MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   31 / 33

90K to 93K   out of 96.8K words

samu komai ba sai harara.
"Mayu kawai,kunzo kun damu mutane,banda wari keda uwartaki babu abinda kuke,na kyautarku ya ƙare tin jiyah,ba an faɗamuku ku kawo kuɗiba?"
Kwallah ce ta zubo a idona na kalleta tareda cewa.
"Amma kawunnawa ance an yankashi jiya"
"Toni na yanka shi,bare kice ya rataya a wuyana,kowa yasam waya yankashi ai,mai takaishi yin musu da Brr. Shehu"
Tunowa abinda yafaɗa yayi jiyah,wanda hakan yasa na fita da gudu zuwa gidan br. Shehun.
Samunsa nayi a zauren sa inda mutanen garin suke kallon sa idan zai musu shari'ah,duk da a sannan ƙaramin lauyane,amma kowa yasanshi da yin nasara,koda kuwa kaikayi cutah,indai kabada kuɗi kaine mai nasara.
Tsugunnawa nayi a gabansa tareda haɗe hannuna.
"Dan Allah bawan Allah ka taimaka,kawuna yacemin zai biya kudin aikin,amma kuma ka kasheshi,kai ɗin ka taimaka ma inna ta"
Zaro ido yayi a gaban mutane tareda wanka min mari,ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba,ni sannan bansan hatsarine nace shiya kasheshi ba.
Wani yaronsa ya kallah akan ya kulleni,saida mutanen wajen sukayi ta bashi haƙuri kafin ya barni na fito,lokacin da ƙyar nake ɗaga ƙafa,saboda mugun duka da yaron yayi min.
A hankali nake tafiyah ina kuka na nufo asibitin,saidai kafinna shiga na tsayah cakk ina kallon yanda nurse ɗin suka turo gawar innata akan kekensu,duk wadda ya kalleta bazaiso sakewa ba,saboda haka takoma tamkar horror dan wahalar duniyah.
Kuka na dungayi,a lokacin bansan hakan shiyafi mata ba,bansan tafiyarta yafi halin datake cikiba,ni sannan baƙinciki nake ta tafi ta barni ni ƙadai dani da umar.
Wani abune mai matukar duhu da kauri ya ziyarci cikin raina,haushin abinda iyha gaji tayi mana,haushin rashin zuwan yayinmu dana malam lokacin da muke matuƙar buƙatarsu,sannnan kuma dana abinda brr shehu yayi mana..
Wani aka bawa kura ya turamana gawar har zuwa gida,sai a lokacin dan takaici mutane suka buga waya aka faɗawa yayinmu mai hake faruwa,tunda danayi ta binsu su faɗamusu babu wanda ya faɗa,saida ta mutu tukunna.
Muna zaune nida umar munsakata a gaba,iyah gaji kuma tana ta waƙar gaɗarta tana tankaɗe,liman ɗin anguwarne yashigo yana jera salati da carbi a hannunsa.
Bayan yaga ɗanyen aikin da iyah gaji takeyi,hmmm jinake kamar na soyata a mai mai zafi,dandai banida ikon yin hakannne.
Ƴan anguwane suka shigo aka wanki innah aka yi mata siturah.
Sai bayan an kaita wajen la'asar kafin su yahuza suka shigo gidan,kowa yana kukan rashin dalili.
Ɗauke kaina nayi daga inda suke,in dutse ya kallesu na kallesu,ko tunanin ba laifinsu bane banayi.
Shima malam a lokacin ya shigo gidan,saidai shi sabanin su,yana shigowa gidan ya saki ƙara tareda zubewa a wajen.
Kansa dukka mukayi muna girgizashi,amma ina ya riga ya suma..
Masu karbar gaisuwane maza suka taimaka muka kaishi ɗakin iyah gaji.
Abundai ya taru mana goma da ashirin.
Malam bai tashi ba sai washagarin mutuwar inna tukunna,nan da ihu ya tashi wanda hakan yasa duk muka afka cikin ɗakin.
Shashima gefe da gefe yake yana cewa baya gani.
Mamaki abin ya bamu,amma kuma da gasken cewa yake baya gani.
Karisawa wajensa mukayi muna kallon fuskarsa,amma shi baya kallonmu,duk idonnasa a buɗe suke tarau.
Wata damuwarce tasake ɗoruwa akan wata damuwar,ga waccar ga kuma waccar.
Haka akayi sadakar bakwai na inna,baban har sannnan baya ganin komai,ya koma makaho.
Har sannan kuwa bana kula su yahuza,duk yadda sukayi naƙi fahimtarsu,umar ne dai shi ba ruwansa,amma kuma koba komai iyah gaji ta rage yimana tsiyah sosai,tunda tana bamu abinci.
Da daddare bayan isha mukaji ance wai iya gaji tayi baƙuwa,kuma wai da mota tazo.
Lokacin nikadai ce a gidan,naraka malam banɗaki na dawo dashi yana alwala.
Har zan kwanta saikuma gulma ta hanani,wanda hakan yasa na leƙo..
Wani mutum nagani ya sungumi malam a kafaɗarsa,iyah gaji kuma tayi lullubi tabi bayansu.
Dan kwalina na ɗaura nima nabi bayansu.
A bakin kofah suka haɗu da su umar da kuka yahuza,dama sune manyan.
Tun kafin suyi wata magana suka buge musu ƙeya da wani abu ta bayah.
Tsoro ne ya shigeni,yayinda nake Allah Allah kar yusuf hamza suma su shigo.
Motar dukka suka shiga,amma a hankali take tafiya saboda cikin garine,kuma ga dare.
Binsu nake ina cin gudu har haki nake.
A gidan gonar brr. Shehu naga sun tsaya,wanda yake bayan gari.
Saida nabari dukka sun shige kafin na fito na nufi wajen a hankali.
Da window nake leƙawa,inda naga matar a zaune itada brr. Shehu da kuma iyah gaji,sai kuma wannan nurse ɗin data harareni a asibiti,mamakin ganinta nayi a wajen.
Kuɗi brr. Shehu ya ƙirga masu yawan gaske ya miƙamata.
"Kai brr. Ɗan wannan kuɗin,wancan satin ma fah nayi maka aikin kashe waccar majinya ciyar,wacce itama tana ɗaya daga cikin masu filayennan"
"Hmmm nida akaso a ganeni,ni manta da wannan matar a cikin wanda za'a kashe,saida wani yayanta ya tunamin.
Kuma tazo gidan sauƙi ashe kishiyar gaji ce,wacce itama tashigo cikinmu yanzu"
"Koma dai mennene,jarirai nawa na kawo maka a shekarar nan,amma kuɗin basuda wani kauri"
"Wannan aikin madam Ateeka ne gata nan a zaune,ita zaki tambaya,domin ita ta bani aikin nemo mata su"
Tsawa matar ta daka musu tareda kallon iya gaji.
"Kumin shuru dalla,yawwa ke gaji,ya za'ayi,tun a kano yarona ya biyo mijinki saboda irin idonsa mukeso a aikinmu,Ƙwayar fara fara kaman ta turawa ita mukeso,sannan zamu ɗauki ziciyarsa ma,nawa kike ganin zamu baki? Miliyan ashirin ya isa?"
Wata zabura iyah gaji tayi tareda cewa "miliyan ashirin,wayyo daɗi."
Kallon inda babana yake nayi wanda ake cinikinsa,da kuma su umar wanda ko farfaɗowa basuyi ba..
Ciniki suka cigaba dayi,inda Hajiya Ateeka tace zata bata Milinyan Hamsin harda su Umar ma,nan take kuwa iyah gaji ta amince,har guɗarta.
Wasu yarane sukayi kansa inda yake kwance,sai a sannan nagano ashe makantarsa sune sukayi,damim basaso idon yacigaba da aiki daga ranar.
Wani abu suka sa suka fitar da idanuwansa,yana kwance kaman gawa,hakan bai ishesu ba suka ƙara ciro zuciyarsa ma.
Jini ne yafara malala a wajen,nikam kasa cigaba nayi da kallah,idanuwansu dukka na kallah kafiran,amma babu wanda yayi ko gezau,kowa acikinsu lokacin duniyace a ransa.
Barin bakin windown nayi jikina yana layi,har zan tafi sai kuma na tuna da su umar,idan suka tafi dasu ina zasu kaisu,buɗe bayan mota ɗaya nayi na shige ina cigaba da sheshshekar kuka na rashin iyayena a cikin sati guda.
Baccine ya ɗaukeni a haka,ban buɗe idona na sai ji nayi an ɗagani sama.
Waresu nayi a wani waje mai tsayin katangu sosai.
Wajen bayyi kama da gidajen mutane ba.
Mazane a wajen,wasu yara wasu kuma kaman yayuna,dukkansu basuda wando tsirara suke.
Saurin rufe idona nayi tareda son farkawa daga mafarkin danakeyi,saidai kuma duk yanda nayi da kin amsar hakn abin ya faskara,muryoyinsu sun ƙi barin kunnena.
Wani ƙaton mutumne dagashi sai gajeren wando ya nufo inda muke.
"Mai kuma wannan jinsin yake a cikin wajennan,kunfi kowa sanin rashin sa'ane wannan ƙazamin naman ya shigo nan wajen koh?"
"Kayi hakuri dumumu,bamusan tana wajen ba,a mota muka ganta a kwance.
Mu fitar da ita ko kuw"
"Ahah ku fara sanar da ateeka tukunna ko ita tazo da itah,kar a sake irin kuskuren baya,kunsan bata da daɗi"
Nidai ina jinsu amma ban bude idona ba,dan banason sake ganin abinda na kallah.
Wani ɗaki aka kaini mai duhu marar daɗin gani.
Jefani sukayi a aciki tareda yimin barka da zuwa gidan jini.
Bangane mai suke nufi ba,burina na fita a wajen na nemo su umar,dan dama dominsu nazo,nakasa ganin wautata takasa taimakonsu a wajen.
Jijjiga bakin ƙofar nake ina ƙara,amma babu wanda ya kulani a masu wucewa ta wajen.
Sai wajen yammane kafin wani yazo ya bude inda nake ciki,fincikata yayi da ƙarfi yafara jana a kan sumuntin wajen,na tabbatar fatar ɗuwawuna ta daye.
Wani ɗaki muka shiga mai matuƙar kyau da gwalagwalai,tamkar mutum ba a duniyah yake ba.
Wannan matar data siyah su babana idona yayi tozali da ita,tana zaune akan kujerar zinare,gefenta kuma wasu kwanuka ne a rufe.
"Hhhhhh yarinya kenan,kema ganan idonki yana kamada na ubanki,rashin sa'ar ɗayah naki jikin mace yake,kashe mace a gidannan ya sabawa dokar mu,amma da tuni naki ma yana jin nan wajen kamanna ubanki"
Ta ƙarisa maganar tana buɗe kwanon,idone guda biyu da zuciya an yi farfesunsu,kuma wai na ubana.
Wani amai ne mai tashin zuciya yazo min,bansan lokacin dana fara kakarinsa ba.
Ɗagowa idona nayi a karo na biyu,daidai lokacin data kai yankan zuciyar bakinta ta tauna.
Juuuuu naji kaina yafara juyawa,sai duhu dayamin sallama.
Buɗe idona nayi naganni a ɗakin da aka kwantar dani ɗazu,saidai kaman safiyah nasake ganin garin,kenan kwana na guda ina bacci a wajen.
Ƙoƙartawa nayi na tashi,hannuna sai karkarwa yake saboda tsananin yunwa.
Kwanon abinci nagani a rufe a gefena.
Saidai ko marmarin budeshi banyi ba,saboda ganin nake idan na buɗe idanuwannan zan gani da zuciya wanda matar takeci.
Maganar ta karshe na tuna kafin na suma wanda take cewa wai.....tayi nasara takai matakin ƙarshe,dasamu babbar dama akan akwatin sirrinta,yanzu itama kuɗadenta zasu fara hauwa ba adadi.....
Kenan dan tayi kuɗin ta cinyemin ubana? Ga ƴan uwana ma har yanzu ban gansu ba.
Kuka na fara tun ina marar sauti har na ɗaga muryah,tsawa masu wajen suke ta dakamin amma ko a jikina,na ma daina tsoronsu yanzu ni.
Wani ne a cikinsu yashigo ya min duka kaman yasamu babbar mata,lokacin ban fi shekara sha ɗaya ba.
Akwance nake ko motsin kirki banayi sai nishi,wani ne yazo yaƙara daukata zuwa wannan ɗakin na jiya..
Saidai yau ba ita kaɗai bace,akwai manyan mutane dayawa a wajen,masu muƙami da faɗa a ji a kasar nan.
Dukkansu jajayen kayane a jikinsu,ita kuma uwar gayyar nata kayan baki itada wasu maza uku,da alama sune manya.suna tacin nama da wani jan abu a kofi,wanda na tabbatar jini ne naman kuma na mutane.
Sunkuyar da kaina nayi bayan na kallesu sau ɗaya.
Tsawa wani babban acikinsu ya dakawa masu kawonin
"Bakuda hankali ne zaku ajiye mace a cikin gidannan,kuma ma ku kawota nan wajen,indai ba member ba rashin sa'a ne mace tazo nan wajen.
Maza ku fita da ita gada gidannan,sannan ku kasheta,ku tabbatar batayi rai ba.
Amsa wa sukayi da angama kafin suka figeni zuwa waje.
Kallon karshe nayiwa yan wajen,idona ya sauka akan matar da banida buri daya wuce naga nata idanun itama akan hannuna,zuciyata ta taure,banajin tsoron kashenin da zasuyi,abinda nake takaici shine zan mutu itakuma tana duniyar hankalinta kwance.
Rufemin ido sukayi da wani bakin ƙyalle kafin suka sakani a cikin wata mota.
Inajin muna tafiya amma kuma gudun sai kace bana motaba,kaman muna jirgi,nasan bai wuce saboda tsafinsu ba.
Fitodani sukayi daga motar tareda ciremin abinda yake idonnawa.
Waresu nayi akan wani kungurmin jeji mai ban tsoro,ko inane wajen oho su suka sani,nidai jira kawai nake naji sun yankani,nima nabi iyayena da yan uwana.
"Kai dallah yi sauri ka kawo igiyar,lanƙayeta zamuyi a jikin bishiyar nan muna kallonta harsai ta daina motsi tukunna"
"Ahah yankata zamuyi yanda shugaba ya faɗa"
Musu suka fara nidai ina zaune ina kallonsu,dan ko ɗaga ido ma da ƙyar nake,bare kuma nayi koƙarin yin wani abu
Ji nayi sunyi shuru da musu kamar ruwa ya cinyesu,ina juyowa na gansu a kwance sun fara bacci,mama ki abin yabani,kafin nayi magana naga wani mutum a ya bullo daga gefena,bashida riga,daga shi sai wani jan wando na fata.
Kallonsa nake da alamar shakku,da alama akwai wani abu tattare dashi.
Rigar jikina ya kama zai cire na riƙe ina kallonsa,ba abinda na wasa kaman cin zarafi.
Wata rigar ya miƙomin mai datti akan nasaka na bashi tawa.
"Ki saka wannan kibani taki,san saka mata jini ne na ajiyemusu,suga kaman sun kasheki"
Karbar ta hannunnasa nayi tareda yin yadda yace.
Bayan yagama shamata jinin wani kurege daya kashe,sai ja hannuna muka fara tafiyah.
Baicemin komai ba nima ban cemasa ba,abubuwan dayake a hanyar suna bani mamaki.
Munyi tafiya mak nisa kafin naga yaja ya tsayah yana kallona.
"Kibi tanan kiyi ta tafiyah zaikai ki jejin mutane,karki juyo idan kina tafiyah,kin sam meyasa na taimakeki?"
Jijjaga masa kai nayi,dan har raina bansani ɗin ba.
"Jiya da daddare naji kina karanta abin musulmannan,sai naga wani haske ya rufeki,yahana tsafin Doƙoji dabaki,da tuni jiyah ya juyarda ra'ayinki kinshiga ƙungiyarsu,saboda kalar idonki alamar nasarace a wajensu"
"Uhhh Qur'ani kake nufi? Addu'ar bacci inaga nayi ,dan nayi mafarki malam ɗalha yana cemin banyi addu' a ba na kwanta"
"Eh ita,hakan dana gani yasa naji kin burgeni,bai kamata ki mutu a haka ba,ni zan koma ,idan kin tsira kice wanda kuke bautawa inason addininsa"
Har yajuya zai tafi na tsaidashi tareda cewa.
"To amma meyasa bazaka taho mu tafi ba tare?"
"Niba mutum bane yarinyah,ni ɗayane daga cikin yaran dasuke ƙira da dodo,mune muke ɗaukar jinin dasuke kawowa mu kaiwa sarkinmu dayake ƙasan teku,shikuma sai ya basu sa'a,bazan iya barin jejinnanba saboda ina ɗaure da sarƙa,konaso tafiyah bazayyiyiu ba"
Tsorone yakamani jin abinda ya fada,saikuma natuna ya taimakeni,watakila bashida niyyar cutarwa.
"Amm ba kace haske yazagayeni ba jiya,mai zai hana ka karbi addini kaima ka karanta,wataƙila sai sarƙar ta sunceka"
Juyowa yayi ya kalleni tareda cewa

"Zaki iya koyamin abin a nan wajen,tayaya ake koyawa"
Murmushi nayi tareda karanta kalamr shahada shima yana karantawa,bayan mungama saina fara karanta ayatul kursiyyu yana bin bakina,jikinsa ne yafara karkarwa amma kuma bai daina faɗa ba,ganin abin yanacin ƙarfinsa ne yasa naja hannunsa da sauri muka fito daga inda yace baya ƙetarawa.
Kamar abin tsafi kuwa sai jikinsa koma yanda yake,haki yafara yana kallon inda bai taba tunani a rayuwarsa zai bar wajen ba..
Zubewa yayi a gabana yace.
"Daga yau naza ma bawanki,ki umarceni duk abinda kikeso"
Saurin jada baya nayi tareda girgiza masa kai.
"Kalmar daka faɗa ka zama musulmi,daga yau kada ka sake durkusawa kowa bayan Allah mahaliccinka,nikuma babu abinda nakeso daga gareka,nagode ma da taimakona dakayi"
Tashi yayi ya tsayah yana mamakin abinda nace,wai bana buƙatar taimako.
"Eh bana buƙatar taimakonka,kaine kake buƙatar taimako nasanin addininka,saidai ni bazan iya yikamaka ba,tunda nima ban sani ba,kashiga duniyah neman ilimi tunda kana da iko"
Ɗagamin kai yayi,.
"Naji abinda kikace,hakiƙa sai yanzu nasan wannan shine addinin gaskiya,ba shan jini da yanka mitane na,baki faɗamin sunanki ba"
"Sunana khadija,zaka iyah cemin deejah"
"Hmmm nikuma sunana Tuddoor,amma yanzu nazama sumail,sunan wani aboki danayi a wajen,aka yankashi a gabana,shine wanda yafara bani labarin addinai da kuma yanda suke"
"Uhm ya kyauta,saikayi tayi masa addu'a"
Tafiyah mukaci gaba dayi tareda shi a cikin jejin,dan yace bazai tafi yanzu ba,baisan kowaba.








Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.








*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)






63••64



Bansan kwana biyu, uku,sati,watanni mukayi muna rayuwa dagani sai sumail ba.
Nidai kawai abinda na sani shine muna kwana mu tashi,munemi abinda zamuci na ƴaƴan itatuwa,na koya masa sallah muyi,in labari yazo na bashi,shima kuma yabani labarai wanda hankali baya ɗauka.
Saidai yau da kullum na fara ganin abubuwan dayake faɗamin normal.
Bayan tsawon lokacin da muka ɗauka a jejin ranar saina ga garin mutane,abin yabani mamaki,a raina ina ganin kaman bamu daɗe da barin wajennan ba,amma kuma jikina yana nuna mun daɗe a wajen.
"Sumail satinmu nawa a cikin jejinnnan?"
"Hhhhh me kikaga kike tambaya"
"Uhm naga mutanenncan shuka sukeyi,kuma lokacin da aka ɗaukeni a gidan kuma an girbe amfanin gona,mai yake faruwa"
"Watanmi goma sha ɗaya a cikin jejinnan,saboda wani lokacin idan mun zauna muna yin wata biyu,zama dani ne yasa ganin tafiyar lokacinki yazama kaman nawa.
Kiyi haƙuri kaman yanda kika faɗa ni yanxu zan tafi,kije ga mutane ƴan uwanki kiyi rayuwa dasu,ta hakane zaki iyah ɗaukar fansar dakike so,idan na samu wanda zanyi karatu a wajensa watarana zan zo nemanki"
Yana gama faɗin hakan ya bacewa ganina,duk da zaman mu dashi inajin wani iri,amma kuma nasaba dashi sosai,yanda yake samomin abinci da tsarona innayi bacci.
Juyawa nayi nafara takawa zuwa inda masu gonar suke.
Suna ɗagowa dasuka kalleni suka furma da gudu,banyi mamaki ba nasan bai wuce shigar jikina ba,ɗayane daga cikinsu ya yi jarumtar tsayawa,magana yayi min amma haka kawai na tsinci kaina da ƙin amsa masa
Ganin yayi yayi naƙi amsawa yasa ya ce nabiyoshi. Tafiya muke har muka iso gidan marayun dana rayu a ciki.
Banyi zaton zan samu mutane dazasu taimakeni ba saida na haɗu inno dakuma sauran ƴan uwana na wajen.
Tun ranar da aka kawoni sabriyya ta shiga raina,saboda yanda tajani a jikinta sosai.
Tambayata tayi sunana,saidai kafin na buɗe bakina na furta mata naji ta ambaceni da sunan KHAMRIYYAH,da farko naso cemata ba sunana haka ba,saidai yanda yaran wajen suke ta dariyah suna maimaita sunan akan bakinsu yasa nayanke hukuncin zama dasu a matsayin wacce suka sakawa suna.
Na yi alƙawarin duk abinda yashafi deeja na baƙinciki bazan bari ya shafi rayuwarsu ba,zan zauna tareda su a matsayin khmariyyah ƴar uwarsu,wacce batasan kowo ba sai su,sannam mai burin sadaukar da komai nata domin ƴan uwanta.
Haka nacigaba da rayuwa tareda mahaifiyar dana samu dakuma yan uwana danayi,har zuwa lokacin da masu ɗaukar yara suka zo na tafi a madadin sabriyyah.
Mutanen da suka ɗaukeni irin wanda suka ɗauki maryam ne,wato masu niyyar kasheni,na zauna a wajensu tsawon wata shida a wani ɗaki tareda wasu yara,sune su biggy.
A wannnan wata shidane Allah yabani iko na samo hanya muka gudu,kafin nan kuma na samu information dayawa a wajen.
Anan na gano Dr. Bukar da brr. Shehu da kuma saifuddeen sunada Alaƙa da wajen.
Saboda koyaushe a gidan suke meeting ɗin mugayen abubuwansu.
A duk lokacin dana kalli brr. Shehu a gidan ji nake kaman na kasheshi,dan sannan bansan sauran mutanen ba,kawai dai nasan saifuddeeen shiyake tura iyayen bogi su ɗauko yara a gidan marayu,ya sayarwa dr. Bukar ya cire ƙodar su,shikuma brr. Shehu ya tsaya musu ta wajen masu son yin ƙara da wasu abubuwan.
Mutane uku kawai nayi nasara guduwa dasu,sune su biggy,sauran kam muna gani suka maida su gidan,suna kuka ina kuka haka muka barsu a ciki muka tafi.
Cikin garin katsina muka shiga bamu san kowa ba,sai muka fara neman hanyar abinci,wankau muke a gidaje dasauran abubuwa,wani lokacin musamu aiki,wani lokacin kuma bama samu.
Ganin nima ga rayuwata yanda take,kuma ina ƙoƙarin jawo wasu cikin ta.
Shawara na basu akan su je gidan marayu na garin,daga nan muka rabu dasu nikuma nacigaba da rayuwata,gefe kuma ina bin diddigin mutane da duk na gani a wannan baƙin gidan.
Ina cikin hakane wata rana nashiga tsangayar Almajirai,babu tsammani saina haɗu da yah shazali,yazo shida iyalansa da kuma almajiransa.
Mamakin ganina yayi,musamman yanda nayi daƙa daƙa ga datti ga kuma yagaggun kayah,wasu ma ko ban tambaye su neman taimako ba ɗauka suke su bani.
Sakani yayi a gaba na bashi labarin abinda ya faru,nan yake bani labarin iyah gaji tayi kuɗi sosai a garin kankia kafin ya taho,shikuma brr. Shehu anyi masa transfer shida wannan nurse ɗin zuwa garinnan.
Banyi mamakin abinda ya faɗa ba,dannasan bazai wuce aikin wannan matar ba,data ruguzamin rayuwa,saboda buƙatar duniyarta.
Duk yanda naso ƙin ɗora masa nauyin rayuwata,kasa barina yayi na tafi.
Karatu na cigaba dayi a wajensa na addini da kuma na boko,dan burina danake dashi bazayyi yiyu ba saida ilimi.
Bayan

31 / 33