Chapter 46 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   46 / 79

135K to 138K   out of 235.1K words

zama da mata biyu yana ganin ba zai iya bari ba, mussaman yanzu da Halisa ta zama hoto a gurinsa dan tsoron tunkararta yake da bukatarsa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo an samu da kyar ta samu lafiya yana jin tsoron yaje ya zunguro mata ciwon ya dawo shiyasa tsayin wattani uku da faruwar al'amarin bai tunkareta da wata maganaba, ba wai dan baya jin sha'awa ba kawai yana daurewa ne domin a zauna"

lafiya.

Misalin karfe hud'u da da kwata na yamma Salim yayi parking din dalleliyar sabuwar motarsa da Kawun

nasa ya siya masa ya fito daga motar cikin shigar 'kananun kaya kamar koda yaushe yasha gayu kana ganinsa kaga dan burni....Daya bangaran ya nufa ya bude mata ta fito Wata matashiyar budurwa ce ta

"fito daga motar mai matsakaicin tsayi! babu laifi tana da kyau daidai gargwado sai dai kuma bleecing din da takeyi ya soma lalata mata fatar jikinta kana kallonta zaka gane idanunta a bude suke! Tana sanye da atampa super dinkin doguwar riga mai falmaran da madauri a baya, tayi wani katon a cuci da yayi tsayi a kanta tayi rolling da karamin gyale kafafunta na sanye da takalmi mai tsayin dunduniya da madaurai! lebenta kuwa yaji jan jan baki tana da fara'a sosai dan data fito daga motar ma sai dariya take tana haske shi da hakoran makkan dake bakinta Salim sai murmushi yake yana jin dadin samun Salimat a matsayin matar da zai aure Salimat ta ture hamshakan maza masu kudi da muqami tace shi take so! shiyasa yau ya dauko ta ya kawo ta ta gaisa da kakaninsa Hajiya da Alhaji! Gefe guda kuma yana so ya cizgunawa zuciyar Naja'atu dan ba karamin jin haushinta yake ba dangane da nuna halin ko in kula da take masa gabadaya ta watsar dashi tana nuna masa dashi da babu duk daya tunda ta samu wanda ya"

fishi! shine shima yau ya dauko Salimat ya kawo musu ita su ganta..

Hajiya da Naja'atu suna zaune a palo su Salim suka shigo! Hajia na ganin Salimat jikinta yayi sanyi ikon

"Allah a ina Salim yaje ya samo wannan tsohuwar ai ta girmeshi! Daurewa tayi ta kawar da abinda ke zuciyarta ta karbi Salimat hannu biyu suka gaisa a mutunce."""

"Naja'atu na dan mirmushi tace""Salim wannan itace antyn nawa."" Yace.""Eh ya kika ganta."" Yar dariya tayi"

"tace""Wallahi tayi kuma kun dace Allah ya nuna mana lokacin yasa zaayi damu."""

Salim baiyi tsammanin haka da gurinta ya dauka za taji haushi sai yaga akasin haka sai ma jan Salimat din

"take da hira. Da zasu tafi hajia tayi wa Salimat kyauta sabulai da turaruka masu kamshi, Naja'atu har"

bakin mota ta raka Salimat din tana daga mata hannu Wannan al'amarin da ya faru ya sanya salim

jikinsa yayi sanyi ashe dai da gaske Naja'atu ta daina sonsa. Koda yake shima yasan Bash yafi shi komai

da komai na rayuwa amma dai duk da haka yasan shine yake da nasara a kanta tinda har ya samu damar ruguza zamantakewar auranta da Kawunsa.dama babban burinsa kenan.

Bayan Sati hud'u Naja'atu ta 'kare iddarta alhamdullhi Mahaifin Bash tare da 'yan uwansa guda biyu

sunzo da sadakinsu an tattauna maganar daurin aure. cikin wad'anda suka kar'bi sadakin sun had'a da

Alhaji Sama'ila Abbas Abbas 'Kanin Baba Malam mai suna Ya sayyadi Nazifi! Abbah Magaji kam koda ya samu labarin zuwan iyayan Bash din cewa yayi yana da uziri a kasuwa ba zai samu zama ba babu wanda ya tursasa shi akan dole ya zauna a karbi sadakin dashi ya kama hanya yayi tafiyarsa kasuwa. Abbah

Abbas kuwa sai bayan sun kar'bi sadakin sun tsayar da ranar daurin aure sati biyu masu zuwa ya sami sukunin tafiya harkokinsa. Naja'atu a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa burinta zai cika na

auran muradin zuciyarta idan ta tuna da cewar harda Abbah Abbas a cikin wa'yanda suka kar'bi sadakinta sai taji wani farin ciki ya lullu'beta tasan komai ya wuce a gurinsa kamar yanda ya fad'a mata a text dinsa tunda har ya tsaya a cikin al'amuranta to tasan da cewar tuntuni ya yafe mata shiyasa ta saki

jikinta take harkokinta cikin kwanciyar hankali.

*Massalacin Juma'a na b.u.k*

Kamar yanda muka sani cewar mafi akasari malaman addini gami da limamai na da wani irin tsari da

"a'kida a kan 'ya'ya yansu na aurar dasu ga wanda suke ganin yana da yanayin aqidar su da d'abi'arsu to hakane ya kasance da *Malam Sharif Bala* wanda ya kasance fitaccen malamin da yayi fice a jahar kano, wanda kuma ya kasance limamin babban massalacin juma'a dake b.u.k. mutumi ga Abbah Abbas"

wanda suke da kyakkyawar alaqa mai kyau a tsakaninsu to yau bayan an idar da sallahr juma'a ya

tsayar da Abbah Abbas din domun ya sheda masa irin kyautar da yayi masa saboda ganin cancantarsa da

kuma yanda yake tsaye a kan addininsa da kuma hidimtawa addinin musulunci yaga dacewar ya bashi 'Yar sa Mai suna Zaibab yar kimanin shekara goma sha biyar

To lokacin da Abbah ya gama sauraran uzirin Limamin sai yayi wani murmushi mai ma'ana yana

"godewa da Allah a zuciyarsa, a lokacin da yake yunkurin dubawa kansa macen da zai aura sai gashi lokaci guda anyi masa kyautarta babu shakka ba zai watsawa mutumin qasa a ido ba, dik da cewar bai san yarinyar ba bai kuma ta'ba ganinta ba hakan ba zai hanashi kar'barta ba a matsayin matar auransa"

"ba, yana adduar Allah yasa auranta ya zama alkairi a rayuwarsa."

Malam Sharif yaji dadi sosai da Amincewar da ya samu daga gurin Abbah Abbas d'in inda a nan take

yace Juma'a mai zuwa za'a a daura aure a ka kawo masa yarinyar gidanshi....Anan shi kuma Abbah

"Abbas din ya kawo masa uzirinsa kan cewar yayi hakuri ya d'an bashi lokaci kadan zai yi wasu shirye shirye, malam sharif ya amince da uzirinsa amma bai yarda a ja dogon lokaci ba."

****

Bayan sati daya da zuwan iyayen Bash ranar Alhamis Sai gasu Munira ita da ka'wayen mommynta da

'Yan uwanta sunyi mota biyu suna tafe da setin akwatina mai shida shida goma sha biyu kenan! Ko wacce akwati sha'ke da kaya tamkar za'a bude dan karamin kanti! akwai wani dan kit dake dauke da gwala gwala manya manya masu masifar nauyi da tsada! Al'amarin da yayi masifar firgita Baba talatu ita da 'Yan uwanta irin wannnan uban kaya da uban gold sai kace ana hauka!!! kafin 'yan kawo kaya su tafi zance ya soma tashi a unguwa cewa ashe Naja'atu mai kudi ta gani shiyasa ta fujirewa auran Mijin 'Yar uwarta kai kowa dai d irin abunda zai fad'a akan al'amarin da yawa daga cikin mutanan unguwa sai suka dawo ganin laifin Baba Malam a ganinsu ai shine bai tursasa yarinyar ta zauna da Auran madadin da akayi mata ba suna ganin shima kamar kwadayin abin duniya ne ya sanya ya amince da rabuwar auran to idan ba hakaba mutanan da sukayi maka hallaci ai bai kamata ya watsa musu qasa a ido ba. Haka

dai rukuni rukunin mata suka dinga shigowa wai sunzo ganin lefa!Baba talatu ita da ido kawai take binsu dashi tana mamakin sanya ido da bindiddigi irin na mutane. Ya Ramlatu data samu labarin abinda ke

faruwa bata zauna ba sai da taje ta kashe kwarkwartar idonta aikuwa ta dinga addua Allah yasa d'an yankan kai yarinyar ta daukowa kanta. Ita kam Naja'atu ko a jikinta al'amarin bai firgitata ba saboda

tasan a irin kaunar da bash yake mata zai iya narkar da gabadaya kud'ad'ansa akanta.

Ana ya gobe daurin auran da yamma Naja'atu ita da Salimat budurwar Salim dan yanzu sun zama

qawaye tun salim na jin haushi har ya hakura ya kyalesu...Salimat ita ta kai Naja'atu gurin gyaran jiki aka gyara mata jikinta sosai sannan akayi mata kitso da lalle wanda yayi masifar yin kyau! Naja'atu ta fito amarya sai wani murmushi take tana jin nishadi Bayan sun dawo ita da Salimat din gidan Baba malam

"suka shiga, nan suka tarar da Aunty maryam da Baba talatu a zaune suna tattauna al'amuran da suka shafesu...Naja'atu koda taga aunty maryam kunya ce ta rufeta sai ta sunkuyar da kanta kasa tana yar"

dariya gami da gaisheta

"Aunty maryam tace""Ai dole kiji kunyata naja'atu abubuwan da kikayi baki kyauta ba koda yake dawo da"

"abinda ya wuce bacin rai ne saboda haka ina miki fatan alkairi da adduar Allah yasa gidan zamanki ne Allah ya baki zaman lafiya da nutsuwa zaman aure da mijinki."" Baba Talatu ta daure fuskarta sosai da"

"sosai tace""Dama inaso na aika a kira ki domin akwai maganganun da nake so nayi dake!"

"Naja'atu tayi shuru gabanta na faduwa Baba talatu tace""Babu abinda zance a cikin wannan auran naki"

sai dai nayi shuru da bakina amma bana yi miki fatan nadama a rayuwarki ammafa ki sani duk wanda kika zalinta a cikinmu idan bai yafe miki ba sai hakki ya kama ki! Gobe za'a daura miko aure da wanda kike so kuma goben dai zaizo ya daukeki ku tafi can inda yake...Ina so na fada miki cewar ki zauna a dakinki duk rintsi duk wuya kada wata wahala tasa kiji sha'awar dawowa gida domin ki 'karasa zubar mana da sauran mutuncin da muke dashi a cikin unguwa! Babu maganar kawo kara ko kuma yaji ki zauna komai wahala tinda ke kikaji kika gani zaki iya! Daga karshe nake miki fatan alkairi da samun

"nutsuwar da kike bukata."""

Kuka kawai takeyi ta kasa cewa komai! shin me wad'annan maganganun na mahaifiyarta suke nufi a

kanta? Idan ta fahimta kenan Baba talatu na nuna mata cewar tunda suka dauketa suka bawa Bash sun yafeta daga zuriarsu kome.? Aunty maryam ce kawai ta rarrasheta amma baba talatu sabgar gabanta kawai takeyi....Jiki a sanyaye suka mike suka nufi gidan Alhaji Suna shiga gate din gidan Abba Abbas na

kokarin fitowa daga mota Salim yayi saurin rufe motar bayan fitowar tasa. Salimat kasancewar tasan

"matsayin sa a gurin Salim yasa da sauri cikin ladabin karya ta tsuguna har kasa tana gaisheshi! ya amsa cikin kulawa gami da kokarin ratse su ya wuce!! Naja'atu ta bisa da wani irin kallo gabanta na fad'uwa, gwiwa a sage suka shiga palon Nan suka sameshi shida mahaifiyarsa suna maganar data shafesu,"

"hajia Abu ganin sun shigo yasa ta saki fuskarta da fad'in"" Naja'atu kun dawo ai ina nan inata fad'a kan cewar wannan irin gyaran jiki ne ace tin safe ku fita babu ci babu sha ai dole ku galaibata! A sanyaye ta zauna kan kujera da fadin."" Wallahi hajia guraran La'asar muka dawo mun shiga gidan baba malam ne"

"kuma munci abinci a can."" Hajia tace""To alhamdullhi dama tunani na inda zaku samu abinci kuci."

"Naja'atu a hankali ta d'an saci kallon inda yake zaune tace""Abbah ina wuni inasu Mussadiq.""? Ya dan"

"kalleta babu yabo babu fallasa yace.""Lafiya lau Naja'atu Mussadiq na gida lafiya."" Shuru tayi na second biyu kafin tace""Abbah Dan Allah gobe a kawo min su inaso na gansu."" Wani irin kallo ya watsa mata wanda yake nuna alamun baki isa ba, ya dauke kansa ba tare da yace komai ba ya mi'ke tsaye yana duba"

agogon hannunsa ya kalli mahaifiyarsa tare da fad'in shi zai wuce gida sai da safe idan ya shigo daurin

"aure."" Hajia tace""To Allah ya kaimu amma kada ka manta ka tawo mana da yaran domin nima ina"

"kewarsu koda yake ai kai dama ka saba rowar 'ya'yanka ko gaisuwar juma'a baka kawo su."" Murmushi kawai yayi ya kama hanyar fita tare da fad'in ""Insha Allahu idan be manta ba zai zo dasu.Hajia tunda taji ya fadi haka tasan ba kawo su zaiyi ba sai kawai ta shiga girgiza kanta tana mamakin hallayar d'an nata"

kamar shi kad'ai ne mai 'ya'ya a duniya baya so ko kad'an 'ya'yansa su matsa daga kusa dashi..

*Littafin na kudi ne...*

Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake. Vip

gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank. Idan kati zaki turo kiyi min

mgn ta whasap da wannnan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

Cikin rashin walwala gami rashin nutsuwar zuciya Abbah Abbas ya shiga gidansa . duk a sakamakon

"tozali da yayi da yarinyar da ya riga ya cire ta gabad'aya daga cikin rayuwarsa to sai gashi a yau ganin da yayi mata ya tayar masa da tsumin sonta da jin wani irin kishinta gami da jin kishin yaron da take shirin aura, tunda ake maganar auran bai ta'ba shiga yanayi na damuwa da tashin hankali irin yau ba, wannan yana nufin cewar yau yayi mata ganin karshe kenan tun gobe zasu daura mata aure da wanda suka kar'bi sadakinta dashi wannan al'amarin shine ya janyo masa ji wasu kibiyoyin kishi wanda suka zo suka tokare masa a maqoshinsa! da kyar yake iya bude baki yayi magana tsabar yanda yake jin wani irin tu'ku'ki! bakin ciki a cikin zuciyarsa, koda ya fito daga motar bai tsaya duguwar magana da Salim ba sai kawai ya daga masa hannu ba tare da yayi wata magana ba ya nufi cikin gidan nasa. Salim kuwa cike da farin ciki ya juya kan motar domin fita daga gidan Halisa ta d'an ji dama dama"

"gabadayansu suna zaune a palo ita da yaran ya shigo, suka shiga yi masa barka da zuwa harda Baba larai dake ta kokarin kintsa musu gurin cin abinci Ya daure sosai ba tare da ya nuna musu damuwar da"

yake ciki ba ya amsa ya d'an tsaya yana magana da yaran kafin ya nufi dakinshi Halisa cikin faduwar

"gaba da tararrabi tabi bayansa, samunsa tayi zaune a gefan gado yana kwance a gogon hannunsa, ta zauna a hankali tana sake yi masa barka da dawowa, bai kyareta ba kuma be hantareta ba kamar yanda yake mata a kwanakin baya ya amsa tare da umartata data hada masa ruwan wanka! Halisa cike da murna da farin ciki ta nufi toilet din tana adduar Allah yasa ya gama fushin da yake da ita dan ba karamin galabaita tayi da tsatstsauran hukuncin da yanke mata ba. To a takaice dai a daran ranar Halisa sai"

da tayi yanda tayi ya kusanceta ita dashi suka kasance cikin wani irin yanayi na tsantsar tashin hankali da

"damuwa, dan gabadaya Halisa tayi wata iriyar bud'ewa koda Abbah yasa joystick dinshi zuruf ta shige ya"

dinga kokarin ganin ya samu satisfaction abun ya fassakara dan gabad'aya joystick d'in yawo ta dinga yi a headquarter din halisa ko'ina ya motsa sai yaji kwararo-kwararo babu inda ya ri'keshi! Gashi a lokacin yayi masifar kwadaituwa da al'amarin burinsa kawai ya samu gamsuwar da yake bukata amma babu dama! Cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa ya zare jikinsa a nata kawai ya zura kafafunsa kasan gado tare da dafe kansa takaici da bakin ciki kamar su kasheshi Halisa ta janyowa kanta babbar illah a rayuwarta ta cutar da kanta da abinda yake da mutukar daraja da martaba a tare da ita a yanzu da ita da babu duk daya suke a gurinsa tunda ta kasa dauke masa bukatarsa dama wannan dalilin ne yasa yayi ta fargabar tunkararta da wata magana saboda yana gudun 'bacin rai Halisa na zubda hawaye ta dafa

"bayansa tana bashi hakuri duk tayi wani irin sanyi ta zama abar tausayi ita kanta tayi masifar tsorata da jin yanayin yanda gabanta ya bud'e! dan duk wani budiri da yake yi a gurin taji kuma ta gani Jijiyarsa ta kasa tsayawa guri daya sai yawo takeyi a gurin ita a karan kanta tayi tayi duburar da za tayi ta ri'keshi abin ya fassakara gurin ya riga ya sakwarkwace! ya saki tamkar bakin tsohuwar rijiyar data zaizaye ta tana kokarin ruftawa! kokarin kama jijiyar tasa takeyi wai tayi masa dabura irin wanda take masa idan tana al'ada! aikuwa a fusace! ya tureta ya mike yana jan tsaki! bandaki ya nufa domin ya gyara jikinsa, Halisa ta dora hannunta aka tana kuka mai tsanani da fad'in ""Na cuci kaina nayi wa rayuwata illah yanzu menene mafita a gareni? na lalata martabata da mutuncinta nasan yanzu zanyi ta fuskantar kalubalan rayuwa. ('Kalubale gareku mata masu sake saken maganin matsi a gabansu wallahi ku kiyayi kanku"

akwai manya manyan cutuka da zaku janyowa kanku)

Koda ya fito ya tarar da ita tana kuka babu walwala ko ta kwabo a tare dashi yace ta bashi guri baya son

"damuwa yana so ya kwanta ya huta! Jikinta a sanyaye ta dauki rigar baccinta tasa ta kama hanya ta fita daga dakin cikin wata iriyar tafiya tamkar wacce ta rasa laka a jikinta, saboda tsananin bacin ran da yake ciki ko binta da kallo beyi ba ya sanya jallabiyarsa ya hau kan dadduma domin gabatar da sallar nafila"

kamar yanda ya saba yi a dik daran duniya.

*KADDARA TA RIGA FATA!!!!!*

To jama'a da yawa sun sheda da daurin auran Naja'atu malam Sani da Bashir Aminu dan jarida akan

sadaki naira dubu hamsin wanda bayan an watse daga gurin daurin auran kowa ya kama gabanshi Alhaji Sama'ila ya samu Naja'atun da kudin sadakinta ya damka mata a hannunta kana kuma cikin tattausan lafazi ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki! daga karshe yayi mata fatan alkairi gami da zaman lafiya da

mijinta. Naja'atu na kuka tana sauraran nasihar da Hajia Abu ke mata itama dai kwatancin irin ta

mijinta tayi mata sannan itama tayi mata fatan alkairi tare da zaman lafiya a gidan auranta. Sannan da

kanta ta dauketa ta kaita gaban iyayenta tace lallai

46 / 79