Chapter 63 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   63 / 79

186K to 189K   out of 235.1K words

sai dai ta daure"

"tace""Dan Allah ki bawa Abbah wayar zanyi magana dashi."

"Zainab tace""Kada ki damu shine yace na dauka ina sauraranki."" Najaatu taji kanta ya sara! da kyar"

"tace""Aa ki dai bashi wayar."" Zainab murmushi tayi cikin sigar kuntatawa tace""Wallahi da gaske nake miki gashi ma yana kimtsawa zai fita kuma da umarninsa nake magana dake ki fad'i maganarki dani dashi duk daya ne."" Najaatu ta dinga jin kamar ba'a guri guda take ba dan wani irin jiri ne ya shiga d'ibanta, sai kawai ta kashe wayar ta jefar da ita lafiyayyun hawaye suka shiga zobowa a kumatunta, wannan wulakanci dame yay kama? Lallai Abbah Na shirin ya dasa mata ciwo a cikin zuciyarta, ashe bai san yanda take bala'in jin kishin matarsa ba zai ce ta daga mata waya aikuwa ba zata qara kiransa ba, kuma"

tafiyarta zatayi tunda dama ba zamansa take ba

Sai da taci kunanta ta qoshi tukkuna taje ta sanar da hajia maganar zuwa jos din Hajia tace'' Hakan yana

da kyau sai ta fara shiri.

Bangaransa kuwa koda ya gama shirinsa bai tambayi zainab komai ba tunda hands free wayar take duk

"yaji komai ya kar'bi wayarsa yayi tafiyarsa harkokinsa, ita kuwa Zainab a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa dan duk ciwo ciwon da take ji a jikinta daina ji tayi sabida abunda tayiwa Najaatu na"

quntatawa kuma taji dadin yanda ya bata goyon baya d'ari bisa d'ari.

"Bayan kwana uku Naja'atu ta shirya kayanta tsaf hajia ta shirya mata tsaraba mai yawa, tace ta kai musu"

"domin sun cancanci abinda yafi haka, a ranar da zata tafi ta shiga gidan Baba Malam da wurwuri tayi musu sallama itama Baba Talatu ta bata abubuwan tsaraba tace ta kai musu, sannan tayi mata fatan"

dawowa lafiya.

"Sai da zata tafi hajia tace""Kinga ikon Allah ko na sha'afa wallahi duk zuwan da Abbansu Saddiqa keyi ban"

"fada masa ba ko kin kirashi a waya ne.""? Da sauri tace""Eh shekaran jiya na fada masa."" Hajia tace""To"

shikkenan dama dan dai kada ya samu labarin tafiyar daga baya ne yasa nayi maganar to Allah ya saukeku lafiya a gaishe mana dasu da kyau.

Naja'atu tace zasuji insha Allahu Hajia. Tare suka fito harabar gidan suna tsaye suna kallonta ta shiga

mota direba yaja suka fita daga gidan Abbah Abbas lokacin daya samu labarin tafiyar ranshi yayi

"masifar 'baci! ya za'ayi saboda rashin hankali ta dauki yaro karami a lokacin sanyi tayi tafiya mai tsayi dashi, shifa gabad'aya garin jos bai masa ba shiyasa bai ta'ba yi mata zancan zuwa ba, ashe jira take ta haihu ta dauki kafa ta tafi ba tare da ta sanar masa ba(Matarka ce ita da zata tsaya fad'a maka ) Hajia ta dinga tausarsa da fadin ita bata san bai sani ba wallahi amma ai ba wani abu bane dan taje ta nunawa mutanan abunda ta haifa saboda sun cancanci hakan Yace.""Hajia ba hana zuwa anyi ba a qalla dai ta"

"bari yaron bayanta yayi kwari ki duba kiga yanda ake busa iska a gari tana iya zuwa da yaron ya samu wata matsalar yanayin gidan da zataje bashi da kyau da tsayin katanga akwai matsala sosai."" Hajia ta dinga mamakin maganarsa tace""To ai lalura a ko'ina ma daukarta akeyi kuma ta tafi da kayan sanyi"

nasan zata kula dashi.

"Shuru kawai yay ya miqe tare da fadin shi zai tafi.Hajia tace to a sauka lafiya, hanyar futa ya kama ta"

bishi da kallo tana mamakin son 'ya'yansa.

"Kasa hakuri yay yana driving ya shiga kiran wayarta, lokacin har ta sauka tana tare dasu Mmn Sajida sai"

"gaishe da juna sukeyi, su Walid da 'Ya'yan Mmn Ladi sun kewayeta tana ta basu tsarabar da taje musu da ita."

"Koda ta duba wayar taga number sa ce sai ta cigaba da abunda takeyi, taki dauka sai da ya kira sau uku"

"tukkuna ta daga, tana kokarin gaisheshi ya dakatar da ita. ""Ashe baki da hankali Najaatu wa kika"

"tambaya wanda ya baki izinin tafiya wani gari? ashe kina nan da halinki na taurin kai ko."""

"Kai tsaye tace""Abbah yi hakuri dan Allah kwana hudu da suka wuce na kira wayarka na tambayaka sai"

"dai idan mantawa kayi."""

"Yace.""Ke bana son karya yaushe kika kira ni kika tambaye ni ai saboda kin san bazan bari ba shiyasa kika"

"'ki sanar dani."" (Takwara zo kiga karfin hali Tace""Wallahi na kira wayarka Zainab ta dauka kuma na fad'a mata maganar sai dai idan itace bata fad'a maka ba."""

"Shuru yay yana tunanin maganar. "" To Gobe Dan Azimi zai zo ya dauke ki dan haka duk wanda kika"

"san zaki gaisa dashi a garin kiyi kokarin gaisawa dashi kafin gobe."" Yana gama maganarsa ya kashe wayarsa.........."

*Littafin na kudi ne...!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip

group #600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank...idan katim waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

_Abbah Abbas ka janyo 'yan group yau na caccakar ka Mum Basma tace idan ka tsaya kallon ruwa

"kwado zaiyi maka kafa, ita kuma Sakina tace"" Kana ruwa sistar Habiba tace Dantalle ya shigo kawai"

ayi dashi tunda kai ka tsaya wasa! To nima dai nace ka ajiye makaman ka dan idan ka tsaya jan aji za'ayi maka shigar sauri Najaatu dai a yanzu allura cikin ruwa ce (mai rabo ka dauka)_

*MADADI74*

"Najaatu shuru kawai tayi tana bin wayar da kallo, mamakin maganarsa take wai zai turo Dan Azimi gobe"

ya dauketa lallai aikuwa yanda yazo haka zai koma domin kuwa bata tunanin zata bishi to wai nauyin waye a kanta da zaice lallai sai ta dawo gida me za tayi masa bayan baya kulata sannan kullum yana tare

da iyalinsa ita kuma sai ya hanata zuwa inda zata ji sassauci zuwanta gidan Mmn Sajida ya saukar mata

"da nutsuwar zuciya ko babu komai zatai kwana biyu bata saka shi a idonta ba, domin watarana ganinsa"

yana janyo mata abubuwa da dama hakuri kawai takeyi tana bin rayuwa a yanda tazo mata.

"Mmn Sajida ta kalleta a sanyaye tace""Najaatu naga jikinki yay sanyi ashe ba'a sani ba kika zo.''? Kallonta"

"tayi tace""Waye ya fad'a miki haka.""? Kai tsaye tace""Gashinan mahaifinki ya kira waya yana miki fad'a."" Mmn Ladi tace""Eh ai nima shiyasa kika ga jikina yay sanyi wallahi."

"Najaatu murmushi tayi a nutse tace""Wai ku waye ya fad'a muku Abbah Abbas mahaifina ne.""? bude baki"

"sukayi suna kallonta, ta sunkuyar da kanta tana dan murmushi wanda ya tsaya iyakacin lebenta."

"Mmn Sajida tace ''To idan bashi ya haife ki ba waye shi a cikin rayuwarki.""? Tana girgiza kanta tace""Shine"

mijina na fari wanda na baku labarinsa farkon zuwana garin nan.

"Suka tsira mata ido suna mamakin maganarta, kwallah ta cika mata ido tace""Kuna mamaki ko? ni kaina"

"ina mamakin kyautayi da tausayi da kyautatawa irin nasa dukkanin irin abubuwan da nayi masa bai sa ya watsar dani da al'amurana ba, yana tsaye a kaina da dukkanin bukatuna."" Mmn Sajida tace""Lallai Najaatu kin tafka babban kuskure a baya waye ya fada miki ana samun nagartattun mutane irin wannan mutumin? yanzu dama a kan an aura miki shi kika gudo garin nan yanzu dan Allah meye aibunsa meye kuma abun'ki a tattare dashi.""? Tana kuka tace""qaddara Mmn Sajida qaddarar wannan yaron dake hannuna ce ta kawo ni garin nan har na had'u daku Wallahi har bana so na tuno abubuwan da suka"

"faru a baya Mmn Sajida ni da kaina nasan na tafka kuskure babba! wanda yanzu nake nadamar aikatashi, yanzu gashi inaji ina gani Abbah yafi karfina sai dai na kalleshi da ido Mmn Sajida a yanzu ne nake masifar so nayi zaman aure dashi shi kuma yana nuna baya so, wallahi bansan iya adadain son da nake masa ba a cikin zuciyata saboda mutumin ya cancanci a soshi duk wata sadaukarwa yayi min yana kanyi min babu namijin da zan aura na samu nutsuwar da nake bukata, Mmn Sajida ba zan 'boye muku halin dana ke ciki ba wallahi saboda halin ko in kula da yake nuna min yasa naji zaman garin ya gundureni na"

"tattaro na tawo nan kuma bana tunanin zan koma a kurkusa sai na huta tukkuna."""

"Mmn Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace""Gaskiya Najaatu naji miki haushi da takaicin rasa wannan mutumin"

to amma tunda kin jingina al'amarin a matsayin qaddara muma zamu jingina shi a hakan ammafa wallahi kema da akwai son zuciyarki wanda shine ya kara sanyawa kika kai kanki ga wahala! saboda haka ni dai shawarar da zan baki wallahi ki lalla'ba da wayo da siyasa ya mayar dake dan nima na tabbatar da cewar a gurinsa ne kadai zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali saboda yanzu duniya kowa kansa ba

kowane namiji ne zai yarda kije masa da d'anki ba.

"""Mmn Ladi wane dabaru zanyi ya mayar dani ni bazan iya fada masa baki da baki ba, na hakura zan"

"cigaba da rainon yarona har Allah yasa ya girma, shikkenan idan na samu daidai dani sai na aura."

"Mmn Sajida tace."" Ni kuma sai nake ganin kamar yana jira yaron ki yay wayo ya bijiro da maganar kome"

"din kin san fa koda zai mayar dake gidansa ba zai mayar dake kina da d'anyan jego ba, wallahi ko kaffara ba zanyi ba yana sonki dan da baya sonki ba zai dinga yi miki wahala ba, haba ki duba fa ki gani shine yazo ya daukar ki anan sannan lokacin da kika kwanta a asibiti kina kiran wayarsa ko minti ashirin ba'ayi ba ya turo da kudiin da'a ka bukata. Duk da kin kasance mai laifi a gurinsa hakan bai hanashi kula"

"dake ba, ki kwantar da hankali da kansa zaiyi miki maganar ki koma gidansa amma kema dole ki dan yawaita kwalliya da gyaran jikinki da kowane lokaci ya dinga ganinki tsaf tsaf zaki janyo hankalinsa"

"sannan kina kiransa a waya kina gaisheshi."""

"Najaatu murmushin takaici tayi tace""Mmn Sajida sau nawa zan kira wayarsa yasa matarsa ta dauka! a"

"gabanki ma fa hakan ya ta'ba faruwa Abbah wani irin mutum ne wanda baka gane gabansa da bayansa."""

"Mmn Ladi tace""Kome baud'ewar halinsa mace na iya sanja shi saboda haka idan kika mayar da hankali"

"akan shawarwarin da muke baki zasu taimake ki."""

"Najaartu shuru kawai tayi tana sauraran maganganunsu, tana daukar na dauka tana watsar dana"

watsarwa bata tunanin zata tunkareshi da maganar ya mayar da ita gidansa idan ya tausaya mata da yaronta ya mayar da ita haka take so idan kuma yana ganin bashi da ra'ayi sai ta hakura ta barwa Allah.

"Sai bayan taci abinci ta nutsu tukkuna ta shiga fito musu da tsarabar data kawo musu , kowacce turmin"

atamfa biyu da mayafi da takalmi sai sabulai na wanka dana wanki da kayan kwalliya irin na mata.

"Sosai suka shiga yi mata godiyar hidimar da tayi musu, ashe da sauran godiya, dan kudinta na haihuwa"

data samu kimanin dubu saba'in da wani abu a ciki ta dauko dubu hamsin ta kawo musu

Mmn Sajida ta miqawa tace su raba. Mmn Sajida ta riqe kudin a hannunta tana kallonta cikin d'umbun

"mamaki! Murmushi tayi ta kalli Mmn Ladi tace""Mmn Ladi naki kudin sai kiyi kokarin ki fara sanaa dasu kafin naga abunda Allah zaiyi anan gaba insha Allahu idan na samu yanda nake so zan qara miki wasu."

"Mmn Ladi fashewa tayi da kuka ta rungumeta tana fad'in ""Wallahi Najaatu na rasa bakin da zan gode"

"miki ashe ke din alkairi ce a tare damu muna mutukar alfahari da sanin da mukayi miki wallahi Kinyi min abunda d'an uwa na jini baiyi min ba, a cikin 'yan uwana akwai masu hali amma babu wanda yay tunanin dauko kwabonsa ya bani da sunan naja jari nayi sana'a sai ke da Allah ya had'ani dake kin gyara min aurena kuma kin dauki kudi kin bamu, kin kawo min babban zani irin wanda banta'ba daurawa ba, babu"

abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da alkairi ya biya miki dukkanin bukatunki.

"Naja'atu tace""Haba Mmn Ladi meye abun kuka wallahi wannan ba komai bane a gurina idan ina da"

"abunda yafi haka zan baku domin kuma kun taimakawa rayuwata a lokacin da nake bukatar taimako saboda haka ki daina kuka kina gode min Allah ne ya had'amu ina fatan zumuncin mu ya d'ore har 'ya'ya da jikoki."" Mmn Sajida tace""Insha Allahu Najaatu Allah zai cika mana burin mu kuma kamar yanda muke"

"zumunci insha Allah 'ya'yanmu suma za suyi."""

Da wannan addua ta Mmn Sajida suka rufe maganar suka shiga hirar Bash da hukuncin da'a ka yanke

masa.

"Laifin Najaatu ya shafi su Halisa a tunzure ya shiga gidan, girkin Halisa ne ganin yanda ya shigo yana shan"

"qamshi yasa bata tunkari inda yake ba gudun wulakanci yasa taje tayi kwanciyar a dakinta tana kallo, har ya gama abinda yake a falo ya shigo yay shirin kwanciya, zama yay gefan gado da wayarsa a hannunsa."

Number Najaatu ya nema

Lokacin dare yayi dan goma da rabi ta wuce duk sunyi shirin kwanciya Mmn Sajida dalilin zuwan

"Najaatun yasa bata fita sana'arta ba, suna hira sama sama kiran wayarsa tasa ya shigo."

"Ta dauka tana dan tunani to me ya kirata yace mata? Shawarar dasu Mmn Sajida suka bata ta tuna, sai"

"kawai ta daga wayar tana wani maqale murya tace""Hello Abbah! barka da dare."" Wani irin yarrr! yaji a jikinsa sakamakon jin yanda muryarta ta ratsa jikinsa, tamaza yay yayi gyaran murya as'usul yace.""Barka dai ina fatan kin suturta yaron nan da kayan sanyi saboda kin san dai yanda ake sanyi gashi na lura"

"gurin da kike bashi da tsaro da sauransu."""

"Dan murmushi tayi tana kallon Mmn Sajida, ta sake kashe murya tace"" Abbah ni baka damu dani ba"

"kenan kana tambayar na suturta Mai sunanka nima ai ina jin sanyi sosai a jikina.""! Cikin shagwaba ta k'arasa maganar."

"Shuru yay na minti biyu kafin yace.""Ke ai kin girma sanyi ba zai miki lahani ba kamar shi so sabida shi na"

"kira wayarki sannan kuma na sake tunasar miki da abinda na fad'a miki d'azu! gobe da wurwuri Dan Azimi zai zo ya daukeki."""

"Kamar za tayi kuka tace""Allah ni bazan dawo gobe ba, Abbah wa na'ajiye a garin kano da zan takurawa"

kaina dawowa ni dai dan Allah ka bari na kwana biyu a gari jos dan ina jin dadin garin sosai da sosai.''

"A hasale yace.""Ke! ashe baki da hankali wannan garin duk babu mutunin arziki a cikinsa ashe kina so ki"

"sake haduwa da wani mara tarbiya kenan( Afuwa mazauna wannan garin banyi da niyyar naci muku fuska ba labari ne yazo a haka a gafarce ni garin jos akwai masu tarbiya sosai ga misalin irinsu Mmn Sajida nan nayi). Tace""Haba dai Abbah ba duka a ka zama d'aya ba Wallahi su Mmn Sajida suna da"

kirki da tarbiya kuma ni da naje ziyara mai zai had'a ni da wani saurayi ko bazawari babu ruwana dasu.

"Yace.""Ni dai na fad'a miki gobe ki zauna cikin shiri domin hankalina bai yarda da zamanki a wannan gari"

"ba."" Kashe wayar yay bai saurari ta bakinta ba. Halisa ta miqe zaune tana hararar bayansa ji take"

"kamar ta makeshi! saboda haushi yana yaudarar kansa yana yaudararsu to meye nasa na damuwa dan ta tafi jos da har zai ce zai tura a daukota. tsaki taja a zuciyarta kafin tace""To wai kai meye na damuwa dan ta tafi wannan gari? babu fa nauyin kowa a kanta da kake cewa ta dawo haba ai ka kyaleta ta huta su"

"gaisa sosai da wannan mutanan da sukayi mata hallaci."""

"Yana jinta yay shuru sai ma ya fara kokarin kwanciya yana kokarin rufe kafafunsa, Halisa bata san sanda"

"taja tsaki ba tace""Abban Mufida kenan ka tsaya wasa wallahi sai dai kaji anayi dan Najaatu a yanzu allura cikin ruwa ce da d'anyan jegon da take dashi ba zata rasa me auranta ba. Fad'in wannan magana da"

"Halisa tayi sai ya fusata! ya miqe zaune ya dinga zazzaga mata masifa da fad'in ""mahaukacin Namiji ne"

zai auri mace da d'anyan jego saboda haka kada ta kuskura ta sake yi masa irin wannan magana.

"Halisa itama ta fusata tace"" To itama kada ya sake zuwa gabanta yayi waya da Najaatu tunda abun nasa"

"ya zama rainin hankali, haka suka dinga cacar baki tana fad'a yana fad'a dan gabanyansu a tunzure suke kowa yana ganin ba'ayi masa daidai ba.......Gabad'ayansu Haka suka kwanta suna jin haushin juna....."

*Infaction*

_Ko wace mace kaji tace miki tana fama da infaction wai shin ya zamuyi mu kare kanmu daga wannan

laluran mai wahalar magani? Idan kina da sanyi koda mijinki bai dashi sai ya samu Ko kuma ke baki

"dashi mijinki nada shi to sai kin samu, idan ya kasance duk kuna dauke da lalurar sai ku durfafi shan magani a tare! dan idan daya yasha daya bai shaba to akin banza kukayi ciwon yana nan babu inda zaije. Kina budurwa kina kyaikayin gaba da zubar da farin ruwa gashi an kusa bikin ki kinja bakinki"

"kinyi shuru baki fadawa mamanki ba, to zaki haifarwa da kanki matsala babba dan idan kikaje gidan mijinki da wannan ciwo kika shafa masa zai miki mummunar fahinta ya dunga yi miki wani irin kallo na daban saboda haka mutukar kina da matsala irin wannan maza ki sanar da mahaifiyarki kafin ki"

sanar dani mahaifiyarki itace mafi kusa dake kuma ita ta haifeki babu kunya a tsakaninku! Ki fada mata

komai zata kaiki gurin mai magani Ni shawara ce kawai a tsakaninmu._

*Idan da tsumma kike using a lokacin da kike jin al'ada to ya kasance kullum kina sanjawa sau uku ko sau

"hudu, sannan idan kin wanke tsumman ki dinga sashi a rana ya bushe kwayoyin cutar zasu mutu. mutukar kina barin matuncin ki da danshin ruwa to ba zaki rabu da kyaikyayin gaba ba,"

wannan guri an fiso kullum ya kasance a bushe. Idan da pad kike using

63 / 79