Chapter 52 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   52 / 79

153K to 156K   out of 235.1K words

wattanin da suka gabata ranar sai daya samu cikakkiyar gamusuwar da yake bukata da yarinyar...Zainab taji maza! ai lokaci guda ta shiga hankalinta ta daina rawar kai kullum a tsorace take da angon nata dan tun ranar daya mayar da ita cikakkiyar mace ya daina d'aga mata k'afa kullum sai ya biya bukatarsa har kwanaki bakwai d'inta suka"

"qare, ta dinga murna tana godewa Allah zata sarara."""

******

'Bangaran Naja'atu kuwa abun babu dad'in ji dan tun ranar data samu labarin auran Abbah Abbas taqi

"lafiya ciwon kai ciwon kirji da dai sauran ciwoka! Gashi sai 'boyewa Mmn Sajida take taqi ta bari ta gane bata da lafiya, to itama Mmn Sajidan da yake 'yar sabga ce bata fahimci komai ba sai dai sa'i da lokaci idan ta kalli Naja'atun takance"" Naja'atu duk kin rame kinyi haske dan Allah ki cire damuwa da fargaba daga ranki! wallahi nasan iyayenki nacan hankalinsu a tashe sakamakon rashin ganinki ke kuma sabida wata manufa taki kin'ki kije garesu, duk fa abinda ya faru da rayuwarki qaddarace iyayenki musulmai ne"

"zasu kar'bi qaddarar da Allah ya dora miki ba zasu guje ki ba."""

Duk sanda Mmn Sajida tayi mata wannan maganar ba ta cewa komai sai da tayi murmushi tayi shuru da

bakinta.

Mmn Sajida haushi yasa ta tattarata ta qyaleta da taurin kanta.

To kamar yanda suka yanke shawara kancewa Hajia Rabi zata je garin jos domin dauko Naja'atu hakane

ya kasance Direba ya dauketa da wurwuri suka nufi garin Sai dai tun kafin direban yayi parking din

motar suka hango gate din gidan garqame da 'katon kwado! Ga unguwar shuru babu wanda zasu tambaya. Hajia Rabi ba tayi qasa a gwiwa ba ta dauko wayarta ta kira mijinta domin sanar dashi halin da

"ake ciki Alhaji Ya shiga mamaki mutuka yace.""Lallai su samu wani a unguwa wanda zasu tambayi domin"

yayi musu qarayin bayani .......Direba ya fito ya tsaya jikin mota yana kallon yanayin unguwar...Cikin ikon

"Allah wani bawan Allah yazo wucewa sai ya tsayar dashi da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa yace.""Malam dan Allah ko kana da labarin mutanan nan gidan nan."" Ya fada yana nuna masa gidan"

"Mutumin ya jima yana kallonsa kafin yace.""Amma ba a garin nan kake ba ko.""? Da sauri yace.""Eh kwarai"

"kuwa."" Mutumin ya girgiza kansa gami da fara bashi labarin abinda ya faru da mutanan gidan ya rufe"

"maganarsa da fad'in 'Wannan gidan da kake gani yanzu yana hannun bank dan haka tun wuri ku bar gurun nan tun kafin jama'a su ankara daku."" Da"

Haruna Direba ya mika masa hannu yana masa godiya ya bude mota ya shiga...Ya kunna da sauri suka

fita daga layin gidan Sai da suka hau titi sosai san Ya sanar da Hajia Rabi abinda mutumin ya fad'a

"masa. A sanyaye tace""Wannan al'amari baiyi dadi ba ko kadan ko yanzu ina Naja'atu take? Kira ne ya"

shigo wayar ta ta dauka da sauri dan ganin wanda ya kira.

"Alhaji yace.""Ina fata kun samu cikakken bayanin inda Naja'atu take, a sanyaye ta shiga fad'a masa"

maganar da mutumin nan ya fad'a dangane da gidan Aminu Dan jaridan....Alhaji yayi shuru yana tunanin inda zasu samu Naja'atun a cikin garin Jos.

*ANA WATA GA WATA*

Wani masifaffan amai ne ya tashe ta daga baccin da takeyi na safe! A guje ta dafe kirjinta ta nufi bakin

rariya ta dinga kwararawa tana wani irin kakari tare da dafe kirjinta. Ta kai minti goma tsugune a

"gurin kafin ta dan samu sassauci ta dauraye bakinta tare da mikewa tana dafa bango(garu) ta ciko buta da ruwa tazo ta wanke gurin data 'bata, tana tangadi ta koma daki ta zauna tana mayar da numfashi Bayan Mintina ashirin tana zaune a takure zazzabi na neman rufeta ta sake jin wani"

"aman ya sake yunkuro mata da masifar qarfi! da sauri ta mike ta nufi bakin rariya ta tsuguna tana yi tana hawaye! tun tana amayo abinci har sai da ta dawo amayo ruwa shima ruwan ya daina fitowa sai miyau da majina ne kadai ke fita, kuka takeyi tana kiran sunan Allah ta samu gefan rariyar (kwata) ta kwanta tana wani irin nishi tare da janyo numfashi da kyar! Naja'atu haka ta yini kwance a bakin rariya daga taji yunkurin amai sai tayi ta kakari amma babu abinda zai fito sai miyau mai dacin gaske Haka Mmn"

"Sajida ta dawo daga cefane ta sameta lokacin ma ta galabaita sosai dan jikinta yayi laushi duk ya saki Hankali a tashe Mmn Sajida ta shiga gidan Mmn Ladi suka fito tare, a daidaita sahu suka samo"

suka kamata dakyar suka sata a ciki suka zazzauna a gefanta domin ri'keta asibitin kudi Mmn Sajida tace su nufa dan ganin yanda Naja'atun ta galabaita yasa ta yanke wannan shawarar tana jin tsoron kada yarinyar mutane ta mutu a hannunta a tuhumeta shiyasa take gani ko nawa ne zata iya kashewa domin

samun lafiyarta.

Gwajin farko Dr ya tabbatar musu da cewar tana da ciki dan kimanin sati tara! Wata biyu da sati daya!

Mmn Sajida Da Mmn Ladi suka shiga cikin mamaki mai tsanani Ciki ciki! lallai Allah ya had'a Naja'atu da babbar qaddara........

*Littafin na kudi ne...!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake. Vip

group #600 normal group #300 accont....0542382124...Binta umar gtbank. Idan katin waya zaki tura sai

kiyi min mgn ta wahsap da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*MANZIR _ALWAFIR ABUJA *

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a

ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar

dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

"*****60 Mmn Ladi tace""Dama fa ni wallahi sai da jikina ya bani cewar haka zata iya kasancewa kawai"

"dai dan yarinyar ta nuna bata san maganar ne yasa nayi shuru amma da tun farko ta dauki maganata da muhimanci munje asibiti sun dubata sosai a lokacin da sai mu san yanda zamuyi da cikin tunda baiyi kwari ba amma yanzu ciki har ya shiga wata na uku ai akwai matsala idan akace za'ayi wani yunkuri a kansa, gaskiya na tausayawa yarinyar domin haihuwa da irin su Bash matsala ne da da yanda za'ayi"

kawai a zubar da cikin nan wallahi.

"A sanyaye Mmn Sajida tace""Nima dai jikina yayi sanyi wallahi amma bari ta tashi daga bacci muji"

"hukuncin data yanke."" Ajiyar zuciyarta da shashshekar kukanta sukaji."

da sauri suka kalli gadon da take kwance! Ta bude idonta a hankali hawaye wani na bin wani ta kalli

"Mmn Sajida murya na rawa tace""Ciki ne dani ko.""? A sanyaye Mmn Sajida ta daga mata kai"

"Rintse idonta tayi hawaye suka cigaba da zubowa'' Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un.""! Ta furta wannan"

kalmar tare da sake bude idonta tana kokarin mikewa zaune. Mmn Ladi dake kusa da ita ta taimaka

mata ta zauna tana goge hawayen fuskarta amma kamar bata gogewa wasu ne suke zubowa.

"""Allah na kar'bi wannan kyautar da kayi min ba zan sake yunkurin sa'ba maka ba Ubangiji Allah ka ingata"

"abinda ke cikina Allah kasa ya zama cikon addinin musulunci."" Wannan maganar ta fad'a tana me tsurawa rufin dakin ido."

"Mmn Ladi tace""Bamu gane me kike nufi ba Naja'atu yanzu sabida baki da hankali sai ki yarda ki haifi cikin"

"nan to wane labari mai dadi zaki bawa d'an da kika haifa idan ya girma? ai kwanciyar hankalinki da samun nutsuwar ki kawai ki zubar dashi shine yafi alkairi a tattare dake."""

Girgiza kanta ta dinga yi tana kallonsu tana kuka kokarin tsayar da ruwan hawayen dake gudana a

"fuskarta, tace""Bazan 'kara aikata kuskuran da nayi a baya ba Mmn Ladi koda ace wannan cikin ta hanyar banza na sameshi ba zan zubar dashi ba sai na haifeshi domin ban san munufar ubangiji a kansa ba."

"Wallahi mutukar kinga ban haifi cikin nan ba to Allah ne bai nufa domin ni yanzu abinda zai kusantani da ubangiji nake so ba abinda zai nesanta ni dashi ba, a baya nayi kuskure wanda har yanzu nake cikin nadamarsa, to bana fatan na sake aikata wani kuskuran da Allah zai yi fushi dani ya tuhume ni a ranar"

lahira kawai ku dai taya ni da addua kan Allah ya rabani dashi lafiya.

"Wannan kalaman nata sune suka kashe musu jiki Mmn Sajida tace""To shikkenan Naja'atu zamu cigaba"

"da taya ki addua kan Allah ya saukeki lafiya ya kuma kawo miki mafita a rayuwarki, ammafa yana da kyau ki koma ga iyayenki domin zaman da kike a tare damu bashi da wani amfani na fad'a miki duk inda iyayenki suke suna can hankalinsu a tashe suna neman inda kike me zai sanya ki dinga jin tsoro da"

"tunanin wani abu daban."""

"Ajiyar zuciya ta sauke tace""Mmn Sajida ko dai kin gaji da zama dani ne? ko kin gaji da ciyar dani abincinki"

"shiyasa kike wannan maganar.""? Mmn Sajida ta shiga girgiza kanta tana murmushi mai ciwo"

"tace""Gaskiya Naja'atu ban ta'ba tsammanin jin wannan maganar daga gurinki ba Haba dan Allah meye"

makwanci meye kuma abinci da har kike tunanin saboda su nake cewa kije ga iyayenki! To idan tunanin da kike kenan ki daina Mmn Sajida ba haka take ba duk wani abu da nake miki inayi miki ne tsakani da

"Allah bada wata manufa ba."""

Naja'atu qasa tayi da kanta tana nadamar maganar data fad'awa Mmn Sajida dan sai bayan ta fad'i

"maganar ne ta gane kamar bata kyauta ba, tasan halin Mmn Sajida macace mai karamci da mutuncin itace zata fad'awa wani hakan"

Likita ne ya shigo dakin hannunsa rike da wata farar takarda! Ya mikawa Mmn Sajida da fadin duk wasu

"bayanai na jikin takardar nan idan kun duba zaku gani."" Mmn Sajida da Mmn Ladi basa jin turanci sosai shiyasa basu fahimci rubutun da likita yayi a jikinta takardar ba."

"Naja'atu ta kar'bi takardar tana dubawa, gabanta ne ya fad'i ganin kudin gadon data kwanta yini guda"

dubo goma sai kudin magungunanta dubu bakwai da dari biyar. qasa tayi da kanta tana jin nauyin fad'a

musu abinda ke rubuce a takardar. To a Ina Mmn Sajida taga dubu goma sha bakwai yanzu gabad'aya

Jarin abincin siyar wa ta baifi na dubu ashirin ba dashi take ci take sha ita da 'yayanta yanxu idan ta

sanadiyar ta ta ruguza mata sana'arta me zata ce.? jikinta ne yayi sanyi sosai ta tsirawa takardar ido tana tunanin yanda za'ayi.

"Mmn Sajida tace""Naja'atu me Dr din ya ruboto."" A dan sanyaye tace""Mmn Sajida me yasa kuka kawo ni"

"pravite hospital baku kaini na gomnati ba.""?"

"Mmn Sajida tace""Naja'atu tsorata nayi da yanayin yanda ganki shiyasa na yanke shawarar kawo ki"

asibitin kudi domin ayi gaggawar dubaki sanin da nayi cewar idan na gomnati mukaje kafin ma mu samu kati babban aiki ne sannan idan mukaje gurin ganin likita nan ma sai mun 'bata lokaci shiyasa kawai na

"yanke wannan shawarar."""

Wasu hawaye masu zafi suka sauko a kumatunta gaskiya ta tabbatar da cewar Mmn Sajida masoyiyarta

ce har ta mutu ba zata ta'ba mantawa da karamcinta ba.

Shuru dakin yayi Mmn Sajida jikinta yayi sanyi itama tana jin tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya

"dawo...Tace""Nawa ne kudin gadon dana maganin insha Allahu ba zai gagara ba."""

"Ta kalleta tana girgiza kanta tace""Dubu goma sha bakwai da dari biyar."" Mmn Ladi ta ri'ke bakinta cike"

"da mamaki tace""Dubu goma sha bakwai harda wata dari biyar a kai! Tabdijam! ko awa hud'u ba kiyi a kwance ba har kinci wannan kudin."""

"Naja'atu tace""Ba kudin gado bane kadai harda na magani."" Mmn Ladi tace""Duk da haka dai wallahi da"

"tsada haba abin yayi yawa dubu goma sha bakwai fa ba kad'an bane gaskiya asibitin nan suna da tsada ta'bdijam.""! Mmn Sajida tace""Duk mu bar maganar dan Allah ko nawa suka rubuta ai hakkinsu ne tunda dai mu muka zo neman taimako kuma sun taimaka mana a lokacin da muke bukata bai kamata mu tsaya surutu ba, Yanzu ni abinda ke hannuna gabad'aya dubu bakwai ne dama na ajiyesu saboda wata matsalar, amma yanzu zan koma gida zan dauki buhun shinkafar dana siyo shekaran jiya zan kaiwa"

maigari mai kanti ya siya nasan idan na siyar za'a had'a kudin

"Girgiza kanta ta shiga yi tace""Kin san Allah Mmn Sajida ba zaki ruguza sana'arki kaina ba! Ban amince ki"

"siyar da shinkafar ki ba."" Mmn Sajida tace""To ya kike so ayi? Kin san dai babu wanda zanje gurinsa da bukatar ya bani aron kudi ya bani kai tsaye mutane yanzu kwata kwata basa bada bashin kudin."

Naja'atu shuru tayi tana tunanin yanda za tayi gaskiya ba zata bari Mmn Sajida ta rusa sana'arta a kanta

"ba tunani ta shiga yi ko ta kira Abbah Magaji a waya ta fad'a masa halin da take ciki! Girgiza kanta tayi, gaskiya ba zata iya kiransa a waya ta fad'a masa cewa ya taimaka mata da kudin magani ba saboda tasan halin masifarsa, kuma bata manta cin fuskar da tayi masa ba tana jin kunya sosai 'Daya bangare na"

zuciyarta yace mata kawai ki kira wayar Abbah Abbas zai taimaka miki tunda dama shi mai tausayi ne zai iya turo da kudi a biya asibiti kudinsu. Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin kamar wannan shawarar data

yanke itace shawarar data dace dan gaskiya ba zata amince da shawarar Mmn Sajida ba. Suna tsaka da

"tunanin mafita likita ya sake shigowa ya kalli Mmn Sajida da fad'in ""Hajiya ku muke saurara dan tuni mun sallameku ku biya asibiti hakkinsa."

"Murya na rawa Mmn Sajida tace"" Dr kayi hakuri yanzu zan je gida insha Allahu kafin goma na dare zan"

"kawo maka kudin."""

"Dr yace""Ni tara tana yi na tashi daga aiki wani ne zai maye gurbina kuma kuka kwana to kud'inku ya"

"qaru zaku biya dubu ashirin da bakwai da dari biyar."" Mmn Ladi ta zare ido tana kallonsa! Ita kuwa Mmn Sajida mi'kewa tayi da sauri tana fad'in ""Insha Allahu yanzu zan dawo."" Dr ya kalli agogon hannunsa da"

"fad'in ""Okey idan kika wuce tara baki dawo ba to ba zaki sameni ba."" Yana gama maganarsa ya juya da"

niyyar fita.

"""Dr."" Muryarta ta katse musu hanzari daga shi har Mmn Sajidan da take kokarin bin yansa domun"

"tafiya. Duk suka juyo suna kallonta, tace""Idan babu damuwa ina bukatar ka bani aron wayarka zan kira"

"mahaifina da ita insha Allah za'a tura maka kudinka."""

Dr yayi kasaqe! yana kallonta kafin ya d'an d'age kafad'arsa ya dauko wayarsa dake gaban aljihun rigarsa

"ta likitoci ya karasa har bakin gadon da take zaune ya miqa mata. Ta kar'ba a sanyaye, tana dubawa"

dama kafin ya bata wayar sai da ya cire mata sucurity da yake kai Tana tararrabi da fargaba ta sanya

numbar Abbah Abbas din a wayar ta shiga gurin kira gabanta na wani irin fad'uwa ta shiga kiran wayar. Daf da zata katse aka d'aga! ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya tana jiran taji muryarsa sai

"kawai taji murya mace mai tafe da iyayi da feleqe! tana fad'in ""Waye yake magana.""? Gabanta ya dinga dukan uku uku! wacece wannan? Take tambayar kanta, tasan muryar Halisa kuma tasan muryar Saddiqa Mussadiq Mufida! muryar wannan me maganar ce bata tantance ba, Zuciyarta tayi saurin fad'a mata cewar amaryarsa ce! ji tayi idanunta na neman rufewa! tsabar fargaba! Tayi gum! da bakinta takasa magantuwa tana jin muryar Zainab sai magana takeyi amma uffan ta kasa cewa. Zainab tace"" To ikon"

Allah waye wannan anata magana yana ji yayi shuru tsaki taja ta kashe wayar. Naja'atu ta shiga

"rarraba idonta a dakin gumi! na tsatstsafo mata! Dr yace.""Ke nake saurare naji kamar an d'aga wayar ana magana kuma baki ce komai ba."

"Da sauri ta dawo hankalinta tace""Yi hakuri Dr bari na sake kiran wayar bana ji sosai shiyasa na kasa"

"magana."" Okey kawai yace ya zuba mata ido yana kallonta tamkar zai lasheta. Zainab hannunta r'ike"

"da wayar ta kama hanyar fita palo inda Abbah Abbas din ke zaune yana hutawa.. tana daf da karasawa inda yake wani kiran ya sake shigowa, a maimakon ta kai masa wayar sai kawai ta d'aga tare da kara wayar a kunnanta da fad'in ""Waye yake magana."" Naja'atu ta daure da kyar tace.""Nice.""? Zainab jin miryar mace yasa gabanta faduwa tace""Kece wa.""? Abbah Abbas yayi saurin juyowa yana kallonta jin"

yanda tayi maganar cikin izzah! da gadara!

'Bangaran Naja'atu kuwa ji tayi tamkar yarinyar ta soka mata wuqa a kirjinta jin yanda take wani daka

"mata tsawa kamar uwarta! har ta hasala! sai kuma ta sassauta zuciyarta tace.""Naja'atu."" Zainab tayi shuru tana mamaki! Naja'atu Naja'atu? tasan sunan rad'au! a bakin yaran gidan kuma ta samu cikakken bayani a bakinsu da sauran jama'ar gari tunda dama hausawa nacewa ko haqa rami kayi ka bunne abu to wata rana sai ya fito an ganshi, duk labarin Naja'atu tasan shi daga farko har'karshe sai dai duk yanda take zungurar maigidan kan maganar koda wasa bai ta'ba bata wani labarin da ya dangace shi dashi da"

"Naja'atun ba. ""Oh! nagane to wa kike nema.""?"

"Naja'atu murmushin takaici tayi Kai tsaye tace""Ina neman mijinki ne idan yana kusa ki basa wayar zanyi"

"magana dashi."" Zainab tace""Okey kada ki damu."" Sai kitt! ta kashe wayar ta nufi inda yake tana wata karairaya ga wani tsadaddan murmushi a fuskarta, zama tayi a kusa dashi tasa hannu a fuskarsa tana shafa gemunsa tare da wasa da karan hancinsa tace""Masoyinta sannu da hutawa."" Kafad'arta ya r'ike hankinsa na kan wayarsa dake hannunta ya kar'ba yana fad'in ""Waye ya kira ne.""? Tace"" Wata ce aka samu akasi ta kira number ka."" Abbah Abbas bai gamsu da maganarta ba

52 / 79