Chapter 30 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 32

87K to 90K   out of 95.6K words

a falon k'asa tayi kicibus da Mabrookahn tana jiranta

"Kwad'ayaiya, nasan dai duk abinda kikeyi nan na kwad'ayi ne dan kinga suna dashi, An saba da maula"

Ran Ummy ya sosu ta wuce zata haura sama ta sake jiyota tana cewa

"In ma so kike ki mallake su karyanki tasha k'arya, Uwa ta saba da bin bokaye dole 'ya ma tad'au hanya. Wayasan abinda aka kitsa miki da kikaje gidan ranan"

Ran Ummy idan yayi dubu ya b'aci, ta sauko k'asan

"Kullum kina zagina ban tab'a maida miki da martani bah, dan har yanzu ina miki kallan wadda ta girme mani, ko ba komai kin fini shekaru bazanyi musu dake bah. Anma yau kin kaini bango"

Wani shewa Mabrookah ta saki tana cewa

"In kinama Allah kada ki k'ara ganin girman nawa"

Murmushin takaici Ummyn tayi tana cewa

"Kiyi ta zagina daga nan har abada anma karki k'ara zagin iyayena dan basu miki komai bah"


Bata ankara bah taji saukan Mari a kuncinta, ta dafe wajan dasauri tana kallan Mabrookahn

"Kika mareni"

Tana huci tace

"An mareki ko zaki rama neh, shegiya 'yar masu bin bokaye"

Mari Ummyn ta d'auke Mabrookahn dashi mai rai da lafiya, nan fa fad'a ya kaure tsakaninsu, kokawa suka shiga yi tsakaninsu dai dai lokacin Jamal ya shigo cikin gidan, kamar zai shiga side d'in Abba sai kuma ya nufi nasa, yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake Falonta ta bugama Ummyn a......


Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Page 90

_*A Gurguje*_

Yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake falonta ta bugama Ummyn akai, Wani k'ara ta saki take ta fad'i wajan a sume jini na fita a kanta.

Jiki na rawa ya k'arasa falon gaba d'aya jikinsa rawa yake, tsugunawa yayi inda Ummy ke wance ya d'agota hawaye cike da idanunsa, d'agowa yayi yana wani irin huci yana kallan Mabrookah wace ya yarda Speakern itama jikinta na rawa tana kuka.

A fusace ya mik'e ta juya zata gudu ya kamota ya soma had'ata da bango yana kuka, ihu take a wahale tana neman agaji, Ammi da Areefah ne sukaji yo ihun Ummy da farko, har Areefahn ta mik'e Ammi ta hanata, jin wani ihun yasa suka mik'e a tare sukayo side d'in.

Suna shiga ya sake bugata da bango ta saki k'ara take itama kanta ya fashe. Ammi ta k'arasa dasauri inda suke tsaye ta rik'esa gaba d'aya ta rud'e

"Jamaludeen karka kasheta, stop! Control your anger"

Ya jefar da ita tare da nunta da yatsa

"Na sakeki! Na sakeki!!"

Harya bud'e baki da niyar furta wani abu Ammi ta d'aukesa da wani gigitacen Mari

"A gabana Jamaludeen!"

Baice komai ba sai hucin dayake, Areefah ko tunda ta shigo ta fashe da kuka ganin Ummy kwance cikin jini, inda take ta k'arasa ta tsugunna tana kuka. Jikinsa na rawa ya d'au Ummyn yayi waje da ita, ko takalmi babu a k'afan Areefah tabi bayansa, mota ya sakata ya ja da k'arfi bayan Areefah ta shiga suka bar gidan.

Fitowansa yayi daidai da fitowan Abba da Areef daga masallaci, da ido sukabi motan ganin yanda yake gudu kamar wanda zai tashi sama. Suna shiga Ammi ta fito daga side d'in rik'e da Mabrookah wacce itama kanta ke jinin

"Subhanallahi meya faru?"

Cewar Abba yana k'arasawa wajan, Ammi bata b'oye masa komai akan abinda ta gani bah, sam Abbah baiji dad'in abinda ya faru bah. Areef yana daga gefe yana cin magani yanata ma Mabrookahn Allah ya k'ara a zuciya dan dama kwata kwata bata burgesa.

Wani Private hospital mafi kusa Jamal yakaita, duk tabi ya rude in banda hawaye babu abinda yake haka Areefah dake gefensa sai kuka take itama, suna isa aka amsheta sukayi Emergency da ita, Wata nurse ta umarce shi daya je ya biya kud'in kati da sauransu, ba musu ya nufi receiption Areefah na biye dashi. Suna nan zaune wata nurse ta fito daga d'akin, Areefah tayi saurin mik'ewa tasha gabanta

"Dan Allah ya jikin nata?"

Nurse d'in ta mata murmushi

"Dasauk'i karku damu"

Bata jira cewar Areefan ba tabar wajan dasauri, suna nan tsaye likitan ya fito, Bayani yama Jamal d'in akan abin bai yi serious ba saidai su kiyaye nan gaba. Sannan ya basu umarnin shiga su ganta.

Kwance suka sameta kan gado kanta nan nad'e da bandage tana bacci hankali kwance, wani nannauyan ajiyan zuciya Jamal ya sauke ya k'arasa bakin gadon, Areefah ta rik'e hannunta hawaye cike a idonta

"Allah zai saka miki Aunty, kuwa wallahi..."

Taji k'wafa ranta b'ace. Shidai Jamal bai iya cewa komai bah. Suna nan Abba ya kira wayan Jamal yana tambayansa mai jiki, halinda ake ciki ya fad'ama Abban sai a lokacin suma hankalinsu ya kwanta.

A gida kuwa Ran Ammi ya b'aci sosai gaba d'aya ji tayi Mabrookah ta fitar mata a rai, babban damuwarta bai wuce cikin dataga alamar Ummyn nadashi bah. Buris tayi da Mabrookahn haka shima Areef ji yake kamar ya rufeta da duka. Dad'in ta d'aya ma dayaji Ammi tace Jamal ya saketa.

Rashin sani gari yasa Abba had'a Mai gadi d'aya da Areef da ita Mabrookahn aka kaita wani Chemist nan kusa akayi mata treating kan. Koda Jamal ya fad'ama Abban halin da Ummyn ke ciki kasa sukuni Ammi tayi, kwatance tasa ya musu Areef ya d'aukesu itada Abba sukaje asibitin. Ammi har hawaye tayi ganin Ummy kwance a kan gado, Kwana biyun nan da sukayi sosai ta shiga ranta.

Ta share hawayen fuskanta tana kallan Abba

"A gaskiya Alhaji zaman Jaleelah da Yarinyan nan Mabrookah bazai yuwu bah"

"Wani irin magana kike haka Hajiya, karki manta fah matarsa neh bamu isa mu rabasa ta itaba"

Shidai Jamal baice komai saboda b'acin rai, ji yake kamar ya kashe Mabrookah ya huta, hannayensa ya saka a aljihu tare da sakin huci mai zafi.

Areefah ta zumb'uro baki

"Ai wallahi bazan yarda bah, wallahi ta k'ara maimaita makamancin haka dukan tsiya zan mata"

Ran Abba ya b'aci, ya daka ma Areefah tsawa abinda bai tab'a yi bah

"Karna k'ara ji"

Ta sake shagwab'e fuska ta kauda kai. Suna nan har ta farka daga baccin, sunata mata sannu har abin ya bata kunya ganin harda Abba a wajan da kuma yanda gaba d'aya suka nuna damuwarsu a kanta.

Ba kunya Jamal ya zauna kusa da ita ya d'an rab'ata da jikinsa sai k'okarin k'wacewa take ta kasa, shiko gogan ko a jikinsa.

Ammi na ganin haka ta mik'e daga kan kujeran datake,

"To bari muje gida mudai"

Ummy najin haka ta tura baki tana kallan Jamal

"Nifa ba inda kemin ciwo dan Allah a sallameni"

Bai iya mata musu ba ya mik'e yace ma su Ammi yana zuwa, wajan likitan yaje ya rok'esa ya sallamesu, X-ray aka rubuta musu da kuwa wasu magunguna sannan yace su bari drip d'in dake jikinta ya k'are.

Godiya yayi ya koma, yana zuwa ya samu su Ammi sun wuce sai Areefah dake d'akin tanata ma Ummyn hira itako sai dariya take cike da nishad'i, Yanda ta damu da Wife d'insa yasa ta sake samun gurbi a zuciyarsa, ya k'araso ya shaida musu yanda sukayi da likitan.

A b'angaren Mabrookah kuwa tana ganin su Ammi sun fita ta fashe da wani matsanancin kuka, sai lokacin kalmar Jamal dayake anbata mata kalmar saki ya dawo mata k'wakwalwarta. Ta sake rushewa da kuka, chan kuma ta mik'e kamar wacce aka tsikara, ta goge hawayenta ta nufi bedroom d'inta dasauri.

Drip d'in na k'arewa aka sallamesu suka dawo gida, Ammi dake falon tana jiransu tana jin shigowan motan ta fito dasauri ta rungume Ummyn tana mata sannu, Hannunta ta kama tana cewa

"Banasan wani tashin tashina, zo muje d'akina"

Jamal ya turo baki gama harda doka k'afa d'aya a k'asa sam ba haka yaso bah, Areefah dake kallansa ta kyalkkyale da dariya ya galla mata harara, ciki sukayi yana binsu a baya har lokacin bai maida bakin bah.

Ganin sun haura sama yasa ya zauna a falo yana cika yana batsewa, Kan gado Ammi ta zaunar da ita tana cigaba da mata sannu

"Kiyi Hak'uri Jaleelah kinji"

Murmushi kawai tayi ta duk'ar dakai k'asa, Ammi ta shiga toilet ta had'a mata ruwa mai d'an zafi ta umarceta taje tayi wanka. Cikin daran nan nan nan da Ummyn Ammi ta dunga yi sai dataga tayi bacci hankalinta ya kwanta.

Tana saukowa ta samu Jamal kwance kan 2seater bacci ya d'aukesa, murmushi tayi ta k'arasa ta tab'asa tana cewa

"Jamaludeen a nan kake bacci, maza tashi kaje ka kwanta"

Ya bud'e ido dakyar

"Ammi ina Wife"

Duka ta d'aka masa ya bud'e ido dakyau yana muzurai

"Maza je ka kwanta, karna dawo na sameka a nan"

Ta haura sama ta barshi nan.

Da Asubah Abba ya sauko dan tashin Areef zuwa masallaci, a d'akin ya samu Jamal kwance kan Tiles yana bacci abinsa hankali kwance, Mamaki ne k'arara a fuskanshi ya k'arasa ya soma tashinsu, Areef ma yayi mamakin Ganin Jamal d'in a d'akin. Tare suka tafi masallacin su uku.

K'arfe takwas na safe duk sun hallara a falon before ayi breakfast, Ummy na zaune k'asa kan carpet kusada k'afar Ammi itada Areefah, Haka Jamal shima zaune kusada Abba, Abba yayi gyaran murya ya soma da cewa

"Wannan zaman yakamata ayishi da d'ayar matarka, saidai kafin tazo inaso nayi magana akan abinda ya faru Jiya"

Jamal ya duk'ar dakai dan yasan dashi za'ayi, Abba ya juya garesa fusaka ba yabo ba fallasa yace

"Da Mabrookah da Jaleelah duk matanka neh, duk sadaki ka biya ka aurosu koh?"

Jamal dake gefe ya gyad'a kai kamar kad'angare kansa k'asa

"Sam banji dad'in abinda ya faru bah jiya, idan rai ya b'aci bai kamata hankali ya gushe bah. Yakamata ka tsaya kayi alk'alanci kafin ka zartar da hukunci. Anma zartar da hukunci cikin fushi babu abinda yake haifarwa sai danasani"

Ya numfasa yace

"Baka kyauta ba sam Jamaludeen"

Ammi dake gefe tace

"Saki nawa ka mata?"

Kansa k'asa yace

"Biyu!"

"What!" Cewar Abba ransa a b'ace

"A haka kakesan mu zauna a nan gidan"

Ya d'ago idanunsa cike da kwalla yace

"Abba dan Allah kayi hak'uri!"

Abba ya sauke ajiyar zuciya yace

"Areefah jeki kiramin Mabrookahn"

Ta mik'e tana zunguro baki ta fita, Side din ta shiga ga mamakinta yanda falon yake jiya haka ta samesa, ta tab'e baki

"Sai shegen k'azanta"

Knocking ta soma a k'ofar bedroom d'in shiru ba amsa tafi minti goma a tsaye taja tsaki ta banko k'ofan ta shiga. Batsa batsa ta samu d'akin kayan wardrobe duk a k'asa da sauran tarkace. Ta taka tana yatsine fuska har Toilet d'in nan ma ta dunga bugawa ba amsa.

Har zata fito idanunta suka sauka kan wani Farin takarda mai d'auke da rubutu da aka d'aurama Kwalbar humra. D'auka tayi ta soma karantawa

_Kayi ma iyayena k'azafi hankalinka bai kwanta bah, ka..._

Tayi saurin dakatar da karatun ta fita dasauri zuwa d'ayan side d'in. Tana shiga tace

"Abba ban ganta ba saidai naga wannan takardan"

Ta mik'a masa ya duka na 'yan mintina sannan ya mik'ama Areef yace ya karanta kowa yaji

_Kayi ma iyayena k'azafi Hankalinka bai kwanta bah, ka d'auko wasu mutane dan suci dukiyar Abba wai kai Iyayenka, to ka sani alhakin Iyayena bazai tab'a barinka bah. Sannan indai Ummy ce wallahi baku isa ku zauna lafiya bah, badai saboda ita ka sakeni bah? To wallahi baku ba samun Farinciki indai ina raye. Na tafi na bar muku waje ku shak'ata saidai ku jirayi dawowata.A_

Daga Matarka abar sonka Mabrookah.

Areef na gama karantawa yaja dogon tsaki

"Abba kagani koh? Ni dama wallahi tunda na ganta sam batamin bah"

Kasa cewa komai Abba yayi Ammi tace

"Areefa kuje keda Ummy sama kuyi breakfast sannan kuyi sauri dan 10 za'a shiga Court gashi 9 yanzu"

Ta kama hannun Ummyn suka haura sama zuwa d'akin Ammin, suna shiga Ummy ta zauna bakin gado ta fashe da kuka, Areefah ta zauna kusada ita dasauri tare da dafa kafad'arta

"Haba Aunty Ummy ki daina kuka, insha Allahu babu abinda Mabrookah ta isa ta miki wanda Allah bai miki bah"

Ta saki murmushin takaici

"Nasan Halin Mabrookah sarai akan abinda takeso tana iya komai Areefah"

Areefah ta soma share mata hawaye

"Oh! Stop crying Allah ya fita"

Bata sake cewa komai ba sai kukan data cigaba, Breakfast d'insu Areefah ta d'auko musu, ba yanda batayi akan Ummyn taci ba taki, saima kwanciya datayi wani mugun zazzab'i ja neman rufeta.

A falo kuwa su Areefah na haurawa Ammi tace

"Gaskiya Alhaji inasan rayuwar d'ana dana matarsa. Banasan abinda zai tab'asu, cikin biyu gaskiya za'a zabi d'aya ko mu zauna dasu ko mu koma gaba d'aya abujan tare"

Jamal ya karb'e da cewa

"Abba Ammi dan Allah ku gafarceni ku yafemin abinda na muku".

Abba yace

"Babu komai anma kada hakan ta k'ara faruwa"

Shiru ne ya biyo baya, Ammi ta sake cewa

"Alhaji bakace komai bah har yanzu"

"Ammi dama inso idan kun amince sai na saida gidan nan na sayi wani a chan Abujan"

Sai a lokacin Abba yace

"Gaskiya nayi matuk'ar mamakin kalaman yarinyan nan, yarinya k'arama kamar wannan da irin wad'an nan maganganun"

"Ba abin mamaki baneh ai Alhaji, ka manta gado?"

Ya sauke ajiyar zuciya yace

"Na aminta da maganar taka bama saika saida gidan bah, chan is ok for us ai"

Ammi ta saki lallausan murmushi

"Allah ya k'ara rufa mana asiri ya kuma karemu daga sharin mak'iya"

Duka suka amsa da Ameen.

Nan Ammi tayi serving musu breakfast sannan ta haura sama wajansu Areefah. Ganin Ummy kwance yasa ta k'arasa
dasauri bakin gadon

"Ummy lafiya?"

Ta d'agota taji jikinta da zafi, gaba d'aya Ammin ta rud'e ta soma neman magani. Dakyar ta samu tad'anci wani abu sannan ta bata magani, kan kace komai ta amayar dashi. Koda lokacin tafiya yayi Ammi tace su tafi ita zata zauna da Ummyn, hankalin Jamal gaba d'aya yana kan Wife d'insa hakanan badan ransa yaso ba suka tafi Court d'in dasu Abba harda Areefah.

A chan suka samu su Ram da Mifzal, bayan alk'ali ya zauna aka gabatar dasu Mami, kallo d'aya zaka musu duk su baka tausayi sunbi sun rame sunyi bak'i kamar basu bah. Idanun Mami na kan Jamal tana hawaye tana kallansa. Bayan an karanto shar'ia aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai.

Ba shiri Jamal ya fashe da kuka a Court d'in, Areef ya fito dashi waje yana lallashinsa. Mami sai kuka take itada Aunty Faty, haka aka fito dasu Aunty Faty na tafiya da k'afafunta while Mami na kan Wheel chair ana turata.

Jamal na ganinsu ya fizge daga rik'on da Areef ya masa ya nufesu Mami ta fashe da kuka

"Ka yafemin Jamaludeen, ka yafemin"

Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu.

Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Page 91

Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu. Guiyawu biyu yasa a k'asa yana bin motan da kallo hawaye na cigaba da zuba daga idanunsa, Areef ne yayi saurin k'arasowa ya d'agosa daga k'asan tare da rungumesa yana hawayen tausayin yayan nasa.

Mifzal wanda fitowansa kenan daga court d'in ya tab'e baki cike da takaici, sosai abin Jamal ke basa mamaki. Abba shima ya k'araso ya rik'e masa hannu yana lallashinsa, mota suka sakashi suka d'au hanyan gida.

Maganganu Masu dad'i Abba ya dunga ma Jamal na kwantar da hankali har ya samu yad'an saki ransa kafin su isa gida. Uffan Areefah batace ba sai bin Jamal d'in datake da kallo.

Koda suka isa gida bai shiga side d'in dasu Ammi suke bah, d'akinsa ya wuce ya kwanta yana sauke Ajiyar zuciya, gaba d'aya jinsa yake wani iri ga zuciyarsa dake masa suya.

Areef ne yaba Ammi labarin hukuncin da aka yanke masu Mamin, hamdala tayi na godiya ga Allah, Areef tace

"Ammi ina Aunty Ummy"

"Ta samu bacci" cewar Ammin tana k'okarin shiga kitchen dan kawo musu abinci.

Koda Ummyn ta farka Alhmdullh jikin nata da sauki sosai, sai zuciyarta dake cigaba da tashi anma Aman yak'i zuwa. Areefa ne ta had'a mata ruwa tayi wanka sanan ta gabatar mata da abincin da Ammi ta mata. Sosai taci dan ya mata dad'i ga kuma yunwa dake damunta.

Kulla da gata Ummy tasha shi ranar, koda Jamal ya fito sallan Azahar a masallacin ya zauna bai shigo ba har akayi sallan La'asar. Ana idarwa Abba ya kama hannunsa suka shiga cikin gidan, kan dinning ya zaunar dashi yasa Areefah ta zuba masa abinci.

Ya yatsine fuska yana kallan Abincin

"Abba na k'oshi"

Abban ya zauna kan kujeran dake kusa dashi yana kallansa cike da tausayawa

"Nasan yanda kakeji a halin yanzu Jamaludeen, anma hak'uri da Addu'a shine abin abinda yafi dacewa. I knw its hard ka manta dasu, mutanen da suka rik'eka duk da ita bata maka rik'on daya dace bah"

Hawayen daya gani sun gangaro ma Jamal d'in ne yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa

"Addu'ar neman gafara shi ne kad'ai soyaiyar da zaka nuna musu a halin yanzu"

Ya daga kafad'arsa yana cewa

"Kasa ranka a inuwa, bansan ganinka cikin damuwa"

Jamal ya gyad'a kai tare da share hawayen idanunsa

"Nagode Abbana"

Abba yayi murmushi ya janyo plate d'in Abincin ya diba a spoon ya kai bakinsa

"Eat my son"

Yayi murmushi tare da bud'e bakin kad'an Abba ya saka masa yana cigaba da masa kalamai masu dadi.

Daga Ammi har Areefa da Ummy wacce ta sauko yanzu sun matuk'ar burgesu bama kamar Ummy, hawaye suka taru mata a ido ta k'arasa kan kujera ta zauna, Tana matuk'ar kewar Mamanta, kawaici kawai take dan bataso ta damesa musamman ganin halin da ake ciki yanzu.

Bayan ya gama ci Abba ya basa ruwa yasha, Sannan ya rik'o hannunsa suka dawo falon, Ummy tayi saurin zamewa daga kan kujeran ta gaida Abban ya amsa tare da tambayanta jikinta. Satan kallanta Jamal keta yi ta kauda kai gefe dan fushi take dashi. Abba yace

"Wai ina Areef ne tunda muka dawo ban gansa bah"

Ammi ta tab'e baki tace

"Kasan Areef da d'an banzan yawo, ba ya soma sanin gari bah"

Jamal yad'anyi murmushi yace

"Abba inaso muje mu gaida Umman Ummy idan ba damuwa nida su Ammi"

Ammi tayi saurin cewa

"Wallahi kamar ka shiga raina, ina zuci zuci na maka magana ka rigani"

Ummy ji tayi kamar an sakata a aljanna, badan su Ammi ba babu abinda zai hanata rungumansa dan

30 / 32