Chapter 12 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 32

33K to 36K   out of 95.6K words

gari kuwa ta saci hanya ta tafi. Ummy na zaune a tsakar gidansu tayi tagumi kamar a mafarki taji muryan sahibar tata. Mik'ewa tayi suka rungume juna a tare kuma suka fashe da kuka, saida sukayi mai isarsu sannan Ummy taja hannunta suka shiga Falo.

Mama suka samu a falon, Laurat ta gaisheta tareda mata gaisuwa, Ummy ta gabatar da Laurat a wajan Mama sannan suka shiga d'akin Ummyn.

Bayan Laurat taci tasha Ummy bata b'oye mata duk abinda ke faruwa bah, sosai Laurat ta tausaya mata, Ummy tace

"Gaskiya Laurat ina cikin tashin hankali, Wallahi bana san aurena da Ya Jamal, Ya Bilal nakeso"

Laurat ta gyara zama tace

"Duk da ban tab'a ganin Bilal d'in nan bah, kuma bansan halaiyarsa bah. Nidai haka nan hankalina yafi kwanciya da Jamal"

Ta dafa kafad'ar Ummyn tace

"Wallahi kun dace keda Jamal sosai"

Ummy tai saurin buge hannun Laurat d'in tace

"Wannan irin magana kikeyi Laurat, kema kina sahun masu san rabani da Ya Bilal kenan"

"Ba nufina kenan ba Ummy, abinda nakeso ki gane a nan shine. Babu abinda yazo zaki iyayi dangane ga maganar nan, karki manta. Yanzu haka kina a matsayin matar Jamal ne, tunda har an d'aura aure ba kuma abinda ya rage daya wuce kiyi hak'uri kima mijinki biyaiya"

Shiru Ummy tayi ta sake rushewa da kuka. Lallashinta Laurat ta soma dakyar ta samu tayi shiru sannan ta mata sallama itada Mama tabar gidan.

Tun daga ranan Innan Bilal ta soma gyaran 'yar nata kamar ba gobe, dan ita sam bata nuna kishi akan auran. Bilal ko abin duniya ne ya ishesa yau ciwo gobe Lafiya, haka Itama Ummyn. Ango Jamal kuwa tunda Haka ta faru tsakanin su da Bilal bai sake zuwa gidan ba duk da yanda zuciyarsa kesan ganin Gimbiyar tasa.

Abba ne da Mami sai Mabrookah dake gefe da kuma Jamal harda Aunty Faty dasu twins.

Gyaran murya Abba yayi sannan yace

"Kamar yanda kuka sani, yau saura sati d'aya d'aurin auren Jamal da Mabrookah, saidai akwai abinda baku sani ba wanda yau nakeso na warware muku"

Mami tace

"Menene kuma Alhaji"

Ya d'anyi murmushi yace

"Sati uku da suka wuce aka d'aura auren Jamal da Ummy"

Mami ta mik'e dasauri

"Ummy fah kace Alhaji"

"Kwarai da gaske ita"

"Haba Alhaji, ya zakayi mana haka yanzu ita Mabrookahn fah"

Nan da nan Mabrookah ta fashe da kuka, Jamal ko sai hararanta yake, ji yake kamar ya shak'eta ta mutu kowa ya huta.

"Bance miki ai baza'a d'aura da Mabrookah bah. Itama idan Allah ya kaimu sati mai zuwa za'a daura nata. Sannan inaso ku sani banasan tashin hankali ko k'ananan maganganu"

Mami ta zauna a sanyaye tana kallan Aunty Faty wacce keta hararan Mamin, ba'a gama magana ba Aunty Faty ta mik'e tabar falon tana huci.

Abba ya cigaba da cewa

"Kamar yanda kika zab'ar mai Mabrookah, haka nima na zab'a masa Ummy saboda na lura yarinya ce marainiya"

Twins sai dariya suke k'asa k'asa cikeda farinciki.

"Gobe a tara 'yan uwa da abokan arziki dan akai lefe gidansu Ummyn, kuma inaso ya zama rana d'aya za'ayi bikin dana Mabrookah"

Mami dai ba amsa sai huci datake yi cikeda bak'in ciki, sallaman su Jamal d'in yayi, Mabrookah ta mik'e tana kuka mai had'e da ihu ta haura sama, Twins ma suka mik'e suka bi bayan Jamal sunata mai Congrat.

"Fisabillahi yanzu Alhaji abinda kayi ya dace"

"Ni ko nasan ya dace"

"Gaskiya Alhaji bazai yuwu bah, a rasa wacce za'a daura ma Jamal sai b'arauniya"

"Ya Isa Maimuna! Ki shiga taitayinki, ya ina magana kina magana. Tho bari kiji, ba gudu baja da baya aure dai an d'aura, kuma kamar yanda na fad'a miki gobe za'a kai lefe gidan su Ummy, sannan set biyu za'a kai mana. Idan kuma kika sake naji wani magana ya taso zamu sabu sab'ani dake sosai"

Ya mik'e fuuuu yabar falon ranshi b'ace.

Haurawa Mami tayi zuwa d'akin Jamal, batareda wani b'ata lokaci ba ta d'auke shi da mari

"Ni! Ni Jamal kakeso ka wulak'anta?"

Ta rushe da kuka

"Ba laifinka baneh"

Ta bar d'akin dasauri, kuka shima Jamal d'in ya fashe dashi, shi yanzu ina zaisa ranshi, ga Ummy bata sanshi, Ga Mami na fushi dashi, ga kuma auren Mabrookah da aka tilasta masa akai.

Ranar Aunty Faty da Mami kacha kacha sukayi, washe gari kamar yanda Abba ya umarta, set biyu na akwati aka d'auka aka barma Mabrookah d'aya, gidan su Ummyn aka kai, Mama tace akai gidansu Innan Bilal, nan Inna tayi kiran Mak'ota aka amsa kayan cikeda farinciki.

Tunda Ummy taji shigowan masu kawo lefen ta fashe da kuka, shikenan tasan aikin gama ya gama an rabata da Ya Bilal d'inta.

A ranar Ramadhan ya diro Zaria, shi kad'ai yazo gidansu Ummyn ya kawo mata kud'in d'inki, dubu hamsin wanda Abba ya bada a kawo. Saida ya dinga had'ata da Allah sannan ta amsa tareda waya k'irar Samsung da Jamal d'in ya bada a kawo mata.

Duk abinda sukeyi Bilal na hango su wanda yake bak'in k'ofar gida, ranshi ya b'aci sosai. Ramadhan d'in na tafiya ta juyo tayi hanyar gida, had'a ido tayi dashi gabanta ya fad'i, baice mata komai ba yayi shige wanshi gida.

A sanyaye ta nufi gida, Mama ta nuna ma kud'in da wayan, tasa albarka sannan tace takaima Inna dan itace mai shirye shiryen. Bata samu ta kaiba sai washe gari, Nan take Inna ta d'au kaya kala goma ta saka a leda ita da kanta takai Ummyn wajan masu d'inki dan tasan idan tace ita kad'ai taje bazata bah.


Tun daga ranar Ummy bata sake ganin Bilal bah, ko ta shiga gidan bata ganinsa. Bahar ta tambaya a nan yake fad'a mata ya tafi abuja wajan Alhajin daya zauna wajansa. Wani k'walla ne ya gangaro mata tasa bayan hannu ta share.

Yau saura kwana hud'u biki, Laurat dakyar ta samu Mami ta barta ta tafi hutu kan cewa marik'iyrata batada lafiya. Tana tafiya tayo gidansu Ummy dan tayata shirye shirye. Sosai Ummy tayi Farinciki da zuwanta.

Wayan da Ramadhan ya kawo mata ta nuna mata, Laurat ta kyalkyale da dariya tana cewa

"Hala ma ko kunnata baki iya bah"
Harara Ummy ta wurga mata

"Ni ina ruwana ma da wayar"

Dariya Laurat tayi ta kunna mata wayan, text ne ya shigo ta bud'e tana cewa

"Ashe ma akwai Sim a ciki, har an turo miki message"

"Ni ina na iya wani karatu balle na karanta" ta k'are maganan tareda turo baki

"To bari na karanta miki"

Ta gyara zama tana kallan Laurat

"Salam! Ina fata gimbiyar tawa tana cikin k'oshin lafiya. Duk da nasan Gimbiyar tawa bana gabanta, anma inaso tasan wani abu guda d'aya..."

Ummy ta ja dogon tsaki

"Dallah ki bari banason ji"

"Haba Ummy bakyau wulak'anta d'an adam, ai sai ki tsaya ki gama sauraran abinda ya rubuto koh"

Ta sake turo baki tace

"Ina jinki"

"Ina sanki Fiyeda yanda nake san kaina, Ina matuk'ar k'aunar ki. Dan Allah ki bani dama na shigo rayuwarki dan na jiyar dake farinciki da annashuwa na rayuwa. ke Alheri ce a rayuwata Ummy! Ke Alheri ce a tare dani. Ina san mu kasance tare koda kuwa zaki rink'a..."


"Kai! Nifa na gaji da sauraran ki"

Ta mik'e tana cewa

"Muje wajan Inna dan tace na dawo d'an anjima"

Laurat ta saki Murmushi ta mik'e suka tafi gidan Innan.

Ana saura kwana uku 'yan Uwan Baba dana Mama suka sake dawowa biki, kan kace me gidan ya cika sosai da mutanen k'auye. Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna.

_dan jin yanda bikin Jamaludeen da Jaleelah da kuma Mabrookah zai kasance sai ku bini a page na gaba_

```Zaku min afuwan jina shiru kwana biyu, hakan ya faru bisa rashin Lafiyan danake D'an fama dashi. Sai ku sakani a addu'a```

Ummy Abduol✍🏻

♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

_Naga sak'on Addu'an ku da dama, ina godiya Allah ya saka da Alkhairi_ ```Maman Ahmad, Ayoush Gidos, Maman Abba, Tintima Shuwa and all My Fans Grp``` Ina godiya

Page 34

Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna.

Bahar na zaune a cikin gida yana waya suka shigo, Inna dake tsakar gida tace

"Maraba da Amarya"

Ummy ta turo baki tana gungunai, ta nemi guri kusada Innan ta zauna

"Ni fa bah amarya bace"

"Ke ko kike amarya Ummy, ni abinda ma ke damuna wannan Raman da kikayi a haka za'ayi bikin"

Laurat tace

"Nima dai haka nace"

Dai dai lokacin Bahar ya gama wayan da yake yana cewa

"Innan mu Ya Bilal ne yace na gaishe ki"

"Aa to madallah ina amsa wah"

Idanun Ummy suka cika da hawaye, Bahar dake gefe yace

"Amarya kinsha k'anshi, d'azu nake ganin katin Programs d'in bikin hannun wani abokina. Allah ya sanya alkhairi"

Batace mai komai ba sai ma kauda kai datayi gefe. Bahar ya mik'e ya fita, tana ganin haka ta mik'e dasauri tabi bayanshi

"Bahar dan Allah numbern Ya Bilal zaka bani"

Ba musu ya bata numbern ta dawo gida cikeda farinciki. Da yanma suna zaune itada Laurat wayan da Ramadhan ya bata ya hau ruri, Laurat ta d'au wayan tana cewa number ce.

"Tho ni ai ko d'aukan kiran ban iya bah"

Dariya Laurat ta mata ta nuna mata yanda ake d'auka, karawa a kunne tayi Muryan Jamal ya daki dodon kunnenta

"Salam Amarya tah"

Sunan da ya kirata dashi sosai taji dad'in shi ta d'anyi murmushi tabace komai bah

"I know kina jina kodai saina sayi muryan neh"

Nan ma shirun ta sakeyi, ya d'an sassauta murya yace

"Kiyi hak'uri muna k'ofar gida nida Abokai na, pls badan niba ki fito"

Ta yanke kiran tana kallan Laurat tana turo baki

"Wai Ya Jamal ne da abokansa a k'ofar gida"

Laurat ta mik'e dasauri tana gyara gyalen kanta, tashi to muje Myb zasu mana magana ne akan abinda zamuyi.

Ummy tayi turus alamar bazata mik'e bah, Inna dake tsakar gida tace

"Wai Ummy baji nayi kince Jamalu na k'ofar gida bah"

Turo baki ta sakeyi ta mik'e tasa hijab suka fito tana turo baki, su Biyar ne jingine jikin motar. Kallo d'aya ta musu ta d'ukar dakai, ji tayi tana jin nauyinsu. Laurat ta d'an tab'ata murya chan k'asa tace

"Dan Allah kar dai ki dizga shi a gabansu"

Hannun Laurat ta rik'e suka k'araso wajan, kunyan su Ummyn keji sosai ta b'oye bayan Laurat tana Murmushi. Laurat tace

"Sannunku da zuwa ina yinin ku"

Karaf Ramadhan yace

"Lah! Abin kunya, ki ma daina jin kunyan wad'an nan"

Ya nuna sauran abokanan yana cewa

"Wad'an nan da kike gani duk shaki yayi neh"

D'aya daga cikinsu mai suna Mifzal yace

"Lallai Ram kaci abinci, anma ba komai zamu rama"

Suka sake kwashewa da dariya, shidai Jamal na gefe sai kallan Gimbiyar tasa yake yana murmushi. Dakyar Ummy ta iya cewa

"Ina yinin ku"

d'aya daga cikinsu yace

"Oh ashe ba haka nan kawai baneh take mana rowan muryan nata"

"Kai wai ya haka, kuyi abinda ya kawo ku dallah mu tafi" cewar Jamal yana hararansu

Mifzal yace

"Ni ban tab'a ganin Ango ma mara kunya irinka bah, waya cema ango na biyo abokai wajan k'awaye"

Harara Jamal ya sake wurga mai, Laurat da Ummy dariya suke musu k'asa k'asa

Taseem yace

"Ni fah tarko na ne ma ya kama kurciya a nan wajan Wallahi"

Ram ya had'e rai yace

"Kai lets be serious"

Mifzal yace

"Saidai bamu san sunan Malaman bah"

Laura tace

"Sunana Laurat"

"Woaw nice name" cewar Taseem yana gyad'a kai

Ram yace

"Dame dame kuke buk'ata wajan hidimar bikin naku"

"Kawai walima zamuyi shikenan"

Taseem yace

"Tho kamar nawa kuke b'ukata"

Laurat ta sake cewa

"Duk abinda Allah ya hore muku babu matsala"

Take Taseem yasa hannu a aljihu ya ciro bandir d'in yan d'ari biyar ya mik'a mata. Ansa tayi ta musu godiya, itadai Ummy har lokacin tana bayan Laurat dan kasa had'a ido tayi dasu.

Takowa Jamal ya soma yi har zuwa bayan Laurat, ya kamo hannun Ummy batareda yace komai ba ya kalli su Mifzal yace

"Idan kun gama ku fad'a mana"

Ganin tana k'okarin turje masa yasa ya d'auketa chak ya sakata a seat d'in bayan motan Ram shima ya shiga suka kulle ya kulle k'ofan.

Baki bud'e su Ram suka bisu da ido. Taseem ya dawo kusada Laurat ya tsaya suna hira. Ram ya sake had'e rai ya matsa chan gefe yana waya fuska a had'e.

Ummy ko ido ta zaro tana kallansa

"Dan Allah ka bud'emin na fita"

Ya janyota jikinshi yana y'ar murmushi

"Wai mena miki ne Yasa baki sona"

Ta turo baki tana tureshi daga jikinta. D'an dariya yayi k'asa k'asa yana kallanta

"Why are uh pretending, ni nasani kina sona. C'ommon ki daina, I love uh so much and i know uh love me too"

Ta turesa da k'arfi tana kokarin bud'e kofan, hannunta yayi saurin rik'ewa ya d'aura mata katuna a hannu yace

"Ga katu nan ki da zaki raba"

Ya d'auko wani k'atan leda ya d'aura kan cinyanta tace

"Gobe akwai Dinner, inaso kisa d'aya daga cikinsu. Jibi kuma akwai Kamu. Zamu zo nida abokaina mu d'auke ki"

Batace komai ba sai bin ledan datake da kallo. Kwankwasa windown motan aka soma, Ya rik'o hannunta tareda yin kissing d'inshi a hankali, zame hannunta tayi dasauri tana turo baki

"I love uh my pearl"

Saurin bud'e kofan tayi ta fito rik'e da ledan da katunan, dakyar ta iya sallama da abokan nasa suka shige gidan Inna. Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai.

_manage it_

Ummy Abduol✍🏻

[3/12, 9:44 PM] ‪+234 903 823 4806‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠
♠♠♠♠
*JAMALUDEEN*
♠♠♠♠
♠♠♠♠♠♠♠♠

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*


Page 35

Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai. Harara yaketa wurga ma Taseem har suka bar wajan.

Ummy na shiga zauren gidansu Inna ta mik'a ma Laurat kedan tana cewa

"Wai kayan dinner da ko menene oho"

Amsa Laurat d'in tayi suka k'arasa cikin gidan, Inna ta mik'ama kayan sannan suka bud'e, Gowns ne guda biyu, d'aya Red mai touch d'in yellow, sai Head Bak'i, d'inkin sosai yayi kyau Laurat sai yaba kayan take.

Da zumud'i ta d'aga d'ayan gown d'in, shi kuma bak'i neh da Farin Head, sai rafan y'an dubu guda biyu daya fad'o. Inna ta d'auka baki bud'e

"Wannan kud'in fah!"

"Ina tunanin na manni neh" cewar Laurat

Itadai Ummy ko uhumm batace bah saima kauda kai gefe datayi tana kallan kayan ta gefen ido, dan itama sun burgeta sosai.

A chan b'angaren Amarya Mabrookah kuwa, shirye shirye ake duk da dukansu babu wanda ransa ke cikin dad'i na maganan Auran Ummy. Bak'i ne cike a gidan daga b'angaren Mami da kuma Abba, itama Aunty Fatyn nata tawagar duk a nan suka yada zango. Su Aunty Zainab duk sun iso, itadai sam batajin dad'in zaman da Aunty Fatyn keyi a gidan Mami, tadaiyi shiru ne dan tasan idan tayi magana zasu iya rabuwa baran baran dan ba hak'uri Aunty Fatyn keda shi bah.

Da daddaran ranar Najma da Najwa suka samu Aunty Zainab Umminsu a d'aki, zama sukayi Najma ta soma rok'onta akan ta barsu suje Gidansu Ummy suyi nasu shagalin. Da mamaji Aunty Zainab tace

"In banda shashanci irin naku, yaushe ake barin sha'anin gida a tafi na bare"

Najwa tace

"Ummi kinga fah mu itace k'awarmu, kuma Aunty Mabrookah ba kulamu takeyi bah"

Nan suka kwashe duk abinda ya faru lokacin da ta tafi suka sanar da ita. Sosai ta tausaya ma Ummyn

"Idan na barku kuka tafi zan jama kaina surutu neh, kuyi hak'uri kawai ku zauna nan"

Ga mamakinta sai gani tayi sun fashe da kuka, binsu da ido take tayi da mamaki. Ajiyan zuciya ta sauke sannan tace

"Shikenan kuje, anma dan Allah ku kiyaye"

Rungumeta sukayi a tare har saida suka fad'a kan gadon datake zaune, duka ta d'aka musu

"Tho ku k'arsani ku huta"

Suka mik'e suna dariya suka nufi d'akinsu, kaya suka loda suka fito tareda ma Ummin nasu sallama. Ram suka samu ya kaisu lokacin anata kiraye kirayen sallan Magriba, dan dama shima Abba ya aikeshi gidan wajan kawun nan Ummy.

A mota Ram ke cewa

"D'azu muka dawo daga gidan, sun ce wallima kawai zasuyi"

Najma tace

"To Ya Ramadhan nawa kuka basu"

"50k" yace a takaice

"Haba Ya Ramadhan, 50k mai zeyi wallahi yayi kad'an."

Murmushi yayi yasa hannu a aljihu ya ciro wani rafan yan d'ari biyar ya mik'a musu

"Wannan fah"

Najwa tace

"Eh to za'ayi managi"

Da mamaki ya d'an kuyo ya kalleta

"Lallai ma yaran nan"

Suka kwashe da dariya daidai lokacin da suka k'arasa gidan.

Dasauri suka fito suka shige cikin gidansu Ummyn, a cike suka samu gidan, dakyar suka iya lalubo Mama, bayan sun gaisa take fad'a musu tana chan mak'ota.

Rige rigen shiga suka soma yi gidan Inna, Ummy dake zaune tsakar gidan kan kujeran tsuguno zatayi alwala ta mik'e cikeda farinciki ta rungumosu tana dariya.

Laurat da Inna suka fito suka musu sannu da zuwa.

Sosai Ummy taji dad'i da suka fad'a mata nan zasu zauna ayi biki.

Inna ma tayi farincikin zuwansu musamman data lura yaran wayaiyu ne kuma sunada tarbiya.

Dakyar suka matsa ma Ummy a daran suka kakkai ma k'awayenta dake layin kati, da kuma maza wad'anda suke abin arziki lokacin da take saida Awara. Laurat ta d'iba taba Bahar dan ya rabama nasa abokanan da kuma 'yan uwa da abokan arziki.

Ranar da daddare Ummy ta k'uduri niyan kiran Bilal dan suyi shawaran abinda za'ayi, dan yace mata kada ta k'ara nuna ma kowa bata san auren.

Bayan kowa yayi bacci ta lalubo numbern Bilal d'in ta danna kamar yanda Laurat ta koya mata. Ringing biyu ya d'auka, sallama ta masa ya amsa a dak'ile

"Ina yini Ya Bilal"

"Lafiya lau ya shirye shiryen biki"

Ta d'anyi Jim batace komai bah

"Na lura duk fad'in sanda kike min k'arya neh. Har yana kawo miki kati kuna rabawa."

"Wallahi ba haka baneh Ya Bilal ni..."

Yayi saurin katseta da cewa

"Ba abinda zaki fad'amin Ummy! Nagode da yaurada ta da kikayi"

"Dan Allah ya Bilal kayi hak'uri, wallahi ina sanka karka min haka"

"Inda kina sona da baki kai har yau da auransa a kanki bah. Nayi dana sanin baki amanar zuciyata Hrt, ashe bazaki iya amanar da kika d'aukan min bah"

Kuka ta fashe dashi ta k'ara rik'e wayan sosai a kunnenta. Shima kukan yake a hankali

"Bazan tab'a rayuwa bake bah. Sai na nuna ma Jamaludeen kuskurensa na san abinda nakeso"

Kan tayi

12 / 32