JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 32

18K to 21K   out of 95.6K words

na fad'uwa, Abba yace

"Yakamata a sanar ma Iyayenta dan susan halin da take ciki"

Mami ta kalli Ummyn cikeda tausayawa tace

"Hakane, saidai ina tsoron sanar dasu dan mahaifinta yanada ciwon zuciya kuma ga makanta"

Jamal ya juya dasauri yana kallan Mamin. Ramadan yayi folding hannuwansa yace

"Dole a sanar dasu Mami coz wannan fa ba k'aramin ciwo bane da za'ace za'a boye musu"

Abba yace "Gaskiya ne Ramadhan"

Shidai Jamal baice komai bah haka kuma bai daina kallan fuskanta bah, Dare ne ya tsala sosai Abba ya d'au Jamal da Ramadan suka tafi gida ita kuma Mami ta kwana da ita.

A chan gida kuwa Bacci ne ya gagari Laurat ta zauna shiru a kitchen ko b'angarensu bata tafi ba, tunanin Ummy ne ya sata gaba so kawai take tasan halinda k'awar nata take ciki. Tana nan zaune a kitchen wuraren karfe biyu na dare su Abba suka dawo, bata san sanda ta fito dagudu ba ta fito falon, ganin Abba dasu Ramadhan yasa taja burki tareda duk'ar dakai

"Yaya dai me kikeyi har yanzu baki tafi b'angaren ku bah"
Cewar Ramadhan yana kallanta
Ta duk'ar dakai hawaye cike da idanunta tace

"Ina jiran dawowan Ummy neh"

Dama kan Jamal na k'asa jin ta ambaci Ummy yasa ya d'ago yace

"An kwantar da ita a asibiti, go and have some rest gobe inasan ganinki da safe"

A sanyaye ta juya ta tafi tana kuka a hankali, kan wheel chair d'in ya sauka ya kama kafad'ar Ramadan yana cewa

"Na gaji da wheel chair d'in nan"

A tare suka haura sama harda Abba ya musu saida safe ya shiga d'akinsa, suma suka shiga na Jamal. Ruwan wanka Ramadan ya had'a masa mai d'an zafi ya shiga ya gasa jikinsa ya fito. Bai cema Ramadhan d'in komai ba ya hau kan gadon ya juya fuska dan duk hankalinsa nakan Ummy.

Washe gari da wuri suka shirya, hau Alhamdulillah k'afar tasa tad'anyi kwari, a falon sama suka had'u da Abba, A tare sukayi breakfast sannan suka sauko k'asa.

Laurat suka samu zaune kan carpet tana jiransu, Jamal ya k'arasa ya zauna ta gaidashi sannan ta gaida Abba da Ramadhan, Jamal ya kalleta yace

"Wacece Ummy a wajanki"

Dan shiru tayi sannan tace

"A nan gidan muka had'u da ita, k'awata ce kawai"

Baice komai ba ya gyad'a kai ya mik'e tareda sa hannayenshi a aljihu yace

"Ok zamuje dake sai ki zauna da ita a asibiti"

Ta gyad'a kai tace

"Tho"

Abba yace "haka yakamata kam"

Mabrookah ce ta sauko daga sama tana yatsine fuska tana kallan Jamal

"Ya Jamal ina Mami"

Wata uwar harara ya wurga mata fuskarsa ba walwala

"Ke a rayuwarki bazaki tab'a Iya gaisuwa ba koh?"

Ta turo baki tareda kauda kai sannan tace

"Ina kwana Abba, Ina kwana Ya Ramadhan"

Tad'an dubi Jamal d'in tace

"Ina kwana Ya Jamal"

Baice mata komai ba saima tsaki dayayi yabar falon.

A motar Abba sukaje asibitin, Ramadhan na driving, Abba na gefensa sai Jamal dake baya shida Laurat. Suna isa suka samu an gungurota a gado za'a maida ita d'akin da take, Mami na biye dasu.

D'akin suka shiga, nan Mami ke sanar dasu cewa anje anyi Xray d'in neh. Laurat ta tsugunna ta gaida Mami sannan ta aje basket d'in kayan breakfast.

Abba yace
"Ya jikin nata?"

"Dasauk'i saidai har yanzu bata farka bah"

Ramadhan da Jamal suka gaisheta ta amsa tareda tambayan jikin Jamal d'in, yace dasauki.

Abba ne yayi dropping Mami a gida shi kuma ya wuce aiki, nan Jamal da Ramadhan suka wuni a d'akin, Laurat nachan gefe zaune duk a takure ranta ba dad'i ganin halinda k'awar nata ke ciki.

Sun dawo la'asar lokacin Laurat na toilet Ummy ta farka, a hankali ta bud'e ido tana bin d'akin da kallo, Jamal ne yayi saurin mik'ewa ya tako zuwa inda take yana kallanta.

Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokacit guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace.

Ummy Abduol✍🏻
♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*



Page 20

Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokaci guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace.

Kuka ta fashe dashi ta runtse idonta gam tana k'okarin sauka daga kan gadon, Laurat ta fito daga toilet ta k'araso ta rik'e

"Lapia Ummy menene"

A k'irjin Laurat ta b'oye fuskanta tana nuna mata Jamal da Hannu, Ramadhan ya rik'e kafad'ar Jamal yace

"I think tsoronka takeji, muje waje tukun" ya k'are maganan da rik'o hannun Jamal d'in, har sun kai bakin k'ofa Jamal ya sake juyowa ya kalleta, sai kuka take tana cigaba da b'oye fuskanta.

Laurat ta d'agata dakyar tana share mata hawaye

"Bud'e idonki baya nan, bud'e kiga"

Dakyar ta samu ta bud'e ta zubasu akan Laurat din har lokacin kuka take

"Ki daina kukan, fad'amin menene"

Nuni ta cigaba da mata da hannu tana cewa

"Laurat Jamal, yana min fatalwa"

Laurat batasan sanda ta kyalkyalle da dariya bah, Ummy ta d'aga kai tana kallanta da mamaki

"Kai! Anma dai Ummy kin cika shirme"

Ta sake kyalkyallewa da dariya ta zauna bakin gadon tana cewa

"Bah fatalwa baneh, Jamal ne da kika sani. Allah ya bashi lapia"

Ummy ta zaro ido da mamaki

"Dan Allah dagaske"

"Ehmana, ashe mutanen b'oye ne a jikinsa ba'a sani ..."

Ramadhan ne ya shigo d'akin da sallama, duk'ar dakai tayi kunya ya kamata

"Lapia dai Ummy"

Laurat tayi dariya tace

"Ta d'auka fatalwa yake mata bata san ya warke bah"

Ramadhan yayi murmushi yace

"Oh Allah sarki, ya jikin naki"

A kunyace tace

"Dasauk'i Alhamdulillah"

Bai kuma cewa komai ba ya fita, chan sai gashi da Jamal d'in sun shigo. Kallo d'aya ya mata ya saki lallausan murmushi, itako sai sunar dakai take cikeda kunya.

Kan kujera ya zauna yace

"Sannu, ya jikin?"

Murya chan ciki kamar mai koyon magana tace

"Da...D..Dasauk'i"

Murmushi ya sake yi ya juya ya kalli Ramadhan yace

"Ram yaushe na zama fatalwa ban sani bah"

Dariya Ramadhan yayi shida Laurat, shi kuma gogan murmushi kawai yayi yana cigaba da kallan Ummyn. Ramadhan yace

"Ka mata uzuri bata sami baneh, kuma kaga tasamu buguwa akai kila ta samu matsala neh"

Maganan Ramadhan ya sosa mata zuciya, wato kenan ya d'auketa mahaukaciya ma kenan, idanunta cikeda kwalla ta d'ago tana kallan Jamal

"Ni ba mahaukaciya bace da hankalina"

Ta fashe da kuka tace

"Kuma ai bansan ka warke baneh shiyasa ka bani tsoro. Ta sake d'agowa tana kallan Jamal wanda shima ita ya zubama ido

"Ni ban kiraka da wannan sunanba sai ku ne zaku kirani da mahaukaciya"

"No bah haka baneh baki fahimceni baneh, I'm sorry ba haka nake nufi ba believe me"
Cewar Ramadhan cikin tattausan murya.

"Nagode Laurat, har dake aka had'u ana zagina bakomai"

Ta kwanta kan gadon ta janyo blanket ta rufe jikinta har kai tana cigaba da kuka.


Tab'o Jamal Ramadhan yayi

"Say something mana"

Guntun tsaki yaja ya mik'e ya kama hannun Ramadhan d'in suka fito daga d'akin. Jamal ya saki Hannunshi yana cewa

"Kaifa Matsalata dakai kenan bakin ka baida control"

"Eh naji bakina ba control, kai kuma idonka da shegen gulma, tun dazu kaketa kallan musu 'ya"

Dukan wasa Jamal ya kaimai yana dariya

"Kai kaidai Ram ta shiga uku"

Laurat ta fito daga d'akin Ramadhan ya tab'o Jamal suka juyo suna kallanta

"Dama inaso ne naje gida na d'auko mata kayan da zata chanza"

Ramadhan yace

"Taci abinci neh"

ta girgiza kai alamar A'a

"Tak'i taci tayi fushi sai kuka take"

Shiru ne ya biyo baya, Ramadhan yace

"Yanzu muje ki d'auko kayan mu dawo"

Gaba tayi Ramadhan ya tab'o Jamal yana y'ar dariya

"Na barka da ita ka lallasheta kasan kai na mata neh"

Bai jira mai Jamal d'in zaice ba yabar wajan dasauri yana masa dariya.

Jim yayi yana tunanin yanda zai shiga d'akin dan shifa bai iya magana da mace ba dan shi a rayuwarsa ko budurwa bashida.

Handle d'in ya murd'a ya shiga da sallama ciki ciki, zaune ya saketa ta jingina da pillow idanunta a lumshe, kan kujeran gabanta ya zauna yayi shiru yana kallanta a hankali yace

"Ummy"

Batace komai bah kuma bata bud'e idon ba saima turo baki datayi ta juya kai gefe, murmushi yayi mai sauti yana shafa sajen fuskansa

"Kiyi hak'uri da abinda Ram ya fad'a dazu, ba ya fad'a baneh dan ranki ya b'aci"

Shiru ne ya biyo baya na y'an mintina ya cigaba da cewa

"And kiyi hak'uri akan abinda ya faru jiya, i wasnt my self har naji miki wannan raunin. And ina godiya da lokacinki da k'arfinki da kikayi wasting wajan lura dani"

A hankali ta bud'e ido tace

"Bana buk'atar godiyanka"

Ya saki murmushi mai sauti yace

"Ok! Ok!! But kiyi hak'uri pls akan abinda ya faru"


"Na hak'ura" ta bashi amsa a takaice.

Shiru ya sakeyi har lokacin idanunshi na kanta, kujeransa ya matso dashi kusada ita sosai yace

"Dan Allah na miki wata tambaya mana"

"Ina jinka"

Ya shafa suman kanshi yace

"Anma dai lokacin da banda lapia baki tab'a min wanka ba koh"



Kuji min Jamal d'in nan fah Fans...Haha

Ummy Abduol✍🏻

[3/12, 8:20 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 21

"Anma dai lokacin da banda Lapia baki tab'a min wanka ba koh"

Maganansa sosai ya bata d'ariya, dakyar tayi k'okarin dakewa tana kallansa k'asa k'asa

"Wanka na nawa kuma"

Ta tab'e baki tace

"K'arshen magana ma jiya ni na maka wanka"

Mutuwar zaune yayi yana kallanta fuska a had'e, anma dai an gama cutar shi wallahi. Dogon tsaki yaja ya mik'e yana hararanta rai b'ace yana nuna kanshi, har ya bud'e baki zaiyi magana Mami ta turo k'ofa ta shigo, ya juyo dasauri yana kallanta har lokacin fuskanshi a had'e

"Mami yanzu abinda akamin an kyauta knan?"

Da mamaki Mami ta kalleshi ta juya ga Ummy tana kallanta

"Me kuma aka maka?"

"A rasa mai min wanka sanda banda lapia sai wannan?"

Ya nuna Ummy fuskan nan nasa a had'e

Mami da Ummy suka kyalkyale da dariya a tare

"Ai Ummy tayi d'awainiya dakai sosai, wankan ka, wankin ka, kai hatta toilet idan kayi ita..."

"Haba Mami! Habaaaaa"

A fusace yabar d'akin yayi waje, Mami ta sake kyalkyalewa da dariya,

"Allah ya shiryeka Jamal"

Itama Ummyn dariya tayi, Mami ta mata sannu tana cewa

"Nace ma dr ya sallameki ki koma gida sai a rink'a zuwa ana dubaki achan"

Godiya tama Mamin, su Ramadhan suka shigo shida Laurat

"Mami meh akaima Jamal ne naganshi yanata kumbure kumbure a waje" cewar Ramadhan.

Mami ce ta fad'amai abinda ya faru, yayi dariya yana kallan Ummy

"Oh kin rama knan"

Harara ta wurga mai ta kauda kai gefe. Likitan da kansa ya kawo musu takadar sallama bayan ya k'ara dubata tareda rubuta mata magunguna. Laurat da Ramadhan suka kwaso kayan da aka kakkawo, Mami ta rik'o Ummy suka fito.

A haraban asibitin suka had'u da Jamal sai cika yake yana batsewa, kallo d'aya Ummy tamai tayi dariya, harara ya zafga mata tareda kauda kai.

Suna isa ya d'au wayan Ramadhan ya kira Layin Abba, saida ya tambayesa ya fad'a masa gaskiya sannan hankalinshi ya kwanta. Kiran ya kashe tareda sauke ajiyar zuciya

"Lallai ma Yarinyan nan"

Yayi k'wafa yace

"Kinci bashi"

K'in saukowa yayi k'asa shi a dole yayi fushi, yayi zamanshi a d'aki abinshi yanata bacci.

Washe gari da safe Ramadhan ya koma Kaduna, hakan baima Jamal dad'i bah dan shi ke d'ebe masa kewa sbda har yanzu Abba yak'i yarda ya fita zuwa wani guri shi kad'ai.

Ummy na zaune a d'akinta, duk hankalinta nakan Iyayenta gashi har weekend yazo ya wuce bataje ba kuma tasan suna chan hankalinsu tashe dan idan har zata jima takan fad'a musu.


Laurat dake gefenta ta d'ibo abinci a plate, shinkafa da miyan naman rago sai salad, d'iba tayi takaima Ummyn baki dan bata iya cin abincin da kanta, ta kauda kai gefe idanunta cikeda kwalla

"Ummy ci mana, tun safe fa
Bakici abincin kirki bah"

"Bazan iya ci bah, bansan halinda Iyayena ke ciki bah yanzu nasan hankalinsu nachan a tashe"

"Haba ki kwantar da hankalinki, ai Mami tace yau ko gobe za'a kwance d'aurin kanki. Kinga hannu ma bazai jima ha knan"

Gigiza kai kawai Ummyn tayi, dakyar Laurat ta lallab'ata tad'anci kad'an sannan ta koma bakin aikinta ta barta ta huta. Harta kwanta aka turo k'ofan d'akin, bata d'agoba dan a tunaninta Laurat ce.

Kujera akaja aka zauna har lokacin ba'ayi magana bah. Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago suka had'a ido da Jamal, ya harareta yana cewa

"Ke baki Iya gaisuwa bah"

Fuska ta yatsine ta kauda kai gefe tace

"Ina wuni"

"Dah ban wuni ba zaki ganni"

"Oho kai za'a tambaya"

Buge mata baki yayi tasa hannuta na dama ta rik'e bakin tareda fashewa da kuka

"Allah ya..."

Rank'washin ta yayi a kai ta saki kuka tana sosa inda ya rank'washetan. Fuskansa ya matso dashi kusada nata yana kallan k'wayar idonta

"I'm a free guy, kowa nawa neh, but banasan rashin kunya"

Yayi murmushi yasa hannu ya shafa gefen fuskanta

"Na lura bakida kunya, kuma gashi ni bansan rashin kunya"

Ya saki murmushi mai sauti

"From now on ke friend d'ita ce and my Maid, uh must obey my rules"

Kallashi kawai Ummyn keyi dan ba abinda ta fahimta a maganarsa
Kwalla ta matse ta kauda kai gefe murya k'asa k'asa tace

"Kai kasan abinda kace, Mugu kawai"

Yayi murmushi tareda mik'ewa

"Mugaye dai, wayasan me kikaita min sanda banda lapia"

Batace mai komai ba ta zunguro baki ta koma ta kwanta.

Mabrookah na shigowa falon taji kamar maganan Jamal a d'akin, ji tayi anyi shiru ta girgiza kai, har ta gota d'akin zata wuce ta k'ara jin magananshi. Ba shiri ta tura k'ofar d'akin ta shiga, tsaye ta sameshi ya bada baya yana rik'e k'ugu sai kallan Ummy yake

"Ya Jamal"

Ya juyo suka had'a ido, ta k'araso kusada shi da mamaki

"Meh kakeyi a nan?"

"Meyasa bakiyi sallama ba da zaki shigo"

Ta b'ata rai

"So nawa zance kiyi sallama Mabrookah"

Ta tsuke fuska ta juya fuu tabar d'akin tana danasanin shiganta gashi ya dizgata a gaban yarinyan daya tsana.

Kallan Ummy yayi yaga ta rufe ido yayi murmushi, kwana biyu kenan da samun lafiyarsa har ya lura da rashin jituwar dake tsakanin Ummy da Mabrookah. D'akin ya bari ya haura sama dan cima Mabrookahn mutunci dan ya tsani yana ma mutum magana ya wuce


*****

Sati biyu kenan da samun lafiyar Jamal, Alhamdulillah jikin Ummy yayi sauk'i sosai har an kwance d'aurin saidai ance ta daina yawan anfani dashi sosai kuma kada ta d'au abu mai nauyi.

A sati biyun nan har saida zaman gidan ya gundureta saboda Jamal, kullum yana d'akin yayita sata surutu kuma bazai bar d'akin ba sai yaga tayi kuka sannan hankalinshi zai kwanta.

Yau Sati kamar yanda ta saba shiri take da zuwa gida sai zumud'i take dan kimanin sati uku kenan bata je gida bah duk hankalinta nakan Iyayen nata.

Kayanta set hud'u ta zuba a leda dan wannan karan kwana uku Mami ta bata. Cikeda farinciki da zumud'i take komai,
Turo k'ofar d'akin da k'arfi, ko ba'a fad'a mata bah tasan Mabrookah ce dan ita kad'ai ke shigo mata d'akin haka.

D'agowa tayi dasauri suka had'a ido

"Zuwa nayi naja kunnenki, ki daina shiga harkan Ya Jamal, ki fita daga harkansa, kada na sake ganin ki kusa dashi. Kina jina"

"Insha Allahu bazan k'ara bah"

Dogon tsaki taja

"Ku dama Talakawa haka kuke, shegen kwad'ayi a tara a kaima iyaye"

Ummy ta d'ago ta kalleta dasauri, hawaye ya gangaro mata ta share. Wani tsakin ta sake ja tabar d'akin tareda bugo k'ofan.

Rushewa da kuka Ummyn tayi, bah abinda ta tsana a rayuwanta kamar a zagan mata iyaye. Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta d'au ledan kayanta tasa hijab ta fito, Mami ta samu a falo ta mata sallama tasa driver ya kaita tayi godiya ta fito.

A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan.

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:29 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 22

A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan.

Binta da ido yayi harta shiga cikin motan, tsayuwa yayi jim sannan ya k'araso ya amsa keyn motan a hannun drivern ya shiga, hankalinta sam bai kai wajansa ba dan duk a tunaninta drivern neh.

Window taketa kallo kwalla na fita daga idonta, abubuwan da Mabrookah ke mata ya soma damunta, musamman yanzu data kirata da talaka kuma kwad'ayaiya. Hawayen idanunta ta share a hankali tace

"Indai Jamal ne daga yau bazan k'ara masa magana bah"

Taja dogon tsaki

"Kema sai ki ja mai kunne ya daina shiga harkana"

Burki taji anja da k'arfi ta juyo, ganin Jamal yasa ta bud'e baki zatayi ihu dan duk a tunainta Garba driver ne ke tuk'in. Ganin tana kokarin yi masa ihu yasa galla mata harara, k'ofan motan ta murd'a ta fita dasauri.

"Ummy ina zaki"

Batace mai komai ba tacigaba da tafiya, hakan yasa dole ya fito ya soma binta, tafiya ta cigaba dayi sauri sauri

"Wai meye haka Ummy, tsaya mana"

Dakyar ya sha gabanta, ta kauda kai gefe

"Dan Allah Ya Jamal ka daina bina, ka koma gida"

Had'e rai yayi dole ta natsu tana kallanshi, ledan kayanta ya amsa a hankali yana kallan fuskanta

"Muje mota and banasan musu"

Ba yanda zatayi hakanan ta soma binshi a baya har motan, gidan baya ya bud'e mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga.

Kallanta yayi nad'an mintina fuskarsa d'auke da damuwa

"Ummy fad'amin damuwarki, me aka miki"

Batace komai saima kauda kai datayi gefe tana kallan Window

"Fad'amin mana"

Hawaye suka gangaro mata ta soma sheshek'a, lumshe ido yayi yana jin kukanta har ransa

"Na lura kuka na miki dad'i"

Hannu tasa ta share hawayenta ta d'ago tana kallan fuskansa

"Wani alfarma nake nema dan Allah"

"Ok ina jinki"

"Inaso dan Allah daga yau ka daina zuwa inda nake, idan mun gaisa shi knan"

Da mamaki yace

"Saboda meh?"

"Babu komai, dan Allah"

Saida ya sauke ajiyar zuciya yace

"Wa yasaki ki daina min magana"

Ta d'an dago ta kalleshi da mamaki, gira ya d'aga mata

"Tell me, ina jinki"

Kuka takesan yi ta b'ata fuska hawaye cike da idonta

"Dan Allah kai kaini gida, ko ka baro na hau adaidaita na tafi"

"Zakije gida but sai kinmin alkawarin zako gad'amin"

"Bazan iya fad'ama ba kayi hak'uri"

Baice komai

7 / 32