Chapter 58 Reading MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE READ HAUSA Novels

MADADI Ba Haram Bane by BINTA UMAR ABBALE

Author :  Binta Umar Abbale Category :  African Stories & Novels

Chapter   58 / 79

171K to 174K   out of 235.1K words

babu yanda baya zartar da ikonsa Abbah Abbas dalilin wannan abu da ya same shi ya janyo masa samun alkairi sosai daga gurin abokanan sana'arsa ta kwangila ita kanta gwamnatin garin sai da ta bashi tallafi dan ganin irin hidimar da yake mata hausawa dama suka ce wani hanin ga Allah baiwa ne, Abbah ya samu matasa wanda suka rasa aikin yi ya samar musu gurbi a cikin rumfunan sa dake kasuwar, Yanzu Abdulhamid shine a matsayin babban yaronsa ya yarda da yaron sosai ya amince da gaskiya da amanarsa shiyasa yaja shi a jikinsa yana nuna masa yanda harkokin kasuwanci suke saboda gaba baya so duk wanda yake karkashinsa ya dawwama a gurin yi masa bauta ya fiso kowa ya tsaya da"

kafafunsa shiyasa ko kad'an baya yiwa yaransa mugunta ta kowane fanni suna jin dadin zama dashi

*( Haka ake so shugaba ya zama adali mai kaunar cigaban na qasa dashi mafi akasarin abinda yake

damun wasu 'yan kasuwar kenan kiga mutum kullum kansa ya sanyi daga zarar yaga wanda yake qasa dashi zai tashi sai ya mayar dashi ya dankwafe! kullum dai yafi so yayi ta zama a karkashinsa yana masa wahala.....Wannan ba adalci bane idan kana so kayi qarko jama'a su dinga fad'in alkairin ka to kada ka saka ganin kyashi da ganin ido a cikin al'amuranka idan ka samu abunda ka samu sai ka sakarwa na qasa

da kai shima ya samu Allah ka karemu da ganin kyashi da hassada)*

*BASH!*

To Bash ya samu nasarar k'etara kasar Najeria inda kai tsaye ya sauka a 'kasar ghana tare da maqudan

kudaden da suka sato a bank. Akwai abokansa a garin saboda haka yana sauka a airport ya kira daya

"daga cikinsu, ko minti talatin baiyi ba a gurin wata zungureriyar bakar mota tazo ta daukeshi, koda ya shiga motar sai yaga duk guyz ne irinsa shi kadai ne musulmi ma a cikinsu dukkaninsu kafurai ne yawancin su ma had'uwa kawai sukayi da juna kowanne da kasar da ya fito."

A daran sukaje gurin canjin kudi zunzurutun kudad'en da bash yaje musu dashi su sanja aka basu irin na

'kasar. Duniya sabuwa suka bud'e dama akwai 'yan garin guda biyu wanda suke da daurin gindi

"kasancewar iyayansu 'kososhi ne a cikin gidan gomanati. shiyasa duk ta'addacin da suke babu wanda ke musu magana, suyi shaye shaye su kama yaran mutane suyi musu fyad'e komai kankantar yarinyar mutukar tsautsayi ya ritsa da ita to basa saurara mata, dan akwai lokacin da suka shiga wata bording skull a garin, suka haikewa yaran mutane sai da sukayi raping din sama da mata talatin suka fito suka barsu cikin jini da wahala, abun mamaki gwamnati ba ta wani dauki mataki mai tsauri a kansu ba. Bash yayi masifar jin dadin had'uwa da guyz d'in nan suka bud'e shafin iskanci irin wanda suke so,"

sace sace shaye shaye fyad'e Luwad'i da duk wani mummunar aikin da Allah ya haramta yi sukeyi Bash tuni ya kafurta kansa ya zama kafuri tunda yaje garin bai kalli gabas da sunan zai gaishe da Ubangiji ba

sharholiyarsa kawai yake babu abunda ya dameshi.

Munira kuwa tayi ciki da Muktar ya koreta daga gidansa yace tun wuri taje ta nemi uban danta kuma ya

"fasa auranta domin abinda yake bukata a gurinta ya samu saboda haka idan ta sake zuwar masa gida sai ya karya mata kafafu! Munira ganin bata da gata yasa ta hakura ta kyaleshi ammafa taci kuka ta koshi kuma tayi nadamar wautar data tafka, yanzu tana gidan kanwar mamanta mai suna Hajia Zulai bakar wahala take bata a cewar matar lokacin da ludayin su yake kan dawo basu taimaka mata da komai ba dan haka bata ga wanda zai dauko wahala ya dora mata ba, Munira hakuri kawai take a gidan Hajia Zulai ita taci mutuncinta 'Ya'yanta su wulakantata watarana da yunwa take kwana ga ciki a jikinta Munira ta"

gane duniya abar tsoro ce dan idan ta juya maka baya sai ka zama tamkar kashi a idanun mutane.

Alhaji Aminu da matarsa kuwa suna can a kulle dan har yanzu ba'a yanke hukunci ba an dai rufesu a

"kebantaccen guri, gwamnati tasa a cigaba da bukince inda Bash din ya fake dan tuntuni an yankewa sauran abokan nasa hukunci kisa bayan sun gama zaman gidan kaso na shekara goma......Tsanani tashin hankali Alhaji Aminu da Mommy suka shiga suka dinga kuka suna dana sanin abinda suka aikata na dora"

"d'ansu a turba mara kyau, duk bayan sati biyu sai 'yan jarida abokanan aikinsa sunzo sun titsiye shi da"

"tambayoyi kamar ma da gayya suke zuwa su turkeshi, takaicin hakan yasa ciwon hawan jini ya kamashi,"

yau da lafiya gobe babu.

****

To zamantakewar gidan Abbah Abbas sai dai muce alhamdullahi dan a tsakanin Halisa da Zainab an

"samu fahimtar juna duk ta dalilin jajurcewar jagoran nasu wato shi wanda ya ajiyesu a gidan, tuntuni Zainab ta daina rawar kai wanda ada take ta daidaita nutsuwarta yanzu ta kanta ma takeyi cikinta yayi wata hud'u! jikinta ya soma amsawa hankali ya fara shiga jikinta! gabad'aya sai tayi rauni ta kasa daukar lalurar mijin nata kamar wacce ta kusa haihuwa haka ta koma ciki wata hud'u, amma har ya fito kasancewar ta mai jiki da tumbi shiyasa cikin yayi saurin nuna kansa. Abbah nada tausayi sosai shiyasa"

baya takura mata da fitina lalla'bata yake da dukkanin abinda take so burinsa kawai ta sauka lafiya.

'Bangaran Halisa ta samu lafiya sosai dan a jikinta ma tana jin hakan ta daina jin kyaikyayi ta kuma daina

"zubar da ruwan da takeyi, sai ta fad'a masa cewar yana da kyau ta sake komawa asibiti su dubata domin su tabbatar mata da ingantuwar lafiyarta, da yake shima a cikin matsala yake sai ya dauketa da kansa ya kaita asibitin, Aikuwa kyakykyawan result ya fito Halisa kwayoyin cutar Gloria da take dauke dasu sun mutu yanzu mu'amula ta aure zata iya cigaba da gudana a tsakaninsu, amma dai duk da haka sai da Dr"

Sa'adatu ta rubuta musu wani magani wanda 'ka'ida ita dashi ne zasuyi amfani dashi.

Abbah Abbas yaji dad'in samun wannan kyakkyawan result d'in dan har sai da ya kasa 'boyewa ya nuna

"a fuskarsa kyautar kudi masu kauri yayi Dr din suka kama hanya suka tafi, Dr Sa'adatu ta dinga murmushi"

tana jin wani iri a jikinta hakika mutumin na burgeta mutuka tana adduar Allah ya bata miji mai irin halinsa.

Tun daga ranar Abbah da Halisa suka d'inke Halisa aka dawo amarya aka dinga gwangwajewa da ango

"ana biyan bukatar juna, sai dai bangaran mutumin naku daurewa kawai yake amma ba wani daidai yake ji ba dan ya tsani yaji ya shiga gurin yaji shi sakwaf-sakwaf! Halisa ta riga ta gama bud'ewa magungunan gurin 'yar Sa'adu sunyi mata mummunar illah! Haka dai yake hakuri yana biya wa kanshi bukata ba tare da ya nuna mata wani abuba, sai duk sanda takaici ya ishe shi kasa hakura yake a cikin kwananta zuwa yake gurin Zainab ya baje kolinsa yanda ranshi yake so sai bayan ya samu nutsuwa zai dawo yana da ya sani dan Zainab kwana takeyi tana kuka da fad'in cikinta ciwo yake hankalinsa ya tashi da kyar yake"

rarrashinta.

Salim abin duniya ya isheshi ya rasa makama kullum yana gida a kwance yana tunani gabadaya yanzu

"kunyar fitowa yake saboda irin kallon da Jama'ar gari ke masa! Ya kai sati biyu a gida baya fitowa sai da daddare nan ma baya dadewa zai dawo gida ya kwanta, mahaifinsa kuwa har ya koma bakin sana'arsa baya amsa gaisuwarsa fushi yake dashi sosai da sosai Ranar Lahadi ya shirya tsaf domin zuwa"

"gidansu Salimat budurwasa wacce aka kai kudin aure da sa rana, ya fito da key din motarsa simi simi ya"

fita daga gidan kai tsaye motarsa ya shiga ya nufi gidansu Salimat..........

"Salimat ta sameshi a cikin mota a zaune ta bude ta shiga ta zauna ta kalleshi tana ta'be bakinta tace""Wai"

"dan Allah kwana biyu me yake damunka ne naga duk kabi ka susuce ka ma daina zuwa gurina kullum kuma idan na kira wayarka sai naji ka a cikin hali na damuwa wai ko ka daina sona ne.""? Salim ya girgiza kansa yana kallonta yace""Ba haka bane salimat kwana biyu bana jin dadi wallahi shiyasa kika kasa gane"

"kaina amma yanxu naji sauki sosai inaso ki fad'a min meye damuwarki."""

"Ta'be bakinta tayi tace""Kasan bani da wata damuwa sai ta kud'i yanzu ma inaso ka sanja min waya"

"sannan na kwana biyu banyi ciye ciye ba inaso muje ka siya min kayan kwalliya da sauran abunda nake bukata."""

"Yace.""Okey shikkenan kada ki damu."" Motar ya kunna kai tsaye suka fita daga cikin unguwar. Kafin su"

"tafi shopping din sai da suka tsaya a P.O.S tana kallo Salim ya bada atm dinsa da accont number nasa, suka bashi abun yasa nambobin sirrin sa duk akan idonta kudin da yake bukata suka miqa masa ya kar'bi"

atm dinsa suka fita daga gurin....

Lokacin da suka shiga motar ya manta bai mayar da atm din cikin wallet dinsa ba ya fad'i kasan site a kan

"idonta sunayi parking a daidai gate din Jujin lambo ya bude motar ya fita ita kuma tana ganin fitarsa tayi saurin sunkuya ta lalubi atm din tasa a cikin pose din dake hannunta ta bude motar tabi bayansa cikin gurun Siyayya yayi mata sosai da sosai suka fito da kaya a hannunsu, kafin ya kaita gida sai da ya siya"

"mata kayan ciye ciye irin wanda take so sannan ya kaita gida, to yaso su danyi abun da suka saba kafin"

"su rabu taki bashi damar hakan tace ita ta gaji gobe ya dawo da wuri zata bashi mamaki! yace shikkenan, sallama sukayi da juna yaja motar yayi gaba. A ranar Salimat kasa bacci tayi saboda tunanin yanda"

"za'ayi ta cire kudaden dake cikin account din Salim gashi ita ba account ne da ita ba, sai ta samu Yayanta Mai suna Naburago mugun dan son banza ne Naburago baya gudun Allah ya isa duk inda yaga bashi sai yaci bashi da sana'a sai buge buge da ita suke rufawa kansu asiri kasancewar su marayu ubansu ya mutu shine kuma namiji shiyasa wahala tayi yawa a kansa, talauci yasa Salimat lalacewa maza babu irin wanda bata sani ba shi kuwa Naburago rigima ko ta uwar uban waye saka kansa yake a ciki ayi ta fafatawa dashi a rabu dashi dan idan yaci bashi aka zo aka turkeshi ya biya sai ya mayar da abun wasa idan mutum ya kaishi gurin 'yan sanda kai tsaye yake fad'a musu bashi da kudin da zai biya bashi idan kuma ana kar'bar shekaru zai lissafa shekarunsa ya biya. Su kansu 'Yan sandan sun sallamawa Naburago shegen kansa"

gashi da kwarjin tsiya komai takatsantsan di'nka a kan kayan sana'ar ka idan yazo kar'ba bashi mutum baya sanin sanda yake dauka ya bashi Salimat shi ta samu da maganar ta fada masa abunda ke

"faruwa, Naburago yayi tsalle da juyi a dakinsa yace.""Bani atm din jeki kwanta ki huta kudi zasu koma"

"account d'ina wahala ta yanke mana."" Salimat ta fad'a masa numbobin sirrin na Salim din yace to"

magana ta kare. Alwala yayi ya yay sallah ya fita da atm din cikin aljihunsa.

A ranar Naburago ya kwashe kudaden account din Salim tas ya mayar nasa accont din Salim sai

shigowar alert kawai yaji yana dubawa yaga a'lamarin daya afku babu abinda ya fara dubawa sai wallet d'insa ya nemi atm dinsa ya rasa a gigice ya nufi motarsa ya shiga dubawa sako da loko babu atm! cikin tsantsar tashin hankali ya shiga motar ya kunna a guje ya nufi P.O.S din da sukaje kawai ya fad'a musu guri kamar mahaukaci yana dube dube. Ai a take wani Police dake gurin ya damqe shi a cewarsa

yaga yayi yanayi da masu laifi dan yanda yaga ya shigo gurin a kid'ime ya nuna masa hakan! aikuwa jama'ar dake gurin suka gazgata hakan dan ganin yanda Salim din ke muzurai yana wani irin gumi! sai rawar baki yake ya kasa magana. Yana ji yana gani aka sashi a mota aka tafi dashi police stion kamar

wanda aka daurewa baki ya kasa cewa komai zufa ce kawai ke tsatstsafowa daga jikinsa..........

_*Yau tafe nake da 'yar tsaraba ta *_

*'Kawata matso kiji wata muhimiyar magana A kwai gurare masu daraja da muhimanci a jikinki 1

Headquarter naki...2 Hamtarki....3 qasan nonuwanki 4 Tsakanin cibiyarki! Wad'annan guraran nada

mutukar mahimanci a gurinki yana da kyau ki kula dasu ki mutunta su. Na farko dai ke kanki kin san

"barin gashin hammata dana headquarter babbar matsala ce a gurinki waccan ka iya janyo miki imfaction gami da rashin jituwa da miji kullum ya kasance kin zama abar kyama a gurinsa, barin gashin hammata a gurinki sam! bai dace ba, ba dan komai ba sai dan ansan ita mace daban take da namiji kada kiga mijinki da gashin hammata kice kema ba zakiyi aski ba a kull! ke daban shi daban! ke ai abun kunya ne a gurinki ki d'aga hammatar ki a ga gashi! Wallahi duk ranar da kikayi kuskure kika bar mijinki yaga d'audar hammatarki kin cuci kanki sannan kika sake mijinki ya shaqi warin hammatarki kin zubar da qimarki duk da kasancewar yanzu muna lokacin sanyi kada kice ai yanxu sanyi ne ba'a wari kiqi yin aski wallahi duk turaran da zaki saka sai yaji warin jikinki saboda haka kiyi hattara. Warin qasan"

"nono na mussaman ne ba ko wace macece ke kula da da wanke qasan nononta ba, to bari kiji mutukar kika ga mijinki a lokacin da kuke sex yana kauda kansa daga gurin nono ki to wallahi wannan warin yake damunsa, ina amfani ace kinyi wanka baki d'aga nonuwanki kin wanke ba ai kamar ba kiyi wanka ba k'awata! Kisa sabulu ki wanke kasan nono tas kisa masa turare na mussaman sai kiga maigida na zumud'in kai kansa gurin Ramin cibiya yana tara daud'a saboda gurin a tsuke yake baida spece"

"sosai, yana da kyau kullum idan kinzo wanka kina sa bakin soso a hankali a hankali kina wankewa kada ki"

bar ramin cibiyarki da daud'a domin hakan na iya janyo miki matsala mai girma. Wannan tsarabar

tawa ba ta mantan aure bace kawai har daku 'Yan mata da zawarawa 'yan kwalisa To sai mun

sake had'uwa daku a fita ta biyu *

Vip gruop #600 normal group #300 account numbar....0542382124...Binta umar gtbank. Wahasap

number. 07084653262

*BINTA UMAR ABBALE*

68******Salim har yamma yana police station a gar'kame hankalinsa yayi masifar tashi ganin duhun

"magariba ya gabato sai kawai ya fara zubar da hawayen nadama! babu shakka wannan al'amari daya faru dashi hakkin Kawunsa daya zalinta ne, yasa hannu ya dauko hankici a cikin aljihunsa ya goge idanunsa tare da sake ri'ke 'karfen da yayi masa katanga da ma'aikan gurin, zare ido kawai yake yana fad'in ""Oga dan girman Allah ka saurari maganata wallahi ni ba 'barawo bane inaso kazo kaji uzirina ni"

"abun a tausayawa ne qaddara da tsautsayi ne suka afka min."""

"'Daya daga cikinsu ya doki! tebur din dake gabansa yace.""Rufe mana baki munafiki kai har kasan"

"qaddara irinku ai ba imani ne daku ba kazo sata sai Allah ya tona maka asiri dama irinku muke nema duk muyi maganinku yanzu D.P.O muke jira yazo mu zartar da hukuncin da zamuyi maka."""

"Salim ya sake rikicewa cikin tsantsar tashin hankali yace.""Wallahi wallahi bana daya daga cikin wa'yan"

"nan mutanan da kuke magana a kansu, ku taimakeni kamar yanda Allah ya taimake ku wallahi ban shiga gurin nan da sunan sata ba Atm dina naje nema a gurin kasancewar kwanaki uku da suka wuce naje na cire kudi a gurun Tiryan tiryan ya fad'a musu abinda ya faru, yace""Idan kuna so ku tabbatar da"

maganata to ku duba waya ta zaku ga text din da banki suka turo min cewar gabadaya kudin dake

"account d'ina babu."""

"Da sauri wanda wayar ke hannunsa ya shiga dubawa, aikuwa da text din yaci karo cike da mamaki ya"

"shiga nunawa 'yan uwansa sai duk jikinsu yayi sanyi, wanda key din cell din ke hannunsa ya miqe da sauri yaje ya bude shi yace.""Kayi hakuri kaji ko Allah ya mayar maka da alkairi."""

Cikin tsananin damuwa da tashin hankali ya kar'bi wayarsa da key din motarsa ya kama hanya ya futa

"daga gurin, sai suka bishi da kallon tausayi kud'i kimanin miliyan daya da rabi an kwashe masa ai dole su jajanta al'amarin Salim na fita daga station din kai tsaye gidansu Salimat ya nufa, yayi parking a kofar"

gidan cikin damuwa ya kira wayarta. Salimat ta fito cikin shiga ta alfarma kamar yanda ta saba ta bude

"mota ta shiga, ganinsa a burkice yasa tasha jinin jikinta, ya kalleta dan jan ido yace.""Salimat 'barayi sun"

kwashe min kudin accont dina yanxu bani da ko kwabo Atm dina ya fad'i a lokacin dana kaiki shopping

"ban ankara ba sai da naga bank sunyi min alert sannan na duba naga abunda ke faruwa...Hakika ina cikin tashin hankali mai tsanani."""

"Cikin alhini tace""Innalilihi wa'ina ilahi raji'un Salim yanzu ya zamuyi da wannan qaddara sai kawai ta"

"fashe da kukan munafurci

58 / 79