma in ya shigo gareta shine sarkin ba itah ba.
Babban falon dayake farkon sashen suka shiga wanda aka malaleshi a jan carpet mai laushi da alfarma.
Ma'aikata zai zirga zirga suke wajen tsaftace wajen da bashi ado na musamman.
Wata matashiyace ta matso inda su deejah suke tsaye,zatayi sa'ar deejan,ko kuma ma ta fita da shekara guda.
"Lahh Yadiko lami sannu da dawowa,baba asaben kuwa ta fita dazu,amma tace ba nisa zatayi ba,taje karbo kayane.
Wannan kuma fah ƴar kice"
"Eh to ƴar tawace,nan take gidan maƙwantammu tace zata biyoni tayi aiki anan"
"Babu komai sai tazo mu dunga wanke wanke muzama mu shida kenan,dama kayan sunada yawa sosai"
"Amma kuma tace ba a nan zatayi aiki ba wai a sashen fulani ateekah zatayi"
Zaro ido budurwar tayi kaman ance mata ga can mutuwa.
"Sashen ........uhmmm kuma?..anan zatayi aiki,yadiko lami ki fada mata mana,da alama batasam mai yake faruwa"
"Ah to Salaha ya zanyi,na faɗamata tace anan zatayi,sai muyi mata fatan allah yasa taji da sauƙi"
"Dama bani zan kai kaina ba,itace zata nemi nayi aikin a wajenta,lokacin data nemi naje kuma bazan ƙi ba,kunga babu zancen cutarwa,idan bata nemeni ba kuma shikennan zan zauna daku a nan muyi aiki har zuwa lokacin daxan tara abinda na tara na tafi.
Nagode yadiko lami dakikamin zirin zuwa nan wajen,kema salaha nagode da haɗuwa dake"
Ɗan murmushi tayi tareda jin daɗin hankalin deejah,dan haka take,tana da baiwar siye mutum da kalaman bakinta,tamkar tanasaka asiri a ciki.
"Kin burgeni sosai,muna miki fatan alkhairi,menene sunanki?"
"Sunana deejah"
"Khadeeja dai ko"
"Ahah deejah ne"
"Tamm shikennan duk yanda kike sonsa dai deejah,muje na kaimiki kayanki ɗakinmu,mu zauna tare kafin ki koma can"
"Kiyi haƙuri na zauna da yadiko lami tukunna kafin saina komai gunku idan bazaki damuba"
"Lahh ba komai,da alama baki da sabo,nizan sakaki mu saba"
Salahan ta faɗa cikin sigar wasa,wanda hakan yasa deejah yin murmushi.
Ɗakin babu laifi saidai rashin privacy kawai,amma akwai silin da fanka da kuma katifa.
Samun waje deejah tayi a gefen katifar salaha ta ajiye kayanta,wani idan ya ga kayan zayyi zaton kwana biyu zatayi ta tafi,saboda baifi kaya biyarba tazo dasu.
Fitowa tayi daga ɗakin domin zuwa ta ɗan jaga cikin gidan.
Iska ce take kaɗawa da alama hadarine ya taso amma yasaki iska,gyalen dayake kan wuyanta take ta ƙoƙarin gyarawa,yayinda idonta kuma yana tsaye kyam akan sashen Fulani ateekah,iya katafaren sashen wajenba abin kallone,kuma yanda labari yake jagayawa itada kanta tasake gina wajen ba wanine ya gidan mata ba.
"Hmmm ki gama duk wani farinciki da walwala da kuɗin da kike taƙama dashi,abinda nasani guda ɗayah shine kinyi kuskure dakika bari na shigo wannan gidan,bazakiyi danasani ba ma saikin gayyaceni cikin inuwarki,a lokacinne nikuma zan fito dake daga cikinta!!!!!"
Wata mata ta gani tafito daga cikin sashen sai sunkuyar dakai take,da alama wani waje zataje.
Jikin deeejah ne ya bata akawai lauje cikin naɗi,wanda hakan yasata tunkarar matar batareda tsoro ko fargaba ba.
Da gangan lokacin da sukayi arba ta bugi kafaɗar matar,ji kake timm ta faɗi a ƙasa,dan batayi mamakin deejah zata bugeta ba.
"Ke kinada hankali kuwa zaki bugeni,kinsan ni wacece?,duk filin gidannan bai isheki ba saikin bangajeni saboda rashin hankali"
Ta ƙarisa maganar tana tashi daga ƙasan,tareda tafa hannunta tana kaɗe ƙurar data ɗiba.
Basarwa deejah tayi na dan wani lokaci,kafin tashi ɗayah sanja zuwa salon nuna tausayi lokaci guda.
Marairaicewa muryah tayi tareda lumshe ido irinna mutane masu sanyin rai.
"Kiyi haƙuri baba,bansan zaki zo ta nan ba da bazan bugeki ba"
"Ke dubeni nayi miki kama da babarki"
Kallonnata deejah tayi kaman yanda ta buƙata,to mai zata ƙirata,banda figyagygyiyar siffarta babu abinda ya haɗata da yara,don tsohuwa ce kaman bishiyar tsamiyah.
"Toh mai zance miki innah"
"Ke ƴar rainin hankali,innah kuma kina ganina yarinya,kicemin zee zee"
Ta faɗa tana kashe ido dayah irinnasu na ƴan bariki.
Dukkansu a tare hankalinsu yakai kan wani ƙullin jan tsumma a ƙasa,wanda zee-zee ta jefar lokacin da deejah ta bugeta.
Deejah ce tayi saurin isa zuwa ɗaukar abin,wanda yake maƙale da wata ƴar takarda anyi rubutu da tawada.
Cikin ƙwarewa da harkar kafin ta miƙa mata har tagama gane mai yake dauke a jikin a takardar.
Karba zee-zee tayi tareda fara tafiya tana karyar dakai,da alama tana cikin fargaba da aikan da akayi mata.
"Maganin ya baci ai"
Juyowa zee-zee tayi tareda buƙatar deejah ta maimaita mata abinda tace.
Ita kuma ganin hakan yasa tayi murmushi tareda juyawa zata tafi.
Da gudu zee-zee ta finciko rigarta tareda juyota tana fuskantar ta.
"Mekikace baiwar allah,taya kikasan magani ne kuma har ya baci.
Nida nakawo shi daren jiyah babu wanda yaganni bansan ya baci ba sai ke,da ban taba ganinki komai kamarki ba a cikin fadar nan"
"Nima bansan lokacin dakika shigo dashi ba saida na gani yanzu,batun bacinsa kuma naga wanda ya 'bata maganin ne a shigowata gidannan"
"Waye ya 'bata maganin,meyasa bamu ganshi ba sai ke"
"Saboda bakuda ikon ganinnasa,sannan batun waye mezakiyi idan na faɗamiki waye"
Fisgewa rigarta deejah tayi zata tafi,amma maganar zee-zee ta dakatar da ita da cigaba da tafiyar.
"Duk abinda kike so ki faɗa zan miki,amma dan allah ki taimakeni ki fadamin mai kika sani,daga ganinki ke ƴar baiwace irin mutanen da muke nema"
"Toh shikenan zan faɗamiki waye ya bata,amma saikin bani labarin maganin menene,sannan waye yake amfani da maganin.
Idan kika yimin hakan,nikuma zan faɗamiki waye ya'bata maganin."
Shuru zee-zee tayi kaman bazata ce komai ba,can kuma saita numfasa tareda cewa
"Inaga ke baƙuwace bakisan jinyar da yarima Mubarak yake ba,wanda yanzu tsawon shekaru goma kenan yana fama dashi,duk wani magani da akayi har yanzu ankasa samun nasara akan ciwon,ko yaushe cigaba yakeyi"
"Wane irin ciwone haka"
"Hmm babu wanda yasani,domin baya magana bare ya faɗi abinda yake damunsa,kullum idanuwansa ne a buɗe yana kallon sama,shikaɗaine alamar datake nuna shi rayayyene ba matacce ba.
Asibiti ba iyah na ƙasarnan ba harda nawaje anje,amma babu nasara,shiyasa aka zubawa sarautar allah ido kawai,domin na hausan ma anyi ta jarrabawa amma shuru kaman ana shuka dusa"
"Uhm to amma ke mai hadinki da neman maganin ,ina mahaifiyarsa take"
"Kee kiyi hattara,maganar Fulani ateeka kikeyi,ina ba so kike kiji harshenki a ƙasa ba"
Ta'be baki deejah tayi,da alama gargadin bai je ko'inaba.
"Shikenan bari na faɗamik,wanda ya 'bata maganin ba mutum bane aljanine wanda jinsinsu yawanci sukan siffanta da dabbobine,yazo a jinsin baƙar kuliyah dazu da rana,shine ya 'bata maganin da kuma kawo gidan.
Sannan kuma da alama akwai wanda bayason tashin majinyacin naku,domin shi baya aiki sai an aikoshi bayan an yanka masa baƙar kaza"
Tsuru tsuru zee-zee tayi lokacin da taji labarin abinda deejah ta faɗamata,kenan babban aikine a gabansu ɗanye.
"Amma in bakazi damu ba in tambayeki?"
Kallonta deejah tayi kaman bazata ce komai ba sai kuma tace
"Eh faɗi inajinki mai ya faru"
"Daga gani keba ƴar nan bace,amma ke wacece"
"Ni makashiyace,mai taimako ce,azzaluma ce,mai jawo ciwoce,sannan kuma mai maganice,mai sanyi ce kuma zazzafa ce,maƙiyyace kuma masoyiyace.
Sai ki zabi da wanda kike ganin zaki kalleni da siffarsa,kowanne kika ɗauka zai bayyana miki wacece ni dadai yanda kika ɗaukeshi"
Ƙamewa zee-zee tayi a wajen,har deejah ta bacewa ganinta bata sani ba,saida ta ƙofta idanuwanta kafin daga bata wajen.
*_______*______*
Dec. Sadeeq ne a gaban madubi yana gyara zaman hularsa,lokaci zuwa lokaci yake furzar da iska.
Kana ganinsa kasan fargaba ce a ransa.
Agogonsa ya ɗauka da key ɗin motarsa tareda fitowa a cikin ɗakin.
A falo yayi kicibis da khaleel wanda yake zaune yana shan lemon daya ɗauko a cikin fridge.
"Bro yaushe kashigo banji motsinka"
"Ban daɗe da dawowa ba,ina ɗaki tunsafe wajen duba case ɗin da kuka bani.
Ajiyeshi zanyi ma dan da alama bayason gaggawa.
Dama akwai wani waje danake son zuwa,toh inaga gobe zan wuce"
"Inane haka daga dawowarka,ya kamata ka zauna ka ɗan huta tukunna"
"Babu zancen hutu ɗan uwa,aikin da dalilinsa yasa nayi wannan karatun shi zanyi yanzu"
"Aiki kuma wane iri?"
Jimm khaleel yayi kaman mai tunani kafin yace miƙe daga kan kujerar.
"Manta kawai Ɗan uwa,in lokaci yayi zakasan menene,amma yanzu bazan iya faɗamaka ba.
Yanzun ina zakaje naga ka sha sabin kaya,a sanina dai banji wani biki kwanannan ba"
"Uhm uhm dama zanje wajen sabriyyah ne,ko zaka rakani mu tafi tare,dan jinake kaman naje kaman karnaje"
"Wacece kuma sabriyyah,ohh Amrah kake nufi.
Gaskiya Sadeeq banyi maka alƙawari ba,a yanda nasake karanta abinda sukayi bazan iya haɗa ido da ita ba yanxu,kasan yanzu case ɗinsu na hannuna,to zan iyah kamata Sadeeq,dan saboda kaine kaji nayi shuru ban kawo maka zancenba.
Babban abinda yasa ban kamasu ba kuma so nake na kamo babbar,sannan na haɗata da zargin danake da Mabaraciyah.
Saboda nasan tunda tana matarka to bazasu gudu ba,amma hukunci dole saisun fuskanceshi,koda kuwa iyayena ne ko naka sadeeq"
Yana maganar ne cikin dakewar muryah,tamkar ba khaleel ɗin da yasani ba a jiyah,wanda ya karbi kukansa tamkar zai taimaka masa,amma yasanja zuwa mai tsaurin ra'ayi.
Jijjiga kai Sadeeq yayi tareda cewa.
"Ammmm.....amma kai kace zaka taimakamin wajen fitar da ita daga wannan halin,babban matsalar ga ciki a jikinta,mai zancewa ɗan idan yaji mamarsa ta taba shiga kurkuku?"
"Hmm bakai bane wannann sadeeq,yakamata ka dawo daga kogin giyar soyayyar daka shiga,bai dace mai bincike irinnamu da naku ya faɗa zurfin soyayya kaman haka ba,saboda za'ayi amfani da hakan a cutar dashi kaman yanda akayi maka.
Karka manta tun farko fah ta aureka ne domin manufarsu badan tana sonka ba,sannan ƴan biyunta tasha zuwa gidanannan domin neman bayanai,amma duk da yanxu kasan hakan bakayi komai ba, burinka shine kayi amfani da aikinka wajen kubutar dasu,saboda matarka ko kuma ɗan cikinta karya ji labarin ka saka uwarsa a kurkuku"
"Khaleel nasan abinda nake ban kyauta ba tun ranar da akan idona khariyyah tafita daga ɗakin bincike,badan komai ba danna nazama mai rauni saboda soyayya.
Amma hakan badaga ni bane babu