Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
kad'ai sannan yanzu kazo kayita dukana"
Ransa idan yayi dubu ya b'aci, d'akinsa ya nufa
yana huci da alama ransa ya matuk'ar b'aci.
Batsa batsa yaga d'akin kamar yanda yabarshi rannan. Ya k'arasa jiki a sanyaye ya soma tattara kayan wajan, tsaf ya gyara komai sannan ya shiga wanka.
Ganin ya shige d'aki yasa Mabrookah fashewa da kuka ta sauka k'asa zuwa nata d'akin.
Jamal bai fito ba sai dayaji ana kiraye kirayen sallahn Magrib, ya fita ya tafi masallaci, bai dawo ba saida akayi isha'i. Falon k'asa ya tarar da Mabrookah zaune taci kwalliya cikin atampha riga da skirt, kallo d'aya ya mata ya kauda kai. Idanunta ya ciko da kwalla ta mik'e dasauri tasha gabansa, rai b'ace yace
"Matsa ki bani waje"
Ta matso inda yake yyi saurin matsawa, ta sake matsowa ya k'ara had'e rai
"Kinaso ki kaini bango Mabrookah, ki matsamin na wuce"
Ta fashe da kuka ta tsugunna guiwa biyu a k'asa
"Wallahi Ina sanka Ya Jamal, ban tab'a san wani a duniya ba inba kai bah, kaji tausayina"
Ya d'aga mata hannu alamar dakatarwa
"Kina sona kika bari aka had'a baki dake aka cutar dani? Menai muku a rayuwa Mabrookah"
Ta sake fashewa da kuka
"Ni ban gane abinda kake nufi bah, wallahi babu wanda na had'a baki dashi dan a maka wani abu. Ka yarda dani Ya Jamal"
Kallanta ya tsaya yi na y'an mintina, batare da yace komai ba ya haura sama. Direct d'akin Ummy ya shiga, yana murd'awa yaji ya bud'e, mamaki ne ya kamasa dan d'azu yanaji sanda ta rufe da key.
Kakarin Amanta yaji daga toilet ya k'arasa dasauri cikin toilet d'in ta rik'eta harta gama. Sannu ya dunga mata tana gyad'a masa kai tana hawaye.
Laulayin Ummy ne ya dawo sabo, haka suka shafe kwana biyu kullum cikin amai da zazzab'i
Cikin kwanakin sunyi zarya a asibiti, abubuwa ne suka taru suka masa yawa, ga Halinda Wife d'insa ke ciki, ga bak'in cikin abinda su Mami suka masa. Ga kuma Mabrookah wacce yanzu ya gama yarda batasan Plan d'in da su Mami sukayi bah, hasalima kullum saita tasashi a gaba tayi ta masa kuka na rashin Mami da Aunty Faty, daga shi har Ummy babu wanda ya iya fad'a masa abinda ya faru.
Yau Sunday babu laifi Ummy tad'anji kwarin jikinta, da kanta ta tashi ta had'a musu breakfast, yana fitowa wanka wayansa ya soma ringing, ganin Numbern Ram yasa ya d'auka had'e da sallama, daga chan b'angaren Ram ya sanar dashi yana san ganinsa Shi da Ummy harda Mabrookah dan akwai tambayoyin dayakeso ya musu dan washe gari za'a shiga court.
Jim Jamal yayi har Ram yayi tunanin baijishi bah, saida ya kira sunansa sannan ya sauke ajiyar zuciya yace
"Ram Mabrookah batasan abinda ke faruwa bah, bansan ta yanda zan fad'a mata bah. And kuma akwai abinda nakeso ku sani"
Ram yayi jim sannan yace
"Ok to ka bari ina nan zuwa anjima sai muyi maganar gaba d'aya"
"Tho" kawai yace ya kashe kiran. Cikin 'yan mintina ya gama shiryawa ya fito falo, dai dai lokacin Ummy ta fito daga kicin da Mugs a hannunta, amsa yayi dasauri
"Haba Wife banace ki daina aiki bah, banaso ki wahalar min da baby nah"
Tayi dariya tace
"Banaso Daddyn Bbyn ya zauna da yunwa, kaga fah tun bayan faruwan abubuwan nan baka wani ci abincin kirki bah"
Harya bud'e baki zaiyi magana, tasa yatsanta a lips d'insa
"Shhhhh...!"
Ta kama hannunsa har zuwa dinning d'in ta zaunar dashi kan kujera, babu surutu kayi breakfast kawai, har zata bud'e Warmern dake gabanta ta dakata tana kallansa
"Na manta ban kira K'anwata bah"
Yayi murmushi mai k'ara masa kyau
"K'anwa!"
Ya maimaita, ta hararesa da wasa
"K'anwata mana ko ka manta nice ta farko"
Dariya yad'anyi mai sauti sannan ya mik'e ya sauka zuwa d'akin Mabrookah, kan gadonta ya sameta ta kwanta ruf da ciki tana kuka a hankali, ya k'arasa dasauri ya d'agota dan yanzu tausayi take basa
"Haba k'anwata kukan nan kuma na menene"
Ta k'ankamesa ta sake fashewa da kuka
"Kullum idan na kira wayan Mummy da Mami bana samu, hankalina yak'i kwanciya ji nake kamar wani abu ya faru dasu"
Yad'anyi jim sannan ya d'ago kanta
"Nasan inda suke"
Da mamaki ta zaro idanunta da suka rune zuwa ja suka kumbura
"Dan Allah dagaske ya Jamal"
Ya gyad'a mata kai da d'an murmushi
"Sosai mah, anma bazan fad'a miki ba sai kin hau sama munci abinci"
Ta b'ata fuska a shagwab'e
"Nidai banajin yunwa, dan Allah ka fad'amin kaji"
Yanda ta langwab'ar dakai ta sake basa tausayi, ya d'agata zaune ya mik'e tare da kama hannunta
"I promise uh indai kikaci abinci zan fad'a miki"
Ba musu ta mik'e tana turo baki suka haura sama, kan dinning suka samu Ummyn tana jiransu, Mabrookah na ganinta ta sake mak'ale Jamal d'in sai wani zumb'ure zumb'ure take, yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna yana kallan Wife d'insa dake ta murmushi wanda ita kad'ai tasan dalilinsa
"Wife serve us please"
Ba musu ta mik'e tayi serving d'insu soyaiyar d'ankali da plantain da kuma kwai, shi ya had'a ma Mabrookahn tea. Itadai Ummy binsu kawai take da ido, Lipton kawai ta had'a dan shi kad'ai yanzu take iya sha.
Mabrookah sai kaud'i take tana wani shagwab'a, Ummy sai kallanta take tana murmushi, tana gamawa ta mik'e tabar Falon ya bita da ido ganin yanda fuskanta ya sauya.
Daru sukayi sosai shida Mabrookah dan k'in fad'a mata yayi wai sai anjima, nan ta tasashi a gaba tanata rera masa kuka. Ya dafe kansa cike da tashin hankali, ga Ummy daga gani Ranta ya b'aci, ga Mabrookah ta tasa shi gaba tana kuka. A ransa yace
"Kai auren mata biyu beyi bah"
A chan police station kuwa Ba'a sha wahala dasu Mami wajan tambaya bah, sun fad'i gaskiya kamar yanda aka buk'ata. Hakan yama Mifzal da Ram dad'i ganin bazasu wahalar da shara'a bah.
Yanma lis Ram yazo gidan, a haraban gidan yayi parking ya aika masu gadi su Kira Jamal d'in dan wayansa na hannun 'yan sanda.
A tare suka fito shida mai gadin, Jamal ya mik'a masa hannu suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa ciki. Mabrookah ya kira sannan ya shiga d'aki ya kira Ummy suka fito tare. Suna zama Mifzal shima ya shigo, duka suka tattaru a falon su Biyar. Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito dashi ya mik'ama Ram.
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 8:20 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Page 85 n 86
Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito ya mik'ama Ram
"Inaso ka karanta kowa yaji"
Ya nuna Mabrookah da Ummy yace
"Yakamata su sani a matsayinsu na iyalai na, sannan kuma ku sani dan bani da aminai kamar ku"
Jikin Ram yayi sanyi dajin maganan abokin nasa, a hankali ya bud'e diaryn ya k'urama rubutun ido sannan ya soma karantawa a natse.
Dukansu saida sukayi mamaki dajin Labarin dake k'unshe cikin diaryn, Ummy ko kuka ta dunga yi na tausayin mijin nata, lallai yanzu take k'ara godema Allah dan duk halin da ta shiga itada iyayenta bai kai wanda Jamal ya fuskanta bah.
Mifzal ya dubi Jamal har lokacin fuskansa d'auke da alamar tambaya
"Nayi mamaki sosai dajin wannan labarin, Abba da Mami dama basu suka haifeka bah"
Ya gyad'a kai idanunsa cike da kwalla, yace
"No Wonder ita da Yayarta suke san kasheka dan suci dukiyarka"
Mabrookah ta kalli Mifzal da alamar tambaya
"Bangane me kake nufi bah"
Mifzal ya juya ya kalleta dakyau dan dama haushinta yakeji
"Da uwarki da k'anwanta Mami suka had'a baki suka kashe Abba, sannan...."
"What!"
Ta mik'e dasauri ko ina na jikinta na rawa, ta fashe da kuka tare da juyawa tana kallan Jamal
"Ya Jamal kanajin abinda yake fad'a? Tayaya Mummy na da Mami zasu kashe Abba me yayi musu"
Ta kuma fashewa da kuka, Ram ya d'anyi gyaran murya yace
"Abinda Mifzal ya fad'a gaskiya neh"
Ta d'ago dasauri ta kallesa ya gyad'a mata kai
"Yanzu haka suna police station a tsare kuma gobe za'a shiga court"
Basu ankara ba ta sulale k'asa ta sume, Ummy ta rarrafa dasauri inda take tana kuka, Jamal ya k'araso wajan gaba d'aya hankalinsa a tashe.
Ram yace
"Ummy samo ruwa yi sauri"
Ta mik'e ta shiga kicin dasauri ta d'auko ruwa, Tallafo ta Jamal yayi ya d'aurata a cinyarsa Ram ya yayyafa mata ruwa, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, wani kukan ta kuma fashewa dashi tana girgiza kai
"Mummy na da Mami bazasu tab'a iya kashe Abba bah"
Ta bud'e ido a hankali ta rik'e hannun Jamal
"Dan Allah Ya Jamal kace min Mafarki nake"
Rungumeta yayi yana shafa kanta duk da shima hankalinsa a tashen yake
"Its ok, ya isa kibar kukan."
Ya mik'ar da ita tsaye ya kama hannunta tana kuka suka sauka k'asa, d'akinta ya kaita ya kwantar da ita tare da lallasheta.
Bai fito d'akin ba saida tayi shiru anma zuciyarta cike yake da bak'in ciki da takaicin abinda taji daga bakin Mifzal. Koda ya koma Falon yanda ya barsu haka ya dawo ya samesu, sai Ummy dake gefe tanata jan majina tana sharan k'walla jefi jefi. Ya k'arasa ya xauna kusa da ita tare da rik'o hannunta yana murzawa a hankali.
Ram yace
"Menene Abinyi yanzu? Akwai abubuwa sosai a gabanmu, na d'aya Court d'in da zamu shiga gobe, na biyu neman Parent d'inka"
Jamal yayi shiru baice komai bah, Mifzal yace
"Gaskiya ne wannan, anma a bari sai an gama case d'in nan sannan sai mu soma binciken real parent d'inka"
Cikin sanyin murya Ram yace
"Kayi hak'uri Friend, kad'au duk abinda ya faru a matsayin Jarabawa, Haka Allah yaso, Haka yaso ka kasance. Allah ya baka ikon cin wannan Jarabawar"
Ya amsa da Ameen Hawaye na gangara daga idonsa
"Har gobe Inasan Mami banasan wani abu ya sameta, ko ba komai Uwace min dan bata rageni wajan Tarbiya da neman Ilimi bah"
Mifzal yayi ajiyar zuciya yace
"Hakaneh, babban tashin hankalina ma shine idan aka shiga court, Allah kad'ai yasan hukuncin da za'a yanke musu. Kasan sharri'a sab'anin hankali ce"
Kuka Ummy keyi sosai daga zaunen datake, wani amai ya taso mata ta mik'e dasauri tayi d'akinta, Jamal ma ya mik'e zaibi bayanta, Mifzal na ganin haka ya mik'e yana gyara rigan jikinsa
"Mu zamu wuce, Pls gobe k'arfe Tara na safe za'a shiga Court, make sure kin iso kamin lokacin"
Kai kawai ya iya gyad'a musu ta bi bayanta dasauri.
Amai sosai ya sameta tanayi, duk abinda tashi saida ya fito, kuka take sosai tana maida numfashi ya k'arasa ya rungumeta ta baya yana mata sannu. Saida ta gama sannan ya saketa ya d'auraye mata baki ya maidota d'aki.
Ya d'aurata kan gado ya k'ara rungumeta tare da lumshe ido. Bashi da wani gata yanzu daya wuce Wife d'insa, duk sanda suke tare sai yaji damuwarsa ya yaye, Maraicinsa ya gushe. Ya k'ara mak'alkaleta itama ta rungumesa murya chan ciki ciki tace
"Ya Jamal rayuwarka darasi ne da kuma ishara ga duk wanda ya jita, nasha wahala sosai a rayuwa ni da Iyayena tunda Mahaifina ya soma rashin lafiya, danaga Rayuwarka na kuma ji labarinka sai nake ganin namu ba komai baneh. Tabbas Rayuwar daka tsinta kanka a ciki Jarabawa ce daga ubangiji, kayi hak'uri sannan ka maida lamuranka ga Allah"
Ta k'ara rungumesa tace
"Kada ka k'ara tunanin bakada kowa, Am here for you, zan zame maka Uwa, uba dangin daka rasa"
Ya fashe da kuka yana rungume da ita
"Thank uh Jaleelah, Allah ya miki Albarka"
Janye jikinta tayi daga nasa ta d'ago fuskanshi dake ta zubar da k'walla
"Shhhh! Ka daina kuka dan Allah, ko kanaso nima nayi?"
Ya girgiza mata kai yana kallan kwayan idanunta dake cike da k'walla
Ta rik'o hannunsa tasa a maranta tana kallansa
"Ni da Babyn mu muna tare dakai"
Ta k'are maganan tana kuka a hankali, ya rungumeta tsam a jikinsa yana lallashinta. Ta shagwab'e fuska tace
"Pls Ya Jamal inaso inje inga Mama, rabona dana ganta wata d'aya kenan kuma nasan itama tanasan ganina kawaici ne ya hanata zuwa"
Ta k'are maganan tana zumb'ura baki, ya ja bakin ta saki k'ara k'adan. Murmushi yayi yace
"Ba yanzu bah, ni nama manta jiya danaje tace na gaishe ki"
Ta kallesa da mamaki, ya kashe mata ido d'aya ya mik'e ya fita, chan sai gashi da wani bak'in leda ya mik'a mata yace
"Tace na baki"
Jiki na rawa ta amsa ta bud'e, kayan k'amshi ta gani da sinadaran girki kala kala, sai wani leda kuma dake ciki shima ta bud'e, magunguna ta gani ko ba'a fad'a mata ba tasan na menene, tad'anyi murmushi tana cigaba da kallan cikin ledan.
Karo sukayi ta d'ago tana kallansa tare da rufe ledan
"Meye kake kallan min sirri"
Ta murgud'a baki tana k'ara b'oye ledan a bayanta, yayi dariya ya k'ara matsowa
"Idan abin ci ne to a raba aba kowa nasa dan bazan yarda bah"
Hararan wasa ta masa
"Bayan ka riga ka bud'e ka d'auka"
Ya d'aga hannu dasauri kamar criminal
"Babu ruwana, yanda ta bani haka na d'auko na aje, duk ke kika mantar dani jiya da nabaki da wuri"
Ta sake turo baki
"Dan Allah Ya Jamal ka kaini"
Ya mak'e kafad'a yana kwaikwayan irin magananta
"Aa nak'iya"
Takai mai dukan wasa ya rik'e hannun ta saki kukan shagwab'a, kwantar da ita yayi kan gadon ya soma lallubenta, ina ganin haka na tattara nabar musu d'akin.
K'arfe takwas da rabi na dare ya fito daga masallaci bayan yayi sallahn isha'i, side d'insu ya shiga dasauri dan so yake ya fita, Mabrookah ya samu a falonta tsaye duk tayi wani laushi, rana d'aya harta fad'a, ya k'arasa kusada ita dan yanzu tausayi take basa ya kama hannunta yad'an matse ta lumshe ido wasu sabin hawaye suka gangaro mata
"Haba k'anwata, banace ki daina kukan nan bah"
Ta bud'e idanunta a hankali tana kallansa
"Bazan iya daina kuka na ya Jamal har sai naje naga Mummy da Mami, dan Allah ka kaini wajansu"
Yad'anyi jim yana kallanta, shima chan d'in yakeso yaje kafin gobe a shiga court yaji yanda za'ayi, dan har a zuciyarsa baisan wani abu ya samesu, ko ba komai Mami tamkar mahaifiya take a garesa, sannan Aunty Faty surikarsa ce. Maganan datayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, ya d'ago yana mata murmushi,
"Ki bari komai will be fine insha Allah"
Ta girgiza masa kai tana cigaba da kuka
"Aa pls, dan Allah Ya Jamal"
Ya k'are maganan da matsanancin kuka, ya d'ago kanta yana share mata hawaye
"Stop crying"
"Dan Allah zanje na gansu"
Ya sassauta rik'on daya maya mata yace
"Jeki shirya"
Dasauri ta shiga d'akinta ya bita da kallo tare da sauke ajiyar zuciya. Sama ya haura ya shiga d'akinsa ya sauya zuwa kaftan ya fito ya shiga d'akin Ummy, ta gama shiryawa kenan cikin doguwar rigar Atampha tana murza powder a fuska ya shigo, wajan mirrown ya k'arasa ya sak'ala hannunsa a wuyanta
"Kinyi kyau sosai Wife"
Tayi murmushi tana kallansa ta mirrown
"Ya Jamal ina zaka?"
Ya sunkuyo da fuskansa kusada nata yace
"Ko kin fasa zuwa wajan Maman neh"
Ai dasauri ta mik'e har tana kokarin turesa ta d'auko Hijab sai dariya yake mata, hannunta ya kama suka fito, a falon k'asa suka samu Mabrookah itama ta shirya, Tana ganinsu tare taja guntun tsaki tayi gaba suna binta a baya, tun daga k'ofar falonsu ya danna button d'in security motar ta k'arasa ta bud'e dasauri ta shige gaba.
Sam Ummy bata nuna damuwa ba ta bud'e baya ta shiga yaja suka bar cikin gidan. Jefi jefi shida Ummyn suke hira har suka k'arasa kofar gidansu Ummyn, ta bud'e dasauri ta fita, ganin bai fitoba yasa ta juya tana kallansa
"Ka shigo mana"
Yad'an kalli Mabrookah dake gefensa tana cika tana batsewa yace
"Zamu d'an fita ne idan zan biyo na d'aukeki sai na shiga mu gaisa"
Batace masa komai ba ta juya ta shiga cikin gidan rai b'ace.
Police station d'in suka nufa, sunyi sa'a sun samu Mifzal bai riga ya tafi bah. Jamal na masa bayani ba b'ata lokaci yasa wani daga cikin 'yan sandan ya fito dasu zuwa secret room.
Mifzal da kansa ya musu jagora zuwa d'akin, Kallo d'aya Mabrookah ta musu ta fashe da kuka ta k'arasa inda suke zazzaune, Mami nakan wheel chair duk sun rame kamar basu bah.
Ta tsugunna gabasu tana kuka tana kallansu
"Mummy, Mami meyasa kukayi haka? Meyasa kuka bari shed'an yaci galaba akan ku"
Barin musu wajan Mifzal yayi, Jamal na bakin k'ofa yana hawaye, kallan Mami yake tayi ganin yanda k'afanta ke nannad'e da bandage sai zuban ruwa yake yana wani irin k'arni.
Daga Mami har Aunty Faty kasa magana sukayi sai bin Mabrookahn suke da kallo, A hankali Jamal ya soma takawa zuwa wajan, Mami da d'ago ad'an tsorace tana kallansa, ya tsugunna guiwa biyu gabanta ya kama k'afarta dabaida ciwo yana kallan fuskanta hawaye na zuba a idanunsa.
Tayi saurin kauda fuska ta fashe da kuka, ya d'ago yace
"Har gobe Mami ke uwace a gareni, har yanzu matsayinki a rayuwata yana nan bai chanza bah, duk abinda kikamin na yafe miki Mamina"
Ta janye k'afanta daya rik'e tana cigaba da kuka
"Rud'in duniya da bin zugan shaid'an su suka jamin na shiga wannan halin, ka gafarce ni D..."
Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai. Kasa magana Mabrookah tayi sai kuka datake kamar ranta zai fita.
Mifzal ya shigo ya fad'a musu lokaci yayi, hakanan sunaji suna gani suka bar wajan suna kuka suna waiwayen su Mamin.
Ransu duk ba dad'i suka shiga mota suka bar station d'in, saida ya tsaya ya d'au Ummy daketa cika tana batsewa sannan suka nufi gida.
Daru suka sha daren ranar shida Ummyn dan sosai ranta ya b'aci na barinta dayayi suka wuce.
Washe gari ranar da za'a shiga Court, da wuri ya tashi ya shirya saidai Yau Wife d'insa ta tashi da zazzab'i, dole saida ya tsaya ta shirya sannan suka sauko yana rik'e da ita dan jiri take gani, Mabrookah suka samu a falo ta shirya tana zaune tana jiransu lokacin k'arfe takwas da rabi.
Shi da kansa ya bud'e ma Ummy mota ta shiga gaba, Mabrookah ta turo baki ta shiga baya suka d'au hanya.
Tara daidai duka isa Court d'in, sun samu mutane duk sun hallara, bayan zazzauna aka soma gabatar da k'aran da Areef d'an Alhaji Ameenu ya kawo akan abi ma Mahaifinsa hak'insa, bada umarnin a kawo Alhaji Ameenun Alk'alin yayi, nan wani d'an sanda ya shigo da Alhajin da Bilal, Ummy dake rakub'e jikin Jamal saboda sanyin datake ji ta zaro ido tare da d'agowa tana kallan Bilal wanda duk ya