Chapter 31 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 32

90K to 93K   out of 95.6K words

farinciki, Abba yace

"Hakan nada kyau, mezai hana kuje yau dan gobe insha Allahu zamu koma"

Ya turo baki

"Pls Abba ku bari kud'an kwana biyu sai mu tafi tare"

Abba yayi murmushi yace

"Nabar abubuwa da dama achan kuma rashina zai iya saka damuwa"

Shiru Jamal yayi fitan da Abba keyi da dare kamar yanda suka gani rannan ya fad'o masa, baice komai bah na d'an lokaci, Ammi tace

"Aa gobe insha Allahu zamu koma, kuma da 'yata zan tafi dan harga Allah ina tsoron Abinda zaije ya dawo musamman wannan yarinyar Mabrookah"

Ya tura baki ya mik'e ya fita yana gungunai, Areefah ta doka tsale ta rungume Ummy tana farinciki, itako Jikinta ne yayi sanyi, tunani ta soma a haka ma bata samu taga Mahaifiyarta balle kuma idan ta k'ara nisa.

Ammi ta dakama Areefah tsawa

"Karki buge min 'ya dallah saketa"

Ta tura baki ta matsa gefe, Ammi ta rik'o hannun Ummyn suka haura sama.

K'arfe bakwai bayan Sallahn Magriba suka je gidan Mama, sosai tayi farinciki da zuwansu, bata wani yi mamaki ba dan Bilal ya bata labarin duk abinda ya faru. Murna wajan Ummy ba'a magana, Abinci Mama ta gabatar musu, babu wani k'yankyami Ammi da Areefah suka ci tare dayin santi dan Mama ba baya bace wajan iya girki. A nan Ammi ke shaida ma Maman tafiyar Ummy Abuja, Jikinta yayi sanyi anma ba yanda ta iya hakanan tad'anyi murmushi tare da musu fatan Alheri. Hira sosai Ammi da Mama sukayi kamar sun dad'e da sanin juna. Tare sukayi sallan Isha'i, suna nan Jamal da Areef suka shigo suka gaida Maman cike da girmamawa.

Sun shiga gidansu Bilal, Umman Bilal tayi farinciki da ganinsu sosai tare da musu godiyan abinda sukayi ma Bilal d'in. Shima Bilal yayi farinciki sosai, A nan Areef ke shaida masa Abba yace ya shirya gobe su koma. Umman Bilal ta soma godiya kamar ta ari baki.

Waya daleliya Jamal yaba Mama bayan ya saka mata sim da recharge card, tayi godiya haka Ammi da Ummyn, Ummy ne ta shiga nuna mata yanda ake anfani da wayan da kuma yanda akeyin kira.

Sun jima a gidan Ummy kamar karta rabu da Mamanta, da hawaye suka fito gidan sai dai bata bari su Ammi sun gani bah. K'arfe Tara da rabi na dare suka shiga gida, Jamal ya wuce side d'insu ita su kuma suka wuce side d'in Abba.

Har Ummyn ta kwanta kusa da Areefah bayan tayi wanka Ammi ta shigo d'akin da sallama

"Jaleelah kinyi bacci neh?"

Ta mik'e zaune

"Aa Ammi idona biyu"

Ammi ta zauna tana gefen gadon tana cewa

"Tashi kije gun mijinki, kinga gobe zamu d'au hanya sai ki shirya daga nan"

A kunyace ta mik'e ta d'aura hijab kan kayan baccin jikinta ta fita kanta k'asa. Koda ta shiga kofar a bud'e sameshi, a hankali ta haura sama zuwa d'akinta. Ga mamakinta d'akin ta samesa kwance yayi ruf da ciki da alama bacci yake.

Tausayinsa ne ya kamata ta k'arasa a hankali kan gadon ta zauna kusa da kansa. Idanunsa a lumshe yana sauke numfashi a hankali, suman kanshi ta soma shafawa a hankali. Charap taji ya chafke hannun ta bud'e ido tana kallansa har lokacin idanunsa a rufe suke ta soma kici kicin kwacewa, bata ankara ba ya mik'e tare da birkitota yana kallan fuskanta

"Thank uh very much Wife, kin daina sona koh"

Ta girgiza masa kai a shagwab'e tana tura baki

"Ba wani ki fad'amin gaskiya"

Ya kai mata light kiss yana d'an murmushi

"Ke da kika yarda akesan rabamu dake"

Ya shagwab'e fuska

"Kwana nawa kenan baki damu dani bah"

Ta fashe masa da kuka mara sauti, lokaci guda ya rude ta kwantota jikinsa yana lallashinta

"To I'm sorry, pls ki daina"

Ya d'ago kanta ya had'a goshinsu waje d'aya

"Menene fad'amin Pls, na miki laifi neh?"

Ta girgiza masa kai alamar Aa

"Ko na mari kaina?"

Nan ma ta sake girgiza masa kai,

"Na ciro kaina na baki"

Dariya tad'anyi mai had'e da kuka, ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta

"Kinga zaki wahalar min da babyna, fad'amin pls me kike so na miki da zaisa ki daina kuka"

Cikin muryan kuka tace

"Babu komai"

Ya sake matseta a jikinsa yace

"Kawai jin dad'in kukan kike"

Ta turo baki, ya kwantar da ita kan gadon ya soma lallubanta yana cewa

"To bari kiyi kukan mai dalili"

K'okarin k'wacewa takeyi ya rik'eta sosai yana cigaba da abinda yake. Ina ganin haka na tattara 'yan matan k'afana tare da taso k'eyar *Khairat* Ummu Manal mukayo waje.

Da Asubah da kansa ya had'a mata kaya tana daga kwance kan gado, zazzab'i taji na neman rufeta na kewar mijinta, saida ya gama tsaf sannan ya d'ago suka had'a ido yana cewa

"Banaso kiyi nisa dani Wife, but Ammi ta matsa ba yanda zanyi"

Ya k'araso bakin gadon ya rungumota jikinsa, hawaye suka zubo mata wanda yajisu akan kafad'arsa, d'agota yayi yasa hannunsa yana goge mata tare da girgiza mata kai a hankali fuskansa d'auke da damuwa

"Its ok kinji, dana gama abinda nakeyi zanzo mu zauna tare har abada"

Tad'anyi murmushi, rad'a ya mata tayi saurin gocewa tana dariya tana k'okarin mik'ewa

"Kai dan Allah wife, bakya tausayina koh. Kinga zamu dad'e bamu had'u bah"

Ta turo baki gaba

"Ni..ni nagaji wallahi"

Yayi saurin kamota ya had'e bakinsu waje d'aya. (Wannan karan Matan Jamaludeen Fans na koro daga d'akin mukayo waje). Lol

K'arfe sha d'aya suka gama shiri tsaf, Tuburewa Areef yayi akan bazai bisu bah, Jamal yace su barshi sai su taho tare. Areef ya d'au akwatin Ummyn ya saka a mota yana cewa

"My Aunty Mudai sai munzo"

Tad'anyi murmushi tana daga bakin k'ofan side d'in, Abba ya shiga gaba gefen Driver, Ammi ta shiga Baya itada Areefah, har Ummy ta bud'e k'ofan zata shiga Jamal yayi saurin Jan Hannunta suka shiga daga Falon side d'in Abba, d'an zaro ido tayi tana kallansa

"Suna jirana fah"

Rungumeta yayi batare da yace komai bah, ta sauke ajiyar zuciya tare da k'ara k'ankamesa, ya d'ago fuskanta ya had'e bakinsu waje d'aya bata hanasa bah har yayi mai isarsa ya janye bakinsa a hankali. D'agowa yayi fuskansa kamar mai shirin kuka

"Zanyi missing d'inki Wife"

Yasa hannunsa cikin riganta yana shafa maranta a hankali

"Take care of ur self and my Baby kinji"

Ta gyad'a masa kai hawaye cike a idanunta, Knocking sukaji daga bakin k'ofan falon Areef yace

"They are still waiting"

Tayi saurin janye jikinta ta fita yana binta a baya, Areef ne ya bud'e mata motan ta shiga, kasa k'arasawa Jamal yayi wajan mota daga chan baya yana d'aga musu hannu.

Kasa d'aga masa hannu tayi ta fashe da kuka mara sauti tana binsa da ido har suka bar gidan. Hijab d'in datasa taja gaba ta rufe fuskanta tana kuka a hankali, a haka bacci ya d'auketa cike da kewar mijinta.

Ba ita ta farka ba sai da suka shigo cikin binnin taraiya, a hankali ta bud'e ido lokacin da suka iso k'ofar gidan. Gate ne k'ato mai kyawun gaske, masu gadi suka bud'e musu suka shiga ciki. Wajan adana motoci drivern yayi parking. Areefah tace

"Kin tashi"

Ta gyad'a kai tare da d'an murmushi, Drivern ya fita dasauri ya bud'e ma Abban, Ammi ta fito Suma suka fifito. Bin gidan da Kallo kawai Ummy keyi cike da sha'awa, duk da irin tsaruwan gidan da ta baro anma nesa ba kusa ba nasu Ammi ya fisa komai.

Areefah ta d'auko Trolleyn Ummyn da nata tana cewa

"Aunty Ummy muje"

Ba musu ta soma binta abaya har suka shiga cikin falon gidan. Nan Ummy ta saki baki tana ganin Aljannar duniya, d'aki mai kyawun gaske Ammi ta zab'a mata Areefah takai mata trolleynta ciki.

Bayan tayi wanka ta fito kiran Jamal ya shigo wayanta, d'auka tayi ta soma masa shagwab'a, cike da damuwa yace

"Baby kin tafi kin barini da kewanki"

Ta tura baki kamar yana kusa da ita

"To ba kak'i ka biyomu bah"

"Ina nan zuwa dana gama abubuwan danake zan zo kinji"

Ta gyad'a kai tare da amsawa, sun dad'e suna hira yana mata kalamai masu dad'i sannan sukayi sallama. Mama ta kira suka gaisa ta shaida mata sun isa Abujan, Addu'a ta mata sosai tare da jadada mata ta zama mai biyaiya ga 'yan uwan mijinta.

Areefah ce ta shigo da sallama tace ta fito suci abinci, ba musu ta fito dinning d'in dake Falon suka zauna itada Areefah sukaci abinci suna hira gwanin ban shawa'awa. Bayan sun gama Areefah ta zagaya da ita taga ciki da wajen gidan, sosai gidan ya burge Ummy dan nesa ba kusa ba yafi nasu Mami tsaruwa. Da daddare Bilal ya iso dan ya shaida ma Abba zai taho daga baya, d'akinsa na daga chan bq shi kad'ai.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Ummy najin dad'in zaman gidan sosai, kullum sai sunyi waya da Jamal fiye da sau biyar, yakan fad'a mata yanda yayi kewanta tare da jadada mata daya gama abinda yake zai taho. Cikin 'yan kwanaki Ummy ta ware ta zama 'yar gida sosai, idan ba ka sani ba bazaka tab'a cewa ba Ammi ta haifi Ummy ba ganin yanda take kula da ita kamar 'yarta.

*Bayan Wata Biyu*

Cikin Ummy ya shiga wata na hud'u, ya d'an fito ya mata kyau sosai, ta k'ara murjewa fatarta tayi kyau har d'an kiba tayi na hutu. Suna zaune a garden d'in gidan itada Areefah suna kallan wani indian Film a system d'in Areefah wayan Ummy yayi k'ara, ganin Jamal yasa ta d'auka cikin shagwab'a tace

"Hello Kaki kazo koh? Kullum sai kace zakazo kak'i zuwa"

Daga chan b'angaren Yace

"Nafiki k'osawa nazo Baby kodan naji d'umin jikin matata na kuma gaisa da baby na"

Ta d'anyi murmushi mai sauti yace

"Kinsan meh"

Ta girgiza kai sannan tace

"Aa"

Yace

"Ki jira zuwana gobe insha Allah, and i will suprise uh tomorrow"

Tad'an tura baki

"Kullum ba haka kake cewa ba anma kaki zuwa"

Ya d'anyi murmushi

"Wallahi dagaske nake"

Bata jira mai zaice ba ta kashe kiran cike da murna

"Gobe Ya Jamal zaizo"

Areefah tace

"Dagaske"

Ta gyad'a mata kai cike da farinciki. Gaba d'aya farinciki ya lullub'e Ummyn kasa kallan tayi haka suka tattara suka koma ciki.

Da daddare Jamal ya kira Ammi ya shida mata zuwansa gobe, Farinciki wajan Ammi ba'a magana.

Ranar kasa bacci Ummy tayi saboda farinciki, sai bacci b'arawo ya saceta. Washe gari ko da wuri Ammi ta tashesu dan su soma shirye shirye dan ya shaida masa da bak'i yake.

Nan fa aka soma girki kala kala, a sauke wanchan a d'aura wanchan. K'arfe D'aya da rabi na rana aka wangale gate d'in gidan, daga d'akinta ta d'aga labule tana kallan motar data shigo, Areefah ta fita dasauri ta k'arasa wajan motan, Areef ya fito daga motan, sannan Jamal shima ya fito, batasan sanda ta sauke wani lallausan murmushi bah. K'ofar baya ya bud'e ta fito tana d'an murmushi, Ummy ta zaro ido kamar zasu fad'o tana kallan Windown.

Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Page 92

K'ofar baya ya bud'e ta fito tana d'an murmushi, Ummy ta zaro ido kamar zasu fad'o tana kallan Windown, K'ara mutsu tsuke idon tayi dan ta tabbatar da abinda take gani.

Ganin Maman ce dai dagaske yasa ta ruga a guje ta fito daga d'akin, a k'ofar Falo sukayi kicibus ta fad'a jikinta tana dariyar farinciki. Mama ta soma tureta ganin su Ammi a wajan itako sai k'ara k'ankameta take tana cigaba da dariya.

Dakyar ta samu ta saketa sai a lokacin ta lura da mutanen dake falon tad'an sadda kai k'asa, Ammi tayi dariya tana cewa

"Iyeh Jaleelah anga Mama"

Ta sake duk'ar dakai k'asa tana Murmushi, sannu da zuwa Ammi tama Maman suka wuce zuwa d'akinta. Gogan kuwa tunda ya shigo ya kafe Wife d'in nasa da ido ko k'iftawa bayayi, ta d'ago suka had'a ido tayi saurin barin wajan tana dariya. Ya bita dasauri tana shiga d'akin ya shigo shima, kallanta ya tsaya yi daga sama har k'asa dan sosai tamasa kyau ga cikinta daya d'an fito yayi d'as a jikinta.

Ganin ya nufota yasa tayi hanyan toilet yayi saurin rik'o hannunta ya janyota ta fad'a jikinsa

"Ina zakije, Wife kekoh? Bakiyi missing d'ina ba koh"

Ta tura baki gaba taba d'an doka k'afa yayi saurin rik'ota

"No tho I'm sorry karki wahalar min da kanki da babyna"

Ya sake matseta ya zira hannunsa a riganta yana shafa cikinta a hankali, lumshe ido tayi tana d'an murmushi bata ankara ba taji ya had'e bakinsu waje d'aya. Dukan k'ofan da ake ne ya dakatar dashi daga abinda yakeyi ya juya yana kallan k'ofar da idanunsa da suka rine

"Wanene?"

Muryan Areefah sukaji tana cewa

"Ammi tace ka fito kuci abinci"

Yad'an sassauta rik'on dayama Ummy tare da sake kai maka peck a kumatu

"I so much miss uh, sai mun had'u anjima"

Ta tura baki yad'anyi dariya ya shafa bakin ya fita yana waiwayenta. A k'ofa ya samu Areefahn tayi masa jagora zuwa falon Abba, nan ya samu an baje masa abinci kala kala, Areefah tayi serving d'insu shida Areef Jama sai santi yake Areefah nata dariya. Abba ya tambaya take shaida masa yayi tafiya shida Bilal.

Tarba mai kyau Mama ta samu daga wajan Ammi har tana mamakin irin kirkinsu. Kunya ne ya hana Ummy zuwa gaida Maman saida Ammi tazo da kanta tasa taje ta gaisheta.

D'akin Ammi ta bar musu dan su gana, Ummy ta tsugunna ta gaida Maman ta amsa da fara'a tana kallanta da sha'awa.

"Ya jikin naki"

Ta amsa da sauk'i tana d'an duk'ar dakai. Mama tace

"Ina mai farinciki sosai da Allah ya baki miji na gari Ummy, ya kuma baki iyayen miji masu sanki."

Maman ta cigaba dacewa

"Sai dai har yau bazan fasa fad'a miki kiyi musu biyaiya da kuma kyautata musu."

"Insha Allahu Mama zanyi k'okarin haka"

Ammi tayi knocking ta shigo tana cewa

"Maman Jaleelah ko a k'aro miki abincin neh"

Da fara'a Mama tace

"Aa Hajiya Alhamdulillah na k'oshi wallahi gama wannan ban cinye bah"

Ammi ta fita daga d'akin tana murmushi. Yinin ranan Mama na tare da Ummynta sunata hira na yaushe gamo. Ummy da Jamal basu samu daman keb'ewa ba shiko yana chan d'akinsa da aka basa yana zuba ido yaga ta inda Wife d'in nasa zata bullo.

Da daddare Abbah ya dawo, Yayi farinciki sosai da ganin 'yayan nasa, bayan yaci abinci ya natsa Ammi ta rako Mama tazo ta gaishe shi, sunyi gaisuwa na mutunci Mama ta soma musu godiya akan d'awainiyar da sukeyi da ita da kuma kulan da suke bama Ummy. Ammi tace

"Haba Maman Jaleelah babu godiya tsakaninmu ai, Wallahi muna jin dad'in zama da Ummy. Muna jinjina muku da irin tarbiyar da kuka bata. Mune da godiya"

Mama ta sadda kai k'asa tana murmushi. Abba yace

"Gobe in Allah ya kaimu Jamal zai kaiki sabon gidan daya siyan miki dan gwara ki zauna kusa dasu karkiyi nisa"

Ido Mama ta ware tana kallan Ammi da mamaki, Ammi tayi dan murmushi, Mama ta soma godiya Ammi tace

"D'anki ne ya siya miki bamu bah"

Har hawaye Mama tayi na farinciki. Ammi ta rakata zuwa d'akin da aka sauketa nan suka baje sunata hira kamar wad'anda suka dad'e dayin sabo.

K'arfe Tara da rabi Ummy ta fito wanka, kintsa kanta tayi da mayuka masu k'amshi da turaruka. Night wears masu kyau ta saka ta kwanta tare da rungume Pillow so take taje wajan Jamal anma kunyan sa dana su Ammi ya hanata.

Kira ne ya shigo wayanta da d'auko tare da dubawa, ganin Jamal yasa ta d'auka ta kara a kunne

"Wife bakya tausayina koh?"

A shagwab'e tace

"Menayi"

"I need uh right now dan Allah kizo karna mutu"

Yanda yayi maganan tausayinsa ya kamata tad'an sassauta murya tace

"Nifa kunyarsu Ammi nakeji"

"Plsss wife ina jira kinji"

Bai jira mai zatace ba ya kashe kiran
Shiru tayi tana tunanin yanda zataje ta samesa har ga Allah tausayinsa take sai dai kunyarsu Ammi bazai bari taje bah. Da haka bacci mai ya d'auketa.

Cikin bacci tayi ana shafata ta mik'e dasauri a razane, duhu ta gani a d'akin, cikin wani irin murya yace

"Shhhh! Ni neh, Pls Wife ki tausaya min"

Yanda ya rik'eta yasa ta soma kokarin kwacewa

"Ni kunyansu Ammi nakeji dan Allah ka tafi d'akinka kada tazo ta samemu"

Bai ce mata komai bah ya kwantar da ita kan gadon tare da soma mata wasu salo wanda yasa hankalinta ya d'auke. (Asubah ta gari Amaryan Jamal"

Kuka ta dunga masa gaf da asubah kan ya koma d'akinsa dakyar ya kyalleta ya fita ransa a d'an bace wanda ta lura da hakan.

Washe gari bata fito da wuri ba sai k'arfe Tara na safe, da Ammi ta soma had'uwa ta durk'usa har k'asa ta gaidata, ta amsa da fara'a tana cewa

"Kije Mama na d'akinta"

To tace ta mik'e ta shiga d'akin, Itada Bilal ta da Jamal ta samesu suna hira, ta k'arasa a sanyaye ta zauna kusada Maman ta gaisheta sannan ta gaida Bilal kanta k'asa, ya amsa shima yana sunne kai dan gaba d'ayansu kunyan juna suke yanzu. Jamal ta gayar saida ya harareta sannan ya amsa tad'anyi murmushi kawai.

A bakin Areefah take jin Maganan Gidan da Jamal yasai ma Mama, da farinciki ta shiga d'akinsa lokacin ya fito wanka yana saka kaya, saurin juya baya tayi tasa hannayenta ta rufe fuskanta tana dariya. Shima murmushi yayi sannan yad'an d'aure fuska

"Kina buk'atan wani abu neh"

Cikin sanyin murya tace

"Mungode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i, ya kuma rabaka da iyayenka Lafiya, ya kareka sa sharin mak'iya"

Sosai yaji dad'in addu'anta ya amsa a hankali yanda bazataji bah sannan yace

"Da akayi meh"

Tad'an waiwaya ta kallesa tace

"Gidan da aka saima Mama"

K'ugu ya rik'e yana murgud'a mata baki, ta saki dariya

"Ina ruwanki toh, ai mamana masai mawa ba naki bah"

Ta ruga ta fad'a jikinsa tare da kaimai kiss a kumatunsa

"Thank uh so much Noorul Qalb"

Ya d'agota da mamaki

"Repeat what u said Plsss Wife"

Murmushi ta masa ta sake rungumesa tana dariya

"I love uh so much Noorul Qalb"

"I love uh more" yace a hankali yana k'ara rungumeta, ganin take takensa yasa ta kwace da k'arfi tayi hanyan k'ofa

"Ni koh"

Tamai gwallo

"Eh d'in"

Binta yayi ta fita da gudu, da Ammi tayi kicibus tayi saurin b'oyewa a bayanta.

"Ammi kingansa koh"

Ammi ta had'e fuska

"Jamaludeen ka kiyayeni fah, kazo kenan zaka daman min 'ya. Baka ganin abinda take tare dashi"

Ya sosa k'eya, Ummy ta masa gwalo yayi kwafa ya koma d'aki yana gungunai. Summ summ tabar wajan ta shiga kicin wajan Areefah.

Bayan la'asar gari yayi sanyi sukaje ganin gidan Ammi, k'aton gida ne mai kyan gaske da tsaruwa, sosai Ummy tayi santin gidan. Suna fitowa suka shiga na

31 / 32