Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
saurin cewa
"Gaskiya ne Mommy, dan tunda nazo gidan nan ba'a tab'a sata ba sai yau"
Itadai Mami batace komai bah, Aunty Faty da Mabrookah suka sauko k'asa zuwa d'akin Ummy, ganin Haka yasa Mami ta biyosu a baya. Har lokacin Ummyn na zaune kan sallaya tana lazimi, yanda aka banko k'ofan ko ba'a fad'a ba tasan Mabrookah ce
"Ke! Tashi"
Ba musu ta mik'e ta koma baya tana kallansu, bincike suka soma ko ina, Mami dai na tsaye tana kallansu. Katifa Mabrookah ta d'aga sai ga sark'a kan katakon gado.
Aunty Faty ta saki salati tareda d'auko sark'an tana nunama Mami
"Tun ba'aje ko ina ba kin gani koh?, ai k'ila ba shi kenan bah"
Kan kace me hawaye ya wanke fuskan Ummy sai kallansu take tana kuka sosai.
"Wallahi Mami bani na d'auka ba, bansan yanda akayi yazo nan d'akin ba"
Aunty Faty ta sake d'aga katakon gadon sai ga k'aramar b'akin jaka na Abba. Wannan karan Mami ce ta saki salati
"Meya kawo jakan Alhaji d'akin nan? Dollar ne a ciki kud'in mutane"
Nan ta sake rushewa da kuka ta matso inda Mamin take tana duba jakar
"Wallahi tallahi Mami bani na d'au...."
Kyawawan Mari guda biyu masu rai da lafiya Mami ta d'auke Ummyn dashi
"Allah wadaran ki Ummy, ashe haka kike? Lallai gaskiyar mutane ne da sukace talaka bai iya samun guri bah. Tho wallahi yau zaki bar gidan nan"
Ba shiri ta sake fashewa da kuka
"Dan Allah kiyi hak'uri Mami, wallahi..."
Wani Marin Mabrookah ta d'auketa dashi
"Dole kibar gidan nan, dan ba gidan ubanki baneh"
Mami tace
"Dama ance idan kaga halin yaro to ka duba ta iyayensa, Uwa ko Uba an saba da sata. Kinsan ko dole itama ta koya"
Ran Ummy ya sake b'aci ta d'ago tace
"Mama na da Babana basa sata, haka nima ban tab'a sa..."
Mami ta sake wanketa da mari, duka Mabrookah ta rufeta dashi, ko kad'an Ummy batayi niyan ramawa bah. Koran kare Mami da Aunty Faty suka mata ta fito daga gidan tana kuka sosai, ga dare yayi kusan k'arfe Goma da rabi.
Jamal na karyo kwanan layin ya hango Ummy tafe tana kuka, ba shiri yaja birki ya fito dasauri. Ta ganashi ta bi ta wuce yanata kwalla mata kira ko waiwayowa batayi ba sai kuka datake yi.
Binta ya soma yi hankalin shi a tashe yana kiran sunanta tareda tambayan abinda ya faru, juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu.
Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:51 PM] +234 703 981 8283: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Banida bakin godiya a gareku Masoyana, kun min komae. Ina alfahari daku kamar yanda kuke alfahari dani, ina matuk'ar sanku kamar yanda kuma kuke sona.*
_Wannan shafin tukwuici ce gareku_
```Sumaiyah Isah (k'awar arzik'i)
Aysha Yusuf
Aisha zagi
Halimatu sa'adiya
Meenah shuwa
Canan Kabir (My swthrt)
Mairo! Maryam sani
Nafisah Jibril
Yahanasu Bello (Your highness)
Abdulhakam
Idris
Sultan
Abba babaye```
_Da sauran wad'anda ban fad'a bah. Duk kuna raina ina sanku sosai.._
Page 28 to 30
Juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu.
"Ka rabu dani, bana san ganinka, kun cutar dani, baxan tab'a yafewa bah"
"Pls Ummy ki tsaya, fad'amin me aka miki?"
Ya rik'o hannunta tana ta k'okarin k'wacewa, fuskanta ya soma dubawa hankalinshi a tashe
"Waya mareki?, Tel me pls"
Batace mai komai ba, ta fizge da k'arfi ta cigaba da tafiya tana kuka sosai, ba irin rok'on da bai mata ba ko sauraransa batayi ba ta cigaba da yafiya.
Haka ya hak'ura ya kyalleta badan ransa yaso ba ya hau mota ya nufi gida.
Tafiya tayi mai nisa dak'yar ta samu mai Napeep ya d'auketa zuwa gida. Koda ta isa gida har Mama ta rufe k'ofar gida, bugawa ta soma tana kuka a hankali, Mama ta fito tana tambayan waye, cikin muryan kuka ta amsa mata, jin Ummyn neh yasa ta bud'e kofan da mamaki tana kallan Ummyn
"Ummy lafiya da wannan tsohon daren"
Kuka ta sake fashewa dashi ta rungume Maman, janta tayi suka shiga cikin gida bayan ta maida k'ofan ta rufe, suna shiga falo Baba ya dogaro sandarsa ya fito
"Waye ne yake buga k'ofa, Aa! Kukan wa nakeji"
"Kaga Mallan Ummy ce da wannan tsohon daren, sai kuka take ga kuma shatin yatsu a fuskanta"
"Mene!" Baba yace yana rarraba ido kamar mai gani
Mama ta d'agota tana share mata hawaye
"Wai menene kiyi mana bayani mana"
Wani sabon kuka ta fashe dashi sannan ta soma basu labari tiryan tiryan, Baba ya saki sallati yace
"Ina! Ni shaida ce akan 'yata, baki sata Ummy, kuma nasan tarbiyan dana baki."
Sosai ran Mama ya b'aci tace
"Share hawayenki, Allah zai saka miki."
Shiru Baba yayi ranshi ba dad'i, musamman dayanji Mabrookah da duki Ummyn. Dakyar suka lallabata ta shiga ta kwanta, duk da ba baccin zatayi ba sai kuka datake tayi.
A b'angaren Jamal kuwa, yana isa gida ko k'wakwaran parking beyi ba ya shiga cikin gidan, Mami, Mabrookah, Aunty Faty dasu Twins ya samu cirko cirko a falo, ga mamakinsa Twins ya gani suna kuka, ya k'araso falon ransa b'ace yana kallan Mabrookah da alamar tambaya
"Meya faru a gidan nan naga Ummy ta fita tana kuka, kuma da shaidar Mari a fuskanta"
Aunty Faty ta turbune fuska
"Ko zaka rama mata neh? Ai sai ka tsaya kaji abinda ya faru koh kamin kazo ka hayaiyak'o mana"
Mami ta aje masa Jakan da aka gani a gabansa bayan ta bud'e dollars d'in dake ciki, ta aje masa sark'an Aunty Faty tace
"Abinda muka gani kenan a d'akinta, kai kanka kasan bazan iya zama da b'arauniya a gidana bah"
Najma tai saurin cewa
"Ya Jamal wallahi Ummy bazata Iya sata bah, ni nasan..."
Aunty Faty ta bige mata baki
"Tho me kike nufi? Mun mata sharri kenan koh, ke kinsan halin talaka kuwa? Talaka shege neh"
Ran Jamal ya k'ara b'aci yace
"Mami bai kamata ki d'au wannan hukuncin bah, batare da kinyi bincike bah."
"Wani bincike zanyi bayan na gani da idona, mu fa muka ciro kayan nan a d'akin"
"Haba Mami, Haba! Wallahi baku kyauta min bah, Meyasa zaku min haka? Yanzu da wani ido zan kalli Iyayen Yarinyan nan. Mami I Love her! Ina santa so na gaske and i want to marry her"
Mari Mami ta d'aukeshi dashi, ya dafe wajan tareda zaro ido yana kallanta, sai a lokacin ya tuna abinda ma yace. Aunty Faty ko ba shiri tayi zaman 'yan bori tana kallan Jamal d'in
"Jamal a gabana kake fad'an irin wad'an nan maganan? Lallai wuyanka ya isa yanka. Ni! Ni Maimunatu?"
Mabrookah ta fashe da kuka itama ta zauna wajan tana tuturje k'afa
"Koda yake ba laifinka bane, ni nasan asiri suka maka. Ai duk abinda kakeyi kallanka kawai nakeyi, duk abinda kake musu inajin labari"
Ta nunashi da yatsa
"Wallahi ka shiga taitayinka, kuma kasani kaida Ummy har abada. Indai ina raye bakada matar data wuce Mabrookah. Wuce ka bani guri"
Wani mummunan kallo yabi Mabrookan dashi sannan ya haura sama, Twins suma suka bishi dukansu ransu ba dad'i.
Yanda Jamal yaga rana haka yaga dare, burinshi kawai safiya tayi ya tafi gidansu Ummy yaga yanda zasu kwashe.
Ana sallan Asubah ya shirya ya fita daga gidan batareda kowa ya sani bah, kaduna ya nufa direct wajan Ramadhan dan maganar bata waya bace.
K'arfe bakwai na safe daidai yayi horn a k'ofar gate d'in gidansu Ramadhan, Mai gadi ne ya bud'e masa ya shiga ya samu guri yayi parking, Ramadhan d'in ya soma nema a waya, cikin muryan bacci ya d'auka Jamal yace
"Dallah ka fito ina k'ofar side d'inka"
Ba shiri Ramadhan d'in ya mik'e, daga shi sai boxers da singlet ya fito haraban gidan da mamaki
"Anma a hanya ka kwana koh"
Jamal ya harareshi
"Kaifa matsala ce dakai, Aa ka manta tun wachan shekaran nake hanya"
Ramadhan ya fashe da dariya yana girgiza kai, side d'in Ramadhan d'in suka Shiga, bayan sunyi breakfast Jamal ya zaiyane wa Ramadhan duk abinda ke faruwa, dan bayada abokin daya wuce shi. Saida Ramadhan ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Tho yanzu kai ya kakeso ayi?"
"Bangane ba Ram, Wallahi inasan Ummy so mai tsanani, kai kasani banda wata budurwa balle kace ko yaudaranta zanyi. Ni yanzu abinda nakeso ayi shine muje dakai ko Allah zaisa ta saurareni sai na bata hak'uri"
"But Jamal, a yanda na fahimta kamar yarinyan nan bata sanka, meyasa zaka shiga inda ba'a buk'atarka"
"She need me Ram, yarinyan da parents d'inta suna buk'atar taimako, Hmm dan baka zauna da ita baneh, Wallahi tayi ta kowane fanni"
Ramadhan ya saki dariya yana girgiza kai
"Kaifa d'an iska ne Ram, ya ina maka magana kana maidani wani abin dariya"
Wani dariyan ya kuma yi, yana cewa
"Ai naga abin naka neh naso ya wuce guri, harda wani ta had'u ta kowani fanni"
Jamal ya b'ata rai, ganin haka yasa Ramadhan mik'ewa yana cigaba da dariya ya shiga bedroom d'insa. Wanka yayi ya sauyo cikin manyan kaya yana kallan Jamal
"Anma dai ba haka zaka gidan sarakan naka ba kawani ci uban zanzaro, ka tashi ka shiga bedroom d'ina akwai kaya kan gado"
Saida ya harari Ramadhan d'in sannan ya mik'e ya shiga d'akin ya chanzo zuwa kaftan, sid'e d'in Iyayen Ramadhan d'in suka ya gaida su sannan suka sake d'aukan hanyan zaria.
Jamal ne ke driving motan har k'ofar gidansu Ummyn. Shiru dukansu sukayi Jamal ya sauke ajiyar zuciya tareda maida dubansa ga Ramadhan
"Ta ina zamu fara?"
"Muje mu nemi yaro ya mana sallama da ita"
Jamal ya saki malalacin murmushi yana girgiza kai. Ramadhan ya fita daga motan, wani almajiri ya samu ya aikashi ya mai kiranta sannan ya idan ya tambaye shi waye yace Jamal neh.
Tana zaune a falo tana tunani Mama na gefenta tana mata fad'an k'in cin abinci datayi, Almajirin ya shigo da sallama ya tsugunna bakin k'ofan ya isar da sako, Ummy tai saurin cewa
"Kaje kace bazata zo bah"
"Haba Ummy, meyasa haka? Ai ba shi ya miki laifi bah. Kije kiji mai zaice"
Ta zunguro baki ta mik'e tad'au hijabinta ta fito, a bakin k'ofar gidan ta toge fuskanta had'e. Kallo d'aya Jamal ya mata yaji gabanshi ya fad'i, jiki a sanyaye ya fito daga motan suka k'arasa shida Ramadhan,
"Salamu alaikum" Ramadhan yace yana murmushi
Bata amsa ba saima juya fuskanta datayi gefe d'aya
"Haba Ummy ai laifin wani baya shafan wani. Ko ba komai yakamata ki amsa sallama nah"
Ta sake kauda kai gefe sannan ta amsa
"Naji duk abinda ya faru kuma banji dad'i bah. Saidai ina rok'onki karki sa abin a ranki. Kiyi hak'uri da duk abinda ya faru"
Hawaye suka cika mata ido tana kallan Ramadhan
"Idan kai akayi ma abinda aka min zakaji dad'i? Talauci ba hauka baneh. Tunda nake ban tab'a sata bah haka iyayena, anma aka kirani da iyayena b'arayi"
Ta rushe da kuka tasa hijab d'inta ta rufe fuska tana cigaba da kuka. Shidai Jamal ba halin magana saima ransa dake suya
"Nasani an miki laifi, anma kiyi hak'uri"
Ta d'ago dasauri tana kallanshi
"Hak'uri? Inyi hak'uri fa kace?"
"Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu y'an adam, karki zama d'aya daga cikin masu bin kururuwan shaid'an. An miki laifi kuma ba'a kyauta miki bah, Anma kiyi hak'uri. Kada ki yanke zumuncin dake tsakanin ki da Jamal Pls"
Shiru tayi batace komai ba sai hawaye datake gogewa. Jamal ya d'ago kai yace
"Pls Ummy badan niba, nasan harda laifina a ciki, anma kiyi hak'uri."
"Shikenan komai ya wuce"
Bata jira mai zasu ce ba tayi shigewanta gida.
Ramadhan ya mik'ama Jamal hannu sukayi musabaha
"Shikenan na gama nawa koh"
Kai Jamal d'in ya gyad'a yana murmushi. Ranar a gidan Ramadhan ya kwana washe gari yasa driver ya maida shi gida.
A ranar Jamal ya d'au su twins ya kaisu gidan su Ummy, tayi murna sosai da ganinsu dan tasan ba laifinsu cikin abinda aka mata, suma sun bata hak'uri dasu Mama, sun d'an jima a gidan sannan Jamal ya dawo ya d'aukesu Ya maida su gida.
Da fad'a Mabrookah ta tari su Twins tana tambayan daga ina suke, Jamal na jinta ko kallanta baiyi ba ya bar wajan zuwa side d'in Abba.
Har suka shiga falo tana balbalesu da masifa, Aunty Faty ce ta soma tambayan mai ya faru, Mabrookah ta soma magana tana cewa
"Tun d'azu nake neman su ashe sun fita neh da Jamal, kuma bayan na fad'a musu zamuje wani guri dasu"
Aunty Faty ta had'e rai tace
"Daga ina kuke?"
Batare da wani d'ar ba Najma tace
"Daga gidansu Ummy, muje bata hak'uri"
Wayan Hannun Mabrookah ne ya fad'i ta saki baki tana kallansu
"Daga gidansu Ummy? Uban wa ya kaiku"
Najwa tace
"Ya Jamal"
Nan Aunty Faty ta soma masifa, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Mabrookah ko side d'in Abba ta nufa a fusace, kishingid'e ta sameshi kan kujera idanunsa a lumshe,
"Ya Jamal! Jamal!"
Bai bud'e idonsa ba saima gyara kwanciya dayayi
"Nasan dai kana jina, akan wani dalili zaka d'au Twins ka kaisu gidansu matsiyaciyar yariny...."
Marin dataji a kuncinta ne ya hanata k'arasa maganan datayi niya, ya mik'e a fusace yana nunata da yatsa
"Kinyi na farko kinyi na k'arshe, wallahi kika sake zagin Ummy sai na lahira ya fiki jin dad'i. Kar kiga kina abinda kika gadama ina saka miki ido, taraki nakeyi, kuma wallahi ko mutuwa zakiyi bazan aureki bah"
Ta tushe da kuka tana nuna kanta
"Akan wata banza zaka..."
Wani marin ya sake d'auketa dashi
"Fita! Kafin na la'anta ki"
"Wallahi bazan fita ba koda kasheni zakayi, akan wannan yarinyan zata dukeni? Me ta fini dashi? Diri ko meh, ko dan ni bak'a ce. Wallahi saina aureka"
Duka ya rufeta dashi dan dama yana ciki da ita, ihu ta dunga yi ba mai kwace ta, haka ya mata ligi ligi yabar side d'in.
Saida tayi kuka mai isarta sannan ta koma side dinsu, Mami ta samu a falo itada Aunty Faty, ta shigo ta fad'a jikin Aunty faty tana kuka tareda labarta mata abinda ya faru.
Ran Aunty Faty ya sake b'aci tace
"Maimuna idan bazaki d'au wani mataki ba zan d'au 'yata nabar miki gidan, akan me d'anki zai kamata yayita jifga kamar ya samu jaka, ai ba shi kad'ai bane Namiji"
"Ni Mommy ba inda zani, ina sanshi"
Hak'uri Mami ta soma ba Aunty Fatyn dakyar ta samu ta shawo kanta, a ranar Jamal yaga b'acin rai wajan Mami anma hakan baisa yayi nadama akan abinda yayi bah.
Bayan kwana biyu ya sake komawa gidansu Ummy, wannan karan ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwarsa, maganan ranan ya sake d'auko mata, nan tayi kicin kicin darai
"Na fad'a maka bazan iya aurenka ba Ya Jamal, yakamata ka cire wannan maganan a ranka indai baso kake ka b'ata shirin dake tsakanin mu bah"
Kurri ya mata yama kasa cewa komai, ya sauke ajiyar zuciya idanunsa cikeda kwalla
"Shikenan Ummy, na bar maganan kuma insha Allahu bazan k'ara tadoshi bah. Saidai inaso ki sa a ranki ni mai k'aunar ki ne koda yaushe"
Jikinta ne yayi sanyi ta zuba masa narkakun idanunta tana kallansa, mik'ewa yayi yamata sallama ya fito daga gidan dan dama a falo suke. Bai sake waiwayo wa ba har ya shiga motarsa ya tada yabar k'ofar gidan a guje.
Bin motar nasa tayi da kallo hawaye na gangara a idonta, tanajin wani abu gameda Jamal tun ba yau ba sai dai bazata iya k'arya alk'awarin data d'aukar wa Bilal bah.
Gida ta koma ta tarar da Mama a falo fuskanta a had'e
"Yanzu abinda kikayi ya dace Ummy? Keda yakamata ki rufama kanki asiri ki aureshi tunda yana sanki. Shi Bilal d'in da kike mawa baya duniya, babban abinda zaki masa yanzu bai wuce Addu'a ba. Ki so Jamal bazaki tab'a danasani bah"
Shiru Ummy tayi tana nazarin maganan Mama
"Mama kiyi hak'uri, bazan iya auren Ya Jamal bah. Ko ba dan shi ba kinga Iyayensa da k'anwarsa basa sona."
"To ai badasu zaki zauna bah. Ni nasan har yanzu Maganan Bilal ne a ranki kuma yakamata ki cire shi tunda baya raye. Yau da Bilal na raye Jamal yazo bazan tab'a yarda ki auri Jamal ba sai Bilal, to k'addara ta riga fata, kawai sai muce Allah ya sa haka shi yafi alheri"
Kuka Ummyn ta fashe dashi ta shige d'akinta.
*Bayan sati d'aya*
Hurama Abba wuta Mami tayi dole aka saka ranar bikin Jamal da Mabrookah wata d'aya, ranar karka so kaga Jamal sai ya baka tausayi, abin duniya ya taru ya masa yawa, ga sa ranan sa da Mabrookah ga Abinda ya faru tsakaninsa da Ummy. Dan tun daga ranar bai sake taka k'afarsa gidan bah. Wanda hakan sosai ya damu Ummyn dan tasan fushi yayi.
Ranar juma'a da daddare Jamal ya shirya cikin farar yadi sai baza k'anshi yake, keyn motarsa ya d'auka bai zame ko ina ba sai gidansu Ummy.
Yana isa k'ofar gidan yaga Wasu matasa run fito daga gidan d'auke da Baba Ummy ba biye dasu tana kuka, a rud'e ya k'arasa yana tambayan abinda ya faru, Mama ce tayi k'arfin halin sanar dashi ciwon sa ne ya tashi. Da taimakon sa aka sakashi a motarsa, Ummy da Mama suka shiga dukansu suna kuka, direct shika yayi dashi, nan likitoci suka duk'ufa kansa, cikin y'an mintoci Baba Ya cika.
Innalillahi wa inna ilaihi raijun!
Karku so kuga Ummy a lokacin, rikid'ewa tayi kamar mai hauka, Mama ko suma tayi saboda tsananin firgita, shima Jamal kuka ne ya sub'uce masa na tausayin halinda Ummy da Mama suka shiga, Ambulance ya biya suka d'auko gawan Baba aka mai doshi gida.
Washe gari da safe aka masa sallah, ciki harda Abba da Ramadhan da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Ummy ta koma abin tausayi, tun tana kuka sautin na fitowa har muryanta ya dishe, fuskanta ya kumbura yayi sintim gwanin ban tausayi.
Abba da kansa ya ingizo k'eyar Mami dasu Aunty Faty harda Twins da Mabrookah sukazo sukayi gaisuwa sunata yatsine yatsine, dan ranar da aka sanar dashi abinda ya faru na koran Ummy, ranar yayi fad'a sosai kamar ya ari baki, Ranar saida kowa na gidan ya gane kuransa saboda yanda ran Abban ya b'aci.
Sadakan kayan Abinci Abba yasa aka kawo, tun daga kan Shinkafa, masara, taliya, wake da sauran kayan masarufi dan yaji dad'in zama da Ummy nad'an kad'an bah.
Ranar Uku Yannin Baba su biyu sukazo daga k'auyen wudil, kallansu Ummy take cikeda takaici, tunda aka haifeta bata tab'a ganin sunzo gidansu ba saidai su Ummyn suje, anma yanzu daya rasu gashi sun d'auko k'afa suna kukan munafinci.
Bayan anyi addu'an uku