Author : Ummy Abduol Category : African Stories & Novels
kai dakyar
"Dan Allah karku kashe shi, ni na yarda ku kashe ni a madadin sa dan Allah"
Ta k'are maganan da matsanancin kuka. Ya saki wani irin dariya yace
"Mu umarnin da aka bamu kenan mu kashe ku duka ke dashi koda an bada kud'in"
Ya sake sakin dariya ya mik'e ya fita. Ta bisa da kallo tana kuka tare da kiran sunan Allah.
••••••
Jamal ko ya dad'e yana kai kukansa wajan Ubangiji yana kuka yana rok'on Allah ya kawo masa d'auki akan abinda ke faruwa dashi har zuwa goshin asubah sannan ya mik'e dakyar dan shima kanshi ne ke wani irin sarawa ya fito daga side d'in ko tsoron dare bayayi.
Side d'inshi ya shiga ya haura zuwa d'akinsa, Diary d'in nan yaci karo dashi a kan gado ya k'arasa ya d'auka ya bud'e page d'in daya tsaya ya cigaba da karantawa
_Watan gaririya muka soma cikin anguwan da muke gashi dare nata yi bamu samu wajan saka hak'arkarin mu bah. Kwatsam munzo wucewa ta wani bola mukayi muka soma jiyo kukan Jariri a cikin bolan, cikin tsoro muka matsa, Jamila matata ya rik'o hannuna tace_
" _Gaske ne wanna kukan mutum neh_ "
_Duk da ina cikin tsoro hakan bai hanani k'arasawa wajan bah, nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsaya ku....._
Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka.
*Toh Fah!*
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
_Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar yanda nakeyi dah_
*Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da kwana kad'an zan gama*
Page 72 n 73
Already dama ya sayi Ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma k'irga kud'in yana sakawa cikin Ghana must gon batare da wani tunanin bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa.
*A gurguje*
Ram ya kali Mifzal fuskanshi ba walwala
"Naji High court wajan lawyern dayazo da Wannan Alhaji Tijjanin, abin was terrible"
Mifzal ya gyara zama yace
"Kamar yah?"
Ram ya sauke ajiyar zuciya yace
"Anyi hayansa ne kawai yaje ya bada shaida akan bashin da akace Alhaji Tijjani na binsa"
Sosai Mifzal yayi mamaki, yace
"To yanzu menene abin yi?"
Ram ya gyara zama ya matso kusada Mifzal yace
"Kama Barr nan zakuyi ku tuhumesa, or a turashi state CID for investigation"
Sosai Mifzal yaji dad'in shawaran Ram, ya mik'e yana cewa
"Muje tare dan akwai tambayoyin da nakeso Alhaji Ameenu ya amsa min kuma inaso ya kasance a gabanka"
A tare suka mik'e suka fito, already dama Mifzal yasa record a wayansa, inda Alhaji Ameenu yake suna nufa, Mifzal ya zauna kan kujera Ram kuma na tsaye gefensa
"To Alhaji tunda ga lawyern ka a kusa dakai yanzu ina iya maka tambayoyi koh"
Harara Alhaji Ameenu ya wurga masa, Mifzal yayi murmushi sannan yace
"Inaso nasan ko kai wanene"
Saida Alhaji Ameenu ya kalli Lawyernsa ya gyad'a masa kai sannan yace
"Sunana Ameenu Jibril, ni d'an Kano neh, inada mata d'aya da kuma 'ya'ya biyu namiji da mace. Mafi yawan zama na a Egypt nake yinsa tare da iyalina"
Mifzal ya jinjina kai sannan yace
"Ko zan iya sanin sana'arka?"
Barr. Ishaq ya karb'e da cewa
"D'an kasuwa neh ku..."
Saurin d'aya masa hannu Mifzal yayi ransa b'ace
"Ina magana neh da Alhaji Ameenu Jibril bakai bah"
Gum Barr. Ishaq yayi sai hararan Mifzal d'in yake a fakaice. Alhaji Ameenu yace
"Kamar yanda lawyer na ya fad'a ni bussiness man neh, a da ne nayi siyasa"
"Menene Alak'ar ka da Alhaji Surajo"
"Mene kuwa tsakanin mu? Ni ko sunansa ban tab'a ji ba balle nasan shi"
Sosai yanda Alhaji Ameenu ya daburce yaba Mifzal dariya
"Come down Alhaji"
Gaba d'aya Alhaji ya tsure sai muzurai yake yana zufa, Mifzal yace
"An kashe Alhaji Surajo Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe shi, ko zaka iya fad'amin ranar kana ina"
Alhaji Ameenu ya k'ara tsurewa, muryansa na rawa yace
"I...inna k..kuwa? Ina gidana dake Abuja mana"
Barr. Ishaq yayi saurin cewa
"Why all this questions? Ni Lawyern Alhaji Surajo kadiri neh, haka zalika ni Lawyern Alhaji Ameenu neh. Kuma inada tabbacin babu wanda yasan wani tsakanin su"
Ran Mifzal in yayi dubu ya b'aci musamman yanda Barr. Ishaq ke d'aga murya yana magana a fad'ace. Yace
"Kullum da daddare wuraren k'arfe tara zuwa goma kana fita daga gida ina kake zuwa?"
Alhaji Ameenu ya juya ya kalli Barr sannan ya juyo ga Mifzal
"Bana zuwa ko ina sai wajan kasuwanci nah"
"Detective wannan tambayoyin ya isa haka, ba hannun Alhaji Ameenu a duk wad'an nan abubuwan. Kuyi gaggawan sakinsa ko na maka ku a kotu"
Wani dariya Mifzal ya saki
"Dako naji dad'i idan ka kaini kotu"
A fusace ya mik'e yama Ram nuni ya biyosa, ba musu suka fita daga seil d'in. Barr ya kalli Alhaji Ameenu yace
"Alhaji ka kwantar da hankalin ka komai zaizo k'arshe yau d'in nan"
Mifzal na fita yasa wasu 'yan sanda su fito masa da Barr Ishaq, cikin sauri suka fito dashi aka kaishi Secret room sai fizge fizge yake yana fad'a.
State CID aka kira sukazo suka tafi dashi dan a tuhumesa. Mifzal yace
"Jamal na cikin wani hali na rashin Ummy, idan ka ganshi sai ya matuk'ar baka tausayi"
Jikin Ram yayi sanyi yace
"Kafin mu samu wani information akan Barr Ishaq mu duba Jamal d'in mu dawo. sai shima mu tambaya ko sun k'ara kira"
Ba musu Mifzal ya zari key suka bar office d'in.
A b'angaren Jamal kuwa, Cikin Awa d'aya zuwa da rabi ya gama had'a kud'in tsaf ya saka a ghana must go kamar yanda suka buk'ata. Zama yayi yana jiran kiransu dan su fad'a masa inda zai aje kud'in.
Ba dad'ewa wayansa ya soma ringing, numbern Ummyn neh yayi appearing ya d'auka dasauri jikinsa na rawa ya kara a kunnensa
"Hello Wife!"
Muryan namijin nan neh ya sake ji, gabansa ya fad'i ya yayi saurin cewa
"Ina matata? Ina take? Ga kud'in ku na had'a muku ina zan sameku"
Daga chan b'angaren yace
"Good Boy! Lallai kana san matar nan taka."
"Dan Allah ka bani naji muryanta, dan Allah"
Ba musu ya kara ma Ummyn a kunne, tana kuka tace
"Ya Jamal ina kake? Dan Allah kazo ka tafi dani, ban..."
Akayi saurin fizge wayan, hawaye ne suka soma zarya a fuskansa yace
"Pls karku tab'ata, ku fad'amin inda zan aje muku kud'in na d'auki matata"
Cikin wani irin dariya Mutumin yace
"Ka aje kud'in a wajan bishiyoyin Bomo Village, daka iso wajan zamu ganka by 11:00am dot, kana wucewa zamu kasheta"
Wani k'ara ya saki, kamin yayi magana aka kashe wayan, agogo ya duba yaga 10:15am. Ya fashe da kuka ya d'au ghana must go d'in dakyar ya fita, bai ko kalli Mabrookah dake masa magana tana k'okarin k'arasowa inda yake.
Yayi saurin shiga motan ya tada ya bar gidan a guje.
Fitanshi Express yayi daidai da k'arasowan su Mifzal bakin Layin, sam Jamal bai lura dasu bah ya k'arama motar wuta yayi gaba, da Mamaki Mifzal yabi motar da kallo
"Kaga Jamal chan ina kuma zashi"
Ram yace
"Ji yanda yake driving da gudu, anya kamar ba lafiya bah mu bisa"
Ba musu ya juya kan motan suka soma binsa da gudu suma. Hold up ya samu wajan ABU ya daki stiering motan wasu hawaye suka sake gangaro masa, agogo ya duba 10:40am, ya rushe da kuka yanata danna horn. Yakai Minti Biyar a wajan ya samu ya wuce ya cigaba da gudu su Mifzal na binshi, Bomo Village sukaga ya shiga suka suka sa kan motarsu ciki.
Daga mirrown gaban motan ya Hango motar Mifzal d'in, ya sake dukan Stiering yayi saurin Parking ya fito yana kuka. Suma suna ganin Haka sukayi parking, ya k'araso inda suke tsaye
"Dan Allah ku koma, ku kyalleni Pls karsu kashe min matana. Amsota zanje yi, dan Allahu ku koma"
Gaba d'aya ya basu tausayi, Ram yace
"Ka samu kud'in neh?"
Ya duba Agogon Hannunsa 10:50am, wasu Hawaye suka sake zubo masa, cikin fad'a yace
"Ku rabu dani! Ku tafi ku kyalleni"
Ya sassauta murya cikin kuka yace
"Zasu kashemin matata idan har bankai bah har 11:00am bah"
Ha had'e hannayensa alamar bada hak'uri
"Dan Allah ku koma, kuyi hak'uri"
Hawaye Ram ya share na tausayin abokin nasa, ya duba agogon Hannusa 10:54am, Mifzal yace
"Yi sauri tho" cewar Mifzal. Da gudu ya shiga mota ya figa a guje yabar wajan.
Da wani matsiyacin gudu ya k'arasa inda sukace masa, Parking yayi ya bud'e booth ya ciro kud'in, a hankali yake tafiya har ya k'arasa wajan da akace ya ajiye.
Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motansa, K'aran Harbin Bindiga yaji from no where.
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
Dis page goes to
Sumaiya Eesah
Aunty Nurse
Precious Girl
Xeeaction
Team Bilal
Team Jamal
Maman Ahmad
Ahmad yusuf
And All Jamaludeen Fans Both Whtsapp and Facebook.💯❤ ILYSM
Page 71
Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka sosai
"Wai meke shirin faruwa dani neh? Allah ka kawo min d'auki a wannan hali danake ciki"
Ya sake fashewa da kuka, diaryn ya d'auka zaiyi gurgi dashi sai kuma ya tsaya yana kallanshi yana cigaba da kuka, dakyar ya sassauta gabansa na fad'uwa sosai ya sake bud'ewa ya cigaba da karantawa.
_nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsala kuka, ni da matata mun matuk'ar tausaya maka. Matata tasa hannu cikin fargaba ta d'agaka, wasu daloli muka gani shak'e da akwatin da kuma wasu zinarai duk a ciki._
_Munyi matuk'ar mamaki tare dajin tsoro, haka muka d'aukeka da akwatin muka nufi wani runfar mai k'osai muka kwanta har lokacin muna cikin fargaba._
Wani kuka ya sake zuwa masa yana cigaba da karantawa
_Washe gari da safe na duba cikin Jakan, inda na tsinci wata wasik'a a ciki wanda aka rubuta cewa kanada Iyaye Uwa da uba, sannan kai ba shege baneh. Da kuma wasu hotuna a ciki. Haka mukayi ta rainonka da kud'in da muka tsince ka dashi. Kud'i ne masu d'inbin yawa wanda na dunga chanza su a hankali na fara juyawa_
_Ina sanka fiye da yanda nake san kaina, haka matata ta d'auke ka kamar d'an data haifah. Na juya kud'in sosai kuma sun hab'aka fiye da tunanina. Ana haka Allah ya amshi matata Jamila ta sanadin Haihuwa inda bata ruga da ta haifi abinda ke cikinta ba ta rasu_
_Lokacin kanada shekara bakwai, nayi kuka haka kaima kayi kukan rashin Jamila. Ana haka Allah ya had'ani da Maimuna na aureta, sam na hanata sanar dakai cewa ba ita ta haifeka bah, sannan ko ita ban sanar ma ba Jamila ta haifeka bah. Wannan na rik'esa a matsayin sirrina da naka_
_Nayi matuk'ar kuskure da ban fad'a maka da wuri bah. Nayi tunanin barinsa a raina sai daga baya naga rashin dacewar hakan. Ka yafemin d'ana abin k'aunata, ka yafemin rashin fad'a maka ko kai waye....._
Page d'in gaba ya bud'e yana kuka yaga a daidai nan rubutun ya tsaya.
Ya rungume Diaryn ya sake fashewa da kuka
"Na yafe maka Abbana, Allah ya jikan ka kaida Mamana, nima ina sanku"
Tsam ya rungume Diaryn a jikinsa yana cigaba da kuka, gyangyad'i ya soma hakan yasa ya kishingid'a jikin gadon har lokacin Diaryn na jikinsa. A haka bacci ya d'aukesa mai cike da mafarkai kala kala, kiran sallahn Asubah ne ya tayar dashi ya mik'e zaune yana mik'a a hankali, juyawa yayi gefensa yaga diaryn a fad'ai k'asa ya bud'e.
Wani rubutu ya gani hakan yasa ya d'auka dasauri yana dubawa
_Ajiyarka yana cikin system d'in dake had'e da wannan littafi_
Dasauri ya mik'e ya nufi inda Jakan yake, wani zip ya bud'e sai ga system k'irar toshiba ta baiyana. Dasauri ya ciro ya kunna yayi sa'a akwai chargi, Yana kunnawa yaga password, bai sha wahala ba dan yasan password d'in Abban na komai nasa.
Bincike ya soma har Allah yasa ya samu wani information na wani b'oyayyen gidan Abban dake gyallesu, Harda inda keyn yake.
Wani lallausan Murmushi Jamal d'in ya saki
"Thank Uh dad! I love uh so much"
Ya share guntun kwallar data gangaro masa. Toilet ya shiga yayo alwala ya fito.
Koda ya isa masallacin har an tada sallah, yana idarwa ya fito dasauri ya shiga side d'in Abban. D'akinsa ya shiga ya duba inda yace Keyn gidan yake ya d'auka ya fito.
Motarsa yama key yabar gidan dasauri duk da yanda garin yake duk'u duk'u dan garin bai soma haske bah. Cikin 'yan mintina ya isa gyallesu kwatancen ya soma bi har ya isa k'ofar wani madaidaicin gida. Keyn ya d'auka ya bud'e gidan ya shiga da k'afar dama.
Ya bud'e gidan ya shiga yana haskawa da torch d'in wayansa. Gaba d'aya gidan yayi k'ura sosai, bedroom d'in daya gani ya shiga ya d'aga katifan kan gadon sai ga k'aton Akwati ya baiyana. Akwatin yajawo ya fito dashi ya bud'e.
Ba shiri ya koma baya ganin mak'udan kud'i dollars da kuma naira a ciki, ware ido yayi da mamaki yana bin kud'in da kallo. Daga saman kud'in akwai wata farar takarda inda aka rubuta
"Dukiyarka kenan d'ana Jamal, ka Gafarceni na rashin sanar dakai da wuri"
Hawaye suka gangaro masa, ya duba k'asan takardan inda aka rubuta
"Duk wani abu dakakeso ka sani game da kai kana iya duba cikin wardrobe"
Ya aje takardan a hankali yana cigaba da hawaye, wardrobe d'in ya bud'e yaga wani akwati mai d'an girma duk ya kod'e. D'aukowa yayi ya fita dashi zuwa mota sannan ya dawo ya d'au na kud'in dakyar ya kai mota shima.
A police station kuwa, kamar yanda Mifzal da Lawyern Alhaji Alameen sukayi, k'arfe bakwai tama Lawyern a police station d'in. Mifzal bai iso ba sai wuraren k'arfe Bakwai da rabi. A wajan canther ya samu Lawyern, Mifzal na ganinsa ya cire eye glasses d'in dake idonsa yana kallansa da Mamaki
"Are uh not Barr Ishak Haruna Lawyern Alhaji Surajo"
Yayi saurin gyad'a kai yace
"Yes nine"
Mifzal ya sauke ajiyar zuciya ya bashi dama suka shiga office d'inshi, bayan sun zauna Mifzal ya mik'a masa hannu sukayi musabaha
"Sunanan detective Mifzal Ibrahim, muna zargin Alhaji Ameenu neh da laifi guda biyu, Murder da kuma kiddnapping"
Da Mamaki Barristern yace
"Anma kuwa wannan abin da mamaki yake, duka duka watan Alhaji Ameenu nawa da dawowa k'asar Nigeria da zama"
Knocking akayi Mifzal ya bada umarnin a shigo, Ramadhan ne ya shigo da sallama yana sanye cikin Suit b'aki da wani breifcase a hannunsa. Sosai Mifzal yaji dad'in ganinsa ya nuna masa kujera ya zauna.
Mifzal ya nuna Ram yace
"Barrister Ramadhan Ahmad kenan Lawyern Jamaludeen Surajo"
Sukayi musabaha, Ram sai kallan Barristern yake da harara. Barr. Ishak yace
"Zan iya ganin Alhaji Ameenun"
Mifzal yace
"Why not"
Waya ya d'auka ya kira, chan sai ga wani d'an sanda, ya bashi Umarnin yakai Barr. Inda Alhaji Ameenu yake tsare.
Yana fita Ram ya kalli Mifzal yace
"Akwai wani abu mai matuk'ar d'aure kai dake faruwa"
Jamal bai zame ko ina ba sai gida, bai samu kowa a farfajiyan gidan bah, ya kinkimi Akwatin yakai d'akinsa, ya dawo yad'au d'ayan yakai. Already dama yasayi ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma irga kud'in yana sakawa cikin ghana must go d'in batare da wani tunani bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa.
Ummy Abduol✍🏻
[4/26, 8:16 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
By *Ummy Abduol*
Dedicated to My *Late Siblings*
*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/
_Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar yanda nakeyi dah_
*Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da kwana kad'an zan gama*
Page 72 n 73
Already dama ya sayi Ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma k'irga kud'in yana sakawa cikin Ghana must gon batare da wani tunanin bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa.
*A gurguje*
Ram ya kali Mifzal fuskanshi ba walwala
"Naji High court wajan lawyern dayazo da Wannan Alhaji Tijjanin, abin was terrible"
Mifzal ya gyara zama yace
"Kamar yah?"
Ram ya sauke ajiyar zuciya yace
"Anyi hayansa ne kawai yaje ya bada shaida akan bashin da akace Alhaji Tijjani na binsa"
Sosai Mifzal yayi mamaki, yace
"To yanzu menene abin yi?"
Ram ya gyara zama ya matso kusada Mifzal yace
"Kama Barr nan zakuyi ku tuhumesa, or a turashi state CID for investigation"
Sosai Mifzal yaji dad'in shawaran Ram, ya mik'e yana cewa
"Muje tare dan akwai tambayoyin da nakeso Alhaji Ameenu ya amsa min kuma inaso ya kasance a gabanka"
A tare suka mik'e suka fito, already dama Mifzal yasa record a wayansa, inda Alhaji Ameenu yake suna nufa, Mifzal ya zauna kan kujera Ram kuma na tsaye gefensa
"To Alhaji tunda ga lawyern ka a kusa dakai yanzu ina iya maka tambayoyi koh"
Harara Alhaji Ameenu ya wurga masa, Mifzal yayi murmushi sannan yace
"Inaso nasan ko kai wanene"
Saida Alhaji Ameenu ya kalli Lawyernsa ya gyad'a masa kai sannan yace
"Sunana Ameenu Jibril, ni d'an Kano neh, inada mata d'aya da kuma 'ya'ya biyu namiji da mace. Mafi yawan zama na a Egypt nake yinsa tare da iyalina"
Mifzal ya jinjina kai sannan yace
"Ko zan iya sanin sana'arka?"
Barr. Ishaq ya karb'e da cewa
"D'an kasuwa neh ku..."
Saurin d'aya masa hannu Mifzal yayi ransa b'ace
"Ina magana neh da Alhaji Ameenu Jibril bakai bah"
Gum Barr. Ishaq yayi sai hararan Mifzal d'in yake a fakaice. Alhaji Ameenu yace
"Kamar yanda lawyer na ya fad'a ni bussiness man neh, a da ne nayi siyasa"
"Menene Alak'ar ka da Alhaji Surajo"
"Mene kuwa tsakanin mu? Ni ko sunansa ban tab'a ji ba balle nasan shi"
Sosai yanda Alhaji Ameenu ya daburce yaba Mifzal dariya
"Come down Alhaji"
Gaba d'aya Alhaji ya tsure sai muzurai yake yana zufa, Mifzal yace
"An kashe Alhaji Surajo Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan