Chapter 67 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   67 / 79

198K to 201K   out of 235.1K words

yasa yaran suka ruga a guje suka rungumeta suna murna...Halisa na murmushi

"tace""Najaatu ke kika fara zuwa kenan sannu da zuwa karaso ki zauna."

A nutse ta riqe hannun Mussadiq suka karasa falon ta samu guri ta zauna a nutse ta kalleshi yana tsaye a

"inda yake yana mata wani irin kallo mai kama da harara ita tasan ko kallon menene sai ta basar tace""Abbah ina kwana? 'kin amsawa yay ya kalli Saddiqa da fad'in ta tashi maza taje gurin Zainab tace ta duba masa gilas d'insa a dakinta, Saddiqa tayi saurin miqewa domin tafiya aiken da yayi mata, Najaatu ba tayi zuciya ba ta sake gaishe shi, a dakile ya amsa ya bar gurin... murmushi kawai tayi ta juya suka"

cigaba da magana da Halisa......

*Littafin na kudi ne. !*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip

gruop#600 normal group #300 account..... 0542382124...Binta umar gtbabk...Idan kati zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

"79******Halisa na murmushi tace"" Ya kuma naganki a haka ina kika baro maigidan nawa.""? Tace""Yana"

"goye a bayan Yaya Ramlatu lokacin da zamu tawo yana bacci shine tace na kyaleshi kawai ta tawo dashi."" Halisa tace"" Ayya amma kin shiga gurin maijegon ko.""? ""Eh Hajia Rabi ma can na baro ta."" Shuru falon yayi kowa yana tunani a cikin ransa. Kamshin turaransa ne ya sanya dukkaninsu suka dago kai"

"suna kallonsa, Najaatu kallon sharia kawai tayi masa tayi kasa da kanta tana jin wani irin yanayi a jikinta,"

"a duk lokacin da zata kalleshi sai sonsa da kaunarsa sun sake karuwa a cikin zuciyarta, Abbah Abbas"

"kwata kwata baya tsufa kullum kara masa kuruciya ake babu wanda zai kalleshi yace yayi shekara hamsin a duniya saboda shi mutum ne dan gayu mai kula da kansa, Yanzu ma yayi ado cikin wani had'addan filtex irin na maza dark blue abinka da farin mutum sai yayi masa wani irin kyau, hula mai farin zanen zare yay amfani da ita, kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai shaninig yake, farin gilashin da yake sakaye a idonsa yayi masa masifar kyau, Najaatu ta dinga jin wani irin sanyi na ziyartar jikinta sha'awarsa ce take taso mata a jikinta sai ta shiga tunawa da irin zazzafar soyayyar da ya dinga nuna mata a lokacin da suke tare.......Muryarsa taji yana magana...""Yau ma kin bar yaron nan a gida ko ashe ke ba'a isa a fad'a miki magana guda kiji ba? yanzu meye amfanin saka wannan mayafin na jikinki da kin"

sani kin yar dashi a hanya dan bashi da wani amfani tunda gashinan a zahiri komai na jikinki ana gani.

Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abinda cewa ba kawai tana ganin kamar shurun shi yafi

amfani saboda gudun kada ta fada masa wata maganar yace tayi masa rashin kunya.

"Halisa tace"" Ni sai nake ganin ai ba wani abu bane dan ta bar yaron a gurin Yaya Ramlatu tunda yanzu"

zasu zo maganar hijabi kuma ka ajiyeshi a gefe yau daya dan tasa mayafi ai ba laifi bane tunda bata da nauyin kowa a kanta kuma ni wallahi banga abunda mayafinta ya nuna ba. tana yar dariya ta karashe

maganar.

"Yace."" Ni na gani ai tunda ke baki gani ba, sannan ni nasan tana da wata munufa ta yafa mayafin tunda"

"keda ita duk kun san bana son irin wannan mayafan marasa sirri saboda haka idan zaku tafi ki kar'bi hijabi gurin Halisa ki suturta jikinki baki burgeni ba idan dani kikayi Halisa tace""Ikon Allah shikkenan"

"sai tayi kwalliya dan kai kad'ai bazawara ce fa kuma kowa yasan zawarawa da 'yan mata gurin ado da kwalliya me zai sanya ka damu kanka. Yace.""Ai shine abinda nake so ki fahinta ta bud'e tsaraicinta ne"

"dan ni ko wani a waje ya gani yaji sha'awa to ni duk irin wannan basa burgeni."""

"Jin abinda yake cewa ne yasa tace""Haba Abbah yanzu dan Allah ina tsaraici anan.""? Tafada tana cire"

"mayafin jikinta tare da gyara zamanta a kan kujerar. Saurin dauke kansa yay sakamakon ganin tudun nonowanta da suka fito ta saman riga. Aunty Halisa tace""To nima dai haka na gani wallahi."" Najaatu ta"

"cigaba da cewa""Wallahi ni banyi kwalliyata dan kowa ba dan kaina nayi kuma Aunty Halisa ni bazan fitar"

"da tsaraicina saboda na samu mijin aure ba saboda nasan ko yanzu na bukaci aure zanyi tunda ni nasan kaina ba k'aramar mace bace."""

"Halisa ta dinga dariya tana kallonsa yana tsaye yana kallonsu, kowa dai yay zagi a kasuwa yasan da"

"wanda yake, shuru kawai yay musu ya zauna kan kujera mai cin mutum daya, agogon hannunsa ya duba, ya kalli Mussadiq dake fama da game yace""Jeka gurun Zainab kace tazo amma tazo da baby Ummi."""

Yaron ya ajiye game din da sauri ya tafi aiken da akai masa.

"Abbah shuru yay yana jin Halisa na fad'in ""Najaatu kin birgeni wallahi ai dama nace ke ba k'aramar mace"

"bace koda baki sa mayafi ba ya kasance kullum a cikin hijabi kike na tabbata ba zaki rasa miji ba haba ai ido ba mudu ba yasan 'kima."""

Shiru yay bai tanka ba dan ya lura Halisa naso ta tona masa asiri a gurin yarinyar shiyasa yaja bakinsa yay

shuru ya shiga girgiza kafafunsa. Halisa kallonsa take a fakaice tana 'boye dariyarta ita wallahi idan yana

muzurai a kan rashin gaskiya dariya yake bata wai shi lallai ba zai fito fili ya nuna cewar ya damu da yarinyar ba alhalin duk gashinan ya nuna alama a zahiri kowa ya gani.

Zainab ta shigo falon rugume da 'yarta ganin Halisa da Najaatu na hira cikin fahimtar juna yasa taji

"haushin hakan, dauke kanta tayi ta nufi gurun mijinta. Baby Ummi ya kar'ba daga hannuta ya"

"rungumeta a gefan hannunsa na hagu sai ya janyo zainab din ya d'ora a cinyarsa, ya rike kungunta da hannunsa na dama wayarsa ya bata yace tayi musu hoto Wannan al'amari ya duguzunma zuciyar"

"Najaatu da Halisa ba kamar najaatu da taji gurin na juyawa da ita, Ita kuwa Halisa d'aga murya tayi"

"tace""Me yasa ba kaje can gurinta kunyi hoton ba ai ina ganin kamar hakan sai yafi armashi."""

"Yace.""Akwai jamaa a gurun ne ko banda ikon nayi abinda nake so a inda na gada dama."" Ta'be bakinta"

"tayi tace""Aa kayi komai babu damuwa ai."""

"Ya kalli su Saddiqa da fad'in su taso suzo gurinsa, yaran suka kewaye shi Zainab na zaune daram! a"

"cinyarsa tana ta daukarsu a hoto farin ciki kamar ya kasheta hakika tayi farin ciki da yanda ya nuna musu cewa ita mai muhimanci ce a rayuwarsa, in da shi kuma anasa bangaran da biyu yake haka duk dan ya cuzguna musu, aikuwa ya hango tsantsar kishi da tashin hankali a idanun Najaatu dan har ja idanunta sukayi saboda tsabar bacin rai da takaici Sai da suka gama dauke dauke hotonsu sannan yazo inda"

"suke zaune da yake duguwar kujera ce sai ya shiga tsakaninsu, Najaatu kamar ta miqe ta bar gurin haka taji sai dai ta daure ta matsa gefe saboda jin yanda ya takureta. Baby Ummi ya kar'ba ya riqe yasa su"

"Saddiqa suka shigo kowa ya tsaya, sannan ya umarci Zainab din ta daukesu, hakan be mata ciwo ba saboda tasan ita ya fara nunawa muhimanci.....Zainab tayi musu kusan biyar ta miqa masa wayar, tare da fad'in ""Zata koma gurin 'yan uwanta! Babyn ya miqa mata tare da fatan a tashi taro lafiya. Ta 'karbi"

'yarta ta tafi ba tare da ta kula kowa a gurin ba. Shima tana fita ya miqe daga tsakiyarsu ya kama

"hanyar futa, babu wanda ya kulashi sai yaransa sune sukayi masa adawo lafiya."

Ya amsa cike da walwala da farin ciki yasan yau da Halisa Da Najaatu dukkaninsu ba zasu yini cikin farin

"ciki ba, wato harshi zasu sa a gaba sunawa dariya sun mayar dashi sakarai shiyasa yay musu haka. bayan fitarsa Najaatu mamaki take sosai da yanda Halisa tayi sanyi yanzu gabadaya ta mayar da rayuwa ba wani abuba, idan da lokacin baya ne ai bai isa yayi mata irin wannan rashin kyautawa a falonta ba gaskiya kamar da akwai cin fuska a ciki sai taga kamar ma ita ta fita jin haushin al'amarin amma dai"

yanda ta dauke kanta daga kan abunda yayi yasa taji ta burgeta mutuka

Taron sunan Zainab yayi kyau ya kuma k'ayatar anci ansha maijego ta fito sosai dan sai da tayi shigar

kaya kala goma cikinsu duk babu na yarwa abunda yay musu cikas kawai rashin Dan Asharrale amma dai duk da haka ba suyi bikin Lami ba sai da suka saka (Mp) mai kid'an tsiya suka dinga jin wakokin

*Gwanja* suna cashewa sai rawa suke suna murguda mazaunai maijego dadi ya isheta ta dinga yi musu liki Gabadaya d'abi'un 'yan uwan Zainab na banza ne 'ya'yan malam ne amma kuma sunqi halin

malam rashin arziki kawai suke yanda ransu yake so.

*BAYAN SATI BIYU*

"Al'amura suna ta gudanawa yanda ya kamata, ta bangaran Najaatu ta bude wuta sosai da ado da"

"kwalliya da ta daidaici lokacin zuwansa gidan zata fito ta zauna kan kujera tana baza kamshi tururuka...Ita kanta hajia sai da taji dad'in salon da yarinyar ta tsiro dashi tasan tabbas yin hakan zai sake janyo hankalinsa kanta, aikuwa dai a tsakankanin kwanakin daurewa kawai yake yi amma yarinyar na mutukar galabaitar da zuciyarsa dan dai kawai mutum ne mai dauriya da dauke kansa a kan abu shiyasa baya bari kowa ya gane halin da yake ciki, duk sanda zai shiga gidan yakan sakaye idanunsa da gilashi gudun kada kwayoyin idonsa su nuna abinda yake zuciyarsa. Najaatu halin ko'in kulan da yake nuna"

mata bai dameta ba kwalliya da sauran abubuwa ba zata daina ba tunda ta fahimci suna tasiri a tare dashi..... Da yake tana da yawan gashi mai kitso har gida take zuwa ta 'bata lokaci gurin tsantsara mata kunshi kuwa da ya goge zatayi wani Al'amarin daya sanya shi tunanin sanja shawara akan wacce

"sukayi da hajia yana ganin kamar d'aura auran a kurkusa shine kwanciyar hankalinsa idan yace zai cigaba da zama tsayin watanni yana ganin yarinyar hankalinsa na tashi to babu shakka zai iya shiga halin ni 'yasu dalilin daya sa ya yanke shawarar tunkarar abokinsa da maganar. Abbah Magaji yace""To"

"tunda kana ganin hakan yayi maka shikkenan sai kawai ka sanya a ranar da kakeso a daura auran."" Yace.""Yau insha Allah idan na shiga unguwar zan zauna da Malam da Alhaji a kan maganar."" Abbah"

"Magaji yace.""To shikkenan Allah ya sanya alkairi yasa anyi kenan."" Ya amsa da ameen ameen."

Najaatu duk wani abu da ake bata da labarinsa dan tunda aka tsayar da maganar daurin aure shi bai

"kirata ya fada mata ba kuma har yanzu babu wata kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tana dai jin maganar sama sama a gurun hajia da Yaya Ramlatu suma kuma babu wacce tace mata komai a kan al'amarin Ranar Lahadi da safe yazo gidan, Hajia na sama tana sallar walha Yaya Ramlatu da Hajia"

"Rabi sun tafi asibiti duba Salim ashe tun ranar da Naburago ya watsa masa kudin auransa ya kwanta ciwo kamar ba zaiyi rai ba, sai da aka kwantar dashi a asibiti sannan Sakina ta aiko aka sanar da mahaifiyarsa shine fa Alhaji yace maza maza suje su duba jikin nasa ai hannunka baya ru'bewa ka yanke"

"ka yar........Tana daki tana gyara jakar kayanta yay sallama a dakin, gabanta ya fadi dajin miryarsa,"

daidaita nutsuwarta tayi ta dan juya tana amsawa Idonsa kuri kan gashinta wanda akayi mata wani

"irin kitso mai kyau jelolin gashin sun dan sauka bayanta, Najaatu nada gashi daidai gwargwado gashi baki mai daukar ido. Ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta lalubi dankwalinta ta daura, a sanyaye"

"tace""Abbah sannu da zuwa."""

"Da sassauci a tare dashi ya amsa tare da neman guri ya zauna yana kallonta, gaishe tayi ta dan gyara"

zamanta tana jira taji da abinda yazo dashi.

"Gyaran mirya yay as'usul yace.""Naji gidan shuru tunda na shigo banji motsin mutum ba ina fata dai"

"lafiya.""? Tace""Wallahi tun safe Alhaji da Hajia Rabi yaya"

"Ramlatu suka tafi asibitin gadon kaya wai ashe Salim ne bai da lafiya yana can a kwance, ita kuma hajia"

"na sama tana sallar walha."" shuru yay na minti biyu kafin yace.""Tun yaushe ne baida lafiyar.''? Tace""Wallahi ban sani ba jiya Matar babansa ta aiko aka fad'a."""

"Allah ya sawwake."" yafada yana me tsurawa yatsun hannunta ido Dakin yay shuru kowa na tunani,"

"Abbah tunanin ta inda zai fara yake, da kyar ya iya kiran sunanta."

Ta daga kanta ta kalleshi kafin ta mayar dashi kasa

"""Kina da labarin maganar daurin auramu ranar jumaa mai zuwa kuwa.""? Gabanta ya fadi tayi saurin"

"kallonsa, girarsa ya daga mata ya lumshe idonsa, a hankali yace."" Naso na bari yaronki ya kara kwari amma na kasa saboda ni kadai nasan yanda nake jinki a cikin zuciyata, Halisa tace ba zan ta'ba samun nutsuwa ba sai dake sai nake kokarin k'aryata maganarta saboda ina ganin ke baki isa ki tauyemin rayuwata ta kowane fanni ba, ashe so ba haka yake ba, dalilin yin hakan da nayi yasa ya mayar dani sakarai mara nutsuwa gami da saninan muhumacinsa, hakika a cikin 'yan kwanakin nan ni kadai nasan irin azabtuwar da nake a kanki Najaatu zan sake auranki a karo na biyu inaso ki bani hankalinki da nutsuwarki da dukkanin kulawarki bana so a yanzu dani dake muyi auran Madadi inaso muyi aure naso"

"da kauna wanda zamu rayu a cikinsa cikin farin ciki da walwala har karshen rayuwarmu."""

"Wani irin farin ciki ya ciki mata zuciyarta hawayen farin ciki ya shiga sauka akan kumatunta, mirya na"

"rawa tace""Abbah ka daina kokwanto akaina a yanzu zan aureka na zauna da kai tsakani na da Allah, Wallahi ban ta'ba kaunar wani namiji ba kamar ka, Abbah bani da za'bi sai naka bani da bakin godiya a gareka kayi min dukkanin sadaukarwa a rayuwata inaso yau na fad'a maka da bakina cewar ina sonka wanda ban san iya adadinsa ba, ina rokonka daka yafe min abubuwan da suka faru a baya kuruciya ce da"

"kuma qaddara yanzu zan zauna zaman aure da kai tsakani da Allah da kuma so da kauna insha Allah."""

"Ya dinga wani murmushin farin ciki da jin dadi yana wani lumshe idanunsa a kanta, mirmushi tayi ta"

"sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da hannayenta yace.""Nayi farin cikin jin wannan magana taki Najaatu"

"ashe yanzu ina da babban matsayi a cikin zuciyarki ban sani ba, a gaskiya dole wannan karon nayi shiri"

"mai kyau inaso na nuna miki ni daban nake da sauran maza sai kin kasance a matsayin matata zaki gazgata hakan."" Yakare maganar yana jifanta da wani shu'umin kallo...Kunya ce ta rufe ta da sauri ta rufe"

fuskarta tana dariya.

*ALHAMDULLILAHI FAD'AN MASOYA HUTU NE INJI BAHAUSHE*

"Salim zazza'bi typoid ne yaci karfinsa inda har ya ta'ba masa hanjin jikinsa,wannan bayanin likitan dake"

kula dashi yayiwa Alhaji hankalinsa ya tashi Yaya Ramlatu kuwa kuka kawai take tana fad'in ''Yanzu wata da wattani d'anta yana kwance yana ciwo a kasa fada mata wato da sai dai taji labarin mutuwarsa

"kenan, babu shakka abunda Sakina tayi mata bata kyauta ba"

Ita dai Sakina hakuri kawai take bata dan gabadayan su Hankalinsu ya tashi jin cewar hanjin cikinsa ya

'bule dole sai anyi masa aiki.

"Abbah Abbas ma da yazo dubashi sai da hankalinsa ya tashi, a take yasa hannu ya kuma biya zunzurutun"

"kud'aden da asibitin ke bukata yace maza a shiga dashi teater , Allah sarki Yaya Ramlatu kuka kawai take dan gani take tamkar gawarsa za'a fito mata da ita, sai dai kuma ba a nan take ita cuta ba mutuwa bace mai lafiya ma yana iya mutuwa ya bar wanda yake da shekara goma yana jinya. Lafiya lau aka fito da"

Salim anyi aiki cikin nasara yanzu abinda yay saura kula da shan magani akan 'ka'ida.

*****

Alhaji Aminu Dan jarida da kyar ya samu gurin zama bayan fitowarsu daga prison sai kowa ya gudunsu

"dalilin daya sa kenan ya harhada 'yan kudaden da suka rage masa ya gudu k'yauyen zaria shida iyalinsa ya samu ya siyi wani lalataccen gida, sauran kudin suka siyi kayan abinci Mommy ta fara sanar sai da"

gwanjo a cikin kyauyen sai ta shiga cikin gari ta siyo tazo ta baza a kofar gidan jama'ar garin na siya da

wannan sanaa suke rufawa kansu asiri. A lokacin

Munira ta dade da haihuwa inda ta haifi Da namiji a hannun kanwar Momynta Laila. 'Kaskanci da

"wulakanci babu irin wanda Munira bata gani ba, taci wuya sosai wanda sai da ta kai ta kawo ta daina fitowa waje dan da ta fito za'a soma yi mata waka mai cikin shega babanta karto d'an uwanta 'barawo wasu yaran ma har jifanta suke wannan dalilin yasa take zama a gida taci kukanta ta koshi Lailah ta ta cigaba da azabtar da ita. Tunda ta samu labarin dawowar iyayenta ta gudu ta koma gurinsu, dan gwara"

tayi rayuwa a cikin kyauyen da suke a kan azabar da Laila take gana mata.

*RANAR JUMA'A*

Ranar aka daura auran Abbah Abbas da Najaatu a karo na biyu daurin auran yayi albarka sosai dan ya

samu halartar manya manyan mutane

daga bangaran Alhaji Abbas mai girma governor dashi da mukarrabansa ma sun samu hallatar daurin

auran Abbah Abbas ranar kasa rufe bakinsa yay sai murmushi yake yana gaisawa da jamaa cikin walwala da farin ciki.........Najaatu ta sake zama matarsa a karo na biyu ai dole ya nunawa Ubangiji farin cikinsa..

*'Kawata kada kiyi wasa da wanke bakin ki domun ana saurin gane tsabtar mutum ta

ha'koransa. Akwai damuwa ace wai idan kikayi brush da safe ba zaki

67 / 79