Chapter 31 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 79

90K to 93K   out of 235.1K words

na'isa irin kwanakin baya."

"Tace""Wallahi babu inda zanje to me akayi min a gidan da zanje kofar na'isa."

"Yace.""Ai ba dole sai anyi miki laifi ba nasan ki da rawar kai ne idan kika je kofar na'isa kin san labari zai"

"same ni sai na 'bata miki rai."""

"Tace""Insha Allahu ba zani ba."

Juyawa tayi zata fita ya ri'ko hannunta ta juyo tana kallonsa.

Gani tayi yana mata wani irin kallo.

'bata rai tayi ta dauke kanta ta gane kome yake nufi

"Jin hucin numfashinsa dai-dai wuyanta yasa tayi saurin fizge hannunta ta bude dakin ta fita, lallai ina zata"

"iya tsayawa ya tayar mata da hankali ya barta da wahala...Yaji takaicin abinda tayi masa dalilin da yasa da ya fito bai ko kalli inda suke zaune ba ya nufi kofar fita, Halisa da azama tabi bayansa, ita kuwa Naja'atu tana jin yaran nayi masa a dawo lafiya tayi shuru da bakinta."

"Salim na zaune saman mota ya hangi fitowarsu, sai ya sakko daga motar yana wani sunkuyar da kansa"

"kamar wani mutumin kirki! Yace.""Kawu barka da asuba.'' Abbah ya mika masa hannu suka gaisa Salim ya kalli Halisa yana murmushi yace.""Big anty an tashi lafiya."" Tace""Lafiya kalau Salim ina Yaya Ramaltu.'' Yace.""Tana nan kalau."" Tace ka gaisheta! Yana kokarin budewa Abbah Abbas mota yace""Insha Allah zan"

fada mata...Halisa bata koma cikin gida ba sai da taga motarsu ta fita daga gidan tukkuna

"Tana kokarin shiga sukayi karo da Naja'atu zata fita. Tace""A'a naja'atu ina zakije kuma.""? Ko kallonta ba"

"tayi ba ta kama hanyar fita...Halisa tace""Naja'atu kina ji ina miki magana kin share ni."

"Hannu ta daga mata a fusace! tace""Kinga Anty Halisa bana son gulma da munafurci dan Allah bake kike"

aurena ba ballantana ki dameni da tuhumar ina zani aikin banza aikin hofi kawai wallahi kada ki dauka

"duk abinda kike bana ganewa ina sane, kuma ke kika damu da wannan tsohon har kike satar kwana ki rubuta ki ajiye na kusa fita na bar miki gidanki dan banga gurin zama a cikinsa ba."""

Halisa ta bude bakinta tana kallonta cike da mamaki! Naja'atu buge zaninta tayi ta bar gurin Halisa ta

juya tana wani irin murmushi ta nufi cikin gidan ranta wasai bukatarta ta kusa biya.

Dakinta ta shiga ta dauki wayarta ta kira maigidan nasu.

"Yace""Allah yasa dai lafiya. cikin alhini da yanayi na a tausaya mata tace""Yanzu yanzu na Naja'atu ta gama"

zagina saboda kawai na tambayeta ina zata je shikkenan take zagina harda kiran ka tsoho da fadin cewar na fad'a maka wai a kurkusa zata bar maka gidanka domun kuwa ba taga gurin zama ba.

"Cike da mamaki yace.""Naja'atu tace fada miki hakan."" Salim dake driving yasa kunne sosai jin an kira"

sunan Naja'atu.

"Halisa tace""Kwarai kuwa wallahi ni kaina banji dadi ba me yayi zafi! ni banga abin'ki a tattare da kai ba."""

"Jikinsa a sanyaye yace.""Koda ta dawo gidan kada ki sake shiga sabgarta ballantana ta sake zagin ki ki rabu da ita dani take zancen zan dawo na sameta. Halisa farin ciki ya wanke mata zuciya tace""To"

"shikkenan Yallabai Allah ya dawo mana da kai lafiya."" Ya amsa da amin tare da kashe wayarsa."

Naja'atu kam tana zama a gidan anty maryam kuka tasa. Anty maryam ta zauna kawai tana kallonta

"dan babu yanda ba tayi da ita ba akan tayi shuru tayi mata bayanin abinda ke faruwa amma taki tayi shuru sai da taga dama tukkuna ta share hawayenta tana kallon aunty maryam din tace""Anty wallahi bashi da lafiya."" Anty maryam ta zuba mata ido tana kallonta da fadin""Waye bashi da lafiya."" ? Kai tsaye tace""Abbah Abbas mana Allah aunty yana da matsala babba ni bazan iya zama ba dan cutata kawai"

yake. Anty maryam duk shekarunta kasa gane inda maganar ta dosa tayi.

"Tace""Kinga ni kiyi min bayani yanda zan fuskanta wace irin rashin lafiya yake.""? Hanci taja tace""Baya iya"

"biya mun bukatata kullum sai dai ya tayar min da hankali ya barni cikin sha'awa saboda haka tun kafin tafiyar nan tayi nisa ku san yanda zakuyi ku warware shi."""

"Anty maryam tayi 'kasa da kanta kunya kamar ta sa ta nutse a gurin, ashe naja'atu bata da kunya haka"

har ta iya zuwa tazo tana yi mata wannan maganar gaba da gaba lallai 'yan matan zamani halinsu sai su!

"Sai da ta aro jarumta tukkuna ta dago kanta tana kallon Naja'atun ta 'bata fuska sosai tace""Ke Naja'atu"

bana son sharri wallahi! Ni tunda nake da Halimatu da Halisa babu wacce na ta'ba jin tayi wannan maganar! Sharri ne kawai irin naki! sannan har yaushe akayi auran naku da zaki tantance yanda al'amarin yake har kike cewa baya biya miki bukatarki wallahi kiji tsoran Allah.

"Itama shan kunu tayi tace""Aunty Maryam ya zaki fad'i wannan maganar ? nifa macace kuma ina da"

sha'awa sai kuma kice wani abu ni wallahi gaskiya na fad'a banyi masa sharri ba ki fadawa mijinki a san yanda za'ayi.

"Anty Maryam ta rike bakinta tana kallonta cike da mamaki tace""Wai ke baki da hankali ne? wai kike"

"tunanin zan fadawa wannan maganar? Humm! ba dani ba ke idan kina ganin kina cutuwa sai ki tsaya yayan naki ya dawo ki fada masa amma ni babu ruwana. Cikin takaici tace""To shikkenan ai kuwa wallahi"

in tura ta kai bango sai na fad'a! ai sune suka cuce ni yama za'ayi su auran min tsoho mara kuzari ni kam

ba zan iya wannan takaicin ba.

Anty maryam shuru kawai tayi tana kallonta mamakin ta kawai take lallai *Zamani* Indai akace maka

*Zamani* to magana ta 'kare ita kam tana jin koda mijinta baya iya gamsar da ita zata hakura ta zauna sabida tana jin kunyar taje gida ta fad'a to taya ma zata farayi wa iyayenta bayani

*(Wannan ba dabara bace Aunty Maryam akwai 'kwaruwa ace namiji baya biya wa matarsa bukatarta

"sai dai ya biya tashi, akwai matsala babba! matsalar da kan iya janyowa mace fad'awa ga halaka! mata da yawa suna nan sun fad'a harkar madigo duk sabida irin wannan matsalar akwai wanda kuma suke bin mazan waje da auransu da komai amma kuma mazajen nasu sun zama hoto a gurinsu. 'Yar uwa idan"

kina fuskantar irin wannan matsalar kada ki zauna kiyi ta cutar kanki ko kuma ki jefa kanki ga sa'bon Allah! Akan ki sa'bi Allah gwara kin kashe auran kije kiyi wani shine yafi miki alkairi ko kuto kika kai

al'kali ba zai ce miki don me ba sabida shima yasan matsalar gagarima ce. Allah kasa mu dace)*

"Aunty Maryam ta mike da sanyayyan jiki ta kalli Naja'atun tace""Ni dai duk wannan surutun da kikeyi"

"babu wanda na dauka a ciki dan sabida nasan karya kikewa bawan Allah nan wallahi ki sanja halinki Naja'atu."""

*(Eh gaskiya kam Naja'atu karya tayi wa Abbah Abbas lafiyarsa lau kawai Halisa ce tayi musu farraqu)*

"Ganin anty maryam din na kokarin shiga kicin yasa tace""Dan Allah dan bani aron wayarki zan kira"

"kawata."" Anty Maryam tace""Tana dakina ki shiga ki dauka."

Da sauri ta mike ta nufi dakin nata...Kan mirror taga wayar ta dauka tare da zama bakin bed

dinta...Numbar Munira tasa bugu daya tayi ta daga wayar.

"Munira najin muryar Naja'atu tace""Kamar *Na'ja'atu Abbas qofa* Naja'atu tace""Eh nice kinyi mamaki"

"ko."" Munira tace""Eh lallai nayi mamaki Naja'atu yau kin tuna dani kenan ai wallahi baki da kirki Naja'atu."""

"Murmushi tayi tace""Nasan dole dama ki fadi haka amma dan Allah kiyi hakuri kinji ko wayata ce ta lalace"

"shiyasa kika ga na kiraki da wannan numbar wayar aunty na ce."""

"Munira tace""Babu komai ' k'awata ya kwana biyu! wallahi baki yanda nake ji ba a duk sanda na tuno"

rayuwarmu ta makaranta.

"Naja tayi murmushi tace""Wallahi nima haka munira ina kewarki sosai cikinmu duk ke kad'ai ce mai"

"zumunci kinyi kokarin ziyartar inda nake nima a lokaci da nake shirye shiryen kawo miki ziyara wata kaddara ta gifta min."""

"Munira tace""Innalilihi Naja'atu me ya faru da rayuwarki Naja'atu ta goge hawayen dake zubo mata ta"

"shiga bata labarin abinda ya faru bayan rabuwarsu. Munira tace""Yanzu dama Mamma Halimatu ba"

"itace ta haifeki ba.""? Tace""Wallahi munira nima ban sani ba sai bayan mutuwarta. Munira tace""Ubangiji"

"Allah ya jikanta halinta na gari ya bita, ammafa 'kawata Abbah Abbas yayi masifar bani mamaki lallai shi ko kunya baiji ba yazo ya wani aureki sabida son kai ai wallahi idan nice ba zan yarda ba gaskiya an cutar dake."""

"Naja'atu zuciyarta ta sake karyewa tana zirarar da hawaye tace""Munira na rasa wane mataki zan dauka"

"wallahi mutumin nan ya nace min dik wani wulakanci da iskanci nayi masa kamar maye yaki yayi zuciya ya sakeni."""

"Munira tace""Kici kwalarsa kawai in ta kama ma ki zazzage shi!! nasan zai sake ki idan kikayi masa haka."""

"Naja'atu shuru tayi tana nazarin maganar! Anya kuwa zata iya cin kwalar Abbah Abbas! Tace""Munira ba zan iya yi masa hakaba yana da babban matsayi a zuciyata bazan tozarta shi irin wannan ba. Munira tace""To shikkenan wace shawara kika yanke ni dai idan zaki dauki shawara ta kiyi masa haka."" Tace""Idan na yanke shawara zanyi miki waya."" Tace""To shikkenan ni kuwa ina Salim kuma yaya yayi da yaji faruwar"

"wannan al'amarin.""?"

"Murmushin takaici tayi tace""Ya shiga tashin hankali da farko amma yanzu gani nayi kamar ma ya daina"

"sona tunda har yake iya kirana da auntynsa."" Munira tace""Lallai Salim gaskiya baiyi hallaci ba amma babu komai koda bai aureki ba ai idan kin futo ba zaki rasa saurayi mai jini a jika ya aureki ba, alhamdullhi kina da kyau da duk suffofin da ake so a jikin mace, wallahi akwai wani abokin Muktar wanda zan aura kenan dan gayu ne sosai sunansa khamis yana da hankali da nutsuwa ga kuma kudi da"

"duk abunda mace take bukuta, insha Allah zan hadaki dashi nasan ya ganki zai soki tunda kin cika mace."""

"Naja'atu tace""Ni yanzu babban burina na rabu da auran wannan tsohon saboda na tabbatar da cewar ba"

"zanyi wani nauyi ba zan samu daidai dani na aura."" Munira tace""To shikkenan ina sauraranki idan kin yanke shawarar sai ki kirani ki fada min ni kuma zan taimaka miki saboda darajar k'awancen mu."" Tace""To nagode kawata sai kinji ni."" Sallama sukayi da juna, ta kashe wayar tare da 'kurawa kasan kafet"

din dakin ido tana tunanin shawarar da zata yankewa kanta...

*Littafin na kudi ne!*

Koda zaki ganshi a gruops to na sata idan kina bukatar biyan kudin karatu toga yanda abun yake

Vip gruop#600

Normal#300

Account: 0542382124..Binta Umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan

numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

mddbhrbn36

"Aunty Maryam ce ta shigo dakin ta ganta ta zabga tagumi dan gabad'aya ma bata san ta shigo dakin ba,"

"aunty Maryam Jikinta ne yayi sanyi ta tsira mata ido cikin zuciyarta tace""Kodai yarinyar nan da gaske takeyi da maganar da tazo mata dashi to idan ba haka ba me zai sanya ta shiga damuwa irin haka, gaskiya to idan ya kasance gaskiya ne yarinyar zata shiga damuwa tunda ta lura bata da hakuri ta wannan bangaran kuma tana da karfin sha'awa tabbas kuwa tunda har ta iya zuwa tafad'a mata"

maganar abin na damunta saboda haka zata yi dubarar fad'awa maigidanta taji abinda zaice.

"Zama tayi a kusa da ita ta dafa kafadarta a sanyaye ta kira sunanta, ta juyo tana kallonta idonta na"

kokarin kawo ruwa.

"Anty maryam tace""Ki daina kuka kinji ko! jikina kuma yayi sanyi yanzu dana ganki cikin damuwa, tabbas"

hakan tana iya kasancewa gaskiya ne insha Allah idan Abbah Magaji ya dawo zan fad'a masa abinda yake faruwa sai muji abinda zai ce a kan matsalar abokin nasa ke kuma dan Allah ki daina wannan kukan da kikeyi ita mace da kawaici da hakuri a kasanta.

"Dan ta 'kara tunzura Anty maryam din tace""Ni wallahi anty bazan iya hakuri na jure ba ni bani da hakuri"

"ta wannan bangaran kawai a san yanda za'ayi."""

"Aunty Maryam tace""Ni abinda yake bani mamaki anan kince bakya sonsa to ya akayi kike sakin jikinki"

"dashi har wata mu'amula take shiga tsakaninku kike jin dadi wanda har kike ganin kamar yana cutarki."""

"Tace""Aunty shine kullum sai yazo yayi wasu abubuwa wanda suke sawa hankali na ya tashi ni wallahi da"

"baya ta'ba min jikina bazan damu ba amma kullum sai yayi ta damuna ni kuma na kasa hakuri."""

"Aunty Maryam tace""Tom magana dai ta wuce kija bakinki kiyi shuru kada ki fadawa kowa kuma kada ki"

"sake Halisa ta sani dan za tayi farin cikin hakan ki cigaba da bashi kulawa insha Allah idan bashi da lafiya to zai samu sauki ai kowace cuta nada maganinta."""

Shuru tayi kawai Aunty maryam ta cigaba dayi mata nasiha gami da koya mata dabarun zama da miji da

kishiya Naja'atu jinta kawai takeyi domin ita ta riga ta gama yankewa kanta hukunci.

"Sai bayan la'asar ta koma gidan, nan tarar da wata dattijuwa a zaune a palo ita dasu Saddiqa, ta zauna"

"kan kujera tana fuskantar matar suka gaisa a nutse, matar tace""Sunana Larai daga gidan Hajiya nake tasa aka kawo ni nan gidan domin na dinga taimakawa matan gidan da aikace-akaice."""

"Sai da matar tayi mata bayani sannan ta gane cewar mai'aiki aka kawo musu, tace""To sannu da zuwa"

"Allah ya bamu hakurin zama da juna."" Matar tace""Ameen ya Allah."

"Tace""Ina kayanki suke."" Larai tace""Suna can wani daki a harabar gidan Hajiya tasa an kai mun can tace"

"can ne masaukina."""

"Tace""To hakan yayi Allah ya taimaka."""

"Larai tace""Ameen"" Halisa ce ta fito daga dakinta ganin Naja'atu da larai suna hira sai ranta ya 'baci! Ta"

"kalli Larai fuska a 'bace! dama can halisa akwai girman kai tace""Yana da kyau ki shiga kicin ki fara aikin ko."""

"Larai ta mike da sauri tana fadin ""To Hajiya a nuna min kicin din."" Tace""Muje na nuna miki yanda ake"

"amfani da komai."" Larai tace""To."" kicin din suka nufa Naja'atu ta bisu da kallo tana girgiza kanta, Halisa"

"ba 'yar gidan uban kowa ba amma dan kawai tana auran mai kudi sai shegen girman kan tsiya, tsaki taja"

ta kalli Mussadiq dake mata magana

"Tace""Ba gidan Alhaji naje ba gidan Aunty Maryam naje."" Yaron yace""Da kin sani kinje dani Yaya Naja'atu."

"Tace''Wani weakend din sai ku tambayi Abbanku kuje ku yini a can."""

"Mufida tace""Aikuwa zamu tambaye shi."" Ta kalli Saddiqa da fadin""Saddiqa ya hannunki."" Yarinyar"

"tace""Hannu ya warke kinga yanzu ina iya amfani dashi ba tare dana ji zafi ba."" Tana kokarin mikewa tace""Allah ya kara sauki."" dakin yaran ta nufa, ta shiga wanka ta fito daure da zanin atamfar jikinta jakar kayanta ta bude taga babu duk ta sanye su sai 'kananu irin na kanti sai dogwayen riguna ita kam ba zata sa doguwar riga ana zafi ba riga da sket ta dauka tasa a jikinta ta gyara gashinta tasa masa ribborn ta gaji da rashin kitso tana ganin dole ta tambaye shi zuwa kitso kanta kusan satin sa biyu a tsefe! gashi tubarkalla tana da gashi babu laifi....Dankwali abaya ta daura a kanta ta zauna tana hada kayanta dana yaran wanda da sukayi daud'a! ta fito palon tana kallon Mufida tace""Kije bakin gate kiga idan me muku"

"wanki nan kice yazo ya dauka."""

"Yarinyar tace""To"" Da sauri ta mike zata fita..Halisa ta fito daga kicin tace""Ke ina zakije.''? Tace""Yaya"

Naja'atu tace naje na kira Yunusa mai wanki.''

"Cikin tsawa tace""Koma ki zauna idan ita ba zata je ba to ta aiki wanda take da iko dasu."

Yarinyar ta kalli Naja'atu dake tsaye tana kallonsu...Jikinta a sanyaye taje ta zauna saboda tana masifar

jin tsoron mommyn nata tana kuma tsoron irin dukan da take mata....Saddiqa ta mike ta nufi dakinsu ta sako hijabinta ta nufi kofar fita.

"Naja'atu kuwa murmushi tayi ta zauna kan kujera da fad'in ""Allah yasa nima na haifa kafin ki haifa"

"ballantana kiyi min gori ina da masu share min hawaye ehe.""!! Halisa na jinta tayi mata banza so take kawai maigidan ya dawo taga irin hukuncin da zaiyi wa yarinyar na fita ba tare da saninsa ba kuma tasan ya tsani yawo komai shirin da kuke dashi kukan iya 'batawa dashi idan yaji maganar zuwa unguwa"

shiyasa itama bata fiye zuwa sabgogin danginta ba saboda kullen da yake musu.

Larai tuwo tayi musu na farar shinkafa yayi kyau sosai ga lafiyayyar miyar bushashshiyar kubewa da taji

"nama da daddawa da kayan kamshi, cikin nutsuwa ta shirya musu gurin cin abincin tayi musu sallama ta nufi masaukinta."

Halisa kuwa zuwa akayi ka cancad'o ado da wani uban material mai tsadar gaske sai dai anyi masa

"banzan dinki riga da siket ne duk an tsaga shi hannun riga mai tsayi da gajere tasa turare mai kamshin gaske, palon ta fito tana shan k'amshi"

"Naja'atu da yaran suka bita da kallo, Naja'atu Kallo guda tayi mata ta dauke kanta tana kunshe dariya!"

Halisa ta lura da ita sai ta shareta ta zauna kan kujera hade da daukar romot tana dannawa! Yaran kuwa

motsin kirki sun kasa yi wanda da kafin fitowar Halisa hayaniya suke akan film din da suke kallo amma

zamanta a gurin duk yasa sun shiga taitayinsu Haka suna ji suna gani ta sanja musu tashar da suke

"kallo ta mayar dashi Mbc1 tashar larabawa, gabadaya yaran basu ji dadi ba dan yanayin su sai da ya nuna. Naja'atu ta kalleta a da'kire! tace""Kallo fa suke zaki dauke musu dan Allah ki mayar musu su"

'karasa.

Halisa ko kallonta ba tayi ba ta cigaba da kallon dramar da akeyi a tashar mbc1 din.

Naja'atu ta mi'ka hannu zata dauki romot din ta wani fizge hannunta ta dauke romat din ta rike a

hannunta.

"Naja'atu tace""To ikon Allah! kina Iko da abinda ba naki ba? Kayan kallon nan fa ba daga gidanku kika zo"

"dashi ba maigidan ne ya siya ya ajiye domun 'ya'yansa kawai kuma sai ki dinga 'kuntatawa yara kina son zuciyarki."" Halisa ba tare data kalleta ba tace""Ki cigaba da zagina kina min rashin kunya zaki gane baki da wayo wallahi."""

"Naja'atu tace""Babu wani zan gane bani da wayo ai gaskiya na fada miki dama ni tuntuni abinda yake"

"had'ani dake son kai aikin banza kawai."" A fusace! Halisa ta juyo ta wanke mata fuskarta da mari ta mike tsaye tana wani irin huci! tace""Ke na gaji da rashin mutuncin da kike miki wai dan uwarki ni sa'arki ce.""! Naja'atu ta dafe fuskarta tana kallonta ta'b!!! Mikewa tsaye tayi a zafafe! kawai suka ji sallamarsa a palon...Naja'atu ta fashe da kuka tana sake rike fuskarta ta da fadin ""Kawai daga na fad'a miki gaskiya"

"shine zaki mareni har

31 / 79