Chapter 71 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   71 / 79

210K to 213K   out of 235.1K words

zatayi masa hauka ba, hakika yaji dadin yanda ta tar'beshi ta bashi abincinta mai dad'i ya cika cikinsa."

"Sai da ya nutsu tukunna tazo ta zauna kusa dashi tare da ri'ke hannunsa cikin alhini tace"" Wallahi tunda"

"ka fita na kasa samu nutsuwa sai sa'ke-sake nake a zuciyata na abubuwa marasa kyau amma naji dad'i da naji kace jikin yarinyar da sauqi ina rokon Allah ya bata lafiya."""

"Abbah yana kallonta da kyakkyawan murmushi a fuskarsa yace."" Ameeen ya Allah nagode sosai da kika"

"fahimce ni, ni kaina banyi tunanin yau zan zama busy ba wallahi naci burin na zauna a tare dake na gwangwaje amarcina sai wannan matsalar ta shigo ciwo ya wuce komai mussaman na k'aramin yaro bayan mun dawo daga asibiti ina kokarin dawowa gareki aka sanar dani ina da 'baki a kasuwa wannan"

"dalilin ne yasa kikaga ban shigo da wuri ba ina fata dai ranki bai 'baci ba."""

"Murmushi tayi tace""Haba dai raina bai 'baci ba wallahi nasan ai duk inda kake ina cikin zuciyarka kuma"

"dole aiyi maka uziri duba da yanayin yanda kake hurd'a da jamaa.'' Yay mirmushi mai kyatarwa, yace.""Jeki dauki min abokina mu gaisa."

"A hankali ta miqe ta isa inda Daddy ke kwance ta daukoshi, Abbah ya kar'bi yaron yana dariya tare da"

"daga shi sama yana masa wasa, yaron ya dinga dariya yana cilla kafafunsa, Ya kalleta da da mirmushi a fuskarsa yace.""Yaron nan wai zaiyi wata nawa yanzu."" ?"

"""Watanshi takwas da 'yan kwanaki."" Ya shiga girgiza kansa da fad'in abin babu wuya to Allah ya raya"

"mana shi.'' Ta amsa da ameen tare da kar'ba yaron daga hannunsa....Abbah loptop d'insa ya janyo ya shiga dubawa kamar yanda ya saba, Tana kusa dashi suna hira sama- sama har ya d'an duba abunda zai duba ya rufe loptp din idanu a lumshe ta kalleta, tana kokarin miqewa dady za taje ta gyarawa shimfida, sai kawai ya bita da kallo har ta shiga bedroom din.....Minti biyar ya miqe yabi bayanta, lokaci har tasawa yaron pampars tasa shi a net tana kokarin miqewa ya shigo, hannunta ya rike suka zauna gefan gado, ta kalleshi taga yanayin da yake ciki sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi...Yace.""Ina tunanin cikin satin nan zamuje miyi umara mu dan huta dan idan banyi da gaske ba jamaa na iya hanani na more"

"amarcina so ki zauna cikin shiri insha Allah acikin satin nan zan shirya mana tafiya zuwa kasa mai tsarki."""

"Da murmushi a fuskarta tace""To shikkenan amma sai nake ganin anan din ma za'aka iya amarcinka."""

"Girgiza kansa yay yana wasa da hannayesa a jikinta yace.""Nafi so nayi nesa da gari sai nafi samun nutsuwa. shuru tayi tana jin yanda tsigar jikinta ke tashi, ya riga ya zuge mata zif din rigarta yana ta"

"cakuda mata nonowa! gabadaya jikinta ya saki gashi wanka take so tayi A hankali tace""Abbah ka bari"

"nayi wanka."" Fuskarsa yake goga mata a wuyanta gemunsa sai tsikararta yake yace.""Ba sai kinyi wanka a haka ma kina kamshi ."" shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya. Abbah rikita mata lissafi ya shiga yi da"

kalolin soyayyarsa wanda yasa ta hautsine ta dinga mayar masa da martani tana kesses din fuskarsa tare da shasshafa jikinsa. Maqale junansu sukayi bayan sun raba jikinsu da kaya suka dinga wasanni da

jikinsu.

Najaatu ta dinga bashi mamaki ganin yanda take sarrafa shi sai kace wata babbar mace ko Halisa da taga

"jiya da yau ba zata nunawa Najaatu komai ba, a daidai lokacin da suke daf da biyawa junansu bukata, kiran waya ya katse musu hanzari Abbah gabansa ya fad'i! sai ya shiga tunanin wayar jiya zuciyarsa"

"tace masa watakila jikin Ummi ne ya tashi, sai kawai ya fara kokarin sauka! Najaatu ta kamoshi ta qamqame shi tsam! ta hanashi sauka tana masa magana qasa-qasa! sam bai ma ji abinda take cewa ba yace.""Ki bari na duba wayar nan na gani ina tunanin Zainab ce."" Ranta ya sake 'baci! a sarqe tace""Umum!"

"kawai ka cigaba idan komai yayi kammala sai ka kirata kaji komeye."""

"Kallonta yay duk da da akwai duhu a dakin sai da ya fahimci cewa tana cikin yanayi. Yace.""Bana jin zan"

"iya samun wani kuzari a yanzu hankalina ba'a jikina yake ba dan ina tunanin jikin ummi ne ta tashi."""

Sai kawai ya zare jikinsa ta zura kafafunsa kasa wayar ya laluba kan bedside ya d'auka daidai lokacin

wani kiran ya sake shigowa ganin sunan Zainab kan screen din wayar yasa da sauri ya daga wayar. Yau

"ma da innalilhi ta fara kuma kukan da take har yaci uwar na jiya tace ""Abban Mufada Ummi tun misalin sha daya da rabi numfashinta ya dauke gashi yanzu sha biyu da rabi bata farfado ba.""! Cikin damuwa gami da tashin hankali yace."" Me yasa tun lokacin baki kirani ba sai yanzu..""? Haba Abban Mufida tun yaushe nake kiran wayar taka kaqi dauka ni dai har na fitar da rai da yarinyar nan wallahi."" Cikin gursheken kuka ta karashe maganar. ""Kashe wayar yay ya mike ciki tashin hankali ya lalubi jallabiyarsa"

"da gajeran wanda yasa gabadaya ma baiyi tunanin wanke najasar dake jikinsa ba ya kama hanyar fita. Najaatu miqewa zaune tayi rai a bace ta kira sunansa""Abbah.""! Juyowa yay yana kallonta da"

"fad'in ""Najaatu kiyi hakuri kinji ko bari naje na duba yarinyar nan naga halin da take ciki "" Karya ne fa"

wallahi Ummi lafiyarta lau kawai tana so ta hanaka nutsuwa ne bayan haka kuma tana so ta kuntatawa zuciyata shiyasa ta d'orawa 'yarta ciwo.

"A fusace! Yace""Saboda rashin hankali haka kawai sai ta d'orawa 'yarta ciwo ashe kenan abinda Dr ya"

"fad'a karya ne ko? kada ki sake wannan maganar kawai kiyi addua Allah ya bata lafiya."" Najaatu sakin baki kawai tayi tana kallonsa ya kama handile zai bude kofa tace""To kada ka fita da najasa yana da kyau ka wanke ta."" karamin tsaki yaja ya dawo da sauri ya shiga toilet din, yayi wanka ya fito ya sanja jallabiya da gajeran wando duk tana zaune tana kallonsa yasa kai ya fice daga dakin ba tare da ya tanka mata ba, lallai kawai saboda tace ciwon Ummi karya ne yake jin haushi, lallai babu shakka Zainab tana so ta sanyawa mijinsu rashin nutsuwa, a gida da waje al'amarin gabadaya sai ya tsaya mata a rai ta dinga jin"

wani irin tausayinsa na ratsa mata zuciya...

*Afuwa Mommy naga Comment d'inki......Tunda Halisa ta ha'kura ta sakarwa Najaatu to ina ganin

"abinda Zainab take 'karamin alhaki ne, Najaatu ta riga tayi mata illah tunda har ta fahimci cewa itace"

tauraruwa a zuciyar mijinta to duk wani makircin ta gami da sharin ta ba za suyi tasiri ba dole za tayi ta

gaji ta daina*

*Littafin na kudi ne *

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip

group #600 normal group #300 account.... 0542382124...Binta umar gtbabk idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

"******84 Abbah cikin damuwa gami da mayar da al'amuransa ga Allah ya isa gidan, yanayin yanda"

"yake horn da karfi yasa maigadi ya tashi a firgice!! ya fito da daga dakinsa da toch a hannunsa, k'aramar kofa ya bud'e tare da leka kansa, ganin motar maigidan yasa da sauri ya nufi bakin gate ya fara kokarin bud'ewa, ko 'karasa budewa baiyi ba yasa hancin motar a gidan, maigadin yay saurin ya matsa gefe, nan bakin gate din ya faka motar ya bude ya fito, maigadin ne ya karasa da sauri yana gaishe tare da fad'in ""Alhaji ina fata dai lafiya nagan ka cikin dare."" Yace.""Malam Halliru babu lafiya wallahi yarinya ce bata da lafiya."" Malam Halliru yace.""Ayya nima dama ganinka a cikin wannan daren yasa na zargi akwai wani to Ubangiji Allah ya bata lafiya."" Abbah na kokarin shiga gurin Zainab ya amsa da ameen Zainab"

"dasu aunty Balaraba suna zaune suna magana kasa _kasa jin sallamarsa yasa Zainab ta shiga sheshshekar kuka had'e da fad'in ""Aunty Balaraba ki cigaba da shafa mata ruwa a fuskarta ko Allah zai sanya numfashinta ya dawo ni kam na fitar da raina da yarinyar nan."" Cikin kuka ta'karashe maganar, Aunty Balaraba dake rungume da baby ummi wacce take bacci sai kawai ta shiga shafa mata ruwa a fuskarta da jikinta tana fad'in ""Haba Zainab cuta ai ba mutuwa bace yarinyar nan dogon suma tayi zata farfad'o"

"insha Allah."""

"Zainab na sha'kar hanci tace""Ai abun ne ya tsorata ni wallahi kina ganin fa ko motsi ba tayi."" Aunty"

Balaraba na kokarin magana ya shigo dakin

Zainab a guje taje ta rungumeshi tana kuka na fitar hankali take fadin shikkenan Abban mufida na rasa

"'yata gatanan a hannun aunty Balaraba tun dazu ake shafa mata ruwa numfashinta yaki ya dawo."""

Cikin sanyi jiki gami da miqa al'amuransa ga Allah ya cireta daga jikinsa ya nufi inda aunt Balaraba ke

"zaune. Hannu yasa ya kar'bi yarinyar aunty Balaraba na share hawaye tace""Gata nan dai mun rasa"

"abinda ke damunta numfashinta ya dauke ya dawo haka yake gashinan dai yanzu ya dawo saboda ruwan da nake shafa mata a fuska da jikinta."""

"Ba tare da yace komai ba ya nemi gefan gado ya zauna da yarinyar a hannunsa, aunty Balaraba ita da yar"

uwarta suka mi'ke simi simi suka fita daga dakin.

Abbah yarinyar ya zubawa ido dake ta faman sauke ajiyar zuciya dalili ruwan da aunty balaraba ke sa

"mata a jiki mai sanyi ne sai ma ta shiga makyarkyata tana cilla kafafunta da hannuwanta sama kafin ta fara wani irin kuka da atishawa."""

"Da sauri Zainab tazo ta zauna kusa dashi tare da fadin ""Alhamdullhi Allah nagode maka daka dawo min"

"da numfashin yarinta Allah kaine abin godiya."""

"Kokarin kar'barta take daga hannunsa, ya hanata ido kawai ya tsirawa yarinyar kamar me neman wani"

"abu, yana so ne ya gazgata naganar Najaatu nacewar rashin lafiyar na karya ne sai dai kuma yanda yarinyar ke janyo numfashi da kyar tana atishawa da makyarkyata yasa ya 'karyata maganarta tabbas ciwon Ummi ba karya bane gaskiya ne. Yace."" Jeki dauki mata kayan sanyi masu kauri ki shiryata"

"muje likitanta ya dubata."" Zainab da sauri ta miqe daga kusa dashi ta nufi drowar kayan yarinyar. Shi"

"kuwa cikin dubara ya cirewa yarinyar kayan jikinta saboda tsananin mugunta da rashin imani aunty Balaraba ta ji'ka mata jikinta jagab da ruwan sanyi......cikin tausayi ya shirya 'yarsa har pampars shi yasa mata, abinda bai ta'bayi ba amma yau yayi a kan Ummi wani irin tausayin yarinyar ne ke ratsa zuciyar"

Karbar yarinyar tayi kamar gaske tasa towel ta goya ta mikewa yay yasa hannu cikin aljihun jallabiyar

"jikinsa ya dauko wayarsa, number Dr Mahir ya nema yana addua Allah yasa ya sameshi Cikin ikon"

"Allah kuwa tana fara ringing ya daga, gaisawa sukayi kafin ya sheda masa abinda keda akwai, Mahir yace kawai su sameshi a asibiti.......Dr Mahir ya jima yana duba yarinyar domin sanin abinda ke damunta, tabbas binkicensa bai nuna masa komai ba sai abinda ya nuna masa a baya sai kuma zazzabi da mura daya fahimci sun d'an kama yarinyar suma kuma ba suyi karfi ba amma maganar daukewar numfashi shi dai duk iya binkicen da yayi a kan yarinyar bai ga abinda zai janyo numfashinta ya dauke ba na farko yarinyar bata da sanyi a jiki mura mai zafi ko asma da sai sauran cututtukan dake sanya numfashin"

mutum ya sar'ke! yarinyar nada lafiya matsalar rashin samun ingantaccen nono ne kawai yake damunta

Wannan bayanin shi yayi Abbah Abbas yana sake jaddada masa cewar yarinyarsa lafiyayyace dan duk

"binkicensa bai ga abinda ya sar'ke mata numfashi har ta suma ba sai dai yanzu daya fahimci shigar zazzabi da mura a jikinta yace."" Amma kuma hakan na iya faruwa da yarinyar mussaman idan ta nemi"

nono a lokacin da take bukata bata samu akan lokaci ba hakan na iya janyowa tayi kuka mai tsanani

"wanda zai sanya har numfashinta ya dauke """

"Abbah ajiyar zuciya ya sauk'e! bayan ya gama jin jawabin Dr mahir din yace."" Dr idan na fahimci"

"maganarka kana so ka tabbatar min da cewar Yarinyar nan babu wani ciwo mai zafi a tare da ita wanda zai janyo mata shiga matsalar da muka zo maka da ita kenan."" Dr mahir yace.""Kwarai kuwa yarinya lafiyarta lau in bayan abubuwan dana fad'a maka a baya suma kuma ina ganin idan an kiyaye to ba za'a sake samun wata matsala ba."" Abbah yay shuru yana nazarin maganar ikon Allah dai ya wuce komai amma kuma ya soma hango k'amshin gaskiya a kan maganar Najaatu ta dazu Ajiyar zuciya ya sauke ya"

"miqawa Dr din hannu tare da fadin Nagode kwarai dr insha Allah za'a kiyaye da dokokin daka fad'a."" Dr mahir "" Ya miqawa Zainab wata leda da magunguna a ciki yace."" Wad'annan magungunan zasu taimaka"

"insha Allah yanzu ma idan kunje gida sai abata maganin mura da zazzabi ne."""

"Zainab tace""To mungode Dr."" Abbah hannu ya sake miqa masa hannu sukayi sallama kafin su fita daga"

ofis din Tun mota yake nazari akan al'amarin tabbas yana ganin zai sanya ido sosai domin ya tabbatar

da gaskiyar magana. maimakon daya sauketa ya wuce gidan Najaatu sai kawai yasa maigadi ya rufe

"gate din, Zainab na gani haka taji tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha dan farin ciki Tare suka nufi"

"dakinta ya zauna gefan bed yana kallonta tana ta wani lallaba yarinyar yace ta zauna ta bata nono tukkuna sai ta bata maganinta, ta zauna kusa dashi ta fito da nono tasawa yarinyar a baki, Allah sarki baby Ummi ta kama nono ta dinga tsotsa kamar ba zata bari ba hakika Zainab na zalintar 'yarta. Sai da"

"ta koshi tukkuna ta cire nonon daga bakinta, ya fito da maganin ya na nuna mata yanda zata bata"

"Kar'ba tayi a nutse ta bata maganin ya kar'beta daga hannunta, addua yay mata ya tofa mata a jiki"

"sannan ya sata a net dinta ya rufeta da bargo......Zainab kuwa kayan bacci tasa tazo ta kwanta kusa dashi tare da fad'in ""Abbahn Mufida ba zaka tafi ba dare yayi fa."""

"Yace""Zan kwana tare daku domin naga yanayin jikin Ummi.'' Farin ciki kamar ya kasheta tace""To ka"

"kwanta ka huta mana."" Yace.""Kada ki damu zan kwanta. Shuru tayi tare da rufe jikinta da bargo,"

Wayarsa ya dauko ya duba lokaci d'aya da kwata na dare! Yanzu Najaatu watakila tayi bacci kuma bai

"zama lallai ta bar wayarta a kunne ba, gwada kiran wayar yay sai ta shiga. Najaatu sai da taci"

"kukanta ta koshi tukkuna taje ta tsarkake jikinta ta dawo ta kwanta da sha'awarta dan gabadaya ta kasa samun nutsuwar da take bukata, so take tayi bacci takaici da bakin ciki ya hanata, sai ta dauki wayarta ta kunna tana dube dube nan taga har d'aya tayi bai dawo ba jikinta yay sanyi zuciyarta tace watakila acan zai kwana kawai kiyi kwanciyarki ki kyaleshi kuma kada ki kira wayarsa. da wannan shawarar"

"take kokarin kashe wayar sai kiransa ya shigo, da kamar kada ta dauka sai dai ta d'aga ciki ciki tayi"

"sallama da fadin""Ya jikin Ummi."""

"Abbah ya sauke ajiyar zuciya a nutse yace.""Da sauki yanzu yanzu muka dawo daga asibiti dama na kira ki"

"ne domin na fad'a miki cewar zan kwana tare dasu saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo ba dai fata nake wani abun ya 'kara faruwa ba""."

"Ta daure zuciyarta tace""Eh dama nima abunda nake tunanin kiran ka na fad'a maka kenan babu damuwa"

"ka zauna kawai sai da safe."" Tayi gaggawar kashe wayarta dan ma kada yayi mata wata maganar da zata sanya ta fada masa mai zafi............shuru yay da waya a hannunsa yana mamakin katse masa hanzari da tayi, wannan maganar data fad'a ba har cikin zuciyarta ta fad'a ba saboda shi ba yaro bane ya fahimci kamar gatse tayi masa to idan ma hakane baya tunanin zai koma gidanta har sai ya tabbatar da zarginsa.....Wayarsa ya kashe ya dan juya bayansa gurin Zainab inda ita kuma tayi saurin rufe idonta kamar me bacci nan kuwa a kunnanta komai ya faru, murna da farin cikinta sai 'kara nunkuwa suke a"

cikin zuciyarta.

"Kwanciyar rigingine yayi a kusa da ita ya cigaba da nazari da tunanin al'amuran da suke faruwa, da"

wannan tunanin bacci ya daukeshi Kiran sallar farko a kunnanshi ya miqe da sauri ya nufi toilet

"wanka yayi ya fito daure da alwala, bashi da matsalar kayan sawa tunda ko'ina yana dasu, ya sanja jallabiya ya fita zuwa massalaci.......Zainab yana fita ta tashi da sauri ta bude kofa ta nufi dakin dasu aunty Balaraba suke kwana. Cikin murna da farin ciki take sheda musu abunda ya faru. Aunty balaraba murmushin samun nasara tayi tace""Ai na fad'a miki sharrina yafi kala dubu kinga dai lokaci kankani kin rikita musu lissafi jiya ya yini a kasuwa yau kuma ya kwana a gidanki haka zaki dinga kirkirar abubuwa iri iri duk ranar girkina dan ki raba masu hankali."" Zainab tace""Ai naji dadin shawarwarin ki wallahi dama ni babban burina na k'untatawa shegiya."" Aunty balaraba murmushi tayi ta miqe ta nufi toilet domin daura alwala Zainab zama tayi har suka idar da sallar suka cigaba da shirye shiryen makirci da sharrin da zasu shiryawa Najaatu. Abbah bai dawo gidan da wuri ba kasancewa ya tsaya gurin jana'izar wani"

"bawan Allah daya rasu a bayan gidanshi a massalaci a kasanar da mutuwar sai ya tsaya akayi jana'iza dashi sannan ya dawo gidan koda ya shiga gidan kai tsaye gurin

71 / 79