Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
asibiti,badan komai ba saboda lalurin jinya ne da kuma babu mai taimaka masa sai ita a wajen.
Hakan take tsakanin mu dakai,kai marar lafiyane ni mai taimaka maka,saboda wani baya wajen,dan haka kasaki wannan ran daka haɗe.
Yana abu kamar mace,sa'a kaci ma dan kaine,da wanine ko kallonsa bazanyi ba,bare yayimin iyayi"
Ta ƙarisa kalmar ƙarshen ciki ciki tana cuna baki.
Kallonta yayi tareda cewa
"Me kikace?"
"Ni ba abinda nace,cewa nayi sannu kawai"
"Hmmm zaki faɗi gaskiya koba yanzu ba"
Ya faɗa yana saka hannunsa a cikin rigar,idonta ne yakai kan tsokar jikinsa yanda take juyawa duk sanda ya motsa jikinsa,haka kawai daji wani irin abu ya jira mata cikin zuciyarta
Saurin kawar da kanta tayi tareda yin gyaran muryah.
Zuba mata ido yayi da kuma jikinnasa wanda yanzu ya rufeshi da rigar.
Ganin ya gama saka hannun ne yasa ta juyo tareda balle masa maɗalllin rigar.
"Nakawo maka wani abune kaci kafin ya dawo,daga gani babu abinda kaci tun jiya?"
"Bazan iya cin wani abuba inba maganin nasha ba,ki bari kawai nagode"
"Sannu eemran,haƙiƙa nake ganin tawa rayuwar cikin chakwakiya,taka har tafi tawa ma"
"Meyasa kika faɗi haka"
"Duk naji abinda kuka faɗa kaida saleem,lokacin da maganar take dukan dodon kunnena,ji nake kamar a mafarki nake saurarensu,amma sainaga kaman ba kaiba yanzun,yanzu kafi kyau da fari akan yanda nake kallonka"
"Hhhh har kin ban dariyah,kinada surutu deejah wasa wasa,inbanda abinki da haka nake fita ai da yanzu an ganeni koh,ko bakya ganin ina kama da su jalal da mubarak har ma mahaifiyata a haka?"
"Eh nagani kam,dan inba a nan ɗakin naganka ba bazan ganeka ba nima sosai,amma fah ni zan ganeka"
"Ke ta dabance deejah,inaji a jikina,kema kinfi kyau yanzu akan sanda nake ganinki"
"Kai ka kalli hakan,amma ni babu abinda na shafa,kaine dai ka shafa"
Suna cikin hirarne saleem ya shigo ɗauke da ƙullin magani dakuma gwamgwamin madara a hannunsa.
Zubawa yayi a kofi tareda juye madarar a ciki itama.
Wani ruwan rubutu na tawada ya juye a ciki wanda ya taho dashi.
Miƙawa deejah kofin yayi dayake tafi kusada shi.
Kaman bazai shaba saikuma ya miƙa bakinsa tasaka masa kofin yashanye dukka..
A jiye kofin tayi tana yimasa sannu.
Rintse ido yake da alama ciwon bai gama sauƙa ba har yanzu,sai daga baya kuma gumi ya feso masa,baccin wahala ya ɗaukeshi.
Matsawa tayi gefe saleem ya gyara masa kwanciyarsa.
Share hawayen idonta tayi tareda cewa.
"Amma wane irin ciwone haka daga shan minti"
"Ba minti bane ai,wani abun tsafinne ta ajiye shikuma ya ɗauka yasha,koma menene da alama gubace"
"Amma bata sakeshi ba har na tsawon lokacinnnan"
"Yace mindai rabonda abin ya tashi masa tun shekara biyar shida baya,sai yanzu daya shigo gidannan tukunna,da alama abin yanada alaƙa da kusancinsa da nan wajen"
"Hmmm amma yakamata ayi wani abu,ba'a dunga kawai bashi maganin lafawarsa ba,idan kuma ya tashi babu maganin fah"
"Idan babu magani saidai yayi ta aman jini har na tsawon kusan sati,idan abin ya lafa sai a ƙaramasa jini,haka ake a lokacin baya"
Jinjina lamarin deejah tayi a ranta,tareda ƙara tsinewa hajiya fulani a ranta,ɗan ta ma kenan inaga wani kuma.
Tashi tayi tareda yiwa saleem sallama,akan zata dawo an jima idan ya tashi.
Da yamma wajen magriba deejah ta nufi sashen su eemran da kwanon abinci a hannunta, ranar da tunanin halin dayake ciki ta wuni,duk santa da cire hakan a ranta abu ya faskara.
A bakin ƙofar ta haɗu da saleem yana gyara takalmansa,gaisawa sukayi sai kuma tayi shuru batace komai ba.
"Lahh ki shiga mana ya tashi yanzu,sallah ma yakeyi"
Dama abinda take jira kenan,babu 'bata lokaci kuwa tasa kai ɗakin.
A zaune ta hangeshi ya bata baya yana kallon gabas,da fara jallabiya a jikinsa,da alama har wanka yayi.
Samun waje tayi ta zauna har ya idar da sallahr,juyowa yayi yana kallonta yanda ta tanƙwashe kafa tana kallonsa.
"Ya jikinnaka yanzu "
"Da sauƙi,ya aiki?"
"Ƙalau,yanzu kam zaka iya cin abinci koh?"
"Eh zan iya ci yanxu,amma bamai nauyi ba"
"Eh nasani"
Bude kwanon tayi ta zuba jallof ɗin dankalen turawan da tayi da hanta a cikin pilate,sai kamshi yakeyi na kayan kamshi.
"Deejah a ina kika samu abincinnan,nasan dai ba irin wanda ake bayarwa a gidannan bane"
"Eh nice na girka yanzunnan,bana gidan bane,na gidan shinkafa ce,nasan bazaka iya cinta ba,shiyasa na yi maka wannan "
"Amm...."
"Da kuɗina nayi eemran,koba zaka kar'bi kyautatawa daga gareni ba"
"Ahah bahaka bane deejah,naga yanayin rayuwarne"
"Ko kuɗina kenan zan iya yimaka,mutunci yafi kuɗi a wajena"
Matsawa tayi da pilate ɗin gabansa tareda sakamasa cokali a ciki.
Bismillah yayi tareda ɗiba a cokalin yakai bakinsa.
Hannunsa ya ɗaga tareda yimata alamar yayi daɗi,yanda yayinne yasaka ta murmushi tareda boye fuska.
Suna nan zaune yanacin abincin bai san lokacin daya kusa tashi dana kularba.
A sakawa na ukune yace mata ya ƙoshi.
"Uhm yanzu kam na ƙoshi,nasan na ɗan ci dayawa koh?"
Dariya tasaka masa tareda nuna masa kular,sauran kaɗan a ciki,shima zaro ido yayi cike da mamaki,yana ɗan majewa alama yaji kunya.
"Abincinne yayi daɗi sosai,shiyasa bansan lokacin danaci dayawa ba,na baki lambar yabo da wannan fannin.
Amma a ina kika koyi abinci haka.
"Abin sirrine,kaidai kawai tunda kayi santi ya wadatar,barina tafi tunda na tabbatar kaci dayawa.
Ina wayarka ko baka da itah,ɗan sarki guda mai jiran gado"
Zaro ido yayi tareda haɗe fuska,"rufamin asiri kina ganin jalal ido rufe yake neman sarautar"
"Wazai bashi kuma,yarintarsa kawai yake,inkai baka ra'ayi ma ga mubarak nan,duk da yana kwance amma inshaallah tunda an gano mai yake damunsa ,maganin ma bazai gagaraba"
"Hmmm allah ya tashi kafaɗunsa"
Wayar ya ɗauka ƴar ƙarama ya miƙamata,lambar wayarta tasaka tareda kira ya shigo cikin nata wayar.
"Gashi zan ƙiraka naji ya jikin in anjima,ka kula da kanka eemran,mukwan lafiyah"
Bata bari taji mai zaice ba ta bar ɗakin.
Ɗakinsu tashiga tareda ɗauko wata jaka a cikin kayanta ta fita daga ɗakin,lambun gidan ta nufa can wajen inda babu kowa ta zauna.
System ta jawo a cikin jakar ta kunna.
Hotonta a screen din da kayan bara a jikinta wanda ta saka lokacin dazata ɗauke brr. Shehu.
Password ɗin tasaka mai dauke da MABARACIYAH,kafin system ɗin ta buɗe.
Shedule ɗin aikinta ne kala kala a ciki kowanne da ranar yinsa dakuma wanda tayiwa,hotunan su amal da nemo itada madeena,take ta turawa wata photunnan.
Rubutu tayi a ƙasan photon kamar haka.
"Karamar itace wacce zaku kama gobe da safe,babbar kuma ƙarin bayani nakeso gameda rayuwarta,ku tabbatar kun samo kafinnna da gobe da daddare idan nazo zan ƙarba.
Sannna inaso ku samo min labarin babban dan sarkin garinnan junaid wanda ya bata"
Tana gama turawa ta shiga wasu file ɗin,abubuwa ne birjik,aikinda ta aikata harma da wanda ba ita ta aikata ba,dan hatta abubuwan dasu khamriyya sukayi tana dashi,tundaga aikinsu na farko akan Saifuddeen har wanda sukayiwa dr. Bukar.
"Ƙananan ƙwari"
Ta faɗa a hankali.
Magana taji an shigo ana yi a cikin lambun.
Kashe system ɗin tayi a hankali tareda leƙawa taga waye..
Hajiya fulani ce ita da wata mata,wacce zainabu tace mata ta hannun damanta ce.
"Kinsan menene silver,kwananann inajin jinin junaid yana kusa dani,sannan ran dodo yasake baci da rashin karisa aikin da banyiba a kan junaid ɗin,ni nayi zaton ya manta ashe bai manta ba,tsawon wannan lokacin yana ta ƙoƙarin shanye jininsa,jiya Damzuk yake faɗamin.
Na basu ruhin mubarak a matsayin na junaid amma sunyi shuru,su basu lasheshi ba su kuma basu sakeshi ba,sannan shi junaid basu ƙyaleshi ba"
"Toh shugaba yakike ganin abin zai kasance"
"Ni yanzu danasanin sallama mubarak nake akan junaid,zanyi ƙoƙarin nemo junaid na ƙarisa aikin akansa su ɗaukeshi,dan dama sunfi son jinninsa,shiyasa basu ɗauki mubarak ba.
Idan yaso saisu sakemin mubarak ,idan na kashe sarkin yanzu nasan bazasu yarda da jalal a matsayin sarki ba,amma kuma zasu yadda da mubarak,kinga na kawar da junaid da kuma ubansa,sainayi duk yanda zanyi shima mubarak ɗin na dunga juyashi akan mulkin.
Abin takaicinma dodo ya daina magana dani yanxu,idan nasamu wani wanda zai iya ɗakkomin ruhin da karfin gaske tsabbb zan aikata hakan"
"Hakan yaya amma hakan yanada matuƙar hatsari fah gashi......"
Shuru tayi bata ƙarisa ba jin motsin da ake a bayanta.
Waigawa tayi tareda ɗaga murya tace
"Waye a nan,koma waye ya fito idan yana son ransa"
Fitowa deejah tayi daga wajen bayan ta tabbatar tagama recording abinda sukace tasaka a jakarta,dama da gangan ta yi ƙara da domin su jita.
Hannunta ta ɗaga tana karkarwa cikin salon alamar shiga tsoro da fargaba.
"Ninnnnni.......bazan faɗawa kowaba kimin rai ranki ya daɗe"
Kallon kallon suke a tsakaninsu,yama akayi basu kulada mutum a wajenba harsaida suka buɗe sirrinsu.
"Zan taimaka miki wajen ƙwato ruhin mubarak idan kika min rai ranki ya daɗe"
"Mai take faɗa haka shugaba,barina yanke mata kai kawai da wuƙah"
"Ahah ƙyaleta silver yarinyar tana da ƙwarewa akan aiki,itace wacce na faɗamiki ta gano mai yake damun mubarak"
"Amma duk da haka taji abubuwa dayawa fah"
"Karki damu,batada ikon buɗe harshenta ga kowa,idan tayi hakan tasan sauran.
"Me kike anan wajen ke kaɗai"
"Amm nazo shan isaka ne kawai,bansan zakuzo wajen ba"
"Uhm naji,yanzu tunda kinji abinda bai kamata kijishi ba,kisa a ranki kin shiga tarkon da bazaki iya fitaba,aikin dazan baki shine.
Inason ki ganomin a cikin gidannan wanene kikega zayyi kama da yarima junaid ke a ganinki,sannan kinada damar fita kana ki shigo lokacin da kikd buƙata,saboda ko yana gefen masarautarne ba a cikinta ba.
Abu nagaba kuma inaso ki cigaba da binciken yanda za'ayi a ƙwato kuruwar mubarak daga inda aka ajiyeta"
"Naji ranki ya daɗe,amma da kin bani labarin a ina kuruwar take,dannan ji ƙarfin gwiwar yin binciken"
Harara silver ta watsawa deejah tareda cewa.
"Wannann ba huruminki bane jin inda take,dan an jawoki cikin aiki bashine ke nuna zakiyi abinda ranki yakeso ba"
"Na fahimta ƙaramar shugaba,zanyi binciken sosai,amma babu yanda za'ayi a fitarda shi daga cikin gidannan?"
"Fitar dashi zuwa ina "
"Inda kika yarda dashi shugaba,amma yin aikin a wajennan bazai yiyuba"
"Shikenan zan shiryah fita dashi ,lokacin da kike buƙatar hakan saiki faɗamin"
"Nagode shugaba"
Sunkuyar dakanta tayi har suka bar wajen.
Ɗaga ido tayi tana kallon fitarsu tareda ɗaga gira tana ƴar iskar dariyah.
"Saini deejah,natsinci damin sa'a a akala.
Da kunsan mai nake shiryawa da bakuyi saurin yarda daniba,taku ta ƙare idan nayi nasarar mallakar akwatinnan da kuma ɗauke mubarak daga gareku,
Banda su shashashu mutumin da zuciyata takeso zan faɗamuku inda yake domin ku kasheshi......!?"
Saida ta tabbatar babu mai kulada ita duhu ya fara kafin ta ɗauki jakar system ɗinta tabar wajen.
Da daddare wajen misalin karfe tara,har ta ɗaga wayarta zata ƙira eemran sai taga shigowar ƙiransa.
Ɗagawa tayi tareda gaisheshi da jikin.
"Wannan jikidai ya warke yanxu"
"Eh duk da haka ni hankalina bai gama kwanciya ba,sainaga ka fito aiki tukunna"
"Uhm gobe zan fito aiki ai,nima zaman basonsa nakeba"
"Idan zaka fito kayi wannan baɗɗa kamar sosai da sosai,yanda babu wanda zai ganeka"
"Meyasa kika ce haka?"
"Ahah babu komai,kawai hankalina bai kwanta bane"
"Uhm karki damu,gobe inason muyi wata magana idan kinda lokaci"
"Amma saida daddare,yanzu bazan iya haɗuwa dakai da rana ba,saboda wani dalili"
Jimm yayi kaman mai son faɗan wani abu,saikuma yayi shuru tarede cewa
"Shikenan yanda kikace,allah ya kiyaye koma menene,ki kula sosai.
Saida safe"
Daga haka ya kashe wayar.
Ta dan daɗe tana kallon wayar kafin ta ajiyeta ta kwanta,tasan da alama fushi yayi amma hakan yafi mata da hajiya fulani ta ganoshi.
Washa gari ƙarfe bakwai deejah tashiga ɗakin amal tareda buga gefen gadonnata.
Tashi tayi tana harare harare da kuma tsuka.
Bata kulata ba dacigaba da cewa
"Yakamata ki tashi yanxu ki shiryah,kar driver yazo yayi ta jiranku"
"To in ya jirani mai tsiyarki a ciki,nifah banason shishshigi,dan maita nace ki daina yimin aiki amma kinƙi"
"Saboda bake kika ɗaukeni ba shiyasa,wanda ta ɗaukeni intace na daina zan daina"
"Mtsswww mayyah kawai"
Buge deejah tayi da ƙarfi ta wuce banɗaki,kana ganin idonta cikeda bacci,da alama jiya tayi dare tana hira da yayarta.
"Kiyi ki gama,iya nayaune,nagaji da shanye wulaƙancinki,gobe idan ance kiyi bazakiyi ba"
A haka ta gama shiryawar tana zuba rashin mutunci..
Jakarta ma ƙin ɗauka tayi sai deejah ce ta riƙe mata.
Saida tashi motar kafin ta bata ta ɗora akan cinyarta.
Saida taga ƙulewarsu kafin ta koma gefe ta ƙira waya.
"Ku shirya sun fito daga gida,karku manta fah iya ita kaɗai zaku ɗauke,banda yaron..........shikenan idan kun kammala ku ajiyeta ina zuwa da daddare"
Tana sauƙe wayar suka haɗa ido da yarima jalal yazo wucewa,saurin juyawa yayi zai sanja hanya..
Fito ta fara da bakinta wanda hakan yasashi juyowa,da idonta ta nuna masa wani corridor.
Binta yayi a baya har suka wuce babu wanda ya gansu.
"Inason ka kawomin akwatinnna a yau,dan gobe aikinsa zai fara,idan baka kawomin ba ka tabbatar iyanxu kana sume irinna ɗan uwanka.
Zata fita da yamma,bazata fita da akwarinba yau,dan haka ka ɗaukomin!!"
"Tam zan ɗauko ranki ya daɗe"
"Hhhhh ɗan sarki mai jiran gado yana faɗawa mai aiki ranta da yadaɗe"
"Amma bazaki tashi mubarak ba ina yanda mukayi alƙawari koh"
"Hmm kaita mubarak kake koh,ita kuma uwarka ta kuɗurin kasheku takeyi,yanda bazaku kawomata matsala,musamman ma kai da tasan fankone,kawo wa akwatinnan shine tserar da ranka dazakayi daga hannunta"
Mazari jikinsa yafara,gumi yana tsatstsafo masa,saurin barin wajen yayi domin fara zartar da aikin.
"Hmm ana son duniyah ana tsoron mutuwa,haka mutane muke"
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
Taku_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
43••44
Assigment ɗin ta batasamu damaryi a gida ba tafara a cikin motar kafin su isa.
Jitayi motar ta tsayah yayinda suka shiga wani titi mai shuru babu alamar motsin mutane.
"Kai saleem menene naga ka tsaya lafiya?"
"Ina kuwa lafiyah gimbiya,wasu matane masu jajayen kaya a gabanmu su uku,kuma dukkan su riƙe suke da bindiga"
"Me bindiga?,mai mukayi musu toh?"
"Taya zan sani,alama suke mana dai karmu kuskura mucigab da tafiya"
manyane matan sosai su biyun,sai kuma ɗayar bata ƙarisa girmansu ba.
Gidan baya suka bude tareda zaro amal daga cikin motar,ta faɗi a ƙasa farin kayanta ya baci da jar ƙasa.
"Kai driver ja motarka ka tafi,mun ɗauki abinda muke biɗa"
"Amma dan allah ku rufamin asiri,makaranta zan kaisu,bansan mai zance ba idan aka tambayeni a gida,ku taimakeni"
"Kai ka rufe mana baki komu ruguruguza kanka yanzu nan,ina ruwanmu da mai zaka ce,wannan kaita shafa ba mu ba"
Babbar cikinnasu tana gama faɗar hakan suka ja amal kiiiiii zuwa cikin jejin wajen.
Bayyi kasa a gwiwa ba shima ya fito daga motar tareda bin bayan su inda sukayi..saidai wayam babu su babu alamar su.
Cije yatsa yayi tareda juya akalar motar zuwa gida,dan abdul sai ihu yake yana ƙiran sunan addar tasa da aka samfe da ita.
Yana yin parcking motar a harabar gidan abdul yafito daga ciki, tareda runtumawa da gudu sashen mahaifiyar tasu.
Kuka yake yana faɗin abinda yake faruwa kan gari ya gari,kafin ya isa gareta har labarin yazaga ko ina ƴan kidnapping sun ɗauke amal.
Wasu na allah ya ƙara,wasu kuma suna alhinin abin.
Salati da sallallami hajiya saratu tafara,tareda maganganun da ba kansu ba ƙasansu.
"Ya ilahi,hikuma jarabawar ɗaukemin ƴaƴa haka ta ganni?,an ɗaukemin ƴaƴana biyu kwanan su biyu da haihuwa ,yamzu kuma ita wannan an ɗauketa,yanzu hakama wanda yarabani da ƴaƴana tun suna tsumman zani shine ya rabani da wannan ma,bazan taba yafewa mai kwashemin yaƴa ba.
Sai zan ɗaga magana ace nayi shuru,gidan sarauta bayason a dunga buɗe irin wannan magana,to da mai zanji a rayuwar nan.wayyyoooo"
Yadiko lami ce ta riƙeta ganin tana ƙoƙarin zarewa,yayinda ita kuma deejah ta tsayah tana kallonta,ganin a sanadiyyar koyawa yarimyar hankali,da alama ta tabo mata gyambon dayake mata kaikayi a cikin zuciyarta.
"Kiyi haƙuri haka hajiya,inshaallah ba irin wancan bane,wannan za'a ganta,ninafi hasashen masu ɗauke mutanene suce a basu kuɗi,zakiji sunyi magana a yau inshaallah.."
Itadai hajiya saratu batace komai ba,abinda ya isheta ya isheta.
Madeenah ce ta take kukan ɗauke ƙanwartata ta dubi hajiyan tareda cewa.
"Ummah wane ƴaƴa aka ɗauke kuma"
Kallonta tayi da ido jawur kafin tace.
"Yanzu ba lokacin magana irin wannan bane,nidai a fito min da ƴa ta nakeso kawai"
Rabewa deejah tayi tabar falon,kana ganinta kasan tunani take saƙawa a ranta,kona menene oho.
Shuru akayi ta jiran ƙiran wanda suka ɗauketa amma babu ƙira ba alamarsa.
Kowa a gidan yayi jugum yana jiran abinda Allah zayyi,duk da wasu a cikinsu ganin idone yasa sukayi,dan a ransu murnar bacewarta suke,dan dama ta damesu.
A bangaren yarima jalal kuwa cikin fargaba da bugawar zuciya ya nufi ɗakin mahaifiyartasa.
Kowanne taku dayake zuwa ɗakin yasan yana kasada ne da rsyuwarsa,saidai ya zayyi ya jefa kansa cikin halin tsaka mai wuyah,rana zafi inuwa ƙuna.
Abinda yake sakawa a ransa shine,gwanda ya kamu a hannun uwarsa daya kasa aiwatar da aikin da deejah tasaka shi,saboda koba komai hajiya fulani uwarsa ce,kuma yasan shu'umancinta.
Amma ita deejah bashi da masniyar mai zata iyah aikatawa,kuma babu alaƙar data haɗashi da ita.
Da wannan tunanin ya isa gaban gadonnata tareda tsugunnawa yana kallon cikin.
Wani wajen ya danna gadon yayi sama,ya fidda akwati na zinare an yi masa ado.
To anan gizo yake saƙar,taya zai fito da akwatin ya maye gurbinsa dana hannunsa. Bayan baisan password ɗin ba.
Dannawa ya farayi yana saka sunan da kuma abinda yasan zai iya dadai,amma babu wanda yayi daidai.
'J' yasaka sai yaga yayi dadai,sunansa ya saka amma yaƙi buɗewa,sunan yayansa ne ya faɗo masa a rai,wato JUNAID ga mamakinsa sai wajen ya buɗe.
Dama har yanzu bata manta dashi ba,yanda yasani itace ta cutar dashi,to kuma ya akayi sunansa ya zamo mabuɗin sirrinta,tunanin ya kawar a aransa tareda buɗe abinda yake gabansa.
Fitar da akwatin yayi sak irinna na hannunsa,ya akayi deejah ta gane irinsa oho,Allah masani.
Mayarda wanda deejah ta bashi yayi wajen,kafin ya fice daga sashen da sauri,kafin tazo ta sameshi tayi wainarsa.
Ƙara wayar tayi,tana dubawa taga ƙiran jalal,da sauri ta ɗaga,
"Hello ka ɗaukomin akwatin ?"
"Eh na ɗakko,kizo sashena ki karba,sannan ki tunada alƙawarina"
Tana kashe wayar ta nufi sashennasa,burinta shine tayi ido biyu da abinda ta daɗe tana burin mallaka..
Bata ganshi a falo ba,dam haka direct ta wuce ɗakinsa,dan taga ƙofar a buɗe,da alama yana ciki.
A bakin gadonsa ta sameshi a zaune,gefensa kuma akwatinne yana shafa jikinsa,wani murmushi ya ɗago da wurga mata ma shu'umai,lokacin data shigo ɗakin
"Na cika miki alƙawarinki na ɗakko akwati,saura abu ɗaya shine ki cikamin naki alƙawarin na bani kanki a yanzu,da fatan dama da shirinki kika zo"
Itama dayake jar wuyace idonta tsar akan akwatin,da alama wani abun take saƙawa.
"Sumail ka dauki akwatin ka tafi dashi ketare ƙasar nan,dan idan yana cikin ƙasar nan zata iya bin diddiginsa da shu'umancinta,ka lalata tsafinta dayake cikinsa,amma karka share sunan mubarak tukunna,dan idan ka share nemo rauhinsa a wajensu zayyi mana wuyah"
Tana gama faɗan hakan akwatin ya 'bace 'batt a ɗakin tamkar bai taba wanzuwa ba.
Waige waige jalal ya fara yana neman inda akwatin ya shiga,kenan aljanace ita duk tsawon lokacinnnan bai sani ba?
Matsawa ya farayi yana girgiza kai ,ita kuma ganinsa cikin hakan sai ya sakata nishaɗi,koba komai tayi wani abun dazai ƙaramasa tsoronta.
Takawa take a hankali shikuma yana da baya,har taje bakin gadon da niyyar hawa,shikuma har yakai karshen gadon.
"Haba yarima mai