Chapter 76 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   76 / 79

225K to 228K   out of 235.1K words

tayi masa tayi tare da fad'a masa abinda yake so ta dafa Yace.""A"

"'koshe yake da zai tafi ta dakatar dashi tare da fadin tana so tayi magana dashi, yace sai dai ta bari sai da safe dan yanzu sauri yake Koda ta fito falo samunsa tayi yana magana da Munira tana fad'a masa"

"cewar gobe zata tafi da safe. Yace.""To kada ki tafi sai nazo."" Najaatu gabanta ya dinga bugawa ta tsirawa bayansa ido har ya fita daga falon, kasa zama a falon tayi ta shiga daki ta kwanta, to itama Munirar ganin matar gidan na cikin damuwa yasa ta kashe tv taje ta kwanta. Najaatu kasa hakuri tayi ta dauki"

"wayarta ta kirasa, ya dauka sama sama take jin muryarsa."""

"Hawaye ta share tana kokarin aro dauriya tace""Da kace kada ta tafi sai ta jira ka me za kayi mata idan"

"sonta kake sai ka fad'a min ni zan baka goyon baya."""

"Murmushi yayi dan ya bata haushi yace.""Ai ba raham bane dan nace ina sonta nace kada ta tafi sabida"

"akwai sirri a tsakanina da ita."" Sai kawai ya kashe wayarsa yana murmushin jin dadi shi dai yana so yaga ana kishi a kansa, Halisa ta gama yanzu Zainab da Najaatu ne keyi aure sai ya cikashe hud'u idan ma zasu hakura su hakura Najaatu ta dinga jin kamar taje dakin Munirar ta tuhumeta abinda ke tsakaninta da"

"mijinta sai dai ta daure ta dinga nanata kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji""un. Da kyar bacci ya dauketa. Da safe Munira kasa gane kanta tayi sai tasha jinin jikinta tayi sanyi ta dinga Allah Allah"

maigidan ya shigo ya sallameta ta tafi dan ta lura zamanta a gidan na nema ya haifar da matsala.

Cikin galleliyar shaddarsa (wagambari) ya shigo gidan yay kyau har ya gaji kana kallonsa zaka gane bai da

"damuwa dan har wani 'kiba da haske ya 'kara matsalarsa kawai rashin samun abunda yake so ranakun kwanan Halisa da Zainab, kamshin turaransa ya cika falon Munira ta gaishe shi tana sunkuyar da kanta"

"wani abu take rayawa a ranta, inama inama! sake dago fuskarta tayi ta kalleshi tay saurin sunkuyar da kanta kasa tabbas ruwa ba sa'an kwando bane. Yace.""Ina matar gidan take ta barki ke daya a"

"falo.""tace""Tana ciki bata fito ba."" Kai tsaye dakinta ya nufa. Najaatu na sane tasa k'ananun kayan da"

"suka matseta wando iya gwiwa da rigar da bata rufe mata cibiya ba, kayan sun mata kyau sosai kuma dole su rikita wanda akayi dominsa. Ganin irin shigar dake jikinta yasa ya tsaya daga bakin kofa"

"sabida tsaro, kallonsa tayi tace""Ina kwana.""? Cikin basarwa ya amsa, yana wani kauda kansa, Yace ina"

fata baku da wata matsala ko.''?

"''Uhm."" tace tare da mi'kewa yay saurin dauke kansa xuwa tayi ta gifta shi, kofa ta bude ta fita ta barshi"

a tsaye a dakin Gabadaya ji yay gwiwarsa tayi sanyi anya kuwa zai iya wannan ya'kin? daurewa yayi ya

"fita falon nan ya same su suna magana, Ya kalleta da fad'in Abunda yasa Nace 'kawarki ta tsaya kada ta tafi sabida bukatarki da kika fad'a a kanta inaso naji abinda take bukata kafin na fita. Kamar tace masa"

"kaida kake da sirri da ita kuma! sai ta share maganar tana dauke kai tace""Sana'a zata fara bata da jari shine nace ko zaka taimaka mata."" Da sauri yace.""Me zai hana muka taimakawa na waje ma ballantana na gida, insha Allah zan tura miki sai kuje tare idan kin cire ki bata, ya kalleta da fadin "" Munira Allah ya"

"kiyaye hanya a gaishe da mutanan gida."" Munira tace""Zasuji insha Allah nagode sosai Abbah Allah ya"

"raya zuria."" Ya amsa da amin hankalinsa a kan Najaatu dake ta faman dauke kanta har yanzu taki sakar"

masa fuska. Shi kam jikinsa ne yayi sanyi sanin da yayi yau a gidanta yake fargabarsa kada dare yayi

"labari yasha bambam dan ya lura a fusace take, sasauta murya yayi yace.""Ni na tafi kasuwa."" Tace""Allah ya bada sa'a."" .Yana kokarin bude kofar falon ya amsa da amin ya rabbi"

Abbah dubu dari cif ya bawa Munira Najaatu ta cire mata kudinta ta bata tare da kara mata dubu goma

"akai bayan sutturu da kayan kwalliyar data had'a mata, Hajia da baba talatu suka harhad'a mata kayayyaki masu yawa, Munira kasa daurewa tayi ta dinga kuka tana gode musu ashe dama Najaatu alkairi ce a garesu! Allah kenan, Dan Azimi ne ya dauketa a mota ita da kayan ta domun kaita can"

kyauyen nasu.

*BAYAN WATA UKU*

Salim yaji sauki sosai sai dai kullum yana gida babu abunyi sai yamma tayi yake fita ya zauna a cikin

"abokansa marasa sana'a! Mahaifinsa ya yanke shawarar siya masa adaidaita sahu ya fara ja domin zaman hakan bashi da amfani, koda Sakina ta sheda masa maganar farin ciki yayi domin shima zaman ya isheshi, yanzu yana jiran dawowar mahaifin nasa daga tafiya tunda yace idan ya dawo zasuje gurin siyar"

da napep din tare.

"Abbah Abbas a nutse ya kalli 'yar uwarsa yace.""Bana jin dadin ganin Salim a zaune a bakin titi babu babu"

"abinyi kullum idan zan shigo unguwar nan sai na ganshi a zaune wannan dalilin yasa na yanke bud'e masa gurin gurin siyar da takalma anan bakin titin unguwar taku nasan ba za'a rasa shaguna ba, dan haka zan nemeshi akan maganar idan yaso sai ya fara bunkicen gurin zama."

"Yaya Ramlatu fashewa tayi da kuka tace"" Hakika dan uwana Bani da abinda zance maka sai dai na roki"

"Allah yasa ka gama da duniya lafiya nagode sosai da wannan karamcin naka, dama shekaran jiya yazo yana fada min cewar mahaifinsa yay masa alkawarin zai siya masa adaidata sahu to kuma sai gashi kazo da wannan maganar ."""

"Yace.""Ai ba wani abu bane idan ya siya masa adaidata sahun zai iya hada kasuwanci biyu."" Hajia"

"tace""Hakane kam kaima kayi zumunci Allah ya saka da alkairi."" Amsawa yay da amin amin kana yayi musu sallama ya tafi gurin iyalinshi Ya Ramlatu a waya ta kira Salim ta sheda masa maganar a ranar"

Salim da kyar ya iya bacci sabida murna da farin ciki hakika bai ta'ba ganin mutum mai kyakkyawar

zuciya irin Kawun sa ba.......

*BA HARAM BANE!!*

*****90 Cikin sati biyu kacal komai ya kammala Abbah yasa an zubawa Salim kaya a k'aton shagonsa

"takalma na manya da yara maza da mata, Salim tsabar farin ciki har hawaye sai da ya zubar Mahaifinsa kuwa har kasuwa yaje gurun Abbah Abbas din ya nuna masa farin cikinsa dangane da alkairin da yayi masa ya dinga godiya kamar wanda aka bashi kyautar kujerar makka. Abbah Abbas dakatar dashi yayi"

"yace masa dan yayiwa Salim abu bai kamata yazo yana masa godiya ba saboda a har yanzu a matsayin uba yake a gurinsa dan haka ya daina masa godiya akan abinda yayi."" Ayuba ya dinga jinjina nagartarsa tabbas a yanzu samun mutune masu yin abu domin Allah irinsa sai an tona babu shakka Alhaji Abbas"

yana kokarin aikata aikin alkairi da tarin dukiyar da Allah ya bashi.

*BAYAN WATA BIYU*

"Al'amura na tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali, a zamantakewar gidan Abbah an samu daidaito ta"

"kowane bangare yana kokarin ganin ya sauke hakkin dake kansa, shiyasa suma matan suka samu nutsuwa tunda ko wacce yana yi mata abinda take bukata, sai suyi wata da watanni basu had'u da junansu ba mutukar ba wani taro akeyi a 'bangaran maigidan nasu ba, to nan ma idan sun had'u su ukun suna gaisawar mutunci suna kokarin danne kishi a tsakaninsu, wannan nutsuwar daya samu ne yasa hankalinsa ya kwanta harkokin kasuwancinsa suka cigaba da bun'kasa, arziki da wadata sai nunnkuwa suke sai dai godiyar Allah Cikin Halisa nada wata shida Najaatu ta harbu, to da yake cikin nata ba"

"me laulayi bane yasa babu wanda ya san tana da ciki harshi maigidan shuru tayi masa bata fad'a masa ba, ta godewa Allah da yasa cikin ba mai wahala bane irin na Daddy, ashe jira yake ya k'ara kwari ya bayyana akanshi, kariris ta kwanta ciwo dan sabida rashin kwarin jikinta sai kiran Dr Saadatu yay a waya yace tazo"

"gidan ta dubata,"

Dr Saadatu kallo daya tayi mata ta gane abinda ke faruwa amma sabida ta tabbatar yasa tayi mata gwaje

"gwaje result ya fito tana murmushi ta fad'a masa cewar ciki ne da ita na wata uku, Abbah Abbas kasa"

'boye farin cikinsa yayi godiya yake mata kamar itace ta bashi kyautar cikin kyauta yayi mata ta mussaman kamar koda yaushe.

"Najaatu ta dinga mamakin irin murnar da yake kamar wanda ba'a ta'ba yi masa haihuwa ba, a ranar yini"

"yayi tare da ita ya'ki zuwa kasuwa, sai yamma ya fita. koda yaje gidan Alhaji kasa shuru yay sai da ya"

fad'awa hajia itama ta dinga farin ciki tana addua Allah ya raba lafiya. kasancewar ranar ba girkinta

"bane yasa ya roki alfarma gurun 'yar uwarsa akan taje ta zauna da ita, Yaya Ramlatu ta shirya kayanta"

"tsaf ta tafi gidan, Najaatu taji dad'in zuwanta dama tana ta tunanin yanda za'ayi ta kwana ita kadai a"

gidan.

'Bangaran Salim da Salimat kuwa sun sake daidaita kansu a karo na biyu yanzu tsarkakken aure suke so

"suyi Salim yini yake a shagonsa na siyar da takalma da daddare kuma ya dauki a daidata sahun sa ya tafi aiki, cikin kankani lokaci ya had'a kudin aure! Mahaifinsa da d'an uwansa sune suka je har gidan su Salimat din domin nema masa a auranta a karo na biyu, Naburago da Kanin babansa su suka kar'bi kudin"

auran da sadakin kana suka tsayar da ranar daurin aure wata biyu masu zuwa.......

To duk abunda ke faruwa Zainab bata da labari Halisa ce kawai tasan Najaatu nada ciki itama bashi ne ya

"fad'a mata ba a bakin Yaya Ramlatu taji a lokacin da tazo dubata, taji takaicin abunda yayi mata meye a ciki dan ya fada mata najaatu nada a ciki ita a yanzu daga Najaatun har Zainab din bata daukesu a matsayin kishiyoyinta ba a matsayin 'kannenta ta daukesu, koda ta nuna masa b'acin ranta hakuri ya bata yace mantawa yayi, be fada mata ba, A nasa bangaran kuwa yana ganin rashin fad'ar shi yafi alkairi a gurinsa dan zai iya zuwa ya fad'a musu su mayar da abin kishi mussaman Zainab da ko maganar Najaatu bata so yayi idan yana gurinta shiyasa yake takatsantsan da al'amarin ko wacce dan baya so su dinga daukarsa a matsayin mutum mara adalci, Halisa Addua tayi akan Allah duk ya rabasu lafiya da"

abinda suke dauke dashi.

*RANAR BIKIN SALIM*

Zainab da Halisa tare suka tafi gidan bikin ko wacce tayi ado daidai misali mussaman Zainab sarkin

"kwalliya komai na jikinta mai tsada ne ta shirya 'yarta cikin 'yan kanti masu kyau, Halisa cikin atamfa super ta shirya tayi amfani da gold d'inta irin na Najaatu to da yake hijabi tasa shine dalilin daya sa Zainab bata gani ba, gabad'ayasu harsu Saddiqa direba ya daukesu a mota gidan Alhaji ake taron bikin"

kafin yamma suje suga dakin amarya.

Lokacin da suka shiga Zainab sai da ta kusa fad'uwa ganin Najaatu a hakimce akan kujera tayi wani 'bul

"'bul kana ganinta kaga mai yaron ciki fuskarta sai sheki take annuri yana sauka, tayi kyau har ta gaji tana sanye da Material pink color mai wani irin kyalli da duwatsu, tunda suka shiga falon Zainab ta kasa dauke idonta daga kanta, Uban gold din da taga ni a wuyanta shine yayi masifar tayar mata da hankali, tsabar hassada yasa taji hawaye na kokarin kufce mata, 'kasa tayi da kanta tana kokarin daidata nutsuwarta"

kada jamaar dake gurin su gane halin da take ciki.

Sai da ta daidata nutsuwarta tukkuna ta d'ago kanta tana ya'ke ta shiga gaishe da Hajia da jamaar dake

gurin Najaatu janyo hannun Ummi tayi tana mata wasa yarinyar ta bata sha'awa sosai ganin yanda

mamanta tayi mata gayu tana kaunar 'ya mace a rayuwarta. Zainab dik irin kulawar da Najaatu takeyi

"akan 'yarta hakan be burgeta ba harararta ma takeyi a fakaice k'yashi da bakin ciki duk ya cika mata zuciyarta..............Halisa kuwa da yake tayi sabo da dangin mijin nasu tana cikinsu suna ta hira Hajiya Rakiya tace"" Yanzu kuma idan an gama wannan taron sai na haihuwarki dan banyi tunanin ma zaki zo"

"taron bikin nan ba ganin yanda cikin ki ya tsufa."""

"Halisa tace"" Lallai kuwa ni kam ko na haihu babu taro sai dai ku bari idan k'anwata ta haihu sai kuyi ni na"

girma da taron suna.

"Hajia Rakiya tace""To ashe bake kadai ce mai cikin ba. Najaatu tayi saurin sunkuyar da kanta tana jin"

"kunya, Hajia Rakiya dariya tasa ganin yanda Najaatu ke sunkuyar da kanta tace""Allah to ya rabaku lafiya.....Zainab gumi ne ya shiga tsatstsafo mata lallai ma! Najaatu nada ciki ita tana zaune tabdijam! hankalinta ne ya tashi taji gabadaya zaman gidan ya isheta, daurewa kawai tayi la'asar tayi ta kalli Halisa tace""Ni ina ganin tafiya zanyi tunda kinga ni zanyi girki.'' Halisa tace ba zaki tsaya muje muga dakin"

amarya ba.

"Girzgiza kai tayi tana gyarawa 'yarta takalmi tace""Watarana naje."" Najaatu ta ri'ke hannun Ummi da"

"fad'in ""Zainab ki bani ita ta kwana biyu mana."""

"Girgiza kanta tayi babu kunya tace""Ba zan iya ba."""

"Gabadaya mutanan dake falon suka zuba mata ido da mamaki a tare dasu Ya Ramlatu tace""Kafin ki"

"haifa ita ta haifa gashin nan ma wani cikin ne da ita kije ki rike 'yarki haba jamaa ni ban ta'ba ganin mara kawaici irin wannan yarinyar ba wallahi."" Zainab tayi kwal kwal da ido tana so tayi kuka, Ya Ramlatu ta dinga farfada mata magana, hajia Rakiya ganin abun na nema ya zama rigima yasa ta dakatar da Yaya"

Ramlatu daga hayaniyar da take.

Zainab sama ta hau tayiwa Hajia sallama ta sakko babu wanda ta kula a cikinsu taja hannun 'yarta suka

fita. Abinka da taron mata tana fita kowa ya shiga fad'in albarkacin bakinsa a kanta.

"Zainab sai da taci kukanta ta koshi tukkuna ta dauki waya ta kirasa, Abbah jin yanda take sheshshekar"

"kuka yasa hankalinsa ya tashi yace.''Tayi shuru tayi masa bayanin abinda ke faruwa, 'ki tayi tace""Ita dai yazo gida bata da lafiya....Jin maganar rashin lafiyasa yasa ya bar abinda yake ya tafi gidan nasa"

A falo ya sameta ta had'a kai da gwiwa abun duniya ya isheta Najaatu nada ciki Halisa nada ciki sannan

"sun had'e mata kai sunsa gold iri daya ita bata dashi bayan nan kuma Yaya Ramlatu ta tsaneta taci mata mutunci tare da zagin iyayenta, wannan abubuwan sune suka dameta suka tsaya mata a wuya."

Da kyar ya rarrasheta ta shiga shirya masa karya da gaskiya tana kuka take fada masa Yaya Ramlatu ta

"tara Jama'a taci mata mutunci tare da zagin iyayenta akan wani dalili wanda bai taka kara ya karya ba, Abbah yaji ransa ya 'baci amma baiyi saurin yanke hukunci ba sai da yace ta fada masa dalili Tace"""

"Saboda kawai na 'kar'bi Ummi a hannun Najaatu shikkenan sai cin mutunci ya biyo baya wai nayiwa Najaatu gorin haihuwa kafin na haifa ita ta haifa gashinan zata sake haihuwar wani gabad""ayansu haka suka dinga cin mutuncina akan rashin gaskiya. Yace""Kiyi hakuri zanji dalilin daya sa suka tozarki a"

"gaban jamaa taro idan na Ramlatu ne ki daina zuwa tunda bakwa jituwa da juna ita kuma Najaatu data bada goyon bayan aciki mutuncinki zanji dalili! ni kike aure ba wani ba saboda haka taro kin daina zuwa tunda ba alkairi suke shukawa ba! Tace"" sannan kuma Naga gold aunty Halisa da Najaatu sun sa iri d'aya"

"ni ina nawa."""

Gabansa ne ya fad'i! kai Zainab rigimammiya ce tabbas gold din nan ne da Najaatu ta siyo musu lokacin

"da sukaje umara ta gani, domin ya wanke kansa daga zarginta yace""Najaatu ce ta daukar musu su biyu kema zan baki kudi kwatankwacin na gold din ki siya."" Tana kuka tace""Ni wallahi irin nasu nake so me yasa bakya ce ta d'aukar min ba kaga irin rashin adalcin naka ko wannan uban gold din"

"ai bai zama lallai a samu irinsa anan ba."" Yace.""To shikkenan ki bari idan munje tare sai ki siya dama"

"farkon azimi nake so na sake tafiya zamuje tare insha Allah."" Shuru tayi tana goge fuska yace""Ina fata dai babu wanda kikayi wa rashin kunya acikin mutanan dake gurin."""

"""Babu wanda nayi wa magana ai ganin sun had'e min kai suna cin mutuncina yasa nacewa aunt Halisa"

"zan dawo gida."" Yace.""Ita Halisan tana zaune ake zagin ki ba tayi magana ba.""?"

"""Eh ba tace komai ba har na fito daga gidan."" Abbah ya jima kansa a kasa yana nazarin al'amarin tabbas"

idan yay binkice ya tabbatar da gaskiya lamari to babu shakka Halisa da Najaatu sai sun raina kansu wato har dasu za'a hadu a ciwa matarsa mutunci ya rasa me yasa tsakanin Yaya Ramlatu da Zainab basa shiri A ranar beje gidan ba saboda yasan cike yake da jamaa zamansa yay tare da Zainab din tana

ta kalallameshi da kalamai sai 'kara rura wutar al'amarin take. Bayan ya dawo daga sallar ishai gurin

"Halisa ya wuce yaga bata dawo ba, rai a bace ya kirata a waya lokacin suna gidan Salim suna kar'bar amarya tunda sune iyaye.'' Hayaniya yasa ta fita daga cikin Jamaa ko kafin tace komai taji yana magana a fusace! Tace""Yi hakuri Abban Mufida na rana d'aya dai ai ka d'aga mana k'afa yanzu haka ma muna gidan amarya nida Najaatu."" Yace.""Dole sai daku za'a kar'bi amaryar kinfi kowa sanin bana son kuyi dare a waje sabida haka dake da ita Najaatu ina son ganinku a gida dan tun la'asar na dawo naji kuma"

"dukkanin irin rashin arzikin da kukayi."""

"Halisa na kokarin tayi magana ya katseta da fadin""Ina jiranku yanzu yanzu."" Kashe

76 / 79