Chapter 60 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   60 / 79

177K to 180K   out of 235.1K words

a gurguje ya nufi gidan mutuwar domin yayi gaisuwa ya wuce

"harkokinsa, gabad'aya bai sanya lamarin Naja'atu a cikin ransa ba ballantana ya dameshi yana fitowa daga inda take ya ajiyeta a gefe guda ba zaije ko'ina da damuwarta ba bare ta hanashi gudanar da abubuwan da suke gabansa."

"Koda su hajia suka dawo kasa gane kanta sukayi, hajia ta dinga tambayarta ko wani abu na damunta,"

"girgiza kanta kawai takeyi tace""Babu komai baccin data yini tanayi ne ya sanya yanayin ta ya sanja to hajia dai taji ne amma bata amince da maganar ba, haka yamma tanayi data fahimci ya kusa shigowa gidan sai kawai ta shige daki ta kwanta bata so ta ganshi saboda gudun abunda ka iya zuwa ya dawo"

tana ganin zata iya fashewa da kuka mutukar zata kalli fuskarsa.

To shima a nasa 'bangaran bai damu da rashin ganinta a falon ba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa sai

"kawai ya ajiye ledojin hannunsa wanda ita tasan ko na menene kayan ciye ciyen Naja'atu ne wanda yake siyo mata kullum ta Alla. Sallama yayi mata yace.""Idan ya fito daga massalaci gida zai wuce ba zai dawo"

"ba. Hajia tayi masa fatan alkairi tare da bashi saqon gaisuwarta gurin su Saddiqa, ba tare da damuwar"

komai ba ya bar gidan.

"Koda ya isa gidan nasa kai tsaye gurin Halisa ya nufa duk da cewar ba itake keda girki ba, sai da ya duba"

ta sosai sannan ya fito ya nufi gurin Zainab Ita da yaran suna zaune a falo gwanin sha'awa sukayi masa

"sannu da zuwa ya amsa a sake, yana kallon Zainab yau tayi kwaliya sosai sai dai babu walwala a tare da ita, bece mata komai ba ya nufi dakinsa, ta mike tabi bayansa tana wani cika da batsewa."

Ya tu'be kayan jikinsa yana kokarin shiga wanka ta shigo dakin sai ya tsaya yana kallonta har ta qaraso ta

"samu guri ta zauna tare da fadin."" Abban Mufida sannu da zuwa."" Ya amsa yana sake nazarinta yace.""Da alama yau akwai abunda ke damunki na karanci rashin walwala a fuskarki ina fatan ba yaro na bane yake"

"takura miki."""

"Girgixa kanta tayi tana dan ta'be bakinta tace""Idan shine yake takura min ai da sauqi Abban mufida"

"zuciyata ta kasa nutsuwa kwana biyu sai tunani nake da wasiwahsi dan Allah kada ka dauki maganata da wata manufa naga kamar kana so ka dawo da Naja'atu gidanka saboda dawainiyar da kake mata har taso tayi yawa wani abun ma sai dai mu samu labari, nida aunty Halisa kullum cikin tunani muke idan dawo da ita za kayi gwara kawai ka fad'a mana mu sani dan ina ganin kamar 'boye-'boyen da kake mana sam"

bashi da wani amfani.''

Tunda ta soma maganar ya zuba mata ido yana kallonta mamaki yana kasheshi! shi dai tunda Allah ya

had'ashi aure da qananun yara yake ganin rashin kunya iri iri Wai Zainab ce ta turkeshi take kokarin sai

"ta 'kure shi a ganinta yana 'boye musu abinda ke tsakaninsa da Naja'atu, idan tunaninsu kenan to babu"

shakka zai basu mamaki! Dauke kansa yayi daga kanta ba ta tare da yace mata komai ba ya nufo toilet cikin d'umbun mamakin yarinyar.

*NA DAWO *

*'Kawata matso kiji wata magana mai muhimanci nasan kin san da cewar yanxu muna lokaci na sanyi

jiki na bushewa kammani na sauyawa to bari kiji wata magana maza a irin wannan lokacin jaraba da

"fitinarsu take tashi, me ya kamata kiyi domin ganin kin gyara kanki da kowane lokaci mijinki na samun"

nutsuwa dake Kada ki mayar da hankalinki kacokan kan gyaran fatar jikinki baki inganta ni'imarki ba Ina amfanin fatar ki tayi luwai luwai kina gayu da tunkawo kuma sai dare yayi maigida yaji guri a

bushe kada ki sake haka ta faru 'Kawata! kamar yanda zaki kula da fatar jikinki to ki kula da Ni'imar ki ya kasance kullum idan maigida yazo yaji zam!zam kada kiyi wasa da shan ruwan kaninfari had'e da shan kayan marmari ina ganin koga wannan kika tsaya zaki gamsar da maigidanki Wannan itace

tsarabar da nake tafe da ita *

Vip gruop#600 normal group #300 account.. 0542382124.//Binta umar gtbank .....WhatsApp number....

07084653262

*MADADI*

70Zainab na zaune tana sa'kawa da kwancewa ya fito daga toilet yanda taga fuskarsa a had'e! shine

"yasa jikinta mutuwa gabanta ya dinga fad'uwa, tana kallonsa har ya kimtsa jikinsa ya kama hanya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka mata ba...Jikinta a mace ta miqe salo salo tabi bayansa falon gurin cin abinci ta sameshi a zaune yana duba karamar wayarsa Saddiqa na kokarin zuba masa abinci."

"Da sauri ta karasa gurin, cikin kokarin wanke kanta ta kar'bi plate din dake hannun Saddiqar tace taje ta"

zauna.

"Abbah duba wayarsa kawai yake yi bai kalleta ba har ta gama zuba masa abinci ta ajiye masa a gabansa,"

ya ajiye wayar a nutse ya dan yanyo plate din gabansa yayi bisimillah kamar koda yaushe ya fara cikin abincin.

"Ta kalleshi a sanyaye tace""Abban Mussadiq naga kamar maganata ta 'bata maka rai dan Allah kayi hakuri"

"wallahi ni haka nake bana iya ajiye abu a raina."""

"Yayi mata wani kallo mai kama da harara yace.""Surutu da fad'i ba'a tambaye ki ba shine yake damunki"

"ba abinda kika fad'a ba, Okey zan kira Halisa yanzu itama naji ta bakinta akan maganar da kika fad'a min tunda kun dauke ni munafiki wanda ke 'boye muku tsakaninsa da Naja'atu."""

"Da sauri tace""Wallahi ba haka nake nufi ba shiyasa fa tun farko kafin na fad'i maganar nan sai da nace ka"

"fahimceni amma meye sai an kira anty Halisa dan Allah kada ka kirata."""

"Yace.""Ai a inda ba qasa nan ake gaddamar kokawa tunda kince keda ita kuna cikin wasiwahsi kullum"

"kuna tunani da zargina kan na 'boye muku wani abu to dole itama tazo ta fad'a min da bakinta kamar yanda kika fad'i naki."""

"Zainab idonta ya ciko da kwalla! Tunda suke basu ta'ba zancan Naja'atu da Halisa ba, tunda ta ta'ba yi"

mata maganar a gidan Alhaji Halisan ta nuna bata son maganar bata qara tunkararta ba ita kadai abun ke damu kawai ta sako sunan Halisa a cikin maganarta ne wai ko zai dauki abun da muhimanci ya fad'a

musu abunda ke zuciyarsa.

Yana kammala cin abincinsa ya barta a gurin yaje ya zauna kan kujera yana kiran wayar Halisa. Zainab

"kasa motsawa tayi tana zaune a inda take har Halisa ta shigo falon.....Umartar su Saddiqa yayi dasu je su kwanta, yaran suka miqa da sauri suka nufi dakinsu."

"Halisa ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa itama tunda taga yanda yasha kunu sai tasha jinin jikinta,"

barka da dare tayi masa taja bakinta tayi shuru.

"Ba tare daya juya ba yace.""Zainab zo nan."" Ta miqe a hankali taje ta zauna nadama da dana sani kawai"

takeyi data san tozartata zaiyi a gaban kishiya da ta daure ba tayi masa maganar ba. Ya kalli Halisa a

"kaurare yace.""Ashe idan bana nan munafurcina kukeyi? Har kuna zargina akan ina 'boye muku tsakanina da Naja'atu shin idan nace zan dawo da ita akwai wacce ta isa ta hanani dawo da ita a cikinku.""!"

"Halisa ta bud'e bakinta cike da mamaki da tsoro tace""Yaushe akayi hakan Abbah Mufida wallahi duk"

"wanda ya fad'a maka maganar nan karya yake ni meye nawa a ciki idan ka dawo da Naja'atu gidanka gaskiya ka 'kara yin bunkice a kan maganar nan.."""

A tsanake ya kalleta ya kalli Zainab da tayi tsuru tsuru nan ya tabbatar da cewar 'karya yarinyar tayiwa

"Halisan, yace.""Ba wani ne ya fad'a min ba Zainab ce gata nan tana jinki abunda yasa kuma na yarda da maganarta saboda ina ganin zaki iya aikata hakan tunda kema ba qaunar Naja'atun kike ba."""

"Halisa tace.""To ikon Allah idan da ranka kasha kallo ina zaune anyi min sharri yanzu ke dan Allah dan"

"annabi Zainab yaushe mukayi wannan maganar dake ashe kin manta maganar da mukayi dake a gidan alhaji, haka kawai zakiyi maganarki sai kisa sunana.""!"

"Ganin yanda Halisan ta hasala! ne yasa ya daga mata hannu yace.""Ya isa! kina nufin ba kiyi ba kenan.""? A"

"fusace! tace""Wai dan Allah wace irin magana kakeyi? da da yanzu ba d'aya bane kai kanka ka san yanzu na gyara kuskurena sannan naji kana wata magana wai bana qaunar Naja'atu shiyasa zan zauna da Zainab mu zageta! a kan wane dalili ni Naja'atu da iyayenta basuyi min komai ba wallahi saboda haka ko"

"yau ka dawo da ita gidanka ina maraba da ita."""

Tana gama maganarta ta miqe rai a 'bace! ta fita daga falon Maganganun da Halisa tayi ya nuna

"masa gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta, kuma yaji dadin hakan Halisa ta daina adawa da Naja'atu ta barwa Zainab, a nutse ya juya yana kallonta tayi tsilli tsilli kunya da nauyi duk sun rufeta sai yanzu ta gane itama wauta da kuruciya na damunta to idan ba haka yaushe ma zata turkeshi da irin wannan"

maganar.

"""Zainab."" Ya kira sunanta tare da tsira mata idonsa, ta amsa murya na rawa. Yace."" Saboda ina yiwa"

"Naja'atu hidima kike ganin kamar zan dawo da ita gidana."" Fashewa tayi da kuka tace""Aa wallahi."" Yace.""Hakane mana! kina kishi da Naja'atu alhalin zama bai ta'ba had'aki da ita ba, to ki kwantar da hankalinki kinji ko dik wata hidima da kika ga inayi mata inayi ne dan Allah da manzonsa da kuma tausayawa abinda ke cikinta, amma babu maganar na sake zaman aure da ita! saboda haka ki samu nutsuwa ki daina wasiwahsi kamar yanda kika fad'a! Sai dai da kowane lokaci zan iya kawo muku abokiyar zama dalili ni mutum ne meso ya cikasa sinnar ma'aiki Annabi Muhammad (slw) inaso kafin Allah ya dauki raina na had'a mata hudu a gidana su haifa min tarin yara masu albarka saboda haka kisa"

"a ranki cewar akwai sauran abokanan zamanki da zasu zo mutukar Allah ya qaddara min hakan."""

Zainab shuru tayi tana goge hawaye itakam wauta da rashin dubara na damunta amma daga yau tayi

"alqawari zata dinga kiyaye harshenta domin gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, dan gaskiya itama ba"

"laifinta bane kishin naja""atu ne ya tunxura mata zuciyarta amma dai za tayi kokarin ganin ta dauke kanta akan dukkanin abinda zata gani ko taji labarin yayiwa Naja'atun.."

To kamar yanda yayi mata alkawarin zai siya mata waya hakan ya faru dan Abbah Abbas waya mai kyau

"da tsada ya siya mata sabuwa dal a kwalinta, ranar da ya bata wayar tayi ta murna da farin ciki tana masa godiya. babu wanda ta fara kira da wayar sai Mmn Sajida. suka shafe mintina da dama suna hira A gaskiya Naja'atu tayi farin ciki da samuwar wayar a hannunta dan sabida tasan ba qaramin kewa zata"

d'ebe mata ba.

******

"""Kaga Salisu ina jin tsoron ranar da asiri zai tuno ni dai da zaka bi ta shawarata da kaje ka samu mutumin"

"nan kayi masa bayani watakila ma yace mu rike kudin tunda nasa ne ."" Mahaifiyar Naburago ce take wannan maganar"

"Gyara zamansa yayi yana kallonta yace.""Haba Mama ki daina tsoro mana babu ta yanda zaayi asiri ya"

"tuno kudi sun riga sun shigo hannuna."" Tace.""A'a ni daina nafi so kaje kayi masa bayani wannan kudin ba zasuyi maka albarka ba tunda na sata ne kaga kenan sata ta saci sata kaima idan da tsautsayi wani sai ya damfare ka tunda dai kasan inda zaka samu mutumin nan to kaje kayi masa bayani ka bashi hakuri ni na"

"fada maka ba zaice komai ba watakila ma yace ka rike kudin."""

"Naburago yace.""Mamma wannan shawarar taki gurguwa yace yama za'ayi na samu kudi a sama kice"

"naje fad'awa wanda yake dasu ni ba zanje ba wallahi, na riga na shirya tsaf akwai sana'ar da nake so na fara dasu sana'a ce mai inganci kuma ina da ya'kinin zata kawo min kudi dan lokaci guda zan zama multi mollonia."".. Girgiza kanta kawai tayi tace.""Shikkenan ai tunda kaki daukar shawara."" Miqewa yay ya kama hanya ya fita, kai tsaye ya hau sabon babur dinsa wanda ya siya dubu dari biyu da hamsin, sannan yayi sabbanin d'unkuna ya kuma bibbiya bashin da ake binsa, daga haka sai kawai ya cigaba da facakarsa da kudin, dan ita kanta wacce tayi sanadiyar samuwar kudin da kyar yake bata wani abu, Naburago ya tattare kudin yayi bukatarsa dasu yanzu saura dubu dari takwas dasu yake so ya fara sanar cah-cah dan yana ganin yanda sana'ar take sanya mutane da yawa suyi mahaukanta kud'i to shima dama rashin kudi a hannu ne yasa bai fad'a harkar ba tunda yanzu ya samu dama to zai shiga a dama"

"dashi, babur dinsa ya hau ya nufi mahad'arta su."

*****

'Bangaran 'Yar Sa'adu kuwa sai da tayi sati a barikin sojoji suna azabtar da ita sannan suka saketa ta

"dawo gidanta a mutukar galabaice jikinta duk yayi rud'u rud'u da shatin bulala abinka da farar mace ko'ina yayi tabo a jikinta, haka ta kwanta ciwo duk a cikin matan dake mata fadanci a kara rasa wacce zata zauna tayi jinyarta, sai da ta dan samu sauqi ta tattara komatsanta ta tafi garinsu tana ganin ba zata iya cigaba da zama ba haka kawai tana zaune wata ta sake janyo mata masifa gwara ta koma"

garinsu ta cigaba da harkokinta a can.

****

"To kwanaki na tafiya wattani na shiga suna mutuwa, komai na tafiya ne da ikon Allah da kuma"

"amincewarsa Naja'atu al'amuranta sun tsananta dan dab take da haihuwa cikinta ya shiga wata na tara har yayi kwanaki! gabadaya hankalin wanda yake kusanci da ita ya tashi saboda tunda cikin ya shiga wattanin haihuwarsa ta kumbura mussaman qafafunta, duk da Likita ya dubata ya tabbatar musu da cewar babu matsala hankalinsu bai kwanta ba. Abbah Abbas da hajia sunfi kowa tada hankalinsu a kan al'amarin Baba malam da baba talatu kawaici da alkunya yasa duk damuwar da suke ciki game da 'Yar"

tasu sun kasa nunawa gabad'aya ma Baba talatu d'auke kanta tayi da kanta sai dai kullum cikin yi mata addua take......B'angaran Abbah Abbas kuwa gudun zargin da mutane ke masa yasa yake boye damuwarsa akan halin da Naja'atu take ciki amma zahirin gaskiya yana cikin tsanani da damuwa mussaman idan yazo gidan ya ganta a jibge a kan kujera! sai dik jikinsa ya mutu kullum haka yake yini ya kwana cikin alhini da jiran tsammani yanda ma ya damu da haihuwar Naja'atu kamar bai damu data Zainab ba su kansu matansa sun fahimci hakan sai dai kowacce na kokarin dauke kanta akai amma hakikanin gaskiya abun yana damunsu mutukar aka cigaba da tafiya a haka to suna cikin matsala gwara

ya dawo da ita gidan hankalinsu zaifi kwanciya akan ya dinga shiga halin damuwa akanta.

Ranar Alhamis da daddare ta farka da ciwon haihuwa mai tsanani dama tun sanda cikin nata ya tsufa

"Yaya Ramlatu take kwana da ita a daki, jin motsinta yasa ta tashi da sauri tana tambayarta, Naja'atu na zufa tana kiran sunan Allah tace""Watakila haihuwa zanyi dan ciwon da nake ji yafi na kullum."" Ya Ramlatu tace""To ikon Allah bari na kira hajia sannu kinji ko."" Fita tayi daga dakin da saurin gaske Tare suka dawo dakin da hajia da sauri ta d'ago ta ta rungumeta a jikinta, tana mata sannu!"

"Yaya Ramlatu ta shiga hada kayan haihuwa! Hajia t""Ta kalli Ramlatu da fadin''Ki sanar da hajia Rabi Naja'atu na kan gwiwa."" Ya Ramlatu da sauri ta futa daga dakin Hajia ta rike ta sosai tana tofa mata"

"adduoi lokacin ita Naja'atu, ciwon ya tsananta dan dab take da haihuwa, shiyasa ta kasa tsugunawa"

sai kawai ta silale a gurin ta kwanta tana wani irin kifkif da idanunta! hannunta tasa ta janyo na hajian tana jan salati! Hajia ta shiga tashin hankali ganin irin abinda Naja'atun takeyi sai hawaye ya soma zubo mata addua take Allah y yanke mata wahala.....Hajia Rabi da Ramlatu na shigowa faya ta fashe! sai

yunkuri kawai sukaji tana wani irin nishi!! da sauri suka rufu a kanta kowanne na iya bakin

kokarinsa. Naja'atu Ganin Yaya Ramlatu itace mai kwari a cikinsu sai kawai ta d'amko ta ri'keta gam!

gam! a tare suka dinga nakud'ar suna nishi! tare! Sosai Ramlatu taji jiki ta kuma tabbatar riqon bana Naja'atu bane na mala'iku ne. Cikin ikon Allah da hukuncinsa yaro ya fad'o a cikin zanin da suka rufa

"mata, sai kawai kukansa sukaji Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu suka had'a baki gurin fad'ar"

"""Alhamdullhi."""

*Littafin na kudi ne. !*

Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin littafin ga yanda abin yake. Vip

group #600 normal group #300...account... 0542382124...Binta umar gtbank. Idan katin waya zaki tura

kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*BA HARAM BANE!*

71 Yaya Ramlatu ce tayi dubarar d'auko babyn dake ta tsanyara kuka alamu sun nuna cewar yaron yana

"da qoshin lafiya dan tunda ya sauka ya cika musu kunne da kuka.........Hajia Rabi tace""Namiji ne ko mace.""? Yaya Ramaltu na murmushi tana sake riqe yaron a hannunta tace.""Namiji ne gashinan tubarkallah masha Allah."" Hajia ta rike Naja'atu sosai a jikinta tana fad'in ""To Allah ya raya shi tafarkin addinin musulunci."" Suka amsa da amin amin Yaya Ramlatu ta nad'e yaron a towel ta ajiyeshi kan"

gado da sauri tazo ta taimakawa hajia

Rabi gurin rirriqe Naja'atun dake ta wani irin nishi!!! 'Yan dabaru suka shiga yi mata domin mahaifa ta

fad'o amma abun yaci tura

Hajia ganin lokaci yana ja mahaifar taqi ta fad'o sai kawai ta yanke shawara akan su tafi asibiti zaifi

"kwanciyar hankali......... Hankali a tashe Ramlatu ta bude wardrobe cikin sauri ta dauko riga da zani na atampa, hajian ta kar'ba tana kokarin sanya mata Allah

60 / 79
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted