Chapter 16 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 32

45K to 48K   out of 95.6K words

da kuka

"Baka shigowa d'akina, baka kula da alamura nah"

"Jaraban ki ce ta rufe miki ido har kika ga bana shiga d'akinki. So nawa ina fad'a miki sai Ummy ce uwargida and saina gama mata ranakunta tukun"

Ta rushe da kuka ta fad'a kan gado

"Bakayin adalci Ya Jamal"

Tsaki yayi ya fita daga d'akin dan yasan ransa ne zai cigaba da b'aci a banza a hofi.

Haka rayuwar gidan Jamaludeen ta cigaba da kasancewa kullum Ummy zatayi girki tasa ma Abba, Ran Mami ko ya k'ara b'aci. Har side d'insu Ummyn tazo ta mata kacha kacha, ta kuma mata kashedin karta sake sakama Abba abinci.

Kullum lesson teachern ta saiya zo, tana jin dad'in karatun sosai. Haka idan Jamal ya dawo daga office zai zauna ya sake mata bita da kuma k'arin bayani.

Shak'uwa kam tsakanin Jamal da Ummy ba'a magana. Saidai Abu d'aya da kullum ke damunta rashin k'aunar da Mami da Mabrookah ke mata. Haka ango Jamal ya gama kwanakin sa wajan uwargida ya dawo wajan amarya.

Ranar da zai dawo karku so kuga Mabrookah baki har kunne, sai rawar k'afa ake da iyayi anama Ummy kallan banza.

Ranar bataje school ba da kanta ta shiga kicin tamai girki sai k'anshi ke tashi a gidan. Bayan ya dawo daga office sama ya haura yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska. D'akin Ummy ya lek'a ya sameta kwance ta takure waje d'aya, ya k'arasa bakin gadon ya tab'a jikinta yaji ba zafi

"Wife ya dai"

Zaune ta tashi saiga hawaye shar, nan da nan ya rud'e

"Lapia Wife me aka miki"

Kuka ta fashe dashi, ya rungumota jikinsa yana lallshinta, duk yabi ya rud'e dan ko kad'an baisan kukan Wife d'in tasa.

"Fad'amin me aka miki, waya tab'aki"

A shagwab'e tace

"Ni inaso naje gida naga Mama"

Ya d'ago fuskanta yana share mata hawaye

"Mama kikeson gani"

Ta gyad'a masa kai, wani hawayen na gangara a idonta.

"Dauko mayafinki muje"

Ta d'ago kai dasauri tace

"Dagaske"

Kai yad'an gyad'a mata, ta rungumeshi tana dariya. Murmushin jin dad'i yayi, ya k'ara janyota jikinshi ya had'a bakinsu guri d'aya. Mutsu mutsu ta soma ya rik'eta sosai. Sun dad'e a haka sannan ya janye bakinsa ya dafe kansa da hannayenshi.

Tayi saurin mik'ewa tana turo baki ta shige toilet, dakyar ya iya tashi ya koma d'akinsa. Wanka ya sakeyi ya sauya kaya zuwa kaftan fari k'ar.
A falo suka had'u itama ta shirya cikin pink shadda dogon riga. Ya matso ya kama kugunta da hannayensa biyu yana mata murmushi

"Kinyi kyau sosai Wife"

"Nagode" tace a hankali.

Bakinsa yakai wuyanta yad'anyi kissing, tayi saurin lumshe ido dan sak'on nasa ya shigeta sosai. Murya a sanyaye ya rad'a mata

"Yaushe zaki bari na nuna miki san danake miki, I'm suffering alot i need uh"

Ta janye jikinta dasauri tana murmushi, sauka tayi k'asa, yad'anyi jim tareda sauke ajiyar zuciya sannnan yabi bayanta.

Tana saukowa ta samu Mabrookah a falonta, tayi gayu cikin Top fari mai kyau da wando iya guiwa, ya matseta sosai, fuskan nan yasha makeup. Tayi kyau sosai dan itama mai kyau ce. Kallo d'aya Ummy ta mata ta kauda kai ta fita, tsaki Mabrookahn taja chan saiga Jamal ya sauko. zumbur ta mik'e ta k'araso tana karairaya

"Haba Honey ina kuma zaka bayan kasan kwana na neh yau"

Yad'an yatsine fuska tareda matsawa gefe sbda kokarin datake na chafko rigansa.

"Uzuri ne ya kama zamu fita, but idan nadawo ai shiknan"

Bai jira mai zatace ba ya fice ya barta tsaye cikeda takaici. Har tayi hanyan k'ofa dan zuwa sanar da Mami sai kuma ta fasa tuna abinda ya fad'a mata rannan. Hakanan badan ranta yaso ba ta koma ta zauna ranta b'ace.

Bakin motarsa Ummy taja ta tsaya harya k'araso, bud'e mata yayi ta shiga sannan shima ya shiga suka d'au hanya. Tsaraba ya tsaya yama Maman nad'an abinda ba'a rasa ba sannan suka k'arasa.

Dagudu ta shiga cikin gidan ta fad'a jikin Mama dake falo tana lazumi, a tsorace Mama ta janye jikinta dan bata ga fuskan waye bah, ganin Ummy ce yasa itama ta rungumeta tana tambayanta gida.

Kuka Ummy ta fashe dashi tunawa da kullum idan ta dawo gidan aikinta, Bayan ta gaida Mama wayan Baba take zuwa su sha fira abinsu. Nan ta sake rushewa da kuka, Mama ta soma lallashinta, itama ta kasa daurewa sukayita kukan tare. Dakyar sukayi shiru, Mama ta tambayeta 'yan gidan nasu ta amsa da lafiya kawai.

Jamal jin shiru shiru ba Ummy yasa yad'au ledan tsaraban ya shiga da sallama, jin sallaman shi yasa Mama gyara hijabin jikinta, ai sai kice min da mijinki kuke. Kai Ummy ta duk'ar ya shigo ya samu guri ya zauna tareda gaida Maman.

Ledan ya mik'ama Ummy ta mik'ama Mama, godiya Mama tayi tana cewa

"Badai ka gajiya"

Yayi murmushi baice komai bah, Mama tace

"D'an leka ki gaida Innan Bilal"

Had'a ido sukayi da Jamal taga yayi kini kini darai, ya mik'e yana ma Mama sallama yace yana waje. A tare suka fito da ita, a cikin zaure ya kamo hannunta yana cewa

"Badan Mama tace kije ba da bazan yarda bah"

"Babu fa komai Ya Jamal, Innansa ce zan gaishar idan kuma baka gamsu ba muje tare"

Ga mamakinta sai ji tayi yace

"To muje"

Dariya suka sa duka, saida ya tsaya zauren Innan ta shiga ta fad'a mata sannan ya shiga, sun gaida sosai ta musu nasiha mai ratsa jiki, Sannan suka fito bayan ta dire mata bandir d'in yan d'ari biyu ta amsa dakyar.

Shi mamaki yake yanda Innan Bilal take ba ruwanta da kuma san mutane, cikin gida Ummy ta koma shi kuma Jamal ya koma mota ya zauna, message d'in Bilal ne ya shigo wanda ya zama ka'ida kullum saiya turo masa, bud'ewa yayi ya karanta kamar haka

_Bazan fasa fad'ama baka isa ka mallaki abinda nakeso na kuma dad'e ina muradi bah. Ina gaf dana kwace muradina daga hannunka, na kuma maka tabon da har ka mutu bazaka manta bah. Saboda kaso abinda nakeso_

Murmushi yayi bayan ya gama karantawa, shi messages d'in Bilal dariya ma suke bashi. Ummy dakyar ta banbaro daga jikin Mama ta fito suka tafi badan ranta yaso bah. Koda sukaje gida har lokacin Mabrookah na falon ta cika tayi fam.

Wuceta Ummy ta sakeyi ta haura sama, chan saiga shi shima ya shigo

"Sannu da zuwa" tace fuska ba walwala

"Yauwa sannu" ya haura sama abinsa.

Wanka ya sakeyi ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya saida ya fara shiga d'akin Ummy ya mata sallama sai turo baki take kamar zatayi kuka. Shi kansa baisan rabuwa da Baebyn saidai ba yanda ya iya, lallashinta yayi har bacci ya d'auketa sannan ya sauko k'asa.

Kan dinning ya zauna, ya taho tana karairaya ta d'an dafa kafad'arsa

"Honey mai za'a zubama"

"Koma menene" yace atakaice.

Fried rice ta zuba masa da farfesun kaza ta tura masa gabansa tareda janyo kujera ta zauna kusa dashi

"Ko nabaka a baki neh Honey"

Ya girgiza mata kai alamar Aa, spoon ya d'auka ya d'ibo tareda bismillah ya kai bakinsa, taunawa ya soma yi yana yatsine fuska. Dakyar ya iya had'iyewa ya juyo yace

"Waya girka abincin nan"

Ta langwab'ar dakai tace

"Ni ce, ko beyi dad'i baneh"

Cike da takaici yace

"Yayi sosai"

Tayi murmushi ta sakala hannunta a wuyansa. Spoon uku ya k'ara dakyar ya ture yace ya k'oshi. Sama ya haura ta koma d'akinta ta sauya zuwa wani fitinanen night gown ta haura saman zuwa d'akinsa.

Koda ta shiga dind'in ta samu d'akin ya kashe fitila da alama ya kwanta neh. A hankali ta k'arasa ta kwanta a bayanshi, shiko takaici ne ya cika shi, ta dunga matsowa har ta cin masa, ta rungumesa tana shagwaba

"Honey shine ka juya min baya"

Yi yayi kamar bai jita bah, k'ara mak'ale shi tayi tana mai waiwayi a k'irji. Saurin rik'e hannunta yayi a harzuk'e yace

"Wai meye haka Mabrookah ki kyaleni bacci nakeji"

"Haba Ya Jamal ni fa wallahi...."

Kasa k'arasa maganan tayi jin ya turata gefen. Ba shiri ta fashe masa da kuka. Dogon tsaki yaja ya mik'e yad'au filo ya koma falo.

(Wayyo Jamalu baka kyauta bah)

Haka sukayi ta rigima har kwana bakwai, har mamakin rashin kunyan Mabrookah yake yanda ta nuna masa k'irki k'iri sex takeso, abinda shi ko a labari bai tab'aji ba ga Amarya bah. A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah.

Ummy Abduol✍🏻

[3/29, 8:36 AM] ‪+234 701 141 1639‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*



Page 44

A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah.

*****

*Bayan wata biyu*

Abubuwa dayawa sun faru, ciki harda fara karatun Ummy a demostration dake cikin ABU, dan tana k'okari sosai. Dakyar malaman suka yarda aka sakata a SS1 kuma ba laifi tana fahimta. Yanzu tana iya karatu saidai idan kalma babba ce bata iya karantawa. Duk da saida aka kai ruwa rana tsakanin Mami da Jamal, dakyar suka samu ta amince.

Tayi farinciki sosai da fara zuwanta makaranta. Yanzu sam batada lokaci, tana dawowa k'arfe biyu zatayi sallah ta jira lesson teachernta.

Yau saturday ba aiki, tun safe Jamal ke d'akinsa yana bacci. K'arfe sha d'aya da rabi Ummy ta shiga d'akin, kan gado ta hangoshi yana sharan bacci abinsa hankali kwance. A hankali sad'af sad'af ta k'arasa ta zauna kusa dashi ta soma mai tafiyar tsuntsu a k'irji.

Tunda ta shigo ya farka, lamo yayi yana sauraran abinda zatayi, salon datazo masa dashi yasa yad'anyi tsam duk da bai bud'e ido ba balle ya motsa. Ita kuwa cigaba tayi tana 'yar murmushi ita a dole tana masa mugunta.

Tun yana daurewa har ya hankalinsa ya soma tashi, bata ankara ba taji ya janyota ta fad'a kan gadon, yayi saurin danneta ya mata runfa da jikinshi

"Wife ke koh"

Baki ta chuno gaba,

"To ba kai baneh tun d'azu ina jiranka"

Ya d'an sauke lallausan murmushi

"Zaki bani sugarn ki neh?"

Jin haka yasa ta soma kici kicin zamewa, ya saki 'yar dariya

"Ai baki isa ba yarinya, tunda har kika zo sai na sha zuman nan"

Ido ta runtse dasauri jin maganan dayake, mamaki ne a ranta yanda yau yake gaya mata maganan bako kunya.

Shafata ya soma tayi saurin rik'e hannusa

"Yaaa Jamal dan Allah ka bari"

Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata

"Ina wahala sosai Wife, ki bari nasamu natsuwa. Ba wani wahala zan baki ba indai zaki saki jikinki"

Ta sake matse jikinta hawaye na gangara a idonta

"Haba Wife ni neh fah"

Bai jira mai zatace ba ya cusa bakinsa cikin nata. Wasa da ita ya soma, ina juyawa na hango 'yan Jamaludeen Fans grp sunata lek'e ta window. Zahra, Hafcycy, Xaboorah, Aunty Nurse, Zeenart, Maman sadeek sune 'yan gaba gaba. Lol

Sun d'au mintina a haka, Ummy ba abinda take sai kuka, shiko baima san tanayi bah. Saida ya jagwal gwalata sannan ya fad'a gefe yana mayar da numfashi dakyar.

Tana ganin haka tayi saurin mayar da zip d'in riganta ta fita daga d'akin dasauri tana cigaba da hawaye.

Ya dad'e a haka sannan ya mik'e dakyar ya shiga toilet. Wanka yayi ya sa kaya, Top Blue da Brown trouser. Sosai yayi kyau sai baza k'anshi yake.

Kasancewar ranar girkin Ummy ne d'akinta ya shiga, kan gado ya sameta kwance tayi samo. Murmushi yayi mai sauti ya k'arasa ya zauna kan gadon kusada ita, a tsorace ta mik'e ta zauna tareda duk'ar dakanta.

"Yaya dai Wife, ko karatun mu na d'azu bai isheki baneh a cigaba"

Ba shiri ta mik'e tana turo baki tareda girgiza kai

"Ni dai banasan wannan karatun"

'Kai Wife! Fad'a gaskiya. Bayan gashi har kinyi wanka kin chanza kaya bayan kuma nasan d'azu kinyi"

Kunya ne ya kamata kamar ta nutse k'asa haka takeji.

"Ni dai tashi muje kiyi serving d'ina, yunwa nakeji inyaso idan muka dawo sai mu cigaba da karatun tunda naga kinfi fahimtarsa sosai"

Kafa ta soma bubugawa a k'asa tana kukan shagawb'a

"Ni dai wallahi banaso"

Hannunta ya kama yana 'yar dariya suka fito falonta, da kansa yaja mata kujera ta zauna tana cigaba da turo baki. Shi da kansa yayi serving dinsu dan yasan bataci komai ba tana jiransa. Kamar yanda suka saba 'yan watanin nan shi da kansa yake bata a baki har ta k'oshi. Yauma hakan neh, duk abinda sukeyi Mabrookah na hangensu ta wajan staircase tana kallansu. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya, lokaci guda kuma ta fashe da kuka ta sauka k'asa ta koma d'akinta.

Bayan sun gama cin abincin, Ummy ta tattara kayan takai kitchen ta wanke ta dawo, A falo ta hangoshi zaune yana kallo, k'arasawa yayi ta zauna tana cewa

"Yau bamu je mun gaida Abba bah"

"Ai yau a wajansa zan yini harda gobe"

Ummy ta jinjina kai ta maida dubanta ga Tv. Wayansa dake hannunsa tayi k'ara ganin suna Abba ne yasa ya d'auka dasauri tareda karawa a kunne

"Barka da safiya Abba, to gani nan zuwa"

Ya kashe ya maida dubansa ga Ummy

"Barinje Abba na kirana"

Ta mik'e tana cewa

"Yau fa bamuje mun gaida su bah"

Ya tako a hankali ya k'araso inda take, k'ugunta ya rik'e da d'an murmushi yace

"Nagode da yanda kike nuna damuwarki akan iyayena. I love uh so much"

Murmushi ta masa, ya kai bakinsa kusada nata, tayi saurin kuccewa tana dariya

"Allah zaki sai Wife"

Gwalo ta masa yayo kanta ta gudu zuwa d'aki tana dariya.

Kwafa yayi ya sauka k'asa, dakin Mabrookah ya leka ya sameta kwance kan gado tana kuka a hankali, har ya juya sai kuma ya dawo ya k'arasa kan gadon ya zauna tareda d'agota ya had'ata da k'irjinsa

"Kukan menene kuma?"

Sake rushewa tayi da kuka ta k'ara mak'aleshi sosai

"Ya Jamal ina sanka sosai, banasan naga wata na rab'anka. Hakan na damuna. Dan Allah ka soni Wallahi ina sanka"

Ya d'ago fuskanta yana share mata hawaye

"Haba k'anwata, bar kukan ai duk abinda ke faruwa ke kikaja. Meyasa bakya jin magana nah"

Ta turo baki, hancinta ya lakata 'yar murmushi

"Its Ok ya isa haka, barin dawo sai muyi magana kinji"

Ta gyad'a masa kai ya mik'e ya fita. Ihu ta saki ta fad'a kan gado tana murna, ko ba komai yau ya rungumeta. Waya ta d'auka ta soma kiran layin Aunty Faty, bugu d'aya ta d'auka ta saki k'ara

"Shiyasa nake sanki Ummata, wallahi yau har rungumeni yayi"

Daga chan b'angaren Aunty Faty tace

"Ai bakiga komai bah, indai Jamal ne kin kusa samunsa har abada. Akwai wani magani dana amso wajan wani malami. Kina saka masa a abinci angama"

"To Mommy yaushe zaki kawo min"

"Ina nan zuwa musamman na kawo miki. Kedai kawai a yanzu ki cigaba da bin shawarata"

"Tho Mommy"

Hira suka cigaba, Aunty Faty nata kitsa mata abubuwa iri iri na yanda zata janyo hankalin Oga Jamal.

***

Da sallama ya shiga d'akin Abban, zaune ya samesa kan gado ya d'aura system a cinyarsa yana wasu ayuka. Kusada shi ya zauna ya gaida shi ya amsa yana kallansa

"Abbana gani"

Suman kanshi Abba ya shafa yana murmushi

"Ina jin dad'in yanda kake tafiyar da aiki a companyn nan, Allah ya maka Albarka"

Da Murmushi a fuskansa yace

"Ameen Abbana"

Abba ya aje System d'in dake cinyarsa ya cire medicated glass d'in fuskansa yace

"Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai"

Ummy Abduol✍🏻
[3/29, 8:36 AM] ‪+234 701 141 1639‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*



Page 45 n 46

"Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai"

Gyara zama Jamal yayi yace

"To Abba"

Abba ya cigaba da cewa

"Har yau bazan fasa fad'a maka kayi adalci a tsakanin Matanka bah. Rik'on mata biyu abu ne mai wahalar gaske, saboda kok'arin sauke hak'i. Nasani Mabrookah ba zab'inka baneh, hakan kuma kada ya tab'a saka ka wulak'anta tah."

Ya sauke ajiyar zuciya yace

"Duk wuya duk rintsi karka rabu da Mabrookah, sannan kayi k'okari ka rik'esu Amana. Karka manta dukansu Marayu ne, babu mai mahaifi a cikinsu"

Jamal ya gyad'a kai ya sake sunkuyar da kai k'asa.

"Jaleelah yarinya ce ta gari, bani fatan naga abinda zai wulak'antata a rayuwa, saboda 'yar halak ce. Ka rik'eta amana Jamal"

"To Abba insha Allahu"

Wani Jaka mai kama dana system Abba ya d'auko ya aje a gabanshi yana cewa

"Inasan ka ajiye min wannan jakan a wajanka, akwai abubuwa muhimmai a ciki. Dan ina ganin kwanan nan zanyi wani tafiya"

Kallan jakan Jamal ketayi ko k'iftawa bayayi

"Amana ce tsakanina dakai. Idan Allah ya dawo dani daga tafiyar zan amsa sannan na maka k'arin bayani"

"To Abba, anma ina zaka haka"

Saida Yayi murmushi sannan yace

"Chan wani guri zani, idan lokacin yayi zakaji"

Jamal ya jinjina kai tareda jawo jakan gabansa ya ajiye.

"Tashi kaje Allah ya maka albarka"

Ba musu ya mik'e yama Abba sallama ya koma side d'inshi. D'akinsa yakai jakar ya aje cikin wardrobe ya saka key ya kulle.

Yinin ranar Abba da Jamal suna tare, hatta abinci tare suka ci na rana dana dare. Washe gari ma haka, tare sukaje asubah, tare sukayi breakfast. Sosai Jamal yayi enjoying moments d'in, dan Nasihohi sosai ya dunga masa da nunaswa through out the day.

Uwargida Ummy tana fito wanka kenan da bayan isha'i Jamal ya shigo d'akin bayan sun dawo sallan Isha'i da Abba, sam bata lura dashi ba sboda towel d'in dake fuskanta tana goge kanta dashi.

Karo taji tayi da mutum, ba shiri ta matsa gefe a tsorace. Janyota yayi jikinsa yana k'are mata kallo. Cikin sanyin murya yace

"Wife kina horani dayawa. Bakya tausayina koh"

Baki ta turo tana kok'arin kwacewa

"Dan Allah ka bari"

Ya sake janyota jikinsa yana shin shina wuyanta

"I badly need uh Wife, Plsss"

Bai jira mai zatace ba ya soma kissing d'inta a hankali, biye

16 / 32