Chapter 77 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   77 / 79

228K to 231K   out of 235.1K words

wayarsa yayi ya ajiye"

"gefe ya cigaba da girgiza kafafunsa, Zainab duk wasu matakan kare kanta ta tanade su tana jiran suzo ayi wacce za'ayi."

"Halisa Najaatu taja gefe ta fad'a mata abinda ke faruwa, dukkaninsu jikinsu yayi sanyi da kiran gaggawar"

"da mijin nasu yake musu. Halisa na draving tace""Najaatu anya ba Zainab ce taje masa da wani sharrin"

"ba."" ? Cikin rashin damuwa tace""Idan taje masa da sharri kanta zai koma insha Allahu mu dai babu abinda mukayi mata."""

"Halisa ta shiga girgiza kanta tare da fad'in ""Al'amarin Zainab sai gyaran Allah ni tun zamanta a gurin na"

"fuskancin sanjawarta tunda lafiya lau muka zo to amma ganin gold din dake wuyanki da wuyana yasa ta sanja fuska nasan abinda ya tayar mata da hankali kenan.""Murmushi Najaatu tayi tace"" To ai sai taje tayi ta damuwa ita ciwo zai kama ba wani ba gold kuwa ni dake nake so muyi anko ita tayi nata ita kadai tunda bata da mutunci da kawaici wallahi ba kiji yanda raina ya 'baci ba data fito fili ta nuna ba zata bani"

'yarta ba.''

"Halisa tace""Ai sai kiyi hakuri ki kyale mata 'yarta kema Allah zai baki."

"A harabar gidan suka sameshi zaune akan wata farar kujera, Halisa ta gyara parking Najaatu ta bude"

mata kofar motar ta fito tana yatsine fuskarta dan zaman draving din nan da tayi ya janyo mata ciwon mara dama dai tanayi sama sama tun a gidan bikin daurewa kawai take mikewa yay ya nufi gurun

"Zainab duk suka rufa masa baya,zama yay kan kujera Zainab tayi wanka ta sanja kwalliya ta zauna kusa dashi tare da d'ora kafa d'aya kan daya a haka suka shiga suka same su. dukkaninsu sai da wani abu ya"

"ta'ba zuciyarsu amma suka dake suka zazzauna, falon ne ya dauki shuru na minti biyu kafin yayi gyaran mirya ya kallesu d'aya bayan d'aya yace""Halisa kece babba a cikinku inaso ki fad'a min abunda ya faru a gidan bikin Salim."" Halisa tace""Bangane na fada maka abinda ya faru ba okey tazo ta fad'a maka wata magana ne.""? Tsawa ya buga mata yace.""Kada ki mayar dani sakarai mana kin san komai kina nuna baki sani ba kome akayiwa Zainab ai kune kuka bada goyon baya saboda kunga kuna da fada a gidan jamaa sunfi sanin ku shine zaku ware ta ku had'u kuci mutuncinta akan wane dalili.""? Yakare maganar cikin"

tsawa.

"Najaatu a dake! tace""Wallahi Zainab kiji tsoron Allah yanzu me akayi miki da har zaki zo ki fad'a masa"

"duk dan ki had'ashi da 'yar uwarsa.""! A fusace! Tace""Ke dallah malama kiyi mana shuru duk bake ce kika janyo komai ba da har zakice naji tsoron Allah kune dai zakuji tsoron Allah bani ba."" Halisa tace""Kawai"

"saboda ta nuna kaunarta akan 'yarki sai ki mayar da abin sharri a gaskiya Zainab ki sanja hali wallahi."""

"""Ba zan canza Hali ba sai dai ku su sanja hali ni ba munafuka bace shiyasa ai kuka ware ni saboda ban iya"

"gulma da munafurci ba yanzu meye na ware ni kuka saka gold irin d'aya bayan ni kunsan bani dashi Ai wallahi Najaatu kece babbar munufaka."" Najaatu ta bud'e baki tana kallonta cike da mamaki tace""Ni kike"

"kira munafuka."""

"""To idan ba munafuka ba mecece da har zaki siyo muku gold iri daya banda ni."""

"Dariya tayi tace""Okey sai yanzu na gane abinda ke damunki ba'kin ciki da hassada kikeyi mana gold kuma"

na siyo bakya cikin tsarina shiyasa bana so nayi irin d'aya dake banza mara hankali kaw. kafin ta karasa

ya buga mata tsawa wai tayi shuru! Ta kalleshi cike da mamaki me yasa lokacin da zainab take magana

"bece komai sai ita zai katsewa hanzari aikuwa sai ta fusata! ta cigaba da watsawa Zainab ba'ka'ken maganganu wanda yasa itama ta fusata! ta miqe tsaye ta fara mayar da martani! kafin kice kwabo gurin ya hargitse Najaatu da Zainab sai hayaniya suke Halisa dashi uban gayyar na hanasu amma kamar sake tunzura su suke....Halisa ta kalleshi rai a b'ace tace""Yanzu meye amfanin abunda kayi ashe dama taramu kayi domin muyi hayaniya kawai saboda Zainab tazo ta fad'a maka magana sai ka hau kai ka zauna babu binkice wallahi ka gyara zamantak. Katseta yayi cikin d'aukar chaji yace.""Fita ki bani guri ki koma"

"gurin ki."" Halisa tsaki taja ta dauki jakarta tinkis tinkis ta kama hanyar fita ba zata iya da jarabar nan ba......Shi kuwa tsakaninsu ya shiga yana musu magana su bari dan gabadaya hankalinsa ya tashi da"

yasan hayaniya zasuyi da bai tarasu a guri d'aya ba.

Najaatu jakarta ta dauko ido jawur ta kama hanyar fita sai dai kafin ta karasa bakin kofar ta yanke jiki ta

"fad'i! A take ta shiga yin wani irin hakki! tana rike kirjinta, bashi kadai ba har Zainab din sai da hankalinta ya tashi, a gigice ya rirriketa yana kokarin mikar da ita tsaye tana kokarin kwanciya, Zainab tazo ta tsaya gabanta na faduwa! Abbah fita yay da sauri ya fito da mota ya umarci maigadi ya bude gate, Najaatun ya hango ta fito daga gurin Zainab tana kokarin fita. Bayanta yabi da sauri yana kiran sunanta ta bude"

"karamar kofa da sauri ta fita daga gidan, hanya ta fara bi hawaye na zubo mata wannan masifa ina zata iya da ita ace mutum ya kasa fin karfin gidansa. Halisa ce ta fito daga gurinta tana kiransa, ya"

"tsaya yana kallonta dik ya zama kamar zautacce mata suna so su haukatar dashi, tana cizar lips dinta tace""Haihuwa zanyi fa ka fito da mota muje asibiti."" Sai ya rasa ina zai nufa gurin Najaatu ko gurin Halisa (Allah sarki ya bani tausayi ) Gurin Halisan ya nufa ya taimaka mata suka fito tare mota ya sata ya kira"

Zainab a gurguje ta fito ta shiga motar suka nufi asibiti.

Najaatu kuwa na fita ta samu adaidaita sahu gidan Alhaji ta nufa ranta a mutukar 'bace! amma koda taje

bata shedawa kowa abinda ya faru ba kawai ta bar abun a cikin ranta.

Karfe tara da rabi na dare Halisa ta haihu an samu 'ya mace katuwa tubarkallah babyn na kama da

babanta sosai dama duk yawanci 'ya'yansa kama suke dashI Ummi ce kawai ke kama da mamanta. Dr

"Sa'adatu itace ta tsaya tsai a kan Halisa har sai da tabbatar komai yay daidai tukkuna hankalinta ya kwanta baby da mamanta sunyi tsaf gwanin sha'awa, karamcin Dr Sa'adatu ya tsaya masa a rai matar na mutukar kaunarsa da iyalinsa yasan duk abinda takeyi yafi karfin irin kudin da yake bata, lokacin guda yaji yana tausayinta a cikin ransa yana son mace mai hankali wacce tasan abinda take tabbas Dr Sa'adatu"

ta cancanta a sota.

"Sha d'aya shaura na dare ya shiga gidan Alhaji shuru gidan lokacin duk sun kwanta, gurin hajia Rabi ya"

"shiga Allah yasa ba tayi bacci ba jin sallama yasa ta fito da sauri, ganinsa a tsaye yasa gabanta ya fad'i Tace.""Allah yasa dai lafiya."" Yace.""Lafiya lau Halisa ce ta sauka ta hafi 'ya mace yanzu haka tana gida"

lafiya lau ita da yarinyar.

"Hajia Rabi ta fad'ad'a fuskarta da faraa tace""Ikon Allah d'azu fa muna tare da ita babu wata alamar"

"haihuwa a tare da ita koda yake ai ikon Allah ya wuce wasa.' Yace.""Wallahi kuwa Allah ya kawo mata da sauki."" Tace""Haka ake so ai Allah ya raya."" Ameen ya Allah bari na shiga gurin hajia."" bayansa tabi tana fad'in ""Allah yasa ba tayi bacci ba dan tun dazu naji tana kukan kafafunta na ciwo. jin muryoyinsu"

"yasa Yaya Ramlatu da Najaatu suka fito daga daki da sauri, Hajia Rabi ta kalli Ramlatu da fad'in "" Kunji halisa ta haihu yanzu yanzu an samu 'ya mace."" Dukkaninsu farin ciki ya nuna a fuskarsu Yaya Ramlatu ta kalli Dan uwan nata cike da farin ciki tace""Yanzu tana asibiti ko tana gida.""? Hankalinsa nakan Najaatu yace tana gida yanzu haka."" Ramlatu tace""To ai sai mu tafi tare da kai na zauna a gurinta."" Tausayi ta bashi jin abinda tace Ramlatu na tsaye a kansa da iyalinsa mussaman Najaatu da Halisa amma ya rasa me yasa take nuna kiyayyarta akan Zainab, Hajia Rabi na kokarin fita tace""Hajia dai yanzu tayi bacci kada a tasheta da safe sai na sanar dasu haihuwar ita da Alhaji."" Yace.""To Allah ya kaimu."" Najaatu bayan Yaya Ramlatu tabi ba tare data kulashi ba, dan har yanzu haushinsa takeji Yaya Ramlatu tace""Kema ai sai"

kizo mu tafi tare ko.''

Shuru tayi tana nazari! da tayi rantsuwar ba zata 'kara shiga gidan ba saboda abunda ya faru amma dole

ta karya rantsuwarta Halisa ta wuce komai a gurinta.......Mayafi ta yafa suka fito tare. Abbah ganinta

"tare da Yaya Ramlatun yasa shi sauke ajiyar zuciya, ya kama hanyar fita suka bi bayansa."

Sai bayan sun hau titi ya kalleta tana zaune kusa dashi fuskarta babu yabo babu fallasa dan farin cikin

"haihuwar Halisa yasa ta danji sasaauci a cikin zuciyarta. Sassauta murya yay yace.""Yaran sunyi bacci"

"ko.""? Umm sunyi bacci sai dai da safe Dan Azimi ya kawo su."" Yace.""To shikkenan."" babu wanda ya sake magana a cikinsu har suka isa gidan."

"Yaya Ramlatu da Najaatu kai tsaye gurin Halisa suka nufa, ikon Allah suna shiga dakin suka tarar da"

"Zainab zaune a gefan gado da baby a hannunta ita kuma Halisa lokacin tana toilet Zainab saurin sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar had'a ido da Ramlatu addua take Allah yasa Najaatu bata fad'a mata abinda ya faru ba. Ya Ramlatu zama tayi kan sofa tare da cewa bani 'yar."" Zainab da sauri ta"

"miqa mata babyn tana gaisheta. amsawa tayi hankalinta nakan babyn tana murmushi! Zainab simi simi ta kama hanyar fita! Najaatu ta bita da kallo cike da takaici Karo suka ci dashi yazo zai shigo yace."""

"Kina ciki dama."" Tace""Eh Aunty Halisan ta shiga toilet. "" Nazarinta yay na minti biyu kafin yace.""okey kije"

"gurinki ganin nan zuwa."" Zainab ta wuce shi shi kuma ya shiga dakin Halisan.........."

*MADADI!*

*91*******Najaatu kasa tayi da kanta lokacin daya shigo d'akin kallon fuskarsa bata kaunar tayi saboda

"abinda yayi musu dazu ita da Halisa a ganinta duk wani rashin son zaman lafiya daga gurin Zainab yake fitowa kuma yasan gaskiya amma yake takewa yake goyan bayan Zainab din a duk lokacin da zata kawo masa magana baya tsayawa yayi binkice a kai zai hau ya zauna ya yanke hukuncin da bai dace ba, tabbas Zainab zata iya raba zumuncin dake tsakaninsa da 'yar uwarsa tunda bata da hakuri! ta tabbata"

Yaya Ramlatu ba itace bata kauna ba halinta ne bata so yanzu ina laifin wanda ya nuna yana kaunar

d'anka a gaban mutane ta kunyata ta nuna ba zata bata 'yarta ba a gaskiya al'amarin yayi mata ciwo

sosai tana rokon Allah ya bata nata itama.

"Muryar Ramlatu taji tana fad'in ""Au! ashe wuta tazo ta kunna maka a gida anya kuwa Abbas wannan"

"yarinyar baso take ta had'aka da kowa ba, ina tunanin ma zumuncin dake tsakanina da kai zata raba tunda har ta iya zuwa ta kawo maka 'karata kai kuma kazo ka tsaya a kaina kana tuhumata."""

"Sassauta murya yay yace.""Nifa ba hayaniya nace kiyi ba magana muke ta fahimtar juna Zainab tazo tana"

"kuka tana fad'in ""Kin tara jamaa kun taru kun ci mutuncinta shine nake so naji dalili amma ni Zainab bata isa ta had'ani da kowa ba."""

"Yaya Ramlatu za tayi magana Najaatu ta katseta da fad'in ""Yaya kiyi shuru dan Allah ba girmanki bane"

tunda ita ta raina ki bata ganin kimarki mu muna gani bana so kina sa kanki a cikin sabgar da zata sa girmanki ya zube.

"Ramlatu tace""A'a Najaatu ba zanyi shuru ba tilas nayi masa bayani dan saboda ya daina ganin kamar"

takurawa matarsa akayi ni da ita daku duk d'aya kuke a gurina abinda yasa na tsaneta mugun halinta kuma har yanzu idan na kalleta sai raina ya baci idan na tuna da marin da tayi min bayan haka tasa dan

"uwana ya dauko min 'yan sanda."" Fashewa tayi da kuka tana fyatar majina!"

Hankalinsa ne ya tashi shifa baya tayar da maganar bane dan rai ya 'baci yana so su fahimci juna da 'yar

"uwarsa dan baya son irin bambamcin da take nunawa a tsakanin matansa amma ba dan ya 'bata mata rai ya tayar da maganar ba, Najaatu ganin Yaya Ramlatu na kuka sai itama ta fara, Halisa ta fito daga toilet ta tarar dasu suna kuka shi kuma sai magana yake musu. Tace""Yanzu ashe Abbah Mufida"

"maganar nan bata mutu ba nifa tashin hankalin nan ya tayar min da nakuda wallahi."" Yace.""Halisa"

"magana ta mutu tuntuni tambayarta nake akan abinda ya faru shine take kuka sabida rashin fahinta."""

"Halisa ta samu guri ta zauna tare da fad'in ""Yaya dan Allah ki daina kuka Zainab fa karya take ta shiga"

"tsakaninki da Dan uwanki kome za tayi kuwa ki daina damuwa."""

"Yaya Ramlatu ta goge hawaye tare da kallonsa tace""Kace kana so kaji abinda yasa matarka kasa zama a"

"gidan biki ta dawo gida ko."" Yace.""Eh."" Tace""To Najaatu tayi sha'awar 'yarta sai ta nuna ta bata aro tayi mata kwana biyu kai tsaye tace ba zata bayar ba, haushin haka yasa nayi mata fad'a saboda raina ya 'baci sosai da yanda ta nuna rashin kwaicinta a kan 'yar uwarta amma babu wanda ya zage ta ko yaci"

"mutuncin iyayenta duk wata magana da tazo ta fad'a maka karya take."""

Shuru yay yana nazarin maganar. Abinda yasa yay saurin yarda da maganar Zainab din sabida yasan

"akwai rashin jituwa a tsakaninsu sannan Halisa da Najaatu sun nuna masa kansu a had'e yake ma'ana sun cire Zainab daga cikin su shiyasa ya yarda da cewar za'a iya had'a baki dasu aci mutuncinta tunda kishiyarsu, sai kuma yanzu da yaji farkon al'amarin ya fahimci furucin Zainab din ya janyo duk hatsaniyar shima yaji rashin dad'in abinda tayi ina laifin wanda ya nuna yana son naka, a zamansa da Zainab ya fahimci halinta na rashin iya magana da rashin kawaici da hakuri mutukar akan hakkinta ne bata iya yin shuru shiyasa yake tsoron wani abu na sa'bani ya shiga tsakaninsa da ita sabida hanashi bacci take da daddare, ya lura su kuma su Halisan suna ganin kamar tsoro ne yasa yake biyewa Zainab din da duk abinda tazo masa dashi wanda kwata kwata ba haka bane a gurinsa kawai yana jin tsoron rashin hakurin ta da mitar ta dan kwata kwata abu naya wucewa a gurinta ta dinga nanata magana kenan Ya jima a tsaye a dakin yana nazarin al'amarin kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Halisa"

"dake kokarin sawa babynta nono yace.""Ina fata babu wata matsala ko.""? Tace""Babu matsala."" Yace.""To sai kiyi kokari kici abinci kamar yanda Dr Saadatu ta fad'a miki kisha magani kafin ki kwanta."" Tace.""Insha Allahu."" Sallama yayi musu ya juya da niyyar fita daga dakin 'Yar uwarsa ce kawai tayi masa magana"

Halisa da Najaatu shuru sukayi suka bishi da kallo har ya fice daga dakin.

Bayan ya dawo daga sallar asubahi ya sameta ta idar da sallah zama yay gefan gado had'e da kiran

"sunanta"" Zainab'' amsawa tayi tare da juyowa tana kallonsa, yace."" zo nan."" Jiki a sanyaye ta miqe taje ta zauna kusa dashi."" kallonta yayi a nutse yace.""Jiya Yaya Ramlatu dik ta sheda min abinda ya faru a tsakaninku wanda har yanjo ta kasa hakuri tayi miki fad'a kan abinda kikayi wanda ke kika daukeshi da wata manufa, banji dadin abinda kikayiwa Najaatu ba ina laifin wanda ya nuna yana son naka."" Shuru"

"tayi tana zumbura bakinta ita yama za'ayi ta dauki 'yarta ta bawa ma'kiyarta ai ba zai yiwu ba."""

"Yace.""Koda ba zaki bata ba ai bai kamata ki fito ki fad'a mata gaban jamaa ba kin nuna mata iyakarta"

akan abinda take da iko dashi koda bana auranta zan iya bata d'ana ta ri'ke sabida cancantarta to ballanata a matsayin uwa take a gurin Ummi tabbas nasan kamar yanda zata kula da d'an cikinta haka

"zata kula da Ummi amma meye na nuna mata iyakarta."""

"""Abbah Mufida nifa koda ba ita taba ba zan iya bada d'ana yaje wani guri ya kwana bs kuma ni ban fad'i"

"maganar da wata manufa ba dan da nasan zasu dauki zafi to da nayi shuru da bakina yarinya dai 'yata ce sai nayi niyya zan bayar."""

"Cikin 'bacin rai yace.""Kiyi min shuru nace! wato har wani fuffuka kike kina maganar yarinya yarki ce"

"bayan kin gama azabtar da ita ashe akwai ranar da zata zo kiyi wannan maganar to ki daina cika baki idan nayi niyya wallahi zan dauke yarinyar daga hannuki na kaita duk inda raina yake so sai naga k'aryar so."" Shuru tayi gabanta na bugawa jin abinda yake fada."

"Yace""Anjima ki shiga gurin Halisa Yaya Ramlatun nan ki bata hakuri kan abinda ya faru kinji ko."" Murya"

"na rawa tace ""To."""

"Kwanciya yay kan bed din tare da tsirawa rufin dakin ido, Zainab hijabin jikinta ta cire taje ta kwanta"

"kusa dashi, itafa tunda taga Najaatu da ciki to itama sai ta samu hankalinta zai kwanta, jikinsa ta shiga tana shashshafa kirjinsa tare da sumbatar fuskarsa, duk da yasan wuya zata bashi hakan be hanashi kar'bar tayin ta ba rungumeta yay a jikinsa yana mayar mata da martanin abinda take masa."

"Najaatu da Yaya Ramlatu na zaune suna karyawa suka shigo tare, Tinda tayi musu kallo daya ta dauke"

"kanta, Zainab ta nemi guri ta zauna shi kuma ya tsaya suna gaisawa da 'yar uwarsa, Najaatu ba tare ta kallesa ba ta gaisheshi cikin kulawa ya amsa yana tambayarta Halisa tace""Tana bandaki Bakin bed din"

"ya zauna yace ""Bani yarinyar."" Babyn dake hannuta ta bashi kamar yanda ya bukata ta juya ta cigaba"

dayin break dinta.

"Zainab a sanyaye tace""Yaya Ramlatu dan Allah kiyi

77 / 79