Chapter 64 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   64 / 79

189K to 192K   out of 235.1K words

lokacin haila yana da kyau kina

sanjawa a kai kai kada kisa tun safe ki barshi sai dare dole gabanki yayi miki kyaikyayi daga haka kuma

"kwayoyin cuta su shiga jikinki, wannan kyakiyayin masifa ne, saboda haka dan Allah muyi hattara *"

Vip group #600 normal group #300 accont...0542382124....Binta umat gtbank...WhatsApp number...

07084653262

_Yau mura ta hana ni nayi muku post akan lokaci duk naga adduoin ku dana pravite dana group

Nagode sosai Binta tana tare daku insha Allah _

*BHRMBN 74_75*

"Da maganar Halisa ya kwanta bacci ya kuma tashi da maganar a cikin ransa, ya jima yana nazarin"

maganar da tunanin abinda zai biyo baya a jos din mutukar an san ita din bazawara ce to tabbas

"maganar Halisa na iya kasacancewa a samu wanda zai ce yana sonta duk da jegon da take dashi, dan"

"haka yana dawowa daga masallaci ya nemi number wayar Dan Azimi suka gaisa da juna yace.""Ina fatan dai ka shirya ka tafi da wuri bana so kuyi shigowar dare."

"Dan Azimi yace.""Eh gani nama fito Insha Allahu yanzu zan tafi, Yace."" to Allah ya kiyaye hanya inda ka"

"sauka sai ka kira ni ka sanar dani ."" Dan Azimi yace.""Insha Allah ranka ya dade."" Sallama sukayi ya kashe wayar ya miqe ya fita falo zama yay kan kujera yana jiyo motsin Halisa a kicin, tsabar 'bacin rai Halisa"

"ko gaisheshi ba tayi ba, yana kallonta ta fito daga kicin ta nufi dakinta ko kallonsa ba tayi ba, miqewa yay yana girgiza kansa ya nufi gurin Zainab, babu kowa a falon lokacin da shiga sai ya nufi dakin yaran sa domin duba su, suna tare da Baba Larai tana taimaka musu da shirin makaranta, a nutse yaran suka gaishe shi ya amsa cikin kulawa shima ya gaishe da Baba larai ya tsaya suka danyi maganar yaran da ita"

kafin ya fita daga dakin.

Zainab tana zaune kan dadduma tunda tayi sallah ta kasa motsawa daga inda take marar ta ce take wani

"irin ciwo Cikin mawuyacin hali ya sameta, hankalinsa ya tashi ya taimaka mata ta miqe tsaye, yana"

"tambayarta abinda ke damunta, cikin halin ciwo ta fada masa cewar mararta ke ciwo, zaunar da ita yay gefan gado yace.""Bari na kira Baba Larai ta dubaki ko haihuwa za kayi....Fita yay daga dakin sauri, koda baba larai taga yanayin Zainab a take ta fahimci cewa haihuwa za tayi, tace""Alhaji haihuwa yarinyar nan za tayi amma yana da kyau aje asibiti domin a sake tabbatarwa, Yace.""Okey bari na sanar da Halisa....Halisa jin cewa zainab zata haihu yasa ta biyo bayansa halin da taga Zainab a ciki yasa jikinta sanyi, kayan haihuwa kawai suka hada suka nufi asibiti Zainab duk ta rikice da ihu! gabadaya ta manta da addua sai ihu take tana kiran a taimaka mata gabadaya hankalinsu ya tashi harshi Abbah Abbas din"

dake driving hankali a tashe ya kara karfin motar suka isa asibitin nasarawa.

Zainab bata dade tana doguwar naquda ba Allah ya sauketa lafiya inda ta haifi 'ya mace mai kama da ita

"sai dai ta dauko hasken fatar babanta, Abbah yayi farin ciki sosai ganin yanda Allah ya raba lafiya maijego da babynta lafiyarsu lau Kafin su bar asibitin Abbah ya sanar da duk wanda ya dace ya san"

"haihuwa, awa biyu kacal sukayi a asibitin aka sallamesu Suna koma gidan suka tarar da 'yan uwan"

"Zainab sun cika gidan, Abbah ya tsaya suka gaisa a gurguje ya fita ya basu guri"

Bangaran Halisa ya koma domin ya kimtsa jikinsa. Allah sarki Halisa ganin yanda yake ta murna da

"haihuwar zainab din yasa itama taji tana sha'awar haihuwa tunda ta haihu sau biyu bata sake haihuwa ba, mufida yanzu shekaranta goma sha uku amma ko 'batan wata ta sake ba, zama tayi ta zabga tagumi"

abin duniya ya isheta.

Ganin ya shigo dakin ne yasa ta miqe ta fita ta basa guri gabad'aya duniya tayi mata zafi tana ta nadamar

cutar da kanta da tayi tana tunanin ko magungunan turawan data dinga d'ubga ne ya toshe mata mahaifa gaskiya dole ma taje asibiti a dubata tunda ba wuce haihuwa tayi ba.

Zainab na tsakiyar 'yan uwanta suna ta zugata ita kuma ta saki baki sai fad'a musu karya da gaskiya

"takeyi...Wata yayarta tace""To yanzu ai duk wani abu da kika san kina bukata ki rubuta masa kuma kada ki sake kiyi amfani da kyan babyn nan ya sake siya miki wasu, sannan kice kina so ya siya miki set gold"

zakiyi fitar bikin suna dashi.

"Zainab tace""Duk abinda nake so yana kaina ke har mota nima sai ya siya min tunda na tabbatar wacce"

aunty Halisa take hawa shi ya siya mata.

"Yayar tata tace""Ato idan kika tsaya wasa sai ki zama koma baya tunda kin haihu dashi ai kin zama kujera"

a gidansa....Zainab murmushin jin dadi tayi ta juya ta kalli babynta dake kwance a gefanta.

Yaya Ramlatu da Hajia Rabi da Baba Talatu ne sukayi sallama a dakin.

"Da sauri Yayar zainab ta miqe tana musu barka da zuwa ta basu guri suka zauna suna gaisawa, Babyn ta"

"dauko ta miqawa baba talatu da fadin ""Ga bakuwar duniya mai kama da babanta."" Baba Talatu ta karbi yarinyar tana murmushi cikin nutsuwa tace""Masha Allah Allah yayi mata albarka babu shakka yarinya ta dauko gida Allah y raya mana ita."

suka amsa da amin. Baba talatu ta miqawa Hajia Rabi itama ta karbe ta tayi mata addua sannan ta

miqawa Yaya Ramlatu.

"Yaya Ramlatu tayi murmushi idonta a kan babyn tace""Yarinya dai ta dauko hasken fatar gida amma"

"kuma kammaninta sak na uwarta."" Zainab tayi saurin kallonta tana mamakin maganarta, ita kuwa yayarta cikin ya'ke tace""Aikuwa baki ji bahaushe yana cewa kyawun d'a ya gaji uwarsa ba."" Ya Ramlatu tayi dariya cikin sigar kuntatawa tace"" Kyawun d'a ya gaji ubansa ake cewa yarinya ta gaji ubanta gurin"

"haske fata kammani kuma na uwarta ne Allah yasa kada ta dauko halinta."""

"Hajia rabi tace""Wace irin magana ce wannan.""? cikin takaici Ramlatu tace""Hajia duk sanda zan kalli"

"yarinyar nan sai na tuna sanda ta wanke ni da mari ni kam a tarihin rayuwata ba zan taba mancewa da ita ba."""

"Jin wannan magana yasa 'yan uwan Zainab jikinsu yay sanyi kunya duk ta dabaibayesu, Zainab kuwa tuni"

ta fashe da kuka gabanta sai faduwa yake Ramlatu tazo ta tona mata asiri a gurin 'yan uwanta

"Yayar Zainab tace""Dan Allah kiyi hakuri 'yar uwa maganar tone tone duk bata taso ba alheri da farin ciki"

ne ya kawo muku gidan nan saboda haka idan zainab tayi miki wani wanda bakiji dadinsa ba ki gafarce ta akwai kuruciya a tare da ita

"Ramlatu tace""Iskanci dai ba kuruciya ba, ai magana ni ta wuce a gurina wallahi kawai dai idan na tuna"

"al'amarin raina yake baci."""

"Cikin fusata! Yayar zainab din tace"" Ashe dama abunda kike yi kenan yanzu kamar wannan matar tana a"

"matsayin yayar mijinki ki fitar da hannu ki mareta to Sai ki bata hakuri tunda ke baki da mutunci."""

"Zainab na kuka tace""Yaya Ramlatu ki gafarce ni wallahi tsautsayi ne."" Cike da takaici tace ""Dena kuka ai"

"na yafe miki tuntuni saura kuma idan ya dawo ki fada masa ga abinda nazo nayi miki kisa shi ya kawo min rundunar sojoji."" Zainab tace""Wallahi ko wancan karan ma bani nasa shi ba kiyi hakuri."""

"Baba Talatu tace""Ke kam Ramlatu abu baya wuce wa a gurinki ne? yarinyar nan ta baki hakuri magana ta"

kare dan Allah.

"Yaya Ramlatu tace""Magana ta wuce baba insha Allah bazan sake tada ita ba."""

"Karfe uku saura na rana Dan Azimi yayi parking din mota a kofar gidan Mmn Sajida, sai dai me? yana"

fitowa yaga katon kwado kulle da kyauran gidan Ya jima yana mamaki kafin ya bude motar ya zauna

"ya shiga kiran wanda ya aikoshi, ya sheda masa abunda yake faruwa."

Abbah jin abinda dan Azimi yake fad'a masa yasa ko gama sauraransa baiyi ba ya kashe wayar da sauri ya

"nemi number ta......Lokacin suna gidan bikin sunan k'anwar Mmn Ladi, dan da zasu tafi cewa tayi ba"

zata zauna ita kadai a gida ba sai ta shirya tsaf sukayi tafiyarsu bayan tasan da maganar zuwan Dan Azimi.

Hayaniyar jama'a ya hanata taji abinda yake cewa sai kawai ta kashe wayar ta ta ajiye tasan dai maganar

zuwan Dan Azimi zaiyi mata ita kuwa ba taga dalilin da zai sanya ta koma gida a yanzu ba.

Abbah ya shiga mamaki mai tsananin gaske yau shi Najaatu ta kashewa waya! to wai shin ma ina ta tafi

a garin da bata da kowa hakika yarinyar nan na nema ta d'ora masa ciwon zuciya.

Wayar ya sake kira sai ta miqe daga cikin mutane ta samu gurin da babu hayaniya sosai ta daga a

"sanyaye tace""Abbah ina kwana wallahi ina cikin jamaa ne shiyasa bana jinka sosai."""

"Yace.""Kina ina Dan Azimi tuntuni yazo daukar ki bakya nan to har in dai na isa dake duk inda kike kiyi"

"maza ki koma yana zaman jiran ki."" Abbah dan Katse ta yay da sauri yace.""Kina so ki 'bata min rai ko?"

na fad'a miki bana son zamanki a wannan garin nasan dai daga jiya zuwa yau duk wanda kika sani a garin kin gaisa dashi to zaman me za kiyi kuma gashi nan kwana d'aya kacal da zuwanki kin fita yawo shin me kike so ki zama? saboda haka na gama magana idan na isa na fad'a miki kiji to ki tabbatar kin

biyo Dan Azimi kun

"n dawo gida a tare."" Kashe wayarsa yay bayan ya gama maganarsa."

"Tun kafin ta zauna Mmn Sajida ke kallonta, tace""Najaatu yana ga jikinki a sanyaye ina fata ba wata"

"matsala bace."""

"A sanyaye tace""Abbah ne ya kira wai yanzu haka Dan Azimi nacan kofar gidanki yana jirana yace lallai"

dole sai na bishi mun koma gida a tare ni kuma wallahi bana jin zan iya binsa sai dai idan ya gaji da zama ya tafi bari ma kawai na kashe wayar ta kada ya sake kira.

"Mmn Sajida tace""A'a bada ni za'ayi wannan rashin hankalin ba, Najaatu ba zaki had'a kai dani ki 'batawa"

"wannan bawan Allahn rai ba, tunda yace ki tafi to gaskiya yana da kyau kibi umarninsa kada ki nuna masa bai isa dake ba, haba keda kike nema ya mayar dake gidansa me zai sanya ki dinga yi masa gaddama akan dukkanin abinda zai umarceki kawai ki tashi mu tafi na tayaki hada kayanki ai mun gaisa"

kuma insha Allah muma zamu inda kike.

"Murya na rawa tace""Mmn Sajida korata kike a gidanki? Wai shin dan Allah idan na koma me zanyi masa"

"zama fa kawai zanyi a gida shi kuma kullum yana gurin iyalinsa to ba gwara na zauna na samu nutsuwa ba."""

"Mmn Sajida tace""Lallai ta yaro kyau tace bata qarko wallahi Najaatu baki da wayo har yanzu Mutumin"

"nan dafa baya sonki ba zai damu dake haka ba, yanzu dama kika samu a hannunki wacce zaki sake janyo hankalinsa kanki ta hanyoyi daban daban, baki da wayo wallahi har yanzu kiyi tunani akan shawarwarin"

dana baki jiya da daddare wallahi mutukar kin dauki shawara ta baza'a ja dogon lokaci ba zai kawo kansa

gurinki.

"Najaatu tayi shuru tana nazarin maganar da Mmn Sajida keyi, "" A sanyaye tace."" Shikkenan Mmn Sajida"

"zan gwada Daukar shawararki nagode sosai da kulawarki a kaina."""

"Mmn Sajida tace""Babu komai wallahi aike yanzu 'kanwata ce duk abinda nayi miki ban fadi ba, saboda"

"haka yanzu tashi muje ki shirya kayanki."""

"Miqewa sukayi suna gyara mayafi, Mmn Ladi ta fito daga dakin mejego ganin sun miqe tace""Aa ina"

"zakuje naga kun miqe.""? A takaice Mmn Sajida tayi mata bayani...Mmn Ladi tace""Eh lallai haka shine yafi alkairi dake Naja'atu mungode kwarai da ziyara kuma insha Allah muma muna kan hanyar zuwa. Tare"

suka fita daga gidan Mmn Ladi har bakin titi ta rakasu sai da ta tabbatar sun hau adaidaita sahu sannan

ta koma cikin gidan

Dan Azimi na ganin saukar su Najaatu daga a daidata sahu ya shiga murna dama tun dazu wanda ya turo

shi yake ta kiransa a waya yana tambayarsa yanda ake ciki sai bayan sun shiga gidan ne yay saurin kiransa ya fada masa cewa gata nan ta dawo nan ba da jimawa ba zasu dauko hanya.

"Abbah Abbas ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.''To Alhamdullhi Allah ya kawo ku lafiya."". Najaatu"

"cikin kunci da damuwa ta fito Mmn Sajida tasa mata jakar kayanta a motar dukkaninsu idan ka gansu za kagane suna cikin alhini na rabuwa da junansu Mmn Sajida sai daure zuciyarta take tana kwantar mata da hankali, sai bayan data shiga motar ne hawayen da take 'boyewa suka shiga zuba, hannu kawai ta daga mata ta kauda kanta gefe guda. Dan Azimi na jan motar Mmn Sajida ta juya da sauri ta shiga"

"gidanta tana goge hawayen daya 'kwace mata, Allah kenan mai had'a mutum da mutum."

Dan Azimi sai hira yake mata ta shareshi haushinsa takeji kamar shine yay mata laifi to shima daya lura

bata son hirar sai yaja bakinsa yay shuru kawai ya cigaba da fafara gudu a kan kwalta.

"daidai sanda suka shiga zaria Abbah ya sake kiran wayar Dan Azimin yana tambayarsa hanya,"

"Yace.""Gamu a zaria ai mun kusa isowa gida insha Allah."""

"Abbah ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in ""Allah ya saukeku lafiya.'' ya kashe wayar yana jin tamkar"

"wanda aka yayewa dukkanin damuwar dake damunsa tabbas Tafiyar Najaatu garin jos ta daga masa hankali sosai dan gani yake kamar zata sake had'uwa da wani dan ta'addahn! ya yaudareta, shi da kansa a yanzu ya gazgata abinda ke damunsa a kan yarinyar ya daina wahalar da kansa da yaudarar kansa a kan cewar shi ba son aure yake mata ba so yake mata irin na uba da 'yarsa! Gaskiya da yayi nazari sosai ya gane ba irin wannan son yake mata ba, yarinyar ita da d'anta sunyi masifar tsaya masa a rai! kuma ya yarda da maganar Halisa inda take cewa samun nutsuwar sa Najaatu na kusa dashi, hakane tunda tun jiya yake cikin tararrabi gami da rashin kwanciyar hankali saboda tayi nesa daga inda"

"yake, gabadaya haihuwar Zainab bata dameshi ba akan yanda ya damu da lallai sai Najaatu ta dawo gida."

Sai wajejen tara da rabi na dare suka sauka. Dama tuntuni ya gayawa Hajia cewa ya tura Dan Azimi ya

"daukota hajia ta dinga mamakinsa, sai dai tayi shuru kawai tana binsa da dukkanin abinda yake tsara mata akan tafiyar. Najaatu kukan takaici ta zauna ta nayi Hajia ta zauna tana ta rarrashinta da bata"

hakuri ita kuwa Yaya Ramlatu d'an ta dauka ta goya tana taya hajian rarrashin da take. A ranar dai

Najaatu bakin ciki da takaici tayi bacci dan taji bala'in haushin abun dan dai babu yanda za tayi ne.

"Sai da safe take jin labarin haihuwar Zainab a bakin Ramlatu tace Allah Ya raya abunda aka samu, Hajia"

"tace""Idan anyi la'asar sai muje nima banje naga 'yar ba."

"Tace""To shikkenan Hajia Allah ya kaimu lafiya."

To kamar yanda hajia ta fada hakane ya kasance bayan sunyi sallar la'asar a gida suka shirya tsaf suka

"nufi gidan masu jegon......Gate din Zainab cike yake da 'yan uwanta tamkar ma ranar ne suna Zainab famliy nasu suna da yawa shiyasa tunda akayi haihuwar suke shige da fice a gidan, mutum uku ma a gidan suka kwana kuma duk da auransu kawai daular gidan Zainab din ce take d'ibarsu suka zauna suna d'orawa da saukewa, 'Ya'yan sheik Nazifi 'Ya'yan malam kaqi halin malam ne yawanci su basu da hali mai"

"kyau mazajensu na hakuri dasu mutuka, kuma mafi akasari almajiransa suke aure shiyasa suke rashin"

mutuncinsu iya san ransu sabida mazajen nasu najin kunya da nauyin tunkarar shehin malamin da wata

"magana, a cikinsu Zainab ce karama kuma itace ke auran Alhaji (mai kudi) shiyasa tunda suka zo suke zugata ga yanda za tayi ta gina kanta a gidan.......Harabar gurin Zainab yayi kaca kaca da kayan miya gefe"

katon kasko ne akan murhu wuta sai ci take anata soya nama tamkar ranar sallah.

Ganin shigowarsu Hajian gidan yasa suka dan shiga nutsuwarsu cikin girmamawa suke shiga yi mata

"barka da zuwa, Babbar yayar su zainab din itace ta jagorance su har inda maijego take. Zainab taci"

kwalliya tamkar wata amarya da babynta a hannu tana shayar da ita cike da murna takewa hajian barka da zuwa.

Hajia Abu ta samu guri ta zauna a nutse Najaatu ma ta zauna kusa da ita tana kokarin kwance Daddy

dake motsi a bayanta.

Zainab ta miqawa Hajia yarinyar kana cikin neman gindin zama ta tsuguna har qasa tana gaishe

"ta....Hajia cike da farin cikin ganin Zainab da 'yarta kalau ta amsa tana fad'in ""Sannu Zainab Allah ya qara miki lafiya tare da abunda kika haifa naji dadin ganinki kalau keda yarinyarki Allah ya rayata tafarkin"

"addinin musulunci."" Zainab na dan murmushi ta amsa tare da komawa ta zauna a gefan gado."

Dakin ne yay shuru Zainab 'Yar rainin hankali wai jira take Najaatu ta gaisheta tayi mata

"barka. Najaatu kuwa tunda tayi mata kallo daya ta dauke kanta,babyn kawai ta kar'ba hannun hajia"

"tana dubata gami da sa mata albarka, a tsakaninsu babu wacce ta kulawa kowa. Hajia tayi mamakin"

al'amarin kwarai da gaske kuma ta fahimci abinda yake da akwai sai tayi shuru da bakinta ba wai dan bata da abincewa ba sai dan ganin kamar shuru din da tayi shi yafi alkairi.

Sun kai kimanin Mintina ashirin a dakin Zainab din kafi su miqe Hajia tace zasu shiga gurin halisa su

"gaisa."" Zainab tace""To hajia nagode sosai Allah ya qara girma."" Hajia ta amsa da ameeen sannan suka fita daga dakin."

"Yanayin yanda suka samu Halisa cikin damuwa yasa daga hajian har Najaatun suka tausaya mata, Halisa"

"bata 'boyewa hajia abinda ke damunta ba sai da fad'a mata komai Hajia tace""Kada ta damu insha Allahu ita da kanta za tai masa maganar zuwa asibitin insha Allahu kuma za'a dace idan anje dan haka ta daina damuwa."" Halisa taji dadin zuwan hajian sosai da sosai kuma tasan tunda tace zatayi masa magana to

64 / 79