Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃
15••16
Abun ne nake jinsa tamkar a mafarki,shikenan khamriyyyah ta tafi,bazan sake ganinta ba,duk da tace zata dawo amma ban yadda da wanann zancen ba,duk yaron da'aka tafi dashi baya dawowa,nasan ta faÉ—aminne kawai dan na saki raina.
Ina cikin tunani khairiyya ta dafani,É—agowa nayi na kalleta ganin itama damuwarce a ranta.
"Sabrah nasan kina kewarta koh,nima ina kewarta sosai,zata iyah komai damin mu,duk da ƙarancin shekarunta amma zata iyah tukarar abinda yafi ƙarfinta domin masoyanta."
"Hakane khairi,muna mata fatan alkhairi a duk inda take"
Bayan tafiyar khamriyyah da sati É—ayah inno tasamu baba shehu tayi masa magana akan ya kaimu makarantar kwana,nasan tana tsoron muma ta rasamune,ko kuma tana so murage kewar da muke ciki.
Bayan tayi masa bayani kuwa ya amince da hakan,akan xai kaimu makarantar su anty juwairah wanda ita paper suke suna aji ƙarshe na matakin secondry.
Munyi murna sosai amma ba kaman idan khamriyyah da maryam suna tare damu ba.
A satin akayi mana shriri muka tafi,dan har an fara karatu.
Ikon allah mai yadda yaso,da farko muna tunanin mu uku zamu tafi,sai gashi ashe mu biyune zamu tafi kawai.
Kaya dayawa inno ta haɗa mana,su sukari,gari,ƙarago,da kuma ƴar madara,saboda in mukaji yunwa mu ɗan saka a cikinmu,duk da bamu san makarantar kwana ba amma kuma muna jin labarin wuyarta.
Saidai duk da haka abinka da yaro mai son tafiyah makarantar kwana,munason zuwa.
Baba shehune ya kaimu har makarantar da kansa,tundaga bakin ƙofar makarantar muke ƙaremata kallo,finally yau gamu a makarantar kwana zamu shiga cikinta,waiwayawa nayi na kalli khairyyah,itama niɗin take kallo tana dariyah.
Office É—in principle ya shige damu tareda kayanmu,muna zaune suka gama magana da malaman,aka bashi wasu takardu,yasaka hannu da sauransu,mudai namu idone kawai.
Bayan sun gamane aka aika a ƙirah Juwairah usman,daga baya kuma mai aiken tadawo wai bata nan suna paper.
"Toh kuna son makarantar kwana gashinan na kawoku,sai ku dage kuyi karatu,dan kun fi kowa sanin shine gatanku a yanzu.
Yayartaku tana É—akin jarabawa,idan ta fito zata zo ta É—aukeku ku jirata a nan,ni zan tafi sai nazo muku visit.
Kuka khariyyah tafara tana ƙiran inno,tsayawa yayi yana kallonta tareda rarrashinta,amma ganin zata bata masa lokaci yafa yi mata faɗa.
"Jimin sakaliyar yarinyah,idan bazaki zauna a makarantar ba kizo mu tafi toh,duk uwarku ce ta lalata ku"
Gani ya balbaleta da masifa tayi gum da bakinta,dariyah nayi ƙasa ƙasa.
Haba dama khairiyyah ta iyah sakalci da kuka,inba hakan yayi mata ba bazatayi shuru ba.
Sai can wajen ƙarfe huɗu anty juwairah ta fito daga paper,duk da muna son zuwa wajenta amma munsan kwanannan zata tafi ta barmu mu kaɗai.
Da gudu ta taho inda muke tana ware mana hannu,muma da sauri muka tashi muka tareta muna dariyah.
Rungumemu tayi dukkanmu,
"Iyeee yaran inno sun girma sun shigo makaranta,ina sauran to naga ku kaÉ—ai"
TafaÉ—a tana dudduba bayan mu.
Murnar da muke muka daina muna wawwara idanuwa,dan bamu sam ma mai zamuce mata ba,raahin daÉ—i kam dole tajishi.
"Uhm.....anty juwairah dd..dama wasu sun É—auki maryam da kuma khamriyyah,wancan watan"
Sakin mu tayi tareda yin jimm,idonta ne yayi ƙwal ƙwal kaman mai shirij kuka,sai kuma tayi saurin kawar dashi tareda jan hannuwanmu.
"Ssshikenan kuzo mutafi ku huta kafin gobe ku tafi aji koh?"
Bin bayan ta mukayi tana tafiyah,shuru babu wanda yace komai,kowa da abinda yake saƙawa a ransa har muka isa hostel ɗinsu.
Shiiya mana kayanmu tayi a kwanar ta,tareda kaimana ruwan wanka da kuma abinci.
Ƴan riguna ta fitar mana a kayan muka saka da daddare,anata hira tana nuna mu ga ƙawayenta,cewar ga ƙannenta sun zo.
"Hmmm naji kunyi shuru baku bani labarin abinda ya faru ba,ina bakin surutun koh ya mutu kai?"
Dariyah nayi tarede 'boye fuskata,tunda muka zo kam mun kasa cewa komai.
Labarin abinda ya faru na bata,tareda sanar mata yanda za'a tafi da khairiyyah amma khamriyyah tace ita ta yarda a tafi da ita
"Inno tayi ƙoƙarin cewa ta zauna,amma taƙi amincewa,a cewarta bazata juri rabamu da inda muka tashi ba,sannan bataso a rabani da ƴar uwata,itace ya kamata ta tafi ba muba"
Dafa ni anty juwairah tayi idonta ya kawo ƙwallah tacd
"Allah sarki maryam,kusan ni nayi rainonta,yarinya ce mai hankali sosai,ina addu'ar allah yasa ta samu gidan kirki dazasu riƙeta da amana.
Khamriyyah kuma nakasa cewa komai,yarinyar tasha wahala a rayuwarta da take buƙatar wanda zasu tallafeta,duk da ita mutumce da bata nuna wahalarta,burinta kullum ta 'boye tace babu komai,saidai ma ta tallafeka.
Duk da É—aukar mutum a gidanmu kamata yayi a masa murna idan yasamu gidan kwanciyar hankali,saidai har cikin raina ina fatan khamriyya ta dawo garemu,amma kuma ina mata fatan allah yabata farin ciki,allah yasa su inganta rayuwarta ta manta da abinda yafaru da rayuwarta a baya"
Sake rungumo mu tayi muna ƙara yin kukan rashin ƴan uwannamu.
Hankalinmu kwance muke rayuwa da anty juwairan,babu wanda yake dukanmu ko kuma saka mu aiki,saboda muna ƙannen ta,rayuwar daɗi sosai.
Satinmu biyu da zuwa ita kuma anty juwairah ta gama makarantar,bayan an ga jarabawa anyi bikin candy da komai.
Sabon kuka muka kafa lokacin dazzata bar makarantar,khairiyya kam ma cewa tayi zata bita su koma gida,saida taga dole sai ta zauna kafin ta haƙura.
Tun a daren muka fara ganin sanji a makarantar,ashe dama sauran ɗaliban da su anty juwairah suke ƙasansu haushin mu suke ji sosai.
Kasancewar kowane ɗalibi yana punishment mu bama yi,da daddare muna kwance sai jin zubar ruwa nayi akaina mai shegen sanyi,zaburah nayi na tashi tareda sauƙe ajiyar zuciyah,wanda ashe itama khairyyah haka tayi.
Wata bufurwace zata kai anty juwairah a haife da bulala a hannunta.
"Hhhhh wato ku ga ƙannen sister juwairah koh,kowanne yaro zayyi aiki amma ku kuna zaune,dan ubanku wa kuka fi a makarantar nan"
"Kiyi haƙuri" shine abinda na samu damar faɗa.
"Haƙuri,naibishi da gudu ba wando,ƴam bantan ƙaniyah,ke Lawisah kwantar minsu yanzunnan,kowacce sai na yi mata bulala sha biyu,sannan kuma idan ku dawo daga aiki gobe akwai wankina yana nan zakuyimin shi"
Duk haƙuri damuke bata haka tayi biriss damu aka kwantar mu kaman yanda ta umarta.
Bulalar take É—agawa tana zambaÉ—a mana muna ihu,bata daina ba har saida tayi mana adadin yanda tace tukunna.
Fita sukayi daga É—akin bayan sun gama zagemu tass,yaran dasuke É—akin babu wanda yayi tari,duk da idonsu biyu sunga mai ya faru,saidai babu mai ikon cewa komai.
Ajiyar zuciya muka cigaba dayi har bacci yasake É—aukemu.
Da safe da wuri muka tashi,jikin mu yayi tsami saboda dukan da muka sha a wajen sister Lubabatu,da mukaji ashe itace labour É—in lokacin.
Gugu gugu haka mukayi wanka da ruwan sanyi kafin muka saka uniform É—in mu zuwa aji.
Bayan mun taso kuwa hostel É—in sister lubabatu muka wuce,yin wankin datace zamuyi jiya da daddare,haka babu imani tasaka mu kneeldown a rana na kusan awa guda kafin ya bamu wankin.
Lokacin babu ruwa a makaranta ya ƙare,haka muka yi tafiyah mai nisa a inda aka kwatanta mana kafin muka samo muka wanke mata,duk jikinmu a tsorace yake karmu sake wani laifin.
Lallai lokacin da anty juwairah take nan ba'a makarantar kwana muke ba sai yanxu tukunna.
Watan mu guda babu itah har mun saba da duk wata wahala da ake gallazamana,mun bi sahun yaran wajen muma.
Kwannan baba shehu yazo mana visit,ji mukayi kaman mu bishi gida muce mun fasa karstun,amma babu halin yin hakan,tunda muka fara toh dole sai mun ƙare.
Sannan kaman yanda kowanne yara suke jurewa muma dole mu jure mu saba da hakan.
Lokacin da mukayi hutun zango na farko murna kaman zata kashemu zamuje muga gida,kowa ranar kasa bacci yayi ana gobe hutu.
Kaman yanda baba shehu ya faɗa mana kuwa ƙarfe sha biyu tayi masa a makarantar mu,kasancewar dole sai ya taho daga garinmu zuwa cikin katsinan,mudai sunan muna cikin birni,amma bama zuwa bakin get sai ranar dazamu bar makarantar zuwa gida.
Tundaga mota da muka tsayah khairiyya bata tsayaba tayi cikin gidan da gudu tana ƙiran inno,nice ma nayi ɗan dauriyar ɗaukar jakata..
Ganin khairiyyah ta É—ale inno nikuma na É—ale anty juwairah wacce itama taji muryar khairiyyah ta fito.
Dariyah aka dungayi tareda bada labarin yaushe gamo,inno ce ta katsemu ganin labarin bazai ƙare ba,
"Kunga ya isa haka,muje kucire kaya kuci abinci ku huta tukunna,kafin koma menene sai ku faÉ—a"
Wayyo gida daÉ—i rahama,kowa yabar gida gida ya barshi kam,can ayita dukanmu ana samu aiki,nan kuma yimana komai za'ayi.
Result É—inmu muka fitar daga jakar,tun kafin na gama cirewa naji anty juwairah ta fizgeshi daga hannuna,tana dariyah.
Kallona tayi tareda dagani sama lokacin data nawa naci.
Nice nayi na biyar 5,khairiyyah kuma tayi na bakwai 7.
Saidai tafini cin math da computer,don ranta yana son subject É—in sosai.
Murna inno tayi sosai itada sauran iyayen mu ganin mun maida hankali mun dage sosai a karatun.
Toh fah da hutu ya ƙare aka ce mana wani satin komawa duk sai muyi wani iri,dan shi deen har ya koma jiyah,shikam dai to ba ƙoƙari gaskiya,dan na kusan hamsin yayi a cikin su sittin.
Haushi maman yara taji sosai,dan har dukansa tayi.
Haka babu yanda mukayi muka tattara muka koma aka cigaba da gashi.
_bayan shekara uku_
Abubuwa da dama sun faru,ciki harda jssce da muka zana,yau muke shirin tafiyah gida yin hutun wata uku.
Yanzu mun saba da makarantar sosai,munyi ƙawaye sannan munyi suna saboda ilimin mu da kuma ƙarewa,da rawar kai komai muna ciki.
Suhaila na kalle wacce take haÉ—a kayanta nace
"Sully gobe sai a kama hanyar zariyah kenan"
"Ai wannan dolene sabrah,ina zan tsayah,za'aje ayi dogon hutu kafin mu dawo kuma a cigaba daga inda aka tsayah"
"Hakane kam allah ya kaimu lokacin da rai da lafiyah"
Kaman yanda muka saba shigowa gida koyaushe yau kam bamuyi wanann gudun sosai ba,dan ba laifi an fara girma da kuma hankali,saidai murna kam baza'a rasa yi ba.
Leƙawa nayi banga anty juwairah ba,sanann wani daban shima baba shehu ya tura ya ɗaukomu.
"Ah inno banga anty juwairah na ina take?"
"Hmmm yanzu kuka dawo ku huta tukunna koma menene sai kuji daga baya"
Gabana ne yayi rass ya faɗi,mai yake faruwa haka,daga ganin yanayin mutanen gidan kasan ba ƙalau ba kam.
Saidai tunda inno tace zamuji daga baya toh bamuda hurumin takurata sai munji a lokacin,duk da kuwa munason jin mai yake faruwan.
Wanka na farayi sanann na jona khairiyyah a wajen cin abinci,lakutar abincin nakeyi nakasa ci sosai,zullumi da fargaba gaba É—ayah su suka cika min kirjina.
Tashi nayi daga waken cin abincin nasha ruwa tareda zubawa inno ido,ko ban ce komai ba tasan mai muke son ji daga bakinta.
Ajiyar zuciya tayi da alamun bataso wannan yazamo abinda zai tarbemu ba bayan dawowar mu,saidai yazama dole mu sani saboda muma É—aya ne daga cikin ahalin gidan.
Ɗaga ido tayi ta sauƙe akaina,dan tasan abinda zata fada zaifi tabani fiyeda khairiyyah.
"Sabrah inaso ku kwantar da hankalinku idan kukaji abinda zance,banaso kusaka damuwa aranku tundaga yanzu da ƙuruciyarku.
Nasan kunsan wasu sunzo sun tafi da maryam daga garin katsina koh akan zasu riƙeta?........
Dokar gidannan ne dole idan wanda basuda yara ko kuma suna buƙatar riƙe marayu indai sun cika sharuɗai to dole mu miƙa musu ɗan da suka buƙaci ɗauka,wani hankalinmu yana kwanciya da yaayinsa,wanin kuma saidai muyi tayiwa yaron addu'a a sallolinmu kan cewar allah yabashi ikon zama dasu cikin sauƙi.
Yanda ta faru da maryam yana É—aya daga cikin wanda muka yarda dasu sanann hankalinmu ya kwanta damu basu amanar ta.
Saidai kash!,abinda kake gani a zahiri bashine yake faruwa a gaske ba.
Ashe wanda suka É—auki maryam ba ma'aurata bane wanda basuda yara,hasalima basu san juna ba aikine ya haÉ—asu,wanda aka biyasu domin su yishi.
Ba ɗaukarta sukayi domin su riƙeta ba,ɗaukarta sukayi domin su sayar da itah ga wasu mutane daban,saidai har yanzu ba'a gano wanda suka sayarwa itaba"
Tashi nayi zumbur na miƙe ina kallon inno tareda tariyo abinda ta faɗamin ɗin yanzu,mai take son cewa,sayarwa ƴar uwarmu suka sayar kaman wata akuyah,mai mukayiwa mutane muke ganin wannan ƙalubalen,yanzu rashin iyaye da mukayi laifi ne kenan? Shin mune muka kashe iyayen na mu da kanmu ko kuma muka gudu muna jinjirai?.
Yanzu da a gaban iyayenta take shin zasu samu kwarin gwiwar zuwa kawai su É—auketa dan kawai su sayar ta?.........wannan abin dame zan fasaltashi a cikin raina tukunna,wayema ya siyeta sannan tana ina mai ya sameta,ashema bangama jin labarin ba daga wajen inno.
"Inno ya akayi aka gano hakan toh,sannan ina take"
Yanayin fuskarta ne ya ƙara sauyawa dataji tambayar danayi mata.
"Hmmm ƴar nan ina kuwa take banda gidan ta na gaskiyah inda kowa dolensa sai yaje,tsawon shekara uku da ƙarbarta a wajensu take,tana shika shekara sha biyar suka sayar da itah,bamusan ina bane,saidai jikinta ya nuna tasha azaba sosai kafin a kasheta,sanann da aka duba gawar babu ƙodah ko guda ɗayah a jikinta,wanda hakan yake nuna inaga masu tsafi ne suka kasheta.
Antynku ce wata biyu da suka wuce ta gano gawar da'akayi da É—orawa a facebook ko akwai wanda yasanta?,da gudu tazo ta nuna mana hoton,hajja kam hadda sumanta data gani .
A nan ne muka nunawa baba shehu,a ranar suka tafi birnin katsinnan itada shi.
Office É—in Æ´an sandan da suka tsinceta suka je,tareda bada labarin yanda suke da itah da kuma yanda aka taho da itah nan.
Bincike akayi tayi ganin wanda suka santa sunzo,har aka samu makarantar da take zuwa da kuma gidan mariƙannata.
Saidai babu kowa a gidan sun gudu ba'a gansu ba.
Duk binciken da'akayi ba'a samosu ba,saidai dayake munada hotonsu lokacin da suka zo nan to sai aka É—orashi a media koda wanda yagansu,bayan an faÉ—i lbarin abinda suka aikata.
Zancen danake muku an samu labarinsu a garin bauchi,nan da nan kuwa aka kamosu zuwa garin katsinnan bayan an baki da Æ´an sandan can.
Tun daga lokacin ake ta shari'ah ana bincike akan hakan,wancan satin sunyi zama aka É—aga shi sai yau.
Abinda yafi bada tashin hankali ma ashe ba iyah maryam kaɗai suka sayar ba harda wasu yara guda biyar,kuma dukkansu an samu gawar su babu ƙoda da wasu sassa a jikinsu,lokacin da mukaji labarinnan munyi kuka har mun gaji,musamman idan mutum yaga yanda aka wulaƙanta gawar,dan a binciken an tabbatar ansha kwanciyah da ita babu adadi......
Yanzu dai suna can wajen shari'ar kuma ance a yau za'a rufe case,É—in muna fatan tunda shaidu sun fito to a hukuntasu hukunci mai tsanani,daidai da abinda suka aikata.
Kallon inno nake wadda take shabar kuka tun sanda ta fara bada labarin,saidai ba iyha ita kaɗai take buƙatar rarrashi ba,dukkanmu kowa yanaso,musamamn ma ni da bana iyah yin kuka saidai abin yayi tacin zuciya ta.
Wani yawu nasamu na haɗiyah wanda tun ɗazu ya riƙe a maƙwagarona yaƙi wucewa,sai yanzu nasamu ya tafi.
Tafiyah nake a hankali ina ƙokartawa dan kada na faɗi har na samu damar zuwa bayan ɗakunan mu inda babu kowa.
Zama nayi a wajen tareda tsurawa wani waje ido nagagara ɗaukewa,wanda yake kallona a lokacin zai ɗauka wajen nake kallo,saidai haƙiƙanin gaskiya hankalina yana wani waje daban ne. Na dulmiyah cikin kogin tunanin rayuwar da mukayi da maryam ɗin,da kuma abinda inno tafaɗamin ya faru da itah.
Halayenta nake tunowa na shuru da kuma koyaushe cikin murmushi,amma duk da hakan dan rashin imani irin na É—an adam aka keta mafarkanta,aka keta maraicinta,aka keta darajarta sanann kuma aka keta rayuwarta gaba É—aya.
Fyaɗe,kisan gillah,azabtarwa da kuma cire sassan jikinta,dukka akan ƙaramar yarinya marainiyar Allha?"
Wani tafashashshen hawayene ya zubomin mai ɗumin gaske akan kuncina,dan na rasa mai zanyi ma naji sauƙi suyar da kirjina yakemin.
Share hawayen nayi ganin hakan babu abinda zai ƙaramin,sai bata lokaci kawai,wanda ta mutu ta riga ta mutu,tana can insha'allah ta dace da gidan ƙarshe,tunda zaluntarta akayi tayi tsawon zamanta dasu.
Tashi nayi na fito daga wajen,inda na hango anty juwairah ta shigo gidan itada baba shehu.
Ƙarisawa wajensu nayi,duk da zuciyata tana tsoron abinda zanji daga garesu amma kuma inaso najin.
Kallon yanayin fuskarta ya tabbatar babu alamar nasara a shari'ar,saidai duk da hakan ban gazaba wajen tambayarta mai yake faruwa.
"Ant.....ty... Juwairah meya faru an zartar musu da hukunci"
"Uhm sabrah yaushe kuka dawo? Ba haka bane bari muyi sallahr la'asar tukunna kinji"
Daga mata kaina nayi tareda nata hanya ta wuce,shikuma baba shehu ya tafi gidansa.
Sai a wajen cin abincin dare inno ta tambayi anty juwairah mai yake faruwa,ganin taƙi faɗamusu komai.
Kallonmu take da alamar batason faÉ—a a gabanmu.
"Anty juwairah muma muna son jin mai yake faruwa,maryam Æ´ar uwarmu ce dan allah ki faÉ—amana mai yake faruwa"
"Inno bamu da yanda zamuyi,idna kanada kuɗi to kanada komai,zakayi abinda kaga dama babu wanda zai taka maka birki,marar kuɗi kuwa,ko kisan kai aka masa bashida ikon komai,to ina ga kuma wanda shi ko iyaye bashida bare kuma zancen kuɗi,muna gani ƙiriƙiri shaidu sun nuna Haƙiƙa tabbas gaskiyane ankama su sa sayarda yaran,amma kuma shari'ah ta murɗe aka sakesu tamkar basuyi komai ba........."
Kuka ta rusa wanda hakan yasa ta kasa ƙarisa maganar datakeyi.
Matsawa kusada itah nayi na riƙeta ina matse nima nawa idon.
Jan numfashi tayi kafin ta cigaba da maganar.
"Maryam ta tafi,sun kasheta sun tafi a banza,jininta ya zuba an kasa yimata adalci,saboda wanda sukayi sunada É—aurin gindin manya."
Haka tashigaba ta kukanta ta maganganu amma babu wanda yasamu ƙwarin gwiwar hanata a cikinmu.
Zaman makoki mukayi iyah mu kaÉ—ai,dan babu wanda ya santa ma bare ya yazo mana gaisuwa.
Kowa idan ka ganshi yayi wani iri,anty juwairah kam ma ko magana sosai batayi,ko yaushe tana ɗaki,nasan ba komai yake damunta ba sai yanda tanaji tana gani duk koƙarinta amma aka kasa yimata adalci akan ƙanwarta,saboda batada galihu ita marsiniyace wacce batasan suwaye iyayen ta ba.
Bayan wata É—ayah da case É—in maryam mun fara komawa dadai,saidai addu'a da muke yi mata a kowacce sallah.
Tareda fatan allah yasa hutunta kenan.
Tiren dayake hannuna na jefar fass a ƙasa ganin wacce take tsaye a gabana.
Abaya ce a jikinta baƙa ta yafa mayafin akanta,wanda hakan yaƙara fito da farar fatarta mai kalar golden.
Murmushi take yimin da dan karamin bakinta,kana ganin murmushin zaka É—auka Æ´ar shekara ashirin ce da wani abu takeyi ba Æ´ar shekara sha shida ba.
Takawa na farayi a hankali zuwa gareta,yayinda zuciyata take jiyemini kar ko mafarki nakeyi zan farka.
Faɗawa nayi jikinta da ƙarfi tareda sakin kukan farinciki.
"Khamriyyah!!!!"
Na fada hankali,itama rungumenj tayi ta baya tareda sakin dariyah mai ɗan ƙarfi
"Sabriyyah menene kuma na kukan,na cika alƙawarin dana ɗauka miki na cewa zan dawo ,gashi kuwa na dawo gareku,bakiyi farinciki bane kike kuka?"
Sakin ta nayi tareda kai mata dukan wasa ta tare hannuna.
"Harma zakice bana farinciki,tambaya ma kike koh"
"Meyasa bazan tambaya ba,naganki wani iri kaman bakyason dawowa tah"
ÆŠan gajeren murmushi nayi kafin nasake kallon ta.
"Khamriyyah kinyi kyau kin sanja sosai kaman bakece wannan yarinyar ba"
"Eh ke É—in kece wanann mai shegen tsokanar wacce kullum in anyi faÉ—a toh da ita ake"
"Hmmm to naji, yakamata mu shiga ciki,dan daga gani babu wanda yasan kin shigo gidan koh.
"Eh babu wanda ya ganni kece ta farko,ina anty juwairah da kuma khairiyyah"
"Suna ciki dukkansu muje