Chapter 28 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 32

81K to 84K   out of 95.6K words

rame kamar bashi bah.

Gaban Jamal ya fad'i sanda ya d'ago ya kalli Alhaji Ameenu, Ummy ko Areef ta k'urama ido sannan ta juya ta kalli Jamal wanda har lokacin Alhaji Ameenu yake kallo.

K'ara aka karanto sannan aka umarci Mifzal ya tashi yayi bayani, bayan ya gama Lawyern Alhaji Ameenu wanda d'ansa Areef ya samo masa yayi k'orafi tare da rok'on kotu tabi ma Alhaji Ameenu kadinsa na cin zarafi da aka masa.

*A gurguje*

Nan kotu tabada umarnin a saki Alhaji Ameenu da Bilal, Ummy dake gefe ta kalli Jamal murya chan k'asa saboda yanda take jin jikinta tace

"Ya Jamal kaga wani mai kama dakai"

Ya juyaga Areef yana kallansa shima da Mamaki har lokacin gabansa bai daina bugawa bah. Su Mami aka shigo dasu, Ram wanda shine Lawyern Jamal ya mik'e ya soma Jawabi, kasancewar su Mami basu da Lawyer sannan basuyi musu akan laifin da ake tuhumar su ba yasa shari'an baid'au dogon lokaci bah. Mabrookah dake gefe sai kuka take jin Abubuwan da su Mami suka aikata. An d'aga shari'a sai bayan kwana uku sannan a dawo dan Sauraran hukuncin da Za'a yanke ma su Mamin.

Mabrookah ta fashe da kuka haka Ummy, Jamal ko hankalinsa ne ya tashi yabar Court d'in dasauri, Mifzal yabi dake k'okarin shiga mota

"Mifzal ya duba dan Allah, kada a yanke ma su Mami hukunc...."

Mifzal yayi saurin katseshi da cewa

"Kana bani mamaki Jamal, matarda batada nufi na alheri a gareka anma kabi ka d'aga hankalinka akanta"

Ran Jamal ya b'aci

"Wanne irin magana kakeyi Mifzal, kasa...."

Mifzal ya shiga mota yaja yabar Haraban Court d'in ransa shima a b'ace. Juyawa yayi a sanyaye ya nufi wajan motansa, yana danna security Mabrookah dake kuka ta bangaje Ummy ta shiga gaba ta zauna. Ummy ta bita da kallo cike da takaici.

Har suka isa gida babu wanda yace k'ala, Yana Parking ya fito ya shiga side d'insu daga Ummy har Mabrookah binshi sukayi da kallo. D'akinsa ya shiga ya fad'a kan gado ta fashe da matsanancin kuka kamar k'aramin yaro. Koda Ummy ta haura sama kamar ta shiga d'akinsa sai kuma ta fasa tunawa da tayi itama fushi take.

Ya dad'e yana kuka har tsawon wani lokaci, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru ya mik'e ya shiga toilet yayo alwala. Yana fitowa Ya kalli akwatin da ya d'auko ranar daga gidan, sai kallan Akwatin yake ko k'iftawa bayayi, nan ya tuna cewa shine akwatin da Abba ya rubuta masa cewa duk abinda yake san sani game dashi zai samu ciki.

Batare da wani b'ata lokaci ba ya janyo jakan ya bud'e a hankali gabansa na fad'uwa.

Showel yaci karo dashi da wani overall duk sunyi k'ura, ya d'agasu zai duba sauran abubuwan dake ciki, wasu hotuna nr suka zubo ya sunkuya ya d'auka yana kallo.

"Innalillahi wa inna illaihi raj'iun"

Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa.


_Gaisuwa ta musamman ga Jamaludeen Maher_ Ina yinka irin sosai d'in nan.

Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Wannan shafin Tukuici ce ga *Real Jamaludeen* Ina godiya sosai da bani goyon baya dakake yi, Thank uh so Much Bro

Page 87

"Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun"

Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa.

Wayansa ya d'auka cikin yanayi na tashin hankali ya soma neman layin Mifzal, saida ya kirasa kusan sau hud'u sannan ya d'auka, dan yayi tunanin zai kirasa ne akan maganan su Mami, cikin muryan kuka Jamal yace

"Dan Allah kada ka bari Alhaji Ameenu ya tafi"

"Saboda meh" cewar Jamal,

Hankali tashe yace

"Just do what i said, gani nan zuwa ka jirani a Station"

Muryansa ya sake rauni,

"Dan Allah karka bari su tafi"

Mifzal baice masa komai ba ya kashe kiran sannan ya juya hancin motarsa ya koma Court, bai samesu ba sai 'yan tsurarun motane dake wajan da wasu 'yan sanda, tambayansu yayi a nan d'aya daga cikinsu yake shaida masa yaji suna cewa zasu je Hospital a duba lafiyarsu Alhajin.

Jamal kuwa gaba d'aya ya rikice, kaya ya saka ya kinkimi akwatin daya ciro hotunan ya fito, Ummy dake falo ta bisa da kallo da mamaki, ko kallanta baiyi ba ya sauka k'asa yasa kayan cikin mota ya figa a guje yabar gidan. Mifzal ya sake kira ya shaida masa yana Court, direct chan yayi har lokacin hawaye bai daina zuwa daga idonsa bah. Yana isa yayi parking ya fito dasauri

"Ka gansu?"

Ya girgiza masa kai alamar Aa, Cikin wani irin yanayi Jamal yace

"Dole muje Abuja ayau d'in nan Mifzal"

Ya kallesa da mamaki, har zai tambayesa dalili sai kuma ya fasa yace

"Suna cikin Zaria dan yanzu na tambaya aka shaida min anji suna cewa zasu Asibiti"

Jamal najin haka yace

"Wat are we waiting for? Mu tafi kawai"

Mifzal ya zafga masa harara

"Aina zamu fara nemansu"

Dai dai nan Ram ya k'araso wajan dan tun d'azu yana cikin Court d'in, Mifzal ne ya masa bayani, Ram yace

"Nemansu Abu ne mai sauk'i, na lura d'ansa yanada san asani da kuma nuna isa, Zai iya yuwuwa ABUTH sukaje"

Mifzal yayi saurin cewa

"Yes u're right"

Duk a motar Jamal suka had'u suka d'unguma zuwa asibitin, cikin sa'a suna Parking suka hango su Alhajin sun fito daga asibitin harda Bilal, Jamal ya fita daga motan dasauri ya k'arasa inda suke,

"Dan Allah ku tsaya"

Dukansu suka juyo suna kallansa, Gaban Alhaji ne ya fad'i ya k'urama Jamal Ido, haka itama Matarsa sai kallansa take ko k'iftawa batayi ga gabanta daketa fad'uwa.

Areef d'in Alhaji Ameenu ya juyo a fusace yana kallansa,

"Waye kai?, me kakeso"

Daidai lokacin Ram da Mifzal suka k'araso wajan, Nan da nan Alhaji Ameenu ya had'e rai haka d'ansa Areef, Areef yana kallansu Mifzal yace

"Wai me kukeso damu neh? Inace shari'ar ta k'are? Ko kunzo ne wannan karan ku kamamu duka"

Yana maganan yana tada jijiyoyin wuya ransa a b'ace

"Na k'yalleku ne kawai saboda Abbana ya hanani d'aukaka k'ara, Ashe haka zama Nigeria yake"

Ram ya katsesa da cewa

"Babu abinda ya kawo mu, kuma dakake maganar zaman Nigeria, ai babu inda yakaita dad'i ma dan Asalin k'asar. Dan a nan ne kad'ai yake da 'yancin yayi duk abinda yakeso"

Jamal yayi saurin d'agama Ram Hannu Alamar yayi shiru, Alhaji Ameenu yace

"Ku fad'a mana abinda ke tafe daku dan sauri muke"

Jamal ya tsugunna guiwa biyu a k'asa, gaba d'ayansu binshi sukayi da kallo bama kamar Bilal dake gefe yana muzurai,

"Sunana Jamaludeen, ku...."

Alhaji Ameenu yayi saurin nuna Jamal da yatsa yana cewa

"Dama kaine Jamaludeen d"in da ake fad'a?"

Ammi dake gefe tace

"Shine yayi causing all this Problems"

Har Areef ya bud'e baki zaiyi magana Alhaji yayi saurin d'aga masa hannu sannan ya maida dubansa ga Jamal yana cewa

"Tunda nake ba'a tab'a cin mutuncina kamar yanda kasa akamin bah"

Jamal ya fashe da kuka daga tsugunan dayake, Mifzal sai hararansa yake kamar ya mangaresa.

"Abbana ka gafarceni, kayi hak'uri"

"Waye Abban naka?" Cewar Areef a fusace

Ya d'ago fuska yana kallan Ammi wacce itama tun d'azu shi take kallo

"Ammi meyasa kuka kasa rik'eni, kuka zab'i yardani"

Babu wanda bai razana a wajan bah, Lokaci d'aya Ammi ta fashe da kuka tana kallan Jamal d'in, Shi kansa Alhaju Ameenun Yanayin fuskansa ne ya sauya, anma ya dake yace
l
"Wani irin magana kakeyi neh?, me kake nufi"

Ammi tayi saurin cewa

"Areef kaine?"

Areef ya zaro ido yana kallan Ammi da mamaki, Ram wanda ya gane inda maganar tasu ta dosa ya k'araso yana cewa

"Wannan maganan ba'a nan yakamat ayita bah, ya kamata a natsa sai a zauna a tattauna"

Ya mik'ar da Jamal tsaye, Mifzal yace

"Alhaji ku shiga mota kubi bayanmu muje a tattauna a gida"

Ba musu suka shishiga mota Jamal ya shiga nasa motan, Ram ne ke driving har zuwa gidansu Jamal. Suna isa Jamal ya musu Jagora zuwa side d'in Abba. Bayan an zazzauna ya koma cikin mota ya d'auko akwatin nan ya shigo dashi d'akin, Ammi na gani ta mik'e tsaye dasauri tana bin akwatin da kallo.

Haka shima Alhaji zazzare ido yayi yana kallan akwatin, Areef da Bilal da kuma su Mifzal gaba d'aya bin su Abban suke da kallon Mamaki, Alhaji yayi k'arfin halin cewa

"Ina ka samu akwatin nan"

Jamal bai b'oye musu komai ba dangane ga abinda ya sani, Ammi ta fashe da kuka tana cewa

"Na dad'e ina burin ganin wannan ranar gashi Allah ya kawoshi"

Areef ya kalleta da Mamaki

"Ammi kun sakani a duhu meke faruwa neh"

Alhaji wanda shima k'walla ke zuba a idonsa yace yana nuna Jamal

"Wannan yayanka neh, mu muka haifesa, sunansa kaci bayan mun rasa shi da muka haifeka muka maida maka da sunansa"

Jamal dake gefe shima yana hawaye yace

"Ammi meyasa kuka yar dani, baku damu da halin dazan shiga bah, baku damu da mai zai iya samu na a daran da kuka yardani bah"

Ya fashe da kuka sannan ya cigaba da cewa

"Ance tsakanin d'a da uwa akwai wata irin shak'uwa mai tsanani, meyasa Ammi kika yarda aka yardani, kuma baku k'ara waiwayan halinda zan shiga bah"

Abba ya girgiza kai yana share hawayen dake gangaro masa

"Ba laifin mu baneh Areef, ba laifin mu baneh"

Haryanzu binsu da kallo Areef keyi cike da mamaki da kuma kokwanto, Alhaji ya soma magana cikin raunin murya

"Sunana Alhaji Ameenu Jibril, ni haifafen Garin karaye ne dake Kano. Na taso cikin gata na iyaye kasancewar mahaifina hamshak'in attajiri ne a wanchan lokacin, nayi ilimin Addini dana boko sosai, ana haka iyayena suka rasu duka, hakan yasa na dawo garin kaduna da zama, inda na had'u da Hajiya zainab na aureta, cikin ikon Allah na fara sana'ar saida gwal da taimakon wani ubangidana danayi zuwana Kaduna"


Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa

"Harkokin kasuwanci ya cigaba da bud'ewa, ina samun Alkahiri da dama haka ina samun cigaba a harkata, har nakaiga inacin gashin kaina nima inada yara, tunda sauran mutanen da muka fara sana'ar tare sukaga haka suka soma mini bak'in ciki, a haka na cigaba da sana'ata, na tara k'addara masu yawa, na gina gida na gani na fad'a. Ana haka matata ta haifeka inda muka saka maka suna Areef"

Areef dake gefe ya zaro ido yana kallan Alhajin, Bilal ko k'uri ya musu shida Jamal tabbas ga kama nan da sukeyi da juna, haka kuma suna yanayi da Alhajin, ya cigaba da cewa

"Ina sanka Areef fiyeda yanda nakesan kaina, dan kai ka zamo mini a matsayin 'yan uwana dana rasa, duk wani kula da jin dad'i nida matata munayi maka, ana haka wata rana da daddare wuraren k'arfe biyu na dare, mukajiyo shigowan b'arayi gidan, Sosai mukaji tsoro, Matata banda kuka babu abinda take, sunyi sunyi na bud'e k'ofa nak'i, a nan suke shaida min ba kud'i suke nema ba raina dana Matata dana d"ana suke nema, inajin mata jikina dana matata ya soma rawa, da kaina na sakaka a akwati na saka dukiya mai yawa a ciki, na mik'ama matata nace su gudu, ta k'ofar baya suka gudu ni kuma na sadak'ar nazo na bud'e musu k'ofan.
Ganin ba iyalina yasa ransu ya b'aci suka sakar min harbi Allah ya taimakeni a Hannu neh, suna ganin na fad'i sukayi tafiyarsu"

Ammi na kuka ta d'aura da cewa

"Mun fita nayita gudu ina kuka, har Allah ya had'ani da wani mai mota inda ya sanar dani Zaria yayi, ba yanda na iya hakanan na bisa ya saukeni a wani anguwa nayi ta masa godiya dan bai amsa ko sisina bah, haka na kwana a wajan wani bola har washe gari da safe, na yini banci komai bah, da daddare yunwa ya addabeni dole na maidakai cikin akwatin dan bazan iya d'aukanka saboda jikina daba k'arfi, a nan na barka na tafi neman abinci, kafin na dawo an d'aukeka a wajan"

Ta k'are maganan cikin kuka, Ram dake gefe yace

"To ya akayi kuka had'u da mijinki"

Ta share hawayen fuskanta tace

"Nayi rayuwa a zaria na kusan shekara d'aya inayi ma wata mai abinci bauta, sannan daga baya na koma Kaduna wajan Iyayena inda anan na sake had'uwa da Mijina ashe yanada sauran kwana"

Mifzal dake gefe ya tab'e dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa.

Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Page 88

Mifzal dake gefe ya tab'e baki dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa.

Alhaji Ameenu ya zamo daga kan kujeran dayake ya xauna a k'asa yana kuka a hankali

"Tun dawowar Zainab danaji labarin b'atanka daga wajanta, babu irin kukan da bamuyi bah da nemenka anma babu wani labari, Wallahi Areef dakai kullum nake kwana a raina har Yau, kullum ina addu'ar ganinka dan a kullum inaji a jikina kanada Rai"

Ammi cikin kuka tace

"Ka gafarce mu Areef sam bamu yarda kai bah"

A hankali ya rarrafa shima yana kuka ya rungume Abba yana kuka a hankali

"Ka daina kuka Abbana, bakumin komai bah."

Ya juya zuwaga Ammi itama ya rungumeta ya saki wani kuka mai sauti tare da ajiyar zuciya, Babu wanda baiyi k'walla a wajan bah, Ya saki Ammi da Abba yayi sujada yana mai godiya ga Allah.

Hannu ya bud'ema Areef k'arami ya k'arasa ya rungumesa ya saki kuka yana cewa

"I'm so sorry Bro been so Rude"

Jamal ya girgiza masa kai yana share masa hawaye

"Its Ok"

Mifzal yayi gyaran murya yace

"To Alhamdulillah Allah muna godiya daka kawomu wannan rana"

Ya kalli Jamal yace

"Ina tayaka Farinciki da ganin wannan rana, ranar da kaga Iyayenka na asali."

Jamal ya mik'e zumbur yace

"Ina zuwa pls"

Bai jira mai zasuce ba yabar Falon dasauri, side d'inshi ya shiga ya samu Mabrookah zaune ta zabga tagumi, ya k'arasa tare da kamo hannunta, firgigit tayi ta d'ago tana kallansa, murmushi ya mata itama ta mayar masa

"D'auko Hijabinki ina zuwa"

Ya haura dasauri zuwa sama, d'aki ya samu Ummy tana bacci wanda yanzu ya zaman mata k'aida kullum da rana sai tayishi, hura mata iska yayi a kunne tare da kai mata kiss a bakinta, tad'an bud'e ido a hankali tana kallansa

"Baeby tashi kiji"

Ta turo baki ta k'ara lumshe ido

"Bacci fa nakeyi"

Shima ya shagwab'e fuska yana tura baki

"Yanada mahimmanci neh"

Dakyar ya lallab'ata ta tashi ya d'auko mata hijab tasa suka fito, Mabrookah na nan falonta tana jiranshi, tana ganinsu tare taja tsaki yad'anyi murmushi daidai sanda suka k'arasa saukowa falon k'asan, Hannun Mabrookahn ya rik'e suka fito su duka.

Bai sake hannayen nasu ba saida suka kai k'ofar falon Abba, ya shiga da sallama suma suka bi bayansa, Chak Ummy ta tsaya ganin Bilal a falon, Jamal ya janyo hannunta suka k'arasa cikin falon sosai, dukansu a k'asa kan Carpet suka zauna, Cike da girmamawa Ummy ta gaishe su, ganin haka yasa itama Mabrookah gaidasu tana yatsine fuska.

Jamal ya nuna Abba da Ammi

"Alhamdulillah ku tayani murna naga Parents d'ina"

Ummy ta d'ago dasauri cike da fara'a

"Dagaske?"

Ya gyad'a mata kai yana nuna Abba

"Wannan shine Abbana"

Ya nuna Ammi sannan ya nuna Areef yana cewa

"Wannan kuma k'anina Areef"

Kallo d'aya zakama Ummy ka gane tana cikin farinciki, Mabrookah ko sai yatsine yatsine take daga gefe. Ya d'an duk'ar dakai yana sosa k'eya

"Ummmm Abba wad'an nan Ummmm Ma..Matana neh"

Ammi ta rik'e baki da mamaki

"Duka matanka?"

Ya sake duk'ar da kai yana murmushi, Albarka Abba ya saka musu sannan yace

"Baka fad'a mana meya faru ba bayan rabuwan mu dakai"

Nan ya gyara zama ya zaiyane musu komai har zuwa ranar, Ammi kuka take sosai na tausayin d'an nata, Jin gagarumar gudunmawar da Ummy taba d'an nata yasa taji ta shiga ranta sosai. Kallanta kawai take tana zubar da kwalla.

Ganin yanda Ammin ke kuka sosai yasa Jamal ya rarrafa ya rungumeta yana shafa bayanta

"Its ok Ammina, yau ranar farinciki ne garemu duka"

Ta d'ago kanta tana mai zubar da kwalla tana shafa fuskansa

"We are so sor..."

Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai, sosai Suka burge duka mutanen dake falon. Areef dake gefe yayi murmushi yace

"Abba Lil sis fah na gida"

Abba yace

"Hakane"

Ya juya ga Jamal yace

"Areef nada k'anwa sunanta Areefa"

Jamal ya saki lallausan murmushi cike da faribciki yace

"Woaw ashe inada k'anni dayawa"

Duka falon sukasa dariya, waya Abba ya d'auka ya kira Areefan tana d'auka ta fashe da kuka tana shagwab'an barinta da akayi ita kad'ai, Abba ya soma lallashinta sannan yace gobe tasa driver ya kawota zaria idan suka iso sai ta kirasa. Cikin wani irin ihun murna ta amsa tare da kashe kiran.

Har lokacin Ammi bata daina kallan Ummy bah wacce kanta ke k'asa tana ta murmushi, Ram yace

"Bilal kayi hak'uri akan abinda ya faru, rashin sani neh"

Bilal yayi saurin girgiza kai yana 'yar murmushi

"Babu damuwa, rashin sani ne ai"

Jamal ya sake bashi hak'uri, nan ma ya nuna babu damuwa. Sannan ya mik'e ya musu sallama dan zaije gida, driver Jamal yasa ya d'aukesa ya kaisa gidan bayan ya masa kyautar kud'i yaki karba.

Gaba d'aya Jamal jinsa yake cikin wani irin farinciki, ji yake kamar an d'auke masa kaya. Mifzal da Ram suka musu sallama suma suka tafi, Jamal ya kalli Areef yace

"Bro zo ka tayani wani aiki"

Ba musu Areef ya mik'e yabi bayansa, Mabrookah na ganin sun fita ta mik'e tana wani cin magani tabar Falon, Ammi ta kalli Ummy tace

"Tashi kije abinki Ummy Allah ya miki albarka"

Cikin jin kunya ta amsa ta mik'e ta musu sallama cike da girmamawa. Ammi ta kalli Abba bayan Ummyn ta fita tace

"Yau na fara ganin yarinyan nan, anma wallhi ta shiga raina sosai"

Abba yace

"Nima haka wallahi, kum daga gani tanada natsuwa da kamun kai"

Ammi ta gyad'a kai tana murmushi.

Mabrookah na fita taga Jamal da Areef sun shiga side d'in Mami, harta juya zata koma nasu side d'in sai kuma ta juyo tabi bayansu. Suna shiga Jamal yace

"Wannan side d'in Mami ce itada wicked Sistern tah. Inaso ka tayani mu fitarda komai na ciki inaso Ammina ta dawo nan"

Karaf a kunnen Mabrookah wacce take k'ofar falon tana kallansu fuska a had'e, ta k'araso ciki dasauri tana huci

"Wallahi bazai yuwu ba Ya Jamal, me kake nufi a fitar da kayan Iyayena asa wani"

Ya juyo ya kalleta rai b'ace

"Saboda masu gidan wanda suke da iko da komai na

28 / 32