Author : Auwal sadiya Category : Free Novels Online (Read & Download)
abinda nake son yi.
Na ɗaukeki a matsayin mai kuladashi,daga yanxu zaki iya shigowa ki fita lokacin da kike so"
Gefenta deejah ta waiwaya bayan hajiya fulani tabar wajen suka haɗa ido da yareema jalal wanda yake zaune.
Ƙifta masa ido tayi tareda barin falon tana murmushin samun nasara.
Toh fah ku taho dai,deejah tayi nasarar shiga inuwar hajiya fulani..........saura kuma me?.....
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
39••40
Hankali kwance kaman tsumma a randa haka deejah tayi kwanciyarta,ko tunanin mai gobe zatazo da ita bata kawowa a ranta.
Ɗakin amal da buɗe tana kwance akan gadon kaman kullum,damma yau ba makaranta weekend ne.
Bata yaye labulen ɗakin ba saita fara ta gyara kayan data zubar a tsakar ɗakin jiya da daddare.
Tattarasu tayi ta kaisu cikin kwandon wanki,sauran kuma wanda taga sunada wanki tafara nade mata..
Kwata kwata hankalinta baya kan abinda take,sai jin ruwa tayi a bayan mai sanyi .
Ajiyar zuciya tasaka tareda zuyowa tana kallon amal wacce take riƙe da kofi a hannunta,yaushema ta ɗebo ruwan deejah bata sani ba.
"Ko zaki ramane,tun ɗazu ina miki magana kinyimin banza kaman bakya jina,ki wanke min wannan kayan dakika kai wajen wanki,in kuma kin fi karfi ki sanar dani"
Baki deejah tasake,takula rainin hankalin yarinyar karuwa yake,dolene ta koya mata hankali.
Fita tayi tana ƙiran mommy tun daga ɗakinnata,ta kula halinta ne hakan kullum da safe.
"Mommmy dagaskene abinda Anty mubeena ta faɗamin wai,tana zuwa gobe?"
"To kuma tafada miki karin bayani kike nema"
"Ahah,yanzu dai yunwa nakeji,oh..... Naji wai yah sadeeq yazo shida umma,hadda meena suka zo?"
"Ahah su kaɗaine,meena tana gida"
Har wajen ƙarfe takwasa kafin deejah tagama wanke kayan amal ta shanya,wannan bacin injin wankin ai su akayiwa masu aiki.
Daga wajen inda take shanyar tana kallon eemran yana haɗa dusa a cikin darom kwanuka.
Yazage sai aiki yake kaman dama haka yatashi yana yi.
Dariya yabata wanda hakan yasata tuntsurewa da dariyah.
Takawa take a hankali har ta isa wajensa ta tsugunna.
Dagowa idonsa yayi yana kallonta tanayi masa dariya.
"Menene kike min dariyah da safennan,mafarkina kikayi ina wasan musha dariyah?"
"Ko ɗayah,kawai yanda kake aikinne ka dage yabani dariyah,gaskiya daga gani za'ayi jarumin namiji mai neman nakansa.
Jiya da daddare dazan wuce naga kanata turanci kaman ba kaiba,dama ka iya turanci haka?"
"Uhm nayi karatu,kaman kema na ganki kina magana ke kaɗai rannan,shin kina magana da aljanune?"
"Yaushe ka ganni?"
"Ranar da kika cemin kin gano rashin lafiyar yarima mubarak,"
Shuru deejah tayi da zancen tareda ƙoƙarin sanja akalar maganar.
"Shin kanason shiga sashen hajiya fulani?"
"Meyasa kika tambayeni?"
"Kawai naga kanason shigane,saboda wani lokacin inaganin yanda kake kallon wajen shigar"
"Eh inason shiga sosai,saboda akwai wani abu danake son ganowa,wanda ya shigemin duhu"
"Zan taimaka maka ka gano koma menene ya shige maka duhun,nasan wani abu gameda kai kana boyewa ne,yayinda nima nasan ka fahimci akwai abinda ban fito na bayyana ba.
Alaƙarmu tana birgeni yanda kowa ke mutunta sirrin kowa,duk da haka inaso kasani har cikin raina.
Na yarda dakai emran,kuma a shirye nake na taimaka maka idan bukatar hakan tazo,kaman yanda kake ƙokarin kuladani nima"
Dan lumshe idonsa yayi tareda ɗaga mata kai alamar yaji.
"Uhm kasaitarce ta motsa kaƙi yimin magana,anya kuwa kai ba jinin sarauta bane?"
"Ke ma wani lokacin idan ina kallonki a cikin gidannan,saina dunga kallonki kaman jinin shugabanci,kinada kwarjini da kuma cika a tattare dake,naga yanzu yarima jalal ma shakkar ku hada hanya yake,jiya ina kallonsa ya canja hanya yafi uku idan ya tunkareki"
"Hhhhh yaushe hakan ta faru,ashe dama kana kallon duk abinda nake,da wanine yayimin haka saina ji tsoron kar ayimin wani abu,amma yanzu hankalina kwance tunda kaine kake kallona ba wani daban ba"
"Hakane ki kwantar da hankalinki,fatana karkiyi abinda zai cutar dake ko kuma wani daban,ta hakanne idan kinyi zanyi koƙarin taka miki burki,amma bayan wannan idan wanine yake ƙokarin yimiki wani abun zan tsaidashi tun kafin ki sani"
"Uhm yanzu ka dawo normal kana surutu,duk da nasan iyani akewa wannan dogon maganar,barina shiga sashen hajiya fulani,zan duba jikin yarima,idan kanada buƙatar bina saimu tsara yanda za'ayi,"
"Ba damuwa zakijini idan inada buƙatar hakan"
Tashi tayi tabar wajen tana waiwayensa har tashige.
Jijjiga kai yayi bayan ta ƙule tareda cewa.
"Yah Allah ga bawanka,nasan kaine ka jarrabeni da wannan soyayyar mai matuƙar zurfi da kuma makanta,ALLAH kayimin mai kyau"
Kai tsaye ɗakin yarima mubarak deejah ta wuce,bata nemi ganin hajiya fulani ba,dan tasan bazata iya ganinta a lokacin ba.
Tsayawa tayi a gabansa tana kallon idanuwansa dasuka tsaya cakk a waje guda.
"Inshaallah zanyi iya ƙoƙarina wajen ganin na taimakeka,ta kwantar da ɗaya,ta kashe ɗaya,ta lalata ɗaya,ta rabu da ɗaya. Wannan wace irin uwace haka,wanda zuwanta cikin al'aumma bai haifar komai ba illah masifah.
Inta kama in nata kuruwar zan bayar subada naka zan bayar,kayi sa'a naji tausayinka a cikin raina,ganin yanda ka zauna a wajennan ba iya na kwana ɗaya,biyu,sati,shekara daya ba,har shekara goma sha huɗu.
Hmmm hajiya fulani kin shiga uku da a zaluncinki kika tabi wacce bata yafiyah,yanda kikamin aradu kema sainamiki,sa'arki ɗaya inda mutunci,da saina wulaƙanta rayuwar ƴaƴanki,dan an ce laifin uwa baya shafar ɗan ta ne da sai na rabaki da kowa tukunna kafin na hukuntaki"
Duk wannan maganar cikin ranta takeyinta tana kallon fuskar mubarak ɗin..
Duddubashi tayi tareda jaraba yan wasu magunguna wanda tasan bayi zasuyiba,kawai danta shigo wajenne ta taho dasu.
______________________________
Sabrah ce a zaune idonta yayi luhu kaman an zuba mata garin barkono,khairiyyah tayi aikin rarrashin harta gaji tayi shuru,.
"Yanzu sabrah bazakiyi shuru ba,dan bai zoba amma ai ya ƙiraki ya faɗamiki halin da 'ake ciki,kenan haka zakiyi idan an miki kishiyar ma kisata a gaba kiyi ta kuka..
Ina kissarki da iyah kalallame miji suka tafi?"
"Hmmm khairi kennan,wane kalallama yanzu zanyi,bayan aurennawa ma shirin gundulewa yake,nasan badam abinda ya faru ummah taƙiniba,sabida ni ba ƴar kowa bace,banida asali,ni shegiyace marar asali, banda uban dazan bugi ƙirji na nuna,kuma sannan ɗanta yana sona fiyeda ƴar yayanta.
Shiyasa ta tsaneni,inba haka ita macece mai maraba da kowa,nikaɗai nake ganin wannan bangare na jikinta.
Shima wani lokacin batayimin sai abin ya taso tukunna.
Khairi ina zan saka kaina,yarinyar fah wai ƴar sarkice,taya kike tunanin zan haɗa kaina da ita a fannin komai?.
Kodayake meyasa ma nake damun kai na,nida zanje kurku bayan ɗaurin auren,nasan ko mijina bai kamani ya kaini ba khaleel ɗan uwansa idan ya kamo khamriyyah da mabaraciyah muma zai kamamu,sai muyi zaman mu a can,bangani ba bare na damu,ko ƴar uwa?"
Kallonta khairiyya take kaman wanda ta tabu haka take zubo magana,juyawa tayi zata ƙira inno,saikuma sukayi kibis da ita,ashe tana tsaye a wajen tun ɗazu.
Hawayen fuskarta ta share tareda isa inda sabrah take zaune akan gadon.
"Karkice haka kinji ƴata,kinada kowa kinada wanda baya bacci wato ALLAH,ga kuma ni da ƴan uwanki,iya wuyah bazamu barki ba muna tare.
Ki fawwalawa Allah lamuranki kinji?,karki saka damuwa a ranki har yakaiki ga cutar da lafiyarki,mijinkine yana sonki,babu wanda ya isa ya canja hakan idan ba Allah ba"
Rarrashinta inno ta cigaba dayi,tareda kwantar mata da hankalinta,tana ajiyar zuciya har bacci ya ɗauketa.
Fitowa sukayi daga ɗakin bayan sun tabbatar ta samu bacci.
"Khairi babu matsala da bakije aiki ba,kinga baki daɗe ta fara aikinba kar oganku ya miki magana"
"Inno babu matsala,ko akwai ma bazan iya tafiyah na barta a wannna halin ba,abin yana damuna sosai,musamman daba ita kaɗai bace,sai tana tunamin da anty juwairah,shiyasa banasonta ganin halin karayar zuciya,kaman yanda nayi ta kallon anty a ciki harta koma ga mahaliccinta.
Barina je ɗauko su fadeelah a makaranta,deen baya nan ya tafi neman aiki an ƙirasu"
"To shikenan,ni ya zancen uban yarannan ne,yana rayene har yanzu"
"Eh yana raye,kwanaki ma nagani a labarai wai an kaishi ƙasar india za'ayi masa aiki,iyayen dayayi biris dasu yanxu sune suke ta fama dashi,tunda kuɗinsa kam babu.
Aikin yayi kyau aka ce ta tashi,amma shida haihuwa kam saidai yagani a wajen wasu"
"Hmmm Allah ya kyauta,shima kam baiyi daidai ba abinda ya aikata mana"
"Shiyasa shima aka nuna masa rashin daidai ɗin ai,saboda ya ɗanɗana yaji"
Daga haka khairiyya tafita a gidan zuwa makarantar su fadeelan.
_______________________
Wata matashiyar budurwace a gaban aji tana danna iphone12 ɗin da take hannunta.
"Am madeena wai dagaske kike yau zaki shige gida,ko hutawa bazakiyi ba gobe ki wuce,sai kace ana korarki"
"Hmmm kina ce ƙarya nake Summy,yau zan tafi akwai wata maganar ma da ummah takeson muyi,bansan na menene ba amma kuma naji tana ambatar yah Sadeeq"
Zaro ido wacce aka kirada summy tayi kafin tace.
"Awwn Yah sadeeq naki dai koh,uhmm allah yasa bikin za'ayi mufara shirye shiryen zuwa katsina"
"Saiku shirya kam,abinda aka daɗe ana jira yazo inshaallah"
"Amma kuma naji ance yanada mata,da kishiya zaki zauna kenan?"
"Hmmm mai ruwana da itah,naji ance ummansa bata sonta ko kaɗan,kinga nikuma wannan ce damata,yanda ummah deejah take sona komai zata iyah don na samu soyayyar yah sadeeq"
Wayarta ce tayi ringing,tana dubawa taga number drivern da aka turo mata ne.
Da sauri sukayi sallama itada summy ta nufi inda yayi mata kwatancen yana can..
Dayake hutun sati biyune bata ɗauki komai nataba banda jakarta.
A bakin motar ta ganshi ya riƙe mata murfin ƙofar,ita kuwa kai ya ƙara fasuwa,duk da batakai amal taƙama ba.
Tana shiga motar yamaida murfin tareda shiga wajen driver
"Ran gimbiyar katsina ya daɗe,shin zamu iya kama hanya?"
"Eh mutafi,kaine saleem ko?"
"Kwarai kuwa nine da wannan suna"
"Amal tayimin zancenka ai,tace kanada kirki,Allah yasa naga hakan nima"
"Inshaallah gimbiyah"
Daga haka suka cigaba da tafiya babu wanda yasake cewa komai har suka shiga garin katsina.
Tarya ta musamman akayi mata,dan hajiya saratu tana ji da ita ba kaɗan ba.
Deejah ce itada salaha suka shigo sashen domin yiwa madeena barka da dawowa.
Itada amal ne a ɗakinnata suna ta zancen makaranta.
"Wlh anty madeena bakiji yanda nakeji ba da wannan shegiyar secondryn ,ALLAH ALLAH nake na gama nima na zo jami'a,haba asha chilling"
"Oh chilling ma zakiyi kenan,barina faɗawa baba toh.
Ke ya jikin yah mubarak kuwa,yah jalal na ganshi da muka shigo zai fita a mota,ko kalloba bayyi ba bare ya tsaya mu gaisa,narada yaushe zai daina wannan girman kan"
"Hmmm ni dama ina ruwana dashi,girman kansa yayi yawa,shiga kyakykyawa,sai kace wani mummuna ne.
Yah mubarak yana nan jiki irin na yanda kika sani,har yanzu babu wani canji,keee...... Nifah nafi zargar inaga da hannun Hajiya a rashin lafiyarsa,gashi taƙi yarda Baba ya fita dashi madeena"
"Toh ina ruwanki,bazaki daina gulma ba koh amal"
Shigowar su deejah ne ta katsemusu hirar,inda suka tsugunna a tsakar ɗakin suna mata sannu da dawowa.
Amsawa tayi cikin sakin fuska,dan dama tafi amal daɗin sha'ani wani lokacin.
Ɗago ido deejah tayi tana ƙaremata kallo,har saida amal ta kulada hakan,dama garinsu da tsakuwa ita da ita.
"Ke miye kika wani zuba mata ido kaman zaki cinyeta,kuruwar ta kur haramiyarki,tasha li'ilafi da su falaƙi,saidai ki lashi kanki"
Buge hannunta madeena tayi,yayinda deejah taja hannun salaha suka bar dakin.
Suna fita salaha ta kalleta cikin tsoro tareda cewa
"Deejah kinajin tana faɗa amma bazaki bata haƙuri ba"
"Haƙuri akan me kenan,ba itace ma zata ban haƙurin ba,hmmm inaga yarinyar nan saina koya mata hankali tukunna,zata san matsayina"
"Iyeeee deejah wane matsayi dake daya wuce nasu?"
"Karkiso sanin matsayina,dan hakan bazai miki kyau ba,abar kaza da gashin ta kawai"
Fizge hannunta deejah tayi tareda barin wajen,ta bar salaha a tsaye tana sakin baki,na mamakin deejan.
Tana barin wajen data leƙa babu wanda yake kallonta ta ɗauko waya a kunkuminta.
"Ke biggy kuna ina ne yanzu haka"
"Eh ogah ni ina wajen abinci,iklima kuma ta tafi saro kayan gwanzonta"
"Zeety fah tana ina?"
"Eh ita .....uhm ta koma shaye shayenta fah"
"Meee..........dagaske kike?"
"Eh ogah ta gaske nake,amma fah tace dan allah karmu gaya miki"
"Hmmm batta zamu jone,yanzudai wani aiki nakeson kuyimin,wata yarinya nakeso ku ɗauke a hanyar makaranta,zan turo muku hotonta,gobe zata tafi makaranta da safe,EMIRATE NUR.PRI.SEC.SCH.takeyi,itada ƙaninta suke zuwa,iya ita kaɗai zaku ɗauka.
Bance ku daketa ba fah,kawai gidana zaku kaimin ita,zanzo da daddare gobe idan kun kaitan"
Tana gama maganar ta kashe wayar tareda ɗaga gira tana murmushi.
"Zakici butar ƙaniyarki gobe,na kula inba gyaraki nayi ba bazaki daina ƙonamin rai ba,marar kunya kawai"
Tana kashe ƙirannsu ta ƙira yarima jalal. Da farko bai gane wayeba sai daga baya ya tashi ya zauna daga kan gadonnasa.
"Hel.....hello kece?"
"Nice mana da waye,ka dauko ko har yanzu baka ɗauko ba?"
Zan ɗauko dai,ɗazu tashiga wanka nashiga ɗakin,tun kafin nayi wani motsi naji ta baci sunana daga banɗakin,inaga fah akwai wani waje da take ganin mai shiga ɗakin da akwatin yake.
Saidai karki damu zan jaraba yau da daddare idan ta tafi meeting,amma fah ina tsoron ta ganeni,dan zata iya kasheni idan tasan na sauya akwatinnan da wani daban"
"Mtswww to ina ruwana da abinda zatayi,ni kashekan zanyi idan baka kawomin ba,ina jiranka nan da dare,idan har baka kawomin ba gobe zan ɗau mataki akanka,nayi zaton zan daɗe a gidannan to abubuwa sun cakuɗe inason gamawa da sauri"
"Aikin me kikeyi amma a gidannan,tunda ni zan zama sarki inada haƙƙin na sani"
"Hhhhhhh karka min shashanci,in ba sokake nasaka aljanun dazasu dunga dubamin kai ba"
Kashe wayarta tayi ƙitt,tana nazarin yanda abubuwanta zasu kasance. Ita kanta tasan ɗauko mata wannan akwati dole zai ɗau lokaci,barazan kawai take masa domin yayi akan lokaci.
Har tazo shiga ɗakinsu saitaga wata paper a soke a jikin katangarsu,duba tayi babu kowa,bare taga wanda ya ajiye.
Sunanta tagani a jikin takardar,wanda hakan yasa ta bude.
_aminci ya tabbata a gareki Khadeejah,kinyi kyau a cikin jan kayan da kika saka yau.
Kwanannan naga hankalinki baya waje daya,da alama wani abun kike,kullum ina faɗamiki ki kulada kanki,karki saka kanki cikin wani abu mai haɗari.
Bana ɗanjin daɗi yau,bazamu fita yawon ba kaman yanda nayi miki alƙawari,saidai ko wani lokacin.
Eemran_
Ninke paper tayi kirjinta yana bugawa.
Hannunta takai saitin zuciyarta ta dafe,yanzu kam ba itace tasaka tsoron a ranta ba,zuciyarta ce ta saka dan kanta,ambaton bashida lafiya dayayi duk sai taji babu daɗi.
Maganar sumail ce ta faɗo mata a ranta,dayace kar a garin nuna masa kulawa bana gaskiya ba,domin neman wani abu ita kuma zuciyarta ta faɗa soyayyarsa a gaske,yazatayi kenan.
"Hasbunallahu a wani'imal wakil,Allah gani gareka"
Hanyar sashensu ta nufah da sauri domin ganin mai yake faruwa dashi.
A bakin ɗakinnasu ta tsayah tana shakkar ƙwanƙwasawa.
Haka kawai taji bai kamata tazo wajen ba bayan bata sanar masa,ko wani yakamata tasamu namiji ya rakota wanda zai faɗamasa tazo.
Har ta juya zata tafi sai kuma tajiyo muryar emran yana faɗar wani abun.
"Nima kaina saleem a dole nake zaune a gidannan,tsawon lokaci na gudu na buya a duniya tamkar wani matsoraci,ni kadaine naga abinda ta aikata shekara goma sha huɗu bayah.
A gabana ta nuna mubarak da wani abu ya faɗi,ni kuma ina aman abinda naci a ɗakinta mai kaman minti,nayi zaton ta ajiyene domin ta bamu,bansan abin cutarwane dazata bawa wani ba.
Saleem nakasa manta wanann ranar a cikin idona,nakasa yafewa kaina dana kasa ɗaukar mataki,nakasa fitowa duniya na faɗawa mutane abinda ta aikata saleem.
Mahaifiyata matsafiyace,amma bazan iya faɗawa mutaneba,saboda babu wanda zai yarda dani,ta toshe duk wata ƙofah dazata nuna ita wacece,su kansu manyan garin da kuma mai martabar dukkansu a ƙarkashin ikonta suke.
Khadeejah batada uwar dazata nuna in an tambayeta,mubarak raine dashi amma bashida ikon amfanar rayuwarsa,shikuma jalal ta maidashi tamkar ɗan awaki,ta sangartashi.
Nikuma nakasa zaman gidan ubana,wanda bashida uba ma yafi ni,ina gidan ubana saleem amma banida ikon bayyana nine,domin yin hakan tamkar tasoda fitina ce.
Ga cutar dana kamu da ita a ranar,duk lokacin daya tashi min jinake tamkar zan mutu,jinin jikina kaɗanne yake saura.
Saboda tasan gubar dake jikin abin shiyasa ta bayyanwa duniya na mutu,dan tasan bazan iya rayuwa da ita ba.
Bazan iya fadawa mutane ainihij sunana ba,na YAREEMA JUNAID,saboda mahaifiyata"
Karaff ƙofar ta bada ƙara lokacin da deejah tajingina a jikinta,bata ma sani ba.
Dukkansu ɗagowa sukayi su na kallonta,harda emran wanda ya riƙe kirjinsa,bakinsa duk aman jinin dayayi a lokacin......
Taku
_sadi-sakhna_
Ƴar mutan jama'are.
*MABARACIYAH*
_haƙƙin mallaka_
_*sadi-sakhna*_
(Yar mutan Jama'are)
41••42
Sun kai kusan minti goma kowa kaman gawa yadaina motsi.
Su suna kallonta da tsoron ko taji abinda suka faɗa,yayinda ita kuma take musu kallon abinda suka faɗa gaskiyane.
Wani tarine ya kwacewa eemran wanda hakan yasa suka mayarda kallonsu gareshi.
Gudan jinine yake fitowa daga bakinsa,yayinda yake mayar da numfashin wahala.
Tsugunnawa deejah tayi a gabansa,dukkan ilahirin jikinta rawa yakeyi,saboda ganin yanayin data ga masoyinnata a ciki..
Saleem ne yayi saurin cewa.
"Ka daure junaid,na ɗan lokaci kawai,barina je na karbo maganin,inshaallah yanzu zan dawo bazan jimaba"
Cikin damuwa yake maganar da tunanin halin da abokinnasa yake ciki.
Tsallakeshi yayi har ya fita ya dawo ya kalli deejah.
"Ki kuladashi barina je na dawo yanzunnan,karki bar wajensa har sai na dawo"
Ɗaga kanta tayi hawaye yana zuba a idonta,don baƙaramin tsorita tayi da yanayinnasa ba.
"Eemraaan mai yake damunka ka boyemin ban saniba"
"Bakiso sanin mai yake damuna ba deejah,alaƙar dake tsakaninmu naso tafi yanda take a yanzu,kowa a cikinmu yaboye sirrinsa ga ɗayan,ko kaɗan bayaso yasani,duk da mun san akwai sirrin.
Shiya......sa nasan bazaki so sanin mai yake damunabaaaa,mai yasa zan nemeki na faɗamiki wanene ni,bayan bansan ke wacece ba"
"Dan allah karka ce haka,indai abin yakai haka,nayi alƙwarin faɗamaka abinda yake faruwa harma da wacece ni,karka sake boyemin irin wannan jinyar,zanzo nasani emrann"
Kuka dake haƙƙun,yayinda shikuma yake riƙeda kirjinsa,zuwa yanzu saura kaɗam ya kwanta,hannunsa daya dafene suka yimasa katanga da ƙasan.
"Shikennan,ki daina wannan kukan haka,inshaallah babu abinda zai faru,dama ba yau na fara ba,
Nayi alƙawarin faɗamiki idan ina halin daya zai iya ɗaga miki hankali,ki share hawayen"
Share hawayen tayi tareda matsowa domin taimaka masa ya zauna,gani yana buƙatar taimakon hakan.
Saurin dagatar da ita yayi kafin hanunta ya taba jikinsa.
"Ahah deejah karki kusanto gareni,keba muharrama ta bace,sannan bamu kasance jinsi ɗaya nida keba,ki bari zan iyah jurewa ba komai."
Basar da zancensa tayi tareda riƙo kafaɗunsa ta gyara fillon daya jingina dashi ɗazu.
Ruwa ta gani da tsumma a gefenta,da alama saleem ne ya ajiye a wajen.
Ɗauka tayi ta matse tareda goge masa kirjinsa inda duk jini ya bata,har da bakinsa inda shima jinin ya zuba.
Kallonta yake amma ko haɗa ido dashi taƙiyi,sai aikin gabanta takeyi,duk da cikin ranta kasan abubuwa ne cunkushe a cikinsu.
A haka ta gyara masa jikinsa tareda ɗauko rigarsa wacce ta gani a akan katifa.
Ɗaukowa tayi tareda matsowa tasaka ta bayansa tana jira yasaka hannayensa,ganin bayyi bane yasata ɗan harareshi tareda cewa
"Alaramma eemran,nima nayi karatu nasan hukuncin dayake tsakaninmu,amma kasan ko ma'aikaciyar jinya tana duba namiji a