Chapter 53 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   53 / 79

156K to 159K   out of 235.1K words

ya 'kurawa number ido, wayarsa babba ce sosai shiyasa daga ko wane gari ko wace qasa aka kirashi sai ta nuna masa, ganin number daga garin jos ne yasa ya d'an shiga mamaki! Sai kawai ya tsinci kansa da kiran wayar...Lokacin Dr har ya kar'bi wayarsa zai fita kiran ya shigo, da sauri ya dawo da baya ya miqa mata wayar. Rai a"

"'bace! ta daga wayar ta kara a kunnanta tace""Ke! dallah malama! ki bawa mai wayar abarsa mana wai ke"

"amarya sai hauka kikewa mutane mtssw! ki bawa mai waya wayarsa zanyi magana dashi."""

Muryarta ta dinga dukan kunnansa yayi shuru yana sauraranta har sai da ta gama hayaniyar sannan yayi

"gyaran murya a nutse ya kira sunanta. *""Naja'atu!!!*"

"Wani irin yarrr! taji tun daga saman kanta har i zuwa tafin 'kafarta a sanyaye tace""Na'am Abbah Ina"

"wuni.""? Ajiyar zuciya ya sauke da fad'in ""Lafiya lau ya kike ya maigidanki."" ? Ya nuna kamar bai san abinda ke faruwa ba."

"Kuka tasa masa tace""Abbah bani da lafiya gani a kwance a gadon asibiti likita na bukatar kudi bani dashi"

"bani da wanda zai biya min shine na kira ka ko zaka taimaka min kamar yanda Allah yake taimaka maka."" Jin maganar rashin lafiya yasa ya mayar da abin serious yace.""Baki da lafiya Baki da wanda zai biya miki kudin magani ina mijinki yake.""? Tana kuka tace""Ya sake ni ai.""? Shuru yayi dama abinda yake so kenan yaji daga gareta...Yace.""Yanzu kina ina.""? Cikin shashshekar kuka tace""Ina tare da wata mata mai kirki tana taimakona."" Girgiza kansa yayi yace""To Allah ya sawwaqe! Bani Likitan zamuyi magana dashi."" Tayi saurin miqawa Dr din wayar. Tana jinsu suna magana da Dr din yana tambayarsa abinda ke damunta"

Dr yayi masa cikakken bayani sannan ya fad'a masa kudin da ake buqata. Yace Yanzu ya tura masa

"account number nasa zai sa masa kudin Sallama sukayi da juna Dr ya kallesu a nutse yace.""To"

"alhmdullhi zaku iya tafiya yanzu."" Mmn Sajida da Mmn Ladi sukace ""To mungode."" Da sauri Dr ya fita daga dakin su kuma suka shiga shirye shiryen tafiya gida......"

*_Allah yasa cikin ya zube Aunty Binta ci kuma!!! dan Allah kada ta haihu da Bash Aunty Binta

wannan pege d'in ya bani haushi Wato kuna so rabo ya kashe ni ko? To Yanda Allah ya saukar

da ikonsa a kan Naja'atu nima 'yar kallo da addua ce........Alhamdullhi saqona na cikin littafin nan ya

"soma isa, ha'kika wani baya ta'ba haihuwar d'an wani Allah ya qaddarta akwai rabo mai zafi a tsakanin Bash da Naja'atu shiyasa suka rabu da Abbah Abbas cikin 'kan'kani lokaci ta auri Bash shima suka rabu"

"cin 'kan'kanin lokaci bayan ya saukar da ikonsa a kansu, babu wani wanda yasan gaibu sai Allah *"

*Littafin na kudi ne. !*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip group

#600 normal group #300 account....0542382124....Binta umar gtbank. Idan katin waya zaki tura kiyi

min mgn ta whasap da wannan number.

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

"****61 Abbah Abbas shuru yayi da wayar a hannunsa yana tunanin maganar da dr ya fad'a masa,"

"Naja'atu na dauke da cikin wannan lalataccen yaron! hakika wannan al'amarin ya tsaya masa a rai mutuka, ba wai yana kishi ne da faruwar hakan ba yasan Allah ba yanda baya tsara al'amarinsa, yarinyar kawai yake tausayawa had'uwar jininsu da yaron da duniya tasan mutumin banza ne, koda yake Ubangiji kan saukar da shiriya akan bayinsa a lokacin da yaso, wannan dalilin ya sanya yaji zuciyarsa tayi sanyi sai kawai yayi addua a kam Allah ya shiryi Bash din ita kuma Naja'atun Allah ya sauketa lafiya ya sanya rabuwar auranta da Bash din shine alkairi Zainab kuwa kunya ce ta isheta tana jin tsoron kada ya"

"tuhumeta a kan me yasa tayi masa karya bayan ta gane Naja'atu ce ta kira wayarsa, sai taga gabad'aya"

ma hankalinsa da tunaninsa bayan kanta yana can wani tunani na daban.

"Sai goma shaura na dare suka isa gida, Mmn Ladi kai tsaye gidanta ta wuce saboda tasan mijinta ya"

"dawo kuma bata fad'a masa zata fita ba tunda bata da waya, yanzu babu laifi sun shirya sun daina fada sosai duk a sakamakon nasihar da Naja'atu tayi mata. Mmn Sajida ganin mutane sun cika rumfar"

"kwanon siyar da abincinta yasa ta sallamesu da fadin yau babu abinci sai gobe idan Allah ya nufa. Dantalle ya nufo inda suke ya sha shaddarsa 'yar rini hannunsa rike da mukkulin lifan d'insa,"

"yana washe baki yace.""Mmn Sajida dama wannan qanwar taki tana nan.""? Mmn Sajida tace""Eh tana nan Dantalle ya gida ya iyali.""? Ya amsa idanunsa a tsaye a kan Naja'atu."" Yace."" 'Yan mata ya kike ya gari ya jin dadi.""? Naja'atu duk da halin ciwon da take ciki sai da ya bata dariya, wai shi dole sai ya burgeta ta lura mutumin yana so ya wuce gona da iri Tace""Lafiya lau jin dadi na gurinku.""' Dantalle dadi ya isheshi"

"ya kalli Mmn Sajida yace yau babu abinci naga alamar ma kamar daga unguwa kuka dawo ko.""? Mmn"

"sajida tace wallahi kuwa munje wani guri ne."" Yace.""To bbu laifi bari naje na dawo kada ku rufe gida da"

"wuri."" Mmn Sajida tace""To shikkenan."" Ya juya da sauri ya nufi inda lifan dinsa yake Su kuma suka"

"shiga gidan Mmn Sajida na fad'in ""Wahalalle kawai ya fito ya bar iyalinsa yana biye biyen gidajen abinci gabad'aya Dantalle baiyi ba wallahi."" Naja'atu murmushi tayi tace.""Ni kam gani nayi ma kamar sonki yake."" Mmn Sajida na kokarin bude dakinta tace""Ai ko maza sun kare a duniya ba zan auri dantalle ba"

"Gwara nayi ta zama a haka."""

Walid da Sajida tuntuni sunyi bacci da yake Walid nada wayo shine yayi musu shimfida ya daura musu

"net suka kwanta, ita kuma Mmn Sajida kicin ta nufa da sauri da yake tana da karamin gas sai ta fara kokarin d'ora ruwa ta dafa musu indomee sai kawai sukaji sallamar Dantalle daga waje Mmn Sajida"

"tace""Naja'atu gashi can ya dawo ko zaki 'kokarta kije kiji dame yazo.'' Naja'atu tace""Rabani da wannan guy Mmn Sajida ki daure dai kije kada yace an masa wulakanci."" Mmn Sajida ta dauki mayafinta ta fita. Minti biyar sai gata ta shigo hannunta rike da manya manyan ledoji Dantalle yaje ya kashe musu"

"kudi gurin siyayyar kayan ciye ciye gami da kayan masarufi."" Sosai Naja'atu ta dinga mamakin siyayyar tafi ta dubu biyar haka kawai bai ka gidansa ba yazo yana bawa duniya kai Allah ya shiryi mazan dakewa iyalinsu mugunta suna bayarwa a waje Mmn Sajida tace""Kadan kika gani in dai Dantalle ne kuma"

wannan hidimar da yake yi da biyu yake wallahi ko shakka bana yi saboda dake yake yi.

Naja'atu ta shiga girgiza kanta tana mamakin al'amarin wasu mazan........To Sai da suka zo kwanciya

"Mmn Sajida take tambayarta dazu da wa tayi a waya a asibiti...Naja'atu kai tsaye tace mahaifinta ne anan Mmn Sajida tace na fada miki dama suma iyayen naki suna can hankalinsu a tashe dan Allah kiyi hakuri ki koma garesu ko kya samu nutsuwar zuciyarki idan kina zaune a gurina lalattatun maza irinsu Dantalle zasuyi ta kawo miki farmaki."" Tace""Mmn Sajida insha Allah zan tafi gida amma sai jikina ya warware tukkuna."" Mmn Sajida tace to Ubangiji Allah ya baki lafiya mai amfani kuma ya rabaki da abinda"

"ke cikin ki lafiya."""

Bayan wata biyu cikin Naja'atu yayi wata hudu da 'yan kwanaki A lokacin ne Allah ya azurta Zainab da

"samun nata cikin, murna a gurinta tamkar me! shima Abbah Abbas din sosai ya nuna farin cikinsa a kan karuwar daya samu, ya shiga lalla'bata gami da nuna mata so da kulawa, yarinyar ta samu sake sosai sai abinda take so takeyi a gidan Halisa ta sake shiga cikin wani irin hali na tashin hankali da damuwa dan"

duk irin kokarin sauke hakkinta da maigidan yake yi gani take kamar baya adalci a tsakaninsu tana gani tamkar yafi fifita Zainab din a kanta lokaci guda tayi wata iriyar rama mara kyawun gani Zainab mai

"wayo gami da so ta siye zuciyar mijinta ai tuni ta janye yaran sun koma bangaranta yanzu komai nasu na gurinta haka take kulawa dasu gami da sanyasu farin ciki, tuni yaran suka manta da wata Naja'atu saboda sun samu wacce ta maye musu gurbinta sai dai sa'i da lokaci Mussadiq yana tunawa da ita. Ranar wata Alhamis da yamma Yaya Ramlatu ta dira a gidan, kai tsaye bangaran Halisa ta nufa, ta"

"zauna suna gaisawa! Halisa tace""Yaya Ramlatu sai yau aka tuna dani.""? Ta'be bakinta tayi tace""Halisa"

kenan ai lamarin ki ne yake bani haushi wallahi dubeki dan Allah duk kin lalace yarinya qarama tazo ta

"kwace miki miji da gida da yara kin kyaleta ba zaki dauki mataki ba."""

"Halisa tayi shuru tana nazarin maganar Tace""Yaya kenan ni yanzu ba tashin hankali ne a gabana ba"

"ingantuwar lafiyata kawai nake bukata.'' Ramaltu ta ta'be bakinta tace"" ai shikkenan tunda kin mayar da kanki sususu!! ni kinga tafiyata."" Sai kawai ta miqe ta kama hanya ta futa."

"Tana fitowa ta durfafi bangaran Zainab, lokacin suna zaune ita da yara a palo suna kallo suna wasa da"

dariya! Kawai sai ganin mace tayi ta shigo mata babu sallama. Yaran duk sukayi tsuru-tsuru murya na

rawa suka shiga gaisheta! Ramlatu ta samu guri ta zauna tana muzurai sai bin palon da kallo take tana watsawa Zainab kallon banza. Zainab dama a ciki take da matar domin ta tsani d'abiar da take mata

kamar ba babba ba sai ta dinga shigo mata babu sallama...sai kawai ta dauke kanta taqi kallonta

ballantana ma ta gaisheta.

"Yaya Ramlatu ta fusata! sosai ! tace""Ke baki san matsayina bane da ba zaki gaisheni ki bani girma ba.""?"

"Wani irin kallo Zainab tayi mata tace""Nasan matsayin ki mana kina so nayi miki sujjada ne.""?"

"Ya Ramlatu tace""Ko baki yi min sujjada ba ai sai ki mutuntani a matsayina na yayar mijinki."" Zainab ta"

"ta'be bakinta tare da dauke kanta. Wannan abun da tayi ya fusata Yaya Ramlatu mutuka, sai kawai ta"

"shiga zaginta tana fad'in ""Ita bata daukar raini wallahi idan tace rashin kunya za tayi mata sai taci mutuncinta."

"Zainab tace""Kinga dan Allah ki tashi ki fice min a gida ni ban gayyatoki ba haka kawai kizo kina min"

"masifa me nayi miki kike zagin iyayena to bari kiji ni ba Naja'atu da kuka raina bace nasan daraja da mutuncin iyayena."" Ya Ramlatu ta miqe ta iska inda take tana zaginta hade da dungure mata kai tace.""Za kici ubanki zanyi maganin Kafin ta qarasa yarinyar ta miqe a fusace! ta wanke ta da mari!"

"Tace""Wallahi ba zanji kunyar cin mutuncinki ba mutukar zaki ta'ba martabar iyayena."

Yaya Ramltu ta dafe kumatunta jikinta na wani irin tsuma mamaki da al'ajabi kamar ya kasheta 'yar

qaramar yarinya da bata wuce jikarta ba itace ta mareta! Sai kawai ta rufe ta da duka ta ko'ina! Zainab ta dinga ihu! tana kokarin kwatar kanta Ramlatu ta haye kanta sai jibga take. A kid'ime! Saddiqa taje ta

"fad'awa Halisa halin da ake ciki sai gata sun shigo ita da Baba Larai! gabadayansu sun firgita da ganin duk da Ramlatu takewa Zainab! da kyar suka janyeta sai haki take tana fad'in ""Tunda take a duniya babu"

wanda ya ta'ba marinta sai yarinyar na saboda haka sai ta dauki tsatstsauran mataki a kanta. Baba Larai

ta bude bakinta za tayi magana ta buga mata tsawa da fadin tayi mata shuru bata son munuafurci. Yafan

mayafinta ta gyara ta dauki jakarta ta kama hanyar fita sai zage zage take...

Halisa ma juyawa tayi ta nufi gurinta uffan ba tace ba dama itama haushin zainab din take ji shiyasa taji

dadin dukan da Ramlatu tayi mata

Baba Larai ta taimaka mata ta tashi zaune tana kuka kamar ranta zai fita Baba larai ta rarrasheta gami da

"yi mata nasiha akan ta zauna lafiya sannan ta fita daga sabgar Ramlatu tunda ba mutunci ne da ita ba, Zainab jinta kawai takeyi saboda haka tana fita ta dauki wayarta ta kira mijinta tana wani irin kuka ta shiga zayyane masa abinda ke faruwa tace tana kwance ta kasa tashi cikinta sai ciwo yake. Wannan"

"al'amarin ya daga masa hankali sosai ashe Ramlatu ba zata kyaleshi ya huta ba! Dama yana jin haushin abinda tayi masa a kan Halisa kawai ya kyaleta ne, to yanzu kuma shine taje har gidansa ta daki matarsa da 'karamin ciki a jikinta wannan karan zai dauki mataki a kanta. Kasuwar ya bari ya nufi gidan, ya dauki"

"Zainab sukaje asibiti aka dubata sosai komai lafiya ya dawo da ita gida tare da tarin siye siyen da yayi mata a hanya, yarinyar sai narkewa take tana kuka gami da riqe cikinta ya dinga rarrashinta yana bata hakuri da kyar ta barshi ya koma kasuwa. Koda ya tashi daga kasuwa, wani jami'in 'Dan sanda yaje"

ya dauko a motarsa suka nufi gidan Ramlatu dake tudun wuzurci Tana zaune a tsakar gida tana gyara

"kayan miya, yaro ya shigo yace.""Wai Ramlatu tazo su gaisa da dan uwanta yana waje. duk a tunaninta Alhassan ne saboda sa'i da lokaci yakan kawo mata ziyara, ta yafa mayafi ta fita, sai ganin Abbas tayi da dan sanda! jikinta a sanyaye take kallonsa yayi bala'in shan kunu tare da umartar d'ansandan ya daure mata hannu! Kuka ta fashe dashi taje ""Abbas ni zaka tozarta a kan matarka.""? Ko kallonta baiyi ba ya sake Umartar dansandan da maganar, Yaya Ramlatu ta juyo da sauri zata shiga gidanta shi kuma police din nan ya kama hannunta ta baya yasa mata takunkumi! Yara suka cika a gurin Sakina kishiyarta ta fito tana tambayar ba'asi! Abbah kuwa yana ganin an soma taruwa a gurin ya shiga mota ya sauke glass din motarsa mai duhu yana hango artabun da police din keyi da ita taqi sai turjewa take tana kuka da fad'in "" Dan uwana ne fa matarsa ce tasa yazo yaci mutuncina wallahi banyi laifin komai ba."" Jama'a sai kace kace ake a gurin ya cika sosai Abbah Abbas Yana kokarin jan motarsa ya bar gurun Salim yayi parking"

"din motarsa ganin abinda ke faruwa yasa hankalinsa ya tashi har ya nufi inda mahaifiyarsa take Abbah ya dan sauke glass din motar ya kirashi Da sauri ya karaso gurin yana risinawa! Abbah yace.""Ina fatan"

"ka kammala ayyukan dana sanya ka kafin barowa ta kasuwa.""? Yace.""Eh Kawu na had'a komai kamar yanda kace!."" Yace.""Okey jeka ce da wancan D'an sandan nace ya kwance mata abinda ya daura mata a hannu."" Salim yace.""Kawu wai meke faruwa ne.""? Yana kokarin kunna motarsa domin barin gurin yace kaje ka tambayeta zata fada maka."" Kawai yaja motarsa da sauri ya bar gurin ba tare da mutane sun"

farga dashi ba

Yaya Ramlatu ta muzanta mutu'ka kafin police din ya kwance mata hannunta ya qara gaba abunsa ita

kuwa yara ne suka kewayeta suna surutai a kanta gami da qananun maganganu! Salim jikinsa a sanyaye yaja hannunta tana wani irin kuka na tsantsar kunya da takaicin tozarcin da dan uwanta yayi mata cikin

unguwa a kan titi tunda gidan nata a kan titi yake shiyasa jamaa yara da manya suka cika gurin cikin

gidan suka shiga ita da Salim rayukansu a mugun 'bace. 'Karya da gaskiya Ramlatu ta shiga fad'awa

"'Danta tana kuka da fad'in ''Yana da kyau ya dauki mataki kan irin tozarcin da Dan uwan nata yayi mata, Salim ya fusata sosai bai ta'ba jin tsanar Kawun nasa ba sai ranar ko lokacin da ya auri naja'atu bai ji haushinsa ba kamar yanzu yace.""Kiyi hakuri Mama nagane abinda yasa mutumin nan yake miki wulakanci saboda Allah ya fifitashi a kanku yana da kudi yana da iko shiyasa duk wulakancinsa yake qarewa a kanki to insha Allah sai nayi miki maganinsa sai kinji mummunan labari wallahi sai na daukar miki fansar tozarcin da yayi miki a unguwa."" Ramlatu jin furucin da yaron nata yayi yasa ta tsagaita da"

kukan da take tana qara tunzura masa zuciya a kan yabi ta qarqashin qasa ya tagayyara Dan uwan nata

'Bangaran Naja'atu sai dai godiyar Allah dan wannan cikin na jikinta da alama lafiyyye ne ya hanata sakat!

"kullum cikin ciye ciye kwadayi iri iri idan ba taci kaza mai kuli kuli ba ji take tamkar zata mutu! al'amarin ya dinga bawa Mmn Sajida tsoro wannan wane irin d'an gayun ciki ne, duk kokarinta sai da ta gaza domin yau da gobe kayan Allah ne kuma tana jin tsoron saka Dantalle cikin harkar sabida kada ya nemi ya fanshe hidimarsa ta rasa bakin magana. Kawai sai ta shirya da sassafe tayi mata sallama tace zata je"

"wani guri! Asibiti ta nufa, cikin ikon Allah kuwa ta hadu da Dr shima shigowarsa kenan, suka gaisa a"

"mutunce kafin ta tambayeshi bukatar da ta kawo ta, Dr yace to Allah yasa bangoge numbar ba bari na duba dai."" Tace""To Allah yasa dai baka goge ba."

"Ya jima yana dube dube a wayar tasa kafin yace.""Alhamdullhi kinga number nan. Ajiyar zuciya ta sauke"

"tace to dan Allah rubuta min a takarda bani da waya wallahi."" Biro ya ciro a gaban aljihunsa ya bude wallet dinsa ya dan yagi jikin wata takarda ya rubuta mata number a gurguje ya mika mata ya wuce cikin asibitin Tana murna ta fita daga cikin asibitin ta danyi tafiya kadan ta samu masu communication"

"tace""Dan Allah zanyi waya ta minti biyar ko goma nawa zan biya.''? Guy yace.""Kawo naira dari."" Ta bashi kudin had'e da miqa masa number yasa a

53 / 79