Chapter 2 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 32

3K to 6K   out of 95.6K words

dake gefenshi tace


"Mama barin shiga wajan Inna Yanzu zan dawo" (gidansu Bilal)


"Tho a dawo lapia, karki dad'e"


Tho tace ta mik'e ta fita, a zauren gidansu Bilal ta had'u da kaninshi Bahar, Gaidashi tayi ya amsa yana cewa


"Ya kewar Yaya"


D'an murmushi tayi kanta k'asa
"Har yau bama samun wayansa, ina ga zanzo ne na bishi Abujan nan kawai dan jikina na bani ba lafiya"


"Yanzu idan kaje Abujan ta ina zaka fara? Ance. Tanada girma sosai, mezai hana muje inda suke aiki ko zamu samu labarin shi wajan abokanan aikinsu dake nan"


Gyad'a kai yayi


"Hakane kin kawo shawara"


"Barin shiga na gaida Inna sai na fito mu tafi"



A tare suka shiga gidan, Inna na zaune tsakar gida tana bakace masara


"Ummy ce da tsakar ranan nan"


A kunyace ta tsugunna ta gaida Innan,


"Ya Babanku da jiki?"


"Dasauk'i" tace a hankali har lokacin kanta k'asa. Sallaman da akayi ne ya katse su, wata dilaliya ce dake anguwan ta shigo tana cigaba da rafka sallama, Ummy da Inna suka amsa mata ta k'araso ta nemi guri ta zauna, Ummy ce ta soma
Gaidata sannan ta mik'e


"Inna bari muje wajan aikinsu Ya Bilal yanzu zamu dawo"


"Tho a dawo lapia" inna ta amsa mata, tana kok'arin fita daga gidan taji dilaliyan na cewa


"Wallahi Ladidi wasu gidaje ne aka kawo min cigiyan masu aiki kuma za'a samu alheri dan ba gidajen k'ananan mutane baneh gashi har yanzu ban samu yarinya ba"


Fita daga gidan tayi da sauri suka had'u da Bahar suka wuce wajan, mutanen dake wajan suka tambaya a nan suke shaida musu mummunan labari, d'ayansu ne yace


"Ranar da suka tafi motarsu tai hatsari duka sun rasu babu wanda ya fita, dan achan aka musu sallah saboda yanda gawawakinsu sukayi"



Ai bai k'arasa maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya..


Ummy Abduol✍🏻
[3/11, 11:36 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


​Page 5​

Ai bai k'arasa Maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya. A gigice Bahar yayi kanta yana kuka, jama'ar dake wajan sun tausaya sosai. Masu aikin wajan suka tsare musu napep suka saka Ummy dake sume a cikin napep d'in suka nufi gida.


Suna isa gida Mai napep da Bahar suka shi da Ummy cikin gida sai kuka yake, a nan yake sanar da Inna abinda ke faruwa, nan itama ta sume a wajan kamin kace me unguwan gaba d'aya ta d'auka ko wane lungu da sak'o sunji labarin rasuwar Bilal..

Sosai rasuwansa ya girgiza mutane saboda Bilal mutum ne mai Gaskiya da rik'on amana, ga addini da son jama'a. Ba abnda ke tashi daga gidan Inna sai koke koke, Baba da Mama suna daga cikin sukajiyo kuka daga gidan Inna, ta yafa mayafinta ta fito tun a kofar gida ta soma cin karo mutane sunata shiga, itama ba'a barta a baya ba tana shiga taji wannan mummunan labari.


Kuka ta soma ta k'arasa inda ze zaune ta rungumeta tareda fashewa da kuka


"Allah ya jik'anka Bilal yasa ka huta"

Ta k'ara rushewa da wani sabon kuka, Ummy ko dogon suma tayi bata farka ba sai washe gari da safe, a hankali ta bud'e idonta ta suka k'ankance Mama ta gani kusada Ita itama fuskanta ba walwala, mik'ewan datake k'okarin yi yasa Mama tasan ta farka


"Sannu Ummy, ina zakije"


Fashewa da kuka tayi tana kallan Mama


"Mama yanzu dagaske ne Ya Bilal ya rasu"


Kanta Mama ta shafa tana lallashinta


"Bilal lokaci yayi Ummy, yanzu addu'an mu yake nema ba kuka ba kinji. Kiyi hakuri ki fawala wa Allah"


Girgiza kai take tana kuka da k'arfi


"Aa Mama, Ya Bilal bai mutu ba ni nasani bazai tab'a mutuwa yabarni ba. Dan Allah Mama idan wasa yake kuce ya daina ya dawo"


Hawaye suka gangaro ma Mama na tausayin y'ar nata, dama tasan dole za'ayi haka, kuka sosai Ummy keyi tana k'okarin sauka daga kan gadon


"Mama d'an Allah ki sakeni zanje na nemo Ya Bilal ince ya dawo nida Inna muna kewarsa"


Rik'eta Mama tayi


"Haba Ummy kin tab'ajin anyi wasa da mutuwa?"


Baba ne ya shigo d'akin yana jejefa sandarsa yana laluban waje, saida ya laluba waji tabarma sannan ya zauna, inda yake jiyo kukan Ummy ya maida fuskanci yace


"Ummy Rayuwa da mutuwa duk ta Allah ce, Allah ya fimu sanshi shiyasa ya d'aukeshi. Kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. Kiyi hak'uri ki mik'a lamuranki ga Allah, muma duk zaman jiranta muke, shida ya rigamu baiyi sauri ba mu kuma da muka rage bamuyi jinkiri ba, kiyi hak'uri uwata Allah yana tare damu."


Duk'ar da kai kawai tayi tana kuka sosai, Haka suka cigaba da lallashinta anma sam Ummy tak'i daina kuka. Kullum sai ta shiga gidansu Bilal itada Mama, ba abinda take daga kuka sai kuka, Inna tayi tayi Ummy ta daina kuka anma ina. Cikin kwana biyu duk ta rame ta zafge kamar ba Ummy ba, sam ta daina cin abinci, Mama tayi fad'an harta gaji. Haka Inna itama tun tana binta da lallama harta soma fad'a anma Ummy taki.


Haka aka gama zaman makoki kowa ya watse ya bar gidajen biyu cikin kewa da damuwa. Idan kaga Ummy saika tausaya mata yanda ta koma lokaci guda, sosai abin ke damun Mama musamman yanzu yanda ta daina magana saidai ta kur'ama abu idanu tayita kallanshi kamar tab'abb'a..


​​Bayan Wata Shidda​​


Ummy tad'an sake kad'an bakaman da bah saidai yanzu ta koma shiru shiru batada yawan magana, har yanzu dai bata daina kukan Rashin Yayanta kuma masoyinta Bilal ba, Inna na tausayama Ummy sosai halinda take ciki. Yanzu Masa suka komayi da Safe da yanma kuma ba laifi suna d'an ciniki. Dashi suka dogara, duk riban da aka samu a rana dashi ake cin abinci a ranan. Bahar ko tuni ya koma yana a inda Ya Bilal yake aiki d'ah dan ya taimaki kanshi da Mahaifiyarshi..


Yau tun dare ciwon Baba ya tashi, Ummy nachan d'akinta tana bacci bayan ta gama kukanta wanda kullum sai tayishi kafin ta kwanta. A daddafe suka kai Asubah, Mama ce ta fara fitowa jin kiraye kirayen sallah, Kwankwasa kofan Ummy tayi itama ta fito



"Sannu Mama"


"Yauwa Sannu Ummy, jiya bamuyi bacci ba jikin Mallan"


Idanun Ummy ne ya ciko da k'walla


"Meya sameshi Mama?"


"Ciwon nan ne dai nashi ya tashi"


D'akin Ummy ta lek'a ta samu yana bacci, ajiyan zuciya ta sauke ta fito tayi alwala. Da gari yayi haske tana k'okarin fita da kayan sana'arta Jikin Baba yayi zafi sosai sai tari yake akai akai, d'akin ta shiga ta samu Mama kusa dashi tanamai sannu, Tari Mai K'arfi ya k'arayi saiga jini. Kuka Ummy ta saki ta d'aura hannayenta a kai



"jini kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun mun shiga uku"


Kamin kace me Baba ya fita hayyacin shi, Ummy da Mama ba abinda sukeyi sai kuka, da gudu Ummy ta fita ta samu mai napep suka d'au Baban suka sakashi sukai asibiti dashi..


Saida suka isa Mama tace


"Ummy yanzu da muka d'auko Mallan muka kawoshi Asibiti da wani kud'in zamu biya"


Hawaye ta share da bayan hannu

"Insha Allahu Mama zamu samu abinda zamu abinda zamu biya, mu fara bada y'an kud'in dake wajanmu"


An k'arbi Baba an bashi gado, kud'in hannunsu kwata kwata dubu d'aya ne da d'ari hud'u gashi sun kashe d'ari biyu wajan zuwa asibiti. Suna nan zaune aka likitan ya fito ya mik'ama Mama wata takarda


"Muna buk'atar wad'an nan magungunan yanzu kuyi sauri"


Kallan kallo suka tsaya yi da Ummy, jiki ba k'wari Ummy ta amsa takardan ta nufi pharmacy, Calculating aka musu kud'in dubu bakwai da d'ari biyar, ai nurse d'in bata gama fad'aba Ummy ta saki kuka mai k'arfi.


Wata hajiya ce ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajanta ta tsaya tana k'are mata kallo



Ummy Abduol✍🏻
[3/11, 11:38 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


​Page 6​


Wata hajiyace ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajan ta tsaya tana k'are mata kallo


"Y'an mata lapia dai wani naki ne ya rasu"


D'agowa tayi idanunt cikeda hawaye

"Aa Babana aka kwantar kuma bamuda kud'in da zamu biya na magani"


Takardan Hannun Ummy ta amsa ta duba sannan ta mik'ama nurse d'in


"Gashi ki basu magungunan, da kud'in gado na sati d'aya sai kiyi min total harda nawa"


Ummy najin haka ta tsugunna guiwa biyu tana godiya sosai, hannu biyu hajiyan tasa ta d'agota tana share mata hawaye


"Aa ki daina mini godiya, Allah ya bashi lapia"


"Ameen" tace tana cigaba da godiya kanta k'asa, nurse d'in ta miko mata magungunan ta tafi tana waiwayen hajiyan har ta bar pharmacyn. Bata b'oyema Mama ba ta sanar da ita duk yanda sukayi da hajiyan, Itama tayi godiya tareda ma hajiyan addu'oi na fatan alheri.


Cikin ikon Allah kwanan Baba shidda aka sallameshi, suka dawo gida bayan likita ya jajja musu kunne akan kula da maganin Baban da kula gudun abinda zai rink'a bata mai rai saboda ciwon zuciya dake damunshi..


Koda suka dawo gida d'aki Ummy ta shiga ta zauna tana tunanin ciwon Babanta, dole ta nemi kud'i dan cigaba da siyamai magani. Tana cikin tunanin Mama ta shigo d'akin da sallama, Ummy ta amsa tareda Gyara xama


"Ummy nazo ne muyi wata shawara dake"


"Shawaran meh kuma Mama"


Saida Mama ta nisa sannan tace

"Shekaranki Goma sha takwas yanzu ya kamata ache kin bar soye soye a k'ofar gida. Babban burina yanzu Ummy bai wuce ace kinyi aure bah anma nasan komai lokaci neh, fatana kawai Allah ya baki miji na gari"


Duk'ar da kai Ummy tayi tana murmushi


"Dama cewa nayi mai zai hana mu koma sana'a ta cikin gda"


"Tho Mama wace sana'a kike ganin zamu koma yi na cikin gda? Ni wallahi babban tashin hankalina ma magungunan Baba inda zamu rink'a samun dubu uku na magani"


Ajiyan zuciya Mama ta sauke

"Dama ni cewa nayi naga gidajen bayanmu suna neman masu wankau ko shi zamu koma yi ana kawo mana munayi ana biyan mu"


Jim Ummy tayi tana nazarin maganan Mama, sam batasan taga iyayenta sun wahala. Wankau aikine mai wahala tabbas kuma gashi Mama ta girma


"Tho Ummy mai kikace"


Maganan dilalliya ne ya fad'o mata a rai, wani lallausan murmushi ta sauke


"Kwanaki chan na tab'ajin dilalliya na cigiyan y'an aiki wai wasu sun bata sautun a sama musu, shine nace mai zai hana naje idan har yanzu ana nema sai nayi kuma na tabbatar za'a samu alheri"


Jim Mama tayi tana nazari


"Anya kuwa Ummy aikatau kuma?"


"Mama dan Allah karkice Aa, ki bari nayi wannan hanyan tamafi sauk'i kinga duk karshen wata mutun nada albashi"


"Banak'i bane Ummy ina tunanin Mallan neh"


Hannun Mama ta saka a nata

"Indai kin amince Mama shiknan ni nasan na Baba abu mai sauk'i neh"


"Shiknan Ummy Allah dai ya zab'a abinda yafi zama alheri, Allah kuma ya mana jagora"


"Ameen Mama"


A tare suka fito suka soma aiki gyaran gidan. Inna najin motsin su ta shiga ta k'ara gaida Baban dan dama taje ta gaidashi a asibiti.



Bayan kwana biyu Ummy ta tari Baba da maganan aikin da takeso ta fara, da farko yak'i yarda dakyar ta shawo kanshi ya yarda dakyar.


Nasiha ya mata sosai akan kare mutuncinta sannan ya bata izini taje gidan Dilalliyan ta tambayo, tana zuwa ko tace mata dama gida d'aya ya rage kuma har yanzu ba'asamu bah. Sosai Ummy taji dad'i sun aje akan washe gari zasuje ta kaita gidan.


Da farinciki ta dawo ta sanar dasu Mama sun mata fatan Alheri sosai da haka ta soma shirinta na gobe dan zuwa gidan babban fatanta Allah yasa kud'in da xa'a biyata yakai dubu uku dan tasamu na sayama Babanta Magani..



​This is just the Beginning​


Ummy Abduol✍🏻
[3/11, 11:40 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


​Page 7​


Babban fatanta Allah yasa kud'in da za'a biyata yakai dubu uku dan ta rik'a samu tana sayama babanta magani.

Washe gari da wuri ta tashi ta gama duk wani aikinta, tana shiryawa ta leka d'akin Baba tamai sallama ta fito, Addu'an nasara Mama ta mata sannan ta fita ta nufi gidan dilalliya.


Tana zuwa suka d'au hanyan samaru, itadai Ummy sai rarraba idanu take tana kallan hanya, a wajan aviation suka sauka wani anguwa da ake cema hanyin mallan, nan suka k'ara hawa mashin suka d'au hanyan cikin anguwan, gine gine na zamani masu kyawun gaske suketa wucewa har suka kawo wani had'adden gida gate d'in gidan k'ato ne ga tsayi sai shek'i yake. Dilalliya ta biya masu mashin sannnan ta soma kwankwasa gidan, bin gate din da kallo kawai Ummy keyi da sha'awa, wani ne ya bud'e karamin k'ofan ya leko yana wani yatsine fuska


"Lapia dai koh?"


Dilalliya aka washe baki

"Aa lapia lau, dan Allah iso za'a mana ace ma Hajiyar dilalliya ce"


Baice komai ba ya rufe k'ofan, suna nan tsaye aka k'ara bud'ewa nan ya basu izinin shigowa, suna shiga Ummy ta bud'e baki tana kallan gidan, dank'ararren gida ne na gani na fad'a, Main building d'in na tsakiya sai kuma wasu parts guda hud'u, biyu gefen hagu, biyu a dama. Sosai gidan ya burge Ummy musamman Swimming pole d'inda ta hango a chan gefe d'aya, sai kuma wani d'an garden daga gefensa d'an cage ne a ciki akwai kaya na wasan yara iri iri, ganin tana k'okarin fad'uwa Dilalliya ta rik'eta tana b'ata rai


"Wannan wanne irin kallo ne haka sai kinje kin fad'i kinjima kanki ciwo, keda a nan zaki cigaba da rayuwa"


Itadai Ummy batace komai bah har suka k'arasa falon, nan ma Ummy tasha kallo dan tunda take bata tab'a ganin gida mai tsaruwa irin wannan ba. Hajiyar suka hango zaune a falon tasa Laptop a gaba tana daddanawa hannunta rik'e da wani paper.


Dilalliya ta zauna kan carpet chan nesa da Hajiyar ta gaidata, batareda hajiyan ta kalleta ta amsa gaisuwan, Ummy itama ta gaidata har lokcin idanun Hajiyan nakan abinda takeyi.

"Dilalliya maike tafe dake"

Nan fa ta gyara zama ta soma magana cikin ladabi


"Hajiya dama akan maganan y'araikin da kikamin kwanaki neh, tho gashi na samo miki"


Kurrri tama Hajiyar tana jira taji mai zatace, saida tad'au minti Goma sannan ta d'ago tana duban Dilalliyar


"Ai na riga na samu, danaji shiru sai naba wata cigiya"


Ummy wacce kanta ke k'asa hawaye suka taru mata a ido ta d'ago da sauri tace


"Hajiya d'an Allah ki taimakeni ki d'aukeni, ina buk'atar aikin nan dan Allah Hajiya"


Ta k'are maganan da fashewa da kuka, Kallanta Hajiyan take bako kyaftawa


"Menene Sunanki?"


D'an dagowa tayi batareda ta kalli Hajiyar ba


"Sunana Jaleelah anma Ummy ake ce min"


"Ummy d'ago idanunki ki kalleni"


Bah musu ta d'ago suka had'a ido da Hajiyar, sai a sannan ta shaidata Hajiyar data taimaketa a asibiti rannan kan tayi magana Hajiyar ta rigata


"Ya jikin Mahaifinki?"


"Dasauk'i Hajiya mun gode"


Dilalliya sai kallansu take da mamaki


"Ummy dama kunsan juna neh"


Hajiyar tace

"Babu damuwa zan d'aukeki aiki Ummy, tun randa na fara ganinki naji kin kwanta min arai, ina miki kallon kamar y'a a wajena"



"Tho Tho Madallah Hajiya" cewar Dilalliya


"Zakiyi hak'uri da abinda zan rinka baki dan ba yawa dubu goma ne"


Ai a rud'e Ummy ta d'ago idanunta taf da hawaye


"Nagode Hajiya Allah ya saka da Alheri ya k'ara bud'i"


Ameen Hajiyar tace tana lumshe ido, Sosai taji dad'in addu'ar da Ummyn ta mata.


"Abu na gaba shine a nan zaki rink'a zama saida sabda lalluran mahaifinki zan rink'a sawak'e miki kina zuwa gida duk ranar Sati ki dawo lahadi"


Shiru Ummy tayi kanta k'asa

"Ke nake saurare" cewar Hajiya


"Amm da an bari sainayi shawara da iyayena tukun"


"Tho babu damuwa zaki iya zuwa"


Mik'ewa tayi ta haura sama chan ta sauko rik'e da wani envelop ta mik'ama Ummyn tana cewa


"Gashi nan idan sun amince sai ki bar musu gobe ki fara zuwa aiki"


Hannu biyu tasa ta karb'a tana godiya, Itama Dilalliyar an mata ihsani suka fito dukansu cikeda farinciki.


Tana zuwa ta zaiyanema Iyayen nata duk yanda sukayi sosai sukaji dad'i kuma suka bata goyon baya, Mama ta mik'ama envelop d'in ta bud'e, kudi ne dubu goma sha biyar, Baba yasa albarka haka Mama.


Kud'in ta amsa ta tafi kasuwa ta musu sayaiyan duk abinda suke buk'ata harda Inna tad'an mata siyaiya daga nan kuma ta saima Baba maganinsa ta dawo gida..
Albarka Su Mama suketa sa mata tanata murmushi cikeda jin dad'i, batasamu kaima Inna nata ba saida daddare a nan take fad'a mata aikin data samu itama tayi mata murna tareda Addu'a, a nan suka sha kukansu na tunawa da Bilal sannan Ummy ta dawo gida.


Daren ranan kuka Ummy tayi sosai rungume da hannunta wanda ta sanya zoben da Bilal ya bata. Addu'an Naiman rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarta tak'i aminta da cewa Bilal ya rasu..


Ummy Abduol✍🏻
[3/12, 8:22 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠


By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*



​Page 8​


Addu'an naiman Rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarya tak'i aminta da cewa Bilal ya Rasu.


Washe gari da wuri ta gama ayyukanta, Mama da kanta ta had'a mata kayanta a ghana must go k'arama, Ummy ko sai kukan rabuwa da iyayen nata take dan tunda take bata tab'a matsawa daga kusada Iyayenta na kwana

2 / 32