Chapter 16 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 79

45K to 48K   out of 235.1K words

yana kallon bayansa, duk da akwai duhu a"

"dakin bai hanashi hangota a can 'kuryar gado ba, ya dan shafa kansa cikin wani irin hali na damuwa gami da bukatuwa ya mike ya nufi toilet domin ya tsarkake jikinsa. Har ya fito daga toilet din bai daina jin"

"sheshshakar kukanta ba, sai ya kunna fitilar dakin a take dakin ya gauraye da haske."

"Rintse idonta tayi da saurin gaske tana sake matse jikinta guri guda, bed din ya hau, sai ta zabura tana"

"rawar jiki tace""Abbah dan Allah kayi hakuri kada kayi min komai."""

Ganin yanda take ta makale jikinta a jikin bed din yasa ya dan janyo hannunta aikuwa ta 'kwala 'kara!

had'e da fizge hannunta ta sauka daga bed din tana kare jikinta da bedshirt din hannunta.

"Ranshi ne ya 'baci da abinda take yi kawai sai ya rabu da ita ya kai hannu ya kashe hasken dakin,"

kwanciyarsa yayi ya rufe kafafunsa da blankent.

Ita kuwa kan Sofa ta lalla'ba taje ta zauna tana me tsirawa bed ido gani take kamar zai biyo ta kan

"kujerar................Abbah Abbas bacci ne ya dauke shi bacci mara dad'i baccin da ya sanya shi mafarkai barkatai. Naja'atu kuwa yanda taga dare haka taga rana sai gefin asuba bacci ya soma fizgarta, jin motsin"

tashinsa yasa firgigit ta mike zaune tana zazzare ido.

Yana kunna hasken dakin ya mike ya nufi toilet ya daura alwala kamar dai yanda ya saba ya gabatar da

nafila kafin ya wuce massalaci Sai da ya fita sannan ta sauke ajiyar zuciya ta mike da sauri taje ta duba

rigarta tasa ta dauki hijabinta ta zura da sauri ta fita daga dakin.

"Dakin su Saddiqa ta nufa koda ta shiga dakin sai ta gansu duk a kwance basu tashi ba, taji dadin hakan"

"da sauri ta nufi toilet din dakin, ta tub'e kayan jikinta, ruwa ta hada tayi wanka kana tayi brush sai ta daura alwala ta fito A gurguje ta shirya ta tsaya kan Saddiqa tana tashinta, gabadayansu suka tashi"

"tace""Ku tashi kuje kuyi alwala."""

"Saddiqa ce ta fara tashi ta nufi toilet din, ita kuma ta gyara dadduma ta tayar da sallah."

Bayan ta idar da sallar kwanciya tayi kan daddumar ta takure jikinta daga zarar ta tuno da abinda ya faru

a tsakaninta da Abbah Abbas sai gabanta ya yanke ya fad'i! har yanzu le'bunanta zafi suke mata idan ta tuno da yanda ya dinga shan bakinta tsigar jikinta duk sai ta mike.

"Mussadiq ne yazo ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ta mike a sanyaye tana amsawa, Saddiqa da"

Mufida ma suka gaisheta a nutse ta amsa musu. 'Dakin ya shigo hannunsa ri'ke da wani

"maidaidaicin carbi, Naja'atu tayi saurin sunkuyar da kanta 'kasa kwata-kwata bata so ta had'a ido dashi."

"Ya tsaya daga bakin kofa yana fadin ""Ashe kun tashi."" Mussadiq yace.""Eh Yaya Naja'atu ce ta tashe mu."""

"Ya d'an kalleta da gefan idonsa, ya kauda kansa yana amsawa gaisuwar 'yayansa, juyawa yayi zai fita yaji muryarta tana gaishe shi, ba tare da ya Juya ba ya amsa, ya bude kofar dakin ya fita."

"Gabad'ayan su suka mike zasu fita tace""Ina zakuje.""? Saddiqa tace""Zamuje mu gaisa da Mommy ne."""

shuru tayi tana kallonsu suka fita daga dakin..

"Lokacin da suka shiga gaishe da Halisa yana tsaye a dakin suna magana, ya bisu da kallo har suka fita"

"yana mamakin ina ita Naja'atun wato ba taji maganarsa ta jiya ba kenan? a tunaninsa zata biyo yaran suzo gaishe da Halisan tare, Inda ita kuma sam ba tayi tunanin hakaba saboda ba gaishe da Halisa ne a gabanta ba abinda ke gabanta shi ya dameta.........Ya kalli Halisa a nutse yace.""To yanzu nawa kike ganin"

zasu isa.?

"Mikewa tayi daga kan daddumar da take zaune tana kokarin cire hijabin da tayi sallah dashi tace""To ka"

"zauna mana sai nayi maka lissafi."" Jim yayi kafin ya zauna! dan yana sane ya'ki zama a dakin saboda yasan halin da yake ciki na sha'awa baya so taja ra'ayinsa ya aikata wani abun da ita a cikin hakkin wata."

"Zama tayi kusa dashi tana nanikar jikinsa, ya kalleta babu yabo babu fallasa yace.""Kiyi min bayanin nace"

"kamar nawa ne zai isa da zaki siyo mata sutturun da suka dace."""

Fuskarsa ta shafa da hannunta ta kai bakinta kan kuncinsa ta manna masa kiss! tana me d'ora hannunta

"a cinyarsa, ganin irin abinda take masa ne yasa ya gane abinda take nufi! Yace.""Kin san dai ba'a cikin kwanakin ki kike ba ko.""? Marairaicewa tayi tace""Haba ai kaima kasan ba zab iya bari har sai nan da"

"kwana shida ba wallahi, ni dai gaskiya a bukace nake."""

"Kallonta ya shiga yi yana mamakin maganarta, yace.""To nima bani nake da kaina ba sai kije ki tambayi"

"mai hakki idan ta baki aro na shikkenan."""

"'Bata rai tayi tana sake shigewa jikinsa tace""Allah ya kiyaye na tambayi yarinyar nan wani abu kaine kake"

"da iko da kanka kuma kafi kowa sanin halin da nake shiga idan ina cikin wannan halin dan haka ni ba zan iya sauraran komai ba sai na samu biyan bukatata."" Kallonta kawai yake dan shi ya rasa ma abinda zai ce mata, yana jinta tana ta shashshafa jikinsa tana masa salo iri-iri to abinka da wanda dama yake a bukace"

"a take ya bada kai bori ya hau, suka shiga biyawa junansu bukata..."

Gabad'ayansu har ita suka fito palo suka zazzauna suna hira kar'fe takwas shuru basu ga gilmawar masu

"gidan ba, tara ma tayi shuru, basu fito ba, A hankali ta kalli Mussadiq tace""Ko Abbanku ya fita ne.""? Yaron ya girgiza kansa da fad'in ""Wallahi ban sani ba dazu dai da muka shiga gaishe da Mommy na ganshi a dakin."""

"Shuru tayi tana nazarin maganar yaron, ta kalleshi cikin sanyin jiki tace""Kana jin yunwa ko.""? Kai ya"

"d'aga mata, mi'kewa tayi ta kalli Saddiqa da Mufida tace""Kuzo ku nuna min kicin din na had'a muku break fast."" Suka mike da sauri suna murna, tare suka shiga kicin din nan suka shiga aiki kowanne ta bashi abinda zai taimaka mata dashi Halisa ta samu abinda take so sosai ta ri'ke wuta ta'ki"

barinsa ya huta shi kuma jinta zam-zam! ya dinga d'imautar dashi ya kasa hakura da ita suka dinga abu daya kamar jaraba koda yake dama can sun saba tunda jajayen sawun su. Sai kusan goma da rabi ya

"fito daga dakin, lokacin su har sunyi break dinsu suna zaune dai a palon suna hira wanda take saka musu baki jefi-jefi Ido suka had'a ita dashi lokacin da ya fito daga dakin Halisan duk sai ya diririce! lokaci"

"guda ta gane rashin gaskiyarsa kuma ta gane abinda suka dade sunayi a dakin, wace irin magana ce za'ace an shiga daki sama da awa uku anayi ai da akwai alamun tambaya. 'Dauke kanta tayi sam"

"bata wani ji ciwo ba dan ba wai sonsa take ba ballanta taji haushin abinda sukayi mata, cigaba tayi da dan dudduba wayarta dake hannunta, Shi kuma da sauri yake kokarin shiga dakinsa. Mussadiq"

"yace.""Yawwa Yaya Naja'atu ga Abban namu ya fito dama nace miki bai futa ba."""

Da sauri ta kalli yaron tana d'an hararasa! Shi kuma Abbah Abbas din tsayawa yayi yana kallon Mussadiq

"din yace.""Waye yazo nema na.""? Shuru tayi, Mussadiq yayi karaf yace."" 'Dazu ne Yaya Naja'atu take tambaya ta wai ko ka fita saboda munji shuru bamu ga ka fito daga dakin ka ba shine nace mata kana"

"dakin Mommy."""

Naja'atu taji kamar ta kwad'awa yaron mari! kada fa Ya d'auka ko sonsa take shiyasa take tambayarsa

"Shi kuwa Abbah Abbas murmushi yayi yana dan shafa gemunsa ya kalleta a nutse yace.""Ina tare da"

"Halisa muna tattauna magana mai muhimanci insha Allah anjima zakuje tare dake da ita ki za'bi irin kayan da kike so domin ita na wakilta ta had'a miki lefe."" Tsakaninsa da Allah ya fad'i maganar dan shi"

yana ganin meye a ciki dan Halisa ta had'a mata lefe ai duk a zaman d'aya!

Ita kuwa Naja'atu maganar ce ta girmi tunanin ta wannan ma ai rainin hankali ne da zaice Halisa ta had'a

"mata lefe kuma har ya iya fad'a mata da bakinsa, zuciyarta tace mata ""To ke meye abin damuwa ai ba sonsa kike ballanta na dan yace Halisa ta had'a miki lefe kiji haushi!!! "" Eh duk da ba sonsa nake ba amma ai hakan bai dace ba abin kamar yazo da cin fuska a ciki, to idan ya kasance tana sonsa kuma haka zai dinga d'ora kishiyarta kan al'amuranta abinda ba zata iya jurewa ba kenan don ita ba Yaya Halimatu bace. Dauk'e kanta tayi ba tare da tace masa komai ba, shi kuma yanayin yanda yaga ta nuna sai"

"yaji wani farin ciki ya lullu'beshi yana addua Allah yasa yarinyar ta soma sonsa. Yana shiga daki, Ita"

"kuma ta shiga fad'a da zuciyarta ganin kamar tana so ta takura mata gurin ganin kamar anyi mata rashin adalci a gidan zuciyarta sai ingizata take akan ta dauki mataki ta bishi daki ta tambaye shi me tsaya yayi a dakin Halisa har tsayin awa uku alhalin yasan a cikin kwanakin auranta yake, sannan kuma tace ita bata yarda Halisa ta had'a mata lefe ba!.....Allah mai iko! abinda zuciyarta keta sa'ka mata kenan duk ta kasa samun nutsuwa a gurin sai kallon kofar dakin nasa take tana tununin taje ko kada taje? Mikewa tayi ba tare da dogon nazari ba ta nufi dakin nasa har tasa hannu zata bude kofar sai kuma ta fasa, ta juya cikin"

sanyi jiki ta nufi dakinsu Saddiqa kwanciya tayi ruf da ciki kawai ta tsinci kanta da fashewa da kuka.

*Tofah! Ko kukan me Naja'atu take? Ita da take ikirarin bata kaunar Abbah Abbas din to meye najin

haushi dan ta ga ya dad'e a dakin matarsa? Lallai akwai alamun tambaya dangane da Al'amarin Akwai-Akwai_Akwai!! Rikita_Rikita anan agaba! Wai shin ya zata kaya ne a tsakanin

Abbah Abbas da Amaryarsa? Shin zai samu nasarar kar'bar budurcinta ko kuwa? Salim zai kyale Naja'atu tayi rayuwar aure da Mijinta Kuwa? Wane Babban kuskure Naja'atu zata tafka anan gaba? Meye makomar Yaya Ramlatu da Halisa? akwai sauran labari anan gaba!!!! Ga duk wanda yake da ikon biyan kudin littafin nan ya biya ya karanta #300 ko #600 basu isa su biya kudin littafin nan ba Koda yake ai 'KARYA ce amma dai ni nasan 'karyar tawa tana Tasiri a wani gurin dan haka da kai da ke ina so duk ku

biyo ni domin a cigaba da tafiyar daku Single #300 Vip #600 Babu tsada Kada ki nuna ganin 'kyashin

biyan kudi ki karanta kice bari ki bari idan an sato ki kiranta Allah ya isa! Idan anyi magana kice kema

"gani kikayi an turo shiyasa kika karanta, to duk wanda ya'ki sharar massalaci zaiyi ta kasuwa! *"

*Masu had'a min decoment na books daga zarar na gama bazan ce komai ba sai dai na ro'ki Allah ya

tattara muku zunuban da na d'auka gurin rubuta littafin ya d'ora muku a kanku Shikkenan sai a raba mana zunubin tare daku kun rage min nauyi.*

*Masu tambayar wai ni bana littafin free ne sai na kudi: Amsa To farkon littafina Nana Khadija Free ne

"zagi da 'korafi gami da rashin hakuri irin na redars yasa na mayar dashi na kudi, tun daga haka shikkenan na daina littafin kyauta amma akwai book dina RUWAN DARE free ne book1 yana nan yana yawo a groups ga duk mai bukatar karantawa sai ya tambaya a groups insha Allah idan na gama rubuta littafin MADADI zab cigaba da typing d'insa RUWAN DARE free ne bana kudi bane! idan na gama Madadi zan"

cigaba da rubuta muku shi *

*Masoya masu sahihiyar kauna Ina alfahari daku *

"*GA MASU BUKATAR KARANTA BOOK DIN ZASU TURA #300 SINGLE, VIP GROUP #600 GA ACCONT"

D'IN DA ZA'A TURA KUDIN.......0542382124.....BINTA UMAR GTBANK. IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA

KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBAR......07084653262 IDAN KIN SAN BA BIYAN

KUDIN LITTAFIN NAN ZAKI YI BA DON ALLAH KADA KI KIRA WAYA TA KO KIYI MIN WATA MAGANA TA WHASAP*

*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA SO KU BIYA KUDIN LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN

NUMBARS. 90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE.*

Mdd

*21*

"Halisa kuwa bayan fitar maigidan daga dakin, cikin farin ciki ta d auki wayarta ta shiga kiran Yaya"

"Ramlatu, duk ta shaida mata abinda ke faruwa, ta fada mata cewar maigidan ya bada kud'i kimanin dubu"

dari biyu yace wai a siyawa amaryarsa kayan lefe masu kyau sannan yace ma idan basu isa ba ta fada

"masa. Yaya Ramlatu taja tsaki! tace""Ko dubu dari ba za'a kashe mata ba gurin had'o lefen komai 'kananu za'a siya mata dan haka idan kin tashi tafiya kasuwar ki biyo ta gidana mu tafi tare."" Halisa tace""Eh to da cewa yayi wai muje tare da yarinyar ta duba abinda takeso."" Yaya Ramlatu tace""Ki san dubarar da zaki masa ki fito ke kad'ai meye wani dole sai anje da ita."" Halisa tace""Zan nuna masa yarinyar ta zauna ta kula da yara insha Allah za'a siyo mata komai mai inganci."" Yaya Ramlatu tace""To ke kuma nawa ya baki kudin naki kayan."" ? Murmushi tayi tace.""Nima dubu dari biyu ya bani kamar nata kuma yau da daddare yace zai shigo min da mukkulin sabuwar motata."" Yaya Ramlatu ta rangad'a bud'a tace""To Alhamdullhi babu shakka kwalliya ta soma biyan kudin sabulu dan haka idan zaki zo kada ki manta da al'kawarinmu"

"dake."""

"Halisa na dariya tace""Haba Yaya Ramlatu ai 'Yar halak ce ni insha Allah zan kawo miki."" Cikin farin ciki"

"Yaya Ramlatu tace""To Allah ya 'kara mallaka miki mijinki a hannuki."" Halisa ta amsa da amin tana cike da farin ciki ganin ta kowane 'bangare tana samun biyan bukata. Cikin shararriyar kwalliya ta fito palon"

"ta samu yaran suna zaune a palo suna kallo, ba tare da tace musu komai ba ta nufi dakin maigidan, shima lokacin yana kokarin fitowa cikin shirin fita, ganin uwar kwalliyar da taci tana kamshin turare sai ya 'bata fuska yace.""Keda zaki shiga kasuwa kuma meye nayin kwalliya harda shafa turare."" Tayi fari da ido kamar yanda ta saba idan za tayi masa magana tace""Wallahi shaf na manta ban fad'a maka ba yau ne bikin sunan 'Yar yayata data haihu a unguwar Gaida to inaso in fara zuwa can kafin naje kasuwar."" Yace.""Anya kuwa sai dai ki za'bi d'aya dan idan kin tafi suna da zuwa kasuwa lokaci zai 'kure baki dawo gida ba."" Da sauri tace""Shine ai nace mai zai hana ita Naja'atun ta zauna ta kula da yaran tunda amarya ce bai kamata ace daga zuwanta ta fara yawo ba insha Allah zamuje tare dasu Shamsiyya zan siyo mata komai mai kyau wanda ake yayi."" Yana gyara zaman hularsa a kansa yace.""Wannan shawarar taki tayi"

"kyau dan gabadaya banyi tunanin hakan ba okey muje sai na ajiye ki a gidan bikin."""

"Farin ciki ya cika mata zuciya, ta juya tana wata irin tafiya irin ta manyan mata."

"Tsakiyar palon ya tsaya yana kallonsu, ya kalli Mussadiq da fadin""Ina Yaya Naja'atu.""? Yaron"

"yace.""Tund'azu data shiga daki bata fito ba mybe bacci take."" Ba tare da yace komai ba ya nufi dakin yaran."

Ruf da ciki ya sameta bayan ta gama kukanta bacci ne ya dauketa a haka. Ya tsaya kanta yana k'are mata

kallo. Halin da ya shiga lokacin da yake kiss d'inta jiya kawai yake tunowa yarinyar nada wani sirri

na mussaman a tare da ita. Hannu yasa ya dan shafi gefan fuskarta yana kiran sunanta

Ta bud'e idonta wanda kuka da bacci ya mai dasu wani iri! shi kuwa ai ji yayi tsigar jikinsa ta tashi ganin

yanda idanunta suka jirkice kamar wacce take ciki sha'awa.

Gyaran murya yayi kamar yanda ya saba ya sake kiran sunanta.

"Mikewa zaune tayi tana goge fuskarsa had'e da d'an zum'bura baki ta'ki kallon inda yake tsaye. Yace.""Za"

mu fita tare da Halisa zaki zauna tare da yara kafin ta dawo da nace zakuje tare domin ki duba abinda kike so sai kuma yanzu take ce min zata je bikin suna ina ganin ke sai ki zauna tare da yaran a gida kafin

"Allah yasa ta dawo."" Fuskarta ta goge tana kallon kasan gadon da take zaune tace""Nifa Abba daka bar"

"kudinka bana son wani lefe kayan da nake dasu ma sun isheni."""

"Cikin d'an mamaki yace.""Saboda me? ai hakkinki ne dole nayi miki tunda inada iko."" Kamar ta fad'a"

"masa mara dad'i sai dai tayi shuru tana d'auke kanta, tayi al'kawarin ko an siyo kayan ba za tayi amfani dasu ba."

"Agogon dake daure a hannunsa ya dan kalla sha biyu shaura na rana ya nufi kofar fita yana fad'in ""Sai"

"mun dawo ki kula da kanki da yara."" Wani irin kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin taja tsaki mai karfi ta koma ta kwanta."

"Halisa a bakin titi tasa ya ajiyeta tace ya sauketa zata shiga da 'kafa, nan ya 'kara jaddada mata cewar"

kada ta kai dare tayi ta gama duk abinda za tayi ta koma gida da wuri. ta amsa masa kamar gaske tana d'aga masa hannu

"Tana ganin motarsa ta wuce ta tari a daidaita sahu ta shiga kai tsaye unguwar gwangwanxo ta nufa,"

"dama tun kafin taje ta shaidawa Ramlatu gata nan a kan hanya dan haka a shirye ta tarar da ita ba kuma tare da 'bata lokaci ba suka dauki hanyar gidan 'Yar Sa'adu! koda suka isa gidan cike yake da manyan mata masuji da kansu, kamar dai koda yaushe 'Yar sa'adu na zaune kan kujerarta mata sun kewaye ta suna ta d'aga magungunan mata suna dubawa ita kuma tana musu 'karin bayani a kan maganin, 'Yar

16 / 79