Chapter 8 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 32

21K to 24K   out of 95.6K words

bah ya bud'e kofan ya fito

"Ki dawo gaba" yace a takaice fuskarsa ba walwala

Ba musu ta dawo gaba ta zauna, jan motan ya soma, tafiya kawai yake batareda yasan inda zai nufa bah, ganin suna shirin barin hanyan unguwansu yasa ta kauda kai gefe ta soma mai kwatance, murmushi yayi ya soma bin inda take kwatanta mai har suka kawo k'ofar gidan.

Batace mai komai ba tad'au ledan kayanta zata fita, lock ya danna ta soma k'okarin bud'e kofan ta kasa

"Ummy!"

Ya kira sunnanta a hankali, bata juyo ba tace

"Dan Allah ka bud'emin k'ofa na fita"

"Banida aboki daya wuce Ramadhan, sai kuma keh"

Ta juyo da mamaki tana kallansa, ya gyad'a mata kai

"Kinada babban matsayi a gareni, dan ban d'aukeki a matsayin ma'aikaciya ba, kinada matsayi kamar yanda Mabrookah ke dashi"

Shiru tayi bata daina kallonsa ba

"Nasan zakice ina shiga rayuwarki"

Yayi murmushi tareda danna lock d'in, tayi saurin murd'a kofan ta fita, ko waiwayowa batayi ba tayi shigewanta gida.

Gabanta ne keta fad'uwa, saida ta tsaya bakin zaure ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama, Mama ce ta fito dasauri jin muryan 'yar nata, rungume juna sukayi Ummy ta fashe da kuka

"Ummy ina kika shiga tsawan sati uku bamu ganki bah"

Ta sake rushewa da kuka, dakyar Mama ta samu ta lallasheta suka shiga wajan Baba, saida ta huta sannan take sanar dasu abinda ya faru. Sunyi Alhini sosai tareda farincikin samun Lapian Jamal d'in.

Kwananta Biyu a gida ranar da daddare tana zaune a tsohon d'akinta tana cin abinci yaro ya shigo gidan da sallama, Mama dake tsakar gida ta amsa yace ana sallama da Ummy inji Jamaludeen.

Gaban Ummy ne ya fad'i, Mama tace kace tana zuwa, Ummyn ta soma kwallama kira ta fito tana turo baki

"Wani Jamaludeen neh"

A shagwab'e tace

"Wanda nake aiki gidansu"

Daga d'aki Baba yace

"Maza kije k'ila an aiko shi ne wajanki"

Hijab ta shiga d'aki tasa ta fita tana turo baki, tsaye ta samesa tsaye jikin mota yana sanye da bak'in trouser da farar Tshirt mai mara kauri dan ana Iya Hango singlet d'in jikinshi saboda hasken bulb d'in dake wajan.

Kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ta k'araso wajan ta tsaya chan nesa dashi

"Barka da fitowa" yace yana kallanta

"Ina wuni" tace kamar ansata dole

Murmushi yad'anyi ya amsa mata yana cigaba da kallanta

"Nasan zakiyi mamakin zuwana, and nasan zakice na dameki"

"Ya Jamal ka fahimceni, inaso na tsiratar da kaina da kuma iyayena daga wulak'anci"

Ta d'ago ta kallesa tace

"Kayi hak'uri ka daina bibiyata in har kanasan na cigaba da zama a gidanku"

Ta nuna kanta tace

"Ni nan daka ganni banda k'awa ko aboki, nikad'ai nake rayuwata tun bayan na rasa....

Yayi saurin d'aga mata hannu ranshi b'ace

"Ki fad'amin waye ya hanaki huld'a dani? Tel me mana"

"Kayi hak'uri bazan iya fad'ama bah"

Baice mata komai ba ya zagaya ya shiga motarsa yabar k'ofar gidan a guje.

Ummy ta dad'e tsaye a bakin kofan tana bin hanyan da kallo sannan ta shiga gida jiki a sanyaye.

Kwanakin da aka bata na cika ta dawo bakin aikinta. Aikin da takeyi da ta cigaba dayi, wani abu daya bata mamaki shine tunda ta dawo gidan magana bai tab'a had'ata da Jamal ba, ko sau d'aya idan ta gaida shi baya amsawa. Hakan baima Ummy dad'i kwata kwata dan cikin wata d'ayan nan ta saba da hiranshi da damunta dayake yawan yi. har saida Laurat ta tambayeta tace bakomai.

****
Kimanin wata biyu kenan, yau tana gyara d'akin Mabrookah da safe aka turo k'ofar d'akin, d'an juyowa tayi suka had'a ido da Jamal fuskan nan babu walwala. Aikinda takeyi ta cigaba ya zauna kan bedside dake kusada ita


"Ummy abinda kikeyi ya dace kenan"

Batace komai ba haka bata juyo ta kalleshi ba

"We cant continue like dis, baxan iya jurewa bah. Munyi saba sosai"

gyaran d'akin ta cigaba har ta gama yanata binta da kallo

"Ummy magana nake kinyi banza dani"

Ta juyo ta kalleshi tace

"To me kakeso nacema Ya Jamal? Yanda kayi shine daidai"

Ya mik'e tsaye ya soma takowa zuwa inda take, gabanta ya tsaya har numfashinta na sauka a goshinta

"Nayi miki abinda kikeso saidai na gwada naga bazan iya bah"

Kokarin barin wajan take yayi saurin rik'o hannunta, dai dai nan Mabrookah ta shigo d'akin dasauri dan tayi mantuwan littafinta akab gado. Mutuwar tsaye tayi yana kallansu d'aya bayan d'aya shiko gogan ko a jikinsa, kokarin kwacewa Ummy ketayi ta kasa dakyar ta samu ta kwace ta bar d'akin dasauri. Basarwa yayi yace

"Sis lapia kika dawo"

Dakyar ta iya cewa

"Mantuwan littafi nayi"

Ya gyad'a kai tareda saka hannunshi cikin pockets ya fita daga d'akin.

Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka sosai.


Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:30 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Ina kuke Masoya Littafin JAMALUDEEN wannan shafi sadaukarwa ce gareku a ko ina kuke. Ina matuk'ar godiya da yanda kuke nuna min k'auna. Allah ya barmu tare Ameen*


Page 23

Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka.

Fasa zuwa makarantan tayi ta zauna a d'aki tanata kuka cikeda takaici.

Da daddare bayan Abba ya dawo Mami ta sanar da Abba abinda Mabrookah ta fad'a mata, murmushi yayi yace

"To menene Abin tada hankali Maimuna, karki manta Jamal kowa nasa neh, baida girman kai"

"Anma Alhaji yakamata ace an masa magana, ka tuna fah akwai alkawari akansa tunda ya samu lapia sai ayi magana"

Jim Abba yayi yana tunani, Mabrookah ta shigo falon fuska ba walwala ta zauna sannan ta gaida shi. Ya amsa yana kallanta da murmushi.


Waya ya d'auka ya soma neman layin Jamal, yana d'auka ya sanar dashi yana san ganinshi. Cikin mintina kad'an ya iso falon da sallama ya samu guri ya zauna ya gaida su.

Abba ne ya soma cewa

"Tambayanka nakeso nayi kuma inaso ka fad'amin gaskiya"


Jamal ya d'an d'ago sannan ya maida kai

"Menene tsakanin ka da yarinyan nan Ummy"

Dam! Gabanshi ya fad'i, ya d'ago suka had'a ido da Mami yayi saurin maida kai ganin yanda take kallanshi

"Ba abinda ke tsakanina da ita, kawai mutunci neh"

"To mutuncin shima na hana daga yau" cewar Mami tana kallansa rai b'ace

"Haba Maimuna, wai meyasa kike haka neh? Menene to dan sunyi mutunci"

Mami ta k'ara tsuke fuska tace

"Nidai banaso Alhaji, kasan shi talaka bai iya samun guri bah."

In banda hararan Mabrookah ba abinda Jamal yakeyi dan yasan ita kad'aice zata kai wannan gulman.

"Wannan duk ba magana baneh Maimuna, menene to dan sunyi mutunci a tsakaninsu?"

Abba ya girgiza kai ya maida dubansa ga Jamal daketa Hararan Mabrookah ranshi a b'ace

"Jamal lokaci yayi daya kamata ka koma bakin aikinka, companyn nan na buk'atar jajirtace kamar kah dan haka har na gama magana monday mai zuwa zaka fara zuwa aikin"

"Tho Abba insha Allahu Nagode"

Mami ta hard'e hannayenta biyu tace

"Tho Alhaji Maganan Alkawarin da akayi wanchan lokacin fah"

Abba ya kalli Jamal da Mabrookah

"Ku tashi kuje"

A tare suka mik'e suka bar falon, Abba yace

"Maimuna kina bani mamaki wani lokacin, bai kamata kina irin wad'an nan maganganun bah"

"To Alhaji kayi hak'uri bazan sake bah"

"Yauwa koke fah, sannan kaganan Alkawarin da kike ki bari sai nan gaba, komai ana binshi ne a hankali"

Ta gyad'a kai suka cigaba da hira.

Jamal na fita ya shak'e Mabrookah fuskan nan nashi a had'e

"Ni kike kai k'ara koh?"

"Dan Allah Ya Jamal kayi hak'uri ka sakeni bazan k'ara bah"

Kanta ya buga da bango ta saki kuka, yayi saurin sa yatsanshi a lips d'inshi

"Shhhh! Karki cika mana kunne, and idan har na k'arajin wani magana saina karya ki a gidan nan Stupid kawai"

Ya saketa yabar wajan rai b'ace.
Kuka ta fashe dashi mara sauti ta shige d'akinta ta fad'a kan gado.


Washe gari Abba da Mabrookah na kan dinning suna breakfast, Mami ta sauko cikeda murna ta zauna kan dinning d'in tana cewa

"Yanzu Fatima ta kirani tace suna nan zuwa yau d'in nan itada Zainab"

Wani ihu Mabrookah ta saki cikeda murna

"Dan Allah Mami dagaske?"

Mami ta gyad'a kai, da gudu Mabrookah ta haura sama tana cewa

"Ai yau ba kuma zuwa school sai next week"

In banda murmushi ba abinda Abba yake, ya mik'e bayan ya gama yace

"Na tafi su kuma Allah kawosu Lapia"

Mami ta amsa da amin ya fita. Tana cikin breakfast Ummy ta fito daga d'akinta.

Wajan da Mami ke zaune ta k'arasa ta tsugunna har k'asa ta gaidata, ba yabo ba falasa ta amsa tana dubanta

"Yau munada bak'i suna nan isowa anjima, d'akunan dake sama zaki gyara guda biyu"

Ummy ta amsa mata kanta k'asa

"Kada ki sake ki shiga hurumin da banaki bah"

Ta sake dubanta tace

"Ba ruwanki da Jamal ko Mabrookah, ki tsaya a matsayinki. Banasan shiga sharo ba shannu"

Banbara kwayi Ummy taji maganan, ta amsa da to a takaice sannan ta mik'e ta haura sama. Jikinta a sanyaye tayi ayukanta duka ta koma kicin ta had'u da Laurat, sai a sannan ta tuna yau Laurat d'in zataje ganin gida. Nan hankalinta ya sake tashi idanunta suka ciko da kwalla, da taimakon Ummyn Laurat ta had'a kayanta, Ummy ta rik'o mata kayanta suka fito haraban gida.

Daidai lokacin da Jamal
ya fito daga Falon, Laurat ya hango Ummy na biye da ita tana hawaye.

D'aya daga cikin ma'aikatan yasa ya kira mai su, tsayuwa Ummyn tayi tak'i motsi da kyar Laurat taja hannunta suka k'arasa inda yake tsaye. Fuskan Ummyn yaketa kallo yana d'an murmushi ganin yanda ta had'e rai, Laurat ta d'an rusunna ta gaidashi ya amsa yana tambayanta inda zata, ba tareda b'ata lokaci ba ta amsa masa.

Kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata tayi godiya sosai, driver yasa ya kaita tasha. Haka Ummy tanaji tana gani Laurat ta shiga mota suka bar gidan tanata d'ago mata hannu. Wani kuka ne yazo mata ta fashe da kuka tayi hanyar Garden a guje.

Kan Grass Carpet d'in dake malalle akan Garden d'in ta kwanta tana cigaba da kuka. A haka ya k'araso ya sameta, baice mata komai ba ya zauna kusada ita tareda tank'washe k'afarsa yana kallanta zuciyarsa na masa zafi.

Sam bata lura dashi ba saida tayi mai isarta sannan ta mik'e zaune tana goge hawayen idanunta, ganinshi tayi zaune kusada ita har saida ta tsorata tad'an matsa kad'an tana kallansa da idanunta da suka kumbure saboda kuka.

"Ummy meyasa kikesan kuka? Kiyi hak'uri ai zata dawo"

Batace komai ba ta mik'e tana kakkab'e jikinta, harta juya zata bar wajan ya mik'e dasauri yace

"Meyasa kike guduna Jaleelah"

Da mamaki ta juyo suka had'a ido dan batayi tunanin yasan sunanta, damuwa ne sosai a fuskansa ya soma takowa zuwa inda take tsaye.

"Baki bani amsa ba, meyasa kike guduna yanzu"

Ya juya fuska idanunta cikeda kwalla tace

"Kayi hak'uri ka daina bina, bansan na rasa aikina dan dashi muka dogara, idan na rasa aikina bansan yanda zanyi bah"

Ta matse hawayen daya cika mata ido ta juyo tana kallansa ido cikin ido, abinda bata tab'a yi bah

"Gaisuwa kawai ta wadatar a tsakanin mu, ka daina zuwa inda nake dan Allah"

Ta had'e hannayenta biyu tana hawaye

"I know Mami ce ko Mabrookah suka miki magana koh? ki kyalle maganan su Pls, Allah ne ya had'a mu kuma babu mai rabamu"

Ya sauke ajiyar zuciya ya kama hannunta ya zaunar da ita shima ya zauna suna facing juna

"Duk abinda Mabrookah ke miki ina sane, harda wanda ta miki baya, ki cigaba da hak'uri kinji"

Tayi saurin janye hannunta daga nasa

"Yakamata kaso abinda Mahaifiyarka da K'anwarka sukeso, ka rabu dani dan Allah, dan su suna tunanin ko soyaiya mukeyi kuma b..."

Yayi saurin katseta yana girgiza kai rai b'ace

"Mabrookah ba k'anwata bace..."

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:34 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 24

"Mabrookah ba k'anwata bace"

Ummy ta d'ago ido da mamaki tana kallansa. Ya gyad'a mata kai

"Bah k'anwata bace, Sistern Mami ce ta haifeta"

Ummy ta jinjina kai cikeda Mamaki, yace

"Ni kad'ai Mamina ta haifeni, banida yaya banida k'ani, shiyasa ta d'auko Mabrookah ta zauna tareda ita"

Fuska yatsine tareda lumshe ido yana shafa sumar kanshi

"Banasan zamanta a gidanan, i hate her"

Itadai Ummy ido kawai ta zuba masa tana kallansa, ya d'ago suka had'a ido ta sakar mata murmushi, mik'ewa tayi shima ya mik'e dasauri

"Ina zaki?"

Baya ta juya masa ta soma tafiya tana cewa

"Zanje ne na cigaba da aikina, ni zan chanji Laurat har sanda zata dawo"

Bata jira mai zaice ba tabar wajan dasauri ta wuce kicin.

Wanka Mabrookah ta sake d'auka ta sanyo wani Bak'in shadda dogon riga wanda yaji aiki Golden, saukowa tayi k'asa ta shiga kicin. Harda ita akayita shirye shiryen tarban bak'in, ranar Ma'aikatan kicin sunsha Masifa bama kamar Ummy har saida tayi kwalla. Cikin lokaci k'alilan aka gama komai aka zuwa a sababbin cooler aka kai dinning d'in sama.

Ummy na ganin an gama ta koma d'akinta ta zauna, wuraren k'arfe biyu Mami ta dawo aiki itama ta soma nata shirye shiryen. Jamal na side d'in Abba yana bacci baisan wainar da ake toyawa ba a gidan.

K'arfe Hud'u da rabi na yanma aka wangale gate d'in gidan, bak'ar mercedes ce ta shigo tayi parking a k'ofar side d'in Mami, Ummy dake jikin window sai bin motan take da kallo dan ba irin motan gidan baneh.

Mabrookah ta fito a guje tana dariya cikeda farinciki.

Wata 'yar dattijuwa ce ta fito daga gaban motan, kamansu d'aya da Mabrookahn, ta k'araso ta rungumeta tana dariya.

"Oyoyo Mummy! Sannu da zuwa"

'Yan mata ne kyawawa suma suka fito daga bacl seat, kallo d'aya zaka musu ka gane 'yan biyu neh, suna sanye da Pink atampha d'inkin dogon riga, Mabrookah ta saki matar ta k'arasa ta rungumesu

"Oyoyo Twins d'in Aunty"

Suma suka rungumeta a tare suna mai farinciki, sakinsu tayi ta k'arasa ta rungume d'ayar matar da suke tare itama tana kama da Mami sosai.

K'walawa Ummy kira Mabrookah ta fara bayan ta fito da Trolleys d'in dake booth d'in motan. Dasauri ta fito ta gaidasu, ta tura mata kayan tana hararanta

"D'auka shi shiga dasu sama"

Akwatuna hud'u neh, dakyar ta iya d'aukan Biyu ta haura dasu sama sannan ta dawo ta d'au biyu ta kai tanata haki dan kayan sunada nauyi sosai.

Nan falon k'asa suka baje anata hira, sosai Mami da Mabrookah suka yi farincikin zuwansu.

Mami ta sake kwallama Ummy kira ta fito dasauri ta k'araso falon, Abincin da aka kai Saman tasa ta sauko musu dashi dan sunce nan zasu zauna. Nan Ummyn ta soma zarya daga falon sama zuwa k'asa tana kwaso abincin. Tana gamawa d'aya daga cikin bak'in tace

"Ina kika samo wannan yarinyan, ke haka ake bama mutane abinci bazaki zuba musu bah"

Kanta k'asa ta tsugunna ta soma zuba musu d'aya bayan d'aya. Jamal ne ya shigo falon cikin takunsa na k'asaita, turus yayi yana binsu da kallo cikeda mamaki, dan baisan da zuwansu bah, twins d'in suka mik'e cikeda murna suka doso inda yake d'aya na cewa

"Ya Jamal Sannu ya jiki"

Murmushi ya musu ya kama hannuwansu suka k'arasa falon, mai kama da Mabrookah tace

"Dole ka kallemu mana, tun d'azu muke gidan nan ka kasa zuwa ka gaishemu kuma bayan dan kai mukazo"

Yayi murmushi ya zauna yana kallansu

"Haba Aunty Faty bah haka baneh bansan da zuwanku ba wanda ya gayamin"

Wacce aka kira da Aunty Faty tace

"Ba wani nan kawai dai kace mulkin kane daka saba ya motsa"

Murmushi kawai yayi ya maida dubansa ga d'ayar dake kusada Aunty Fatyn

"Sannu Aunty Zainab kunzo lafiya"

Tayi murmushi tace

"Lapia lau ya jiki? Allah ya k'ara sauk'i"

Ya amsa da lapia lau tareda maida dubansa ga Twins

"Najma da Najwa kunyi girma fah, yaushe yaushe na ganku"

Daidai lokacin Ummy ta gama serving d'insu tabar falon, binta da ido Jamal yayi har ta shige kwanan d'akinta, Aunty Faty sai kallanshi take da mamaki

"Kaji Jamal da wani zance, shekaran su ashirin kenan, kaida kake zaune kan kujeran k'arfe har shekara uku ya za'ayi dama kasan wad'an nan"

Twins dasu Mabrookah sukasa Dariya, nan suka cigaba da hiransu Aunty Faty sai tsokanan shi take yana bata amsa, itako Aunty Zainab ba ruwanta saidai idan anyi abin dariya tayi.

Suna gamawa Mami ta sake kiran Ummy dan tazo ta kwashe kayan da'aka ci abinci. Mami tace

"Mabrookah Mama tazo an wani mak'ale mata, ai zata tafi ne muna nan dake"

Ummy ta d'ago dan taga wacece Maman Mabrookah, Aunty Fatyn nan tagani Mabrookan ta mak'ale mawa, ta sauke ido dasauri ganin sun had'a ido da ita ta soma kwashe kayan.

D'aya daga cikin twins d'in ta mik'e ta soma tattara kayan tana cewa

"Barin tayaki kwashewa, Umm mu mun saba dayin aikin gida"

Tana tattarawa d'ayar itama ta mik'e ta soma tayata, Mami tace

"Trainning d'in Zainab kenan, kedai har yanzu bakison mai aiki"

Murmushi Aunty Zainab tayi ta gyara zama tace

"Aa nikam ba ruwana da mai aiki, tunda chan ban santa balle yanzu gani da yara kaman su Najma ai sai suyi"

Aunty Faty ta tab'e baki, Ummy ta shigo taga su twins sun d'auko kayan tayi maza ta rik'e tana cewa

"Aa ku bari na kai ku huta"

K'in yarda sukayi hakanan suka cigaba da kai kayan tare sannan Ummy ta koma d'akinta.


Da daddare Ummy bata samu hutu bah, tana d'an zama Mami zata k'walla mata kira tayi wani aikin. Bata samu ta runtsa ba sai k'arfe sha biyu da rabi, sosai Jamal ya tausaya mata dan yana ganin duk abinda ke faruwa kasancewar a side d'in ya wuni.

Da safe wuraren k'arfe bakwai da rabi Ummy ta fito kicin ta had'u da d'aya daga cikin twins d'in ta sauko, Murmushi tama Ummyn tace

"Sannu da aiki, kina k'okari maine sunanki"

"Jaleelah, anma Ummy ake kirana"

Ta gyad'a kai tace

"Ni kuma sunana Najma, and my twin sister Najwa. Kuma nice Hasana"

Ummy ta gyad'a kai da murmushi

"Allah sarki, sannu"

"Keh Najma me kikeyi a nan wajan"

A tare suka d'aga kai sukaga Aunty Faty ce tana k'okarin saukowa daga benen gidan

Najma ta zumb'uro baki tana d'an bubbuga k'afa

"Dake fa nake magana Najma kinyi banza dani"

"Babu komai, kawai muna magana neh. I want her to be my friend"

Aunty Faty ta zaro ido da mamaki ta k'araso inda suke tsaye

"What! Kinsan meh kike fad'a kuwa?"

Ta juya tana kallan Ummyn fuska

8 / 32