Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
saratu to yayi ƙarya,dan akalla sashen zai yi ɗarin na hajiya saratu a ƙyau da kuma alatun duniya.
Dan mutum zai ɗauka ba a nigeria yakeba.
Kalle kalle deejah take tayi har suka isa falo na uku a wajen.
Komai na wajen kama daga kujeru da kuma su dinning da adon wajen da gold akayi musu ado,ga ƙamshin turarukan muski irinna zahirinnan.
Mutum idan ba shiga yayi yagani ba zai ɗauka da gaske bane,sabida abin ya wuce tunanin mai hasashe.
Wasu ma'aikatane mata masu kaya iri daya suka fara jera mata abin sha,dukkansu fararene basuyi kama da ƴan nigeria ba,basa fitowa a wajen,iyakacinsu yin hidimar abinci da kulada adon wajen.
Ita dai deejah tana kallonsu har suka gama shirya komai a wajen,amma batayi yunƙurin taba komai a wajen ba har akayi minti biyar.
Wata ƙoface tayi sliding ta buɗe da kanta,hajiya fulanice ta fito daga wajen jikinta sanye da wani jan yadi mai daraja,dan kodaga hada ido dashi mutum yasan in basshida shi nai isa sakawa ba.
Tanada dan jiki amma batakai hajiya saratu ba.
Saidai ita farace sol har jaja take,ga kyau kaman ita tazana kanta,musamman yanda jan yadin ya dauki fatarta.
Zama tayi a kujerar tadake mazaunin mutum dayah,kuma take kallon inda muke zaune a ƙasa.
"Naji abinda zainabu tacemin kin fada gameda maganin rashin lafiyar mubarak.
Shin ke wacece kuma daga ina kike,sannan menene yakawoki wannan masarautar?"
Shuru deejah tayi batace komai ba,da alama tambayoyin yawo suke mata akanta.
"Ba roƙonki nake ko kuma neman jin uzurinki ba,umarni ne nabaki ki faɗamin,dan haka dolene yanzu ki fadamin ke wacece"
Haɗiye wani yawu deejah tayi kafin tace.
"Sunana deejah,ni yar gidan wani maharbine dayake ƙauyen garin Kurfi.
Duk da shi maharbine to kuma yana bada magani,sanan kuma yanada sani akan ciwukan dasuka shafi sanyi,sammu,asiri,da kuma na aljanu. Nima nagaji abinda yakene saboda tun ina yarinya tare muke zuwa nemo magani a cikin jeji.
Hakannne yasa na ƙware wajen gane ciwo da kuma nemo makarins.
Muna zaune ne mu biyu,kasancewar mahaifiyata ta rasu. Wata rana sai aka kawomana harin,wanda mu taka sawun barawo mukayi. Wasu fulanine suka biyo barayin shanunsu,sukuma barayin sai suka iyo yankimmu,garin tsautsayi suna harbinsu suka harbe babana a wajen.
Ina ƴar shekara goma sha biyu lokacin da aka kasheshi,hakanne yasa nashigo garin kurfi a daren na hau motar da bansan ta inace ba.
A garin daura aka sauƙeni,bansan kowa ba hakan yasa na fara bara.
A nan allah ya haɗani da wani bawan allah yarikeni bayan yaji labarina.
Ina nan zaune a wajensa na fara karatu.
Zuwa nan kuma wata makwanciyarsa ce taje gida,data faɗamin anan take aiki saina biyota domin nasamu abin kaina nima"
Dahaka deejah ta karisa labarin muryarta tana rauni,da alamar batason tunoda abinda ya wuce.
Jan numfashi hajiya fulani tayi,bayan taji abinda deejah tace,ganin babu wani abin zargi cikin labarin yasa tasaki ranta tareda sake jeho mata wata tambayar.
"Naji mai kikace,har yanzu kim iyah haɗa magani ko kuma kin manta ,iya mai bata maganin kawai kika samu damar gani"
"Eh bazanje ba,amma duk wani laƙani da babana ya koyamin yana cikin kaina,yine kawai banayi da ina gidan mariƙina"
"Toh idan baki manta ba,inason na jarabaki zakiyimin wani aiki,idan kin ci jarabawar zaki zauna a sashennan kuma a cikin falonnan,sannan kuma aikin dazakiyimin zan biyaki da tsoka,kudin dazan baki sai ya gigita ki ma.
idan kuma baki ciba akwai gagarumin hukuncin dazan baki wanda zai iya sanadiyyar tafiyarki barzahu,ma'ana a bakacin ranki na batamin lokaci da kikayi,idan kin shiryah ki fadamin"
"Eh naji abinda kikace ranki ya daɗe,kuma na yarda na karbi aikin zanyi"
Mamaki abin yabawa ba iya zainabu ba harda hajiya fulani,dan tayi zaton deejah zata fara karkarwa,saikuma taga babu abinda tayi,tana cikin nutsuwarta,kaman bata fahimci sharadin da aka bata ba.
"Okay shikenan ki biyoni toh "
Tashi hajiya fulani tayi tareda nufar wata ƙofah.
Binta sukayi suma a baya itada zainabu.
Deejah tayi zaton daki zata gani idan an buɗe ƙofar,saikuma taga ashe wani irin wajene da aka kewayeshi da glass,tsakiyar wajen kuma wani farin balarabene a kwance yana kallon sama,gefensa duk wasu wayoyine na wayarin ɗin abinci zuwa cikin jikinsa.
Wasu mutane kuma mace da na miji sanye da fararen kaya suna ta bincike,da alama likitocine masu kulada shi.
Ƙarisawa sukayi har gabansa,deejah tasamu damar ƙaremasa kallo,labarinsa taji amma batayi zaton ganinsa yanzu ba. Lallai duniya abin mamaki,tamkar za'a ƙirashi ya amsa,amma kuma babu damar hakan.
"Ina so kiganomin abinda yake damunsa,wanda masu magani dayawa suka kasa ganowa.
Gobe inada zuwa singapore,sati guda zanyi idan nadawo zanji amsarki.
Kafinnan kizama cikin shiri,sannan karki kuskura naji zancen a wani ware,domin ina son sirri,wanda kuma bazai iya ajiyewa a ransa ba to zan karbi harshensa,ta yanda ko yaso faɗa baxai sami iko ba.
Ki kula yarinya zansa masu dubamin ke kafin zuwa nanda satin. Kinada damar fita inda kike so,domin nemo amsar gwajinnaki"
Hajiya fulani tana gama fadan hakan suka fito daga ɗakin da ɗannata yake ciki.
Ita kuma deejah ta fita daga sashen jikinta sanyi ƙalau.
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
33••34
Tafiya take gaba ɗaya ta dulmiya cikin tunanin aikin da hajiya fulani ta bata,kwata kwata yanzu tsoron aikin takeyi,bayan kuma ta amsa zata iyah,tasan ko giyar wake tasha to babu damar ta zanye tace bazata iya ba,aikin gama ya riga da yagama.
Mutum taji ta buga ta ƙarfi,da alama shima tahowa yayi da karfi bai kulada ita ba.
Goshinta ta dafe tana murza wajen, tareda ɗaga ido dan ganin wanene.
"Mai doki" shine abinda ta faɗa hankali kaman mai raɗa,hannunta kuma dafe da goshinta tana mulmulawa,wanda yake mata raɗaɗi"
Shima gishinnasa ya dan riƙe,kafin yakalli bayanta inda ta fito,wato sashen hajiyah fulani,mamaki abin yabashi,dan shima ɗazu ya kula a can sashen ya ganta tana aiki,yanzu kuma da daddare ta fito anan.
Share tantamarsa yayi saurin yi,dan a yanda yaketa saurin kar ya rasa sallahr isha ko cikekken lokacin tunani bashida shi.
Bai ce mata komai ba ya juya da gudu yayi hanyar masallacin da suke shirin gama raka'ah ta farko.
Har deejah tajuya zata tafi saikuma ta kalli carbinsa fari daya jefar a lokacin da sukayi gware.
Tsugunnawa tayi ta dauka tareda hango bayansa yana daff da shigewa masallacin dayake gefenta.
Nannaɗeshi tayi a hannunta kaman igiya tareda kaɗa kanta ta nufi sashensu danyin tata sallahr,da niyyar gobe insun haɗu ta bashi abinsa.
Bayan ta gama sallahr salaha ta kawomusu abincin dare,sai mita take wai ina ta fita kalan saitayi gamo da aljani.
Dariyah deejah tayi amma batace komai ba saicin abincin data fara,wace aljana zata gamuda ita bayan ita kanta itama aljanarce?.
Haka suka gama cin abincin sai surutu salaha take mata,amma wani ta amsa wani kuma tace hm.
Gabaɗaya tunaninta ya tafi yanda zata samo amsar ciwon yarima mubarak,domin samun shiga sashen hajiya fulani kaman yanda take fata.
Dare mahutar bawa kowa yana bacci,amma deejah tana zaune ta saka wani waje ido a bakin barandar ɗakinsu,hannunta kuma wasu duwatsune guda biyu tana juyawa.
Wani farin mutum ne shiba a sama ba bakuma a ƙasa ba yana kallonta da wasu fararen idanuwa,wamda ko kaɗan basuyi kamada na bil'adama ba.
"Sumail yaushe ka dawo,kuma mai kake anan wajen?"
"Uhm saboda kin manta dani saina manta dake?,jiya nadawo,saikuma na shinshinoki a inda ba'anan nasaba jinki ba"
"Kuttt wai har yanzu baka cire ajiyarka a jikina na,tukunna ma a ina kasaka iyee?"
Ta faɗa tana tashi tsaye tareda dudduba jikinta.
Dariya yayi mai wata irin sauti irinnasu,saikuma yayi shuru tareda cewa.
"Meyake damunki naga kin fada kogin tunani,tun dazu nake wajennan amma baki kulada ni ba,menene yafaru ki faɗamin yanzu,tunda abokinki yadawo ki share hawayenki,koma waye saina juyarda kamanninsa"
Zare ido tayi tareda galla masa harara,
"Har yanxu ka tuna wanann kalmomin,bai kamata yanzu ka dunga fadan haka ba?"
"Ke da gangan nake,dazu ina tafiya sainaga jejin da muka zauna,abubuwa da yawa sun dawomin loka.........."
"Dakata Sumail,ya isa haka dan allah,kafi kowa sanin yanda na tsani wannan lokacin"
"Kiyi haƙuri nadaina,amma kuma ki fadamin yanzu mai ya faru"
"Kasan mai nake a gidannan .....?"
"Ahah sai kin faɗa naji"
"Nan gidan Hajiya fulani ne,nasan ka tuna sunan koh"
"Zaro ido yayi yana jijjaga kai tareda cewa.
"Ai wannan dai wacce nasani,wato........."
Saurin saka hannunta tayi bakinta tareda kallon gefenta,saida kuma tayi hakan ta tuna ashe babu mai jin maganarsa sai ita,ajiyar zuciya tayi tareda kwashe abinda tazoyi ta fadamasa,harma da aikin data bata,wanda idan batayishi a sati ɗaya ba sunanta gawa.
Kuma tafi kowa sanin zata aikata hakan.
"Ya kake ganin za'ayi Sumail,nima banyi tunanin zata bani aiki irin wanann ba,sumail idan har hajiya fulani takasheni kafin nasamo mata amsar abinda ta tambayeni,bazan iya yafewa kaina ba harna dudduge a cikin ƙasa.
Duk da haka banso fadamaka ba sumail,saboda taimakon damukayiwa juna bamuyi danna roƙeka wani abuba"
"Deeejah nasha faɗamiki duk lokacin dakike buƙatar taimakona ki faɗamin,bana ziyartarki dan ki nemi wani abu a wajena kibiyani ta wata hanya,alaƙarmu bata irin sauran masu ƙiran aljanu bace kaman yanda kike,kece sanadiyyar shiriyata,wanda a yanxune nakejin ni rayayyane sabanin da.
Dan haka a shirye nake dana taimaka miki.
"to naji,maika kake ganin za'ayi,"
"Eh to haƙiƙanin gaskiya bazan iya shiga wajen ba,dole saina koma shaiɗani yanda nake a da,inkuma ba haka ba musamu wani yaje mana,ko kuma ......"
"Ko kuma me?"
"Ko kuma ki dole saikin samo kunnen jaki na jikin tsamiyah(wani ɗan ƙaramin ganye ne dayake fitowa a ƙasan bishiyoyi),da kuma ruwan rijiyar data shekara ɗari,za'a saka ganyen a cikin ruwan sai a yayyafa masa,akwai abinda nake zargi,in shine zamu gane da wuri"
"Bazan iya ganin ka koma gidan jiyaba,sannan bazan bi sa'bawa allah wajen ƙiran wani arne ba.
Babu ta yanda za'a gane menene a jikinsa inba tanan ba,kona ɗauko maka hotonsa bazayyi ba?"
"Ahah bazayyi ba deeejah,saboda akwai abinda zan duba ba iya na ganshi ba. Tunda bakyason wanann dole saidai a nemo kunnen jakin,shikuma gaskiya in ba'a samuba to zai ɗauki lokaci,dan kuwa abin yanada matuƙar wahalar samu"
Komawa deejah tayi jagwabbb ta zauna jin abinda sumail yafaɗa,gabaɗaya tashiga damuwa.
"Kinga ki kwantar da hankalinki,tunda wanann shine aikinki na ƙarshe,zanyi iya ƙoƙarina wajen nemomiki inshaallah,ki tsimayi dawowata a ranar na uku,in kuma bansamu ba har ranar ƙarshe to zanzo musan nayi.
Kije ki kwanta ki huta,sanann kicire damuwa a ranki"
Yana gama faɗan hakan ya 'bace 'batt tareda barta cikin tunanin daya sameta dama a ciki.
Tashi tayi cikin sanyin jiki tashiga ɗakinnasu,gaskiyar sumail ɗinnne gwanda ta kwanta ta huta.
Washagari ta da ƙarfe takwas tashiga sashen hajiya saratu domin gyara ɗakin amal,wanda yake cikin aikinta.
Babu kowa a falon,dan haka kai tsaye da wuce ɗakinnata,saboda ranar monday ne tayi tunanin bazata sameta ba,saikuma ta ganta a cikin bargo sai juyi take.
Yaye labulen window ta fara,domin bawa harske damar yalwata ɗakin.
Wata tsuka amal taja kaman gaiwa,tareda dagowa dan ganin wanene ya aikata hakan.
Haɗa ido sukayi da deejah waccce itama kallon idonnata takeyi,dan yarinyar tun a jiya taƙara bata haushi data mareta,musamman ma data tuno yanzu sanadiyyar haɗa idon da sukayi.
"Waye ubanki da har kike da ƙarfin gwiwar shigowa ɗakina ki buɗe min window,ke kika rufesu da,wai me kikeji dashine dakike wa mutane wani jiji dakai,to kiyi hankali dani inba haka ba zan saitaki a gidannan kaman sauran.
Idan kuma kinga bazaki bini ba kiyi yadda nace to ƙofa a buɗe take ki bar gidannan"
Ta faɗa tana daga murya tareda gallawa deejah harara.
Ita abin ma mamaki ya bada,dan haka tasaki baki tana kallonta,anyi kuwa yarinyar nan kanta daya kuwa?,wata zuciyar tace mata ,kanta ɗaya,kawai so take a ɗorata akan hanya.
Wani ɗan murmushi deejah tayi tareda cewa,"aikuwa zan saka ta hanyar,dan gidan tazo wajen saka mutane a hanya"
Wannan karon amal tabari da mamaki,ganin maimakon deejah ta bata haƙuri,saima dariya data yi"
"Yarinya ki tashi kitafi makaranta ba faɗa zaki tsaya yiba,nikuma ki bani waje nayi aikina,in kuma kinaga bazaki jeba,ke tashafa,nidai ki bani waje toh"
"Kuttt anya kuwa kinsan dawa kike magana,harni zakice na tashi na baki waje zakiyi aikinki,kuma a ɗakina?"
"To wacece ke banda wacce nake gani a gabana,ko ƙafa uku ce dake tawa biyu,faɗamin naji,ko kuma kanki ne biyu nawa ɗayah,da banbanci ne nida ke a halitta da allah ya fifitani akanki.
Inkuma batun muƙamin ubane,naga babankine sarkin bakeba,sannan uwarki ce sarauniyar bakeba,shikansa muƙamin Gimbiya yana hannun babbar yayarkkune wato Nana khadijah"
Zaro ido amal tayi,jin a cikin jimla ɗaya deejah ta gama da ita,rasa abinda zatayi tayi,wanda hakan yasa tajefi deejah da filon dayake gefenta,tareda fita da gudu tana ƙwalawa mahaifiyarta ƙira.
"Mommy! Mommy!!,"
"Miye kike zubamin ƙira haka,wai yaushe zaki girmane da,wannan sangartakar,koh abdul yayi abinda kike ne?"
"Mommy,wanann mai aikin dakika ɗaukamin jiya na koreta bana sonta,banda raini babu abinda takemin,kiji abinda take faɗa waini ba gimbiyar gidannan bace?"
"Karya take toh,yaushe kika zama gimbiyar bayan antynku tana raye,kedai kawai ƴar sarki ce,amma banda muƙamin gimbiyar katsina kam"
Dafiyah abdul yasaka wanda yake sanye da uniform yana shan tea.
Harara amal ta watsamasa tareda buga ƙafarta.
"Kaikuma wayasaka dakai iyee"
"Kekika saka dashi,tukunna ma tashinki kenan,baki shiryaba,kinyi sallahr asuba kuwa,na bugamiki ƙofah kuma banji motsinki ba"
Shuru tayi tana soka kai tareda turo baki,kobata faɗana yanayinta ya nuna batayi ba kenan.
"Wai nikam yaushe zaki girma na huta da wanann takaicin,sai son mulki kaman wata mai jiran gado,mainene a mulkin banda ni ƴasu,karatun danake ƙoƙarin sakaki kina ƙin yi shine dai gatanki bayan na allah,inkin maida hankali kanki,babu abinda kika sani kai kamar fanko,sai shegen girman kai.
Deejah kuma dakika kawomin ƙara babu sanjatan da zanyi,inkuwa kika ƙara kawomim ƙararta,ko kuma tacemin kin mata wani abu,wlh keda mai aiki saidai kiga anayi,komai ke zakiyi dakanki.
Zancen sallah kuwa allah yaga nayi iya yina,kabarin na daban naki daban,dan haka ke kika sani"
Ganin ita da takawo ƙara karshe fadan ya koma kanta yasa takoma ɗakin,motsin deejah taji a banɗakin wanda hakan ya tabbatar mata wanke banɗakin take.
Zama tayi a bakin gadon tareda shiga whatsapp tana jiranta ta fito.
Har deejah kuwa ta fito daga banɗakin bata tashi ta shiga ba,ƙarfi da yaji bazata makarantar ba take nufi.
Itadai data gama aikinta fitowa tayi suka gaisa da hajiya saratu,daga nan tafito domin yin nata harkar.
Eemran ta hango a wajen dawakai,ya zage sai gyara jikin wani doki yake,wanda baya daga cikin wanda Hajiya saratu tazo dashi.
Riga da wandone a jikinsa na yadi mai matsakaicin kuɗi,amma kuma babu wanda zai kallah yaga kazanta,bayan rashin kuɗin daya gani a jiki.
Deejah batasan lokacin da murmushi ya subuce a bakinta ba ganin yanda ya ɗan zaburah yayi gefe,sa'adda dokin yayi wani haniniya alamar bai sanshi ba.
Juyawa yayi gefe da gefe,ganin babu wanda yake kallonsa sai ya sau ajiyar zuciya,dan abin da kunya kana kulada doki,kace gadon gidankune kuma a kanga kana tsoronsa.
"Uhm ka kwantar da hankalinka,babu wanda ya ganka,amma ni naganka ai"
Dagowa yayi ya kalli deejah wacce ta tsayah a gabansa tareda riƙe ƙugu tana kallonsa tareda yin murmushi,wanda yafito da ainihin jinin fulanin dayake kan fuskarta.
"Wayace miki tsoro nake toh"
"Nima bance tsoro kake ba,kawai nace na ganka"
"Meya kawoki nan wajen,bakida aikine da safennan?"
"Daga wajen aikin nake nagama,zan wucene nace barina kawo maka carbin daka jefar a hanyar da muka yi gware"
Mamakine ya kwanta akan fuskarsa tareda tunani.
"Awwn nayi ta nemansa dana gama sallah ban jishiba,sai nayi tunanin ko a ɗaki na barshi,dana koma na duba kuma banganshi ba"
"Uhm to jefarshi kayi jiyah,a hanya kana sauri"
"Dama nima inaso na baki haƙuri akan bugekin danayi jiyah,ban kula bane sam,ina sauri karna rasa sallah"
"Ayyah bakomai,nima kayi haƙuri toh"
"Haƙurin mefah,nine na bugeki ai bake kika bugeni ba"
"Bana wanann bane,nayi amfani da carbinka ne naja tasbih da asuba"
Da faɗa tana miƙamasa,har ya miƙo hannu zai karba,jin abinda tace yasashi janye hannunsa tareda cewa.
"Ahh to ki barshi a wajenki na baki,daama biyune dani,zan dunga amfani da wancan"
"Ammma....."
"Karki ce komai,har raina nabaki,banaso nayiwa mutum kyauta ya maryamin dashi,ko yaƙi amsa,zanyi zaton kin raina ne"
"Ahah ban raina ba,nagode sosai da kyautar ka"
Har a fuskarsa ta kula yanda yaji daɗin kyautar datayimasa.
Suna cikin tsaye babu wanda yasake cewa komai sai sukaji hayaniya a bayansu.
Dukkansu juyawa sukai suna kallom Yarima Jalal,ɗan gata majida kyau da kuma ƙuruciyah,kallo ɗaya mace take ta fola,wannan shine abubuwan da aka sanshi dashi.
Cikin taƙama yake tunkarosu har yazo daff da inda suke,wasu maza guda biyu suna biyedashi,irin manannannun abokannan,masu mannewa ƴaƴan masu kuɗi.
Ingarmar dokin yakama tareda ɗora hannunsa akan bayansa.
"Wow ya wanku yayi kyau kuwa,daɗin jawo hankali,ko dokin sarki iyakaci,tunda nine mai hawa karagar garin kunga dolene nafara abinda za'a ƙara sanina a garin,ko ya kukace?"
"Wannan haka yake,ko mutane basaso kaine zaka hau kujerar garinnan,babu wani yarima a yanzu bayan kai"
Wani murmushi yayi tana kallon eemran tareda ciro kuɗi a wallet dinsa dollar.
"Kayi ƙoƙari wajen gyarashi yanda nace,inaga zan ɗaukeka aiki ka daina yiwa waccar matar,ni zan ninka maka kuɗin data baka zuwa ɗari ma idan kanada buƙata"
Yaƙarisa maganar tareda watsawa eemaran dalolin suna bin yadin jikinsa zuwa ƙasa.
Kollonsu eemran yake a ƙasan,dan daman kansa a sunkuye yake.
Duk abin mutum bazai fadi shin baƙincikine ko kuma takaici kwance akan fuskarsa ba.
Juyawa yareema jalal yayi zai bar wajen,kaman ya tafi saikuma ya dawo tareda sauƙe idonsa akan deejah,wacce take tsaye kamar bata wajen tana kallon mai yake faruwa.
"Ke kuma fah zazzafa,bansanki cikin masu aikin gidanann ba,yaushe kika zo"
Jalal ya faɗa yana ƙarisa inda take,lallausan hannunsa yasaka tareda ɗago fuskarta,yana cizar jar fatar bakinsa ta ƙasa.
Duk macen data kalleshi a lokacin sai allah ya kareta kafin tatsare kanta daga faɗawa tarkonsa.
Fincike fuskarta tayi tareda komawa bayan Eemran wanda yake kallon jalal ɗin.
"Kuttt kin san kuwa ni waye,har nace na yaba da surarki ki nuna min turjiyah,ki bani kanki nashayar dake daulah da kuma zuma,ki amince ko kuma ki amince dan dole"
Ya faɗa da yaidararriyar muryarsa yana yarfar da hannunsa daya tabata dashi.
"Kin batamin hannu da dattin talaucinki,dole saina jiƙaki da nairah tukunna da kuma gyara kafin kiyi daidai da wanda zanyi harka,zo nan wajen yanzunnan"
Yafaɗa yana mata murmushin yaudara.
Sake maƙalewa tayi a bayan eemran,duk da bata tabashi ba amma yana jin sautin numfashinta yana sauƙa akan bayansa,da alama tashiga cikin firgici"
"Kayi haƙuri ranka ya dade,bazata samu amsa gayyatarka ba,saboda ita ɗin budurwata ce,an riga anyi mana baiko"
Kallon ƙeyar eemran deejah tayi,jin abinda yafaɗa wanda yayi mungun bata mamaki.
Shima yasan dole zatayi mamakin,dan yanajin yanda kallom da take masa yana shiga jikinsa.
"Hmmm ina ruwana da baikonku,sati ɗaya kawai zanyi da itah ta dawo gareka,a tunaninka aurenta zanyi,ina kwanciya da matan aure ma idan sunyimin bare wata budurwarka.
Nidai tunda na ƙyasa to saina kashe kishriwata da ita.
Jameel ku miƙomin ita yanzunnan"
Tahowa sukayi zasu riƙo deejah daga bayan eemran,shikuma ya riƙe hannun wanda aka ƙira da jameel ɗin,ƙarass ya karyashi kaman ya