Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
ta yatsine
"Ke kuma zaki b'acemin da gani ko saina b'alla ki"
Ai a guje tabar wajan gabanta na fad'uwa. Fad'a sosai taima Najman dan tunda suka had'a ido da Ummyn taji yarinyan bata mata bah, ga kuma labarinta dataji wajan Mabrookah a daran jiya sai taji ta k'ara tsanan yarinyan.
Ranar Ummy ta wahala sosai wajan Aunty Faty, duk bayan mintina sai tasa an kira mata ita tasata aiki, duk da ta gaji sosai anma bata nuna musu bah haka taketa daurewa tana aikin.
Tana kwance a d'akinta wuraren la'asar aka turo k'ofar d'akin nata aka shigo, d'an d'agowa tayi sannan ta mik'e ta zauna ganin Najma da Najwa.
"Ana kirana neh?" Ta tambayesu tana kallansu
"Aa ba kiranki ake ba munzo tayaki hira neh"
Ta d'anyi kasak'e tana kallansu da mamaki, d'aya daga cikinsu tace
"Mene sunana?"
"Najma" tace da murmushi
Dariya suka fashe dashi, d'aya tace
"Ni ce fah Najma"
Ta nuna wacce tai ma Ummyn tambayan tace
"Ita kuma Najwa"
Ta kafesu da ido tana k'okarin banbance tsakaninsu, kan gadonta suka zauna suka soma mata hira. Sakin jiki tayi sunata hira, a nan take sannin cewa Aunty Faty yayar Mami ce, Aunty Zainab kuma itace mamansu kuma k'anwar Mamin ce.
Sun dad'e suna hira kamin daga baya Mabrookah ta shigo ta korasu bayan ta zage Ummyn tas.
******
Ranar monday da safe Jamal ya shirya cikin suit
Blue da farin shirt a ciki, k'afarsa sanye da Black cover shoes kanfanin versace, falon ya shigo bai tarar da kowa bah, d'akin Ummy yayi knocking a hankali yanayi yana kallan step, jin shiru yasa ya murd'a a hankali ya shiga. Kan sallaya ya sameta tana lazimi, ya k'arasa ya zauna kan gado yana kallanta, ganin ya zauna yasa tayi saurin shafa addu'an datake ta juyo tana kallansa
"Ya Jamal me kakeyi a nan?"
Ya mik'e ya k'araso inda take ya tsugunna yana kallanta da murmushi
"Bah gaisuwa sai tambaya"
"Ina kwana" tace dasauri a d'an tsorace tana kallan k'ofar d'akin
"Karki damu basu tashi bah, i just came to see uh kuma kimin addu'a yau zan fara zuwa aiki"
Ta sauke ajiyan zuciya ta d'an kalleshi tace
"Allah ya tsare ya kareka daga sharrin mak'iya"
Sosai yaji dad'in addu'arta ya amsa da amin tareda shafa gefen fuskanta yana murmushi
"Matsoraciya kawai"
Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falon, ya d'an zaro ido
"Jamal zo nan"
Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:38 PM] +234 703 981 8283: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
Page 25 n 26
Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falo, ya d'an zaro ido
"Jamal zo nan"
Sunne kai yayi ya k'araso ya zauna kan kujera yace
"Ina kwana"
"Yanzu dai Jamal ka daina jin magana ta"
"Mai kuma nayi Mami tah"
"Mai nacema akan maganan yarinyar nan"
Ya sunnar dakai yana jujuya wayan dake hannunsa
"Da kanajin magana ta anma yanzu ka daina, ka kiyayeni in ba haka ba ta kusa daina aiki a gidan nan"
Ba shiri ya d'ago da mamaki yana kallanta
"Kiyi hak'uri Mami bazan sake bah"
"Menene tsakaninka da yarinyan nan neh wai"
Ya sake duk'ar dakai baice komai bah, ba shiri ba mik'e tsaye dasauri
"Noo! Karka cemin santa kake, dan bazan yarda bah, ya zakayi da Mabrookah daketa jiranka"
Ya turbune fuska danshi harga Allah baisan Mabrookah, Aunty Faty ta sauko jin tashin muryan Mami
"Lapia Maimuna kiketa d'aga murya haka"
Nuna Jamal tayi tana cewa
"Zo ki tayani jin abin kunyan da Jamal keso ya d'auko min"
"Na meh?" Aunty Faty ta tambaya tana kallan Mami
"Yaran nan ace duk jiran da Mabrookah ta masa yanzu ya samu lapia yake so ya watsa mana k'asa a ido"
"Mami kiyi hak'uri ni fa ba san Ummy nake ba"
Sai a sannan Aunty Faty ta gane inda Mami ta dosa
"Jamaludeen me zakayi da mai aiki talaka, wacce ko boko batayi bah"
Sosai maganan Aunty Faty ya b'atamai rai, Abba ne ya shigo falon da sallama, wayancewa sukayi Aunty Faty tace
"Allah ya tsare ya bada sa'a Jamal"
Wuf ya mik'e dan dama hanya yake nema, Abba ya gaishar ya musu sallama ya bar gidan zuciyarsa na masa suya.
Nan Mami da Aunty Faty suka soma shawaran yanda zasu b'ulloma alamarin. Cikin satin Ummy tasha wuya wajan Aunty Faty kamar ba gobe, itadai Aunty Zainab Ummin su Twins batace wa komai sai ido data zuba musu, itama kanta batajin dad'in abinda akema Ummyn.
Sosai Ummy ta shak'u dasu Twins, so dayawa suna tare a kicin suna aiki tare, ko idan tana gyaran d'aki su tayana, wani lokacin kuma suna d'akinta suna hira. Ba yanda Aunty Faty batayi ba akan ta hanasu anma sunk'i ji.
Ranar Juma'a da safe akayi ma ma'aikatan albashi, bakin Ummy har kunne musamman dataga wannan karan shima dubu d'arin aka biyata.
Dak'yar Mami ta yarda ta barta ta tafi gida weekend gida. Hankalin su twins sosai ya tashi ganin Ummyn zata tafi dan saboda ita gidan ke musu dad'i.
Har bakin gate suka rakota suka koma cikin gida a sanyaye. Napep ta tara ta shiga, suna karyo kwanan layinsu ta hango gidan su da masu aikin gini kamar gyara yake a gidan. Da mamaki ta shiga tana bin ma'aikatan da kallo, dakunansu taga an had'e an fitar da two bedroom mai kyau, Mama ta fito daga Falor ganin Ummy yasa ta rungumota cikeda murna.
"Mama wannan aikin fah"
Hannunta Mama ta kama suka shiga cikin Palourn, nan Ummy ta saki baki tana kallan yanda gidan nasu ya koma, had'adden set d'in kujeru ta gani, ga tiles da aka malale falon dashi, sosai falon yayi kyau, tabi Plasman dake jikin bango har lokacin idanunta a warwaje
"Mama wannan kayan daga ina"
Baba ya fito daga d'aki yana dogara sandarsa yana murmushi
"Muryan wa nakeji kamar na Ummyna"
Dasauri ta k'arasa ta rungumeshi tana dariya
"Baba ni ce"
Ya shafa kanta yana cewa
"Ba abinda zamuce ma yaron nan sai Allah ya mai albarka"
"Baba Ya Bilal ya dawo neh? Dama nasan bai mutu ba zai dawo"
Mama tace
"Duk wannan abubuwan da kika gani, duk aikin Jamaludeen neh, kuma yace yayi dan Allah ne ba wani abu bah"
Yatsine fuska Ummy tayi tace
"To an gode"
Ta shiga bedroom, nan ma taga an gyara shi tsaf harda sabon funitures, ta tab'e baki ta aje jakanta sannan ta fito. Albashinta ta mik'ama Baba kamar yanda ta saba, Albarka ya saka mata yace
"Wannan karan ki adana kud'inki dan munada komai dangane ga kayan abinci"
Ummy tayi murmushi tace
"Tho Baba, anma yakamata mu sake komawa asibiti ka sake ganin likita"
"Hakaneh" cewar Mama
"Aa Ummy, nikam Alhamdulillah naji sauk'i, yanzu babban burina bai wuce naga kin daina bauta bah, kin koma makaranta ko kinyi aure"
Mama tace
"Komai Lokaci ne Mallan, Fatan mu ka samu lapia, komai yazo daga baya"
Murmushin takaici kawai Baban yayi baice komai bah.
Washe gari lahadi, masu aikin ginin basu zo ba suna hutu, yau D'anwake Ummyn tayi musu dan Baba nasan d'anwake sosai, bayan ta zuba musu nasu ta d'au nata ta fito tsakar gida kan tabarma tana ci. Ta saka loma kenan ta jiyo sallaman su Twins, dakyar ta iya had'iyewa suko mai zasuyi in ba dariya bah. Mik'ewa tayi dasauri ta rungumesu tana dariya
"Sannunku da zuwa, ya akayi kukasan gidan mu"
"Ya Jamal ne ya kawo mu yana waje" cewar Najma
Ciki ta shiga dasu suka gaisa da Baba da Mama, sannan suka dawo waje dan ciki akwai zafi, d'an waken ta zubo musu suka soma ci suna santi, Ummy ko me zatayi inba dariya bah.
Mama ta lek'o tareda rik'e hab'a
"Oh ikon Allah, ashe ku nan zama kukayi kuka bar Yayan naku a waje"
Sai a sannan suka tuna ashe da Jamal suke, Mama tace Ummy ta tashi tace mai ya shigo, turo baki tayi taja hijab a igiya ta fita, cikin mota ta sameshi yana waya, ta k'arasa ta juya fuska gefe tace
"Ance ka shigo"
Bata jira mai zaice ba ta koma ciki, shi dariya ma abin ya bashi Ummy sai kace mai Juju, wani lokaci ka gansu Lafiya suna shiri, watan kuma a yini ba'a masa magana bah.
Da sallama ya shiga ciki, Najma da Najwa na zaune tsakar gidan suna cin abinci
"Dama nan kukafi auki, Ci, Ci!"
Najma ta b'ata fuska, Najwa ko Dariya tayi ta sake kai loma tana kallansa. Dariya yad'anyi ya girgiza kai ya shiga falon da sallama.
Har k'asa ya tsugunna ya gaidasu, Ummy ta had'o mai d'anwaken. Ba ko kunya ya soma ci suna hira da Baba, Ummy sai binsu da kallon mamaki take ganin yanda suke hira kamar wad'anda sukayi shekara da sabo.
Waje ta koma suka cigaba da hiransu da Twins, bayan sun gama Jamal yama su Mama sallama yace ma su twins suzo su wuce, Mama ta lek'o tace
"Ummy ina ce kema yau zaki koma, kizo ki d'au kayanki mana ki bisu"
Baki ta zungure tace
"Mama ni sai anjima"
Jamal yayi murmushi ya fita, har bakin mota ta rakosu tanata d'agama su Twins hannu, har yayi gaba ya dawo yayi parking ya fito
"Wai Twins kad'ai kika gani neh"
Ta galla masa harara
"Ni su kad'ai na gani"
"Koh"
Ta kauda kai gefe
"Zaki sani neh ai"
"Zamu sani zakace"
Yayi murmushi yana girgiza kai ya shiga yaja motan yabar anguwan.
Sai bayan la'asar Ummy ta shirya tsaf dan komawa bakin aikinta, d'aki ta samu Baba dan masa sallama, ya rik'o hannunta yana cewa
"Jamaludeen, Bahar da mahaifiyarsa duka ba abin yarwa baneh. Ki rik'esu Hannu bibiyu kinji"
"Insha Allahu Baba"
"Ki zama mai hak'uri a duk inda kike, ki kare mutuncin ki, ki zama mai biyaiyya da girmama nagaba dake, ki rik'e addininki, In kikayi haka insha Allahu bazaki tab'a tab'ewa bah. Kin faranta min Ummy, tunda na haifeki baki tab'a min abinda kika b'atamin bah, Allah ya miki albarka Ummy"
"Amin Baba, Kai kuma Allah ya baka lafiya"
"Ameen!"
Ta fito sukayi sallama da Mama ta fita ta tari adaidaita ta hau ta koma gidan aikinta.
Tana shiga dasu Twins tayi arba sunata murna, jakan hannunta suka amsa suka shigan mata dashi d'aki. Duk abinda sukeyi Aunty Faty na kallo, ranta sosai ya b'aci ta haura sama zuwa d'akinsu Tana mita.
A ranar Aunty Zainab mahaifiyarsu Twins ta koma, su kuma zasu d'an yi hutu, Aunty Faty ko cewa tayi ba yanzu bah. Babban abinda ya d'aurema Ummy kai bai wuce rashin ganin Laurat bah, dan tun sanda zata tafi ta fad'a mata sati d'aya kawai zatayi gashi yau kusan kwana Shad'aya kenan.
Da daddaren ranar Mami da Abba suna falon side dinshi, Mami tace
"Alhaji magana nazo muyi"
Yace
"Ina jinki"
D'an jim tayi tace
"Alhaji har yanzu bakace komaiy kan alkawarin auren Jamal da Mabrookah bah"
"Tho mai kikeso nace Maimuna"
"Yakamata ace yanzu anyi auren nan, tunda ya samu Lafiya ga kuma aiki ya fara"
Abba yad'anyi murmushi
"Maimunatu kenan, abinda nakeso ki gane a nan shine, yanzu ba d'ah baneh, yanzu an daina wannan had'in. Gwara a bar yara su zab'i abinda sukeso"
"Haba Alhaji yanzu ya za'ayi da alkawarin da aka d'aukan ma Yaya Faty, kuma itama Mabrookahn tana sanshi sosai, shima nasan yana santa"
"Sanda kukayi alkawarin ai bana wajan, ba sai daga baya kike gayamin da alkawari bah"
Fusata Mami ta fara ta juya fuska gefe
"Mafita a nan shine, zan tarasu na tambayesu idan har duka suka amsa suna san juna shiknan"
"Anma Alhaj...."
"Aa Maimuna, wannan shine magana"
Mik'ewa tayi tabar falon ta nufi side d'insu, Aunty Faty ta samu a falo ta sanar da ita yanda sukayi da Alhajin
"Maimuna kina bani mamaki, yanzu ke bazak'i iya tank'wara d'anki bah"
Shiru Mami tayi ta haura zuwa d'akin Jamal, bata ganshi ba ta sauko ta fita haraban gidan, nan ma ba kowa ta dawo, harta gota d'akin Ummy sai ta juyo muryan mutane a d'akin, a hankali ta dawo ta murd'a kofan. Jamal ta gani da Twins da Ummy sunata hira.
Tsawa ta dakama Twins suka fito daga d'akin dasauri, ta hararai Jamal tace
"Ka fito inasan ganinka"
Tana tafe yana binta a baya har d'akinta, gefen gado ta zauna shi kuma yaja stool ya zauna
"Jamal wannan shine zai zama magana ta k'arshe da zan maka akan yarinyan nan Ummy, wallahi ka fita idona na rufe"
Ya duk'ar dakai k'asa
"Wai mai kakeso ka zama ne Jamal, baso d'aya ba baso biyu ba na fad'ama banasan ganinka da yarinyan nan"
"Mami kiyi hak'uri"
"Duk ba wannan ba, ya maganan da mukayi dakai na Mabrookah"
Dam! Gabansa ya fad'i
"Mami pls kiyi hak'uri, wallahi i have no feelings for her"
Da Mamaki tace
"Me kake nufi knan"
Ya sake duk'ar dakai
"Yanzu Jamal bazaka iya cikama yayata burinta ba, yarta d'aya Mabrookah, batada burin daya wuce taga tayi aure."
Ta turo baki yana jujuya kai
"Alhaji zai kiraku ya tambayeku idan kunasan juna, inaso ka amsa kana santa. Hakan ne kad'ai xai sani farinciki"
Ya gyad'a kai yace
"To shikenan Mami"
Tayi murmushi tace
"Allah ya maka albarka"
Ya mik'e yabar d'akin yana gungunai.
Bacci ne ya gagari idon Jamal, shi gaskiya harga Allah bazai Iya auren Mabrookah ba dan baya santa.
Wuraren sha biyu ya mik'e kamar wanda aka tsikara ya sauko k'asa, d'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are.
Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:41 PM] +234 703 981 8283: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
Page 27
D'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are. Tsaye ya sameta kan sallaya tana sallah, gefen gadon ya zauna yana kallan yanda take ganawa da ubangijinta cikin natsuwa. Ji yayi ta k'ara birgeshi, ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallanta.
Tana idarwa ko addu'a bata tsaya yi ba ta juyo dasauri tana kallansa da mamaki
"Lapia Ya Jamal meya kawoka d'akina da daran nan"
"Nazo ne muyi wani magana"
"Magana? Ka bari mana sai gobe yanzu dare yayi"
Baice komai ba ya mik'e ya k'araso inda take zaune shima ya zauna yana cigaba da kallanta
"Bazan iya hak'uri har sai gobe bah, maganar nada mahimmanci sosai"
Ta gyara zama tana facing d'inshi
"Ina jinka, saidai kayi sauri saboda dare kuma ina sallah neh"
Ya sauke dogon ajiyar zuciya yana kallanta
"Nayi tunanin na b'oye abinda ke raina game dake, wani abu yana neman yazo min wanda bana so"
Kurrri Ummyn tayi tana kallanshi, dan sam bata san inda maganar tasa ta dosa bah.
"Ina sanki Ummy, wallahi i so much love uh"
Ba shiri ta mik'e a zabure tana kallansa da mamaki
"Ki yarda ki aureni banasan Mabrookah, na miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso pls"
Hawaye suka soma gangaro mata a fuska tana girgiza kao tana kallanshi
"So kuma? Haba Ya Jamal, dan Allah ka daina wannan wasan"
Ya mik'e tsaye
"Tun ranar dana fara ganinki naji ina sanki, ina sanki badan komai naki ba, komae....
"Ya isa! Ya isa!! Banaso inji"
Hannayenta biyu tasa ta toshe kunnuwanta tana kuka sosai
"Abinda yasa kenan kaje ka gyara mana gida, ka siyan mana kayan alatu dan ka siya iyayena...."
"No! Ummy ki fahimceni, wallahi ko kad'an badan wani abu nayi haka...."
Tayi saurin katseshi cikin muryan kuka
"Ka makara, inada wanda nakeso, koda banida shi bazan tab'a sanka bah Ya Jamal. Tun bayan warkewanka nake cikin k'unci da hantara a gidan nan. Talauci bah hauka baneh, indai haka ake k'udi kada Allah ya bani"
"No pls Ummy, ki tsaya ki saurareni"
Cikin d'aga murya tace
"Bazan ji bah, Ya Jamal ka fitar min daga d'aki banasan ji! Ka fita"
Kallo ya bita dashi cikin tashin hankali ya fita ya haura zuwa d'akinsa.
Ranar daga Ummy har Jamal babu wanda ya runtsa. Washe gari yana kan dinning yana breakfast tazo ta wuce idanunta a kukumbure, hakan ya tabbatar masa da cewa tayi kuka daran jiya. Wani tausayinta neh ya k'ara shiga ranshi, harga Allah yanasan Ummy, so na tsakani da Allah. Dan shi a shirye yake dayayi komai a kanta.
Kamar wanda aka tsikara ya mik'e dasauri ya nufi side d'in Abba, saidai kash yana zuwa ya samu Mami a falon, k'eya ya sosa ya juya Abba yace
"Yaya dai Jamal, akwai wani abu neh?"
Yayi saurin cewa
"Aa ba komai"
Da sauri ya fita daga falon ya shiga motarshi yabar gidan.
Saida Abba ya fita dan ranar zaiyi tafiya, sannan Mami ta fito daga side d'in ta dawo nata, Mabrookah ce ta soma saukowa tana murmushi
"Mami dan Allah kiban kud'in, yau nakeso muje nida k'awayena mu fitar da ankon"
Sosai maganan Mabrookah yaba Mami dariya, saida tayi mai isarta sannan tace
"Mabrookah kenan! Ke kin tab'a ganin inda aka fitar da anko ba'a sa rana bah"
Baki ta turo gaba
"Mami ai ba sai ansaka rana bah, already Abba ya bashi ni, haka an bani shi. Kuma Mommy ce tace na fitar yanzu"
Kai Mami ta girgiza zata haura ta d'auko handbag d'inta ta fita aiki.
Ranar sukuku Ummy ta wuni, har lokacin maganan Jamal ne a ranta, harga Allah bazata iya san Ya Jamal ba dan har yanzu bata gasgata maganan rasuwan Bilal bah, har lokacin tana nan rik'e da alkawarin data masa na bazata tab'a auren kowa ba sa shi.
*****
Wuraren k'arfe tara da rabi, Ummy na d'aki tana sallan isha'i dan tayi lattin sallan saboda aikin da Aunty Faty keta sata.
Muryan Aunty Faty ta jiyo tana salati tana cewa
"Maimuna! Maimunatu!! Ina kike an sace min sark'a"
Mami dake falon k'asa itada Mabrookah sukayi saurin mik'ewa
"Sark'a kuma? Wane irin sark'a"
Cewar Mami
"Sark'an nan dana siya mana danaje Dubai, Million d'aya da dubu d'ari shidda shi na nema ban gani bah"
"Toooh!" Cewar Mabrookah tana rik'e da hab'a
Mami tace
"Aa bafa zai tab'a yuwuwa bah, dan gidan nan ba'a sata. Yaya Faty kidai k'ara dubawa"
"Bafa inda ban duba ba, sark'an nan d'auka akayi"
"Mudai je mu sake dubawa"
Duka suka haura sama zuwa d'akin Aunty Fatyn, batsa batsa sukayi da d'akin suna nema anma bah sarka.
Mabrookah ta rik'e k'ugu tana bin d'akin da kallo
"Gaskiya abin nan da mamaki yake, kuma nasan dai masu aiki basa haurowa nan saman"
Aunty Faty tai saurin cewa
"Saidai Ummy ai ita ke shigowa tana gyare gyare, dan babu wanda zai d'au sark'an nan saboda ke Maimuna da Mabrookah kunfi k'arfin wannan"
"Aa Yaya Faty, bana tunanin Ummy zata d'au sark'an nan. Dan duk abin yarinyan nan bata sata"
"Maimuna! Lallai baki san talaka ba har yanzu, nidai gaskiya bazan yarda. Million d'aya harda dubu d'ari shidda ba k'aramin kud'i baneh. Gaskiya ban yarda ba sai anyi chaje kuma masu aikin nan za'a duba"
Mabrookah tai