Chapter 45 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   45 / 79

132K to 135K   out of 235.1K words

Abbas ya zauna gurin cin abinci da wayarsa a hannunsa, Salim ya kira yace maza yazo ya daukeshi da wuri yake so ya fita....Bayan sun gama waya da Salim a nutse ya karya ya"

"mike ya nufi dakin Halisa, nan ya tarar da ita tana kuka ta takure jikinta a guri guda."

Cike da mamaki yake tambayarta abinda yake faruwa take kuka da safe dan shi gabad'aya ma ya manta

"da abunda ya faru da ita a jiya. Kasa fada masa tayi saboda tana jin tsoro kada yayi mata fad'a! Yace""Ba"

zaki fad'a min abinda ke da akwai ba kin zauna kina kuka meye amfanin hakan da kikeyi ke ba yarinyar kankanuwa ba ki zauna kina aikata abu irin na yara.

"Da kyar tace""Wallahi tun jiya wani abu yayi tsiro daga gabana na rasa kome ye nayi nayi ya koma ya'ki"

"komawa."" Cike da mamaki yace.""Wane abu ne zaiyi tsiro ya fito daga matuncinki sai kace wanda akayi shuka gurin Kinga kiyi min bayani yanda zan fahimta.'' Hawaye ta share tace""Wallahi Abban Mufida ba"

karya nake ba nima na tsorata mutuka wata 'Yar tsokace ta bullutso daga gurin !

"'Yar dariya yayi domin shi abun ma dariya ya bashi Kai tsaye yace""Bud'e min naga tsokar naman data"

"bullutso."" Yafad'a yana nufar inda take. Halisa a tsorace take kallonsa dan gabadaya bata so yaga abin"

tana jin tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo

"Zama yayi kusa da ita yana jan kafafunta had'e da so ya yaye zanin dake jikinta, jikinta ne ya dinga rawa"

"cike da fargaba da tsoro tace""Abban mufida ka bari dan Allah ba sai ka gani ba."

"Yace.""Aikuwa dole sai naga wannan tsokar data bullutso komai 'boye 'boyen ki sai na duba nagaji."" Cike"

da zolaya yake maganar dan gabadaya ma ya mayar da abun wasa da dariya! Halisa hakura kawai tayi ta kyaleshi ya bude mata jikinta yana duba headquarter dinta yana laluben abun da idonsa

Lokacin da idonsa yayi masa tozali da abinda halisa ke fada masa sai da gabansa ya fadi! da sauri ya

"kalleta cikin wani irin yanayi na tashin hankali yace.""Wannan wane irin abune ya fito miki a matunci gashinan har yana kokarin rufe miki kofa shin tun yaushe ne hakan ya kasance dake.""?"

"Halisa data muzanta! mirya na rawa tace""Jiya ne bayan abunda ya faru tsakaninmu sai kawai naji kamar"

ana caccaka min allurai a ciki ga kaikyayin da gurin ya dinga yi bayan na gama sosawa ina shiga bandaki naga abun ya fito.

"Kici kici da fuska yayi yana mata wani irin kallo yace.""Ki dauko min maganin da kika sa wanda ya janyo"

"miki wannan masifar.""! Rantse rantse ta shaga yi ita wallahi bata sa komai ba...Yace.""Halisa kome ki keyi fa na sani nasan irin shaye shayen magunan da kikeyi akaina kuma watarana ina ganinsu da idona na tabbata akwai abinda kikasa a gabanki wanda ya janyo miki wannan abu saboda haka tun kafin ranki ya 'baci ki tashi ki dauko min maganin."" ! Halisa ganin yanda yasha kunu ne yasa ta mike a sanyaye ta bude wardrobe inda take ajiye ajiyen magungunanta ta laluba ta dauko kwalbar maganin saboda haukanta sai"

da ta kusa sanya maganin gabadayansa kadan ta rage bayan kuma ba haka 'Yar sa'adu tace mata ba!

Mika masa tayi ya kar'ba yana dubawa! Bude kwalbar yayi ya shanshana maganin yaji yana wani irin

kamshi tabbas idan bai manta ba jiya yaji kamshin maganin a jikinsa dangwalar maganin yayi a hannunsa yaji wani irin danqo tamkar cingum!! yatsun hannunsa suka had'u da maganin suka manne

guri guda!

"Yace.""A ina kika samo shi.""? Shuru tayi gabanta na faduwa! Tambayar ya sake maimaitawa babu rahama"

ko kadan a tare dashi!. Halisa dake neman mafita tana kuka ta shiga fad'a masa cewa a gurin wata

"matane da Yaya Ramlatu take kaita gurinta. Jin ta kira sunan Ramaltu sai abin ya bashi mamaki yace."""

"Me yasa ko Yaya Ramlatu a cikin shirmen ki? ko dama ita take saki kina shaye shayen maganin mata bana son kiyi mata sharri dan ganin matsala na kokarin afkuwa dake."""

"Tace""Wallahi tunda nake ban san hanyar gidan boka da malami ba sai ta hanyar 'Yar uwarka Ramaltu"

"kome nakeyi itace take d'ora ni a hanya."" Abbah Abbas bude bakinsa yayi kawai yana kallonta yace.""Halisa da bakinki kike fad'a min kina zuwa gidajen bokaye.""? Wani irin kuka ya kwace mata tace""Abbah Mufida ka gafarce ni wallahi ba laifina ne ni kad'ai ba Yaya Ramaltu itace take sani a gaba"

muyi komai tare ni yanzu babbar matsalata wannan matsalar data tunkaro ni!

Girgixa kansa kawai yake yana mamakin al'amarin! ikon Allah 'Yar uwarsa uwa daya uba d'aya itace ke

cutar dashi da iyalinsa yanzu meye amfanin d'ora Halisa a turba mara kyau da Ramlatu keyi! menene amfanin cutar dashi da takeyi? me yayi mata a rayuwa da har zata bada goyan baya a cutar dashi idan halisa tayi masa asiri matarsa ce zata iya aikatawa amma ita saboda k'arfin zumunci da 'yan uwantaka

bai kamata tayi masa haka ba

Ya jima yana kallonta gabadaya kansa ya kulle ya rasa wane irin tunani zaiyi dangane da wannan

mummunar maganar da yaji daga bakinta wai Ramlatu 'Yar uwarsa uwa daya uba daya itace take jagorantar matarsa domin xuwa gurin bokaye a asirce shi Halisa ganin yanda ya zuba mata ido yana

mata wani irin kallo yasa takasa tsayar da hawayen dake zubo mata sai yanzu ta fahimci wautar da ta tafka gabadaya bata cikin hayyacinta shiyasa tayi su'butar baki ta fad'a masa abinda suke shukawa shin yanzu idan yayi bunkice ya tabbatar da gaskiyar maganarta da wane ido zata kalleshi na farko dai ita da kanta ta fad'a masa tana zuwa gurin malamai da bokaye babu wanda yayi mata sharri ballantana ta kare

kanta...Sunkuyar da kanta tayi ta cigaba da kuka tana murza yatsun hannuwanta!....

"Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya Mi'ke tare da duba agogon dake daure hannusa yace."" Idan kina"

iyawa ki tashi muje asibiti domin a duba a ga abinda keda akwai amma ki sani bani kika cuta ba kanki kika cuta wallahi idan kina zuwa gurin boka domin ki mallake ni 'Karyar ki tasha 'karya ni ba irin mazajen da mata ke kaiwa gurin bokaye bane wai ko kunyata baki ji ba da bakin ki kika fada min cewar kina zuwa gurin malamai! shin me na rage ki dashi? meye bana miki a rayuwa zaki dinga biye biyen bokaye me kike nema a duniyar nan wanda bana miki? Halisa tayi shuru sai kuka take. Ya girgiza kansa yana jin wani irin

"takaici da mugun haushinta yace.""Kada kiga na rabu da Naja'atu ki dauka zan zauna dake ke kadai 'Karya kike koda baki kaini gurin malamanki ba sai na sake aure kuma budurwa zan aura in yaso sai ki sake d'aura d'amarar kai sunana gurin bokayenki. Sannan kuma maganin banza da kike sha a kaina kada ki daina kanki kike cuta bani ba."" Halisa kuka kawai take tana bashi hakuri wai wallahi tsautsayi ne ita bata"

kaishi gurin malami dan a cutar dashi ba!

Cikin tsawa mai tafe da hantara yace tayi masa shuru domin kwata kwata shi ba zai saurari maganarta ba

"da bakinta ta fada ba wani shege ne yayi mata qazafi ba. Shuru tayi kamar ruwa ya cinyeta hawaye sai tsiyaya yake a kuncinta tana jinsa yana ta zabga mata cin mutunci tayi 'kus! da bakinta addua ma take ka da yace ya saketa!! Da zai fita daga dakin a fusace! yace.""Idan kinga dama kina iya fitowa na kaiki"

"asibiti ba dan halinki ba."" Yana gama maganarsa ya fita daga dakin rai a 'bace!"

Sosai Dr Sa'adatu ta shiga tsananin tashin hankali ganin abinda ya zazzago daga cikin matuncin Halisa

dake kwance a wani hado kafafunta a bud'e! Dr Sa'adatu kasa aikin tayi ita kadai sai da ta kira 'Yar

uwarta suka zo suna ta wagewa Halisa kafarta suna haska headquarter d'inta da wata 'yar 'karamar fitila

"irin tasu! Dr Na'ima ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Halisa da cinyoyinta suke rawa tsabar tension hawayen ma sun daina zuba sai zazzare ido kawai take Dr Na'ima tace""Gaskiya Hajia Halisa kin bani mamaki"

wallahi! yanzu da girmanki da shekarunki kike aikata aiki irin na matasan yara kefa uwace ke zakiga yara na aikata abu mara kyau ki hanasu Fisabillilahi yanzu abinda kikayi ya kamata? ina amfanin cushe cushen maganin mata da kukeyi? kullum maganar da mukeyi kenan a kafafan sadarwa kancewar mata su daina irin wannan kwamacalar saboda muhimancin virginal d'insu ya wuce ace su had'a shi da komai! Guri ne mai muhimanci a jikinki mace da ya kamata ta mutuntuna shi amma saboda cutar kai kawai sai kuje ku dinga siyan maganin da baku san da wace tsiyar aka had'ashi ba kuzo ku cusa a matuncinku wai duk dan ku mallaki namiji humm! wannan zalintar kaine dan a yayin da wata matsala ta afku dake shi wanda kikeyi dominsa bazai saurareki ba karshe ma kina zaune ya dallo miki amarya sabuwa dal kuma baki isa ki hanashi ya aikata abinda yake so da ita ba. Yanzu dan Allah wa gari ya waya? Hajia Halisa kin dade

kina sake saken maganin mata a gabanki ba tare da kina tunanin wata matsalar ba sai gashi kuma lokaci guda matsalar ta afko miki a sanda bakiyi tsammani ba. Dole na sanar miki da abinda ke faruwa dake

hajia cikin tsokokin naman dake gabanki wani bangare ya samu nakasu sakamakon cushe cushen maganin da kike yasa naman gurin ya zazzago ya fito wanda idan ba'ayi da gaske ba to ruwan dake a fita a gurin zai iya janyo miki shiga matsala babba dan gurin zai iya fitar da tsutsa ba tare da kinyi tsammani ba! amma yanzu munyi kokarin mayar da tsokar data fito insha Allah akwai magungunan da zamu rubuta miki mutukar an siya kuma kina amfani dasu a kan 'ka'ida wannan ruwan dake fita a jikinki zai tsaya kuma wannan abun daya fito zai koma mazauninsa amma akwai sharad'i kan cewar maigida zai daina kusantarki har sai mun tabbatar da cewar gurin ya daidaita sannan sai ku koma mu'amular aure kamar koda yaushe! Sai kuma shawarata karshe da zamu baki dake da masu aikata hakan dan Allah ku daina ba lallai sai ta wannan hanyar bane zaku mallaki mazajenku kuma ku daina yarda da rantse rantse da dik wata mai magani za tayi muku akan ko wane irin maganin da zata baku tace kusa a gabanku. duk macen da tayi sabo da cushe cushen magani a gabanta to babu shakka tana tattare da dana sani anan

gaba.

Halisa kunyar duniya ce ta isheta Yara 'kananu sun gane mata sirrinta suna farfada mata maganar da

"suka ga dama! kai gaskiya bata ta'ba nadamar rayuwa ba irin ta yau! tayi data sani yafi sau dari a cikin zuciyarta kuma sai yanzu tagane wautarta ta kuma gane mugunta Yaya Ramlatu take mata ai itama macace me yasa koda wasa bata ta'ba yarda ta siyi magani tayi amfani dashi ba, sai dai ita tayi ta ingixata tana siya da kudi mai tsada gashi yanzu matsala mai muni ta afkar mata ita tana gefe guda babu abunda ya dameta. Cike da kunya ta mike zaune tana gyara daurin zaninta gabadaya ta kasa had'a ido"

dasu sabida kunya su kuwa da yake akan aikinsu suke sai bayani suke mata suna gargadinta akan ta

daina abinda take aikatawa domin cutar da kanta take..

*Littafin na kudi ne..!*

Koda zaki ganshi a gruop to na sata ne idan kina bukatar karanta book din ga yanda abin yake...Vip

gruop#600 normal gruop#300 account 0542382124...Binta umar gtbank...Idan kati zaki turo kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*MANZIR _ALWAFIR ABUJA *

_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a

ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar

dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_

53

"To koda Halisa ta kira Yaya Ramlatu a waya ta sanar mata da halin da take ciki, Ya Ramlatu sosai ta shiga"

tashin hankali mutuka domin a yanda Halisan take kuka tana fad'a mata abinda ya sameta ko waye dole ya tsorata sannan kuma hankalinsa ya tashi...Da yake mijinta ya dawo kuma itace da girki yasa ba taje gidan a ranar ba sai dai kullum tana kiranta a waya tana tambayar ta yanayin jikin nata. To da sauki

dai za'ace dan Halisa ta shiga taitayinta sosai da sosai kuma bata wasa da shan magani da wanda akace ta dinga sawa a cikin headquarter din nata kullum sai tasa sau uku a rana shiyasa al'amarin yayi sauki dan ruwan dake fitowa ya ragu sannan kuma abinda yayi tsiro fito ya koma amma dai duk da haka idan

tasa hannunta tana ta'boshi sai dai ba kamar kwanaki uku da suka wuce ba....

Gabad'aya Halisa tayi sanyi a gidan kullum tana daki a kwance tana tunane tunane tana zubda hawaye!

Baba larai da yaran sai da suka fahimci cewar matar gidan na cikin damuwa dan duk irin iko da isar da takeyi a gidan ta rage ko magana za tayi musu cikin sanyin murya take...Shi kuwa Maigidan sabgar gabansa kawai yake yi dan a cikin kwanakin al'amuran sa suka sake bunkusa Ya samu wasu manya manyan kwangila daga gomnati shiyasa gabadaya baya samun lokacin kansa ballanatana na wani amma dai duk da haka yana kokarin shiga dakin halisan ya dubata kafin ya fice harkokinsa. Kofar na'isa ma

tun ranar da yaje bai samu damar sake zuwa ba sai dai idan ya dawo gida yakan kira iyayen nasa a waya

su gaisa da juna.

Yaya Ramlatu bata samu damar zuwa duba Halisa ba sai da mijinta ya tafi tukkuna dan Kishiyarta Sakina

"zaunar da mijin nasu tayi ta sheda masa duk irin abunda Ramlatun takeyi idan baya gari! Aikuwa ya fusata sosai dan sabida yasan halin sakina ba zata ta'ba fada masa karya ba, ya bud'ewa Ramlatu wuta sosai sukayi ta babu kyau babu dad'i! wanda har sai da Salim d'ansu ya shiga tsakani jin mahaifin nasa na yunkurin sakin mahaifiyar tasa hankalinsa ya tashi ya dinga bawa mahaifin nasa hakuri da kyar ya hakura ya kyaleta amma yayi mata tas tas! kuma jikinta yayi sanyi mutuka dan tunda taji furucinsa a kanta ta shiga hankalinta idan ya saketa ai ya cuceta da girmanta da komai yasa ta zawarci! sai ta hakura ta kyaleshi har ya gama hutunsa na sati uku ya tafi , a ranar kuwa da ya tafi ta dauki mayafi ta yafa ta fice"

daga gidan tana yar da habaici! Sakina girgiza kanta tayi tana mamakin taurin kai irin na kishiyar tata

Halisa ta warware samul! sai dai rashin walwalar maigidan a tare da ita ya sanya duk wani kuzari da

"karsashinta ya dakushe a gidan, al'amarin da ya dameta mutuka gaisuwa kawai ke had'ata dashi da safe......idan kuwa ya dawo daga kasuwa da daddare ya zauna a palo yana dube dubensa a loptop to ta sake ta tunkari inda yake sai tayi nadama dan sai ya farfad'a mata munanan maganganun da zasu sanya zuciyarta bugawa. Dalilin da yasa kenan take kaffa-kaffa dashi amma dai duk wata kyautatawa tana yi"

masa domin ta wanke kanta a gurinsa.

Ga'badaya Halisa 'kin kar'bar uzirin Yaya Ramlatu tayi ta nuna mata fushinta sosai akan abinda tayi mata

ace tayi ciwo irin wannan amma ba zata zo ta dubata akan lokaci ba sai da ta samu sauki sannan zata zo gaskiya ba taji dadin wannan abunba.

Ramlatu ta fad'a mata cewar maigidanta ne ya dawo shiyasa bata samu damar zuwa ba kuma ina laifi

tunda kullum tana kiranta a waya suna gaisawa! Jin haka yasa Halisa ta sake karatun ta nutsu ashe itace mara kishin kanta wacce take wulakanta auranta tana daukar mayafi ba tare da mijinta ya sani ba tana fita! gaskiya bata ta'ba tsammanin haka halin Ramaltu yake ba sai yanzu dole ne kuwa tayi taka tsantsan da ita dan ba zata sake yarda da ita ba tana ingizata inda zata ta kaita inda zata cutu ita kuma tana gefe

guda babu abinda ya dameta.........

To haka al'amura suka cigaba da tafiya tsakanin 'bangarori guda kowanne 'bangare yana yin abinda yake

ganin shine daidai da rayuwarsa' Bangaran Naja'atu sai abinda yayi gaba dangane da soyayyarta da Bash

kullum suna ma'kale a waya suna soyayya sunyi wani irin sabo na ban mamaki! Naja'atu ba tajin kunyar

yin ko wace irin magana da Bash mutukar ta shafi soyayyarsu! Ta daina jin kunyarsa yanzu ko wace magana ya fad'a mata da wacce ta dace da wacce bata dace ba sai ta mayar masa da martaninta sosai ta zama mara kunya saboda alqarta da Bash wanda take ganin shine dadai da rayuwarta. A tsakanin

wattani uku da tayi a gidan Alhaji tayi wani irin qiba da kyau na ban mamaki komai nata ya ciko ta bunkusa ta kai ta kawo babu abinda take bukata sai namiji ita kanta tasan tana da sha'awa a kusa shiyasa take Allah Allah ta 'karasa iddarta a daura musu aure dan ita dashi duk a matse suke da junansu

Bash yace tana kammala idda da sati biyu za'a daura auransu dan ba za'a ja dogon lokaci ba.

'Bangaran Abbah Abbas kuwa tuni ya cire wata Naja'atu cikin zuciyarsa a da da farko ne al'amarin yake

"damunsa daga baya kuma da yaga yanda rabuwarsu ya janyo masa kwanciyar hankali a gidansa dashi kankin kansa da kuma cigaba ta fannin harkokinsa sai kawai ya cireta a ransa ya godewa Allah gami da adduar Allah yasa hakan shine alkairi! Yanzu babban burinsa ya samu nutsuwa ayyukan dake gabansa suyi sauqi ya shiga duba wacce zai maye gurbin Naja'atu da ita dan tunda ya saba

45 / 79