Chapter 3 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 32

6K to 9K   out of 95.6K words

d'aya ba ma. Mama taita lallashinta har tayi shiru, d'akin Baba ta shiga da mai sallama, Lalluban kanta yayi ya d'aura hannunsa akai ya mata addu'a tareda nasiha, har lokacin kuka Ummyn keyi. Yana gamawa tayi mai sallama ta fito, suka k'ara sallama da Mama ta fito ta shiga gidan Inna itama sallaman tayi mata sannan ta fito ta tari adaidaita sahu ta hau.


Kasancewar ranar Lahadi neh Hanyar duk yad'an chuse saboda masu zuwa church, cikin idon Allah suka isa kofar gidan, Mai gadi na ganinta ya shaidata saboda Hajiyan tamai bayaninta, Cikin gidan ta nufa kai tsaye a k'ofar falon ta soma knocking chan aka bud'e wata y'ar budurwa black beauty ce tsaye sanye da Legins bak'i daidai guiwa da farin top gashin kanta mai tsaye, d'an rusunawa Ummy tayi ta gaidata


"Daga ina?" Cewar budurwar

Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace

"Hajiya ce tace na dawo yau"


Yatsine fuska tayi tana kallanta up and down

"Kice y'an maula ne, tho Hajiyar na bacci"


Kalmar da budurwar ta kirata dashi sosai ya b'atamata rai, batace komai ba ta k'ara d'ukar dakai. Tsaki taja ta bugo kofan, hawaye suka taru a idanunta a hankali ta juya ta soma tafiya, wata y'ar dattijuwa ce ta tareta tana tambayanta lapia, Bata b'oye mata komai bah, Tsohuwar tayi murmushin takaici.


"Badai Hajiyar bace tace kizo"

Kai Ummy ta gyad'a, Tsohuwar tace


"Ki nemi waje ki zauna, anjima idan Hajiyar ta sauko zan mata magana"

Godiya taima matar ta samu waje chan wajan gate ta zauna tana k'ara bin Gidan da kallo. Tana nan zaune wani ya shigo gidan shida wata daga gani likita ne sabda yarinya dake binshi a baya kayan nurses ne a jikinta ta rik'e wani folder. Suna shigowa kai tsaye cikin gidan suka shige.

Binsu da kallo Ummy tayi tana tunanin kodai Hajiyarce bata lafiya shiyasa aka hanata ganinta. Takai kusan awa d'aya sannan taga fitowar likitan tareda Hajiya, mik'ewa tayi dasauri ta k'araso wajan daidai lokacin sun gama magana da likitan.


"Ina kwana Hajiya"


"Aa Ummy lapia lau, har nayi tunanin bazaki dawo bah"


Kan Ummy a k'asa tace "Aa ai tun d'axu na shigo ance ne baki tashi bah"


Hajiyar ta soma tafiya sannan tace "Biyoni"

Falon suka shiga, wani d'aki dake nan k'asan Hajiya ta kaita tareda shaida mata nan ne d'akinta. D'akin ba k'aramin burge Ummy yayi ba duk da ba wani abubuwa bane a d'akin, Gado ne d'an k'arami sai wardrobe dukansu Pink, daga gefen hagu akwai wata k'ofa da alama Band'aki neh.


Kayanta ta aje suka koma falo itada Hajiyar, Kan Carpet ta zauna ita kuma Hajiyar ta hakince a kujera


"Inaso ki natsu kiji abinda zan fad'a miki"


"Tho Hajiya"


Hajiya ta gyara zama tace

"A tsarina banasan Katsalandan ma'ana banasan mutum na shiga hurumin da ba nashi bah, Sannan ki tsaya a matsayinki na y'ar aiki ba ruwanki da shiga inda ban umarceki bah."


Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace "Tho Hajiya"


Budurwan nan ne ta sauko tana wani juyi da alama wak'a takeji dan ta rufe kunnuwanta da katon earpiece, Tana ganin Ummy tayi saurin zame earpiece d'in daga kunnenta


"Danace ki tafi wato baki tafi ba koh"


Hajiya tayi saurin cewa
"Haba Mabrooka, why kike koranmin mutane idan sunzo gurina"


Ta turo baki tareda zama tana hararan Ummy


Hajiya ta nuna Budurwar tana cewa


"Ga y'ata sunanta Mabrooka sannan inada d'a namiji sunanshi Jamaludeen"


Kai Ummy ta gyada har lokacin kanta a k'asa


"Mami me tazoyi gidan nan"

"Aiki tazoyi" Hajiya ta bata amsa


Mabrooka ta gyara zama tana murmushi


"Yauwa Mami kamar kinsan Wallahi banasan aikin wannan Baban bata iya gyaran d'aki ba"


Murmushi Hajiya tayi


"Babu damuwa"


Ta maida dubanta ga Ummy

"Aikinki a gidan nan shine gyarama Mabrooka d'akinta da nawa sai ki rink'a taimaka ma Baba da ayukan da takeyi"


"Tho Hajiya"


Hajiya ta k'ara da cewa

"Karki manta da ki tsaya a matsayinki"


Kai Ummy ta gyad'a Hajiya ta sallameta ta koma d'aki. Bayan azahar Mabrookah ta shigo d'akin tana yatsine fuska

"Sai ki taso muje in nuna miki d'akin ki"


Bah musu ta mik'e suka soma zagayawa, Sosai gidan ya burge Ummy tanata kallo harda sakin baki.

Daddare bayan Alhajin gidan ya dawo Mami ta gabatar da Ummy wajanshi, yayi na'am da zuwanta nan Mabrookah ta shiga k'orafin ita hakanan taji yarinyan bata mata bah, Lallashinta Mami tayi dakyar ta amince da Ummyn.


Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

Page 9

Washe gari Ummy na sallan asubah ta fito daga d'aki dan soma aikinta, tsayawa tayi a falon k'asa tana k'arema falon kallo dan batasan ta inda zata fara bah. Wata y'ar budurwa wacce bata wuce sa'arta bah ta shigo falon sanye da riga blue iya guiwa da bak'in wando, Ummy tayi mata murmushi tareda gaidata. Yarinyar ta amsa tana cewa

"Jiya na ganki Aunty Mabrookah na zagayawa dake, kema aiki zaki fara?"

Kai Ummy ta gyad'a tace

"Eh jiya nazo, kema aiki kikeyi"

"Eh ni ina b'angaren kicin neh, Sunana Laurat"

Murmushi Ummy ta sakar mata tana cewa

"Ni kuma sunana Jaleelah anma Ummy ake cemin, Hajiya tace zan rink'a gyara mata d'aki da kuma Mabrookah sai..."

Toshe baki Laurat tayi ta waiga bayanta ta juyo tace tareda sassauta murya

"Kada kija ma kanki dan Wallahi Aunty Mabrook batada mutunci. Wai dole sai an rink'a kiranta da Aunty"

Da mamaki Ummy ta kalleta

"Aunty kuma?"

Laurat ta gyad'a kai tace

"Umm barinje b'angarena zamu had'u anjima wajan amsar abinci"

Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar wajan dasauri, d'aki ta koma ta zauna dan tasan yanzu su Hajiyan basu tashi ba balle tayi aikinta.

K'arfe bakwai da rabi ta fito, Hajiyar ta hango da Mabrookah kan dinning suna breakfast, dasauri ta k'arasa ta rusunna ta gaida Hajiyan, da fara'a ta amsa, ta juya ta gaida Mabrookah daketa cika tana b'atsewa
kauda kai Mabrookah tayi bata amsa bah, Hajiya tad'anyi murmushi tace

"Yau zaki fara aikinki, inaso ki kasance mai gaskiya sannan ki tsaya a matsayin ki. ina fata kin ganeh"

Kai Ummy ta gyad'a tace

"Insha Allahu Hajiya zan kiyaye"

Mabrookah ta mik'e tad'au handbag dintah tana cewa

"Mami zan tafi"
ta juya ta kalli Ummy cikeda tsana tace

"Make sure kin gyara min d'akina yanda nakeso dan idan bai gyaru ba na dawo sai kin sake"

taja dogon tsaki tabar falon tana surutai, ga mamakin Ummy sai ganin Hajiyar tayi itama ta mike tad'au handbag dina da keyn mota ta fita. girgiza kai kawai tayi ta mik'e ta shiga store tad'au tsintsiya, mopper da parker ta haura sama zuwa d'akin Mabrookan.

Batsa batsa ta sameshi kamar ba d'akin mace bah, wani dogon tsaki taja tana bin d'akin da kallo

"Ji d'akin mace, sai shegen k'azanta"

Kayan dake zube a k'asan d'akin ta soma kwashewa, sannan ta cire bedsheet d'in dan shima yayi dati sosai, Wardrobe ta duba ta ciro wani ta shimfid'a, dak'in ta gyara tsaf tayi shara tayi mopping tareda fesa room freshner, nan da nan d'akin yad'au kamshi, toilet ta shiga ta wankeshi tas ta kwashe kayan dake laundary basket ta fito dasu, tana saukowa k'asa ta had'u da wannan likitan data gani da nurse suna haurowa, gefe ta matsa ta gaidasu sannan ta sauko.

Mamaki neh sosai ranta, tho ko meh wad'an nan mutanen ke zuwa yi gidan kullum? Da wannan tunanin ta zagaya chan bayan gidan ta soma wankin kayan, wani tsoho ne ya zo wajan rik'e da bokiti da wasu kaya, tsoho ne sosai dan a kalla zai kai shekara saba'in, gaidashi tayi ya amsa ya soma kici kicin fara wanki da alama kayanshi, k'arasawa tayi inda yake ta rik'e bokitin tace

"Baba kawo na wanke maka"

Ya d'ago dasauri yana kallanta da murmushi

"Aa 'yar nan bashi kawai keda kike naki aikin"

Tad'anyi Murmushi ta kwashe kayan tana cewa

"Ba komai Baba ai zan iya kawo kaga"

Albarka ya soma sa mata tareda tambayan sunanta, ta fad'amai yace shi yana aikin ba flower ruwa neh a gidan. Cikin y'an mintina ta gama wankin ta d'auraye ta shanya ta koma sama.

D'akin Mami ta shiga, d'akin tsaf yake ba datti sai k'anshi dake tashi, bedsheet d'in taja da niyar karkad'ewa, bandle d'in dari biyar ne ya fad'o ta matsa dasauri da mamaki tana kallan kud'in, jim tayi sannan ta d'au kud'in ta aje saida ta gyara d'akin tsaf ta wanke toilet sannan ta d'au kud'in ta aje k'arkashin filo ta fito bayan ta rufe d'akin da key.

Saukowa tayi ta nufi babban kicin d'in side d'in, ma'aikata ta gani sunata aiki duka sanye da irin kayan jikin Laurat, gaidasu tayi ta k'arasa inda Laurat d'in ke tsaye tana wanke wanken kayan da akayi breakfast dasu a sink.

"Ummy har kin gama naki aikin?"

Kai Ummy ta gyad'a tace

"Na gama, nayi sauri koh?"

"Sosai ma" Laurat tace

K'aran bell sukaji Laurat ta wanke hannunta taja hannun Ummy tana cewa

"Lokacin amsan Breakfast yayi muje"

Binta Ummy tayi har zuwa wani runfa chan bayan gidan, nan Ummy ta baza ido ganin ma'aikata daban daban, dukansu sanye da uniform wasu da Blue riga da black wando, wasu Green riga, wasu pink. Sakin baki tayi ganin ma'aikatan gidan harda turawa su hud'u, maza uku mace d'aya, su kuma suna sanye da Arsh riga da bak'in wando. Tab'ata Laurat tayi tana nuna mata plate, a tare suka d'auka suka soma bin layin amsar abincin.

Soyaiyar doyace da k'wai sai Slice d'in bread guda uku da Tea. Ma'aikatan sai kallan Ummy suke ganinta cikinsu kuma babu uniform, suna amsa itada Laurat suka shiga d'akin Ummy suka zauna suka soma karyawa.

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

Page 10

Bayan sun gama Laurat ta soma bin d'akin da kallo cikeda sha'awa

"Keh kam kinji dad'inki, d'akinki daban"

"Ku ya naku yake?"
Ummy ta tambayeta

"Tab aimu d'aki d'aya mutum biyar neh, ko ku nawa neh a b'angaren da kuke aiki to d'akinku d'aya"

Gyad'a kai Ummy tayi sannan tace

"Niko inaso na miki wani tambaya Laurat"

Gyara zama tayi sannan tace

"Ina jinki"

Ummy ta cigaba da cewa

"Naga Kunasa Uniform ma'aikatan kicin, Sauran dana gani ma'aikatan menene"

Laurat tad'anyi murmushi tace

"Ko wani b'angare da uniform d'insa, bakiga ko masu gadin gidan nan da uniform ba"

Ummy ta gyad'a kai, Laurat tace

"Wannan matsiyaciyar Mabrookan ce, da ba'asa Uniform itace ta kawo wannan tsurfan"

"Na lura batada kirki ko kad'an"

Laurat tayi dariya tace

"Keda kikazo ma jiya knan har kin fahimta"

"Tho wad'an nan turawan fa dana gani"

Dasauri Laurat ta mik'e tana cewa

"Ki bari zamuyi magana anjima, barin koma bakin aikina gwara ke har kin gama naki"

Itama Ummyn ta mik'e

"Barinzo muje na tayaki aikin"

Kicin d'in suka nufa Laurat ta cigaba da wanke wankenta Ummy na mata d'auraya. Shanyanta ta kwaso ta nunke ta kai mata d'aki ta koma kicin inda Laurat take.

Haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan, kullum sai taga kud'i a k'arkashin pillown Mami saidai ta aje gefe data gama ta mayar inda ta aje. Kullum tana gama aikinta zata tafi kicin su cigaba da aiki da Laurat.

Hurama Mami wuta Mabrookah tayi dole akayi ma Ummy uniform dan itama asan cewa y'ar aiki ce a gidan, badan taso ba aka d'inka ma Ummyn Purple riga da bak'in wando wanda ita kad'aice mai irin Uniform d'in duk cikin masu aikin.

Yau Sati, da wuri Ummy ta gama ayukanta wuraren k'arfe Sha biyu, Mami ta samu a falo tana rubuce rubuce a wani takarda, ta rusunna tace

"Sannu da hutawa Hajiya"

D'agowa Mamin tayi tace

"Yauwa sannu Ummy"

Jim tayi sannan tace

"Hajiya na shirya zan tafi gida"

"Ohh kinga ko na manta da maganan zuwa gida yin weekend"
Handbag d'inta ta d'auko dake gefenta ta ciro dubu uku ta mika mata tana cewa

"Gashi kiyi kud'in mota ki gaidasu"

Godiya Ummy ta mata ta mik'e ta koma d'akinta, Uniform ta cire tasaka doguwar rigar atampha tasaka hijabinta har k'asa ta fito, Laurat tama sallama da sauran ma'aikatan gidan, tama Baba mai ba flower ruwa sallama ta fito. Saida ta biya kasuwa tayi sayaiyar kayan miya yarda kaza guda d'aya ta nufi gida.

Mama da Baba sunyi farinciki sosai da ganinta, ranar ita ta musu girki sai sa mata albarka sukeyi, sai bayan isha sannan ta shiga gidansu Bilal, itama Umman Bilal tayi murna da ganinta, d'ari biyar ta bata tanata godiya sun d'an tab'a hira sannan tamata sallama ta dawo gida. Ranar sunday sai da yanma sannan ta koma gidan aikinta, Ranar tasha fad'a sosai wajan Mabrookah kan k'in komawanta da wuri. Sadda kai kawai tayi k'asa harta gama fad'anta tayi gaba sannan ta shiga d'akinta.


Washe gari da safe kamar kullum Ummy ta fito dan gaida Hajiya da kuma Mabrookah, yau harda Alhaji ta gani suna breakfast d'in tare, Yau neh karo na biyu da ta tab'a ganin Alhajin gidan, daga gani ko ba'a fad'ama ba kasan babban mutum neh, Tsugunawa tayi har k'asa ta gaidasu duka suka amsa Alhaji yad'au Briefcase d'inshi ya musu sallama ya fita. Mabrookah ma ta mik'e tadau jakanta sai hararan Ummyn take tama Mami sallama ta fita. Har Ummy ta tashi Mami ta kira sunanta tareda nuna mata kujera nan kan dinning, ba musu ta zauna kanta k'asa Mami tace

"Na gwada ki da dama Ummy kuma kinci jarabawar dana miki, Lallai kinada gaskiya da rik'on amana"

Duk'ar dakai Ummyn tayi tana murza zoben dake hannunta, Hajiya ta cigaba da cewa

"Inaso na k'ara miki wani aiki guda d'aya, duk da nasan wannan ba tsarin mai aiki baneh. Anma yanayin aikina neh banida lokaci. Inaso ki rink'a gyara ma Alhaji d'aki duk safiya"

Ummy tad'an d'ago da mamaki tana kallanta, lallaima Matar nan ita ina ta tab'a ganin wata ta gyara ma mutum d'akin miji.

"Kina jina" cewar Hajiya tana kallanta

"Eh Hajiya"

Keyn d'akin ta mik'a mata tana cewa

"Ga keyn d'akin ya zamana yana hannunki. Karnaji ko naga ba daidai ba ina fatar kin ganeh"

Ummy ta gyad'a kai

"Insha Allahu Hajiya zan kiyaye"

Batace komai ba ta Haura sama ta d'auko Handbag d'inta ta fita.

Kallan Keyn Ummy ketayi tana jujuyashi a hannunta, a haka ta shiga kicin inda su Laurat suke, zaune ta sameta tana yanka kankana ta zauna kusada ita

"Kinsan menene?"

Cewar Ummy tana kallan Laurat

"Aa saikin fad'a"

Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ciro keyn da Hajiya ta bata ta nunama Laurat tace

"Wai keyn d'akin Alhaji Hajiya ta bani na rink'a gyara masa"

Magana sukaji daga bayansu ana cewa

"Lallai kam kina cikin tsaka mai muya"

A tare suka juya sukaga wata y'ar dattijuwa wacce zatayi sa'ar Hajiyan saidai Ita Uniform d'inta Green neh, ta k'araso ta dafa Ummyn tace

"Baki ganeni ba koh"

Kai Ummy ta girgiza alamar eh, Matar tayi murmushi tace

"Ni ce wacce na ganki Ranar da kika fara zuwa har Mabrookah ta hanaki shiga"

Sai a sannan Ummy ta shedata tad'anyi murmushi tace

"Na tuna"

Dattijuwar tace

"Sunana talatu, tun ranar dana ganki naji kin kwanta min a rai ganin sauk'in kanki da kuma tarbiyarki. Lallai kin chanchanci aikin da aka saki"

Laurat tace

"Mama Talatu anma Hajiyar nan batada hankali ina aka tab'a ba yar aiki gyaran d'akin miji"

"Kull 'yar nan, kinsan dai irin gidan da kike. Ki kama bakinki kisa masa lunzami"

Turo baki Laurat tayi ta cigaba da aikinta, Mama talatu ta kalli Ummy tace

"Wannan wani aiki neh babba Ummy, ki kula ki tsare gaskiya. Kinsan zuciya batada k'ashi, kiyi taka tsantsan da duk wani abu da kika gani, kada ki zama mai yawan bincike. Ki tsaya a matsayinki inda aka ajeki, banda shishigi akan alamuran gidan nan kinaji"

Kai Ummy ta gyad'a tace

"Nagode Mama Talatu Insha Allahu zan kiyaye"

Mama talatu tace

"Sannan duk abinda baki ganeh ba ki tambayeni, ni ina b'angaren masu share share neh kinji"

Ummy ta k'ara gyad'a kai, Mama talatu ta masu sallama tabar wajan. Laurat ta aje wuk'art hannunta tace

"Aike Ummy kakarki ta yanke sak'a, kinsan su masu kud'in nan wani lokacin mantawa suke da kud'i idan suka aje"

Ta juya ta kalli gabas da yanma ta waigo tana kallan Ummyn

"Karki dai manta dani, idan kin samu ina nan"

Dariya Ummy tayi ta mik'e tace

"Laurat kenan kinada matsala, barin dawo zamuyi magana"

Sama ta haura b'angaren d'akinsu Hajiya, d'akuna ne wajan guda shidda, biyun farko na Hajiya ne da Mabrookah, k'ugu ta rik'e tana kallan d'akunan, na kusada na Hajiyan ta hannun hagu ta saka keyn, murd'awa taitayi yakiyi ta zare tareda murd'a kofan d'akin, take ya bud'e tad'an tab'e baki ta tura ta shiga.

Wani sanyi neh da k'anshi ya dakan mata hanci, a hankali ta shiga tana b'in d'akin da kallo, sosai d'akin ya burgeta komai na d'akin blue hatta labulen d'akin blue neh, d'aga ido da zatayi ta hango mutum zaune kan wheell chair yana facing windown d'akin.

Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

Page 11

A rud'e tabar dak'in jikinta na rawa, bak'in k'ofan ta tsaya tana kallan cikin d'akin, har lokacin yana kallan windown bai juyo bah. Jim tayi wani zufa ya karyo mata, sad'af sad'af ta k'ara shiga d'akin jikinta na cigaba da rawa, ta zagaya gabanshi tana kallan fuskarsa.

Kyakyyawan saurayi ne wanda a k'alla zaikai shekara ashirin da biyar ko fi, fari ne daidai misali dan baya sahun bak'ake, kuma baza'a kirashi wankan tarwad'a bah dan yanada haske. Gashin kansa nada yawa mai tsayi yayi curl sai shek'i yake.

Saje ne kwance kan kyakyawar fuskrsa wanda ya k'ara masa kyau da kwarjini. Idanunsa yan madaidaita masu kyawun gaske, hancinsa ma ba dogo baneh sosai saidai yayi daidai cikin 'yar fuskarsa mai d'an tsayi. Bakinsa irin light red d'in nan neh madaidaici cikin fuskar tasa.

Lumshe ido Ummy tayi ta bud'e tana cigaba da kallanshi, har lokacin idanunshi na kallan windown ko kyaftawa baiyi ba balle yasan da mutum a wajan. Hannu tasa tad'anyi motsi wajan idanunsa anma ko gezau beyi bah, kurrri tamai gabanta na cigaba da fad'uwa anya wannan mutum nada rai kuwa.

Jim tad'anyi na wani lokaci sannan ta fita daga d'akin tana waiwayonsa. Sosai alamarinsa yabata mamaki, a sanyaye

3 / 32