Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
hankali, sun d'an tab'a hira sannan sukayi sallama. Kuka ta sake fashewa dashi na tausayin kanta kafin Jamal ya dawo.
A daran ranar Mifzal ya iso abujan, nan hotel d'in dasu Jamal suka sauka nan shima ya sauka. Washe gari dasafe dukansu suka shirya suka fita. Saida Mifzal ya fara reporting a Station d'in dayakai case d'in sannan suka wuce Wuse 2 dan a nan suka samu labarin Bilal d'in yake.
Daga bakin layin sukayi parking, Mifzal da Ram suka fito suka shiga cikin layin sosai suna takawa suna bin gidajen layin da kallo. Wani mai shago suka samu nan suka zauna kan benchn sa tare da masa sallama. Bayan ya amsa Ram ya mik'a masa dubu d'aya
"Bamu Fayrous guda biyu"
Jiki na rawa mai shagon ya mik'o musu dan yau kusan kwana biyu kenan babu ciniki, ya irgo chanji ya mik'a masa. Mifzal yayi saurin cewa
"Ka bashi, dan Allah mallam in tambayeka mana"
Jiki na rawa yace
"Allah yasa na sani"
"Dan Allah wani nake nema sunansa Bilal, abokina ne sosai saidai lambarsa ta b'ace a wayata. Kuma gashi tun daga Kano nazo nemasa"
Mutumin ya rik'e baki da Mamaki
"Wai! Kace kasha tafiya, sai dai ni bansan wani mai suna Bilal ba anan layin"
Mifzal ya d'au wayansa ya zak'ulo hoton Bilal d'in dake jikin Dp d'insa na whatsapp ya nuna masa
"Ka ganshi nan"
Baki mutumin ya bud'e
"Aa indai wannan ne ai na sanshi, yakanzo nan wayena yasayi sigari"
Ram da Mifzal suka kalli juna da mamaki. Ram ya wayance yace
"Tabbas kuwa shine, dan Allah bakasan gidan dayake bah"
Wani dank'ararren gidan chan gefensa ya nuna musu da hannu
"Ga gidan chan, saidai...."
Yayi saurin yin shiru ya matse bakinsa da hannu, Mifzal ya kallesa yace
"Fad'a abinda kakeso ka fad'a babu komae"
Ram ya ciro dubu uku ya aje masa ga wannan ka tab'a, aiko d'an fulani ya gyara zama
"Akwai abinda mu 'yan unguwan nan bamu gane masa bah"
"Na meh fah" cewar Ram
"Alhajin nan bashi fita sai da daddare, sannan kuma kullum sai kaga wasu murd'a murd'an mutane a k'ofar gidansa wanda mu bamu yarda dasu bah"
Mifzal ya jinjina kai,
"Kamar da wani lokaci sukafi zuwa?"
"Kaman tara haka zuwa goma na dare idan dai kazo nan zaka samesu"
Mifzal ya mik'e dasauri ya mik'a ma d'an fulanin hannu
"Mungode sosai"
Shima Ram ya mik'a masa hannun, d'an fulani ko sai godiya yake. A mota suka samu Jamal jingine da seat ya lumshe ido, jin motsinsu yasa ya bud'e ido ahankali.
Basu ce masa komai ba shima haka, suka shiga ya tada suka bar anguwan. Saida sukayi nisa sannan Mifzal ya soma masa bayanin yanda sukayi da Mai shago, mamaki ne a fuskansa sanda yaji Bilal nashan taba. Police station suka koma suka kai report d'in da kuma record d'in maganan su da d'an fulani.
Ummy kuwa irin jiya ce ta faru, aiki tayi tuk'uru duk ta galabaice ga wani ciwon ciki dake damunta. Yauma saida tayi aikin tas sannan ta wuce side d'insu tana tafiya da k'yar. Yauma kamar jiya saida suka d'anyi daru itada Jamal akan k'in d'aukan wayansa da batayi bah.
Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta.
Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Page 64 n 65
Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta, sosai, har k'arfe sha d'aya na safe bata tashi bah. Ran Aunty Faty idan yayi dubu ya b'aci. Da kanta ta shigo side d'in dan Mabrookah ta tafi makarantah. K'ofan d'akin ta banko ta shigo, k'udundune ta sameta kan gado tana rawar sanyi sosai. Duk da yanda take kad'uwa hakan bai hana Aunty Faty d'aka mata duka a k'afa ba. Ba shiri ta mik'e zaune dakyar, idanunta na wani lumshewa
"Uban me yau ya hanaki zuwa aiki"
Ta fad'a tana huci.
Cikin Kuka Ummyn tace
"Dan Allah kiyi hak'uri Wallahi banajin dad'i neh bazam iya aikin bah"
Wani duka Aunty Faty takai mata a baki har saida bakin ya fashe, ta dafe wajan tana kuka sosai
"Saboda bakida kunya, kin rik'a harni kike cema bazaki iya aikin bah. To wallahi nabaki nan da minti biyar in ganki a falon chan"
Fuuuu ta juya tabar d'akin tana sababi, wani marayan kuka Ummyn ta fashe dashi, ga wani irin sarawa da kanta keyi, dakyar ta iya mik'ewa ta fito ta nufi side d'in tana tafiya a hankali.
Aunty Faty na isa ta labarta ma Mami abinda ke faruwa sannan tace
"Bari tazo na bata ruwan nan, sai nace tasha magani dashi, indai tasha an gama. Haihuwa saidai taji anayi"
Karaf a kunnen Ummyn, tad'anyi jim a k'ofar falon sannan ta shiga da sallama, kini kini darai Mami tayi, ta tsugunna ta gaidata. Anma bata amsa bah.
Haurawa sama tasoma yi a hankali dan ta fara aikinta, Aunty Faty ta kwalla mata kira ta sauko da d'an sauri.
Bottle water ta mik'a mata da wani capsule tace tasha, saida tad'anyi jim sannan tace
"Ban karya bah"
"To idan kin karya sai kisha"
Cewar Aunty Fatyn, ajiyar zuciya tayi ta haura sama da maganin, zubar dashi tayi a toilet, ta saka maganin a WC tayi flushing.
Tana aikin jiri na d'ibanta, so uku tana fad'uwa saboda jiri. Haka tayi aikin dakyar tana kuka. A wahale ta dawo side d'insu ta fad'a kan gado tana kuka tare da kiran sunan Jamal.
A b'angaren su Jamal kuwa washe gari da daddare suka koma layin tare da rakiyar wasu daga cikin 'yan sanda anma bada uniform bah. Nan sukaga wad'an nan murd'a murd'an bak'akken mutanen da D'an fulani yayi maganansu. Suna nan b'obb'oye sukaga Alhajin da Bilal sun fito sun shiga motoci suma mutanen sun shiga suka bar anguwan a guje.
Binsu su Jamal suka somayi anma kamin kace me har sun b'ace musu. Haka suka koma hotel d'in da suka sauka kowa da abinda yake sak'awa a ransa.
Washe gari Tuesday, basu samu ganin Lawyern Abba ba sai da yanma, nan yake nuna alhininsa na rasuwar Abba dan baya k'asar tun lokacin.
Jamal ne ya tambayesa dangane da bashin da Alh Tijjani yake bin Abba, ba tare da b'ata lokaci ba Lawyern ya basa tabbacin akwai bashin.
Haka Jamal ya dawo jiki a sanyaye, Ram dake gefensa zaune yace
"Yanzu Jamal ya xa'ayi maganan Bashin nan"
Wani ajiyan zuciya ya sauke yace
"Nima kaina bansani bah Ram, i knw nothing akan dukiyar Abba. Kuma kaji shima Lawyern yace baisan komai bah"
Mifzal ya gyara zama yace
"To why not ka koma gida ka binciki D'akinsa, Myb ka samu wani abu da zaiyi guiding d'inka zuwa inda abubuwan nasa suke"
Jamal ya gyad'a kai alamar gamsuwa. Wuta ya hura yak'i bari su kwana, a ranar suka d'au hanyan Zaria saidai sun bar Mifzal anchan dan bai gama bincikensa bah.
Saida ya sauke Ram a kaduna sannan ya d'au hanyan zaria. Karfe goma da rabi ya isa gidan. Bai shiga side d'in Mami ba dan yasan sunyi Bacci, side d'insu ya wuce yasa keyn d'insa ya bud'e ya shiga. D'akinsa ya wuce kai tsaye yayi wanka ya sauya kayansa sannan ya shiga na Ummy.
Kwance ya sameta kud'undune cikin bargo tana rawar sanyi sai yamutsa fuska take. Ya hau kan gadon ya rungumota jikinsa a haka sukayi baccin.
Da asubah sosai tayi mamakin ganinsa, ya shafa gefen fuskanta yana binta da kallo
"Wife kinga yanda kika rame? Kin k'arayin ciwo neh"
Girgiza masa kai tayi alamar Aa idanunta cike da kwalla. Da taimakonsa tayi wanka ya gasa mata jikinta sosai sai kuka take dan jikin mata yayi tsami.
Da kanshi ya musu breakfast sukaci. Mabrookah na k'asa ta jiyo muryansa, da mamaki ta haura ta ganshi tsugunne a k'asa yana matsa mata k'afa sai dariya take masa.
Ran Mabrookah in yayi dubu ya b'aci, rai b'ace ta shiga falonsu Mami, kan dinning ta xauna tana turo baki
"Yaya dai" cewar Mami
"Ya Jamal ne ya dawo yana chan yare da wannan maiyar yana matsa mata k'afa"
"What!"cewar Mami
"Har Jamal ya dawo ya kasa zuwa ya gaishe ni? Lallai na yarda Ummy ta shanye min d'a"
Mabrookah ta sake zumb'ura baki tana kallan Aunty Faty
"Ni babban abinda ke damuna ma, Mummy kince in tasha ruwan nan da akasa magani cikin zai zube anma har yanzu naji shiru"
Aunty Faty ta gyara xama
"Nima abin na bani mamaki"
Sallaman Jamal da Ummy ne ya katse su, Mami ta sake had'a rai tare da amsa gaisuwan.
Zama yayi kamar kullun sannan ya gaida su, Ummy ta tsugunna ta gaishe su, babu wanda ya amsa mata, hakan sam baima Jamal dad'i bah. Abin da yafara tambaya shine
"Mami yau naji gidan shiru Ina Ma'aikatan neh bangansu bah"
"Na sallamesu" cewar Mami
Ya zaro ido da mamaki
"Saboda me Mami"
Ta sake b'ata fuska
"Saboda bamu da abinda zamu cigaba da rik'esu"
Bai sake cewa komai ba dan ransa ya b'aci sosai.
"Ka dawo baka iya zuwa ka duba halin danake ciki ba anma ka tafi wajan matarka"
Ya sassauta murya
"Kiyi hak'uri Mami ban dawo da wuri bah cikin dare ne kuma nasan kinji bacci"
Itadai Ummy kanta na k'asa. Aunty Faty ta daka mata tsawa
"Ke! Akuya tashi kiba Uwa da d'a wuri suyi magana"
Dasauri ta mik'e ta fita, Ja juya ransa b'ace wajan Aunty Fatyn
"Matata ba Akuya bace, karki k'ara kiran matata da wannan sunan"
Baki bud'e dukansu suke kallansa
"Jamal yayar tawa kake gayama irin wannan maganan"
"Mami kiyi hak'uri, duk abinda zaki kira matata zan jure anma banda ita"
Ta mik'e fuuuu yabar falon ya barsu tsaye kamar an dasasu dukansu baki bud'e.
Yana fita yabi Ummyn d'akinta, kan gado ya sameta kwance tana kuka a hankali. Janyota yayi jikinsa
"I'm very sorry wife, ki k'ara hak'uri kinji. Wata rana sai labari"
Kwacewa take k'okarin yi tana cigaba da kuka
"Ni na gaji ka kaini gidanmu, bazan zauna bah"
Dukansa ta somayi a k'irji, yayi saurin had'a bakinsu waje d'aya. Daina mutsu mutsun tayi cikin 'yan mintina ya rabata da kayan jikinta, ina ganin haka nayo waje na basu waje.
Soyaiya sosai Jamal ya nunama Wife d'insa a ranar, ita kanta ta k'ara tabbatar da Jamal mai k'aunarta neh. Yinin ranar suna mak'ale da juna. Bai fita ba sai bayan la'asar. Suna ganin ya fita Aunty Faty ta shigo ta mata kacha kacha harda Mari.
Kuka kam Ummy tayi har ta gode Allah. Koda ya dawo tambayan duniya babu wanda bai mata bah anma amsar d'aya cr bakomai. Ranar kwanan zazzab'i tayi sai kuka take jikinsa shiko yana aikin lallashi.
Washe gari da wuri ta tashi dan zazzab'in ya saketa, breakfast ta had'a masa mai rai da lafiya sannan tayi wanka ta shirya cikin Uniform d'in makaranta.
Tana gama shiri ya farka yana binta da kallo
"Wife"
Ya kira sunanta ahankali, ta juyo tana kallansa da murmushi.
Bud'e mata hannu yayi alamar tazo gareshi, dagudu ta k'arasa ta fad'a jikinsa ya rungumeta sosai kamar za'a kwace masa ita
"Wife keda bakida lafiya wani school zaki kuma"
Baki ta turo gaba
"Yau fa zamu fara exams kuma banasan nayi missing"
Yakai mata light kiss a lips d'inta
"Nidai da kin hak'ura kawai, banaso kije ki wahala ki kuma wahalar min da baby"
Turo baki tayi gama ta tureshi ta mik'e dasauri ta fita, wanka yayi ya fito ya sameta kan dinning, kamar kullum tare sukayi breakfast ya bata taci sosai sannan ta mik'e tana duba agogon hannunta
"Nayi latti"
Ta sak'ala jakan makarantar ta
"Pls Wife karkije, kinga fa baki da lafiya"
Kukan shagwab'a ta soma tana doka k'afanta a k'asa, dasauri ya mik'e ya rik'eta
"To naji a dawo lafiya kinji"
Kiss tamasa a baki ta sauka dasauri tana dariya, da murmushi ya dunga binta da kallo harta fita. Side d'in Mami ta shiga dan ta gaishe su, yauma kamar kullun zageta tas Aunty Faty tayi ta fito a sanyaye ta shiga mota driver yaja suka bar gidan.
Duk kewan Ummyn ne ya cika ransa, komawa d'akinsa yayi ya shirya ya fito, baiko lek'a side d'in Mami ba ya shiga motarsa ya fita.
Tafiya yake yana keta layukan cikin anguwan, daga nesa ya hango taron jama'a an kashe hanyar fita unguwan, waje ya samu yayi parking ya k'arasawa wajan, ganin motan gidansu yasa gabanshi ya fad'i.
Kukkutsawa yayi ya shiga cikin wajan sosai, driver ya gani kwance kansa na fitar da jini, ga Hijab d'in Ummy a k'asa da warin takalminta d'aya. Wani k'ara ya saki da k'arfi ya k'arasa inda Drivern ke kwance. Yana ganinsa cikin k'arfin Hali yace
"Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa"
*Ina Jiran Comment*
Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Page 66 n 67
"Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa"
Wani irin kuka ya saki, baisan sanda ya kamo kwalan Drivern ba yana jijigashi cikin kuka yace
"Ina suka kai min Ummy, waye ya d'auketa"
Sumewa Drivern yayi dan ba k'aramin jini ke fita daga kansa bah. Jiniyan 'yansanda ne ya cika wajan, mutanen dake zagaye da wajan suka bud'a hanya 'yan sandan suka k'arasa wajan motan.
Har lokacin Jamal na durk'ushe a wajan yana kuka sosai kamar k'aramin yaro. Ambulance ne suka d'au driver, wasu daga cikin yan sandan suka dunga d'aukan motan hoto harda Jamal d'in. Dakyar aka samu ya tashi daga wajan ya shiga motan 'yansandan har lokacin yana kuka hannayensa biyu akai.
```Waiwaye```
Ummy na shiga mota driver yaja suka bar gidan, hawaye ta soma na tausayin rayuwarta a gidan aure. Sunyi tafiya mai nisa dan daga gidan zuwa bakin anguwan akwai tazara, basu ankara ba wata bak'ar jeep tasha gabansu, ba shiri driver yaja burki ya tsaya yana salati.
Ummy ko k'walalo ido tayi tana kallan motan gabanta na fad'uwa, wasu mutane ne suka fito ciki, ba shiri ta saki k'ara dan ko tantama babu sune wad'anda suka kashe Abba. Numfashinta ne ya soma barazanar d'aukewa, suka bud'e motan wajan su hud'u dukansu da k'aton bindiga a hannunsu.
Ba shiri ta fashe da kuka tana kallansu tare da girgiza kai, d'aya daga cikinsu ya daka ma driver tsawa
"Kai! Fito daga motan nan"
Ba musu ya fito ko ina na jikinsa na rawa ya d'aga hannu sama, d'aya ya bud'e k'ofan baya inda Ummyn ke ciki ta sake sakin k'ara tana kuka. Fincikota yayi daga cikin motan har saida Hijabinta ya cire, ta soma turjewa tana cigaba da kuka kamar ranta zai fita.
Mutanen anguwa na lallab'e suna hango abinda ke faruwa saidai ba halin kawo d'auki saboda manya manyan bindigogin dake hannunsu.
Ganin tana neman b'ata musu lokaci yasa suka saka mata wani hankercief a hanci, ba b'ata lokaci ta tafi luuuu xata fad'i daya daga cikinsu ya d'auketa ya sakata a motan. Driver ya d'aura hannu aka ya matso tareda rik'e rigan d'aya daga cikinsu
"Ina zaku kaita, dan Allah k.."
Saukan kan bindigan dayaji a kansa ne ya hanasa k'arasa maganan dayake, so biyu mutumin na buga masa kan bindigan sannan ya wurgar dashi ya shiga mota suka bar wajan da wani matsiyacin gudu.
Tafiya kawai suke da gudu bako birki, har suka soma barin garin zaria.
****
Har suka isa Police station Jamal bai daina kuka bah, saima k'ara sautin kukan dayake kamar ana zugashi. Duk yanda 'yan sandan sukaso ya musu k'arin bayani kasawa yayi sai neman guri dayayi ya zauna a k'asa.
Haka suka kyallesa dan ya samu zuciyarsa ta sarara. Saida yayi mai isarsa sannan ya d'auko wayansa a aljihu ya soma neman layin Mifzal
Bugu d'aya ya d'auka, cikin wani irin murya yace
"Ya d'aukemin Ummyna, Ya d'aukemin ita"
A razane Mifzal yace
"Bangane ba, waya d'auketa."
"Anyi kidnapping Ummy da safen nan, pls Mifzal ka taimakeni, ciki ne da ita and ba lafiya gareta bah. Karsu cutarmin da ita pls"
Ya sake rushewa da wani kuka,
"Kana ina neh"
"Ina police station"
Dakyar ya masa kwatancen police station d'in dayake. Ganin zaman wajan bazai fishe shi ba yasa ya mik'e dakyar ya fita ya tari adaidaita sahu yahau.
A k'ofar gate ya sauka ya biya mai napeep d'in, kallo d'aya zaka masa ka gane hankalinsa a tashe yake matuk'a.
Kai tsaye side d'in Mami ya shiga, a falon k'asa ya sameta itada Aunty Faty suna hira. Wani kuka ne ya kub'uce masa suka d'ago a firgice suna kallansa. Jikin Mami ya fad'a ya sake fashewa da kuka, Hankalinta ne ya tashi ta d'ago kansa a rude
"Meke Faruwa Jamal! meya sameka"
Itama Aunty Faty ta sauko duk hankalinsu a tashe, Mami ta girgizasa idanunta cike da kwalla
"Jamal yimin magana mana, meke faruwa"
Dakyar cikin kuka yace
"Anyi kidnapping Ummy"
"What!" Mami ta fad'a da k'arfi tana kallansa
Aunty Faty tace
"Ba d'azu tazo mana sallama zata makaranta bah"
Kasa basu amsa yayi sai kuka yake da wani irin gunji, iya rud'ewa Mami da Aunty Faty sun rud'e dan ba k'aramin abu kesa Jamal kuka bah.
Suna nan cirko cirko suka ji k'aran bud'e gate, ba dad'ewa Mifzal ya shigo gidan cikin kakinsa na 'yansanda tare da wasu 'yansandan.
Jikinsa ne yayi sanyi ganin Jamal a wannan halin, durk'usawa yayi kusada Jamal ya d'ago kafad'arsa cike da tausayinsa
"Its All right Jamal, ka daina wannan kukan pls"
Jamal ya d'ago jajayen idanunsa ya zubasu kan Mifzal
"Na daina kuka fa kace Mifzal, kasan yanda Ummy take a cikin raina?"
Ya fashe da kuka ya cigaba da cewa
"Shes My everything Mifzal, ina santa fiye da kaina"
Ya kama hannun Mifzal d'in hawaye na gangara daga idonsa
"Pls ku taimakeni kada wani abu ya samu Ummy, wallahi ba lafiya gareta bah, shes 3month pregnant, Plss"
Duk da dauriya irin na Aunty Faty saida ta fashe da kuka na tausayin halin da Jamal d'in yake Ciki. Mifzal yace
"Insha Allahu zanyi iya k'okarina akan wannan case d'in, Komai zaizo k'arshe"
Ya mik'e zai bar falon, Jamal yayi saurin kamo hannunsa yana hawaye
"Plssss try ur best Mifzal, banasan wani abu ya sameta Pls"
Hawaye suka cika idanun Mifzal, cikin zuciyarsa ko mamakin irin san da abokin nasa kema Ummy yake.
Murmushin k'arfin hali Mifzal d'in ya masa yace
"Insha Allah"
Ya bar falon suka d'au mota suka bar gidan a guje. Falon kuwa Mami kuka, Aunty Faty kuka ga kuma uban gaiya Jamal. Kan kace me zazzab'i mai zafi ya rufesa har lokacin kansa na cinyar Mami, nan ta sake rud'ewa, Aunty Faty ta kira doctor yazo dan ya dubasa. Magunguna