Chapter 5 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 32

12K to 15K   out of 95.6K words

ta girgiza kai alamar A'a, Laurat tace

"Nima d'azu muna hira da Mama Talatu take cemin wad'an nan turawan masu kula da Jamaludeen zasu koma k'asarsu gobe da safe"

Ummy ta zaro ido dasauri

"Kai dan Allah dagaske?"

Laurat ta gyad'a kai

"Wallahi kuwa, wai an kirasu a k'asarau, dama ma'aikatan asibiti neh"

Jikin Ummy neh yayi sanyi tace

"Tho yanzu wazai cigaba da kula dashi?"

"K'ila zasu samo wasu neh ina ganin"

Shiru Ummy tayi duk saitaji hiran ta gunduretah. Haka ta yini jugum ranta bai mata dad'i, tausayin Jamal ne ya cikata. Da safe bayan ta idar da sallan asubah tana zaune kan sallayabtaba lazumi aka banko k'ofan d'akin, Mabrookah ta gani tsaye tana yatsine yatsine tana bin d'akin da kallo

"Ki fito Mami da Abba na kiranki a falo"

Ta sake banko k'ofan ta fita daga d'akin. Girgiza kai Ummy tayi cikeda takaici, saida ta gyara hijabin jikinta sannan ta fito zuwa falon, bataga kowa ba dan haka ta haura zuwa falon sama, hangosu tayi zaune jugum jugum ta shiga da
sallama ta samu guri k'asan carpet chan nesa dasu ta zauna, d'aya bayan d'aya ta gaishe su, Abba ya kalli Mami yace

"Itace yarinyar"

Mami tace

"Itace, kuma nasan zata iya"

Gaban Ummy ya yanke ya fad'i, tad'an d'ago kai tana kallan Mami, Abba yace

"Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu baneh. Nasan kinsan d'ana Jamaludeen"

Ummy tace

"Eh"

Abba ya cigaba da cewa

"Kuma nasan kinsan lalurar dayake tattare dashi"

Nan ma ta sake gyad'a kai

"Akwai turawa wad'anda suke lura dashi dangane ga abincinsa da kuma maganinsa dadai sauran yan abubuwa da suka shafe shi, tho yanzu wa'adin da suka d'iba ya cika kuma sunce bazasu k'ara kwanaki bah. Dan haka shine nake neman wanda zai cigaba da aikinsu"

Ya nuna Mami yace

"Shine Hajiya tacemin zaki iya"

Shiru tayi kanta a k'asa. Hajiya tace

"Bakice komai ba Ummy"

Abba yace

"Karki damu indai maganan albashi neh zan ninka miki akan abinda ake biyanki, zan rink'a biyanki dubu d'ari duk wata"

Da mamaki Ummy ta d'ago ta kalleshi, ya gyad'a mata kai tace

"Zan Iya Alhaji, saidai kud'in yayi yawa"

Mami tayi murmushi tace

"Karki damu buk'atarmu dai ki yarda, sanin halinki da k'wazon ki yasa na amince dake akan aikin"

Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin?

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:26 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

Page 14

Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin

"Ke muke jira har yanzu bakice komai bah"

Mabrookah ta tab'e baki tace

"Mami dama kun kyaleta, wannan ba iyawa zatayi bah"

Mami ta galla mata harara, ta kauda kai gefe tana turo baki. Ummy tad'an d'ago tace

"Zan iya saidai ban iya bashi abinci bah"

"Indai wannan neh karki damu, za'a nuna miki komai" cewar Hajiya

Abba yace

"Tho Alhamdulillah tunda kin amince, sannan aikin bawai zaki dauwama dayi baneh, nad'an wani lokaci ne zuwa sanda za'a samo wad'anda zasu cigaba"

Ummy ta gyad'a kai, Mami ta sallameta ta tashi ta koma d'akinta tana tunani.

Ranar Mami bataje aiki ba saboda tafiyan turawan nan, an musu sha tara ta arziki (abunku da gidan mai naira) har airport aka kaisu suka hau jirgin lagos dan tachan zasu tashi. A ranar Mami ta koya ma Ummy yanda ake feeding d'insa, da kuma nuna mata rosters abincinsa da magugunansa.

Sosai ta fahimta kuma a ranar Mami tace zata fara aikin, Saidai abinda Mamin bata sani bah shine Ummyn bata iya karatu ba dan bata iya karanta abinda ke jikin rostern abincin Jamal d'in.

Wureren k'arfe sha biyu ta shiga kitchen ta samu Laurat tana yankan albasa, murmushi ta mata bayan ta k'araso wajanta

"Taimako zakimin Laurat"

Laurat ta d'ago tana kallanta

"Taimakon meh fah"

Nan ta fad'a mata aikin da Mami ta bata na kula da Jamal, da mamaki Laurat tace

"Anya kuwa zaki iya Ummy?"

Hararan wasa Ummy tai mata tana cewa

"Mai zai hana, wannan ai wani dama ce na samu na samun lada, kinsan kula da mara lafiya akwai lada sosai"

Laurat ta gyad'a kai

"Tho Allah ya bada sa'a"

"Ameen, ni kinsan ma menene Laurat"

Laurat ta girgiza kai

"Wallahi ni rubutun kayan abincin nasa neh bana ganeh wa, dan Allah ko zaki karanta min"

Papern ta mik'a ma Laurat ta duba tareda zaiyane mata duk abinda ke cikin takardan. Godiya ta mata ta amsa tana cewa

"Oh Ikon Allah kenan, jidai duk dukiya irin na mahaifinsa anma ya koma shan kunun gero da dawa"

Cikeda alhini Laurat tace

"Allah kai mana rowan ciwo dai"

Ummy ta amsa da Ameen. Sallama tama Laurat ta haura sama zuwa d'akin Jamal d'in dan lokacin bashi abincin rana yayi, kunun tamba dake flask ta d'iba tasa madara da sugar kad'an sannan tad'au syringe ta soma zuk'a tana d'uramai ta bakin NG tube d'in dake hancinsa.

Tana gamawa ta dama maganinsa shima ta basa. Zama tayi kusada shi tana kallanshi fuskanta d'auke da Murmushi, duk da hali dayake ciki na rashin lapia, ko kad'an baida rama a jikinsa koh alamar wahala sai ma wani k'ara haske dayakeyi. Idanunshi kamar kullum yana nan kyam a wuri d'aya baya kyaftawa.

A haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan har batada lokacin kanta, kullum da sassafe take tashi ta soma gyara d'akinta sannan ta haura nasu Mami ta gyara da side d'in Alhaji. Kula kuwa da Jamal ba'a magana, ta d'aukema masu gyara masa d'akin da wankin kayansa, kullum ita take masa a washing machine dan Mami ta hanata wankin hannu tasa an koya mata yanda ake anfani da machine d'in kuma ta iya, duk weekend tana zuwa wajan iyayenta. Wani lokaci ta shiga gidansu Bilal wata rana kuma bata samun shiga.

Kimanin wata Ummy biyu kenan a gidan, Mami da Abba najin dad'in yanda take kula musu da d'an nasu, kyautatawa na abubuwa da dama tana samu daga wajan Mami da Abba, Mabrookah kuwa har yau ba abinda ya chanza daga halaiyarda take nunawa Ummy.

Yau bayan ta gama duk ayukanta, feeding d'in Jamal take tana kallan kyakyyawar fuskarsa harta gama sannan ta basa maganinsa. Zama tayi kusa dashi kamar kullum tana kallansa, wani dabara ce ta fad'o mata ta mik'e dasauri ta sakamai belt d'in dake wajan hannuwansa, ta saka masa na k'afa ta gunguroshi ta fito dashi daga d'akin.

Dakyar ta sauko dashi k'asa ta fita dashi waje zuwa chan garden d'in dake bayan gidan, ma'aikata sai kallanta sukeyi dan yawancin su basusan ita ke kula dashi bah. Garden d'in ta kaisa ta ajeshi, kneel down tai a gabansa ta sa hannunta ta d'ago fuskanshi tana murmushi

"Yau kaima ka fito kasha iska kaga haske"

Dariya tayi hawaye cike a idonta tana kok'arin yin kuka

"Jamal! Yaushe zakayi magana? Insan jin maganarka. Inasan naga ka warke"

Laurat ta shigo Garden d'in dasauri dan ta hangosu ta windown kitchen sanda take wucewa dashi. Ummy na ganinta tayi saurin share hawayen fuskanta

"Ummy lafiyarki kuwa? Kin tab'a ganin an fito dashi idan ba fita za'ayi dashi bah"

Ummy ta d'ago tana murmushin takaici

"Bantab'a gani bah, anma kuma yanda ake masa baya min dad'i. Bai kamata ace kullum yana guri d'aya bah, yakamata a rink'a fitowa dashi yana chan iska"

"Nidai da zakiji ta nawa da kin maidashi Ummy, karki jama kanki"

Yatsine fuska Ummyn tayi tana cewa

"Nifah bazan koma dashi ba sai mun gama shan iska"

Laurat ta girgiza kai

"Nidai ba ruwana"

Bata jira mai Ummy zatace ba tabar wajan dasauri. Tsaki tayi ta zauna gabansa ta tankwashe k'afarta tana kallansa

Labarin dariya da tatsuniya taita bashi, tanata magana ita kadai ita a dole suna hira, idan ta bada labarin dariya saidai ita tai dariyan, Wani lokaci kuma ta fashe da kuka. haka suka k'arashi zamansu ta gungurashi ta maidashi d'akinsa.

Kamar kullum yauma tana gyara d'akinsa bayan ta gama nasu Mami, wardrobe d'inshi ta bud'e ta soma gyara masa kayansa dake ciki, wani riga ta d'aga wasu hotuna suka zubo daga k'arkashin rigan, hotunan ta d'auka ta soma dubawa, Jamal ne tun yana d'an yaronsa da kuma wani wanda yana
ya fara tasowa har zuwa wanda ya d'addauka sanda yake makaranta a egypt, shagala tayi da kallan hotunan, Allah sarki rayuwa kamar ba'ayi bah. Wasu hawaye suka gangaro mata ta juya tana kallanshi cikeda tausayawa. A sanyaye ta k'arasa gyaran ta dawo kusada shi ta zauna, kurani ta d'auka a kan bedside ta dawo gabansa ta zauna ta soma karantawa cikin zazzak'ar muryarta.

Suratul Yasin ta bud'e tana karantawa a hankali kanta k'asa, tayi shafin farko tana a nabiyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta.

Tho Fah!

Ummy Abduol✍🏻
[3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

OMG gaba d'aya littafin nawa ni kad'ai, Babu abinda zance sai nagode Allah saka da Khairan ya barmu tare my Swt *Ummu Farheen*

Allah yasa yanda kika fara wannan littafi *K'alubalen rayuwa* lapia, Allah yasa ki gama lapia. Ameen

Page 15

Tayi shafin farko tana a na biyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta.

A tsorace ta aje kur'anin ta zaro ido cikeda tsoro, dasauri ta k'asara ta juyoshi dakyar tana kallanshi cike tsoro, ga mamakinta ganin idanunshi tayi a rufe, ba shiri ta fashe da kuka ta soma jijigashi a tsorace

"Jamal, Jamal"

Dagudu ta fito daga d'akin tana kuka wui wui, haraban gidan ta nufa, ko Mabrookah dake gyara parking motanta batayi ba ta nufi wasu maza dake wanke mota da sauran ayukan gida tana cigaba da kuka, rok'onsu tayi su taimaka mata a d'aga shi.

Mabrookah sukazo suka wuce har lokacin tana tsaye bakin motanta, ganin sunyi ciki itama ta bisu dasauri, Ummy ce ta musu jagora har zuwa saman tana cigaba da kuka.

A tsorace suma mazan suka karasa inda take kwance suka d'agoshi, har lokacin yana k'asa idanunshi a rufe, kan wheel chair d'in suka d'aurashi. Daidai nan Mabrookah ta shigo rai b'ace tana binsu da ido, wani razananen k'ara ta saki ganin idaunshi a rufe fuskanshi yayi ja sosai, mazan summ summ suka bar d'akin dan sunsan halinta batada mutunci.

Ummy bata ankara ba taji saukan mari a kuncinta, a gigice ta d'ago idanunta da suka rune zuwa ja tana kallan Mabrookah

"Kin kasheshi kin huta, me ya miki da zaki kasheshi"

Jin maganan Mabrookah yasa Ummy sakin wani sabon kuka mai k'arfi ta fad'i k'asa tana kallanta

"Wallahi ban kasheshi bah, hakanan naga ya fad'i, dan Allah ki yarda dan..."


"Shut ur dirty mouth"

Mabrookah ta fashe da kuka ta fit daga d'akin tana laluban Mami a waya. Kuka sosai Ummy keyi ta rarrafo ta dawo gabanshi ta tsugunna tana kallansa.

"Dan Allah karka mutu, ka rufamin asiri, nikad'ai ce wajan Iyayena, Allah ne gatanmu ni ce gatanmu"

Ta sake rushewa da kuka ta rik'e wandonshi tana girgiza shi a hankali kanta k'asa.

Labari ne ya cika gidan na cewa Jamal ya mutu, duka ma'aikatan gidan sun taru a haraban gidan kowa fuskarsa d'auke da damuwa. Horn akayi masu gadi suka bud'e gidan, Motan Abba da Mami a tare suka shigo, ba wanda yayi k'wakwaran parking Mami sai kuka take suka shiga cikin gidan dasauri.

Mabrookah najin motsinsu ta fito daga d'akinta tana kuka, duk a tare suka shiga d'akin, har lokacin Ummy na tsugunne gabanshi tana kuka. Saurin d'agowa tayi tana kallansu tana girgiza kai

"Wallahi ba abinda na masa Mami ki yarda dani"

Ga mamakinsu ganin shi sukayi zaune yanda yake kamar da, idanun nan nasa a kafe. Wani nauyayyan ajiyar zuciya Abba ya sauke ta sunkuya ya tab'a kirjinsa, jin yana numfashi yasa ya juya yana kallan Mami

"Yanada rai ba abinda ya samesa"

Tsagaita kukanta tayi tana kallan Ummy rai b'ace

"Meh kika masa Ummy"

Cikin kuka tace
"Ki yarda dani Mami ba abinda na masa hakanan ya fad'i"


"Karya kikeyi, hakanan ba abinda kika masa zai fad'i?"
Mabrookah ta fad'a tana nuna Ummy da yatsa

Abba yayi saurin katsesu yace

"Ya isa, tsautsayi neh nasan"

Ya juya ya kalli Ummy yace

"Sai a kiyaye gaba"

Fuuu Mabrookah tabar d'akin, Mami da Abba suka bar d'akin a sanyaye, Mami ce ta fad'ama masu aikin bai mutuba, nan kowa hankalinsa ya kwanta suka koma bakin aikinsu.

Duk da haka hankalin Mami bai kwanta ba saida ta kira likitansa yazo ya dubasa tareda tabbatar musu yanada rai sannan ba abinda ya samesa.

Sosai Mami taja ma Ummy kunne akan kula dashi. zage dantse tayi wajan Feeding d'inshi akan lokaci da kuma bashi magungunansa. Haka kullum takan sauko dashi k'asa taita zagayawa dashi. Sam bata gajiya da d'awainiyar Jamal dan tausayinsa takeji sosai.

Wannan watan kamar yanda Abba ya alkawarta, dubu d'ari ya biyata albashi, murna wajan Ummy ba'a magana har kuka saida tayi data amsa kud'in, dama ranar sati neh, dakyar Mami ta yarda ta barta taje gida weekend dan yanzu bata cika zuwa ba saboda hidimar Jamal, itama sam batasan barinsa saboda halinda yake ciki.


Da murna isa gida, iyayen nata ta tarar a tsakar gida suna shan iska, da murna ta taresu, Mama ta soma fara'a tana

"Lale lale, barka da zuwa"

Ta k'arasa ta rungume Mama tana dariyar farinciki, Baba ma murnar yake yanata lallubenta da hannu, ta rik'o hannunshi ta d'aura a kanta tana dariya, ya shafa kanta yace

"Allah ya miki albarka Jaleelah"

Ameen Mama da Ummy sukace, ba b'ata lokaci ta ciro kud'in albashinta ta d'aurama Baba a hannu tana cewa

"Baba ga albashina na wannan watan"

Kud'in yake tattab'awa baki bud'e

"Ummy ina kika samu wannan kud'in haka? Wannan daga ji yafi albashinki"

Sai a sannan ta musu bayani, Iyayen nata sukaita murna tareda sa mata albarka. Ganin yanda suketa murna yasa ta fashe da kuka, Mama ta rungumeta tana lallashinta.

Kasuwa ta shiga tayi siyaiyan kayan abinci sosai harda Umman Bilal, atamfofi kala shidda ta siya masu sauk'in kudi, tasai shadda d'aya da yadi biyu na Baba sannan tasai masa magungunansa da kuma sauran y'an abubuwan anfanin gida sannan ta dawo.

Atampha uku taba Mama, yadi da shadda taba Baba yanata murna, da kanta takai musu d'inkin, ta biya kud'in. Bata samu shiga gidansu Bilal ba sai dare, ganin kayan abincin da Ummy ta kawo yasa Umman Bilal fashewa da kuka, lallashinta Ummy ta dungayi har Bahar k'anin Bilal ya shigo gidan yana cewa

"Umma wannan shekaran ma na rasa, duk inda nake tunanin samun rancen kud'i naje ban..."

Kasa k'arasa maganan dayake yayi ganin Ummy dan sai a lokacin ya lura da ita, duk da ya girme mata hakan bai hanashi gaisheta ba, dan murmushi tamai tana cewa

"Ni yakamata na gaisheka bakai bah"

Murmushi yayi ta gaida shi ya amsa, atampha ta mik'ama Umma shima ta mik'amai Yadi, nan sukaita zuba godiya kamar sun ari baki har saida tayi hawaye.

Tambayanshi tayi ranchan kud'in me yake nema yace yasan ya rubuta jamb neh ya koma makaranta, batareda bata lokaci ba tace ya biyota gida ya amsa. Umma ta sake fashewa da kuka, Ummy itama ta saki kuka ta rungumo Umman tana cewa

"Ki daina kuka Umma, duk abinda nake muku bazan tab'a biyan Ya Bilal abinda yamin ba a rayuwa"

Sun dade suna kuka, Bahar ne yayita basu baki har sukayi shiru, Umma sai sa mata albarka take ta mata sallama Bahar ya biyota dan amsan kud'in. Bayan ta basa yayi godiya ta rok'eshi alfarman ya amso masu Mama d'inkinsu data bayar nan layin bayansu. Batareda b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya.

Ummy Abduol✍🏻
[3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Xaboorah Hapsert* Wannan shafi kacokan taki ce kyauta. Ina matuk'ar godiya

Page 16

Batare da b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya.

Koda ta dawo gida abinci Mama ta zuba mata, Tuwon shinkafa da miyar egusi sai k'anshi yake, nan kan tabarma suka zauna a waje suna shan iska kasancewar lokacin zafi neh.

D'ibo tuwon Ummy tayi harta kai saitin bakinta Jamal ya fad'o mata a rai, tunani ta soma dan tasan yanzu lokacin cin abincinsa neh, Allah sarki ta fad'a a hankali, dakyar takai loman ta soma taunawa a hankali kamar tana cin magani.

Mama dake gefenta tanaba Baba abinci ta kalleta

"Ummy lapia, ko bakij dad'in abincin baneh?"

Girgiza kai tayi ta kirkiro murmushi

"Aa abincin yayi dad'i sosai, Jamal na tuna nasan ynzu lokacin bashi abinci neh"

Baba yace

"Allah sarki, Allah kenan shiyasa kullum nake k'ara godema Allah dayasa nake ji nake iya magana, kuma nake sauran Alamura na duk da bana gani"

Tausayawa Mahaifin nata tayi tace

"Insha Allahu Baba zak warke, zaka cigaba da gani kamar yanda kowa yake gani"

Murmushin takaici yayi batare da yace komai bah.

Labarin abinda ya faru da Jamal rannan ta basu, Mama tace

"Anya kuwa ciwon yaran nan baida nasaba da mutanen b'oye"

Baba ya gyad'a kai yace

"Maganarki abin dubawa ce, saidai zai iya yuwuwa basu d'in baneh kawai dai ya fad'i neh"

Itadai Ummy batace komai ba sai kallansu datake.

Mama tace

"Anma Mallan wannan alamace ai ta cewa akwai su a tare dashi, kasan su mutanen nan basu san suratul Yasin musamman idan sunyi k'amari"

Baba ya gyad'a kai yace

"Hakaneh maganarki, koma dai basu d'in bane kamata yayi asama masa na gargajiya inaga zaifi na bature"

Ummy tayi murmushi tana kallan Iyayen nata yanda suke hira cikeda sha'awa.

Washe gari wuraren azahar ta baro gida ta dawo bakin aikinta, kasancewar lahadi ce a falon k'asa ta had'u da Mami itada wasu bak'i, gaidasu tayi ta bar wajan ta shiga d'akinta. Saida tad'an huta sannan tasa uniform ta fito ta shiga kicin.

Sun gaisa da mutanen kicin d'in, Laurat ta tareta da fara'a tana cewa

"Oyoyo Nannyn Jamal"

Duka ta d'akama Laurat d'in da wasa tana cewa

"Bakida kirki wallahi"

Dariya sukasa duka, Laurat tace

"Kinbar Mami da aiki dan naga daga jiya zuwa yau ita ta chanje ki"

Ummy tayi murmushi ta d'aga kai tana duba agogon kitchen d'in

"Saura minti talatin lokacin feeding d'insa yayi, barinje zamu had'u anjima"

Fita tayi ta haura sama zuwa d'akinsa, Yau kaftan ce a jikinsa, brown yadi mai tsadan gaske da santsi, d'inkin yayi fitting d'inshi kamar a jikinshi aka d'inka, sosai yama Ummy kyau sai kallansa take kyaftawa batayi.

Muryan Mami ne ya dawo da ita tana cewa

"Yauwa Ummy, gwara da kika dawo da wuri dan fita zanyi"

Ummy tayi murmushi tace

"Dama nayi tunanin wanda

5 / 32