MABARACIYAH Daga Bara Zuwa Firgitar Masu Iko by Auwal sadiya

Author :  Auwal sadiya Category :  Free Novels Online (Read & Download)

Chapter   20 / 33

57K to 60K   out of 96.8K words

samu karas.
Kallon idonsa suke wanda yayi jawur,yayinda jijiyoyin jikinsa sukayi 'baro 'baro a jikinsa.
Duk wanda ya kalleshi a lokacin koda na mijine dole tsronsa ya ɗan ɗarsu a ransa,amma ko kaɗan deejah bataji ɗigon tsoronsa a ranta ba,saima wani jin protective da take ji a tareda shi,koga sumail dayake ba mutum ba batajin hakan kaman yanda take ji ga bawan allah eemran,wanda yaune ganinta na uku dashi a rayuwarta.
Matsawa yarima jalal yayi yana kallon eemran ɗin,shikuwa wanda aka karyawa hannu hankalinsa yana kan ciwon dayake ziyartarsa,sai ihu yakeyi.
Fadawa ne suka rugo da gudu damin ganin mai yake faruwa.
Yarima jalal ne ya kalli ɗaya daga cikinsu tareda cewa.
"Maza yi sauri ka ƙiramin sarkin dogarai da kuma shamaki,haram da Uwar bayi"
__sarkin dogarai a sarautun gargajiyah shine mai kulada dukkan shige da ficen abinda yake faruwa a cikin fada.
__Shamaki shine shugaban masu kulada duk wani doki a cikin fada,kama daga shigowarsu fitada su harma da kuma masu kuladasu da abincinsu.
__Uwar bayi a da itace mai kulada duk wani bawa a cikin fada,kasancewar yanzu zamani yazo,bayin fada sune matsayin ma'aikata,sai yakansance wani wajen ana ƙiranta da uwar ma'aikata na mata,a sashen matan sarki da sauran iyalansa.
__Jakadiyah kuma itace ƴar aike tsakanin sarki da kuma matansa a cikin gida.


Da sauri cikin rawar jiki wanda aka aika ɗin ya furma gidan nemo wanda aka faɗamsa yana baza babbar riga.
Can da kaman minti talatin dukka suna tsaye sai gashi ya dawo suna biyeda shi a bayansa.
Kallonsu yarima jalal yayi shima ransa ya baci sosai.
"Kai sarkin dogarai kaine mai kulada shige da ficen kowa a cikin gidannan,yaushe wanann mutanen suka shigo cikin gidannan.
Sannan kaikuma shamaki waya baka izinin ɗaukar wannan aiki a cikin fada.
Ke kuma shugabar ma'aikata inaso ki faɗamin menene aikin ita wanann a cikin gidannan"
Dukkansu diri diri suka farayi,dan kowa a cikinsu yasan rashin mutuncin yarima jalal a cikin gidan.
Sarkin dogarai ne yafara magana,wanda deejah tana kallonsa ta ganeshi,shine wanda sukayi ta magana shida yadiko lami farkon zuwanta.
"Eh toh ni ban binciki ita wanccar daga inda tazo ba,saboda naga tare suka shigo da lami,wanda an santa sosai tsawon kusan shekara goma.
Shikuma wannan saurayin Hajiya saratu ce tazo dashi daga gidansu,ka tambayi shamaki tunda a bangarensa yake"
Sarkin dogarai yanayin shuru shikuma shamaki ya cigaba.
"Eh hakane,shine ya taho da dawakan hakiya saratu,kuma shike kulada su daga lokacin,dayake nasan babu wani abin cutarwa shiyasa bancd komai ba,musamman da sukace dama a canɗin yake aiki,ba'a taba samun matsala dashi ba"
Ke kumafah shugabar ma'aikata?"
"Eh kaman yanda sarkin dogarai ya faɗa hakane ranka ya daɗe,tare sukazo da lami,tace mana ƴar maƙotansu ce,kuma babu matsala a tareda ita,dan itake kulada sashen hajiya amal ma"
Numfasawa yarima jalal yayi cikin ƙunar rai kafin yace.
"Duk naji abinda kukace,saidai ku sani wanann ƙananan mutanen sun saba dokata saboda basu sanni ba,saboda basusan ƙarfin ikona a gidannan ba.
Kai shamaki inaso a yanzu basai an jimaba ka koroshi daga aiki a gidanann,sanann kaikuma sarkin dogarai ka miƙashi ga dogarai su masa bulala ashirin.
Ita kuma itama ta daina aikin datake a gidannan,kuma zata koma sashena dayin aiki,kullum ita zatayi komai a wajen,harda sharar filin wajen.
Na gama magana koda mai ja anan wajen"
"Gani nan nice mai ja da maganar taka,sanann kuma hukuncinnaka na sokeshi bayyiba,saboda mutanen dakake ƙoƙarin kora nina ɗaukesu bakaiba,dan haka saika bari idan ka dauki naka ma'aikatan sai kayi yanda ranka yakeso,kaji jalal?"
Hajiya saratu ta faɗa lokacin datake ƙarasowa wajen,idonta kyam akan nasa,kana ganin kallon da take masa kasan dama ta daɗe tana shaƙar tijararsa a gidan.
Shima kallonnata yake cikin rashin kunya,idonsa a tsaye.
"Eh ma'aikatankine,amma kuma ni nan mai jiran gadon sarautar garinnan inada ikon dazan zartarwa kowa hukunci a cikin gidannan,ciki kuwa hardake hajiya saratu"
Mari ta watsamasa tassss a kumatunsa na dama,bakinta har rawa yake dan bacin rai.
"Kai harka isa kayimin rashin kunya bayan ka shiga gonata,ga bana aka yankewa yayanka cibi ma ba kaiba,sanann yanda kake ɗan sarki kake taƙama,nima ƴaƴana ƴayansa ne,yanda uwarka take matarsa haka nima nake matarsa,ko kai baka kaini iko a cikin gidanna ba,ƙafa nake ɗagama saboda a zauna lafiya. In jinin sarauta ne na gajeshi tun kafin nazo gidannan.
Inkuma kana ganin ka isa kaman yanda kake faɗa,kasa ubannaka ya koreni a yau basai gobeba,inkuma har yanxu baka kaiba,to ka jira saika hau mulkin da mafarkin banza kake kowa yana kallonka,kaida mulkin garinnnan saidai kaga anayi.
Mai mulkin wajen yana nan yana zuwa idan lokaci yayi.
Karka fasa muzuba nida kai a cikin gidannan,uwarka tayimin ta barni bare kai"
Kana ganin yanda take magana kasan tashaƙa dayawa.
Shima kanƙance ido yayi yana hararata,daga nan yabar wajen yana yimata kallon zasu haɗu.










Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.







*MABARACIYAH*


_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)





35••36















Kowa watsewa yafarayi a wajen,ciki kuwa harda dogaran,ganin wanda ake faɗan dominsu ma sun bar wajen.
Tafi eemran yake deejah tana binsa a baya nesa dashi kadan,babu wanda yake cewa komai a cikinsu,da alama abinda ya faru suke tunawa.
"Kayi haƙuri"
Shine abinda deejah ta faɗa cikin sanyin rai,
"Da akayi me kenan kike bani haƙuri"
"Kana ƙoƙarin rasa aikinka akan kareni daga gareshi,nagode sosai"
"Badan nasanki nayi hakam ba,nayine saboda kina a matsayin ƴa mace,kowacce mace ma idan naga za'ayi mata haka musamman idan tashiga bayana to sai inda ƙarfina ya kare,dan haka ki daina yimin godiya"
Zuciyarta ce ta sosu da maganganunsa,bata san dalilin hakan ba.
Har yafara tafiya ta tafi da sauri tareda shan gabansa.
"Kaine aine mutum na farko a rayuwata bayan mahaifiyata daya taba yunƙurin tsayamin saboda wani abu zai cutar dani.
Koda zaka ganni a matsayin ƴa mace kawai,ko kuma zaka ganni a matsayin wacce kasani,wanann bai shafeni ba,abinda nasani shine ka ƙara daraja a cikin idonanuna fiyeda koyaushe,irinku cikin al'umma ƙalilanne.
Dan haka inayimaka godiyah sosai,ita kaɗaice abinda zan iya baka wacce nake da,idan bazaka karba bama nasan ka jita a kunnuwanka,sannan sunana deejah,koda a ganni a wani wajen zaka ƙirani nikuma ban ganka ba.
Nasan sunanka eemran,suna mai daɗi,indai na ganka koda bazaka amsa ba zan ƙira sunanka,kunnenka su saurari jin amon muryata a duk lokacin da idanuwana sukayi tozali dakai"
Tana gama maganar tasake masa wani murmushi mai tsada tareda dagamasa hannu tabar wajen.
Shikuma ta barshi a tsaye sororo yana binta da kallo.
Wannan ranar haka ta wuce deejah basu sake haɗuwa da eemran ba,kowa yana nasa harkar.
Yau kimanin kwana uku kenan haɗuwar deejah da sumail,gobene yayi mata alƙawarin zaizo idan har yasami abinda yaje nemo mata,idan kuma bai samuba sai ana gobe aikin zai ƙare kafin ya dawo.
Duk wani zirga zirga da murmushi datakeyi na dolene dan babu yadda zatayi.amma cikin zuciyarta jitake tamkar tangaranne yafashe.
A zaune take a wata baranda tana kallon eemran yana sakawa dawaki abinci,shida wani yaron shamaki.
Dariyah ita kaɗai tayi,tun ranar da abin yafaru duk sanda ta ganshi saita ƙira sunansa,wani lokacin da waiwayo bai ce komai ba,wani lokacin kuma ya shareta.
Yanzun ma ɗaga murya tayi yanda zaiji tace.
"Eemraaaaan"
Shuru bai amsa mata ba tasake cewa
"Eeeemraaaaan,bazaka amsa ba ko,idan baka amsa bama,kunnuwanka nasan sunjini kuma sun amsa min,sannu da aiki,na saƙƙo na tayaka?"
Har sanann bai kulata ba,duk da tadan yajita daga yanda yake dan ƙaramin murmushi.
Tashi tayi daga wajen ta nufo inda yake,hannunta riƙe da ɗan karan ciyawa tana juyawa.
Murzashi tayi a bayansa yayi saurin dafewa tareda zuyowa a razane.
Dariyah tasaka harda tsalle,yanda yayi da idon kaman an kwacewa yaro feeda.
"Iyeeee jarumi da tsoron tsinke,nayi zaton yanzun ma bazaka juyoba ai"
"Ke miye haka wai,duk da nayi shuru na rabu dake amma saikinzo har wajennan kina mace,ki daina ƙirana irin haka,kina mace bai kamata kina wannan wasan ba da kuma ɗaga muryah"
Ya faɗa cikin alamar faɗa,da alama ya ƙosa da abinda take masa.
Sanyi jikinta yayi,idonta yayi raurau kaman zai kawo ruwa.
"Kayi haƙuri,banyi tunanin zakaji babu daɗi haka har haka ba dan ina kulaka,dama har haka na takura maka?.
Ba yanda kake zato nake ba,ina ganinka ne kaman wanda nasani kuma nakeda shi a wannan wajen,ina cikin damuwa ne da fargabar rasa rayuwata,ƙiran sunanka danake da tsokanarka shikaɗai ke fidda ni cikin tunanin halin danake ciki.
Amma bazan sake kusantar inda kake ba daga yau eemran,nagode da kyautarka,da kuma cetona dakayi ranar"
Juyawa tayi zata bar wajen,yayinda hawayen dasuke kwance a idonta suka samu damar zubowa.
Har tafara tafiyah taji muryarsa takama haruffan sunanta a karon farko na zamanta dashi.
"Deejah,deejah!!!"
Duk da yanda tayi fushi dashi kuma take ƙoƙarin barin wajen kasawa tayi,ga wani bugu da kirjinta yake kaman ana doka guduma,hannunta tasaka ta riƙeshi domin kar bugun ya wuce makaɗi da rawa.
Takowa yake a hankali zuwa inda take,yayinda itakuma takejin kaman ta zura da gudu,dauriya kawai take.
"Deejah duk abinda kika fahimta akaina ba haka bane,na faɗane saboda ki daina ɗaga muryarki kowa yana ji,sannan kuma kina tsalle maza dayawa suna kallon jikinki,wannan abinne yake batamin rai,gani nake kaman kowa idonsa a kanki yake,kiyi haƙuri ni mutumne mai kishi sosai"
Saurin ɗagowa tayi tana kallomsa da niyyar ya ƙara mata bayani akan abinda yake nufi.
Ɗan murmushi yayi tareda kallon cikin fararen idanuwanta wanda suka ɗan surka ja ja ja a cikinsu.
"Duk tambayar da kike buƙata zan amsamiki da yamma,a lambun da nake zama kina zuwa ƙiran sunana.
Menene ya faru wanda yake ƙoƙarin ɗauke rayuwarki?"
"Nima zan faɗamaka a wajen idan ka bani karin bayanin wannan maganar taka"
"Toh shikenan ina jiranki da ƙarfe huɗu,allah yasa karki banni nayita jiranki"
"Bazan ta'ba barinka kana jirana ba,zanzo,nagode da kulawarka"
"Nima nagode da kulawarki"
Dariya tayi tareda rufe gefen fuskarta tabar wajen,binta yayi ta kallo,jiyake kaman ya bita su zauna karsu rabe koda da daƙiƙa ɗayane.Hannunsa ya ɗauka ya ɗora akan saitin kirjinsa inda zuciyarsa take bugawa dominta.
Da farinciki deejah ta isa ɗakinnasu,gaba daya ta manta da wani abu daya ke shirin tunkarota na dawowar hajiya fulani,burinta kawai yamma tayi,danji take kaman ta jawota.
Kasancewar bawani kayane da itaba,dan haka bada damu kanta ba,dan tasan idan ƙaryar adone daga ita harshi ba wasu bane na azo a gani.
A bakin swimming pool ɗin dayake can bayan gidan ta hangoshi yana saka kafarsa a cikin ruwan.
Duk a wanda ya ganshi a lokacin bazai taba alaƙantashi da kulada dokiba,ga yanda sumar kansa ta kwanta lufff.
A hankali take taka ƙafarta har taje daff da inda yake zaunen.
"Kin ƙara minti biyar a yanda mukayi"
"Kayi haƙuri"
"Ya wuce,zauna ga waje nan"
Ya faɗa yana nuna mata gefensa,zama tayi itama tareda tsoma ƙafar tata a ruwan.
Shuru sukayi kaman kurame babu wanda yake cewa komai,ɗagowa yayi ya kalleta tareda cewa.
"Meyasameki kika canja lokaci ɗaya,ɗinke miki baki akayi ko mai"
"Ahah bakina ƙalau yake,kawai surutun yanzu na barmaka ne,ka manta kai kace kanada abinda zaka faɗamin?"
"Babban abinda nake son sanar dake,bazan iya ba a yanxu koda inada buƙata,saboda wani muhimmin dalili.
Tunda nazo gidannan ko abokina banji inason yin magana dashi ba kaman ke,ina jinki a cikin raina fiyeda yanda kike tunani,wani irin abu zuciyata takeyi idam naganki cikin ƙunci ko kuma naga wani yana kallonki,musamman yanda yarima jalal yayi ƙoƙarin yin.....,......"
Tsayawa yayi da maganar na ɗan lokaci kafin yacigaba da cewa.
"Ki amincemin ƙiran sunanki a duk lokacin dana ganki,sannan inaso yazama nine yanzu zan dunga ɗaga miki hannu a duk lokacin dana ganki. Shin zaki amincemin hakan?...."
Ɗaga masa kai tayi da sauri tareda ƙoƙarin mayarda ƙwallar datake shirin zubowa a idonta.
"Kema kincemin zaki faɗamin wani abu dayake barazana ga rayuwarki,menene wannan ɗin"
"Uhm.....uhm emran daka bar wannan"
"Bazan iyaba deejah,ke kika fara ƙoƙarin fara kulla alaƙa a tsakanin mu,a kisani a zahiri kika rigani,a baɗini na daɗe da son yimiki magana,tun ɗazu zuciyata cikin zullumi take da kuma fargabar shin menene yake damun rayuwarki,ki faɗamin deejah,nikuma nayi alƙawarin taimaka miki matuƙar zan iya.
Sannan bayannna inason kiyi min alƙawarin zaki sanar dani duk wani abu dazai kawo miki barazana a rayuwarki kinji"
Ɗaga kai deejah tayi kafin tafara bashi labarin yanda sukayi da hajiya fulani akan rashin lafiyar yarima mubarak.
Harma da tarihin ƙanzon kuregen data bawa hajiya fulanin.
"Jibine hajiya fulani zata dawo,har yanzu bincike nake akan maganin,amma inshallah nakusa ganowa,saidai kuma har yanzu ina fargabar idan nakasa fah"
Wani zuzzurfan tunani emran ya tafi,wanda babu wanda yasan mai yake damunsa sai sarki allah.
Kukan deejah daya ƙara saurine ya dawo dashi cikin halin dayake ciki.
"Amma meyasa kika karbi wannan aikin bayan kinsan yanada matuƙara wahala"
"Nima bansaniba....tace idan naƙi amincewa ma a bakin raina"
"Hmmm"
Shine abinda emran yace,kana ganin fuskarsa kasan akwai abubuwa kala kala a cikinsu.
A haka zamannasu na wajen yaƙare, emran sai rarrashin deejah yake da bata baki.
Fitowa sukayi daga wajen suna hira da dariyah,kaman basune sukayi jigum ɗazu ba saboda muguntar hajiya fulani.
"Uhm na rakoki yau kam har bakin sashenku,ki shiga ina kallonki kafin na tafi sallah.
Sannan karki manta,banda ɗaga hankali,allah yana tareda ke,nima ina tareda ke"
Murmushi deejah tayi masa tareda ɗaga masa hannu.
"Nagode emran da lokacinka a yau,haƙika kai na musammanne,kayi sauri karka rasa sallah,gobe idan nagama aiki zanzo tayaka hira"
"Shikenan zanyi ta jiranki har sai na ganki,idan kika zo zan barki kibawa doki abinci a hannu"
"Da gaske,wow karka basu abinci harsai nazo,nizan ciyardasu dukka,kaikuma ka koma gefe ka huta"
Juyawa yayi yana kallonta tana kallonsa har ya ƙulewa ganinta.
Da daddare kowa yana kwance,amma deejah sai kaikawo take a barandar ɗakinnasu yauma tana jiran zuwan sumail,agogon karamar wayarta ta duba,ƙarfe biyu da rabi.
Magana ta farayi cikin takaici.
"Hmmm dama nasan ai ba'ayin abu dakai ya tafi daidai,wani inya ganni yace tsafi nake da tsohon darennan,kai ni nagaji"
Hanyar tafiya tayi zata shiga ɗaki,saikuma taji dariyarsa a bayanta.
Tsayawa tayi tareda juyowa ta dire masa harara kaman yanda ta saba.
"Keda waye kike sababi haka,ko saurayinnaki ne ya tabaki"
"Ka ganmu ne ɗazu a zaune?"
"Na ganku mana,lallai kin iya kafce ba kaɗan ba,ji yadda kikeyi kaman gaske"
Kutt da kana nufin bada gaske nakeba?"
"Haba,ki faɗawa wanda bai sanki ba,kece fah deejah kuma Mabaciya ko me?. Taya zan yadda kece zaki faɗa soyayya mai zurfi irin wannan kuma a kwana uku kacal,inaga ko mutuwa yayi sau ukun a lokaci guda,zuciyarki bazata kai kansa ba bare kuma.
Na tabbata wani abu kike so a wajensa idan ba haka ba ko kallonsa bazakiyi ba"
Ya mutsa fuska deejah tayi,da alama ko bataso to sumail ya ganota..
"Ya isa toh,nibada mungun nufi na rabeshi ba,kawai akwai zargin danake akansa ne,daga nagano gaskiya zan barshi yayi harkarsa."
"Zargi wane iri kenan,kuma kike ƙoƙari zefa zuciyarsa cikin kogin sonki,duk da naga shima da alama baya nan yakeso a wajenki,dan hankalinsa yafi kaiwa kanki da kika bashi labarin abinda yafaru tsakaninki da waccar matar"
"Oho shiya ji wajen,dama ina ɗan shakkarsa ne shiyasa nakeson sakashi cikin idanuwana,don jiya na ganshi yana kewaya sashen hajiya fulani da daddare,lokacin danake jiranka.
Oh ni na manta,ina abinda zaka kawomin ɗin,an dace ko kuwa har yanzu dai"
"Ba'a samoba har yanzu dai an......."
"Dan allah dagaske baka samoba"
Ta faɗa tana zare ido.
Dariya yayi tareda miƙamata abin a cikin wata kwalba,da ruwa a cikinta sai kuma ɗan ganyen a ciki.
Karba tayi tareda ajiyar zuciya tana ƙara kallon kwalbar.
"Nagode nagode,yanzu yazamyi kenan?"
"Uhm babu,kawai ruwan zaki fatsa a jikinsa da ganyen,ko yaya indai aljanu ne suka tabashi ko kuma wani ciwone zakiga yayi girgiza.
Idan kuma yayi shuru,ki sake yi a karo na biyu,idan yasake yin shuru kisake a karo na uku.
Idan har sannan shuru to abinda nake zargi ya tabbata,wato babu kuruwa a jikinsa an ɗaiketa,(rauhu).
Rauhunsa baya nan an ɗaukeshi shiyasa bazai motsaba.
Wannan kenna sauran yana aiki na gareki,ni zan koma wajen karatuna,hutun da'aka bani ya ƙare"
"Nagode sosai sumail da taimkonka,allah ya bada sa'a,ya sauƙeka lafiya"
Daga haka ya bace ya barta ita kaɗai da kwalbar a hannu tana kallonta.
Komawa tayi ta kwanta bayan tabawa kwalbar ma'ajiyi mai kyau.
Da safe kuwa gaba ɗaya ta manta da haɗuwa dazasuyi da emran,hanyar sashen hajiya fulani ta nufah,domin a yanzu tafara ganin nasararta ta ɗaukar fansa tana bayyana.
Kallonta suke da mamakin ganinta da safe,amma basuce komai ba suka matsa mata ta wuce.
Kallon falo tayi wanda aka sauƙeta,kaman ba yanzu safiya ta wayeba,ma'aikatan sai hidimarsu suke.
Bata kulasu ba sai wawwara ido take,da alama zainabu take nema.
Hangota tayi akan dinning tana ta wawurar cinyar kaza..
Ƙarisawa wajenta deejah,ita abinma har dariyah ya bata.
"Barka da safiyah yaya zainabu,kin tashi lafiya"
Harara ta watsawa deejah tare cune baki.
"Wannan wane irin sunane haka,wai meyasa ake min kallon tsofine?"
"Saboda ke tsohuwar ce,kuma naga hajiya da zainabu take ƙiranki "
"Naji menene ya kawoki da safennan,kin samo amsar gwajinkine"
"Shinazo na samo dai a yau inshaallah,yanzu izinin ki nake nema zan shiga wajen,tunda kece ta hannun damanta"
"Ta hannun damanta kuma?....kinga nayi kama da wannan matsayin,rufamin asiri na mutu maza su kaini,ta hannun damanta yau zata dawo daga dubai,ta turata wani taro"
Ta faɗa jikinta har rawa yake kaman wanda tayi wani zunubin.
Yar dariyah deejah tayi tareda cewa.
"Naji to,yanzu dai nunamin inda yake,dan na manta ganina dashi na farko."
Tashi zainabu tayi daga wajen kwanon naman,daga gani bata ƙoshiba,dan sai kallon naman take.
Hanyar da sukabi wancan lokacin suka nufah.
Suna tafiyah deejah tana nazarin wajen a cikin kanta har suka zo bakin ɗakin.
Zainabu ce ta buɗe ta shiga,kafin itama deejah tabi bayanta.
Kaman koyaushe yana kwance kansa yana kallon sama kamar zai amsa duk abinda aka faɗamasa.
Raɗawa zainabu tayi a kunne,akan za'a iya bata waje daga ita sai shi?
Jugum zainabu tayi kafin ta kalleta.
"Eh zasu fita kiyi aikinki tunda sakaki akayi,amma minti goma kacal,daganan zasu dawo"
"Bandake za'a fitane ?"
"Ahah kiyi haƙuri,idan inason raina to dole na tsaya a wajennnan,dan har yanxu hajiya bata yadda dake ba,ina baki saniba ma duk gidannan akwai camerar tsaro"
"Okay shikennan,amma ki ɗan koma da baya,idan kina son rayuwar taki yanda kika ambata"
Fitowa da kwalbar deejah tayi a aljihun rigar ta.
Buɗewa tayi kaman mai tsoron karta fashe kafin ta fito da ganyen dayake ciki.
Fatsamasa tayi a fuska na farko,amma shuru bataga alamar motsiba.
Maimaitawa tayi har sau uku amma babu alamar komai,maida kwalbar tayi ta rufe kafin ta kalli zainabu.
"Zamu iya tafiyah nagama abinda zanyi"
Daga kai zainabu tayi kawai,mekenan tayi yanzu,itadai bataga wani canji a jikinsa ba,amma daga ganin fuskar deejah zaka san hankalinta ya kwanta,alamar tasamo abinda aka umarceta.
Fita tayi daga sashen bayan tayiwa zainabu sallama,in ba doleba kwata kwata batason abinda zai kaita wannan wajen. Kowanne sakan dayake bugawa na lokaci a wajen,bugawa yake da ƙara tsanar hajiya fulani,da kuma ƙaramata ƙarfin gwiwa na ɗaukar fansa.
Saida ta fitone wajen ƙarfe goma sannan kafin ta tuna da zancen da sukayi da emran.
Yar tsuka ta ɗanyi har zata tafi sashensu sai kuma taga rashin dacewar hakan,yanzu haka yana cam yana jiranta,ta faɗa a ranta.
A

20 / 33