Chapter 59 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   59 / 79

174K to 177K   out of 235.1K words

Naburago ne ya fito daga gidan, yasha shaddarsa harda hula kamar"

"mutumin kirki kai tsaye motar ya durfafa. Dama sun riga sun gama shirya plan dinsu tun a gida. hannu yasa ya kwankwansa gilashin motar. Da sauri Salim ya sauke gilas din ganin Naburago a tsaye yasa da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa Naburago ya gyara tsayuwarsa yana kallon Salim din yace.""A matsayina na wakilin wannan yarinya Salimat na yanke shawara kancewar mun fasa baka auranta dan sabida munyi kyakkyawan bunkice a kanka mungane kai d'in azzalimi ne macuci maha'inci mun samu labari daga bakunan mutane da yawa kancewa kaine ka kunnawa ubangidanka wuta a cikin dukiyarsa wannan dalilin yasa muka yanke shawarar dawo maka da kudin auranka."" Yana gama maganarsa ya kalli Salimat din cikin tsawa! yace.""Maza ki fito daga motar nan ki shiga gida babu ke babu wannan"

"macucin."""

"Salimat ta bude mota da sauri ta nufi gida tana kuka kamar gaske, Naburago yasa hannu aljihu ya dauko"

"kudin Salim dubu Hamsin yasa masa a jikinsa yace ""Ga kudinka nan babu mu babu kai kada ka kuskura na sake ganin kafarka a kofar gidan nan."" Yana gama maganarsa ya bar gurin."

Salim jikinsa ji'kewa yayi da gumi! tsabar tashin hankali makogwaronsa bushewa yayi qamas ya rasa ma

wane irin tunani zaiyi sai kawai ya kifa kansa akan sitiyarin mota yana zubar da hawayen nadama.

****

"*'Yar Sa'adu* ta jangwalowa kanta masifa, matar wani babban soja za'ayi mata kishiya sai ta samu"

labarin *'Yar Sa'adu* da magungunanta sai kawai ta wanko kafarta ta ciko jakarta da kud'i taje 'Yar Sa'adu ta had'ata da magungunan mata iri iri Matar ta tafi gida ta dinga shan magani babu qa'ida ta

dinga cusa maganin matsi wai ita lallai sai gabanta ya matse dan saboda kada amarya ta fita a gurin miji...

"Aikuwa matsalar data afku da Halisa irinta ce ta afku da ita, Soja mazan fama ya bud'e mata wuta danshi"

"har da duka ma ya had'a mata dashi yace sai tayi masa bayanin yanda akayi al'amuranta suka kasance a haka! Ganin rufa rufar da take bashi da amfani sai kawai ta fad'a masa yanda al'amarin ya kasance, takaici yasa shi yayi mata dukan tsiya da blet kuma ya daina kulata, ashe duk hukuncin da yayi mata bai"

hakura ba mota ya cika da sojoji ya sata a gaba suka nufi gidan *'Yar sa'adu me kayan mata*. 'Yar

sa'adu na tare da baki kawai sukaji ihun yara ga unguwar ta cika da kururuwar motar sojoji ai babu shiri

"ita da matan da take a gidan suka fito waje, ganin zaratan sojoji sun durfafo kofar gidanta yasa ta kusa sakin fitsari a wando! a tsaroce tayi nufin komawa cikin gidan gabanta na wani irin faduwa ganin matar sojan data zo ta hada mata magani makwanni biyu da suka wuce babu shakka akwai abunda ke faruwa, takalmin kafarta ne ya gurde ta tsaya zata gyara matar soja da sojojin dake bayanta suka karaso gurin ba tare da jin tsoron komai ba matar ta nuna 'Yar Sa'adu da fad'in ""Gata nan itace matar da siyar da"

"magunguna kan kudi masu yawa."""

"'Yar sa'adu ta diririce ta hau inda inda, Sojan dake kusa da ita ya taska mata mari da fad'in ""Kece kike"

"cutar mata ko kin zama 'yar damfara ki tara mata ki dinga kar'be musu kudi kina siyar musu da abunda zai cutar dasu ko to yau sai kin gane kuranki."" doguwar bundigar dake hannunsa ya dora mata a wuya a tsawace! yace.""Wuce muje yau kin fad'a komar mu sai kin gane baki da wayo."" Yar Sa'adu kuka ne ya kufce mata jikinta ya shiga kyarma! sai ta shiga d'aga hannunta sama tana basu hakuri Kafin kice"

"kwabo gurin ya cika da jama'a, su kuwa matan da suke tare da ita ganin an shigar da ita mota yasa da"

sauri kowacce ta fece! tsoro da tashin hankali duk ya cika musu zuciya.

****

Watannin Naja'atu biyu da dawowa gida inda ya kama wattanin cikinta shida kenan yanzu cikin nata ya

"fito ana d'an ganinsa amma ba sosai ba kasancewarta doguwa yasa cikin bai bayyana kansa ba sai dai amma ita kadai ta san abinda take ji a jikinta, kusan kullum sai ta 'buya a daki taci kukanta ta koshi haka kawai Bash ya had'ata da wahala ya gudu ya bar mutane da jigilar d'ansa duk sanda ta tuno wannan al'amari takan kwana ta yini cikin kunci da damuwa, mussaman idan taga yanda Abbah Abbas ke hidima da ita da cikin jikinta duk sai hankalinta ya tashi ta shiga nadamar abinda tayi masa a baya, itace ta zama sanadiya gurin lalacewarsa cikinsa gashi ita taje ta dauko ciki ta kawo masa wahala, yanzu saboda ita kullum da safe kafin ya tafi harkokinsa sai yazo ya kofar na'isan sannan bayan ya dawo daga kasuwa ya sake dawowa gabad'aya jama'ar gidan sun fahimci saboda ita yake wannan sintirin dukkaninsu su gane ya damu da yarinyar da cikin jikinta, sai hankalinsu ya kwanta mussaman hajia da Alhaji burinsu kawai yarinyar ta haihu lafiya sai ai maganar kome domin su a ganinsu yanda yake nuna damuwarsa a kan yarinyar suna ganin kamar yana so ya mayar da ita gidansa ne. wanda shi kuma kwata kwata ba haka bane a cikin zuciyarsa haka kawai take bashi tausayi da ita da abinda ke cikinta shiyasa ya mayar da hankalinsa a kanta duk da bashi ne keda alhakin kula da itaba , a yanzu dai cikin zuciyarsa bai dauki"

Naja'atu a matsayin komai ba face 'Yarsa.

Yau asabar yana zuwa da wuri dalili kenan daya sa takasa komawa baccinta na safe ta fito palo ta zauna

"tana jiran zuwan nasa, lokacin daya shigo hajia na sama ita kadai ya samu a zaune tana kallon tashar"

"sunna tv Malam Aminu Daurawa na gabatar da shirin tambaya mabudin ilimi, a nutse ta amsa masa"

sallamarsa ta dan gyara zamanta a hankali tana gaishe shi Ganin yanda take ya mutsa fuska ne yasa ya

"mayar da hankalinsa kanta a nutse yace.""Ina fatan kina lafiya ya jikinki.""?"

"Kamar za tayi kuka tace""Da sauki inasu Mussadiq."" Yace.""Suna gida lafiya lau ina hajia.""? Tana sama."""

"Tafada tana kallon kasan kafafunsa, kai tsaye saman ya nufa sai ta bishi da kallo tana girgiza kanta ita kam a duniya akwai mutumin dake sonta irinsa kuwa? gaskiya babu."

"Ya kai mintina goma sha biyar a saman ya sakko da sauri yana duba agogon hannunsa, dan kallon gefan"

"da take zaune yayi ba tare da yace wani abu ba ya kama hanyar fita. Da kyar ta kira sunanshi, tsayawa"

"yayi yana kallonta. Murya na rawa tace.""Ina so mu gaisa dasu Mmn Sajida matar nan data taimaka"

"min."""

"Jim! yayi kafin yace.""Yanzu dai sauri nakeyi ana jirana idan nazo da yamma sai ayi yanda kikace."""

"tace.""To Abbah Allah ya bada sa'a.""Ya amsa yana kokarin futa daga falon."

Sai bayan futarsa ne ta shiga tunanin yanda za'ayi ma tayi magana dasu Mmn Sajidan tunda lokacin data

"barsu daga ita har Mmn Ladin babu me waya a cikinsu , wannan dalilin ya sanya jikinta yay sanyi taso da hanyar da zata sadata dasu da sun gaisa da juna ta 'kara yi musu godiyar abinda sukayi mata."

To koda ya dawo gidan da Yamma batai masa maganar ba shima al'amuran dake gabansa sun mantar

"dashi, sai kawai ya ajiye mata abubuwan da ya saba siyo mata ako wace rana yay tafiyarsa gurun iyalinsa."

Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan Yana tsaka da shiryawa domin tafiya kasuwa kira ya shigo

"wayarsa, Zainab yasa ta miqa masa wayar ya daga tare da karawa a kunnansa. Mmn Sajida dake"

"d'aya bangaran ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da sauri tace""Sannu ina kwana sunana Mmn Sajida daga jos."" Sai yayi saurin duba number yana so ya tabbatar, ya mayar da wayar kunnansa yace."" Lafiya kalau Mmn Sajida na gane ina fatan kuna lafiya.""? Ta amsa da lafiya lau Alhaji muna fatan kunje gida lafiya."" Yace.""Lafiya lau alhmdullhi."" Tace.""Dama na kira ne idan da dama inaso a bani Naja'atu mu gaisa wallahi har yanzu alhinin rabuwa da ita bai sakemu ba."" Yace.""Ayya! kada ki damu insha Allahu anjima kad'an idan naje Inda take zan bata wayar ku gaisa."" Tace.""To Alhaji mungode sai anjima."" Yace.""To masha Allah."" Kashe wayar yayi ya ajiye kan drowar dake gefansa, Zainab tunda taji ya ambaci"

sunan Naja'atu ta sanja fuska dan har sai da ya fahimci sauyawarta alhalin labari take bashi amma lokaci

guda yaga ta 'bata rai! kwanciya ma tayi ta juya bayanta kishin Naja'atu naso ya dargagaza mata zuciya.

"Sai da ya gama shiryawa tsaf ya juyo yana kallonta a nutse yace.""Zainab lafiya dai ko.? ba tare data jiyo ba tace.""Lafiya lau bacci zanyi shiyasa na kwanta."" Yace.""Okey ni zan fita."" Tace""A dawo lafiya."" ya amsa a nutse ya bude kofar dakin ya fita, mikewa zaune tayi tana jan tsaki! kai gaskiya ta gaji da wasiwahsi gami da takurawa zuciyarta dole yau idan ya dawo ta tambayeshi tsakaninsa da Naja'atun nan da ya"

damu da ita idan mayar da ita zaiyi gwara ya fad'a musu su ya daina wani 'boye-'boye...........

*Littafin na kudi ne. !*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karanta littafin ga yanda abin yake. Vip group

#600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbank. Idan katin waya zaki tura kiyi min

mgn ta WhatsApp da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

69*******Lokacin daya isa gidan Alhajin Naja'atu na daki tana baccinta na qa'ida dama idan tayi sallar

asubahi komawa take ta kwanta tayi ta bacci watarana hajia da kanta take shiga dakin ta tashe ta sannan fa tayi break fast tunda cikinta yayi kwari take wannan bacci mara qa'ida daddare ma tana idar

"da sallar isha'i take kwanciya, hajia da taga abun yayi yawa cewa tayi aje asibiti a dubata, Yaya Ramlatu tace"" Lafiyarta lau kawai yanayin cikin nata ne yazo a haka dama ana samun ciki mai sanya baccin tsiya ta ce ta kwantar da hankalinta bacci lafiya ne. bana cuta ba to wannan maganar da Yaya Ramlatu tayi itace tasa hajian ta kwantar da hankalinta amma dai duk rintsi da daddare bata barinta ta kwanta sai ta"

tabbatar ds taci abinci ta koshi tukkuna.

"Koda ya shigo gidan bai samu kowa ba, wai ashe sun tafi jana'izar 'yar 'kanin Hajia Rabi dake mandawari,"

"da yake mutuwar ta dare ce shiyasa bashi da labari sai daya ya shigo gidan tukkuna maigadi ke fad'a masa. Juyawa yayi da niyyar fita daga gidan sai kuma yayi wani nazari, yana tunanin ko zasuje"

"gidan mutuwar bai zama lallai suje da ita ba shima yasan a daidai lokacin take baccin data saba, dan"

wani lokacin idan yazo baya samun ganinta sai dai kawai ya tambayi hajia lafiyarta.

"Shuru falon lokacin daya shiga, bai jira komai ba ya nufi dakin da take. Kallon sharia yayi mata yayi"

"saurin kauda kansa, yanayin kwanciyar da tayi taso ta saka shi cikin wani yanayi yayi saurin kawar da abun daga cikin ranshi Ya karasa bakin gado tare da tsayawa saitin kafafunta yana kallon fuskarta dake"

"kallon rufin dakin, da yake irin kwanciyar da ba'a masu ciki suyi ita tayi (rigingine) ta tayar da kafafunta sun taka gadon kana ta d'ora dukkanin hannayenta a saman cikin nata. Sunanta ya shiga kira yana"

korar shad'en d'in da yake ra'barshi idan da baiyi wa Mmn Sajida al'kawari ba da yana ganin tafiyarsa

zaiyi dan tsayuwarsa a dakin na nema ta haifar masa da matsala.

Kamar a mafarki taji muryarsa na kiran sunanta! ta bud'e idonta da sauri! shi take gani dishi dishi a

"idonta, shi kuwa yanayin yanda yaga idanunta sun sauya yasa ya dauke kansa yana kallon gefe guda, yace.""Tashi ku gaisa da Uwar dakin ki ta jos dazu ta kira waya tana so ta dubaki."""

Da sauri ta miqe zaune jin cewar Mmn Sajida ta kira waya...Wannan gaggawar miqewar da tayi yasa

"yaron dake cikinta ya kai mata wani irin naushi! yayi fushi! ya samu guri guda ya dunkule mata! Rintse! idonta tayi murya na rawa tace""Wayyo cikina.""! Kafin kice me zufa ta tsatstsafo mata a saman goshi!"

"Rikicewa yayi yay saurin ajiye wayar a kan drowar dake gefan gadon, be san sanda ya zauna kusa da ita"

"ba yana kokarin kamo hannunta. ""Wayyo Allah cikina ya 'kulle a guri d'aya.""Abinda take fad'a kenan"

tana janyo zanin gadon da hannayenta. Kamota yayi yasa a jikinsa yana shafa bayanta a hankali a

"hankali duk ya rasa nutsuwarsa ita kuwa sai kokarin cire jikinta take tana kiran cikinta! Yace.""Me yasa kikayi irin wannan kwanciyar bayan kin san masu ciki ba'aso suyi sannan me yasa kike gaggawa a cikin al'amuranki kin jima a kwance rigingine gashi kin tashi cikin gaggawa dole shima yayi fushi! ya zauna miki"

"a guri guda, sannu ki dinga kula kinji ko."""

"Wannan maganganun yake mata yana dan shafa bayanta a hankali a hankali! Shuru tayi a jikinsa, tana"

jin yanda yaron ke motsi inda ya d'aure yana saki a hankali a hankali cikin nata ya koma daidai ta daina jin ciwo A sanyaye ta cire jikinta a nasa ta sunkuyar da kanta tare da kokarin gyara botiran

"rigarta. Daidaita nutsuwarsa yayi ya dauki wayar daya ajiye yana kallonta yace.""Ina fatan cikin ya daina"

"ciwo."" Kanta ta d'aga tana jin nauyin abinda ya faru Yace.""To sai ki kiyaye gaggawa kuma ki daina irin"

"wannan kwanciyar cikinki yayi kwari yanzu kiyi hakuri kina kwanciyar da yaronki zaiji dadi kema ki inganta lafiyarki."""

"A hankali tace""Wallahi bana sanin sanda nakeyi nafi jin dadin irin kwanciyar."" Dan murmushi yayi"

"yace.""Baki damu da lafiyarki ba shiyasa kike biyewa son zuciyarki kisa a ranki kin daina irin kwanciyar sai kiga kin zauna lafiya."" Tace""To shikkenan insha Allah."""

Dakin ne yayi shuru Abbah na traying din number Mmn Sajida tana fara ringing ta dauka yay saurin

"miqa mata, gani yay ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tana dariyar farin ciki tace.""Mmn Sajida ina kwana ina Mmn Ladi.""? Mmn Sajida cikin da walwala da farin ciki ta amsa da fad'in ""Ga Mmn Ladi a kusa dani muna tare Naja'atu ya kuke je gida? Ya kuma jikinki muna fatan duk komai lafiya."" Tace""Wallahi"

alhmdullhi Mmn Sajida gaskiya naji dadin jin muryarki ina nan ina kewarki ki bani Mmn Ladi mu gaisa

"insha Allahu idan na haihu zanzo nayi muku kwanaki."""

"Mmn Sajida tace.""Muma muna nan duk kewarki ta ishemu dan Walid ma sai da yayi zazzabi Sajida kuwa"

"kullum sai ta kira sunanki tayi kuka."" Najaatu murya na rawa tace""Ayya Allah sarki Walid dan Allah kice ina gaishi da kyau Sajida kuma kice mata idan zanzo zan zo mata da kayan wasa irin wanda take so."

"Mmn Sajida tace""To insha Allah zan fad'a mata ga Mmn Ladi ku gaisa."" Mmn Ladi na washe bakinta ta"

"kar'bi wayar da fad'in ""Naja'atu 'yar albarka mai gyara sinnar ma'aiki ai ni kam babu abinda zance miki daba dan keba da tuni na dade da rabuwa da Saleh wallahi yanzu zaman lafiya muke da juna yanzu ina hakuri da duk abinda ya bani kuma na daina yi masa rashin kunya yanzu Saleh daidai gwargwado yana"

kyautata min muna zaune lafiya da 'ya'yanmu.

"Naja'atu tace"" Amma gaskiya naji dadin wannan labarin naki Mmn Ladi Allah ya qara muku zaman lafiya"

"sannan kuma inaso in tuna miki cewar kada ki manta da al'kawarinmu insha Allah idan nazo garin zan tallafa miki ki fara sana'a kema."""

"Mmn Ladi tace""To nagode kwarai da gaske Naja'atu Allah ya saka da alkairi Allah kuma ya sauke ki"

"lafiya."" Ta amsa da amin tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta."

Abbah na zaune yana kallonta sai dariya take Mmn Sajida ce take bata labarin halin da Dantalle ya shiga

"bayan tafiyarta harda kuka ya dinga yi Naja'atu ta dinga kyalkyala dariya tana fad'in ""Lallai Dantalle to"

"ki bashi hakuri yaje ya rungumi matanshi ya kyautata musu shine abinda ya dace yayi"". Kallon"

"agogon hannunsa yayi yaga lokaci yaja a qallah sun dauki minti ashirin suna wayar gyaran mirya yayi tayi saurin kallonsa, hannunsa ya miqa alamun ta bashi wayar. Da sauri tace"" Mmn Sajida nagode da"

"karamci Abbah zai kar'bi wayarsa insha Allahu idan na haihu lafiya zaku ga nazo muku."" Mmn Sajida"

"tace""To Naja'atu Ubangiji Allah ya raba lafiya sai anjima."" Sallama sukayi cike da farin ciki da kewar juna."

"Tana miqa masa wayar tace""Abbah don Allah kayi serving number ta Mmn Sajida ce."" Wayar yake"

"dubawa a tsanake ba tare da ya dubeta ba yace.""Waye Dantalle.""? Sai tayi saurin kallonsa. Hankalinsa"

"nakan wayar yana kokarin serving din number Ya sake maimaita tambayarsa. A sanyaye tace""Wani"

"mutumi ne a garin tun zuwa na na farko yake naci wai sona yake."""

"Miqewa yayi tare da mai da wayarsa aljihu Yace.""Okey na fahimta to Allah ya tabbatar da alkairi a"

"tsakaninku Wannan number kuma nayi serving insha Allah gobe ko jibi zan kawo miki waya sai ku dinga gaisawa idan kin haihu sai ki fad'a musu dan na fahimci matar tana kaunarki sosai."""

Maganar Allah ya tabbatar musu da alkairi da Dantalle itace duk ta ragargaza mata duk wani farin ciki da

annushuwar da take ciki! sai ta shiga tunani gami da nazarin inda maganar tasa ta dosa! Me yake nufi ne?? Bayansa tabi da kallo har ya fice daga dakin bata samu damar yin wata magaba ba

Jiki a masifar sanyaye ta koma ta kwanta ai sai hawaye suka 'balle mata suka dinga fita tamkar wanda

"aka kwance famfo yanzu idan yace ba zai mayar da ita ba to wa zata aura? waye zai riqe mata d'anta? Waye zai tallafa mata kamar yanda yake mata, gaskiya idan yaqi mayar da ita gidansa ya cuceta dan ta riga ta gama sa rai ganin irin wahalar da yake mata shiyasa ta sakankance da cewar yana jira ne ta haihu"

ya bijiro da maganar da kowa yake tunaninta a kansa

Shi kuwa yana fita motarsa ya shiga

59 / 79