Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
mace, ki bani had'in kai kawai dan yau babu wanda ya isa ya hana damo kaiwa ga harawa"
Kuka take sosai tana matsawa baya yana cigaba da binta, kokarin kwacewa Jamal ketayi yana wani irin k'ara idanunsa na zubar da hawaye, su uku suka rik'esa duk yanda yayi ya kwace kasawa yayi.
Cikin wani irin murya yace
"Kada kayi haka dan Allah, ka fad'i duk abinda kakeso zan maka."
Ya saki dariya yana shafa gefen fuskan Ummyn,
"Bana buk'atar komai sai matarka, tun randa na fara ganinta na kwad'aitu da ita. Dan nasan zan huta da ita sosai"
Jamal yayi saurin runtse ido yana cigaba da hawaye, Ogan ya tsugunna inda take makure a bango yana k'okarin kai hannunsa k'irjinta, tayi saurin goceta ta sake fashewa da kuka
"Dan Allah kayi hak'uri kamin rai, ni matar aurece. Ka dubi girman Allah ka kyalleni"
Ya saki dariya mai sauti yace
"Idan kinga nabar d'akin nan sai naga na aikata abinda nakeso dake"
Kokawa suka soma, Jamal nata ihu yana k'okarin k'wacewa had'e da rok'on ogan. Wani daga cikin yaransa ne ya shigo d'akin dasauri ya k'arasa inda Ogan ke tsugunne yamai magana a kunne.
Mik'ewa yayi dasauri yama sauran yaransa dake rik'e da Jamal alama su sakeshi, ba musu suka sakesa ya fita dasauri suka bisa a baya.
Ummy na ganin haka ta rarrafo ta dawo inda Jamal d'in ke tsugunne ta rungumesa, murya chan k'asa yace
"Kwance ni Wife"
A tsorace ta kalleshi ya gyad'a mata kai, batare da b'ata lokaci ba ta soma kwance sa, hannun ta kwance dakyar sannan ya kwance k'afan da kansa.
Hannayensa ya bud'e mata yana kallanta, dasauri ta fad'a jikinsa tana kuka. Ya lumshe ido yana shafa suman kanta da duk ya b'aci da k'asa
"I'm Sorry Wife"
K'ofar d'akin aka banko, suka d'ago suna kallan k'ofan, ba shiri suka mik'e dukansu suna bin k'ofar da kallo.
Cikin takun k'asaita ta k'araso cikin d'akin Oga da yaransa na mara mata baya, cikin tashin hankali Jamal yace
"Au..Aunty Faty!"
Dariya tayi mai sauti sannan ta juya tana kallan bakin k'ofan, Mami ya gani sanye da bak'in dogon riga tasha No respect a fuska tana taunar chewing gum. Suma neh kawai Jamal baiyi bah, idanunsa kuwa kamar zasu fad'o saboda firgici. Ta k'araso gabansa ta tsaya tana kallansa da murmushi
"Kana Mamaki koh, sai dai ba abin mamaki baneh dan wannan kad'an kenan daga aikin da mutum kan iyayi"
Kuka Jamal ya fashe dashi tana cigaba da kallanta
"Meyasa kikayi Haka Mami? Mena miki? Me Abbana ya miki"
Ta fashe da wani irin dariya tace
"Ban tab'a san Mahaifinka bah, haka kai. Ni nan daka gani na auri Mahaifinka neh kawai dan dukiyarsa. Ganin sanda yake nuna maka yasa abin ya soma damuna shine nasa aka tura maka aljanu dan su hanaka jin dadi ko soyaiyar dake tsakanin ku zai ragu"
Ummy sai rarraba ido take cike da mamaki haka jikinta sai rawa yake jin maganganun dake fita daga bakin Mamin.
Aunty Faty ta karb'e da cewa
"Mun dad'e muna san kawar dakai dan muci dukiyar Mahaifinka saidai kuma hakan bazai yuwu bah in ba mun fara kawar da mahaifin naka bah"
Ba shiri Ummy ta sulale k'asa guiwayu biyu ta fashe da kuka jin maganar da Aunty Faty keyi, haka shima Jamal kukan yake daga tsaye yana kallansu da tsananin firgita. Rai b'ace Mami ta nuna Ummy dake tsugunne tana sharb'ar kuka
"Tun danake a duniya ban taba tsanar wani kamar yanda na tsaneki bah, dan ke kika fara rusa min plan d'ina. Ban tab'a tunanin kawo ki zai shafi abinda nasa agaba bah."
Wani zuciya ne ya ciyo Jamal yayi kan Aunty Faty dasauri Yaran Ogan suka rik'esa yanata k'okarin kwacewa yana kuka
"Kun cuceni Mami bazan tab'a yafemuku kashemin mahaifi da kukayi ba da kuma cutar dani da matata da kukayi"
Mami da Aunty Faty suka kyalkyalle da dariya, wasu documents ta d'auko cikin wani envelop tare da biro tana cewa
"Gidaje guda uku a cikin garin Abuja wanda kowanne yakai darajar Million Ashirin da biyar, Filaye Guda biyar a garin kaduna da kuma gidan gona dake garin Shika. Hannu kawai nakeso kasamin a nan dan na mallaki ab..."
Yayi saurin katseta da cewa
"Bazan sa ba ko kasheni zakuyi bazan sa bah"
Ummy ta sake fashewa da kuka tana kallansu, Mami ta kyalkyale da dariya tana mik'a masa takardan
"Kasa min hannu tun muna shiri nida kai"
Rai b'ace yace
"Bazan sa bah"
Ogan ta kalla, yama yaransa alama, duka suka soma kaima Jamal d'in tako ina yanata ihu. Ummy sai kuka take tana daga gefe dan wasu cikin yaran sun zagaye tah.
Mami ta tsayar dasu sannan ta mik'a masa takardan
"Jamaludeen kasa min hannu a takardan nan"
Ya d'ago fuskanshi dake zubar da jini yana kallanta
"Bazan sa bah"
Aunty Faty tace
"Bai horu baneh dakyau har yanzu"
Sanda Mami ta d'auka dake gefenta ta matso inda Ummy ke zaune tana kallanta, Yaran suka d'agata tsaye tanata san kwacewa tana kuka. Duka Mamin takai Ma Ummy a ciki da k'arfi, wani k'ara ta saki ta sulale wayan.
Jamal ya saki wani irin k'ara ya fizge daga rik'on da suka masa ya k'arasa wajan da Ummyn ke kwance yana kuka.
Yawo Mifzal da sauran tawagar su suketayi a cikin k'auyen tare da yima mazauna k'auyan tambayoyi anma ba wani labari. Har sun cire rai zasu koma suka hango motar Mami ta wuce a guje. Dasauri Mifzal yayi reverse yama sauran 'yan sandan Alama akan su dakata, binta ya soma shida Ram a baya ta yanda bazasu san binsu ake bah. Tafiya sukayi sosai, tayi wata kwana wata babbar mota ta fito itama daga kwanar dole suka tsaya har saida motar ta wuce sannan suka suka shiga. Abin haushi basu ga motarta bah. Mifzal ya daki steiring motan yana tsaki.
Parking yayi gefen Hanya Ram ya fito yana duduba wajan, shima Mifzal ya fito, shedan tayan motan Ram ya gani ya nunama Mifzal, dasauri suka soma bin shedan suna ta tafiya a hankali suna cigaba da bi. Sauran 'yan sandan yama waya tare da musu kwatancen inda suke suma suka biyo bayan motar Mifzal d'in.
Mami ta saki Lallausan Murmushi tana cewa
"Idan baka samin hannu bah, zan kashe Ummy na kashe abinda ke cikinta"
Cikin wani irin kuka yace
"Me na miki a rayuwa Mami? Kefa Uwace a gareni, kinyi min komai a rayuwa kin bani tarbiya, ban chanchanci haka daga gareki bah."
Ta saki dariya tace
"Ni ba Uwarka bace, ban tab'a sanka bah Jamal. Duk abinda kaga inayi yana cikin Plan d'ina neh. Da kuma ganin idon mahaifinka"
Ta mik'a masa takardan
"Karb'a kasa min hannu"
Ya girgiza kai tare da maida dubansa ga Ummy dake kwance bata numfashi, kanta ya d'aga ya d'aura kan cinyarsa yana kuka sosai. Hannu ta mik'ama Oga ya saka mata bindiga, ta saita Ummyn dashi rai b'ace tace
"Ko ka Sa min hannu ko na kashe Ummy"
Yasake rushewa da kuka, he has no choice ya amsa takardan yana kuka ya soma signing hawaye na d'iga jikin Papern. Yana gamawa ya mik'a mata ta amsa ta duba sannan ta maida dubanta ga Oga.
"Ya cika aikinsa sai kuma ku cika naku"
Oga ya saki dariya ya amsa bindigan daga hannunta yana cewa
"An gama ranki ya dad'e yau wasu zasuyi kwanan lahira"
K'ofar d'akin aka banko a tsorace duka suke bin k'ofar da kallo, 'yan sanda ne sukayi ta shigowa kowannen su da bindiga a hannunsa, Mami ta saki salati haka Aunty Faty suna kallan juna. Mifzal da Ram suka shigo a tare
"Drop ur Weapons" cewar Mifzal, ba musu duka yaran Ogan suka aje Bindigogin su. Ram ya k'arasa inda Jamal ke tsugunne yana dubansu da mamaki.
Rai b'ace Mifzal yace
"Mami kinji kunya"
Ta had'e girar sama data k'asa, d'aya daga cikin 'yan sandan yace
"Hands Up every Body"
Dukansu suka d'aga hannu sama, cikin kuka Jamal yace
"Ram Ummyna bata numfashi"
Ram ya d'auketa chak, jini Jamal ya gani a inda aka d'agata ya saki k'ara shima ya fadi a wajan.
Iya rud'ewa Ram da Mifzal sun rud'e, Dasauri Ram yakai Ummyn Mota sannan ya dawo shida wani d'an sanda suka d'au Jamal d'in. Mami ta fizge Bindiga daga hannun Oga ta saita Jamal d'in zata harbasa taji saukan harsashi a k'afarta.
Ta saki Ihu ta fad'i wajan tana kuka dafe da k'afarta, handcop duka akasa musu aka ingiza k'eyarsu, ita kuma wasu 'yan sanda suka d'aukota aka sakata a bayan mota sai kuka take da ihu tana dafe k'afarta.
Asibiti Ram da wani d'an sanda sukayi dasu Jamal, ba b'ata lokaci aka amshesu tare da basu taimakon gaggawa. Cikin awa da bai wuce d'aya ba Jamal ya farka tare da mik'ewa zaune. Ram dake kusa dashi yayi saurin rik'esa yana masa sannu
"Ram ina Ummyna"
Shine Farkon Abinda ya furta, cikin kwantar da hankali yace
"Tana lafiya lau, ka kwanta ka huta"
Ya fizge jikinsa yana k'okarin mik'ewa
"I want to see her Pls"
Ya sake maidasa zaune yana lallashinsa
"Bazan iya zama batare da naga Wife d'ina bah. Dan Allah ka kaini na ganta hankalina ya kwanta"
Hawaye suka cika masa ido, gaba d'aya yanzu tausayi Jamal keba Ram baice komai ba ya mik'e ya kira wata nurse ta cire masa drip d'in hannunsa. Da taimakon Ram d'in yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn take.
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 8:18 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Page 81 n 82
Da taimakon Ram yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn ke take. Duk da yanda yake ganin jiri hakan bai hanasa sakin Ram ba ya murd'a kofan d'akin ya shiga.
Kwance ya sameta kan gadon marasa lafiya tana bacci, hannunta sanye da canular ana mata k'arin jini. Ya k'arasa ya zauna bakin gadon yana kallanta hawaye cike a idonsa, sai yanzu abubuwan da suka faru suka dawo masa. Hawaye ya soma kansa k'asa har lokacin bai bar mamakin Mami da Aunty Faty bah.
Yana nan zaune kusa da ita har bayan minti talatin, Ram da Mifzal suka shigo d'akin a tare. Hannu Mifzal ya mik'a masa sukayi musabaha sannan ya tambayesa ya jikinsa.
"Dasauk'i. Nagode Mifzal"
Ya juya ya kalli Ram yace
"Nagode Ramadhan"
Mifzal yayi murmushi yana d'an bubuga kafad'ar Jamal
"Mu dakai ba godiya"
D'an motsawa Ummyn tayi gaba d'aya hankalinsu ya koma kanta, ta b'ata fuska ta sake juya kwanciyanta. Duk idanunsu nakanta, juye juye ta soma tana rik'e da maranta tana kuka a hankali har lokacin idanunta a lumshe.
A rud'e ya rik'o hannunta
"Open ur eyes Wife, ni neh, Jamal ne"
Kasa bud'e idon tayi har lokacin tana juye juye, Ram ya fita dasauri chan sai gashi shida Dr da wasu nurses. Rok'onsu Likitan yayi akan su bashi waje, dakyar Jamal ya saki hanunta suka fita daga d'akin har lokacin bai daina hawaye bah.
Sun d'an dau mintina sannan suka fito, Jamal ya k'arasa inda likitan yake tsaye
"Dr hw is she"
Da murmushi yace
"Komai Lafiya lau, munyi nasarar ba cikin jikinta kariya, yana lafiya ba wani abu. Jinnin data zubar da kuma buguwan data samu a maranta ne yake haddasa mata ciwo a maranta. But data farka zata dawo normal"
Jamal ya mik'a masa hannu cike da murna, sukayi musabaha ya wuce. Ba yanda ba'ayi da Jamal ya koma d'akinsa bah dan shima yana under observation anma yaki, dole aka d'auko wani gadon aka sa a d'akin da Ummyn take suna karb'an medication tare.
K'arfe takwas da rabi na dare lokacin Ram da Mifzal sun wuce bayan sun aje mai duk abinda yake buk'ata, tashi yayi daga kan gadonsa ya zauna kan kujeran dake kusada Gadon Ummy tare da d'aura kansa kan gadon. Nan da nan bacci mai nauyi da dad'i ya d'aukesa cike da mafarkai kala kala.
A Police Station kuwa, Har aka kai Mami bata daina Ihu bah dan ji take kamar k'afar ya guntule ne gaba d'aya, tana kuka Aunty Faty nayi na danasani.
Wani likita cikin 'yan sandan ne ya cire mata bullet d'in kafar nata tare da Treating wajan aka turasu a ceil itada Aunty Faty. Kan kace me dambe ya kaure tsakanin su wannan tace laifin wannan neh, wannan ma tace Laifin wannan neh. Babu wanda ya tankasu cikin 'yansandan, Mami ko taci duka wajan Aunty Faty dan ta kasa kwatan kanta saboda k'afarta dake mata zugi dan ko takawa bata iyawa.
Iyalen Alhaji Ameenu ne suka zo garin Abuja dan labarin ya riskesu, Hankalinsu a tashe sukazo Police station d'in. Matarsa na ganinsa ta fashe da kuka
"Alhaji haka ka koma? Garin yaya haka ta faru"
Kasa magana Alhaji Ameenu yayi sboda tsananin b'acin rai, d'ansa kuwa ransa idan yayi dubu ya b'aci, kallo d'aya yama Abban nasa ya fita daga Station d'in.
Duk yanda Matar Alhaji Ameenu taso a bada bailing mijinta da Bilal k'i sukayi kan cewa basu gama bincike akansu bah. Ba yanda ta iya hakanan ta hak'ura tabar Station d'in tana kuka.
Wayan d'anta mai suna Areef ta soma kira har ya katse bai d'aga ba kuma ga motarda sukazo dashi a parke a k'ofar station d'in. Cikin motar ta zauna tana cigaba da hawaye na tausayin Mijin nata. Tana nan zaune ta hangosa ya sauka a Napeep shida wani sun shiga Station d'in. Ta fito ta bisa da sauri
"Areef!" Ta kira sunansa, ya juyo tare da amsawa ransa a b'ace
"Ina kaje inata nemanka"
Ba tare da wani tunani ba yace
"Naje Court ne nakai k'ara"
Da mamaki ta kallesa
"Kasan me kake fad'a kuwa"
Kamar zaiyi kuka yace
"Haba Ammi ki dubi abinda akama Abbana fah akan abinda baiji ba bai gani bah, nidai bazan tab'a yarda bah"
Bai jira mai zatace ba ya shiga cikin station d'in.
Mifzal na Office d'insa takardan sanmacin da Areef ya kawo ya samesa, bayan ya karanta ya saki lallausan Murmushi tare da duba date d'in da za'a shiga Kotun, ya sake yin murmushi
"Allah ya kaimu! Ayita ta k'are"
•••••••
Bud'e ido tayi a hankali tana bin d'akin da kallo cike da mamaki, tad'an juya gefenta na dama, Jamal ta gani ya d'aura kansa a gadon da take yana bacci bil hak'i da gaskiya.
Tayi murmushi tare da cusa hannunta cikin suman kanshi tana d'an masa waiwayi, ya bud'e idonsa dakyar dan bacci ne fal a idonsa, murmushi ta masa ya bud'e ido dasauri tare da mik'ewa zaune.
Hannu ta bud'e masa tana masa murmushi dan yanzu gaba d'aya tausayi yake bata, ba musu ta fad'a jikinta suka rungume juna sai hawaye na tausayin junansu, sun dad'e a haka sannan ya janye jikinsa yana kallan fuskanta hawaye na cigaba da gangara daga idonsa
"Kiyi hak'uri Wife, nasan komai was my Fault, Laifi na neh ya sh..."
Tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai,
"Ba laifinka baneh My Prince haka Allah yaso"
Sosai yaji dad'in sunan data kirasa dashi, ya langwabar dakai gwanin tausayi
"Karki danne gaskiya Wife, laifina neh, nine na kasa baki kulawa data dace a matsayina na Mijinki. Ban kasance miji na gari a gareki bah"
Ta b'ata fuska tare da juyawa tana kallan wani gefen, cikin shagwab'a tace
"Nidai zamu b'ata idan kana wannan maganan. Kaddara ce haka Allah yaso"
Ya sake rungumeta yana mai tsananin farinciki. Kula ya soma bata na musamman, shi da kansa yake jinyar abarsa, cikin kwana uku aka sallamesu Ram ya d'aukesu suka dawo gida.
Direct Part d'insu sukayi yana d'auke da ita, Palour ya ajeta ya shiga d'akinta ya gyara tsaf sannan ya d'auketa ya kaita sai turo baki take wai ita ya barta tayi tafiya da kanta. Ya direta kan gado tana cigaba da turo baki
"Zaki fara koh"
Ta sake zumb'uro baki, bata ankara ba taji bakinsa cikin nata sam batayi yunk'urin hanasa ba dan ita kanta tayi missing d'insa alot. Sun dad'e a haka ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta janye jikinta ta mike tana turo baki ta shiga toilet.
Saida ta wanke toilet d'in sannan tayi wankan ta fito, kishingid'e ta samesa kan gado idanunsa a lumshe fuskarsa d'auke da murmushi. Itama murmushin tayi
"Kaje kayi wanka sai ka huta"
Yad'an bud'e idonsa ya zubasu akanta, ya mik'a mata hannu
"Zo kiji na fad'a miki"
Ba musu ta k'arasa inda yake ya janyota ta fad'a jikinsa, juyata yayi ta koma k'asa ya mata runfa da kafadarsa. Ba tare da b'ata lokaci ba yakai bakinsa kan nata, Soyaiya ya shiga nuna mata mai wuyar fassara kuma da alama tana karb'ar karatun nasa. Jin yanaso ya tsallaka yasa ta saki kuka tana turesa
"Dan Allah ka daina"
Ya d'ago idanunsa da suka rune
"Pls Wife"
Ta k'ara turasa tana cigaba da kuka shagwab'a
"Nidai Aa"
Baice mata komai bah ya cigaba da abinda yake, kuka ta cigaba da rera masa a wajan kunnensa, chan dabara ta fad'o mata ta turesa tana cewa
"Dan Allah ka bari, kaje kayi wanka"
Ya d'ago jajayen idanunsa tare da shinshina Armpit d'insa
"Ina tsami koh?"
Ta d'anyi murmushi tana turo baki
"Bafa haka nace bah, ni dai kaje kayi ka dawo"
Ba musu ya mik'e rik'e da maransa yana cije lab'e
"Ki jira dawowana"
Ya fita daga d'akin tana tafiya a hankali, tana ganin ya fita tayi saurin mik'ewa ta d'aura towel ta kulle d'akin da key tana dariyar k'eta.
A falo ya tarar da Mabrookah wacce tun shigowan su ta shigo side d'in ta zauna tana jiranshi, duk tayi tsuru tsuru ta rame ko saboda meye oho.
Sam baima lura da itaba, tana ganinsa ta tashi da gudu ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka
"Ya Jamal ina kuka shiga? Kun barni ni kad...."
Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki.
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 8:19 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Page 83 n 84
Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki
"Karki kuskura ki k'ara tab'ani"
Tsagaita kukan datake tana kallansa da mamaki. Ya nunata da yatsa
"Kin bani mamaki Mabrookah, harda ke za'a had'a baki a cuceni"
Ta fashe da kuka tana kallansa
"Ni abinda kukamin banyi k'orafi ba saikai ne zakay..."
Ya d'auketa da wani kyakyyawan mari, ta sake fashewa da kuka
"Wallahi bazan yarda bah, kutafi ku barni a gida ni