JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 32

9K to 12K   out of 95.6K words

ta bibi duka sauran d'akunan tasa keyn anma beyi bah, k'asa ta koma ta samu Laurat tana aikace aikacenta, zama tayi duk jikinta a mace, Laurat ta matso tana kallanta

"Yadai Ummy meh aka samo mana neh"

Maganan Laurat dariya ya bata tad'anyi murmushi tace

"Laurat knan, maganarki yana bani mamaki, rik'on amana na d'aya daga cikin abinda ke sa a k'ara yarda da kuma san mutum."

Ta mik'e tana murmushi tareda dafa Laurat

"Banida ra'ayin abinda kike fad'i, burina na kasance mai kiyaye duk wani doka da aka shimfid'a min, banasan wuce gona da iri akan lamuran dabai shafeni bah"

Laurat tayi jim tana gyad'a kai

"Gaskiya kika fad'a Ummy"

Taja hannunta suka zauna ta kalli Ummy tace

"Ni y'ar garin kaduna ce a anguwar tudunwada, na taso bansan iyayena bah ina hannun kakata wacce itama ta tsufa. Na tashi cikin talauci da matsin rayuwa saboda itama kakar tawa batada k'arfi, Iyayena y'an garin kano neh so d'aya ta tab'a kaini wajansu, suma basuda k'arfin da zamu iya rik'eni. Hawaye ne suka gangaro mata tasa bayan hannu ta share tace

"Wanchan shekaran kakar tawa ta rasu, nan na koma hannun wata dilalliya dake nan mak'otan mu saboda banida kowa, shine ta d'auko ni ta kawoni nan, yanxu kimanin watana takwas knan a nan"

Ummy ta tausaya mata sosai, tasa hannu tana share mata hawaye

"Ki daina kuka Allah yana tare dake, insha Allahu rayuwarki zan inganta nan gaba"

Gyad'a kai Laurat tayi ta mik'e ta cigaba da aikinta, Ummy tace

"Banfa gyara d'akin bah"

"Meyasa?" Laurat ta tambayeta

Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace

"Ni duk d'akunan dake sama ba wanda ban sa keyn ba baiyi bah, kinma san wani abu kuwa?"

"Aa meya faru?" Laurat ta tambaya, Ummy tace

"Wani d'aki na shiga naga wani mutum zaune a kujeran guragu gashin nan dai kamar baida rai"

Murmushi Laurat tayi tace

"Sau d'aya na tab'a ganinshi tunda nazo gidan nan, nima yanda kika ganshi haka na ganshi"

Da damuwa Ummy tace

"Tho shi wanene?"

Laurat tace

"Ance d'an su Hajiya neh"

Kai Ummy ta gyad'a ta kauda maganan. Hajiya bata dawo gidan ba sai bayan magriba, bayan ta huta Ummy ta sameta a falo ta gaidata tareda shida mata bata gane d'akin bah. Murmushi Hajiya tayi tace

"Ummy kenan, ba a nan b'angaren d'akin Alhaji yake bah, b'angaren dake kusada nan nan neh b'angarensa, bakiga makullin falo baneh"

Sai a sannan Ummy ta duba tagani, Hajiya tace

"Gobe in Allah ya kaimu ki tabbatar kin gyara"

"Tho" Ummy tace ta mik'e ta mata saida safe ta tafi d'akinta.

Washe gari kamar kullum tana gama gyara d'akin Hajiya dana Mabrookah ta wuce b'angaren Alhaji, Sakin baki tayi ganin Aljannar duniya, nesa ba kusaba b'angaren Alhaji yafi nasu Hajiya kyau duk da suma nasu ba baya yake ba.


Gyara tayi sosai dan b'angaren yayi datti dayawa. Haka kullum take aikinta, ta gyara d'akin Hajiya dana Mabrooka ta kuma gyara na Alhaji, tun daga ranar bata k'ara ganin mara lafiyan nan ba duk da kullum idan ta hau sama gyara saita kalli d'akin, yanzu ta gane abinda likitocin nan keyi kullum a gidan.

Yau wankin Inner wears d'in Mabrookahn ta kwaso dan ta mayarda ita kamar jaka. wankin kayanta itace duk da akwai washing machine dake gidan, Guga, da duk wasu sauran ayuka duk ita take mata. K'asa ta sauka zuwa bayan gidan inda ta saba wankin itada Laurat suna hira, Tsohon nan maiba flower ruwa ne ya k'araso wajan yazo cire tiyo daga jikin famfo, Gaidashi Ummy tayi ya amsa da fara'a dan yanzu sun saba dashi sosai, so dayawa idan tazo wanki sukan had'u wani lokacin suyita hira dashi.

Itama Laurat ta gaidashi ya amsa yana cewa

" 'yata wanki akeyi neh"

"Eh Baba, ya aiki"

Ya amsa da lapia lau, har zai wuce Ummy tai saurin cewa

"Baba dama inaso nai maka wani tambaya"

Ya dawo tareda zama kan benchn dake gefensu yace

"Allah yasa na sani 'yata"

Ta nisa tace

"Baba ranan na tab'a ganin wani mara lapia a gidan nan, a wani d'aki yana zaune akan keken guragu. Wai shi wanene"

Nan da nan fara'ar dake fuskan Baba ya kau, ya d'ago yana kallansu yace

"Sunanshi JAMALUDEEN, shine babban d'a ga Alhaji Surajo, nakai shekara goma a gidan nan ina aiki tareda Alhaji, lokacin danazo nasamu Jamaludeen yanada shekara goma sha shidda, Alhaji Surajo mutun ne mai san mutane da kuma tausayin talakawa"

Ummy da Laurat suka zubamai ido suna kallanshi ya cigaba da cewa

"Bakuga ma'aikatan dake gidan nan ba, saboda tausayi dayake dashi yasa yaketa d'aukan marasa k'arfi da marayu suna aiki yana biyansu. Jamaludeen yaro neh mai hazak'a da tarbiya gasan mutanen.....


Ku biyoni a page na gaba dan jin cigaban labarin JAMALUDEEN

UmmyAbduol✍🏻
[3/12, 8:24 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


*Indo Magulmaciya(Aisha Abduolqadeer)* wannan shafin naki neh kyauta

Page 12

"Jamaludeen yaro ne mai hazak'a da tarbiya ga son mutane, ya samu tarbiya mai kyau daga Iyayensa, da wuya kaga Jamaludeen yayi zagi ko wani abu daya sab'a k'aida."

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa

"Yayi karatunsa a nan k'asa nigeria, yayi saukar alkurani tun yana aji hud'u a sakandari, daga bisani mahaifinsa ya turasa k'asar misira ya k'arashe sauran karatunsa..."

Hawaye suka gangaro ma Baba yasa hannu ya share yace

"Ban tab'a ganin abokin fad'an Jamaludeen bah, yaro ne mai ladabi da biyaiya, yana matuk'ar san Iyayensa kamar yanda suma suke sanshi sosai. Ya d'au kowa d'aya a gidan nan, baya nuna banbanci dan mu masu aiki neh.."

Laurat tayi saurin k'atseshi da cewa

"To Baba wai meya samesa neh?"

Ummy ta zungureta tana hararanta

"Keh kin cika garaje"

Baba ya kallesu yana murmushi

"Da gaskiyarta Ummy gwara data tambaya, dan idan na tsaya baku labarin kyawawan hali irin na Jamaludeen zamu kwana neh a nan mu yini bamu gama bah"

"Yauwa Baba ashe ka fahimta" cewar Laurat tana hararan Ummy

"Shekara uku kenan da fara rashin lafiyarsa, bayan kamalla makarantarsa da shekara d'aya ya had'u da wannan tsautsayin a hanyarsa ta zuwa kaduna yayi hatsari."

"Hatsari??"

Ummy ta maimaita tana kallan Baba gabanta na dukan uku uku

"Kwarai y'ar nan, hatsari ya samu akan hanyarsa ta zuwa kaduna, lokacin da aka kawosa duk an d'auka baida rai sai daga baya likitoci suka tabbatar da yanada rai"

Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace

"Wannan wane irin ciwo neh haka? Baba wallahi idan ka ganshi zakayi zatan gawane dan ko kyafta ido bayayi"

Murmushin takaici Baba yayi yace

"A hakan ya samu lapia kenan, dan baki gansa baneh da. Ba k'asar da ba'a kaishi ba anma ba wani cigaba, a nan na yarda da maganan nan da akecewa ba komai dukiya ke siya bah"

"Lallai wannan bawan Allah yaga jarabawar rayuwa"
Cewar Ummy tana rik'e hab'anta

Baba yace

"Kwarai da gaske Ummy, yanzu ina gatan yake? Ina dukiyar da mahaifinsa ya tara? Ina ilimin dayake dashi? Duk kinga basu masa anfani bah"

Laurat ta gyara zama tace

"Anma kuma Baba sai naga kamar Iyayensa basu damu dashi ba yanzu"

D'an dariya yayi yace

"Ina! aiko shi Iyayensa suka damu dashi, har yau har gobe yana cikin gata kamar yanda yake dah. Kunga dai duk dukiya da matsayi irin na mahaifinsa hakan bai hanashi kullum da safe shi da kanshi yake zuwa yanama d'an nasa wanka ya shirya shi, bai yarda wani ya masa wannan bah. Ko turawan nan da kuka gani anfaninsu kawai kula da lokacin shan maganinsa dakuma abincinsa"

"Allah sarki yabani tausayi, Allah ya bashi lapia" cewar Ummy tana girgiza kai cikeda alhini

Baba da Laurat suka amsa da Ameen. Godiya suka masa ya mik'e ya koma bakin aikinsa jiki a sanyaye
Suma kicin suka nufa suka cigaba da ayukansu. Da daddare tunanin Jamaludeen neh ya cikama Ummy zuciya, sosai labarinsa ya bata tausayi har take tunanin bashi nata gudun mawar a rayuwarsa ko Allah zaisa a dace. (Kujimin k'arfin hali)

Tunani ta soma kan yanda zata b'ulowa alamarin a haka bacci ya d'auketa.

Washe gari da safe kasancewar ranar juma'a ce da wuri Ummy ta tashi, yau ana public holiday dan haka Hajiya da Mabrookah suna gida, sai wuraren sha d'aya na rana suka fito daga d'akunan su, saman ta haura bayan ta gaishe su ta soma aikinta, d'akin Hajiya ta gyara farko sannan ta zarce na Mabrookah shima ta gyara tsaf. Fitowa tayi ta juya tana kallan k'ofar d'akin da Jamaludeen d'in ke ciki, wata zuciyar na ingizata akan ta shiga wata zuciyar na hanata. Hajiya ce ta hauro ta tarar da ita a haka, sunanta ta kira tayi firgigit ta juya tana kallanta tareda rusunawa

"Meh kikeyi a nan a tsaye?"

Gabanta ya fad'i ta dake tace

"Fitowa na kenan daga d'akin Aunty Mabrookah na gama gyaran"

Hajiya tad'anyi jim sannan tace

"Yau kibar gyaran b'angaren Alhaji tunda yana nan"

Ta kalli Uniform d'in jikin Ummyn tace

"Kije ki sauya kaya kizo ina jiranki a d'akina"

To tace ta sauka dasauri ta shiga d'akinta, atamfarta ta sallan bara ta ciro daga k'asan ghana must go d'inta ta saka tad'an murza farar hodan dake cikin kayanta, gaban madubi ta tsaya tana kallan kanta, wasu hawaye ne suka gangaro mata, lokaci guda ta fashe da kuka tareda jingina kanta a jikin Mirror tana cigaba da kuka

"Ka tafi ka barni Ya Bilal a lokacin da nafi buk'atarka"

Zoben hannunta ta soma murzawa tana cigaba da hawaye

"Kayimin abubuwa da dama a rayuwa nida Iyayena wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, ciki kuwa harda sutura"

Tad'anja rigar dake jikinta tana kallan fuskanta a madubi tana hawaye, ta dad'e a haka sannan ta shiga toilet ta wanke fuskanta ta fito ta nufi d'akin Hajiyar, a corridor tayi kicibus da wad'an nan turawan maza sun gunguro Jamaludeen suna k'okarin sauka dashi. Binsu da ido tayi tad'an matsa gefe suka wuce, Hajiyar ta samu nan d'akinta, a nan Hajiyar ke sanarda ita cewa zasu fita
ne takeso suje taro. Murmushi tayi tace

"Tho"

Kallan kayan jikinta Hajiyar tayi tad'an yatsine fuska ta juyar dakai, d'akinta ta koma ta d'auko hijab tasa ta fito daidai nan Hajiyar itama ta sauko. Mabrookah wacce shigowanta knan gidan ta kalli Hajiya tace

"Mami naga Jamal a waje ina za'a kaisa?"

Hajiya tace

"I want to spend this day with my son"
Ta k'are maganan tana murmushi, girgiza kai Mabrookahn tayi tareda yatsine fuska

"I'm hungry dana biku"

"Aa kiyi zamanki ga Ummy zata rakani"

Ta nuna Ummyn dake tsaye gefensu tana muzurai

"What?, yanzu Mami da wannan k'azamar zaki salan ta shafa masa wani cutan dama gashi muna fama"

Hajiya ta had'e rai

"Banasan Haka Mabrookah behave ur self whats all dis"

Zumb'ura baki tayi ta haura sama tana gungunai, ita harga Allah batasan Yarinyan nan she dnt knw why. Hajiya ta juya ta kalli Ummy tace

"Kiyi hak'uri ki kyaleta wata rana zata daina"

Kai Ummy ta d'aga suka fita, already sun tarar har an sakashi a motan Hajiyar, Mercedes benz E350 sai d'ayan kuma Camrey wanda Turawa masu aikin Jamal d'in ke ciki. Cikin ABU suka shiga suka d'an zazaga sannan suka fito suka tafi wani park.

Ummy sai raba ido take dan sunan tana zaria neh kawai anma tunda take bata tab'a shiga cikin ABU bah. Bayan sunyi parking motocinsu Hajiya ta fito tareda shimfid'a k'aton carpet a k'asa, turawan suka kamoshi aka d'aurashi kan wheel chair d'insa. Kusa dashi Hajiya ta zauna tana kallanshi idanunta cikeda kwalla

"Allah ya baka lapia Jamal, Ina kewarka sosai, Allah ya tashi..."

Kasa k'arasa maganan tayi ta tushe da kuka, Ummy hawaye ya cika mata ido ta rarrafo kusada Hajiyar tana cewa

"Kiyi hak'uri Hajiya, Addu'a yakamata ki rink'a masa ba kuka bah"

Hajiya ta juyo ta kalleta tareda share hawayen fuskanta, wani malalacin Murmushi tayi tace

"Bakisan yanda nakeji ba Ummy, Inasan Jamal fiyeda komai a duniya, da kud'i zaisa Jamal ya warke da tuni ya warke, banida wani buri yanzu daya wuce naga koda murmushin Jamal koda bazai bud'i baki yayi magana bah"

Hawaye suka gangaro ma Ummy tace

"Kiyi hak'uri Hajiya, kid'au hakan jarabawa ce a gareku gaba d'aya. Kiyi ta masa addu'a insha Allahu zai warke ya dawo yanda yake dah"

Wani kukan Hajiya ta fashe dashi

"Na cire wannan tsamanin Ummy, shekaran Jamal Uku a zaune a wannan kujeran, baya magana, baya motsi"

Hijab d'in jikinta tasa tana sharema Hajiyan hawaye.

"Duk mumini baya cire rai daga rahamar Allah, kiyi hak'uri wata rana sai labari. Insha Allahu wata rana sai kin gaji idan ya fara miki surutu"

Sosai maganan Ummy yaba Hajiya dariya, tad'anyi murmushi tana duban Jamal d'in dake zaune kamar gunki kan keke.

Kayan ciye ciye Hajiya ta siya musu sukaci suka sha, dama shi Jamal yana sanye da NG tube ta hancinsa dan baya iya tauna abinci saidai a d'ura masa abu mai ruwa ruwa ta hancinsa. Maltina Hajiya taba d'aya daga cikin masu kula dashi ta bashi, ta syringe ta soma zuk'a tana d'ura masa ta tube d'in, ganin yanda ake basa abincin tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe.

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:25 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

Page 13

Tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe. Ji tayi duk kayan ciye ciyen sun isheta ta turasu gefe ta d'ago idanunta tana kallan Jamal d'in.

Hajiya ta nisa tace

"Ina jin dad'in zama dake Ummy, kinda Hankali da tarbiya ga natsuwa"

Murmushi Ummyn tayi ta duk'ar da kanta k'asa

"Inaso ki d'aukeni a matsayin Uwa a gareki, kada kiji tsoro ko shakkan sanar dani damuwarki kinji?"

Gyad'a kai tayi sannan tace cikin sanyin Murya

"Nagode Hajiya"

Murmushi Hajiya tayi tace

"Ki rink'a kirana da Mami kamar yanda Mabrookah take kirana. Ke da ita duk d'aya na d'aukeku"

Godiya Ummy ta mata sosai, sun jima sannan suka d'au hanyan gida. A wani boutique suka tsaya Mami tace Ummy ta biyota ciki, kaya Mami keta d'auka na maza ga dukan alamu na Jamal neh, sai kuma wasu data d'auka na mata itadai Ummy sai binta take a baya, juyowa tayi suka had'a ido tace

"Ki d'auka duk abinda kikeso"

Ware ido Ummy tayi tana kallan Hajiyar, kasa d'aukan komai tayi ganin tak'i d'auka yasa Mami ta d'aukan mata dogaren riguna da ready made atamfofi wanda zasu mata. Sun biya Ummy ta d'au ledojin suka nufi mota suka wuce gida.

Saida takaima Hajiyar kayan d'aki sannan ta sauko ta koma d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa uniform ta nufi kicin wajan Laurat, koda taje ta sameta ta cika tayi fam saura kad'an ta fashe. Kallo d'aya Ummy ta mata ta kyalkyalle da dariya

"Hajiya Laurat, yadai meya faru?"

Laurat ta k'ara turo baki ta kauda kai, dariya Ummy ta k'arayi tace

"Ahaf karkiyi maganan, ai gobe ina gida abuna maga da wanda zakiyi"

Jin haka yasa ta juyo dasauri tana yatsine fuska

"Ai kece kin cika abin haushi, ba inda ban nemeki ba a gidan nan ban ganki bah"

"Tho maida wuk'ar, mun fita ne da Hajiya d'azu"

Da mamaki Laurat tace

"Dah Hajiya?"

Ummy ta gyad'a kai tareda zama kusada ita ta soma bata labarin fitar nasu. Hannunta Laurat ta kama tana murmushin farinciki

"Ummy kin shigo gidan nan da k'afar dama, lallai kinada sa'a"

Ummy tai dariya kawai batace komai bah.

Washe gari misalin k'arfe goma Ummy ta fito daga kicin dan tasan a wannan lokacin ya isa ace su Hajiyan sun tashi, sama ta haura tayi knocking d'akin Hajiya, izini Hajiyan ta bata ta shiga da sallama, zaune ta sameta kan stool tana shafa cleanzer a fuskanta, har k'asa ta tsugunna ta gaidata ta amsa tana kallanta da murmushi

"Barin baki guri kiyi aikinki"

Tashi Hajiyan tayi har takai bakin k'ofa sai kuma ta dawo tace

"Jiya shine kika ajemin kayan nan a d'akina? Ai na saya miki neh ki d'auka ki cigaba da anfani dasu."

Ta nuna mata k'aton ledan dake kusada bedside tana cewa

"Gashi chan ki d'auka"

Godiya Ummy ta shiga mata tai saurin girgiza mata kai tana cewa

"Ba godiya a tsakanin mu Ummy, kin wuce haka a wurina"

Bata jira mai zatace ba tabar d'akin, aikinta ta shiga yi ta gyara ko ina tasa turaren wuta mai k'anshi ta fito bayan ta d'au ledan kayan.

K'asa ta sauka ta kai ledan d'aki sannan ta dawo ta shiga d'akin Mabrookah, saida ta gama mata wulak'anci da zagi sannan ta fito ta bata waje. Dama kuka baima Ummy wuya, saida tayi mai isarta sannan ta gyara d'akin ta fito. Yau ko k'ofar d'akin Jamal bata kalla ba ta sauko k'asa ta koma d'akinta.

Kayan da Mami tasai mata ta bud'e ta duduba, kaya ne masu kyan gaske da tsada, set biyu wanda tasan zaima Mamanta ta d'auka tasa a leda sannan ta sauya kaya cikin wanda Mamin tasai mata, dogon riga neh pink swait mai stones a k'irji, sosai kayan suka amsheta tayi kyau sosai, dama Ummyn ba banza ba akwai diri.

Farin hijab tasa ta fito zuwa falo, Mami tama sallama wannan karon driver akasa ya kaita gida. Iyayenta sunyi farinciki da zuwanta, ranar kusan raba dare sukayi suna hira, a nan Ummy ke fad'a musu matsalan Jamal, sunyi alhini tareda mai addu'an samun Lapia.

Washe gari saida ta musu girki da duk wani abu da suke buk'ata sannan ta taho, wannan karan bata shiga gidansu Bilal bah dan wannan satin a kuraren lokaci tazo.

D'akinta ta shiga ta sauya kayanta sannan ta haura sama zuwa d'akin Mami ta shaida mata dawowanta, kicin ta shiga ta samu mutuniyar nata na gyaran alaiyahu, ta gaida sauran mutanen kicin d'in sanan ta zauna kusada Laurat tace

"Sannu da aiki"

"Yauwa, anma fah yau kin dad'e baki dawoba"

Ummy ta saki murmushi tana hararanta da wasa

"Keko ina tsakiyar Baba da Mama mai zai kaini dawowa yanzu"

Murmushin k'arfin hali Laurat tayi, idanunta suka ciko da kwalla tunawa da Kakarta dan ita batasan dad'in Iyayeba saboda tana k'arama suka rasu. Ummy tai saurin kauda zancen da cewa

"Mama na gaishe ki, har y'ar tsaraba ta bani na kawo miki"

Da fara'a Laurat ta d'ago tace

"Kai dan Allah dagaske?"

Ummy ta gyad'a mata kai

"Allah sarki Mama ya take? Ya jikin Baba"

"Dasauki" Ummy ta bata amsa. A tare suka gama gyaran alaiyahun, sannan suka wuce d'akin Ummy, tsaraban ta ciro mata na kayan ciye ciye da Mama ta bata ta kawo mata, su goruba da tsamiyar biri dadai sauransu, sosai Laurat taji dad'i tayi godiya sosai. Sannan tace

"Kinsan meke faruwa a gidan nan kuwa?"

Ummy

4 / 32