Chapter 78 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   78 / 79

231K to 234K   out of 235.1K words

hakuri akan abinda ya faru jiya."" Yaya Ramlatu"

"tace''Haba ai ni bani da ri'ko 'yar nan magana ta wuce a gurina."" Zainab tace""Nagode insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba kema Najaatu ki gafarce ni ban san maganata zata 'bata miki rai ba."""

"Najaatu murmushin takaici tayi tace""Babu komai magana ta wuce."""

Abbah yaji dadi sosai ganin yanda Zainab ta dauki nasihar sa dan baiyi tsammanin zata nemi afuwar

"Najaatu ba sai gashi tayi masa bazata, sosai yaji dadin abinda tayi Sai da halisa ta fito daga toilet suka"

gaisa sannan yay musu sallama ya tafi kasuwa.

"Zainab kuwa zama tayi tana ta kokarin wanke kanta ita lallai sai sun manta abinda ya faru, Halisa dai da"

Ramlatu suna sata a maganarsu amma Najaatu idan tana magana tasa mata baki shuru takeyi dan bata

son abinda zai sake had'asu suyi ta hayaniya sai kace wasu karnuka a ganinta yanzu duk an daina irin wannan kishin jahilcin.

Bayan sallar la'asar ya kirata a waya tare da sheda mata cewar yanzu yay magana da Dan Azimi zai zo ya

"dauketa ya mayar da ita gida."" Tace.""Da kabari idan kazo sai mu tafi tare."" Yace.""Aa ki dai zauna a shirye Dan Azimi zai zo ya dauke ki shawarar dana yanke kenan."" shuru tayi bacin rai ya hanata cewa komai dan ma kada ta kashe masa waya yaji haushi da tuni ta kashe, tana jinsa yana magana ta dinga umm eh"

da ya gaji da abinda take masa sai kawai ya kashe wayarsa ransa a 'bace

Najaatu dauke masa wuta tayi lokacin daya shigo gidan ma tuni ta bar falo ta shige daki tayi kwanciyarta

"tasan abinda yasa yace ta dawo gida sabida yana so yazo ya haye kanta yay abinda yake so, ita da take biya masa bukatarsa ta kowane fanni itace abar wulakantawa a gurinsa aikuwa zata nuna masa tasan"

abinda take sai tayi sati bata amincewa bukatarsa ba in yaso yaje can gurun Zainab din ya 'karata

Abbah babu yanda beyi da ita ba akan ta tashi taci abincin daya shigo dashi tace ta koshi alhalin data

dawo ba tayi girki ba tunda ta cika cikinta da abincin mejego take jinta a koshe!

A kammala cin abincinsa yaje yayi wanka kamar koda yaushe turare ya shafa a jikinsa sannan ya kwanta

"kusa da ita. Matsawa tayi can karshen gado tana takure jikinta, ganin abinda tayi yasa ransa ya"

'baci sha'awarsa ya danne ya juya mata baya tare da jan bargo ya rufe kafafunsa.

A haka sukayi bacci ita tana gabas shi yana yamma!

Ta dauka da safe zai sanja mata fuska sai taga bai nuna mata komai ba yace tayi maza ta shirya da wuri

"zai fita, a gurguje tayi wanka ta shirya ko beak fast ba suyi ba suka fita. Can babban gidan nasa suka"

nufa tare. A tsaitsaye ya duba maijegon da 'yarta ya nufi gurin Zainab itama suka gaisa kana ya wuce kasuwa. Haka suka dinga yi har akayi suna duk ranar girkinta tare suke fitowa da daddare su tafi tsayin

"sati guda babu wata mu'amula da ta shiga tsakaninsu, ya daure ne yana so ya nuna mata cewar bafa lallai sai da jima'i ne zai rayu ba idan dan saboda yana jin dad'i da ita take masa iskanci to taje ta huta. Bangaranta ta dinga mamakin dauriyarsa a yanda tasan shi da rashin hakuri bata ta'ba"

"tsammanin zai iya yin sati daya ba ba tare daya kusance ta ba.......Ranar nan tana bacci kawai ta farka taga baya kusa da ita sai ta dauka ko toilet ya shiga kofar toilet din ta tsirawa ido tana jiran fitowarsa, shuru be fito ba, mikewa zaune tayi da sauri sabida jin maganarsa k'asa-'kasa a falo.'' Ta sauko daga bed din ta bude kofa ta fita. Samun sa tayi cikin duhu maqale da waya a kannensa, jin yana kiran sunan"

"Saadatu yasa taji gabanta ya fad'i!. ""Inaso in aureki mutukar kina sona kuma zaki iya zama da iyalina"

"lafiya."" Abinda kunnuwanta suka jiye mata kenan, ta sake kasa kunne tana sauraransa. ""To nagode"

"sosai dama nasan ke nutststsiya ce kina da ilimi daidai gwargwado dalilin daya sanya ma kenan naji ina sha'awar auranki saboda haka insha Allahu cikin satin nan zan turo da sadaki bana so aja dogon lokaci tunda ni dake duka ba yara bane."" Najaatu jin tana neman faduwa a gurin yasa tayi saurin tura kofar dakinta ta shiga, wanda motsinta yasa yay saurin kallon bakin kofar. A nutse ya cigaba da maganar da"

yake yi da Dr Saadatu a waya ba tare da ya nuna wata damuwa ba

"Sai da ya gama wayarsa tsaf sannan ya koma dakin, samunta yay a zaune yayi saurin d'auke kansa daga"

"kanta yaje ya kwanta inda yake kwanciya baya ya juya mata kamar koda yaushe yaja bargo ya rufe jikinsa, Najaatu taji kamar tayi masa magana sai dai ta daure zuciyarta ta kwanta hawaye na zubo mata"

lallai dama ashe duk wannan abun soyayya ce a tsakaninsu Amma matar ta bata mamaki wallahi sai da

ta gama sanin sirrinsu sannan zata zo ta aure musu miji hummm aikuwa ba ita kadai zata shaqi takaici

ba dole ta sanarwa dasu Halisa halin da ake ciki dan ta lura kamar 'boyewa yake sai ranar daurin aure suji labari to yau dai Allah ya tona masa asiri

"Washe gari da safe kadaran kadahan suka gaisa da juna har ya zauna yayi break fast a gidan, amma babu"

wata mu'amular arziki a tsakaninsu ita dashi dai duk daurewa suke amma suna galabaita kansu

"Koda Halisa taji maganar mamaki tayi sosai tace""Amma Dr Sa'adatu ta bani mamaki wallahi wato shiyasa"

"ta'ki aure ashe shi take so ta aura to Allah ya sanya alkairi."" Najaat cikin takaici tace""Abinda zaki ce kenan aunty Halisa.""? Tace""To me zance in ba haka ba ni dake da zainab babu wacce ta isa ta hanashi abinda yayi niyya saboda haka sai mu taru muyi hakuri Allah yasa abokiyar arziki ce, itama zainab zan"

"sameta nayi mata magana dan na santa da rashin hankali zata iya tada husuma abin yazo ya shafe mu."""

Najaatu dai shuru tayi tana jajanta al'amarin.

"To koda Halisa tayi masa maganar kai tsaye yace.""Gaskiya ne maganar da taji zai auri Dr Sa'adatu a"

"matsayin matarsa ta hud'u kamar yanda Allah ya hallata masa."" Saboda gudun 'bacin rai yasa tace'' To Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar arziki ce."" Cikin jin dadi ya amsa da ameen Zainab kuwa ai"

"haukane kawai ba tayi ba dan shi da kansa ya fad'a mata halin da ake ciki ta rasa inda zata tsoma ranta taji dad'i! hankali a tashe ta samu Halisa wai su tattauna maganar, Halisa tace""Kije ki kwantar da hankalinki kawai aure babu fashi! dan haka tayar da hankalinki na banza ne watakila ma ki janyowa kanki bacin rai! idan ta shigo zata zama daidai dake ai ba budurwa bace bazawara ce mu kuwa kinga da budurcinmu duk ya aure mu ai magana ta kare."" Zainab tayi zukud'um fargaba da damuwa duk sun"

dameta.

"Cikin sati hudu kacal akayi komai aka gama, Halisa da Zainab gida D'aya Najaatu da Dr Sa'adatu a gida"

"d'aya, dan kafin zuwan ranar daurin auran ya siyi wani 'katon fili dake jikin gidansa wato gidan Najaatu ya shigar dashi gidan ya sanya ma'aikatansa suka tashi aiki abunka da masu abu a hannu kafin zuwan"

"lokacin komai ya kammala, yanda ya zubawa Najaatu kayan daki ita amarya haka ya shirya mata dakinta"

ita kadai a ka kawo masa gidan.............

Abban ango sai zumudi yake yi matayen nasa suna kallonsa gami da kallon ikon Allah sai kace wanda zai

auri budurwa duk ya tayar da hankalinsa. Amarya nayin kwana ukunta na musulnci ya dawo

"zagaye kamar yanda ya saba! Zainab taga al'amarin bana zama bane yasa ta dage da gyara jikinta dan shiryawa tayi tsaf taje gurin wata mata me maganin gargajiya ta fada mata dukkanin abinda ke damunta, matar ta had'a mata maganin sanyi masu kyau tayi mata bayanin yanda zatayi amfanin dashi wai ashe rashin ni'ima da kuma bud'ewar da gabanta yay duk sharrin sanyi ne shiyasa bata gamsar da mijinta, sosai zainab taji dadin maganin dan dama itama al'amarin na damunta tasan kuma maigidan nata yana hakuri da lalurata wannan dalilin ya sanya data koma gida ta mayar da hankalinta sosai gurin amfanin da"

maganin.

Tsakanin Najaatu da Dr Sa'adatu akwai fahimtar juna dan duk masu hankali da nutsuwa ne Dr Sa'adatu

duk sanda zata tafi gurin aiki sai ta shiga gurin Najaatu tayi mata sallama itama Najaatun sa'i da lokaci

"tana shiga gurinta a cikin ranar ku da bata da aiki su jima suna hira kafin ta koma gurinta, hakika wannan jituwar da suka samu a tsakaninsu ta janyo suka 'kara martaba a idanun maigidan nasu."

To alhmdullhi Zainab tana ganin amfanin maganin data kar'bo dan tun kafin ya 'kare kwalliya ta biya

kudin sabulu dan duk sanda maigidan nata zai kusance yana samun biyan bukata sosai har ya nemi 'kari kuma itama a nata 'bangaran ta daina jin zafin da take ji tana bashi hadin kai dari bisa dari Abbah

na samun kulawa sosai ta bangaran matayensa guda uku ta bangaran Najaatu ne har yanzu yake da matsala dan kusan sati uku kenan rabon daya had'a shimfida da ita gashi kullum cikin jin sha'awarta yake duk da yana samun biyan bukata a gurin matansa amma yana marmarin ni'imanta mai wahalar samu Yau dai girkinta ne yana ganin dole ya hakura ya nemi shiri dan yini yay yana tunaninta da

yanayin salon soyayyar da take masa idan suna tare.

Tunda ya shiga gurin nata yake ta janta da magana sai wani lalla'bata yake duk inda ta gifta idonsa a

kanta tun bata gane komai ba har ta fahimci cewar ya sakko yana neman shiri wato ya gama zagaye zagayen nasa ya dawo dama ai tayi rantsuwar akan ba zata nemeshi ba tunda tasan tana da amfani a gurinsa dole ya kawo kansa Mikewa yay ya nufi bedroom tare da cewa tazo ta matsa masa jikinsa ya

"gaji, tasan fad'a yay amma ba abinda yake nufi ba kenan Tana sane gurin matsar ta dinga tatta'ba"

masa inda tasan hankalinsa zai tashi! aikuwa ba'aje ko'ina ba ya janyota rungumeta yay 'kam! ya shiga

marmatsa mata jikinta jikinsa in banda rawa babu abinda yake. kirjinsa ta tura ya fad'i a bed din ta

"haye kansa tare da kokarin cire kayan baccin dake jikinta, gabadaya ficewa yay daga hayyancinsa ya dinga sakar mata zafafan kesses tare da murza breast d'inta da mazaunanta, a daran soyayya sukayi irin"

wacce suka dade basu irinta ba

*BAYAN WATA BIYAR*

"Lokacin cikin Najaatu yayi wata tara haihuwa ko yau ko gobe, girman cikin ya sanya babu abinda take"

"iyawa sai dai komai Dr Sa'adatu tayi mata tun cikin na da wata bakwai Dr Sa'adatu ta dauki dawainiyar yi mata girki tsaf ta shirya mata daining kuma miji ya kwana da ita, Dr Sa'adatu nada mutunci da kyawun hali ta dauki ragamar kula da Najaatu hannu bibbiyu abunda take yi akan Najaatun yasa ta kara martaba da daraja a idon mijinta ya dinga alfaharin auranta dan ganin yanda take bada gudumawa a rayuwarsa data iyalinsa kwata kwata bata d nuna kishi ko ganin kyashi a kan abinda take Wannan karon ma Najaatu a gida ta haihu tare da taimakon Dr Sa'adatu Allah ya sauketa"

"lafiya inda ta haifi 'yan tagwaye duk maza lafiyayyu dasu, sai dai bayan haihuwarsu mahaifa tayi gaddamar fitowa kamar dai lokacin haihuwar Daddy Dr Sa'adatu ta dinga fama tana dabaru irin nasu al'amarin yaci tura dan Najaatun tuni ta durkushe a gurin kanta yana juyawa! Da sauri tacewa mijin nasu ya fito da mota suje asibiti itama al'amarin yafi karfinta Abbah bai ta'ba sanin haka mata suke shan wuya gurin haihuwa ba sai akan Najaatu tsabar tausayi sai da ya zubar mata da hawaye, ga dai 'ya'yansa tsaf yana ganinsu da rai da lafiya amma Najaatunsa na halin rai da rayuwa. Tare da ita dashi suka sata"

a mota Dr Sa'adatu ta goya d'aya ta rungume daya a kirjinta ta shiga motar yaja suka tafi asibitin nasarawa inda take aik. Ko kafin su isa ya kira Halisa a waya ya sheda mata tare da bata umarnin ta

"biyo bayansu asibitin domin ta taimakawa Dr din da wani abu, Halisa bata tafi ba sai da ta sanar da zainab Halin da ake ciki Zainab jikinta yay sanyi ta nemi guri ta zauna gabanta na fad'uwa hankalinta ya kwanta ta samu ciki zuwan wannan ranar itace garari gadai Najaatu ta haihu amma rayuwarta na cikin"

k'ila wa'kala! Jiki a sanyaye ta shirya ta nufi asibitin itama.

Najaatu ta galabaita mutuka kafin mahaifar twins d'in ta fito ko bayan ta fito ma jini ne ya tsinke mata

"hankalin narses din yay masifar tashi, itakam Dr Saadatu duk kwarewar ta akan aikinta kasa katabus tayi tsabar fargaba da tashin hankali! (Ubangiji Allah kasa muga da ita lafiya had'arin haihuwa nada yawa)"

"Da kyar aka samu nasarar tsayar da jinin dake fita, aikuwa ba'aja da nisa ba aka sa mata wani gudun"

"abunda ka iya zuwa ya dawo...........Sai bayan hankali ya kwanta ne ya samu damar kiran wayar 'Yar uwarsa Ramlatu ya fad'a mata haihuwar yace ta fad'awa su Hajia suna asibiti, Yaya ramlatu ta tambayeshi lafiyar maijego da yaran yace suna nan lafiya lau be fada mata abinda ya faru da Najaatun ba....."

Naja'atu sai data kwana uku a kwance a asibiti sannan ta dawo daidai ta fahimci abinda ta haifa da kuma

"jamaar dake zuwa dubata! Alhaji da Baba Malam zuwansu biyu asibitin dubata, Baba Talatu kuwa tunda tazo sau daya bata sake zuwa ba tana ganin kamar zuwan nata bashi da amfani tunda ba itake bada lafiya ba bayan haka kuma Mutanan na iya bakin kokarin su akan Yarinyar shiyasa ta zauna a gida ta cigaba dayin addua akan 'yar tata. Aunty Maryam kuwa kullum da ita ake yini a asibitin sai yamma tayi take tafiya. Koda suka koma gida ma haka 'yan uwa da abokanan arziki suka dinga zuwa dubata tare"

da ganin yaran har bayan kwana bakwai 'kafa bata dauke a gidan ba.

Abbah kudi ya fitar masu yawa yayi hidimar haihuwa dasu maijego da 'ya'yanta yay musu hidima sosai

"hakanan suma sauran matansa da 'ya'yansa yayi musu daidai gwargwado ranar da suka ware domin suna kowa ya fito gwanin ban sha'awa, haihuwar Hassan da Husaini tayi albarka sosai dan gidan ma'kil yayi da jamaa ta kowanne fanni kowa yazo nuna farin cikinsa, Zainab ta sauko ta mayar da komai ba komai ba har 'yan uwanta sai da suka zo bikin sunan, Itama Halisa nata 'yan uwan sunzo kamar yanda itama Dr ta gayyato nata dangin dukkaninsu har yaran suka had'u a falon Dr Sa'adatu suka sashi a tsakiya suna ta daukar hotunan tarihi! Abbah Abbas sai murmushi yake duk ya rasa inda zai saka kansa sabida farin ciki duk inda ya waiga sai yaga iyalinsa cikin walwala da farin ciki sai kawai ya shige godewa Allah a bisa ni'imar da yayi masa burinsa ya cika ya had'a mata hud'u gashi sun fara tara masa zuria abinda yake mutukar so a rayuwarsa yanzu 'ya'yansa bakwai bayan d'an da Halisa ta haifa babu rai yana"

rokon Allah ya cigaba da azurta shi da 'ya'ya masu albarka.

Najaatu watanta uku da haihuwa yaranta sunyi kwari ta nemi alfarmar akan ya barta taje jos su gurin su

"Mmm Sajida, hanata yayi yace ba zata je yanzu ba sai yaran sun sake 'kwari hakura tayi ta kyaleshi ta cigaba da kula da 'ya'yanta dama tuntuni Daddy ya zama d'an gidan hajia ya jima a can dan har ya"

manta da cewa itace uwarsa Yaya Ramlatu ya ri'ke a matsayin uwa tunda da ita ya saba.

Lokacin da sukayi wata shida ta sake masa maganar zuwa jos nan ma ya dinga yi mata wasa da hankali

"ya'ki yayi mata magana d'aya, takaici yasa tasa shi a gaba tana kuka tana fad'a masa cewar bai dace ace ta watsar da mutanan ba koda be barta ta kwana ba to ya bari taje ta dawo a rana daya, da kyar ya barta tare da kafa mata dokoki tace to ta amince, Tare da Yaya Ramlatu suka tafi saboda ta taimaka mata da raino, a waya ta kira Mmn Sajida ta fada mata cewar gata nan akan hanya amma ba kwana za tayi ba, Mmn Sajida da sauri ta shiga gidan Mmn Ladi ta sheda mata a take suke shiga hidimar abinda zasu sauketa dashi...............Najaatu tayi mamakin yanda Mmn Sajida da Mmn Ladi suka karramata sun jere gabanta da kayan abinci nau'i nau'i sai farin cikin ganinta suke suna ta nuna farin cikinsu akan kyautar da Allah yay mata Mmn Sajida ta dauki Hassan ta rike tana ta sa masa albarka itama Mmn Ladi ta dauki Hussain sai addua take masa Najaatu hawaye ta shiga sharewa tana mamakin irin kaunar da mutanan ke"

mata. Wannan karon ma manya manyan atampopi ta kawo musu da mayafai masu kyau da tsada

"kana ta basu kudi masu yawa tace su cigaba da juyawa akan wanda suke, rasa bakin godiya sukayi"

dukkinsu sai da suka zubar da hawayen farin ciki Sai da zata tafi Mmn Sajida ke fad'a mata cewar

itama ta kusa aure dan har ta kar'bi sadakin wanda zata aura. Najaatu ta dinga farin ciki

78 / 79