Chapter 18 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 32

51K to 54K   out of 95.6K words

mai komai ba ta sake fashewa kuka ta bar wajan dasauri. Har ga Allah tausayin halin da yake ciki takeji, da kuma nata, sabda mai tare mata fad'an da wulak'ancin da ake mata yanzu baya nan.

Ram ya k'araso yaja hannunshi suka bar wajan dan mutane ne a wajan dank'am suna jiransu dan yin addu'an uku.

Bayan anyi addu'an an gama, Ummy na zaune a falo kusada su Najma wayanta ya soma ruri, bak'uwar number ta gani ta d'auka da sallama, Muryan Ram taji yana cewa

"Hello Ummy kina jina"

"Eh ina jinka" tace a hankali

"Tun shekaran jiya rabon da Jamal yaci abinci, pls prepare something for him."

"To" tace ya kashe kiran


Tashi tayi ta koma side d'insu, rasa abinda zata dafa masa tayi, chan ta d'au dankali ta fere, ta d'ibo kayan miya tayi blending. Aikin take cikin natsuwa, cikin d'an lokaci ta had'a masa faten dankali daya ji kayan lambu sai k'anshi yake.

Bayan ta gama ta kira Ram ta fad'a masa ta gama. Dakyar yaja Jamal zuwa side d'in. Duk yanda yayi yaci abincin k'i yayi. Haka ya hak'ura ya mik'e ya fita daga side d'in ya kira Ummy

"Dan Allah kiyi k'okari kiga yaci abincin nan, baici komai ba tun sanda akayi rasuwan nan."

To tace ta shiga side din a sanyaye. Kan dinning ta samesa zaune ya k'ura ma abincin ido. Tausayinsa ne ya ratsa ta, ta k'arsa taja kujera ta zauna kusa dashi tareda rik'o hannunsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya kalleta

"Ya Jamal meyasa kaki cin abinci, zaka cutar da kanka neh. Dan Allah ka daure kaci"

Girgiza mata kai yayi alamar Aa

"Addu'a yakamata ka rink'a masa ba tunani bah. Rashin cin abincin ka bashi zaisa ya dawo bah"

Rungumota yayi jikinsa ya fashe da kuka kamar yaro, kukan itama ta soma a hankali tana shafa sumar kanshi. Sun dad'e a haka, dakyar ta tsagaita da kukan ta soma lallashin sa. Abincin ta soma bashi a baki yana taunawa dakyar kansa a k'asa. Ba laifi ya d'anci dayawa. Ta tattara takai kayan kitchen ta dawo, d'akinsa ta shiga ta had'a masa ruwan wanka ta fito taja hannunsa zuwa d'akin.

Binta kawai yake da ido har ta kaisa d'akin

"Ga ruwa a toilet kayi k'okari kayi wanka"

Ya nufi toilet d'in a sanyaye, ita kuma ta bud'e Wardrobe d'inshi ta ciro masa kayan da zaisa.

Bayan ya fito ya shirya ya sake fita wajansu Ram da sauran abokansa da suke amsar gaisuwan tare. A ranar Ram ya koma kaduna sai kuma Ranar Bakwai zai dawo.

Sauran 'yan uwa da abokan arziki duk ranar suka kokoma sai kuma ranar bakwai.

Jamal bai shigo gidan ba sai bayan isha'i, side d'insu ya nufa ya haura sama zuwa d'akinsa da wani zazzab'i ne ke neman rufesa. Ummy na falonta taga ya hauro ya shiga d'akinsa sam bai lura da ita a falon bah. Ita kuma tsoro ne ya cikata, dan tunda akayi rasuwan kullum cikin tsoro take da daddare, su Najma ne ke kokarin tayata kwana. To yau suma suka koma saboda makaranta.

Jim tayi a nan falon tanata muzurai, tunawa tayi da abincin da ta masa, hakan yasa ta mik'e dasauri tana waiwayan bayanta saboda tsoro. D'akin ta shiga da sallama, kan gado ta hangosa kwance ya k'udundune cikin bargo sai rawar sanyi yake.

Dasauri ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kallansa hankali tashe

"Ya Jamal bakada lafiya neh"

Goshinsa ta tab'a taji zafi sosai, ta mik'e a rud'e

"Barin je na fad'ama Mami azo a kaika asibiti"

Kallo d'aya zaka mata ka gane hankalinta a tashe yake, dakyar ya iya cewa

"No barki kirasu, i will be fine"

Idanunta suka ciko da kwalla

"Kaga fa jikinka da zafi sosai"

D'agowa yayi dakyar yace

"Zo kiga abinda zaki min"

Ba musu ta matso gabab gadon tana kallansa, janyota yayi ta fad'a kan gadon ya rungumota sosai jikinsa. Idanu Ummy ta zare ta soma mutsu mutsu

"Pls ki tsaya, inaso naji d'umin jikinki neh, sanyi nakeji sosai Wife"

Yanda yayi maganan sosai ya bata tausayi, ta daina mutsu mutsun, rungumeshi tayi sosai ta d'aura kanta akan suman kanshi, d'ayan hannunta kuma tana wasa da suman.

Sun dade a haka har bacci ya d'auketa. Cikin bacci taji kamar ana shafata, a razane ta bud'e ido taga wutan d'akin a kashe, rungumota yayi sosai a jikinsa ya had'e bakinsu waje guda.

Nan ta biye masa sunata kissing juna, salan karatun nasa ne taji ya soma chanzawa jin hannunsa akan k'irjinshi.

Mutsu mutsu ta soma tana k'okarin kwacewa anma ta kasa saboda rik'on daya mata. Lokaci k'ank'ani ya rabata da kayan jikinta. Ba shiri ta fashe masa da kuka tana girgiza masa kai tareda rad'a masa

"Dan Allah Ya Jamal kayi hak'uri wallahi bazan iya bah"

Kasa ce mata komai yayi sai wasa dayake da duk ilahirin jikinta yana wani irin numfashi. Wani kuka ta saki jin hannunsa a k'asanta. Gaba d'aya ya rud'e ya fita daga haiyacinsa. Ba irin rok'on da Ummy bata masa ba a daren ranar anma baiji bah.

Bata k'ara rud'ewa ba saida taji yana addu'ar saduwa da iyali, wani wahalalen kuka ta saki ta k'ankameshi tana girgiza masa kai. Cikin kuka yace

"Pls Wife"

Sake k'ankamesa tayi, chan kuma ta saki wani razananen ihu. Ina ganin haka naja hannun k'awar arziki Sumaiya Eesah mukayo waje.

Ummy Abduol✍🏻
[3/29, 9:23 AM] ‪+234 809 545 5143‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 50 n 51

Sake k'ankamesa tayi, chan kuma ta saki wani razananen ihu. Ina ganin haka naja hannun k'awar arziki Sumaiya Eesah mukayo waje.

K'arfe Sha biyu da kusan rabi ya sarara mata, lokacin ko hannunta bata iya d'agawa. Gefenta ya fad'a yana maida numfashi da kyar, a hankali wasu sabin hawaye suka soma sauko masa, ya juya ya gefensa inda take kwace duk da baya hangota sosai saboda duhun dake d'akin.

Tattaro k'arfinsa yayi ya janyota jikinsa dakyar yana maida numfashi.

Wani wahalalen kuka ta saki a hankali, so take ta turesa daga jikinta anma ta kasa saboda yanda jikinta ya mata tsami.

Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata

"Its Ok Pls ki daina min asaran hawayenki"

Tsoro tareda haushin sa ne suka cikata, tattaro sauran k'arfinta tayi tad'an tureshi ta sakw fashe masa da kuka.

"Oh God!" Ya fad'a tare da dafa goshinsa. Mik'ewa yayi da kyar ya shiga toilet. Wanka yayi sannan ya tara mata ruwa mai d'umi.

D'akin ya koma ya kunna wuta, jan bedsheet tayi ta rufe jikinta dashi tana cigaba da kuka. Bai ce mata komai ba ya k'arasa bakin gadon ya d'auketa ya kaita toilet. Yana sakata cikin ruwan ta saki k'ara a wahale da muryanta daya dishe, Tausayinta ne ya cikasa. Dakyar ya samu ya gasata tareda mata wanka dana tsarki. Duka da kukan shagwab'a kam yasha shi. A toilet ya nad'o ta ya ajeta kan bedside ya cire bedsheet d'in.

Kuka ta sake fashewa dashi, ya dawo da ita kan gadon ya zaunar da ita shi kuma ya tsugunna gabanta

"I'm sorry Wife, i dnt mean to hurt uh"

Ta kauda kai gefe tana kuka tareda turo baki

"Ni wallahi bazan yarda bah, kuma saina had'aka da Mama."

Dariya yad'anyi yana shafa suman kanta dake d'igan ruwa

"Bansan abinda zance dake ba Wife, uh really make my day. Allah ya miki albarka, ya barmu tare. I love uh so much"

"Ni dai ka fita, kuma karka k'ara min magana"

Yanda take maganan cikin shagwab'a ne ya burgesa, ya sa hannu yana k'okarin jan Towel d'in jikinta.

"Wayyo ni ka bari"

Ta sake fashe masa da kuka, dariya yayi ya zauna kusada ita tareda rungumota jikinsa

"Kai Wife, haka zamu fara? Ni fah mabuk'aci ne, inasan kullum na rinka jin d'umin jikinki"

Ta turesa tana k'okarin mik'ewa

"Ahh!"

Ta saki k'ara ta koma ta zauna tana kuka, fuskarsa d'auke da damuwa yace

"Sorry! Ni neh koh"

Ta juya kai gefe tana share hawaye, mik'ewa yayi ya d'auko vasline da kansa ya shafa mata tana ta nok'ewa. Nyt wears marasa nauyi ya d'auko mata a d'akinta ya saka mata yanata dariya ganin yanda ta chuno baki gaba tana b'ata fuska.

"Kada dai bakin yakai gate"

Duka ta d'aka mai ta sake fashe masa da kuka. Yayi saurin rungumota yaja musu bargo yana cewa

"Oh God! Yaudai na shiga uku, bakya gajiya da kuka neh Wife"

"Ni gobe gidan mu zan tafi bazan zauna bah, tunda mugunta kake min"

Dariya yayi mara sauti, yana jinjina rigima irin na Wife d'insa.

Lallashinta ya soma yi a haka bacci mai nauyi ya d'auketa a jikinsa. Murmushi yayi yana jin saukar numfashinta a k'irjinsa. Wani santa da tausayinta ne ke k'ara shigansa.

Hawaye suka gangaro masa na tunawa da halin da suke ciki, gaba d'ayansu yanzu sun zama marayu. Tunane tunane ya soma har bacci ya d'aukesa.

Wuraren biyar da kwata na asubah kukanta ya tashesa, d'an bud'e ido yayi ya hangota chan gefensa ta juya baya tana kuka, ba shiri ya mik'e zaune ya matsa kusada ita, janyota yayi jikinsa yaji jikinta da zafi sosai. Lumshe ido yayi ya bud'e Ya mik'e dasauri

"Im so sorry Wife"

K'ara narkewa tayi a jikinsa tana cigaba da kuka. Lallashinta ya soma ya mik'e dakyar dan shima zazzab'in yaji yana neman rufesa.

Magani ya d'auko a drawer ya fita zuwa kitchen ya d'auko ruwa. Dakyar ta yarda ya bata maganin suka koma suka kwanta.

Makara sukayi ranar, basu suka farka ba sai k'arfe goma na safe. Shi ya fara tashi yana sallati ganin gari yayi haske. Janyeta yayi daga jikinsa ya gyara mata kwanciya ya shiga toilet. Wanka yayi tareda alwala ya fito, zaune ya sameta kan gado tana turo baki, murmushi yayi ya k'arasa bakin gadon ya shafa gefen fuskanta

"Morning Wife"

Ta sake turo baki ta kauda kai, k'ugu ya rik'e ya tsaya gabanta

"Idan baki daina turo min baki bah zan sake"

Nan da nan kwalla ya cika idonta

"Ayyah fah! Ayyah fah!! Ba kyau"

Dariya yayi ya shimfid'a sallaya ya tada sallah. Dak'yar ta mik'e ta shiga toilet ta sake gasa jikinta sannan tayi wanka tareda alwala ta fito.

Ta gabansa ta wuce tana tafiya a hankali tana cije leb'e, tausayinta ne ya kamasa ya mik'e ya d'auko mata hijab d'in da kansa ya saka mata ya kaita kan sallaya.

Ranar da kansa ya musu breakfast sai tattalinta yake. Bashi ya shiga side d'in Mami ba sai bayan sallan Azahar. Zaune ta samesu a falo itada Aunty Faty da Mabrookah sai sauran masu amsar gaisuwa. Har k'asa ya tsugunna ya gaida su, Aunty Faty ta yatsine fuska tace

"Sai yanzu ta sakeka kenan"

Haushin Aunty Faty yakeji yanzu sosai, yace

"Eh Bata da lafiya neh"

Aunty Faty da Mabrookah suka kalli juna a tsorace. Mami ya kalla yace

"Mami kuyi hak'uri Yau Wife bazata samu shigowa ba, batada Lafiya"

Ya mik'e yace

"Barinje waje wajan mutane"

Baki bud'e Aunty Faty ke kallansa harya fita.

Ita kuwa Ummy tana chan tana sharan baccinta dan yace bayasan taje ko ina ta zauna a d'akinta.

Har yakai bakin gate wayansa ta hau ruri, numbern Bilal ne ya fito ya d'auka tareda karawa a kunne. Wani Dariya Bilal ya kwashe dashi kana yace

"Jamaludeen Surajo! Har yanzu kana bani mamaki, lallai bakasan Bilal bah. Kamar yanda na fad'a maka a baya, akan abinda nakeso ina iya yin komai"

Jikin Jamal ne ya soma rawa, ya katse kiran dasauri hankalinshi a tashe. Numbern Mifzal ya soma kira dan d'an sanda neh, ringing d'aya biyu ya d'auka.

"Mifzal na samu wanda ya turo wad'an nan 'yan fashin, kuma yanzu ta tabbatar min da haka"

Daga chan b'angaren Mifzal yace

"Are you sure"

Murya na rawa yace

"I'm very sure."

"To shikenan ka kwantar da hankalinka, ina nan zuwa yanzu"

Bai jira mai Jamal d'in zaice ba ya kashe kiran. Waje ya fita hankalinsa tashe yana jiran k'arasowar Mifzal, cikin 'yan mintina ya iso k'ofar gidan. Bayanin duk abinda ke faruwa Jamal ya masa tareda nuna masa texts d'in daya ke turo masa. Da kuma wayan da sukayi yanzu dan yasa a record.

Mifzal yace

"Lallai bashida imani, anma inaso ka bani had'in kai. Dan a hankali nakeso abi komai, sannan ko kad'an kada ka nunama Ummy ko su Mami abinda ke faruwa"

Kai kawai Jamal ya iya d'agawa. Numbern Bilal d'in yaba Mifzal sukayi musabaha ya tafi tareda alk'awarta masa komai zaizo k'arshe kwanan nan.

Haka Ango Jamal ya cigaba da tattalin Wife d'insa har zuwa ranar da Abba ya cika kwana bakwai. Ranar sunga jama'a daban daban, har 'yan ajinsu Ummy sunzo mata gaisuwa da sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Aunty Faty kam zama daram dan tace nan zata zauna ta taya 'yar uwarta takaba. Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci dajin zaman Aunty Faty a gidan.

Bayan bakwai Jamal ya koma bakin aikinsa, a ranar Ummy ce da girki, taci gayunta cikin Atampa riga da skirt, wanda ya amsa jikinta sosai.

Kitchen ta shiga ta fito da kulolin abinci ta d'aura kan dinning da komai datake buk'ata. Har ta bud'e k'ofar d'akinta ta jiyo k'aran motansa, dasauri ta shiga ta sake fesa turare mai dad'in k'anshi ta fito.

Kamar kullum d'akin Mabrookah ya shiga, itada Aunty Faty ya samesu suna k'us k'us, baice musu komai ba ya haura sama. Tun a stirecase k'amshi ya soma masa sallama. Wani lallausan murmushi ya saki ya k'arasa hawa saman. D'aki ta fito tana takawa a hankali tana masa murmushi

"Sannu da dawowa"

Tasa hannu zata karb'a jakan hannunsa, janyo hannun nata yayi ta fad'o jikinsa ya matseta sosai

"Zaki kasheni da salon gayunki Wife. Kinyi kyau sosai"

"Nagode" tace tana 'yar murmushi. Ya shagwab'e fuska yace

"No Wife, ni dai ba haka nakeso kina min sannu da zuwa bah"

Ya sake janyota jikinsa yace

"Ko kiga yanda akeyi"

Had'a bakinsu yayi waje guda, ya sureta yayi d'akinshi da ita sai wuntsile wuntsile take

"Ni dai dan Allah ka saukeni"

Duk abinda sukeyi Mabrookah na tsaye ta wajan stirecase tana kallansu zuciyarta na tafarfasa. Daga chan k'asa Aunty Faty tace

"Maza jeki barbad'a kafin su fito"

Ta goge kwallan daya taru mata a ido ta k'arasa dinning d'in.


_Manage this pls_ bana d'an jin dad'i neh

Ummy Abduol✍🏻
[3/29, 9:23 AM] ‪+234 809 545 5143‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Assalamu Alaikum. A gaskiya bani da bakin da zan gode muku Fans d'ina, naga sak'o da dama naga kira da dama, ina godiya Allah ya barmu tare Ameen. Alhamdulillah na soma samun sauk'i, saidai zaku cigaba da min afuwa na jina ba akan lokaci bah. But uh guys are always on my heart*

Wannan shafin naku ne Masoya *Ummy Abduol* Ina alfahari daku.

My Facebook Fans kuma ina godiy ba iyaka Musamman Ahmad Yusuf Muhammad. Thank Uh so much.

_ga masu san novels d'ina dana rubuta a baya, suna iya ziyartan Page d'ina na facebook UMMY ABDUOL NOVELS domin samun littafaina_

Page 52 n 53

Ta goge kwallan daya taru mata a ido ta k'arasa dinning d'in.

Yana shiga d'akin bai ajeta ko ina ba sai kan gado, hawa yayi ta soma turo baki tana matsawa

"Ba kyau fah Ya Jamal, ba kyau"

D'an murmushi yayi ya sauka daga kan gadon tareda yin k'wafa, ya juya ya fita dan yabar jakan daya dawo dashi a falo.

Har Mabrookah ta bud'e kulan zata barbad'a ta juyo k'aran kamar za'a bud'e kofa, dasauri ta mayar ta rufe ta shige labule ta b'oye dan yanada kauri sai ka k'ura ido zaka ganta.

Fitowa yayi yad'anyi jim yanabin falon da kallo dan yad'anji motsi, Jakan ya d'auka ya juya Ummy ta fito daga d'akin tana turo baki

"Keh koh!"

Ta k'arasa dinning d'in ta zauna,

"Ni yunwa nakeji, tun dazu nake jiranka"

Baice mata komai ba saima k'arasawa dayayi kusada ita, tashi tayi k'okarin yi yasa hannu ya maidata zaune yana murmushi ya rad'a mata

"Ni kuma ke nake buk'ata sosai Wife"

Tayi saurin tureshi a hankali.

yayi murmushi ya zauna kan kujeran dinning d'in ya k'ura ma k'irjinta ido. Serving d'inshi tayi sannan itama ta zuba nata kad'an ta koma ta zauna. D'aukan nata yayi ya had'a da nasa, ta turo baki tana kallansa.

Mabrookah dake cikin labule sai zufa take tana kallansu, ga wani hawaye dake gangaro mata. Ji take kamar taje ta shak'e Ummy ta kasheta. A baki Jamal ya soma ba Ummy tana ci a hankali tana cigaba da turo baki, Yayi murmushi tareda shafa bakin yace

"Wife rigima"

Kamar ance ta d'aga kai ta hango Mabrookah tsaye cikin labule tana kallansu, sosai ranta ya b'ace Jamal yace

"Yadai Wife naga fuskanki wani iri"

Murmushin yak'e ta masa

"Babu komai"

Ta d'au spoon ta deba abincin takai mai baki tana shagwab'a

"Ni dai inaso naje gida naga Mama"

"Kai Wife! Yaushe yaushe kikaga Maman"

Ta mik'e tana turo baki tareda bubuga k'afa a k'asa tana kukan shagwab'a

"Nidai..Nidai zanje naga Mamana"

Baki bud'e ya kalleta, ta cigaba masa da kuka tana turo baki, janyota yayi ta fad'a jikinsa tareda zagaye wuyansa da hannunta tana murmushi, wanda ita kad'ai tasan dalilinsa

"Wife rigimanki tayi yawa, kinsan meh?"

Ta girgiza masa kai alamar Aa

Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata

"I miss uh so much, pls yau dai ki tausaya min"

Kokarin mik'ewa take ya rik'eta ya had'a bakinsu waje d'aya.

Mabrookah dake cikin labule kamar ta sume haka takeji, kuka kawai take a hankali tana cigaba da kallansu. Biye masa Ummy tayi sunata kissing juna a falon, dakyar ta janye jikinta ta mik'e tareda jan gaban rigansa cikin salo

"Baby tashi muje, dan akwai 'yan sa ido"

Sam bai cikin haiyacinsa dan network d'insa ya riga ya d'auke. Haka ya bita har zuwa d'akinsa.

Mabrookah na ganin sun shige ta fito tana hawaye hannunta aka tana kuka. Bata ko bi takai maganin ba ta sauka zuwa d'akinta. Aunty Faty ta samu a d'akin ta fad'a kan gado tana kuka

"Ni wallahi na gaji, ni ya sawak'e min na huta"

Buge mata baki Aunty Faty tayi rai b'ace

"Anma ban tab'a sanin ke akuya bace Mabrookah sai yau. Ya sawak'e miki?"

Ta maimaitana tana kallan Mabrookahn dake ta sharb'an kuka.

"Umma Jamal baya sona, ko abinci na baya san ci. Bai damu dani ba sai Ummy"

Dogon tsaki Aunty Fatyn taja

"Ke wawiya ce, a gabar da ake ciki yanzu ko da d'ibar namanki zai rink'a yi yana ci karki sake ki rabu dashi. Gidan kud'i fa kike, Allah kad'ai yasan mak'udan

18 / 32