Chapter 27 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 79

78K to 81K   out of 235.1K words

taje ta rufe kofa tana kuka...Halisa ta dinga dukan kofar tana fadin""Shikkenan sun lashe min kurwar 'yata! kai ubangiji Allah ya rabamu da mayen mutum..Mussadiq ya sunkuyar da kansa kasa yana goge hawaye! A fusace! ta kai masa rankwashi a"

"kansa tana fadin""Na tafi na bar muku gidan shegu mutsiyata."" Fuuuu! ta wuceshi ta nufi kofar futa."

"Mussadiq ya tashi yaje ya tsaya a bakin kofar dakin nasu yana kiran sunan Mufida da fadin""Ta bude kofar"

"mommy din ta tafi...Mufida na kuka tace""Mussadiq bazan bude ba sai Abbanmu ya dawo tsoro nake kada mommy ta dakeni."" Mussadiq zama yayi bakin kofar dakin yana kuka hade da bin palon da kallo."

Driving yake tana satar kallonsa ta mirror ganin fuskarsa tayi a hade tamkar tunda aka hallice shi bai

"ta'ba dariya ba, ba tun yau ba tasan shi da masifar son 'ya'ya tayi mamaki ma da hukunci mari ne kawai ya shiga tsakaninsa da Halisa tabbas kowa yaji abunda ta aikata yasan bata kyauta ba, kuma ta nunawa duniya cewar ba zata iya ri'ke yaran tsakani da Allah ba. Ita kuwa sai take ganin to meye amfani kana"

son mutum amma baka son 'yayansa.

Gani tayi yay parking a gurin da suka ta'ba tsayawa yayi musu take away. Yauma gurin taga ya nufa ta

"bisa da kallo har ya shige cikin gurin, sannan ta mayar da hankalinta kan Saddiqa dake bacci a bayan mota, hannu ta mika ta dan shafi wuyanta taji har yanzu da zafi amma ba kamar dazu ba, cikin zuciyarta tace""Allah ya kareku daga sharrin matar nan."" Hango shi tayi ya tawo hannunsa da ledoji kamar yanda ya saba, tausayinsa taji ya ratsa mata zuciya, Abba Abbas mutum ne shi mai zuciya da kula da iyalinsa komai suke bukata sai yayi musu da jikinsa da aljihunsa a tarihin rayuwarta a gidansa bata ta'ba d'aura zani dan 'kasa da dubu biyar ba manyan atampopi da lesuna yake dinka musu shadda kuwa komai tsadarta zai d'inka yasa a jikinsa suma ya d'inka musu, komai nasu mai kyau ne! Idan sallah tazo kuwa"

haka zai kwashe su a mota suyi ta siye-siye wanda har sallah ta wuce basu gama amfani dasu ba.

Gaskiya ta wannan bangaran ya ciri tuta tana jin da tana sonsa to babu abinda zai hanata ta kyautata

"masa, sai dai kash ta rasa a wane matsayi zata ajiye shi a zuciyarta duk da cewar ya kar'bi abu mai muhimanci a gurinta hakan bai sanya ta ta karaya daga kudirin dake cikin zuciyarta ba, tayi alkawarin ba zata kare rayuwarta da auran tsoho ba dole ne ma ya sauwake mata tunda ya kawar da kulafucinsa a"

kanta

Ganin yana kokarin bude motar ne yasa tayi saurin dauke kanta daga kansa...Ya zauna mazauninsa tare

da kunna motar suka bar gurin.

BHRBN

*32*

"Mussadiq najin motsin shigowarsu sai ya mike da sauri yana me kallon kallon kofar shigowa, Naja'atu"

"ganin yaron kamar a furgice yasa tayi saurin 'karasawa kusa dashi tana tambayarsa, sai kawai yasa kuka yana nuna mata dakinsu da hannunsa."

"Tace""Menene kake kuka ina Mufida.""? Yace.""Tana daki ta kulle kofa wai tsoro take kada mommy ta"

daketa alhalin kuma mommy din ta tafi unguwa yanzu.

Da sauri tasa hannunta jikin kofar tana bugawa had'e da kiran sunan yarinyar.

Mufida najin muryar Naja'atu sai tayi saurin bude kofar ta rungumeta tana kuka.

Taja hannunta suka zauna kan kujera tana tambayarta.

Yarinyar na fada mata abunda ya faru ya shigo palon ya tsince karshen maganar inda take cewa

Mommynta ta tafi gidan Baba da jakar kayanta saboda tace ba zata bita ba shine ta doketa. Ba tare

"daya nuna damuwarsa ba ya kalli Naja'atun yace.""Kije dasu daki suci abinci su kwanta amma ki tabbatar da cewar Saddiqatu tasha maganinta kan 'ka'ida."""

A sanyaye ta amsa masa kana ta mike cikin dauriya ta nufi dakin yaran suka bi bayanta. Zama yayi kan

"kujera yana mamakin halin halisa wato saboda ya nuna mata kuskuranta shine tayi yaji, to kuwa babu shakka wannan karon zai nuna mata fushinsa da babu inda zai taka yaje idan ta gaji da zaman gidan ta"

dawo da kafafunta.

Halisa sai bayan ta fita daga gidan kuma sai ta shiga tunanin abunda zata fadawa iyayenta idan taje! duk

"ranar da tayi yaji taje gidansu mahaifinta ba yayi mata da sauk'i! fada sosai yake mata kuma ya daina kawo cefane mai kyau a gidan a yini a kwana ana cin tuwo washe gari kuma a dama kunu asha ko kosai babu sai dai ta fito da kudinta tayi siyi abinda take so, bayan haka kuma shimfidar arziki bata da ita a"

gidan sai da ta had'a summokara ta kwana a kai.

Yanke shawarar zuwa gidan Yaya Ramlatu tayi dan saboda tasan mijinta ba mazauni bane kuma Yaya

Ramlatu tana da spire na daki sai ta shiga ta zauna ta rantse ba zata koma gidan ba sai yazo da kafafunsa ya bata hakuri wannan shine abinda ta kudurta a cikin ranta.

"Yaya Ramlatu na shirye-shiryen kwanciya kawai taji sallamar Halisa a gidan, tayi saurin daga labule ta fito"

tana amsawa.

"Halisa kece da daddaran ina fata dai lafiya.""? Halisa ta girgiza kanta cikin kunar zuciya tace""Mu shiga ciki"

"Yaya."""

Yaya Ramlatu ta rike hannunta suka shiga dakin suka zazzauna. Halisa kafin ta fadawa Ramlatu abunda

ya faru sai da taci kukanta ta koshi!.

"Yaya Ramlatu tace""Ki daina kuka! kada ki jazawa kanki lalura idan baki manta ba dama na fada miki idan"

"yarinyar nan ta shigo gidan to ki tabbatar da cewar auranki na tangal-tangal dan saboda ni narasa wane irin mutane ne su masu masifar d'afar tsiya idan suka rikewa mutum kurwa sai sun rabashi da kowa, amma babu komai ai mune maganinsu, dama dazu bayan mun gama waya dake na kira *'Yar Shagamu* a waya duk na sheda mata abinda ke faruwa tace""Babu matsala zata shigo gobe mu tattauna dan akwai wani malami da take saran kaimu gurinsa insha Allahu kukanki ya kare mutukar mun dangane ga wannan malamin, sabida haka zaki zauna tare dani muga abinda hali zaiyi nasan idan aikin malam ya"

fara tasiri a kansa zai nemi duk inda kike.

"Halisa tace""Nima dama shawarar dana yanke kenan da nayi niyyar tafiya gidanmu sai na tuna idan naje"

can din wahala ce shiyasa na nufo nan domin muyi shawarar abinda ya dace..

"Yaya Ramlatu tace""In dai kin futo da kudi ai komai mai sauki ne."" Tace""Cikin jakata a yanzu bai fi dubu"

bakwai ba amma na fito da Atm dina gobe zan fita na ciro kudin insha Allah.

"Yaya Ramlatu tace""To Alhamdullhi bari na tashi na gyara miki shimfida ki kwanta."" Mikewa tayi ta shiga"

kici kicin sauko da katifa. (Kai jama'ai wai shin ita Ramlatu wace irin mata ce)

Sai da ta tabbatar da cewar yaran sunyi bacci tukkuna sannan ta mike a nutse ta shiga toilet kafin tayi

"wanka sai da ta sake shiga ruwan dumi tukkuna sannan tayi wanka ta fito daure da zanin atamfar jikinta. Tana kokarin bude jakar kayanta domin dauko kayan bacci ya shigo dakin, gabanta ya fadi sai ta"

"shiga addua kan kada Allah yasa yace tazo dakinsa ta kwanta. Yace.""Duk sunyi bacci kenan.""? Kanta a"

"kasa ba tare da ta kalleshi ba tace""Umm."" Sai ya nufi gadon Saddiqa tare da tsayawa a kanta yana"

dubata.

Ganin haka yasa da sauri ta dauki hijabinta tasa ta fito da riga da wando irin na bacci ta ajiye a kusa da

ita ta rufe jakar gabanta sai dukan uku uku yake.

Ya jima yana kallonta yana mamakin abinda tayi to meye kuma na rufe jiki dan shirme! wane dare ne

jemage bai gani ba!

"Gyaran murya yayi, ta zabura! da sauri ta takure jikinta."

"Yace.""Zaki kwanta anan ko kuma zaki zo muje dakina.""?"

"Da sauri tace""Zan kwana tare dasu dan saboda Hannun Saddiqa."" Yace""Okey to zaki iya kwanciya kasan"

kafet kenan.?

"Murya na rawa tace""Eh babu damuwa.""! Yayi shuru yana kallonta da murmushi a fuskarsa tsaf ya gane"

"gudunsa take kuma ta tsorata dashi sosai dama haka yake so yana so ta gane bambamcin aya da tsakuwa yasan yanzu zata gane tsufa ko yawancin shekaru ba zai hanashi kuzari ba, d'an shekara sittin"

ma sai ya fishi fitina

"Ganin ya kama hanyar fita daga dakin yasa taji wani irin sanyi a cikin ranta, yana fita ta mike da sauri"

tasa kayanta ta dauki bargo da pillow ta shimfida kasan kafet ta kwanta.

"Ta dauka ba zai dawo dakin ba shiyasa ta cire hijab din jikinta, kawai sai taji ya turo kofar dakin ya shigo"

hannunsa rike da lallausan bargonsa Mikewa zaune tayi ta had'e gwiwoyinta guri guda taki kallonsa

"Shima ganinta cikin kayan baccin yasa ya shagala da kallonta, yarinyar na masifar tafiya da imaninsa."

Tsayuwar da yayi a kanta yasa ta dinga jin tamkar ta saki fitsari a wando tuni hawaye ya soma d'iga daga

"idonta. A nutse ya tsuguna gabanta yasa hannunsa ya dago fuskarta, sai kawai yaga hawaye na zirara!"

"Ya jima yana kallonta da mamaki a fuskarsa, yace.""Kukan me kikeyi.""? Girgiza kanta tayi tace""Babu"

"komai.""? Yace.""Akwai dalili ki fada min ko tsorona kikeji."" Ta d'aga kanta tana me rike hannunsa dake tallafe da fuskarta tace""Abbah dan Allah kada ka 'kara wallahi ni kadai nasan abinda nake ji."""

"Yaji tausayinta ya kamashi, yace""Ba zan sakeyi ba sai gurun ya warke sosai amma kiyi min alkawari idan"

"nazo zaki bani goyon bayan da nake bukata. Cikin rashin dubara da wayo tace""Allah nayi maka"

"alkawari zan baka."" Yace""To nagode ina rokan Allah yayi miki albarka ya kuma barni tare dake sannan ya"

"albarkace mu da zuria mai albarka."""

Shuru tayi ba tace amin ba babban burinta ya tashi ya bata guri.

"Fuskarta ya tsirawa ido yana kallon karamin bakinta, ji yayi ba zai iya hakura ba dan haka sai ya shiga"

"kusantar fuskarta da tasa, ta wani irintse idonta tana takure jikinta."

Hawayen dake ziraro mata ya shiga lashewa yana dan tsotsar kumatunta cikin wani irin salo na

mussaman! Tayi kasa'ke! sa'kon na ratsa mata jiki.

kafin yasa bakinsa anata sai da ya tsotsi le'bunanta sosai sannan yayi dubarar kama harshenta ya shiga

tsotsa tamkar alawa

"Wani irin yanayi ta dinga ji a jikinta, jikinta ya mutu kasala duk ta dabaibayeta, sosai da sosai takejin"

dadin kiss d'in! ta dinga mutsu mutsu tana so ta tsotsi harshensa ta rasa yanda za tayi dan da tayi yunkuri kamawa sai ya janye nata ya rike yake ta tsosa kamar zai tsinke shi hannunsa da ya riko

fuskarta ta kama ta ri'ke tamau! tana wani lumshe ido hade da d'an gyara zaman da tayi Shi kuwa

ganin ta saki jikinta bata turje-turje yasa ya cigaba da abinda yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

A 'kalla! sun dauki kimanin mintina goma cikin wannan yanayi kafin su rabu da juna! idanunta dake

"lumshe ta bud'e tana kallonsa, sai yayi gaggawar mikewa dan saboda yanayin kallon da tayi masa yayi masifar tayar masa da hankali"

"Hanyar fita ya nufa, kamar shashasha ta bishi da kallo tana ji kamar ta dawo dashi su cigaba da abinda"

sukeyi(Ikon Allah ) zamewa tayi ta kwanta hade da daukar bargon daya ajiye mata ta rufe jikinta har fuskarta tana matse cinyoyinta sakamakon jin wani irin abu da gabanta ke mata tasa hannu a hankali a hankali tana shafa lebunanta tana wani lumshe ido...Wani irin yanayi take ji a jikinta wanda ta kasa tantance na menene? (Naja'atu ta fara fahimtar abunda ke da akwai) Da kyar bacci ya dauketa cikin wani yanayi mara dadi kafin gari ya waye kuwa ta farka ya kai sau uku dan data rintse idonta zata ganta

tare da Abbas din rungume da juna suna abubuwa masu dadi da wuyar mantawa.

"Dalilin da yasa kenan da asubah ta riga kowa tashi a gidan, cikin kasala da mutuwar jiki ta nufi toilet ta"

tu'be gabadaya kayan jikinta har pant bata bari ba dan tana jin danshi danshi a jikinsa shiyasa ta kasa yarda da tayi sallah haka ba tare da tayi wankar tsarki ba.

Wanka tayi kafin tayi bursh ta daura alwala ta fito wanda yayi dai-dai da shigowarsa dakin domin

tashinsu kamar yanda ya saba.

Ganin ta fito daga toilet din ne ya sanya ya sauke ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba ya juya ya fita.

"Bayan ta kintsa jikinta sai ta shiga tashi yaran kamar koda yaushe, sai da ta tabbatar sun tashi sannan ta"

"hau dadduma domin gabatar da sallah.............Yaran bayan sun idar da sallah cikin nutsuwa suka shiga gaisheta ta dinga amsawa cikin sakin fuska, ta kalli Saddiqa da fadin""Ya jikin naki?""? Saddiqa tace""Da sauki yanzu bana jin zafi sosai."" Tace ""Dama ai Dr yace"" zafin ciwon jiya da yau ne kawai insha Allahu idan kina shan magani zai warke."" Saddiqa ta mike ta nufi wardrobe dinsu da hannu daya take kokarin dauko musu inform tace""Ke maye haka? da ciwo a hannuki zakije skull.""? Saddiqa tace""Yaya Naja'atu kin san halin Uncle Aminu ko."" Tace""Komai halinsa dana sani dole ya daga kafa ki kwana biyu a gida hannuki"

ya warke tukkuna. Suna wannan ta'kaddamar ya shigo dakin

Sai suka shiga rige-rigen gaisheshi kamar dai koda yaushe.

"Ya amsa a nutse yana tambayarsu, a nutse tace masa wai skull za taje a haka."""

"Ya kalli Saddiqan tare da fadin""Kiyi hakuri ki zauna a gida kwana biyu ki samu sauki sosai ni da kaina"

zanje na na fadawa ancle din baki da lafiya.

"A sanyaye tace""To shikkenan Abbah Naja'atu ya dan kalla yana so yayi magana sai kuma yayi shuru da"

bakinsa yana sk yaga iya gudun ruwanta kama hanya yayi ya fita daga dakin kamar kuwa tasan

"abinda yake cikin zuciyarsa, ta mike da sauri ta fito da niyyar shiga kicin nan ta sameshi a kan kujera"

yana duba loptop. ganin ta nufi kicin din sai ya sauke ajiyar zuciya me sanyi yana rokon Allah ya tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.

Tsaf ta kammala musu break fast ta shirya daning din gwanin sha'awa duk yana zaune yana kallonta

yanajin wani farin ciki a cikin zuciyarsa ganin ta tashi da kuzari kuma yanayin tafiyarta ya daidaita yaji dadin hakan sosai da sosai.

Tare da yaran ta zauna suna break fast shi kuma yana zaune a inda yake da alama yana duba mihimun

abu cikin loptop din dake gabansa.

"Salim ne yayi sallama ya shigo palon, yana sanye da kananun kaya wanda sukayi masifar yi masa kyau!"

"Salim dan gayu kwana biyu ya sakeyin fresh saboda yana samun kudi sosai gurin Kawun nasa, Salim"

yanzu har bleecing yake yayi wani uban haske ga sumar kansa tasha gyara sai kyalli take. Naja'atu kasa

dauke idonta tayi daga kansa sai murmushi takeyi wanda kana ganinsa kasan na farin cikin ganinsa ne..

"Shi kuwa Salim ganin tana nema ta tona musu asiri yasa yayi gaggawar kauda kansa daga inda take, kai"

"tsaye gurin Abbah Abbas ya nufa ya ritsina tare da mika masa hannu da fadin""Barka da asubah Kawu."""

Cike da kulawa ya bashi hannu sukayi musabaha yana amsawa tare da tambayarsa

"mahaifiyarsa...Yace.""Tana nan lafiya Kawu tace Ma na sake tuna maka da sa'konta."""

"Yace.""Kada ta damu insha Allah zan baka ka kai mata."" Yace.""To godiya take Kawu....Cikin basarwa Salim"

"ya kalleta yana dan ya'ke yace.""Antyna barka da asuba ina fata kin tashi lafiya."""

"Naja'atu wani iri taji jin sunan daya kira dashi...Dauke kanta tayi tana 'bata fuska tace""Barka dai."" Hakan"

da tayi sai ya faranta ran Abbah Abbas din yaji dadi data nuna rashin kulawarta a kan Salim din.

"Salim ya kalli Mussadiq da fadin""Oya ku tashi mu tafi."" Mussadiq da Mufida suka mike sai ya kalli"

"Saddiqa yace""Baby kefa?"" Tace""Ciwo naji a hannuna."

"Abbah Abbas yace ""Yau saddiqa bata zuwa skull ta samu rauni a hannunta saboda haka idan kaje ka"

shedawa ancle dinsu abinda ke faruwa.

"Yace."" Insha Allah Kawu."" Lokacin daya kama hanyar fita tare da yaran Naja'atu binsa tayi da wani irin"

kallo mamaki take sosai wai yau ita Salim ke kira da Aunty lallai Salim gaskiya ya bata mamaki.

Mi'kewa tayi jikinta a sanyaye ta nufi daki ta kwanta! ganinsa yanzu ya sake tayar mata da hankali sai

taji duk ta tsani komai na duniya Abbah Abbas din ma taji bata son kallon fuskarsa. Saddiqa ce ta shigo

"dakin, ta zauna tana kallonta tare da fadin"" Yaya Naja'atu Abbanmu yace.""Wai ki bani magani na."""

"Harararta tayi tace""Kamar baki san inda maganin naki yake ba duba dan Allah da girmanki da komai ake cewa a baki magani kamar wata kankanuwar yarinya."""

Saddiqa ta shiga binta da kallo ganin yanda take mata magana a hasale! sai abin ya bata mamaki! cikin

sanyin jiki taje ta dauki maganin tasha ta kwanta kan bed dinta......

Sai da ya gama abinda yake a tsanake tukkuna ya rufe loptop din ya mike ya nufi gurin cin

abinci Komai gashinan a shirye a kammale cikin tsabta ba kamar tsarin Halisa ba da wani abun ma

"idan tayi yake sashi tashin zuciya. Abinci yaci sosai irin wanda ya jima baici irinsa ba, ya goge bakinsa"

da tissue kafin ya mike ya nufi bedroom dinsa domin kintsawa.

Halisa bayan sun gama karya kummalo sai ta dauki wayarta tana dubawa gaskiya tayi mamaki sosai da

"ko text bata bai turo mata ba, jikinta yayi sanyi sosai hankalinta ya sake tashi, ta azalzali Yaya Ramlatu ta shirye suje har gidan 'Yar shagamun su sameta."

Babu arziki Yaya Ramlatu tayi wanka ta shirya a gurguje suka fito sunayi wa Sakina sallama. Binsu tayi

da kallo har suka fita daga gidan bakinta bai daina yi musu adduar shiriya ba.

*'Yar Shagamu* wacce taga jiya taga yau tsuhuwar kilaki ce ta gama yawan karuwancinta ta siyi gida

"tana tara maza da mata suna she'ke ayarsu a gidan, ita kuma tana gefe ta kasa sigari da goro da shisha duk maiso yazo ya siya...."

"Halisa da taga irin rayuwar da Yar shagamu takeyi a gidan sai data tsorata, tana zaune a tsakar gida daga"

"ita sai breziyya da dogon siket ga maza 'yan bana bakwai sun kewaye ta."""

"Ramlatu da 'Yar shagamu ciki a daidaita sahu suka had'u shikkenan sukayi musayar numbar, tunda Yar"

shagamu ta fahimci cewar Ramlatu yar son duniya ce sai ta makale mata suka kulla abota. sa'i da lokaci Yar shagamu na kawowa Ramlatu ziyara har gidanta itama Ramlatun tana zuwa gidan nata duk da kasancewarsa matattarar 'yan iska.

27 / 79