Chapter 19 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 32

54K to 57K   out of 95.6K words

kud'in da zai gada"

"Ni dai Umma ina sanshi ban damu da kud'insa bah"

Duka Aunty Faty ta d'aka mata tana huci

"Wallahi ki shiga taitayinki, Albasa dai batayi halin ruwa ba Mabrookah"

Ta mik'e a fusace tana cewa

"Ki zauna nan soyaiya ta rufe miki ido, idan bakiyi anfani da maganin nan ba kina nan Ummyn da kika raina zata k'wace gidan gaba d'aya"

Fuuuu tabar d'akin a fusace. Mabrookah ta sake fashewa da kuka tana ganin abubuwan da suka faru d'azu tsakanin Ummy da Jamal take gani a idonta.

Suna shiga d'akin Ummy ta sakeshi ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Kwance ta samesa kan gado fuskansa na kallan ceilng idanunsa a lumshe ta k'arasa bakin gadon

"Ruwan wanka na jiranka"

Yi yayi kamar baiji bah, ta turo baki ta matsa sosai kusa dashi. Yayi saurin janyota ta fad'a kan k'irjinshi, tashi take kokarin yi ya rik'eta sosai a jikinsa

"Dan Allah Ya Jamal ka daina wallahi banaso"

Yanda tayi maganan a shagwab'e yasa shima ya shagwab'e fuska yace

"In ni kuma inaso fah"

Ta mak'e kafad'a dakyar ta janye jikinta, ya mik'e yana cije leb'e ya shiga toilet d'in.

Falo ta koma ta tarar Mabrookah tabar wajan, ta rik'e k'ugu tana murmushin mugunta. D'akinta ta koma ta sake wanka tayi sallan isha'i sannan ta chanza zuwa night wears ta kwanta.

Har bacci ya soma d'aukanta taji kamar ana shafata, a razane ta mik'e zaune taga Jamal ne duk yabi ya susuce, kamar zatayi kuka tace

"Dan Allah ka bari"

"Pls Ki tausaya min wife, a matse nake plssss"

Bai jira mai zatace ba ya soma shafata.

(Asuba ta gari Angon Jaleelah)

Kukan shagwab'a Ummy keyi tana kai masa duka a k'irji, murmushi ya mata ya d'auketa ya kaita toilet. Wanka ya mata ya dawo da ita sai kukan shagwab'a take masa. Dakyar ta yarda ya shiryata cikin dogon riga bak'i mai pink flowers a jiki. Har ya gama bata daina turo baki bah. Murmushi yayi ya d'ago hab'arta ta lumshe ido dasauri.

Cikin sanyin murya yace

"Allah ya miki albarka Wife, bansan da kalmar da zanyi anfani dashi ba wajan gode miki. I love uh so much"

Hannunta ya kama ya saka mata keyn mota ya dunkule hannun

"Tukuicin faranta min da kikayi First night, Thank uh so much"

Tunda ya saka mata keyn a hannu take bin hannun da kallo idaunta waje. Kwantar da ita yayi yaja mata bargo

"Kisha baccin ki dan jiya ban bari kinyi bacci bah"

Cikeda kunyansa tace

"Nago..."

Yatsansa yasa a lips d'inta

"Shhhhhh... Babu godiya tsakanina dake Wife, just sleep"

Tayi saurin lumshe idonta tana murmushi. Farinciki yau yakeji fiye da ko yaushe, dakin ya sauka ya shiga na Mabrookah. Zaune ya sameta kan gado tana shirin zuwa makaranta, kallo d'aya ta masa ta kauda kai, ya zauna kusa da iya da d'an murmushi

"Amarya tah!"

Ta kauda kai gefe tana saka handout a cikin jakanta

"Amarya yau ba magana"

Batace komai bah ta d'au jakanta ta fita tana gungunai, murmushin takaici yayi ya mik'e ya fita.

Sama ya hau yayi wanka ya shirya, d'akin Ummyn ya lek'a ya samu tana bacci, peck ya mata a goshi ya fita. Direct side d'in Mami ya nufa, bai tarar da kowa a falo ba ya haura sama zuwa d'akinta, zaune ya sameta tana latsa waya. Ya zauna k'asa kusada iya ya gaidata. Amsawa tayi tareda aje wayan a gefenta

"Yanzu dai Ummy sai tagadama take zuwa tana gaida ni"

Yad'an sosa k'eya tareda duk'ar dakai

"Batada lafiya ne kwana biyu shiyasa"

Gyad'a kai kawai tayi sannan tace

"Naga sabon mercedes a haraban gida na wanene"

Gabansa ne ya fad'i ya d'an dago suka had'a ido yace

"Na Ummy neh"

"Mene!"

Mami ta furta a fusace

"Na Ummy fah kace, waya bata mota?"

Murya a d'an sark'e yace

"Ni na siya mata"

Ran Mami idan yayi dubu ya b'aci tace

"Ita kuma Mabrookah fah"

Jim yayi chan wayansa ya soma ruri, cirowa yayi daga aljihun shi yafa Mifzal ne yad'an kalli Mami dake ta hararansa

"Tun ba'aje ko inaba kenan ka fara nuna rashin adalci Jamal, yau sati biyu da rasuwan mahaifinka har ka fara b'arna da kud'i"

Shiru dai yayi baice komai bah kansa k'asa

"Ina magana kayi banza dani"

"Dan Allah kiyi hak'uri, kinga fa Mami kwata kwata Mabrookah bata daraja ni taya zanji dad'i har na mata ky..."

"Rufemin baki shanyayen banza, to bari in gaya maka dole itama Mabrookah sai ka saya mata mota itama"

"Anma Mami..."

Ta d'aga masa hannu tana huci

"Na gama magana, ka tashi ka bani guri"

Mik'ewa yayi a sanyaye ya fita daga d'akin, a corridor ya had'u da Aunty Faty, saida ya juya k'eya sannan ya gaidata, harara ta zafga masa bata amsa ba ta bar wajan.

Motansa ya shiga yabar gidan ransa ba dad'i, yana cikin driving Mifzal ta sake kiransa. Gefen titi yayi parking sannan ya kirasa, daga chan b'angaren Mifzal yace

"Idan baka komai kazo Office akwai wasu mahimman abubuwa danakeso na fad'a maka akan Case d'in nan"

Toh kawai Jamal yace ya kashe kiran ya tada motan ya nufi office d'in Mifzal.

Bayan sun gaisa Mifzal ya gyara zama yace

"Kasan hausawa na cewa idan baka iya kama b'arawo ba sai b'arawo ya kamaka"

Ummy Abduol✍🏻

♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 54 n 55

"Kasan hausawa na cewa idan baka iya kama b'arawo ba sai b'arawo ya kamaka"

Jamal ya gyara zama yana sauraronsa

"Bazai yuwu hakanan muje mu kamasa ba duk da akwai hujjoji masu kyau a hannun mu"

Jamal ya b'ata fuska

"To yanzu me kace zaka fad'amin mai mahimmanci"

Mifzal ya cigaba sa cewa

"Munyi bincike a kansa sosai mun gano yana zaune ne a gidan wani hamshak'in mai kud'i mai suna Alhaji Ameenu, sai dai mutanen unguwar babu wanda yasan menene sana'ar mutumin. Kuma kwanan nan suka dawo k'asar dan da ba anan yake bah"

Jimm Jamal yayi yana tunani, Mifzal yace

"Yanzu haka sun bar k'asar shida Alhajin, anma iyalensa na nan. Dole yanzu zamu jira dawowan su dan mu cigaba da bibiyarsa, saboda mu gane shi Alhajin Ameenun wanene, kasan kama babban mutum a k'asar nan nada hatsari. Musamman shi da bamusan meya taka bah"

Mik'ama Mifzal d'in hannu yayi sukayi musabaha

"Nagode sosai Friend, Allah ya saka da Alheri"

Da murmushi ya amsa da

"Ameen. Ka kwantar da hankalinka, insha Allahu zamuyi iya yinmu dan mu kama mai hannu cikin wannan kisan"

Ya lumshe ido ya bud'e a hankali tareda mik'ewa ya masa sallama ya tafi. Office ya nufa yana tunanin abinda Mami tasa shi dole yayi, bawai baida kud'in baneh Aa. Tunaninsa kawai yanda zai b'annatar da kud'insa wajan wacce bata darajasa, da biyaiya ko na second d'aya. Dogon tsaki yaja yasaka hannu cikin suman kanshi yana ya mutsawa yana b'ata fuska.

Waya yayi dan a kawo masa motan, cikin awa da baifi d'aya ba aka kawo masa, sak irin na Ummy ce, saidai na Mabrookah Bak'i neh, ita kuma na Ummy Arsh ce.


Gida yasa suka kai masa motan, shi kuma bayan ya tashi aiki ta biya kasuwa ya sayi kayan masarufi ya nufi gidansu Ummy. Sosai Mama taji dad'in zuwansa, hira sukayi sosai kamar ba suruki bah, sai bayan Magriba sannan ya mata sallama ya tafi tanata saka masa Albarka.

A masallacin k'ofar gidan ya tsaya yayi sallahn Isha'i sannan ya shiga gidan, yanasa k'afa a k'ofar Falon side d'insu gabansa ya fad'i tunawa da yayi yau Girkin Mabrookah neh.

Itakuwa Hajiya Mabrookah yau a shirye take, saboda wani Pills da k'awarta ta bata a makaranta datakai mata complain d'in baya kusantar ta. Ko takan Maganin Aunty Faty batayi ba tunaninta kawai yanda zata zuba masa k'wayar a drink har tasamu yasha.

A sanyaye ya shigo ciki da sallama ya soma takawa a hankali yana bin Falon Mabrookah da kallo, rungumesa yaji anyi ta baya ko ba'a fad'a masa ba yasan Mabrookah ce.

Sabda baisan rigima a daran yasa ya birkito ta yana mata murmushi

"Sannu da zuwa Honey tun dazu nake jiranka"

Fuskanta dayasha makeup ya shafa yana cigaba da murmush, peck ta kai masa a kumatu kana wani shu'umin murmushi

"Nasan ka gaji, shiyasa ta had'a maka ruwan wanka tun d'azu"

Har lokacin ya kasa magana sai binda da ido yake kamar ranar ya soma ganinta, hannunsa taja har sama, Ummy suka samu a falon ta takure waje d'aya da alama tsoro takeji, kallo d'aya ta musu ta kauda kai, janshi Mabrookahn ta cigaba dayi har d'akinsa, ta aje briefcase d'insa akan bedside ta k'arasa inda yake tsaye yana cire agogon hannunsa, mab'allin gaban rigansa ta soma cirewa, sai hanata ba har ta cire ya rage farin singlet, hannu tasa ta cire belt d'in wandonsa, ganin baice komai ba yasa ta samu k'warin guiwa tasa hannu zata cire mab'alli Wandonsa, saurin rik'e hannunta yayi fuskarsa a d'aure

"Meye kuma haka Mabrookah, ki bari mana ko nace miki ne bazan iya cirewa bah"

Ta shagwab'e fuska ta sake matsowa kusada shi tana d'an murmushi

"Kai Yaya, anfa ce yana da kyau mace ta rink'a taimakon jikinta"

Guntun tsaki yaja ya matsar da ita gefe ya shiga toilet d'in ya danna key yanata mita cikin ransa.

Tana ganin ya shiga ta doka tsalle tana dariya ta fita daga d'akin dasauri, har lokacin Ummy na falon a takure wannan karan hawaye ne ke fita daga idonta.

Kallanta Mabrookah tayi ta kwashe da dariya, karairaya ta soma har ta k'arasa inda Ummyn zaune, ta rik'e k'ugu tace

"Ke k'aramar 'yar bariki ce. Yau zan nuna miki ke ba komai bace, ki toshe kunnenki da runtse idanunki dan yau zaki sha mamaki"

Cike da takaici Ummyn ke kallanta, wani k'ollolon bak'in ciki ya tokare mata mak'oshi, kasa ce mata komai tayi. Mabrookah ta sake kwashewa da dariya ta bar wajan tana rawa tana wak'a a hankali.

Sauka tayi ta kwaso abincin data masa ta shiga dashi d'akin. Har lokacin bai fito bah, ta juya ta kalli k'ofar toilet d'in sannan ta ciro tablet d'in da k'awarta ta bata ta bud'e 5alive d'in data kawo ta saka guda uku ta jijiga ta rufe.

Ta sake kallan k'ofan sannan ta mik'e dasauri ta fita ta mayar. Koda ta dawo bata tarar da Ummy a falon bah, tayi dariyar mugunta tareda k'wafa

"Ke k'aramar mara kunya ce"

Taja dogon tsaki ta shiga d'akinsa, zaune ta samesa kan gado daga shi sai towel a waist d'inshi da kuma wani a hannunsa yana tsane ruwan kansa. Cikin tafiyar jan hankali ta k'arasa ta amsa Towel d'in dake hannunsa tana cigaba da tsane masa. Ko uffan baice bah, gaba d'aya hankalinsa na wajan Wife d'insa dan yasan batayi bacci yanzu. K'okarin mik'ewa yake tayi saurin kama hannunsa cikin shagwab'a

"Ina zaka kuma Honey gafa abinci na kawo maka"

Kallan kulolin yayi tad'an yatsine fuska yace

"Am Ok! Nayi attending wani walima kafin nazo"

Tad'an turo baki ta d'au cup ta tsiyaya masa 5alive d'in ta mik'a masa

"To ga wannan kasha tunda ka k'oshi"

Bai mata musu ba ya amsa ya kai bakinsa, saida yasha kusan rabin cup d'in sannan ya aje. Murmushin mugunta tayi ta d'au trayn da fita tana tafe tana dariya k'asa k'asa.

Harya mik'e zai shiga zaije wajan Wife d'insa dan itace a ransa. Wani jiri ne ya kamasa ya koma ya zauna dasauri tareda dafe kansa. Mabrookah ce ta shigo cikin wasu fitinanun kaya tana karairaya, kam cinyansa ta zauna tana shagwab'a duk da yanda gabanta ke fad'uwa

"Honey yadai"

D'agowa yayi ya kalleta har saida ta tsorata ganin yanda idanunsa sukayi ja, rungumota yayi jikinsa ya kwantar da ita kan gadon ya soma aika mata sak'oni masu wuyan fassara, duk abinda yakeyi da zafi zafi yakeyi saboda yanda ya kamu sosai. Mabrookah ba baka ba har kunne, an samu abinda akeso, nidai ina ganin haka nayo waje na basu guri.

Ummy tsoro ne ya cikata, ga wani kishi daya dabaibayeta, k'udundune wa tayi cikin bargo ta rufe har kanta. Tsoro ne ya k'ara cikata dan duk sanda ta rufe idanunta b'arayin nan take gani sanda suka harbi Abba.

A guje ta fito tana kallan bayanta, kuka ta soma mara sauti ta fito falonta ta kunna switch na wuta tahau kan kujera ta kwanta tana cigaba da kuka tana waiwayen bayanta.

Kan 1seater ta koma ta kwanta tasake k'udundunewa tana kuka. A hankali a hankali ta soma jiyo ihun Mabrookah daga d'akin Jamal, wani kukan ta saki mai sauti ta soma wurgi da pillows d'in dake kan kujerun. Ranar batayi bacci bah har saida aka kira sallahn Asubah, dakyar ta mik'e a wajan ta shiga d'akinta ta fad'a toilet tayo alwala. Dakyar ta iya yin sujjada sbda yanda idanunta suka kukumbura.

A b'angaren Jamal da Amarya Mabrookah kuwa, wuraren k'arfe uku ya sarara mata, ya fad'a gefenta yana maida numfashi, sam baiyi tunanin zai samu Mabrookahn a budurwa ba sai gashi ya sameta fil a leda. Albarka ya soma saka mata itako sai kukan shagwab'a take masa da k'ara narkewa a jikinsa.

Da kansa ya mata wanka ya shiryata tanata masa shagwab'a, shima ya shiga wankan, ya fito ya tada sallah, nafilfili ya soma har aka kira sallan asubah ya sake alwala ya fita masallaci.

Bai shigo gidan ba sai k'arfe bakwai da rabi, duk hankalinsa na wajan Wife d'insa, sauri yake yaje gareta tunawa da yayi bai dubata ba daran jiya. A stirecase sukayi kicibus da ita cikin shirin makaranta, fuskanta ya kumbura yayi ja abinda da farar fata. Ta gefensa zata rab'a ta wuce yayi saurin rik'o hannunta

"Wife meya sameki a fuska"

Kwace hannunta ta soma yi idanunta taf da hawaye

"Ka sakeni na wuce, ka kyalleni"

Kalmar datake ta fad'a kenan, da mamaki yaketa kallanta, ta fashe masa da kuka

"Ni ka sakeni, ka kyalleni"

Rungumota yayi jikinsa ta soma kici kicin k'wacewa tana dukansa a k'irji

"Pls wife kiyi hak'uri, nasan nayi laifi. I donno what came over me har na dawo ban dubaki bah"

Harzuk'a tayi dajin maganansa, wato ita zai rainama wayo, turesa tayi da duk iya k'arfinta ta fashe da kuka ta fita daga side d'in da gudu.

Binta yayi yaga tayi side d'in Mami, slow yayi ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya daga bakin side d'insa. A bakin k'ofan Side d'in Mamin ta tsaya saida tayi kuka mai isarta sannan ta goge hawayenta ta tura k'ofan ta shiga da sallama.

A falon k'asa ta had'u da Mamin, suna had'a ido da Aunty Faty gabanta ya fad'i. A hankali ta k'arasa ta zauna k'asa chan nesa dasu tace

"Ina kwana Mami"

Wani dogon tsaki Mamin taja sannan tace

"Sai yau kikasan zakizo ki gaisheni?"

Aunty Faty tace

"Ai ta rik'a, kinsan itace mai gidan"

Kan Ummy a k'asa tana hawaye, Mami tace

"Baki isa ki rabani da d'ana ba wallahi, kuma kuruwana da d'ana kur, naman mu d'aci garesa"

Ta nunata da yatsa ta cigaba da cewa

"Ni nan da kika gani, asiri ya buga dani ya barni, asiri baya cina daga ni har d'ana. Baki isa ki chanza min alk'iblan gidana bah"


Aunty Faty ta tab'e baki tana karkad'a kafa

"Kuma kina dawowa ki kawo min makullin motan da ya baki, dan baki isa kina hawa mota, 'yata na hawa bah" cewar Mami. Aunty Faty tace

"Fita kiba mutane waje"

Dasauri ta fita tana hawaye, har lokacin Jamal na tsaye yana ciranta, ganin ta fito tana hawaye yasa ya runtse ido cike da bak'in ciki. Mota shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah.


_Thank Uh so much My Fans_ I'm now better Alhamdulillah

Ummy Abduol✍🏻
♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 56 n 57

Mota ta shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah.

Ransa duk ba dad'i ya koma side d'insa, dakin Ummyn ya nufa yana murd'awa k'anshin room freshner had'e dana turaren wuta suka masa sallama, a hankali ya shiga ya soma bin d'akin da kallo, komai tsaf tsaf ba datti sai k'amshi had'e da sanyin Ac ke tashi.

Toilet d'inta ya shiga yayo wanka ya fito sannan ya koma nasa d'akin dan babu kayansa a nata. Zaune ya samu Mabrookah sai turo baki take a shagwab'e, yad'anyi murmushi ya k'arasa kan gadon

"Morning Sis"

Baki ta sake turowa idanunta taf da hawaye

"Ayyah Sis kuma, bayan ita Wife kake cemata"

Yanda tayi maganan sosai ta basa dariya, gefen fuskanta ya shafa ya sakar mata murmushi ya mik'e ya soma shiryawa dan yayi latti. Duk abinda yake tana nan ta k'uresa da ido har ya gama shiryawa.

Sosai yake mamakin irin rashin kunyan Mabrookah, ko gezau batayi ba sanda ya warware towel d'in jikinsa zai saka kaya.

Yana gamawa ya juyo da murmushi

"Sai na dawo"

"A dawo Lafiya" tace tana cigaba da turo baki.

Yana fita ya nufi side d'in Mami gabansa na fad'uwa, gaidata yayi itada Aunty Faty, ba yabo ba fallasa Aunty Faty ta amsa masa gaisuwan. Mami ko da fara'a tace

"Naga mota Allah ya saka da alheri"

Shaf shi yama manta da maganar mota, Ameen kawai yace ya mik'e ya musu sallama ya tafi.

Bayan tafiyarsa Mabrookah ta mik'e dakyar ta koma d'akinta, wanka ta sakeyi ta sauya zuwa riga da skirt na material. Da d'angyashi ta shiga side d'in Mami

Kan dinning ta samesu suna breakfast, tunda ta shigo Mami ke binta da ido har taja kujera ta zauna tareda

"Washh" ta yatsine fuska kamar zatayi kuka

"Yaya dai Lafiya?" Cewar Aunty Faty tana kallanta

Ta sake shagwab'e fuska

"Ba Ya Jamal baneh"

Mami ta girgiza kai kawai dan ta fahimci inda maganan nata ta dosa, Aunty Faty tayi kini kini darai

"Me ya miki Jamal d'in"

"Ba shi baneh ya...."

Mami tayi saurin katseta da cewa

"Wannan ai tsakanin su ne na mata da miji, mu ba ruwanmu a ciki"

Kurrrri Aunty Faty tayi ma Mabrookahn tana kallanta. Chan kuma ta girgiza kai ta janyo plate ta zuba mata breakfast d'in ta tura mata gabanta.

Ranar a side d'in Mami ta wuni sai shagwab'a take suna biye mata, bama kamar Aunty Faty har cewa take ta natsu dan k'ila ta samu ciki kada yazo ya b'are suyi asara. Dariya ko Mami tayi har cikinta ya kusa yin ciwo.

A b'angaren Ummy kuwa kuka ta dunga yi a mota, saida taga driver yayi parking a k'ofar makarantan sannan tayi shiru ta goge hawayenta ta fito. Gaba d'aya babu abinda ta

19 / 32