Chapter 22 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 79

63K to 66K   out of 235.1K words

hakan yasa ta sassauta ta nemi guri ta zauna tana haki! ita kuwa Naja'atu mikewa tayi tana kuka ta shige dakinsu Mussadiq Yaya Ramlatu ta bita da kallon banza da fadin ""Aikin banza gayyar tsiya masu raba"

zumun Daga mata hannu yayi yace.''Dan Allah ki daina wannan maganar bata dace ba ni sukayi wa laifi

"ita da Salim din kuma na yafe musu."" Salim baiso ya fadi hakaba yaso ayi ta tak'are a gurun, amma dai duk da haka yaji dadi da yasa masa 'bacin rai a zuciyarsa. Sai ya karyar da kai cikin sassauta mirya"

"yace""Kawu kayi hakuri duk da baka fada min laifina ba amma na dauka ina neman afuwarka kuma insha"

"Allahu ba zan sake ba."""

"Ba tare da ya tanka masa ba ya kama hanyar fita, sai yayi saurin rufa masa baya yana d'agawa"

mahaifiyar tasa hannu.

*Littafin na kudi ne. !*

Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina so ki biya kudin karatu ga yanda abin yake.

VIP Gruop#600

normal gruop#300

Account: 0542382124... Binta Umar gtbank. idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da

wannan numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

Mdd

*27*

Salim da sauri ya 'karaso bakin motar yasa hannu ya bude masa motar hade da matsawa gefe guda yana

"wani sunkuyar da kansa tamkar wani mutumin kirki, Abba Abbas ya shiga motar ya zauna har yanzu fuskarsa a murtuke take, da sauri salim ya rufe motar ya zagaya ya bude mazauninsa ya zauna sannan ya kunna motar suka fita daga gidan Motar shuru tayi kowa na sa'ke-sa'ke a cikin zuciyarsa, Abbah"

"Abbas kamar zai daure maganar azuciyarsa sai ya kasa gyaran murya yayi babu wasa cikin maganarsa yace.""Kai!! wannan hoton da nagani cikin wayar Naja'atu yaushe kukayi dauke shi."" Salim yaji gabansa ya fad'i! cikin dakiya da kokarin kare kansa yace.""Kawu wane hoto ne kake magana akansa."" ? A dan fusace! yace.""Kai bana son rainin hankali malam ya ina tambayarka kana tambayata wato matata kake bibiya ko.""? Salim yace.""Subahanallahi Kawu wannan wace irin magana ce kakeyi ina ni ina matarka Kawu ai wutsiyar ra'kumi tayi nesa da 'kasa ni wallahi yanzu kunyarka ma nake ji idan na tuna wai na ta'ba soyayya da Naja'atu. Abbah ya daga masa hannu da fad'in ""Ba cewa nayi kayi min wasu zancan"

"banza ba ina tambayarka hoton da nagani a cikin wayar matata yaushe kukayi shi.""?"

"Cikin rawan murya Salim yace."" Wallahi Kawu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba kayi min bayani"

yanda zan fahimta saboda nasan ni a yanzu tsakanina da Naja'atu gaisuwar mutunci ce tunda ta zama matarka ai dole na girmamata to kawu ina zan ganta ma ballanta na muyi hoto tare.

"Abbah Abbas yaji zuciyarsa ta danyi sanyi saboda jin maganar da Salim din yayi, Gyara zamansa yayi"

"yace.""Wani banzan hoto nagani kai da ita a cewar ta tun kafin aure ya shiga tsakanina da ita yake kuma saboda shashanci da rashin sanin hakkin aure ta dauki hoton ta dora a fuskar wayarta shiyasa hankalina ya tashi na d'ora zargina gabadaya a kanku kai da ita."""

"Salim ya dinga girgiza kansa cikin sanyin murya yace.""Hakika munyi hotona masu yawa da naja'atu a"

"lokacin da muna soyayya to amma daga lokacin dana tabbatar da cewar tafi karfina sai duk nagoge hotonanta dake cikin wayata Kawu ka yarda dani wallahi bazan ta'ba cutar da kai ba."""

Ajiyar zuciya ya sauke! yanzy yaji sanyi cikin ransa domin kalaman Salim din sunsa ya gazgata maganarsa

kan cewar tsakani da Allah yake zaune dashi kuma a tsakaninsu babu cuta babu cutarwa. Yaya

"Ramlatu kuwa tana ganin maigidan ya fita sai ta mike tabi Naja'atu dakin ta dinga zazzaga mata masifa tana zagin iyayenta da fad'in ""Insha Allahu sai Allah ya tona musu asiri kuma duk asirin da Baba malam"

yakewa zuriarsu da yardar Allah kansu zai koma.

"Naja'atu kasa hakura tayi tace"" Yaya Ramlatu mu bama asiri muna zama da mutum da zuciya daya duk"

"wanda kikaji yana maganar anyi masa asiri to bai yarda da kansa ba Amma ni da iyayena da Allah muka dogara kuma shine zai shige mana gaba. Yaya Ramlatu tace""Eh lallai wuyanki ya isa yanka yarinyar"

nan to dan ubanki Malam Sani!!! Halimatu ma bata iya karawa dani ba ballantana ke karan kad'a miya da har nake magana kina mayar min da martani to ni sai na sabauta miki rayuwa wallahi Tana kuka

"tace""Dan Allah kiyi hakuri na fada miki abinda yake zuciyata ne kuma ni ba rashin kunya nayi miki ba."" Yaya Ramlatu ta gaura mata mari a zafafe tace""Dan uwarki kin tsaya gaba da gaba dani kina fada min"

"maganar da ranki yake so amma kice ba rashin kunya kike min ba to Ubanki kike min kome.""?"

"Halisa ta turo kofar dakin ta shiga tana dan ya mutsa fuska tace""Wai me faruwa ne? tun dazu nake jin"

hayaniya. Yaya Ramlatu ta shiga wassafa mata abinda ya faru.

"Tsaki taja ta kalli Naja'atun tace""Yaya Ramlatu sharrin yarinyar nan yafi kala d'ari komai akace tayi ba"

"zanyi mamaki ba nima nema suke su rabani da 'yata mufida, tunda tazo gidan nan Mufida ta daina zuwa inda nake sai na kwana na yini bansa ta a idona ba tana nane dasu sun lashe mata kurwa."""

"Yaya Ramlatu tace""Ai sai kiyi gaggawar dauke yarinyar ki dan kada su koya mata mugun hali na gado."""

"Naja'atu na tsaye tana jinsu suna ta zaginta iyayenta da kakaninta, sai da suka gaji dan kansu suka fita daga dakin."

Cikin kuka da tashin hankali ta nemi hijabinta tasa ta kama hanya ta fita daga gidan tana kuka kamar

"ranta zai fita. Aunty Maryam taga ta fad'o mata gida tana kuka, a gigice ta mike ta tare ta tana"

"tambayarta abinda ke faruwa, Naja'atu rungumeta tayi tana kuka tace""Aunty Maryam kun kassara min rayuwata kun cutar dani ba zan iya wannan rayuwar ba, gidan Abbah Abbas yafi karfina dan haka wallahi tallahi zan yankewa kaina hukunci da ba zaiyi wa kowa dad'i ba."" Aunty Maryam tace""Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! Naja'atu nutse ki fada min abinda ke faruwa ashe duk kin manta shawarwarin da na baki"

"jiya."""

"Tace""Aunty Maryam wane shawarwari zanyi amfani dasu kullum a gidan a cikin laifi nake Halisa tayi ta yi"

min sharri a gurinsa sai ya dauki maganarta ba zaiyi binkice ba yazo yay tayi min fad'a! Yanzu haka Yaya Ramlatu na gidan kafin na fito ta zage ni ta mare ni yafi sau uku me nayi mata zata dinga dukana nima fa

"ba'ason raina akayi auran nan ba da zasu dinga takurawa rayuwata."""

"Aunty Maryam jikinta yayi sanyi tace""Gaskiya Yaya Ramlatu abunda takeyi bata kyautawa, kawai da"

"girmanta da komai ta dinga zuwa gidan k'aninta tana lalata masa zamantakewar gida, wallahi haka Halimatu tasha wahalarsu, kiyi hakuri ki koma dakinki idan Abba Magaji ya dawo zan fad'a masa abinda"

"ke faruwa gaskiya dole ya samu abokinsa yayi masa magana."""

"Tace""Anty Maryam babu inda zan koma gidan Baba malam ma zan tafi.""? Anty Maryam ta rufe baki cikin"

"tsoro tace""Dan Allah daina wannan maganar kina so ki janyo min fada gurin mijina kenan idan kika tafi gidan baba malam zasu d'ora laifin akaina ki daiyi hakuri insha Allah komai zai daidaita. Naja'atu shuru"

kawai tayi tana sauraran maganar da Anty maryam din keyi har abada bata jin zata iya zaman aure a gidan Abbah Abbas dole ta nemawa kanta mafita dan tana ji tana gani ba zata 'kare rayuwarta cikin

kunci da masifar kishiya ba.

Aunty Maryam ta dinga rarrashinta gami da bata shawarwari masu amfani wanda idan da zata daukesu

"to ba karamin taimakonta zasuyi ba, amma ina! hausawa na cewa wanda yayi nisa baya jin kira dan gabadaya Naja'atu a cikin zuciyarta bata da niyyar zaman aure a gidan Abba Abbas burinta kawai ta samu damar da zata sanya ta kufce daga hannunsa. Sai da tayi sallahar la'asar a gidan Abba Magajin"

"sannan Aunty maryam ta lalla'bata kan ta tafi gida insha Allahu zata sanar da Abba Magaji duk abunda ke faruwa a gidan abokin nasa, Naja'atu kamar gaske tayi mata sallama ta fito daga gidan, kai tsaye sai ta mi'ki titi ta dingi tafiyar 'kafa kofar na'isa ta nufa gidan Baba Malam dan tayi rantsuwar ba zata koma gidan ba, ta riga ta fito kenan Baba malam na zaune kan dadduma a dakalin gidansa ya hangota"

"ta karyo kwanar gidan, idonsa yasa mata yana so ya tantance itace ko ba itace ba, sai da ta kusa zuwa kusa dashi sannan ya gazgata, ganin da yayi mata a firgice yasa hankalinsa ya tashi jikinsa yayi sanyi sosai! ita kuma tana zuwa sai ta zube gabansa ta bude bakinta za tayi magana kuka yaci karfinta, cikin taushin murya yace.""Tashi ki shiga ciki komai yayi tsanani maganinsa Allah."" Ta mike kamar mara lafiya ta nufi cikin gidan Baba Talatu na bakin rariya tana d'auraye kwanuka taji sallamarta da sauri ta juyo tana"

"kallonta tare da amsa sallamar da tayi Itama ganin yanda ta shigo firgai firgai ya tashi hankalinta, sai"

ta mike daga inda take ta karaso kan tabarmar da Naja'atun ke zaune tana tsiyayar da hawaye. Zama

"tayi kusa da ita tare da fadin ""Naja'atu daga ina kike wannan zuwan naki bana alkairi bane.""! Kukanta ne ya sake tsananta ta rike hannun mahaifiyar tata tace"" Baba daga gidan Abbah Abbas nake tunda kuka kaini kuka ajiye ake azabtar dani wahalar yau daban ta gobe daban, Yaya Ramlatu tazo har gidan tayi mun duka ta zageni ta tsine muku ta kira ni mayya babu irin cin mutunci da zagin da ba tayi mun ba, wannan dalilin ya sanya ni bar musu gidan dan bana so na zauna a gidan ta tunzura zuciyata na rama"

zagin iyayena da take ace nayi mata rashin kunya.

"Baba Talatu tace""Haba Naja'atu har yaushe aka kai ki dakin mijin naki da zaki zo da wannan maganar wai"

"shin me yasa ke baki da hakuri ne? shin ba zakiyi koyi da 'yar uwarki ba, Halimatu har ta kwanta dama bata ta'ba zuwa gidan nan ta kawo 'karar mijinta da 'yan uwansa ba tana hakuri cikin ko wane hali kuma tana biyayyar aure amma ke kwana uku kacal kinzo gida shin ko dai kina so ki zubar mana da kima da"

mutunci ne a unguwa.

"Girgiza kanta ta shigayi tace""Baba akwai cutuwa a cikin wannan auran da kuka 'kulla domun kuwa ta"

kowane 'bangare babu sassauci ni ake zalinta kwana uku kacal da nayi a gidan na fuskanci ba gidan zama bane Halisa sai abinda tace akeyi kullum cikin yi min sharri take a gurin Abbah sai yazo yayi tai min fada bani da laifi Baba kuma kin san kowa da halinsa a gaskiya ni ba zauna wani ya dinga zagin iyayena nayi

"shuru ba dan iyaye ba sufi iyaye ba."""

Baba Talatu tayi shuru jikinta duk yayi sanyi da maganganun Naja'atun babu shakka duk d'a nagari ba zai

so a dinga zagin iyayensa a gabansa ba. Baba malam ne ya shigo gidan ya zauna gurin zamansa yana

"kallonsu sunyi jugum! ya kalli Naja'atu da fad'in ""Auta kada kice min yaji kikayi kika zo gida."" Baba Talatu tace""Aikuwa dai abinda tayi kenan Cikin damuwa yace.""To akan me? Ashe ke ba zaki kyautata hakurin"

"da 'yar uwarki tayi a dakin mijinta ba.""! Baba Talatu tace""To abun ne gaskiya da akwai matsala kuma kasan kowa da halinsa ba lallai ne Naja'atu ta kauda kanta daga kan abinda Ramlatu zata zo tayi mata ba, idan baka manta ba kasan haka Halimatu ta sha fama da Ramlatu wallahi ni na rasa wace irin macace"

"wacce kullum girma take amma tana sake lalacewa da rashin hankali."""

"Baba Malam yace.""Duk wani abu da Ramlatu zata zo tayi miki a gidan mijinki idan bada mijinki kuka"

"samu sa'bani ba to komai mai sauki ne! ban lamunce ki dinga dauko kafarki kina zuwa gida akan abinda bai kai ya kawo ba, shin dan Ramlatu ta zage ni ko ta zagi mahaifiyarki sai me? mutukar baki bude baki kin rama ba to kanta take zagi! dan haka daga yau sai yau kada Ramlatu ta sake zuwa gidan mijinki wani sa'bani ya shiga tsakaninki da ita ki d'auko 'kafa ki zo gida, yin hakan zai janyo miki 'bacin raina.'''!! Tayi shuru hawaye nata zirara a fuskarta dama tasan da wuya baba malam ya kyaleta ta zauna masa a gida gashi 'kiri-'kiri yana nema ma ya d'ora laifin a kanta. Yace.""Tun kafin gari yayi duhu ki tashi ki koma"

dakin 'ki farin cikina a duniya shine inga kin zauna lafiya tare da mijinki saboda haka kije ki cigaba da

hakuri insha Allahu zaki ci riba anan gaba.

Mi'kewa tayi tana 'kokarin zura takalminta takaicin duniya ya isheta wai iyayenta da suka haifeta sun

kasa gane abinda take ji a cikin zuciyarta da anyi magana sai suce tayi hakuri idan hakuri na kisa a ganinta to da tuni ya kasheta. Koda ta fita daga gidan kai tsaye gidan Alhaji ta nufa dan yanda Yaya

Ramlatu ta kuntata mata to itama sai ta janyo mata fad'an iyayenta. Hajiya na zaune a palo tana jan

carbi Naja'atun ta shiga da sallama kasa kasa a bakinta

"Kallo guda Hajiya tayi mata ta fahimci akwai damuwa, Naja'atu zama tayi kujerar da take kallon hajiyan"

"tana share hawaye...Hajiya ta ajiye carbin hannunta a nutse ta kalleta tace""Naja'atu tunda na ganki a furgice nasan babu lafiya ki fad'a min abinda ke faruwa.""? wasu sababbin hawaye ne suka zubo mata, murya na rawa ta shiga fad'a mata abinda ke faruwa da irin sharrin da halisan ke mata da kuma yanda Abbah Abbas din ke dauka yazo yayi mata fada ba tare da yabi ba'asi ba, sannan ta fada mata zagi da"

dukan da Ramlatu tazo har gida tayi mata.

"Hajiya shuru tayi takaici kamar ya fasa mata zuciyarta, ita kam ta rasa yaushe Ramlatu za tayi hankali"

"wallahi da girmanta da komai ta dinga daukar kafa tana zuwa gidan yara tana shashanci to babu shakka wannan karon zata fuskanci bacin rai daga gareta. Tace""Kiyi hakuri kinji ko Naja'atu hakika nasan anyi"

"miki ba dai-dai ba amma na roke ki kiyi hakuri ki kwantar kuma da hankalin ki tunda dai kin kawo min 'karar Ramlatu da Abbas to ni kuma zan hukunta miki su saboda haka yanzu ma ba zaki koma gidan ba, har sai shi Abbas din yazo a gabanki zanyi masa fadan kan abinda yake yi ba dai-dai bane."" Naja'atu taji dadi sosai da yanda Hajiya ta goya mata baya sai kawai ta gyara zamanta a palon ta zauna suna dan ta'ba hira da hajiyar..........Abbah Abbas kullum suka taso daga kasuwa kafin su nufi gidajensu shi da Abokinsa Abba Magaji sai sun shiga kofar na'isan sun gaisa da iyayensu wataran ma a can suke sallahr magariba kafin su tafi gida, to yau ma kai tsaye da suka taso daga kasuwar kai tsaye can suka nufa. Ganinta"

a zaune a kusa da hajiya ya bashi mamaki sosai! ita kuma sauri tayi ta dauke kanta tana zum'bura bakinta. Hajiya ta amsa sallamarsa ya shiga palon a nutse ya zaune kan kujerar dake fuskantar hajiyar

"yana gaisheta, Hajiya ta amsa kadar kadahan! tunda yaga haka sai yasha jinin jikinsa. Ya kalli Naja'atu"

"yana tsuke fuska yace.""Ke! wa kika tambaya kan cewar zaki zo nan.""?"

"Hajiya tace""Ai zamanta a gidan baida amfani tunda ka kasa ri'ke amanarta, sannan ka bawa matarka da"

"'yar uwarka lasisin dukanta da zaginta gami da hanata sakat! a cikin gidan."""

"Sai ya kasa gane inda maganar mahaifiyar tasa ta dosa."" Yace.""Hajiya bangane ina maganarki ta dosa"

"ba."" Tace""Ai dama ba zaka gane ba sai na ganar da kai, to wannan yarinyar dai 'karar ka ta kawo min kancewar kuna azabtar da ita kai da matarka sannan kuma yau Ramlatu taje har gidan ta doketa."""

"Maganar ta bashi mugun mamaki! kamar shi da girmansa da shekarunsa a kawo shi 'kara gaban iyayensa,"

"Ya dago kansa yana kallonta sai yaga kanta na kallon wani guri sai faman zum'bura bakinta take, tunda yake da Halimatu da Halisa tsayin shekarun da sukayi a tare babu wacce ta ta'ba kawo 'kararsa gaban iyayensa sai wannan yarinyar gaskiya ya jinjina al'amarin sosai! amma babu komai idan ma raini ne ya"

soma shiga tsakaninsu to dama ya dauki alkawarin yau yake so ya fitar da raini a tsakaninsa da ita.

"......Hajiya ta cigaba da cewa""Wannan dalilin ne yasa nace ba zata koma gidan ba sai kazo naji ta bakin ki,"

"shin me yasa a duk sanda Halisa zata kawo magana baka tsayawa kayi bunkice zaka hau kai ka zauna kazo kana yin abinda ya dace."""

"Rashin abinda zaice ne yasa yace.""Ayi hakuri Hajiya."""

"Tace""To Dan Allah daga yau ka zama mai adalci a tsakanin matanka idan wani abu ya faru a tsakaninsu"

"ka daina dora laifi a kan mutum daya ka dinga yin binkice tukkuna."""

"Tace.""Insha Allah Hajiya to amma ni abinda ke bani mamaki anan shine har yaushe akayi auran da har"

"za'a fara kawo 'kara duka fa yau kwananta hud'u a gidan kuma iya bakin kokari inayi a tsakaninsu.'' Hajiya tace"" To nidai ga abinda tazo ta fada min kuma nasan wannan matar taka babu abinda ba zata aikata ba dan haka kaja mata kunne ita in banda abinta ai kamata yayi ta dauki naja'atu a matsayin kanwarta ba kishiyarta ba kuma itama Ramlatu zata zo ta sameni har gida, idan ta dinga zuwa gidanka tana lalata maka zamantakewar matanka to tun wuri ka taka mata burki tunda har yanzu taki tayi hankali."" Yace.""Ba zan hanata zuwa gidana ba domin suna zumunci da Halisa amma zanyi bunkice sosai kan maganar da ita Naja'atun tazo ta fad'a miki idan na tabbatar da gaske ta doke ta to ni kuma zan"

"nuna mata rashin jin dadi na."""

"Hajiya tace""To Allah ya sa'ba halaye dama nace idan tayi sallah

22 / 79