Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
tasani gameda tsakanin hajiya fulani da deejan,harma da irin rashin tsoro da kasadar deejan.
Abin yabashi mamaki amma ba sosai ba,dan kowa yaganta yasan macece mai kamar maza a ta fuskar kasada,abinda bai sani ba shine yanda deejah tayi yarjejeniya akan ta warkar dasu ita kuma zata bata akwatinta,saidai kuma ta buɗeshi daga ƙarshe,hakan ma bai isheta ba ta saceta a asibiti bayan ta farka.
Bata ɗauketa tana sumeba saida taga ta tashi tukunna.
Tabbas akwai abinda yake faruwa a ƙasa wanda bai sani ba.
"DAUKAR FANSA take,to kennan wacece itah,sunaye mutane biyu hatsabibai ne suka shigo cikin kunnensa.
MABARACIYAH &V-LADY,su biyunnan yafi zaton inaga ɗaya daga cikinsu ce,shitttt gashi har sannan dawowarsa kenan bai san suwaye ba,duk da yanada bayanan su amma kuma mai ya haɗa ɗaya daga cikinsu da hajiya Fulani??????.......
Yana tsaye yana cizon yatsa motocin su Jalal suka shigo gidan daga asibiti. Duk wanda ya fito daga motar sai ya kalleshi har suka ƙare baiga deejah ta fito daga motar ba.
Salaha ya kalla har zata shige ya ɗanyi mata magana.
"Am salaha ina deejah kuwa,banga kun dawo da ita ba"
"Ahah gaskiya bansani ba,inaga ta tsaya wani wajenne a hanya,dan dama tacemin wai zata duba wata mata a asibitin"
Daga haka salaha ta shige ta barshi a wajen batareda ta kawo komai a ranta ba.
Ɗan gefe ya koma yana kare fuskarsa,amma saida khadija ta kulada shi.
"Yah Eemran am nace bah......"
Tun kafin ta gama ta nemeshi ta rasa,suma su hajiya saratu kallon wajen sukayi amma basu ganshi ba,itama komai ta tuna sai tayi shuru da zancen,ashe fah bayan mutanen gidan yaja kunnen kar wanda yayi maganar dawowarsa.
Duk da bata faɗi sunansa ba amma kuma sai taji dai bai dace ba,tunda baya so.
Shikuma kiran da tayi masa sannna yaja saleem da sauri zuwa ɗakinsu.
Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe yana haki.
"Kai khaleel lafiya kuwa?"
"Uhm kaman kasan zan koma kan sunan,lokacin fara aikin su mabaraciyah dana karba zanyi yazo ,saidai kuma tsoro da fargaba sun mamaye zuciyata a yanzun"
"Mai kake nufine,munzo domin
Kama mahaifiyarka mu miƙata ga hukuma,yanzu kuma abin ya juye,wai ta bace ba ganta ba"
"Kai dec. Saleem ina hankalinka ya tafi,ba bacewa tayi ba,ɗauketa akayi,kuma deejah ce ta ɗauketa"
"Whattt mai kake nufi da deejah ce ta ɗauketa,kana da shaidu akan hakan?"
"Shaidu kake nema,ga babbar sheda nan,shin kun dawo tareds ita ne yanxu a mota.
Ta hannun daman Ummee tazo yanxu take faɗamun yanda sukayi da deejah daren da zasu ɗaukemu,sannan kuma ita ta ɗauke akwatin tsafinta ta fasashi,kuma itace ta ɗauke amal ranar da aka nemeta aka rasa.
Kuma inada tabbacin khaleel ma akwai gargaɗin da tayi masa,kaina ya kulle dec. Saleem sosai,reshe yana nema ya kuye dani,gabaɗaya zuciyata so take ta ƙaryata abinda nake ji a cikin raina."
"Gaskiya abin zaiyi maka babu daɗi,yanzu dole mukoma headquater mu buƙaci bayanai daga amal da kuma jalal"
"Karkayi yanda yan gidan zasu sani,har yanzu ban yi niyyar bayyana musu a matsayin khaleel ba tukunna,da sauran lokaci"
"Karka damu ogah za'ayi yanda kace,amma ya kamata ka faɗawa dec. Sadeeq halin da ake ciki,koya kace?"
"Eh zan sanar dashi amma ba yanxu ba saina gano inda deejah ta ajiye Mahaifiyata tukunna"
Kayansu na ɗakin suka fara tattarawa ba tareda kowa ya gansu ba.
Suna gamawa saleem ya ɗaika yakai mota a jiye,shima Khaleel babu wanda ya ganshi ya shige motar suka fita daga gidan.
Saida sukaje bayan gari tukunna saleem ya kalli Dec. Khaleel.
"Toh mun bar area palace yanzu,"
Dec. Khaleel bai ce komai ba sai ɗaye abinda yake fuskarsa da yayi,take ainihin fuskarsa ta bayyana,wanda deejah ta taba kallonsa da ita lokacin yana jinyah.
Shima saleem fuskar wawayen daya saka ya cire tareda furzar da isakar bakinsa.
"Finally back to the business,ammafah nayi missing ɗin wancan saleem ɗin ogah"
"Hmmm ai kana ban dariyah sosai a wancan fuskar,sai kace drivern gasken,inna ganka bazance kaine wanda muke training tare a china ba"
Ƴar dariyah Dec. Saleem yayi tareda cewa.
"Kaima waye zaice kaine wannan mai kulada dawakin hhhhhjj"
"Hmmmm aikin akwai wuyah amma akwai shiga rai,danna saba da dawakan sosai a iya wannan lokacin"
"Ka ƙira shamakin gombe ma kayi masa godiya da taimakon da yayi mana"
"Okay inshaallah,yanzu dai kaini gida nayi wanka na kwanta tukunna,su san nadawo daga tafiyar danayi,amma fa zanyi missing ƙanwar nan taka sosai(amal),dan gaskiya tashiga raina"
"Karka fara wannan wasan,kana nufin tunkararta zakayi kace mata kaine driver,ko zuwa mata zakayi a matsayin sabon mutum?"
"Huhh kumafah nima bansaniba,yazanyi dole na haƙura,duk da nayi kewarta"
Shuru Dec. Khaleel yayi bai kulashi ba har ya ajiyeshi a gidansu shikuma yawuce nasu gidan.
Meena ya gani a falo tasaka headphone tana ta jijjiga kai,ɗaga ido tayi ta kalleshi tareda washe baki,
"Lahh yah Khaleel yaushe ka dawo,ko sanarwa saidai muganka"
"Ina ummah take?"
"Uhm ta tafi fada,wai mama fulani ce ta bata ba a ganta ba"
Ɗaga kai kawai yayi daga nan ya wuce ɗakinsa..
Tunda ya shiga ɗakin tunanin deejah suke son kallame zuciyarsa,amma yaƙi basu dama,har yashiga banɗaki yasaki ruwan sanyi a jikinsa.
Furzar ta iska yake shi kaɗai yana dukan bangon ɗakin,gaba ɗaya yarasa inda zai saka kansa.
"Yah Salaaam" shine abinda ya faɗa a sanyaye.
Toh fah
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
49••50
Kwara mata ruwa tayi a jikinta,hakan yasa taja ajiyar zuciya tareda ware idanuwanta akan deejah,wacce take tsaya tasha riga da wando.
"Kalleni dakyau nice dai ba wataba,mabaraciyar datake aiki akan wasu yau yazo kanki,saiki jiyaryi hukuncinki a yau ba sai gobe ba"
Ko bakin magana hajiya fulani takasa samun yi,tsoron dayake jikinta take ƙoƙarin rikewa ta hanashi ya fito daga jikinta.
Tsugunnawa deejah tayi a gabanta,su biggy kuma suna tsaye kaman samudawa.
Idonta yasha kwalli na rashin mutunci,kana ganinta kaga irin fuskar ƴan farauta.
"Toh barinayi sauri nagama dake kafin masoyina kuma ɗanki yazo ya riskemu,dan yanzu shine keda Akalar ragamar bincikenmu nida Khamriyyah.
Hmm harya fara bani tausayi yanda ɗan uwansa ya bani,da alama ɗanki zai sha wahala,kema kuma zaki sha.
Saina bari yakusa wajennan kafin na yi miki hukunci,saboda karki mutu kafin ya iso saboda zubar jini.
Biggy ku kariso aiki zai fara,ina kun bashi hint ɗin inda muke,ko har yanzu bai ganoba"
"Eh mun nuna masa,idan ya gane to da alama yana shirye shiryen zuwa"
"Okay let we start,hajiya fulani kafin ki suma idan muka fara aiki,barina baki saƙonki.
Kisaka a ranki wannan abinda zan miki shi ake ƙira da Retribution,wato ramuwar gayya kenan,duk abinda kikaga zan miki kwatankwacin yanda kikayiwa ubana ne,babu yafiya kema saina zartar miki shi.
Dan haka muhaɗu a kotu idan kina raye da ranki"
Tana gama faɗan hakan kafin hajiya fulani taja wani numfashi tasheka mata wani abu a hancinta.
Injin katako ta ɗauko,yana kara ta yanke mata ƙafafu dukka.
Bayan hakan bai isheta ba ta saka wani Karfe ta cire mata idanuwa dukka biyu,jini ne yafara ambaliya,hakan yasa tayi baya sauri tareda gode hannunta tana ganin aika aikar da tayi.
Daga fuskarta zaka gano aikin da tayi yana cin ranta,amma haka ta danne ta ajiye wata wasiƙa a kan tebur suka nufi hanyar barin wajen.
Waiwayawa tayi tasake kallon Hajiya fulani wacce jini yake zuba a ƙafafunta da kuma idanuwanta.
"Namiki da daɗi ma akan yanda kika min,kin ci albarkacin ɗanki"
Suna barin wajen baifi da minti biyar ba saiga su Dec. Khaleel sun shigo wajen a motar yan sanda ta sauri.
Dama tun ɗazu suke ta ƙoƙarin nemo wajen a massage ɗin da biggy ta tura musu.
Sai yanxu Allah ya basu ikon gano wajen.
Saidai kash duk yanda yaso dakatar da ita da aikata hakan ya makara,ta riga ta aiwatar da mummunan aikin da yake fargabar kada ya auku.
Takardar da take gefen wajen ya ɗauka tareda sakata a aljihu,bayan ya an fitada Hajiya fulani cikin mummunan yanayi,bata san inda kanta yakeba dan azabar dayake ziyartarta.
Magana dec. Saleem yake masa,amma kwata kwata bays jinsa,fargabar abinda zai gani a cikin takardar data bar masa yakeyi,duk da acikin ransa yana addu'ar Allah yasa bata ɗaya daga cikinsu,Amma kuma zicuyartasa ma tasan gaskiya ai.
Su dec. Saleem ne suka wuce da hajiya fulani asibiti,shikuma yana tsaye a wajen da wasu ƙananan ma'aikata yana duddubawa.
To meyake da tabbacin zai duba a wajen ma,shikansa yasan waye ta aikata hakan,amma kuma yagagara faɗawa kowa wacece.
"Oh yah Allah,dama ashe haka Sadeeq yaji,shi matace ma harda ɗa,nida ko hakkinta ba'a kaina yake ba,jinake kaman zuciyata zata faso kirjina,taya zan iya sakawa wannan hanayen ankwa,bayan mungun son danake yiwa mai su.
Har cikin zuciya ta inada muradin kareta,duk da nasan mai ta aikata,burina shine yazamo tana da wani dalili daya sakata yin wannan aikin. Mai yasa daga dawowata rayuwata ta juye daga kwanciyar hankali zuwa tashin hankali?"
Takrdar dake aljihunsa ya fitar tareda wareta
__Assalamu Alaikum Yarima Junaid,ko kuma nace Dec. Khaleel.
Kayi hakuri da boye maka abubuwa da dama da nayi,babu yanda zanyi ne dole saina aikata hakan.
Kaman yanda kake so na da kuma begena nima haka kake a cikin raina,saidai muradin ɗaukar fansa tasa Alaƙar dakake buƙatar sakawa a tsakaninmu bazata yiyu ba.
Bazan iya furta maka kalmar soyayyata har ta kaimu ga matakin gaba ba,alhalin ina akwai baƙin cikin tabon da mahaifiyarka tayimin a raina.
Da zan iya yafewa nabari ya wuce danayi,saidai ganin duk da soyayyarmu nakasa hakura saida na dau fansa,yasaka bazan iya rayuwa tareda kai ba.
Ka yafemun abinda nayi maka a zaman mu,Sannan ka manta dani ka auri ƴar mutunci,mai halin sanyi da tausayi irinna mata,ba irina ba wacce take da taurarriyar zuciya,da kasa manta abinda akayi mata a baya.
Zanyi kewarka sosai,ina jiran ranar dazaka saka ankwa a hannuna ka kaini ga alƙali masoyina.
Domin dama wannan shine aiki na ƙarshe daya ragemin,samuna zayyi maka wuyah,saboda koda zan kawo maka kaina saina gyara wani abu tukunna,wanda niya kamata na gyarashi,kafin sannnan ka huta,ka kwantar da hankalinka,babu wani aiki dazanyi Bayan wannan.
Nasan hakan zai yi maka wuyah,amma ta hakannne kaɗai zaka manta dani a shafin rayuwarka,ka cigaba daga inda ka tsaya.____
Daga mai sonka da kuma ƙaunarka......
Khadija Abdullahi kankia
(DEEJAH MABARACIYAH)
saurin zefar da takardar yayi tareda ja da baya ya faɗi akan kujerar dake bayansa.
Abinda yake gudu shine ya faru,itace ɗaya daga cikin wanda yake zargi.
Tun yana china yakejin ɗanyen aikin Mabaraciyah,yaji ya tsaneta,burinsa shine ya dawo gida ya fara aikinsa akan ta bayan yagama aikin mahaifiyarsa.
Bai saniba ashe zayyi rayuwa tareda ita,kuma yafaɗa muguwar tarkon soyayyarta.
Riƙe kirjinsa yayi tareda zayyano duk wata addu'a data shigo bakinsa.
Sati guda da faruwar abin aka fita da hajiya fulani ƙasar waje domin yi mata aiki,na idanu da kuma ƙafafu.
Gari kowa ya ɗauka banda tsinuwa akan mabaraciyah babu abinda kake ji.
A tsawon wanann satin Khaleel a killace yayi su,dan ko media baya son leƙawa saboda zagin masoyiyarsa dayake shiga kunnesa.
Ana cikin wannan ne kuma khamriyyah tasako ƙafarta kasar,bayan wani muhimmin aiki dataje koyowa a ƙasar ƙetare,bikin Dec. Sadeeq kuma da Madeena shima saura sati ɗayah.
Khairiyyha ce taje tarota a filin jirgi itada su fadeelah,dan ranar kin zuwa makaranta sukayi.
A hankali take takowa daga cikin jirgin cikin wani salon arnen dafiya mai tafiyar da duk wanda yaga ta burgeshi.
Wandon plazo ne a jikinta na jeans sai kuma top karama data ɗora a rigar saman,sannann ta kawo gyale tayi rolling dashi.
Ga kuma baƙin glass ta toshe fuska.
Buɗe baki khairiyyah tayi daga nesa tana kallon yanda ƴar uwartasu tazama kaman ba itaba,da alama zaman wajen ya ƙarbeta sosai.
"Wow Khamree kinganki kuwa"
"Yane na sauya ne?"
"Tambaya ma kike,yanzu dai muje gida kawai,inada aikinyi nabari nazo daukarki,saboda deen bayanan an turasu Abuja akan neman aikinsu"
Taji abinda khairi tace,amma bata bashi muhimmanci ba sosai saima hankalinta data miƙa kan abin sonnata,wato yaƴan da uwarsu haifarsu kawai tayi,duk wata wahalarsu ita tasha da kanta.
"Fadeen kin kara girma a ɗan wata huɗun danayi bana nan,mai su khari suke baki kikeci"
Kukan shagwaba tasaka,tareda narkewa a jikin khamriyyah,kana tace.
"Anty khairi dukana take kullum,dannace suna soyyyah da uncle deen,kuma ma dan anty sabrah tace,idan uncle Sadeeq yazo bazai kula kowaba saini kaɗai"
"Tabbb dukanki take kenan,banni da ita,babu abinda zan bata a chocolate ɗin mu,fadeel fah,shine kaja ka tsaya kana kallona koh"
"Kiyi haƙuri mommy,nayi murna da kika dawo sosai"
"Toh naji kuzo mutafi kar wannan antynnnaku ta cinyeni ɗanya,tun ban gama shaƙar iskar ƙasar ba"
Daga haka suka shiga motar sai gidannasu.
Tun a bakin kofah maryam da Fareedah suka taryeta,da inno ,balkisu wacce itama tazo taryar khamriyyah daga gidanta,saikuma Dr Nawwarah itama bataje aikiba,sai uwar gidan a wajen Dec. Sadeeq wacce take zaune da tulelen ciki na wata bakwai ya shiga na takwas.
Hararar wasa khamriyyah tayi mata tareda ware mata hannu
Babu yadda ta iya bataso tashi ba haka ta yunƙura ta miƙe tareda nufar khamriyyan.
Rungume juna sukayi tareda saka dariyah a tare.
"Gaskiya na daɗe bana nan,ji yanda wannan matar ta zama ƴar lukuta,khairiyyah tacemim kin fi kowa ci a gidannan.
Tukunna ma ya zancen tsakanim ki da mijinkine har yanxu.
"Komai normal Khamree,yanzu dai zoki ci abinci kiyi wanka ki huta tukunna,saiki bamu labarin Turkey ɗin,da kuma abinda kikayi"
"Hmmm gasane fah aka tura a makarantar danaje ƙarin karatu,banyi ma nasara ba yanda nake so,ta biyu nazo suka bani mota,wata ƴar india ce tayi na ɗaya,saidai yafi babu,dama kawai fitarce ta ja hankalina,bani akayi niyyar turawa ba ma,Abinga nayi naje a madadinta,bayan na kalallameta"
"Kai khamriyyah,kefa indai a wajen kutsene ki zama akan gaba bakida sauƙi kwata kwata"
"Innnnoooo banganki ba,shine ko kimin sannu da dawowa ko inno"
"Saboda nina turaki kije,ko kin faɗamin kika tsallaka kika tafi?"
"Haba inno har yanzu baki huce na,nima na huce bareke,kema fah Garinku kika tafi bansani ba ina makaranta,sai dawowa nayi banganki ba,haka na haƙura shine.....
"
"Naji toh,mai bakin tsiyah karki tona min asiri,yanzu ya hanya,amma karki ƙara irin haka nan gaba.
Ku dunga tunawa ba zaman kanku kuke ba"
"Naji inno bazan ƙaraba daga wannan,ina kin huce koh?"
"Ya zanyi toh in ban huce ba,Allah ya kiyaye gaba"
Yanda sabrah ta faɗa tayi,wato tayi wanka tayi kwanciyarta abinta hankalinta kwance,kaman ba itace ta tafi tabar bayada ƙuraba.
Washagari da safe su sabrah suna jiranta ta fito su ci abinci,sai ganin ta sukayi ta fito da shirin fita wani waje.
Sabrah ce takasa ajiye mamakinta tareda cewa,
"Ke kuma ina zakije daga dawowa jiya,ko kinyi wata ƙawane bamu sani ba a can"
"Babu wata kawa,Wajen aiki zanje mana,na dade ban gaisa da ogah Sadeeq ba,zanje nafaɗa masa zan koma aiki"
Dukkkansu zaro ido sukayi da abinda tace,saidai ita ko a jikinta,saima zama da tayi a gaban abinci tafara ci.
Harda duba agogo irin mutum ya makara a wajen aikinnan.
Babu wanda yasake cemata ƙala,harta gama cin abinci ta nufi waje.
"Inno ƴan uwa saina dawo"
Toh kawai sukace,daga nan tafita daga gidan zuwa waje.
Motar da aka kawomata a daren jiyan ta kalla tareda jagayata,saida ta tabbatar komai yaji kafin tashiga tayi mata key.
Ko yan gidan basu san an kawo motar ba,dan bata faɗamusu yau za'a kawota ba.
Jan iska tayi tareda figar motar zuwa cikin garin.
Sai kalle kalle take a hanya kaman wanda tayi shekaru bata nan.
Dec. Khaleel ne ya kalli Sadeeq tareda cewa.
"Ni narasa ma yazanyi,yanda nake tunanin abin yafi gaban haka sosai,a yanda ta faɗa dai tace shine aikinta na ƙarshe"
"Amma fah karka manta mahaifiyarka ta nakasa,dole abin da ciwo,duk inda take ma dole za'a kamata,dama ita duk tafisu tantiranci"
Zagin deejah Sadeeq ya cigaba dayi,ta inda yake shiga ba ta nan yake fitaba,wanda hakan daidai yake da sukan da zuciyar khaleel ɗin takeyi gameda zagin
"Ya isa haka Sadeeq,kaima fah matarka harda ita a cikin laifinnan,meyasa ka daina shogo da itane da ahalinta sai Deejah kaɗai"
Mamakine ya kwanta akan fuskarsa sadeeq yana ƙarewa khaleel kallo.
"Anya kuwa kaine ɗan uwa,duk wanda yake zagin yarinyar nan fah a bayanka yake,yaukuma kai ke cewa wani ya daina,kuma ma har wani suna naji ka faɗa,wacece haka,ko sunanta kenan?"
"Ah.....ah ba da ita bane,kawai sunan watane ya shigo cikin maganar ba komai........"
Katsewa yayi da maganar saboda turo ƙofar da khamriyyah tayi zuwa cikin office ɗin,tasha dogon hijabi irinna zamaninnan baƙi har ƙasa,farar fuskarta kewayayyiya ta fito a ciki.
Ga kuma baƙin glass ɗin data saka shima.
"Salamu Alaikum,ko tattaunawar sirri kuke na jira a waje?"
Da mamaki suke kallonta,da alama shi khaleel bai ma fahimci wacece ba,amma kuma ganinta sai ya haifar masa da wata faɗuwar gaba,wacce bai san ta mecece ba.
"Khamriyyah mai kike anan wajen kuma yanzu"
Yafaɗa cikeda mamakin ganinta a garin,kuma ma a cikim office ɗinsa kuma a gabansa,babu alamar tsoro da kuma fargaba.
"Lahh ogah ashe ka ganeni,shine koka ce nazo na zauna,aiki na dawo mana,dama ai ba'a koreni ba,akwai abinda zai kawoni nan har office ɗinnan ba inba Zancen aikiba.
Kasan dai kai surukina ne bare kace soyayya ce ta kawoni koh harka koh?"
Ta karisa magana tareda zama akan kujerar da take gefen khaleel.
Tunda ta shigo wajen take magana harta zauna ta dora jakarta akan cinyarta khaleel yake kallonta.
Ita kuwa ko kuladashi batayi ba,saima surutunta da take da sadeeq wanda ya haɗe fuska yana harararta.
Marairaicewa tasake yi,kaman mai shirin kuka tace
"Habaaa ogah dan allah kayi haƙuri,wlh yanzu ba cutarka na dawo yiba,aiki nazo mucigaba,kuma ma yanzu ai babu abinda baka saniba a kaina,Sannan daga wancan aikin ban ƙara wani ba,dama na gama.
Nasan zaka kamani amma har yanzu bakada shaidar nina keyi,dan haka idan muna aiki nasan zaka nemo yanda zaka kamani,nikuma kafin sannan na ɗanyi aiki,zaman gida babu abinda nake ya isheni.
Beside nasan bazaka kamani ba baka kama matarka ba koh?"
Takaicine da haushi ya ishi sadeeq,ganin yanda ta raina masa hankali a baya,yanzu kuma ta dawo hankalinta kawance tana cewa ta dawo aiki.
"Hmmm sha kuruminki,yanxu banine da alhakin kamaki ba,dec. Khaleel ne keda wannan ragamar,kuma har matar tawa za'a haɗa,kinga kuwa bakida mafita"
Nuna inda dec. Sadeeq ya nuna tayi,wato inda Khaleel yake zaune,ganin tana kallonsa yasa ya turnuƙe fuska tareda juyawa gefe.
"Uhm shima ko shiɗinne inada lokacin,naji ance mission ɗinsa akan mabaraciyah yake ina,sai yafara kamata tukunna kafin yazo ya kamani,kafinnan nidai ku barni na dawo aiki,inkuma ba tsorona bansani ba kuka faraji,bayan kuna shugabannina"
Wani kallo khaleel yayimata,jin wai sai yakama mabaraciyah kafin zai kamata,kaiii kuma dai yasan batasan soyayyar dayake mata ba,tunda a yanda yaji jiya ta duro ƙasar.
Wani ƙayataccen murmushi yayi tareda cewa.
"Ba wanda yake tsoronki v-lady,akan rashin barinki aiki,karkiyi zaton dan ana tsoronkine,batun miƙaki ga hukuma kuma wannan dolene idan lokacin yazo.
Ki dawo aiki gobe,sannan karshen tabbatarwa ma kina ƙarƙashin team ɗina nida dec. Saleem,dan haka ki shiryah ,tayamu kama mabaraciyah,idan kikayi hakan wataƙila kisamu rangwamen laifinki"
Yar dariyah khamriyyah tayi tareda cewa.
"Nagode sir,inshaallah zakaji daɗin aiki dani,kuma zan taimaka muku,badan kuyimin