MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   7 / 33

18K to 21K   out of 96.8K words

wanann mutanen har sai nasamu cikar burina,ina matuƙar godiyah da kulawarka da kuma kyautatawarka a gareni,ina roƙon ka yafemin laifin danayi maka a zamana da kai"
Saboda maganganun ta sun kashe masa jiki kasa magana yayi,sai ɗaga kai kawai dayayi mata,alamar yaji abinda tace.
Sassafe taje gidan su yadiko lami ɗin,saboda karta tafi ta barta.
Tasha suka nufah tana tafe tana binta a baya har suka shiga motar katsinan aka hau hanya,Allah ya tsare hanya.

*_____*____*______*

Yanda khairyyah ta bar dec. Sadeeq a zaune a wajen ya ɗade bai motsaba,sai can wajen awa ɗayah yaka ƙafafunsa ya fito a wajen,ba ta zancen khairiyyah yake ba wacce ta gudu,inma yakamata yanzu toh mai zaice?...yakam ƴan biyun matarsa wacce take aikata laifi?...bai kama kuma matar tasa ba tana gida?...bayan itace ta biyu ma a shigabancin yin hakan?.
Wannan lamarin kwata kwata bai yi ma'ana ba.
Bai kula kowa ba sanda yafito a wajen,suma kansu masu tayashi aikin sun rasa ƙwarin gwiwar dakatar da khariyyah daga fita a wajen,matar ogah ce shugaba kuma wayake ta ƙarama kuma.
Hanyar wajen motarsa ya nufah ya buɗe ya shiga.
Ikon Allah ne kaɗai da karewarsa ya kaishi gidannasa lafiyah.
Tun daga bakin ƙofar babu kowa shuru.
Taka carfet ɗin bakin falon yayi,mai makon hakan yasaka shi nishaɗi kaman kullum idan ya dawo ya tunada wacce zayyi arba,sai ya zamo kuma yau hakan ya juye zuwa fargaba da zullumi da abinda zai tarar.
Bayyi magana ba duk da ƙwaƙwalwarsa tana matuƙar bukatar hakan,amma yazayyi da bakin wanda yagagara buɗewa bare ya furta komai.
Kitchen yafata leƙawa babu kowa sannan ya ƙarisa ɗakin kwanansu,nan ma babu kowa,bai gazaba ya leƙa banɗaki nan ma babu kowa,fitowa yayi yana ƙarewa ɗakin kallo.
Nan idonsa ya sauƙa kan wata takarda da wani littafi a kan table ɗin gefen gado..
Ƙarisawa wajen yayi ya ɗauki paper.

......Assalamu alaikum aminci ya tabbata a gareka mijina,nasan zakayi mamakin rashin ganina bayan ka dawo gida.
Bazan iyah jurar jin kalmar saki daga gareka ba idan kazo ka taddani,tabbas da farko na aurekane don samun bayanai da kuma wani abu,amma kuma daga baya na faɗa kogin sonka a zahiri,wanda hakan yasa bazan fuskanceka ba har sai a karanta wanann littafin,anan zaka san tarihinmu da kuma dalilinmu na yin wanann aikin.
Karka tambayeni labarin mabaraciyah wanann bansan nufinta ba sannan ba tare muke aiki ba.

Daga matarka Sabriyyah(Amrah)


Ajiye takardar yayi hannunsa yana rawa kafin ya buɗe littafin,da alama kundin tarihine na rayurwata ta ajiye masa ya karanta,duk da bashida ƙarfin yin wani karatu sannan amma kuma yana buƙatar hujjah.
Da hotonsu yaci karo a farkon shafi su huɗu,khamriyyah,khairiyyah, sabriyyah,sai kuma wata buduwa a tsakiyarsu,bazasu wuce shekaru goma ba a lokacin,kawacce fuskarta ɗauke da murmushi,sannan basu san mai duniyar take cikiba.
Shafin gaba ya buɗe kafin yafara karantawa..................
KASH.......anan fah na batinku ya ƙare my loves.
Nasan kuna ɗauke da sinƙi sinƙin tambayoyi?

#Mai dec. Sadeeq zai karanta a littafin sabriyyah,anyah kuwa abinda zai gani zai isah ya gamsar dashi yafasa kamata,uwa uba kuma ga ƙaramin cikinsa a jikinta,wamda yake nema ruwa a jallo ya haɗa jini dasu?

#shin anyah kuwa khamriyyah ƙarin karatun ta tafi?

# ya aikin da deejah(mabaraciyah )zata gudanar a cikin gidan sarautar katsina,zatayi nasara kuwa kokuma rishene zai juye da mujiyah?

#Mabaraciyah da V-lady mutanene mabanbanta masu aƙida guda ɗayah,kowacce burin shine ɗaukar fansa,tukunna ma fansar menene da dole sai an kashe kaso mai tsoka na manyan gari?
# a yayinda suka gama ɗaukar fansar shari'ah kuma da take jiransu a madakata zata ƙyalesu kuwa?.

#Menene dalilin dayasa ta kirayi kanta mabaraciyah??????........

Dukkan wanann amsoshi suna nan a ɗaure tamau a cikin manhajar AREWABOOKS,naira 10 goma zaka dunga sakawa kana suncesu da kaɗan kaɗan .

Kar a manta da follow da bada haɗin kai please.

Taku
_sadi-sakhan_
Ƴar mutan jama'are.







*(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)*

*MABARACIYAH*
(mai harshen damo)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιε.


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)



Paid book #400
3131951977
Auwal sadiya
First bank

Mai turo kati kuma ta wanann number MTN
09035784150

Mutanen niger su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15

Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.

_____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁‍♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃





11••12



____Garin daurah a shakerar 2008_____

Garin daurah garine ba wani babba sosai ba,amma kuma kowa dayake anihin cikyakykyen ɗan arewancin nigeriya to kuwa yasan labarin garin daurah da kuma irin tarihin daya ƙunsa a ciki.
Kama daga tarihi harda tarihihi yazo mana da yawa wanda garin daurah ya shiga ciki.
Duk kasancewarsa ba wani gari ne babba na azo a ganiba,amma garine da'ake cewa,Jinka yafi ganinka.
Akwai gidaje dayawa kana da iyalai da yawa a garin,zaka samu wanann ya haɗu da wannan,wanann ma ya haɗu da wannan,saidai mu bama ɗayah daga cikin wanann ahali na garin,duk da muhallin mu yana cikin wannan gari amma kuma babu tabbacin muɗin ɗayah ne daga cikinsu.
Dan mu tamkar tsuntsayen dasuka nemi alfarmar zama a shiƙar wasune saboda basuda iko da kuma ƙarfin yin tasu shiƙar,koda sunyi ma su ba ɗayane daga cikin su ba,saidai su rungumi iyah kansu,amma fah su barene a wannan wajen.
Mai karatu bazaka fahimta ba koh,saboda nasaka ka a duhu,kayi haƙuri yanayin rubutunne yazo da haka.
A taƙaice dai ba tareda zagayen ɗan wake ba danake dakai a cikin kwano,sunana Sabriyyah,na tashi na buɗi ido banida kowa banida wanda zangani a matsayin jinina sai ƴar uwata khairiyyah wacce muka zo duniyah tareda itah,amma inji wanda suka tsince mune suka tabbatar da hakan,dan ba uwace garemu ta bamu labarin yanda muka shigo duniya ba,uwar muce ta biyu data rainemu ta bamu wannan labarin.
Dukkan gidan marayun na garin daurah haka yake cikeda tarin yara kala kala,wasu sunsan iyayensu guduwa sukayi suka barsu,wasu kuma 'bata sukayi shikenan aka kawosu nan,wasu kuma iyayensu ne suka haifesu bata hanyar aureba dan tsoron kunyar bazasu iyah fuskantar duniya suna tareda su ba suka kawo sunnan,ko kuma suka ajiye a inda za'a gani a kawosu wajen.
Sai kuma rukuni irinna mu,wanda zai iya fin kowanne muni kuma zai iyah fin kowanne kyau,shine an kama wata mata ta ajiye mu a wajen da zamu iyah a hallaka a tsakanin kowacce daƙiƙi kuwa.
Masu tsaron dare sun bita lokacin da suka ga ta zefa mu a cikin ruwa amma kuma basuyi nasaraba,nasarar ɗayace da sukayi nasarar fito damu daga cikin kogin,kana ganinmu kasan sabuwar haihuwa dan ko cibiyarmu ba'a rababa muna haɗe da juna nida khairiyyah.
Shin itace mahaifiyarmu,in kuwa itace ta kawomu duniyah to tafi kowacce uwa tantiranci,wace uwace zata iyah kashe ƴaƴan ta har guda biyu.
In kuwa ba ita ta haifemu ba to aiki aka bata na kashemu,kokuma ita tayi hakan dan wani kuɗirinta.
Inkuwa hakane to duk wanda yayi hakan ba son mu a raye,da akwai lauje cikin naɗi gameda wannan abin!!...
Babu abinda muke sai kuka,dan shikaɗai ne abinda allah yabami ikon yinsa a lokacin,gidan marayu na garin daurah aka kaimu,dan a lokacin shine waje mafi kusada inda aka tsince mu.
Allah sarki uwar kirki jarumar uwa kuma jajirtacciyar uwa,wato uwar marayun gidan INNO,ta raini yara batasan adadinsu ba tsawon rayuwartah,tun tana da shekara talatin da mijinta ya rasu,ta fara aikin rainon yara marayu marasa galihu,duk da cewar bata ta'ba haihuwa ba amma kuma a sanina babu wanda ya kaita yawan yara da kuma wanda take ƙira a matsayin nata.
Muma muna daga cikin rukuninta,shiyasa rayuwa tazo mana da sauƙi,ba kaman wanda suke sashen HAJJAH ba,hantara da ƙyara ma ya ishi mutum,kullum cikin masifah take da kuma cewa ita tagaji,musamman idan akace ba'a biyasu albashi ba,sannan zakaji masifarta sosai.
Saidai duk da hakan tanada halin kirki,wanda yashiga yafita a lokacin to babh abinda zai faɗa sai rashin kirkinta,amma mu da muka tashi a gabanta munfi kowa sanin halinta,tanada tausayi sanann tana son mu sosai,matsalarta ɗayah bata son wasa irinna su Inno da kuma MAMAN YARA ,yanzu zakasha sanda idan ka kawomata wargi.
Mukuma yara gagararru na gidan da muka ga haka sai yawancin wasan mu da tsokanar mu ta koma kanta.
Dan dama sune abokan wasan mu ,a takaice dai iyaye kuma kakanni,saboda su debe mana kewa da kuma shaƙuwa ta iyaye da bamu samu ba.
Inno itace ta shayar damu da madara,wanda gwamnati take bayarwa,duk da kunsan yanayin tsari na gwamanatinmu,idan ba'a kawo ba da kuɗinta take siya mana.
A lokacin ita kuma Hajjah tana rainon Maryam da kuma shukurah.
Saikuma Maman yarah tana rainon yara huɗu lokaci ɗaya,ciki harda Zaharaddeen da kuma faridah.
Kasancewar kanmu ɗayah sai muka tashi tare kusan mu tarah.
Rashin ji da kuma neman magana ba zancensa,dan inkaji gidan yayi shuru to fah bacci mukayi,inkuwa aka ce safiyah tayi toh bazaka sakejin shuru ba,musamamn idan muka saka Hajjah a gaba,tana binmu muna gudu,sauran suyi ta mana dariyah.
Anty shamsiyyah ce ma da anty juwairah suke hanamu,ita anty shamsiyyah ƴar ɗakin mu ce wajen inno,anty juwairah kuwa ƴar ɗakin hajjah ce,.
Allah baya haɗa biyu,ita anty shamsiyyah faɗane da itah,ita kuma anty juwairah sanyi ne da ita kaman ƙanƙara,idan hajja tana fadanta sai dai tayi shuru,gasu su ƙadaine a lokacin sukayi saura a manya a gidan,dan anyi auren sauran sa'anninsu,mazan kuma sun tafi bayan an basu sana'a,wasu kuma sun gudu neman kuɗi,yayinda wasu kuma aka ɗaukesu,
Duk da cewa kowannne yaro burinsa a ɗaukeshi,sanann ana masa murna idan ya samu hakan,nikuma na tsani a ɗaukeni ko kuma wasu daga cikin ƙawayena,ita kanta inno bata son a ɗaukemu nida khairiyyah,dan tafi ji damu akan duk yaran data ta'a riƙewa,saidai babu yanda zamuyi idan aka tafi da sauran,saidai muyi kukan lokacin daga baya mu manta.
Duk da mun taso gida ɗayah da yawanmu,kuma ba jini ɗaya ba,saidai kuma akwai tarbiyyar da su inno suke koya mana na haɗin kai da kuma rungumar junanmu.
Shekarun anty juwairah a lokacin baifi sha biyar ba amma su suke mana wanki,kitso da kuma sauran kana nan abubuwa,musamman anty juwairah a akwaita da jan yaro a jiki,shiyasa muka saba da itah sosai,muke ganinta tamkar ƴar uwarmu ta jini.
Shekarar mu biyar inno tace a kaimu makaranta mufara karatun boko,da kuma na arabi,dan a halin da muke ciki shine gatan mu bayan allah.
Makarantar babu nisa sosai dan haka da ƙafa muke zuwa muna dawowa,a hanya kullum sai ansha faɗa hadda fasa baki,wani lokacin a tsakanin mu idan muka nufo hanyar gida,wani lokacin kuma da sauran yara ƴah makarantarmu.
Yau ma kamar kullum an tasomu ƙarfe shabiyu,saboda yanzu mun shiga aji ɗaya na primary,su fareedah tun dazu suka tafi gida,su suna nursery three,,
Nida deenne muka shawo kwana muna dariyah,yayinda maryam da khairyyah suke binmu a baya suna kuka sai sun rama dukan da mukayi musu.
"Karka bari su kamaka su rama irinna jiyah,dan nakula maryam tana gudu sosai,amma waccan kam lusarar baya ce"
Nafaɗa ina nuna khairiyyah wacce take can baya.
Ita maryam ba sosai take kuka ba,amma khairyyah kam...sakaliyar inno kakeji,komai kuka zatayi wani inya gani sai yace nafita da shekara guda ba mintuna kaɗan ba,saboda yanda take sakaliyah ga son jiki,kuma ma da ƙarin taimakon inno,dan tafiji da ita fiyeda ni,in an jimu da itah toh tsokanar khairyyah nayi kokuma na ƙwace mata abun wasa.
Binmu suke a bayah,takalminsu a hannu,khairiyyah kam hijabinta ma a hannu yake da jakarta.
"Wlh sabrah idan baki tsaya na rama ba saina faɗawa inno"
"Yeeee ki faɗa ɗin,iyakaci tace bazan bita ƙyauye ba,naji ɗin saina zauna a wajen anty juwairah"
Na faɗa ina dariyah tareda yimata gwalo,hakanne yasake ƙularta ta fashe da kukan dayafi na da ma yawa.
Nikuwa abinka da yaro daɗi naji nasaka ta kuka,a haka muke tafiyah har muka shiga gida.
Ban nufi shashenmu ba sai nabi deen shashen maman yara,dannasan bazata bari inno tamin komai ba,ita kuwa da gudu ta shige ɗaki tana bubbuga ƙafa tareda jefar da jakar a ƙasa.
"Innnnoooooo"
Daga ɗakin madafah take jiyo ƙiran da khairiyyah takeyi mata,wanda hakan yasa ta fito tana cewa
"Miyene khairin inno,yau kuma keda suwaye"
"Ba....ba sabrah bace tah ta lakata min yawu kuma ta dukani a bayah ba lokacin da muka fito a aji,kuma nace ta tsayah na rama taƙi,danace zan faɗamiki sai tace ki faɗa ɗin wai"
Kama baki inno tayi da ludayin miyah a hannunta tana ta'ba girkin da masu yin abincin sukeyi,
"Kai kai wannan yarinyah,nasan yanzu haka tayi ɗakin maman yara,ƙyaleta kinji ƴar inno zan kamata,ina nan zatazo neman kunu ai bazan bataba ke zaki shanye dukka"
Wata dariyah khairiyyah tayi jin za'a bata tashanye itah kaɗai babu ni,nikuwa ina jinsu a bayan labulen maman yara ina leƙowa"
Ganin inno ta koma ɗakin abincinne yasa na lalla'ba na shiga ɗakin domin cire kayana,deen sai dariyah yakemin wai za'a dukani.
Abinka da yaro ashe tana kallona na shige ɗakin,musamman da taji muna faɗan kayan da muka cire,khairiyyah tana cewa nata ne,nima ina cewa shina cire.
Jijjiga kai tayi tasaka dariyah,hakan shikaɗaine farincikinta daya zaunar da itah a gidan,bata samu na jinin ta ba amma kuma tasamu na sauran mutane dasuka kasa riƙewa,itakuma ta zauna ta riƙe da zuciya ɗayah.
Muna cikin faɗan kayanne inno ta shigo ɗakin,ina kallon ta na zaburah zan gudu ta riƙeni tareda cewa
"Ina zakije kuma,wato zakiyi wanann ficewar taki sai la'asar ki dawo ko,inna ƙara gani kinyi wani abu kin bar gida zaki ƙwala,mai rashin ji kawai,bakida aiki zai zaluntar ƴar uwarki,maza ku wuce ku tafi wajen cin abinci an fara ci,idan kuma kuka tsayah faɗa aka cinye yau bazan baku nawa ba,kunun ma sai naƙi damawa"
Da sakina tayi data gama faɗan ta shige ɗakinta,dan dama kowacce akwai ɗakuna a shashenta wanda yaran wajenta zasu na kwana,kumbura baki nayi tareda zangawa khairiyyah harara,saidai kuma bazan sake nayi gangancin dazata fada yin kunun ba,dan daga abincin rana banacin tuwon dare,shi nake yini ina sha,gwara ma khairiyyah tafini cin abinci,duk da wani lokacin ɗayane.
Dan idan nayi wa inno tsiyah dayawa bata dama kunun sai dare,duk da ita nake sakawa a gaba nayi ta kuka,amma kuma nima yunwa tana isa ta.
Fita mukayi daga ɗakin zuwa wajen da muke cin abincin.
Wasu irin manyan faranti ne ,maza a nasu daban mata ma a nasu daban,a cewar dokar gidan ta hakane zamuyi zimunci idan kowa yana cin yawun kowa.
Shiga wajen mukayi a kallah su kusa goma shabiyar,kowa ya kama cin abincin,layin kawanann mu mukaje inda su maryam da farida suke zaune,dariya ta na matse lokacin dana kula da kallon da maryam takemin,ita kuma fareedah ko a jikinta sai loma take,dama duk da fimu cin abinci,duk da ita a haife dama mun fita da kusan shekara biyu.
Kallon fareedan nayi wanda ni lomata ɗaya ma a cikin abincin.
"Fareeda ki daina cika bakinnan naki kaman bazaki ƙoshiba,rumbu kawai"
Murguɗamin baki tayi ta muntsuna shi,dan dama duk gidan ta rufe ƙofah a rashin kunya da tsokana.
"Naci ɗin waya hanaki ci dayawan"
Hannun na miƙa zan kai mata duka muka haɗa ido da anty shamsiyyah wacce suke cin abinci a tire ɗayah itada anty juwairah,harara ta zanbagmin alaamar kar nayi.
Amma hakan bai hana na bugeta kaɗan ba.
Haka muka gama cin abincin babu wanda yasamu damar yin faɗa,dan anty shamsiyyah tana nan tadawo gida bayan tagama makarantar kwanan ta waccen satin.
Har aka gama murnar dawowarta nidam banyiba,dan ninasan takura mana zatayi.
Daɗinta ma aurenta za'ayi da ɗan gidan,amma a sashen hajjah ya tashi,yasamu aikin gwamnati yayi gininsa dadai misali,da yanuna yana sonta dama tun tana ƙarama sai aka saka musu rana.
Bikin duk na cikin gidanne,mune sashen amrayah yayinda su maryam kuma ƴan sashen ango,.
Murna ta ɗaya ce a bikin za'a mana sabon kaya kuma za'ayi su cin cin da nakiya,amma banda wannan babu ruwana da sha'aninsu,dan daga shi har ita amaryar ba shiri mukeyi dasu ba,sai yazo gidan sau uku bamu haɗu ba,kasona kawai nake samu na mintin dayake kawowa.
Itama anty juwarah da take ƴar babba ba wani shiri take sosai ba,dan dama anty shamsiyyah tafita sosai,ko a makaranta ma tazarar shekarah uku ta bata,ita ta gama jss ita kuma ta gama sss,dukkan su hutu suke,amma bayan bikin anty juwairah zata koma ta cigaba da karatunta.
Tunda satin bikin ya kama ƙawayen anty shamsiyyah suka fara zuwa gidan,duk yawancinsu wanda tayi a makaranta ne sai kuma na cikin gari kaɗan,dan dama ita tafi anty juwairah ɗaukar duniyah da zafi,shiyasa ma bawani shiri suke ba,koyaushe tana cikin cemata tafiye sanyi da ƙauyanci,itadai jinta kawai takeyi.
Biki aka sha mai kyau ba laifi,amma ba damu akayi ba tunda sannan bamuda wani wayo,dan ko gidan amaryar ma bamuje ba,iyah anty juwairah ce taje kawai,oho nidama ba san zuwa nake ba,murna ta ɗayace sun bar mana gida zamuyi yanda muke so,musakata mu wala.
Duniyah sabuwa ta koma mana,babu mai cewa mu bari,anty shamsiyyah ce ita kuma ta tafi,hajjah kuwa hmmm ai wannan mun raina mata wayo,idan bata nan har babu daɗi mukeji mun rada wacce zamu tsokana.
Uh shekarun sun fara zuwa har muna aji biyar na primary,zuwa sannan mun ɗan wasu abubuwa,ba kaman da ba,dan yanzu mukan yi wankin kayan mu ƙanana,wani lokacin kuma har wajen girki muke shiga.
Maman yara ce ta tafara cewa mudunga shiga muna ganin yanda ake,inno kuma ta hana,saidai kuma dole mu fara aiki,saboda kowanne lokaci za'a iyah tafiyah damu kokuma aure yazo mana da wuri,dan idan wani yace yana son ɗayar mu a kowanne shekarune indai ya kai sha huɗu to Baba Shahu saka ranar aure zayyi.
Wannan shine ƙalubalen da zamuyi dakon tunkararsa idan yazo,duk da iyayen riƙon namu bazasu so haka ba amma kuma babu yanda zuyi idan ya faru.
Ƙanana nan kayana na tattara ina sanɗa zan kaiwa anty juwairah danaga tana wanki,nasan ina zuwa inna roƙeta zata ƙarba,musamman idan nace zan tayata ɗiban ruwa.
Inno ce ta ganni ina shirin wucewa,aikuwa kash rashin sa'a sai jin muryarta nayi.
"Sabrah ina zaki da kayan dazaki

7 / 33