Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
su tuntubi wanann number
+227 97 21 16 15
Naƙara shafin free har zuwa page 20,zuwa lokacin inka shiryah kazo a fara dakai ranar juma'a.
_____________________
Assalamualaikum barkan mu da wannan lokaci *ABMAR COLLECTION* ina nan na kawo muku kayana masu kyau da sauki👌🏻
KAMAR SU:-
Atamfa, Atamfa Mai golden,💁♀️
Lace ,Shadda lace
Yadi, Shadda
Abayas💥
Kids wear
Takalmi, jaka, mayafai💥
Sleeping dress, kananan kaya na gayu🔥kayan kitchen,
DA DAI SAURANSU ina Sokoto ina tura kaya ko ina da izinin ubangiji mai son kayana pc ina maraba daku siyan daya ko sari👏🏻domin neman karin bayani sai ku neme ni ta wannan number waya👉08101521252
nagode kwarai da gaske💃💃
Free Page 3••4
_Shekarar yanzu_
Katsina____12:00pm
Layin tsitt yake baka jin komai sai kukan karashiyah wanda sukan fito da daddare domin nemo abincin su.
Daga ganin yanayin anguwar kasan masu hannu da shuni ne ke zama a cikinta.
Bisa la'akari da yanda kowanne gida ɗaɗɗaine bashida get,ruwa,da kuma wutar nepa mai kyau.
A hallayah irinta wannan anguwa akan rufe gidan kaman misalin karfe goma,hakanne ya sauƙaƙawa masu shirin shiga wani gida,wanda yafi kowanne gida a kusan wajen kyau.
Su ukune sanye da baƙaƙen kaya,da kuma junduma junduman hijabai,a yanayinsu sunyi kama da mata,saidai kuma yanayin kujarinsu akwai shakku idam matanne,koma matanne to kuwa basuyi kama da masu zama a gidaba suna rainon yaransu.
Ɗaya daga cikinsu ne ya kama katangar wajen ya hau,kaman dama danshi akayi wajen saboda tsabar ƙwarewa.
Saida ya daidaita zamansa a wajen kafin ya mikawa na kasan hannu.
Wani abu ya bashi a gwangwami yafara fesawa security ware tada zagaye gidan mai kaman spray.
Saidai daga yanda yake rike abin cikin kulawa kasan abin da alamar hatsari a tattare dashi,koma ince fiyeda haka.
Cikin abinda bai wice sakanni ba karfen wajen yafara narkewa kaman an zubawa kankara ruwan zafi.
Saida suka tabbatar yabada wajen da mutum zai iya shigewa kafin dukkkan su suka hau,tareda afkawa cikin gidan.
A yanayin yanda suka dire a tiles din gidan,yakai karar ya ankarar da hankalin mai gadin,saidai ko kadan hankalinsa ya tafi ga wata mata dayake mata magana a bakin get
wajen misalin karfe 11:30pm,a cikin magagin bacci mai gadin yaji bugun kofar gidan,tsorone ya ɗarsu a cikin zuciyarsa,dan yasan ba kowa bane sai barayi,shikuwa yanda yake gudawar nan,ko iskan suka saita masa jefarshi zatayi.
Har ya koma zai cigaba da kwanciyarsa dama ga sanyin da'ake,saikuma yaga rashin dacewar hakan,musamman da mutanen gidan suka yarda dashi suka bashi amanar kariyarsu.
Tashi yayi cikin sanyin jiki ya nufi bakin get din,duk da daga kaga tafiyar dayake kasan ƙara ƙadance zata saka ya koma daga inda ya fito.
Shuru yayi yana jiran yaji wanene,ga mamakinsa sai kuma yaji nishin mace,wacce take cikin mawuyacin hali.
"Wayyooo,maga allah daga gidannan ya taimakamin dan allah"
Saurin bude kofar yayi idonsa ya sauƙa kan wata mace,bazata wuce shekara ashirin da biyu ba,ga kuma ciki haihuwa ko yau ko gobe a jikinta.
Kayan jikin ta da kuma yanda take maida numfashi ɗaya bayan ɗaya ya isa ya tabbatarwa da mutum halin data ke ciki.
Karisawa wajenta yayi yadan bawa bakin kofar get din nisa kadan.
Durƙusawa yayi a gabanta tareda tambayarta cikim tausayawa.
"Baiwar allah lafiyah naganki a wannan wajen cikin yanayinnan da tsohon dare haka"
Hannunsa ta kama na hagun wanda yake kusada ita,tamkar dukkan rayuwarta tana jikin hannunasa,numfasawa tayi da ƙyar kafin tace,
"Bawan allah kai musulmine,kadubeni da idon rahma,a matsayina na ƴar uwarka musulma,wasune suke bina zasu kasheni,yanzu haka ƙishirwace ta kamani kaman zan mutu,shine na keso ka taimaka min da ruwan dazan sha dan allah"
"Toh amma baiwar allah bakya bukatar inda zaki zauna kuwa,bai kamata ki zauna a waje ba,idan na shiga gidan ma kinga ke kadaice a wurin"
"Ina bukatar hakan sosai,saidai kar na takuraka dayawa shiyasa kaga nace ka bani ruwan ma ya isa "
"Ahah baza'ayi haka ba,a wanann halin dakike ciki rayuwarki nacikin haɗari sosai,shigo daga cikin na kawo miki ruwan"
Har ta tashi zasu shiga sai idonta ya hango wucewar wani abu cikin gidan. Bata tantance menene ba kawai sai tayi Saurin kama hannun mai gadin wanda yake kokarin juyawa wajen da idonta ya hango,hankalinsa ya bayar kanta ganin yanda ta rike mararta tareda sakin ɗan marayan nishi.
"Sannu baiwar allah,lallai kina ganin rayuwa kam,barina kawomiki ruwan koh"
Ɗaga kai kawai tayi,dan maganar ma ta gagareta.
Bace wa ganinta yayi ya nufi wani lungu na gidan,da alama anan zai samo ruwan. Zama tayi a bakin barandarsa inda ya barta tana maida numfashi.
**______**_______**
A hankali cikin sanɗa suka samu nasarar shigewa gidan,ganin yanda wata mata ta samu nasarar ɗauke masa hankali.
A bakin kofar falon suka tsayah,inda ɗaya daga cikin su ta saka wani a bu a kofar makullin. Nan da nan kofar ta bude suka shige.
Rarrabuwa sukayi kowanne yayi wani wajen,hanyar balcony daya daga cikinsu yayi inda zai kaita dakunan dasuke wajen,kara kunnensa yayi a jikin kofar domin jin wannene na mai gidan.
Ganin sun dade amma basu ganoba yasa dayah daga cikinsu yah daga wayah tareda danna kirah
"Ogah mun kasa gane a wanne ɗaki fah yake,gashi kince karmu kuskura mu bari wani ya ganmu,tayah zamu gane ɗakin dayake toh?"
"Mtsww shiyasa fah nashiga aikinnan dan nasan sai kunyimin shirme,har yanzunku bazaku iyah gane yanda zaku fitar da kurege daga cikin raminsa ba,indai anan dabararku ta ƙare to zan san yanda zanyi daku,ƙanana ma in an basu aiki sun fiku iyawa, ku fito daga gidan kafin a ganku,zanji dashi ni,shiyasa fah nake aikina ni kadai babu ku"
"Kiyi hakuri v-lady zamuyi yanda ya dace sosai,kinsan abinne sai a hankali"
"Okay shikenan na baku minti ashirin ku fitomin dashi daga gidan,idan ba hakaba kuma zan tafi na barku ku kukasani"
Daga ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya,sai a sannan na kula ashe dukkansu matane,tsabar kawai kwarewane da kuma taurin zuciya yasakasu yin abinda ba kowanne na mijinba.
Kiran sauran abokan aikin tayi tareda cewa,
Ɗayace daga cikinsu tace
"Kai ni tsiyata da itah idan wani ya ta'bota to ba sani ba sabo da ƴan uwanta,hmmm inka gane halintane zaka san ya take
Hakane kam,yanzuma tace ta bamu nan da miniti ashirin,mai kuke ganin za'ayi,hmmm gashi tace karmu yi wani abinda zai ta'ba iyalansa,da tuntuni mungama da shi fah"
Tafaɗa cikin ƙosawa,suma jugum sukayi,can sai taji ƙarar massage a wayarta,
Dubawa tayi ganin an saka v- lady,
"Yau yadawo kasar bayan wata biyu,dan haka dole idonsa biyu shida matarsa basuyi bacciba,a dakinsa zai zamo dole suke,saboda kowanne gida yawanci ɗakunan yara na kusada na matar gida.
Dole zakuji dakin yafi kama turaren Emergency,saboda shine turaren dayafi amfani dashi,ku shiga daƙin,kafin tayi wani abu ku fesamata maganin bacci,shima ku fesamasa sanann ku kawo minshi ina jiranku"
"Wow kuga yanda v-lady ta solver abinnan cikin ƙanƙanin lokaci,lallai dole mu sara mata,maza kuzo a kammala aiki"
Sakin hancinsu sukayi domin jin ta ina turaren yafi ƙarfi a gidan,dukkan su samun kamsu sukayi a bakin wata ƙofah wadda take ƙarshen wani corridor.
Dukkan su kallon kansu sukayi,tabbas hasashensu gaskiya ne,dan gashinan suna jiyo numfashinsu a ɗakin.
"Vl4 ki tsaya ta gefen dama,ke kuma Vl5 ki tsayah ta gefen hagu,bari na shiga,ina shiga kowaccenku sai tayi kokarin fesamusu kafin suyi wani ƙoƙari,clear?"
"Yesss Vl3,dukkan su suka haɗa baki.
Tana buɗewa kuwa suka feshemusu fuska da spray ɗin,faɗawa sukayi ta bayansu akan gadon,shikamma uban gayyar daga shi sai gajeren wandon daya samu damar gyarawa lokacin da yaji motsin shigowarsu.
Ɗaukar bargo sukayi suka jefawa matar tasa tareda kinkimarsa suka fita daga gidan.
Ta bakin get din suka zo suka wuce abinsu hankali kwance, Haɗa ido sukayi da matar da take zaune a wajen,ko kallonsu batayiba sai aikin nishinta take,duk kuwa da cewar akan idonta suka wuce ɗin.
Lokacin mai gadin ya kawo mata ruwan,ya tafi nemo mata magani suka wuce,shikuma sannan ya dawo.
"Sannu baiwar allah ya jikin dai,ko nayiwa hajiya magana su taimaka miki,dan naga kaman ko haihuwa zakiyi"
"Ahah baba ba haihuwa bace,kawai wahalar dana shane,watan haihuwar bai kama na tukunna,zan iyah amfani da banɗakinka idam babu laifi"
"Lahh ba komai ki shiga,barina ɗan zagaya kafinnnan"
"Toh nagode allah ya saka"
Bata daɗe da shiga sashennata ba saigata ta fito tana gyara zaninta wanda duk ya yage ,kallon mai gadin tayi wanda yake tsaye tareda cewa,
"Baba zan tafi,dan akwai tasha nan kusa,nasan yanzu wanda suke bina sun wuce,zan je da sassafe na kama hanyar ƙauyenmu,dan dama a wajen ƴar uwata nake anan"
"Da naso kiɗan zauna ganin yanda kike,amma tunda kince haka shikenan,gsshi kuma bansan sunan ki ba"
"Hhh baba kawai ka ƙirani da MABARACIYAH dan haka kowa ke ƙirana,dan nan ɗin ma barar mukeyi dana taho daga garinmu,saida nazo nagane ashe inada ciki na tsohon mijina da muka rabu"
"To shikenan allah ya bada lafiya ki kulada hanya"
Fita tayi a hankali kaman bazata iya kaiwa karshen layinba.
*____*_____*____*
Wata macece mai kaya riga da,zani na hausawa, ta fito daga wani lungu,kaɗan kaɗan ake ganin fuskarta saboda yanayi na dare sosai,a hankali take tafiya kaman mai tsoron kar wani ya ganta,saida tazo saitin wani lungun kafin ta shiga.
Wata leda ta ciro a wani kango ɗan nesa da gidan data fito.
Zanin jikinta ta cire ta jefar da kuma rigar,buɗe ledar tayi saiga baƙaƙen kaya sun bayyan irin na wanda suka dauƙi alhajin,saidai kuma nata akwai purple din macijiya (Viper)ta buɗe baki a bayan rigar ƙatuwa.
Nan da nan ta saka tareda daukar rikagar sanyi mai irin kayan itama ta sakata,sanann ta ɗau Hula da kuma baƙin glass.
Waya taciro a cikin aljihunta tareda yin magana cikin dakewa,
"Kuna ta wajen ina yanzu haka,dafatan babu wanda ya ganku ko"
"Eh V-lady babu wanda ya ganmu,muna karshen layin dakike tahowa".
Tafiya kaɗan kuwa tayi saigata ga baƙar mota,buɗe baya tayi ta shiga,motar ta tashi ta nausa kan hanya,dan dama jiran shigarta akeyi .
Sun dade suna tafiya har suka bar cikin gari suka shiga wani ƙyauye,a bakin wata bukkah suka tsayah a bayan garin.
Dukkansu fitowa sukayi yayinda ɗaya daga cikinsu ta kinkimi mutumin zuwa cikin gidan,yayinda wacce take tuƙa motar kuma ta koma da baya zuwa cikin gari.
Bukkar ƴar karamace bata wuce ace mutum ɗaya ne yake rayuwa a cikinta ba,saboda yanayin ƙanƙantarta da kuma yanda ta tsufah.
Babu komai a cikin bukkar sai fili mai rairaiyi(ƙasa).
Wani key wacce suke kira da v-lady din ta ɗauko tareda sakawa a wani dan abu dayake gefen bangon wajen kaman makunna.
Tsakiyar ɗakinne ya buɗe saiga wani rami ya buɗe,dukkansu faɗawa sukayi cikin wajen..
Boyyayar hanyace ta karkashin ƙasa,wacce zata kaisu wani waje daban,sunyi kaman minti biyar suna tafiyah a wajen kafin suka bullo a fili mai ɗauke da wani gini babba,saidai ba lallai ya ɗauki hankalin mutane ba.
Wasu matane a bakin kofar suka buɗemusu suka shiga.
Abin mamaki da al'ajabi,gidan ko kaɗan baya kama da yanda yake ta waje,saboda kofah kofah ce dashi,sannan kuma da wurare daban daban.
Wani ɗaki na karfe direct suka nufah da mutumin dayake rike a hannunnata,
"Ku dakata ,ina naga kuna nufin kaishine,a zatonku daɗewa zayyi kuke nufin kaishi kejin masu jimawa,ku ajiyeminshi anan"
Ajiyeshi sukayi suna kallon yanda yake sakin jiki saboda magananin bacci da har yanzu bai bar jikinsa ba,
Kujera taja ta zauna tareda ƙaremasa kallo,hankalinsa ma wato akwance kaman bai san inda yake ba.
Ɗaga hannunta tayi iyah ƙarfinta ta zabga masa mari.
Wata gigitacciyar zaburah yayi kafin ya bude idonsa yana ƙwarewa wajen kallo.
"Hajiya salah wayyo"
Hada ido sukayi da itah ta ɗaga masa girarta ta hagun alamar kalleni da kyau.
"Ƙaremin kallo dai doctor mai tashe,dan tsabar dama kai tantirine wato da sunan matarka zaka tashi daga bacci ko kuma inkaji wuyah koh,to ƙirata da kyau dan ba ganinta zaka sake yiba har abada,bari kaji bayani babbakeka zanyi a wajennan babu mai kwatarka,yau ma kuwa basai gobeba"
"Wayyo to wacece keɗin ranki yaɗaɗe?"
" raina ya daɗe? Ameen wanann shi ake fata,danna samuma naci karena babu babbaka ba,inason wanann addu'ar sosai.
Har yanzu yallabai baka ganeni ba,ina ɗaya daga cikin masu tsaron dasuka kaika har gidanka cikin koshin lafiya jiyah,suka kuma yimaka fatana zaman lafiyah,saikuma gashi na laluba na kwamusoka bayan na kaika gidan.
To ya kaji zancen yayi maka daɗi?"
,"mai kike buƙata,idan ƙudine zan baki number dazaki ƙira a baki,nasan kidnapping ɗina kikayi koh?"
Kaga nayimaka kama da wacce take neman kuɗi,wato ku koma da kuɗi zaku fansheshi koh,duk abinda kuka yi idan aka nufo kanku saiku bada kuɗi,saboda kun saku kaji zaku saka musu tsaba koh"
"To mai kike buƙata kika kamani,ko wanine ya aikoki daga cikin maƙiyina,sabod......."
Sake gwaura masa wani marin tayi,idonta babu alamar tausayi.
" yanxu yarinyah kina ta marina,kinsan fah nakusa jika dake,ke kuwa musulma ce kuma bahaushiyah,wane abune yasakaki yin aikin da namiji ma sai wanda aka tsinewa a cikin al'ummah yakeyi?"
"Hhhhhhhhh inama mutanen dakuka mutu kuna nan kuzo kuji Dr. Bukar yana wa'azi,oh wato bai kamata nayi haka ba koh,to ai yawan shekarun daka bani su suke ƙara sakawa na ji daɗi zuciyata tayi sanyi idan na marekan,oh kai a iya marima kake tunanin tsayawata wai.
Vl3 Vl4 Vl5 dukkanku ku fara dukansa da sandunan hannunku ƴan uwa har sai nace ku bari tukunna"
Kaman jira suke kuwa suka fara dukansa kaman an aikosu gareshi,tun yana ihu har yayi shuri,abinka da jikin daya saba da hutun kasashen waje,tashi daya jikinsa yayi luhu luhu kaman jikin kazar turawa wanda aka figeta.
"Ku dakata ya isa haka,nagaji daganinsa ma ni"
"Wyyyo wayoo mmm....mai kike bukata ...kince ba kuɗi ba sanann kince ba aikoki akayi ba to me kike so"
" anzo wajen gwanda da ka tambaya da bakinka,kasan mai nake so yasa na kamoka?......ƘODARKA nake so kabani,so nake ka cirota ka bani ita da hannuka,idan ka ciromin ita zan barka ka tafi abinka,idan kuma baka ciromin itaba nan da minti biyar zanzo na cira da karfin gaske,zabi ya rage ga naka,kokayi da kanka ko kuma ni nayi maka yanzu nan"
Zaro ido yayi hankalinsa yayi matukar tashi,dukan da'akayi masa bai ɗaga masa hankali ba yanda cirar ƙodar ya ɗaga masa hankali.
Jefa masa wuƙa tayi mai masifar kaifi gabansa,tareda jingina a jikin kujrar tana jiransa.
"Wacece ke,lallai ke ba iyah mai bada tsaro bace kawai,ke watace daban,meyasa duk duniya baki biɗi ƙodar kowa ba sai tawa,hakan ma kuma na cire na baki yanzu batareda an bi ƙa'idoji ba na asibiti"
Wata dariyar tasake sheƙewa da ita kafin tace,
"Oh dama wannan ƙa'idojin suna nan kuma suna aiki? ,ni nayi zaton baka sansu ba ai,......minti biyu yarage maka ko buɗe cikin ka ka fitomin da ƙodarka kokuma na kar'ba na cira da kaina,sassauta maka nayi shiyasa nace ka ciromim da kanka,nima na iya cirar"
Zuwa sannan ya kasa cewa komai,babu abinda yake sai kallo wuƙar take gabansa kawai......ƙarar tashin ta ne yasashi zabura yaja daa baya,saidai jikinsa bashida karfin yin hakan ko kaɗan.
"Dr nawwarah(Vl6)fito ina son ganinki anan wajen yanxu"
Fitowa tayi da kaya irinna su maryam a jikinta amma ita da ɗan ƙaramin glass fari a fuskarta.
Razana Dr bukar yayi yana ja da baya,da alama ya shaida Vl6 ɗin,
"V-ladies ku kaishi ɗaki a fara aiki,ina so ki ciremin duka ƙododinsa ki kawomin su nan,ku maye gurbinsu dana roba yanzunan,kawai so nake na gansu.
Tashi ka bisu su ciromin ƙodarka"
Fisgarsa sukayi aka shiga dashi ɗakin da dr nawwarah ta fito,tun tana jiyo ihunsa har yayi shuru.
Can kaman zuwa minti goma saiga Vl4(safiyyah)ta fito da ƙoda biyu akan tire,duk jikinsu jini daga gani sannan suka fito dasu daga inda suke aiki.
Ɗaukar ɗaya tayi daga kan tiren ta mitsitstsiketa a hannunta saida ta fashe jinin cikinta ya fito.
Lumshe ido tayi tareda jan numfsshi kafin tace,
"Aikin ku yayi kyau yan uwa,ina godiyah gareku"
"Bakida buƙatar faɗan hakan ƴar uwa,an zama ɗaya kuma ana tare iya wuyah"
Jefar da ita tayi ta take a ƙasa,
"Wannan na fasata dannaji sauƙin raina,ɗayar kuma ku kaita ga asibiti a sakawa wanda yake buƙatar ........"
Tun kafin tagama magana kira ya shigo wayar tata ,ɗagota tayi kusan fuskarta inda sunan Dec Sadeeq ya bayyana,murmushi tayi kafin ta ɗora wayar akan kunnenta.
"Sir!!!?"
"Ina kike khamriyyah maza ki sanar da sauran abokan aiki kan cewar akwai aikin daya bullo,dan yanzu labari ya ƙara zuwa mana Dr Bukar ya bata a darennan,ina jiran zuwanku office da karfe shida,bayan na gama bincike yanzu"
Sauƙe wayar tayi tana ƴar dariya,
"Ke Maryam (vl3),tunda Sabriyyah bata nan(Vl1),tana kan aiki ki ja ragamar duk abinda za'ayi,ni zan tafi muje mu kama wanda ya sace Dr bukar,bari naje gida na shiryah,sannan ki kiramin khairiyyahh (Vl2)ta turomin document din danace tayi min copy"
Tafaɗa tana kara sautin dariyarta ta rainin hankali,
"Angama v-lad....."
"Ku daina kirana da viper lady idan ina yanayin wasa,ku kirani da ɗaya daga sunana kawai,kunsan inason a dunga ƙirana da sunaye da yawa"
Tana gama shaƙiyancinta ta bar wajen,jijjiga kai maryam tayi tareda cewa "sai oga"cikin dariya da kuma yanda aikin shugabar tasu yake burgeta sosai,ita kanta tana mamakin yanda cikin sauki ogar tasu take sajewa da duk aikin da tasa a ranta sai tayi.
Wani mashin da ɗauka a bayan gidan a cikin garage,wanda yawancin barayi suke amfani dashi saboda gudunsa.
Wata hanya ta nufah a cikin jejin siririyah wacce zata kaita cikin gari a mintina kaɗan.
Ana kiran sallahr farko ta shiga gidan,ɗan karamine madaidaici,amma kuma yanada kyau sosai.
Banɗaki tashiga ta wanke jikinta tass,na aikin data kwana tanayi.
Riga tasaka doguwa sannan ta jumbula hijabi shima doguwa.
Sallayah ta hau tafara da kabbarar harama ta shiga sallah.
A yanayin lokacin da kuma yanda take tayin sallahr ya tabbatar da ba asuba take ba,mai yiyuwa nafila take ko kuma biyan bashi na sallolin baya.
Kiran assalatune yasata yin sallama kafin tashiga sallahr farillah ta asubar.
Bayan ta idar ta naɗe tana addu'o'i kafin ta jawo qur'ani,suratul hijr ta buɗe ta fara karantawa cikin kwarewa,daga jin yanda take karatun kasan ba karamin haddar wajen tayiba,duk karatun cikin ruwayar warash takeyi,mamaki abin yabayar,domin a wanann zamanin da wiyah ka samu mace na yin ruwaya warash,saboda yawanci yanzu ƙira'ar hafs tafi yawa ga mata.
Duba agogo tayi ƙarfe shida dadai,sai a sanann ma ta tuna da aikin da ogah ya ƙirata zasuyi na binciken 'batan Dr bukar.
Hijabin jikinta ta cire da sauri da kuma rigar,wardrobe ɗinta ta buɗe bayan ta ajiye qur'anin.
Kayan state security ta fitar,baƙaƙe amma kuma ba irinna ƴan sanda ba,cikin mintuna kaɗan ta gama shirin kana ta tsayah a gaban madubi tana kallon kanta.
Abubuwa da damane suka bayyana akan fuskarta,alfahari,nadama,ƙunci,cikar buri da kuma rashin danasani.
Ganin suna kokarin dulmiyata wajen da bata shiryah saka kanta a ciki bane yasa ta shafesu tareda ajiye wani murmushi akan fuskarta tana sarawa kanta da kanta ta madubin.
Idontane ya sauka akan barge ɗin take kafaɗarta ta gefen dama,da sunanta da kuma status din ta,a duk sanda ta kallah sai ta tuna da alkawarin datayi wa ƙasarta a ranar daza'a rantsar dasu bayan