Chapter 19 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 79

54K to 57K   out of 235.1K words

na shigo unguwar."" ""Okey."" Yace ya kashe wayarsa ya maida hankalinsa gurun abincin dake gabansa..."

Halisa ce ta fito daga daki tana wani salo-salo idanunta sunyi jawur! zama tayi kusa da kujerar Saddiqa ta

"dafa kanta cikin kissa tace""Sannu da aiki Saddiqa ."" A dan tsorace ta amsa da ""Yawwa Mommy."" Kallonta yayi yace.""Zamu fita tare yanzu za muje hospital mafi kusa a dubaki dan bana son zama da lalura."" Ta sake marairaicewa da fadin ""Wallahi ba kaji yanda nake jin jiki ba gashi yarinyar nan ta 'kara mun wani"

"'bacin ran."""

"Yace.""Ai laifin ki ne tunda kin san halinta me yasa zaki biye mata kuyi ta cacar baki a gaban yara duk"

"ranar data zage ki a gaban yaran nan mutunci ki ya zube wallahi gwara ki kama kanki."""

"Da sauri tace""Dan Allah ka bar wannan maganar da kake kamar baka san halinta ba kafin na fad'i d'aya"

"ta fad'a min goma ni wallahi ban shiga kicin din da wata manufa kawai dai ta raina ni ne shiyasa bata ganin girmana amma yanzu na yanke hukunci kawai ta bar min gidana shi yafi amfani idan kuma lallai a gidan nan zata zauna to a gyara mata d'aya side din taje can ta 'karata."""

"Yace.""Sai an kwana biyu tukkuna abinda dai nake so dake anan shine ki cigaba da hakuri kuma kina"

"kokarin ri'ke girmanki idan kin kama mutuncinki na tabbata komai rashin kunyarta ba zata zage ki ba. Halisa shuru tayi tana jijjiga 'kafafunta, Saddiqa ce ta had'a mata tea ta zuba mata soyayya doya da"

"wainar 'kawai akai tace ""Mommy gashi kiyi break ."" Cikin ya'ke tace""Nagode Saddiqa Allah yayi muku"

"albarka."" Duka suka amsa da amin harda shi,"

"Salim ne yayi sallama ya shigo hannunsa rike da key na mota, Yaran ne duk suka mike suna gyara zaman"

"jakar makarantarsu, Salim ya shiga rarraba ido a palon Naja'atu kawai yake so yayi tozali da ita, da bai ganta ba sai ya nufi dannig area d'in yana wani shafa kansa kai daka ganinsa kaga munafiki Hannu ya"

"mikawa Abba Abbas suka gaisawa yana wani risinawa kamar mutumin kirki! Ya gaishe da Halisa, tana"

washe baki ta amsa tana tambayarsa Yaya Ramlatu.

"Abba Abbas ya mike hade da daukar wayoyinsa dake kan teble din, ya kalli Salim da fad'in ""Ka kai yara"

"skullu daga bisani sai ka biyo ni kasuwar daga baya zamuje hospital da Halisa bata jin dadi."" Salim yace.""Ayya Sannu Big Aunty ashe ba kiji dadi ba Allah ya sawwak'e yasa kaffara ne."" Halisa ta mi'ke tana"

"dan ya mutsa fuska tace""Wallahi kuwa "" ameen ya rabbi idan ka koma gida ka gaishe min da Yaya."" Ya"

"amsa da za taji insha Allahu.........Gabadaya suka fita harabar gidan yaran suka nufi motarsu ta makaranta, shi kuma Salim din ya dan tsaya suna magana da Abba Abbas din kafin yaje ya shiga motar da sauri yaja motar ya fita daga gidan, Halisa ta kame a gidan gaba tana jira ya shigo kawai sai taga ya juya da nufin komawa cikin gidan, cike da mamaki take kallonsa, to me zai komar dashi kuma! 'kwafa tayi ranta ya 'baci babu shakka gurin yarinyar zaije, mtsssw! an girma kamar ba a girma ba a dinga abu irin na yara abinda ta fada kenan a fili tana jan tsaki!. Ganinshi zai dawo cikin gidan yasa tayi saurin"

"sakin labulan window din data la'be tana le'kensu, da sauri ta nufi toilet ta kulle kofa. Kai tsaye daya"

"shigo d'akinsu Saddiqa ya nufa saboda yasan tana ciki Koda bai ganta a dakin ba, sai yayi tunanin tana"

"toilet, ya karasa bakin toilet din yana k'wank'wasawa! da kiran sunanta, tana jinsa tayi masa shuru mugun haushinsa take ji shiyasa ma bata so ta kalli fuskarsa, Abbah Abbas haka ya 'karaci buga kofar toilet din ya hakura, dan ya kai minti goma sha biyar yana tsaye yana aikin buga kofa da kiran sunanta bata saurareshi ba, ransa a 'bace ya fita daga dakin Halisa kuwa cika tayi tai fam! ta dinga hura hanci"

"takaici da bakin ciki kamar su kasheta, haka ita dashi sukayi tafiyar kowa ransa a 'bace!"

*Littafin na kudi ne! Koda zaki ganshi a gruops to na sata ne idan kina so ki biya kudin littafin to ga yanda

abin yake. *

VIP #600

Normal #300

Accont:0542382124...Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min magana ta whasap da

wannan numbar

07084653262

*BINTA UMAR ABBALE*

BHRBN

*24*

"Tana jin fitarsa daga dakin ta fito daga toilet din, zama tayi k'asan kafet ta had'a kai da gwiwa abin"

"duniya duk ya isheta, ta kai minti ashirin a zaune tana sa'kawa da kwancewa kafin ta yanke shawarar mi'kewa ta dauki hijabinta tasa, hanyar fita ta nufa, Gidan Abbah Magaji za taje dan ba za tayi zaman kad'aici ba gabadaya gidan girma yayi mata ta dinga jin tsoro na shigarta. Koda maigadi yaga zata fita"

baice mata komai ba dan shine ma ya bude mata karamar kofa ta fita yana yi mata adawo lafiya. Tana

"kokarin shiga gidan Abbah Magaji Salim ya shigo da mota, tsayawa tayi har yayi parking ya le'ko da kansa yana d'aga mata hannu wai taje, dama sabida ita ya dawo gidan bayan ya ajiye yara a skull, cikin zumudi gami da farin cikin ganinsa ta nufi inda motar take, Ya bude mata ta shiga ta zauna kusa dashi"

"tana fara'a da fadin ""Wallahi naji dadin ganinka."""

"Ya saki wani murmushi yana shafa sumarsa hade da yi mata shegen kallonsa yace.""Na shigo gidan tun"

"dazu ina ta rarraba ido banga sanyin idaniya taba, shiyasa na kasa wucewa kasuwa kamar yanda mijinki ya bukata nace sai na dawo nayi tozali dake."" Tana murmushi tace""Ina dakin su Saddiqa ban san kazo gidan ba."""

"Yace.""Ina fatan dai wani abu bai shiga tsakaninki da wannan dattijon ba."" Gabanta ne ya fadi ta kalleshi a"

"sanyaye tace""Babu wani abu da ya shiga tsakaninmu ai nayi maka al'kawarin kai zan mallakawa kaina."" munafikin murmushi yayi yace.""Nagode Princess yanzu inaso ki d'an yi min abinda zai d'ebi min kewarki idan naje kasuwa."" Tace""Ban gane abinda kake nufi ba."" Kallon kasan ido yayi mata yace.""Haba baby sai nayi miki bayani dalla-dallah ashe har kin manta hirarmu ta jiya da irin amsar da kika bani, yanzu fa kika gama cewa jikin ki da komai naki nawa ne to inaso ki d'an fara gwada min soyayyar da kikeyi min a zahiri."" Cike da mamaki take kallonsa dan ta fahimci inda maganar sa ta dosa, shuru tayi ta kasa magana, kawai taji ya kama hannunta ya rike yana shafawa, Da sauri ta cire tana d'an hararasa tace""Idan sai na rungume ka ko nayi maka kiss sannan zaka gane kaunar da nake maka gaskiya ce, to kuwa sai dai kada ka yarda dani da son da nake maka koda nake cewa komai nawa naka ne ai ba ina nufin mu aikata haramci ba inaso bayan na rabu da wannan 'kaddararran auran muyi aure da kai mu mori junanmu shine abinda nake nufi."" 'Bata fuska yayi yace.""Dan kiyi kissing d'ina ko kin rungume ni ai ba wani abu bane amma tunda kince haka shikkenan."" Cikin rashin walwala ya 'karasa maganar, Tace''Gaskiya kayi hakuri ba zan iya ba."" Cikin fusata yace.""Okey fita a motar nan na tafi inda zani dama duk karya ce ba wani sona"

"kike ba da kina sona ba zaki tsaya jayayya dani ba."""

"Ganin ya fusata! yasa jikinta yayi sanyi murya na rawa tace""Dan Allah kayi hakuri ka gane abinda nake"

"nufi bana so ranka ya 'baci.""! Yaja tsaki mai tsayi da fad'in ""Bacin rai kuma wane iri ai raina ya gama 'baci dake."""

"Tace.""To kayi hakuri my love kada kayi fushi dani zuciyata zata shiga wani yanayi mutukar kana fushi da"

"ita."""

"Ta'be bakinsa yayi yace!.""Ai kin bani mamaki wallahi amma babu komai ina ganin zan hakura dake na"

"fara duba 'yan matan da suke sona sai na fitar da gwanata a cikinsu."" Jin ya fad'i haka sai hankalinta ya"

"tashi murya na rawa tace""Dan Allah kada kayi min haka my Prince. "" Fuskarsa ya mi'ka mata da fadin"" Okey oya kiss me idan kina sona."""

Ta dinga dawurwura kafin ta kai bakinta fuskarsa ta manna masa kissi da sauri ta cire bakinta tana jin

"nauyi da kunyar abinda tayi, murmushi yayi yana shafa gurin da tayi masa kiss din ya kalleta yana wani lumshe idonsa yace.""Allah ya nuna min ranar da zan had'a bakina da naki ina mutukar so naji ina tsotsar wannan lips din naki masu kyau da daukar hankali."" Yana kokarin kai hannusa kan le'bunanta yake maganar, ba ta bari ya kai hannunsa fuskarta ba ta bude motar da sauri ta fita daga ciki gabanta sai faduwa yake Salim ya kalleta cike da mamaki! kamar xaiyi magana kuma sai yayi murmushi yana"

"girgiza kansa ya kunna motar had'e da daga mata hannu da fadin ""Zan kira ki a waya idan anjima akwai"

"labarai masu dadi ina so ki tanadi amsar da zaki bani."""

"Hannunta ta d'aga masa tana ya'ke tace""To shikkenan sai na jika."" Motar yaja ya bar gurin ita kuma da"

sauri ta nufi gidan Abba Magaji tana waiwayen bayanta kamar wata mara gaskiya. Salim yana

"draving yana duba wayarsa yana sakin wani shegen murmushi ashe lokacin da take kiss d'insa ya saita camera......Hoton ya fita sosai kamar dama da son ranta hakan ya kasance fuskarsa da murmushi itama tata fuskarsa a sake duk wanda yaga hoton zai fahimci cewar masoya ne, ba tare da 'bata lokaci ba ya d'ora hoton a fuskar wayarsa domin yana so Allah ya nunawa Kawun nasa hoton ya gani yasan dole"

ransa zai 'baci ! idan ya tambaye shi shi kuma yana da amsar da zai bashi.

"Aunty Maryam na zaune a palo ita kadai yaran duk sun tafi makaranta kawai taji sallamar Naja'atun,"

"cike da mamaki take kallonta har ta 'karaso inda take ta zauna kujerar kusa da ita tana gaisheta, Aunty Maryam ta amsa mata cike da kulawa tace""Naja'atu me ya fito dake ina fatan dai lafiya."""

"Murya na rawa tace""Lafiya lau Anty gidan ne shuru su Saddiqa sun tafi skull Anty Halisa da Abba sun fita"

"a tare ni kuma tsoron gidan nake."""

"Anty Maryam tace""Ayya ai sai a hankali zaki saba ina fatan maigidan ya san zaki zo nan."""

Shuru tayi tana wasa da hannunta.

"Anty Maryam tace""Be sani ba kenan naga kinyi shuru."""

"Tace""Ai na dauka babu wani abu dan nazo tunda koda can muna zuwa da Yaya Halimatu."" Anty Maryam"

"tace''Eh duk da haka dai yana da kyau ya san zaki zo itama marigayi ya kafin ta fita zuwa wani guri ai tana fad'a masa ko baki san yanzu haka mala'iku na tsine miki ba."""

"A sanyaye tace""Na sani anty."" Tace""To amma kin sani kika take.""! Shuru tayi dan bata da abinda zata ce,"

"Anty Maryam tace""Yanzu ki kira wayarsa ki fada masa gaki anan gidan nasan ba zaiyi fad'a ba."" zum'bura baki tayi gaskiya ba tajin zata iya kiran wayarsa dan ba 'karamin haushinsa take ji ba."

"Anty Maryam tace""Dake nake magana fa kodai har yanzu baki saduda kin kar'bi auran ba."" Fashewa tayi"

"da kuka tace""Dan Allah anty ki kyaleni ni bazan kira wayarsa ba saboda bashi da adalci.'' Cike da mamaki antyn take kallonta tace""To ikon Allah wane iri rashin adalci yayi miki kuma.""?"

"Hawaye ta goge tace""Anty duk da bana sonsa da auransa ya dace ya bawa Anty Halisa ta had'a min lefe"

baki ga banzayen kayan data siyo min ba kuma wallahi nasan tana sane tayi haka dan ta bani haushi! sannan kuma d'azu tazo tana zagina harda dukana a baki a maimakon ya tambayi ba'asi kawai sai ya

"dauki laifi ya d'ora mun."""

"Anty Maryam tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas komai akace Halisa ta aikata ba zata musa ba"

"saboda dama tasan halinta, Halimatu tasha wahala a hannunta, dalili kenan da ya sanya basa shiri da juna da ita gasu dai ma'kota kuma mazajensu abokan juna ne amma kowa sabgarsa yake a tsakaninsu babu jituwa ko ta kwabo Cikin rarrashi tace""Kiyi hakuri da Halisa nasan dai kin san hakurin da"

"Marigayiya tayi da ita to kema inaso ki kwatanta ko kifi nat. ""Gaskiya anty ba zan iya ba wallahi.'' Ta"

katse tun kafin ta 'karasa maganar.

"Anty Maryam tace""Ke me yasa bakya tsawa a baki shawara ne? Halisa bata da kirki macace muguwa mai"

"shegen kissar tsiya babbar macace ma ya ta iya da Halisa ballanta na ke! ki tsaya ki saurare ni da kyau! yanzu fushi ke ba naki bane! kamata yayi lokacin da yake fadan sai ki bashi hakuri ki fad'a masa yanda abun yake ba kiyi zuciya ba, kinga yanzu ita bukatarta ta biya ta had'aku fad'a sun ma fita unguwa tare dashi babu abinda ya dameta, to gobe ma haka zata sake miki ke kuma gaki mara wayo sai kiyi fushi ki"

"tsaya girman kai ke ba zaki bada hakuri ba to ba haka ake zamantakewa ba."""

"Tana kuka tace""Anty nayi yunkurin fad'a masa abinda ya faru ya'ki saurarata shiyasa nima na bashi guri."""

"Anty Maryam tace""Yanzu dai magana ta wuce kodan gaba kada ki sake aikata hakan idan wani abun ya shiga tsakaninki da Halisa yazo yana miki fada ki bari ya gama tukkuna sai ki fada masa abinda ya faru"

"kada ki sake bar masa gurin bai dace ba."""

"Cike da mamaki take kallonta tace""Anty sai na zauna kawai ya dinga yi mun fada alhalin ba laifina bane."""

"Anty Maryam tace""To meye yau da gobe da kansa zai gane gaskiya dan me yasa Halimatu ta ciri tuta a gurinsa nasan har ya mutu ba zai mance da ita ba saboda tayi masa ladabi da biyayya."""

Girgixa kanta ta shigayi gaskiya da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Halimatu daban Naja'atu

daban kowa da Halinsa. murya na rawa

"Tace""Anty Maryam wallahi Allah shine d'aya har yanxu bana jin son mutumin nan a cikin zuciyata to ya"

"za'ayi na iya zaman gidansa."" Anty Maryam tace""A hankali zaki ji sonsa na shiga zuciyarki ballantana Alhaji Abbas yayi duk macan da zata ganshi zata so ya zama mallakinta ke na fahimci tsufansa ne bakya so kuma ke kike abunki 'yan mata nawa ne suke neman irinshi su aura 'yan matan da suka fiki kyau da"

"komai ma gasu nan suna yawo a gari amma ke kin samu kina wasa da damarki."""

Shuru tayi tana nazarin maganar anty maryam din itafa sam ba taga wani abun rubibi a gurin dattijo irin

"wannnan ba, kawai mace idan tana so ta more rayuwarta to ta auri dai-dai da ita amma auran tsoho a"

"ganinta duk tauyewa rayuwa hakkine. Anty Maryam tace ""Ki kirashi a waya ki fada masa bana so ya"

samu labarin kina zuwa gidan nan yayi miki fada kinga nima zaiga laifina da nake barin ki kina zama.

"Wayar ta dauka ta nemo numbar tashi, dan dai kawai anty maryam din ta dage ne amma da wallahi ba"

zata fada masa ba. Wayar tashi na hannu Salim dan haka da yaga kiran Naja'atun sai ya katse!

"ya'ki kai masa, Naja'atu ta sake kiran wayar a karo na biyu Salim ya'ki dagawa wayar tayi ta ringing har ta"

"katse!! Ta kalli anty Maryam din tace"" Ya'ki dagawa."" Anty Maryam tace""Watakila yana tare da mutane anjima sai ki sake kiransa."""

Dan ta'be bakinta tayi ta shiga whasap tana dubawa. Anty Maryam mikewa tayi ta nufi kicin tana

"mamakin 'kuruciyar yarinyar yanzu meye abin gudu a dangane da auran ta da Abokin mijin nata, babu shakka kuruciya ce ke damunta kuma idan Halisa ta gane akwai rashin jituwa a tsakaninsu to ita kuma tabbas ta samu hanyar da zata cigaba da shiga tsakaninsu."

"Sai bayan sun fito daga sallahar azahur ne ya samu sararin 'kar'bar wayoyinsa dake hannun Salim, ya"

"zauna gurin zamanshi yana duba wayar, a lokacin yaga miss call din Naja'atun, da sauri ya shiga kiran wayar yana fatan Allah yasa lafiya dan baiyi tsammanin kiran wayarta ba, Lokacin da yake kiran wayar ita kuma tana bedroom din anti maryam tana sallah, Anti Maryam ta daga wayar a nutse tayi masa sallama. Jin muryar anty maryam yasa shi mamaki yace.""Maryam ce ko.""? Tace""Eh wallahi nice ai"

muna tare da Naja'atu tun safe ta shigo tace kunje unguwa yara kuma sun tafi skull wai tana jin tsoron

"zaman gidan shine nace ta kira wayarka ta fada maka to kuma ta kira baka samu dagawa ba."""

"Ajiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyarsa yace.""Wayar bata hannuna a lokacin okey babu"

damuwa bayan sallahr la'asar sai kisa ta ta koma gida tunda ina tsammanin ma yanzu Halisa ta dawo dan dama asibiti na ajiyeta na wuce kasuwa. amma tunda tana son zama dake idan anyi la'asar kisa ta ta

koma gida.

"Anty maryam tace""To insha Allah."" Sallama sukayi anty maryam ta juyo tana kallonta tace''Kinji ashe"

"lokacin da kika kira wayar bata hannunsa, yace babu komai idan kinyi sallah la'asar sai ki koma gidan."""

"zama tayi kusa da ita ba tare da tace komai ba, anty Maryam ta mike tare da fadin ""Bari na kawo mana"

"abinci muci akwai wasu abubuwa da zan baki idan kika mayar da hankali zasu taimake ki."" kicin ta nufa, Naja'atu ta bita da kallo tana tunanin wane abubuwa ne zasu taimaketa."

Halisa kuwa bayan ta gama ganin likita gidansu ta wuce kuma sai da ya gargade ta kan lallai data gama

da asibiti ta koma gida amma saboda ita mai kunnan 'kashi ce ta tafi gidansu......Sai da tayi sallahar la'asar sannan tayi sallama da mahaifiyarta

Anty maryam ta fito daga bedroom dinta hannunta rike da bakar leda guda biyu ta zauna kusa da

"Naja'atun tana bud'ewa ta kalleta a nutse tace"" Wannan garin magani ne na mata mai kyau nice ma na had'a abina da kaina idan kin koma gida ki d'ebi cokali biyu kisa madara da ruwa kisha haka zaki dinga yi kullam, maganin zai taimaka miki Wannan kuma gumba ce itama kisa mata madara ki dama sai kisha,"

"duk da cewar ke amarya ce amma hausawa nacewa idan kana da kyau ka 'kara da wanka, idan kinga"

amfanin maganin nasan zaki sake nemansu a gurina.

"'Karba tayi ba dan za

19 / 79