Chapter 32 Reading JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol READ HAUSA Novels

JAMALUDEEN Alkawarin Da Ya Sauya Komai by Ummy Abduol

Author :  Ummy Abduol Category :  African Stories & Novels

Chapter   32 / 32

93K to 95.6K   out of 95.6K words

kusa dana Ummyn, A nan yake shaida musu nan ne zasu zauna. Gidan shima yayi kyau matuk'a, bakin Ummy yak'i rufuwa saboda farinciki.

Ammi da Areefah suka tayasu Mama yi masa godiya ya kauda kai gefe yana murmushi tare da girgiza kai. Da farinciki duka suka koma gida, ba yanda baiyi Ummy taje d'akinsa ba tak'i. Haka ya hak'ura ya kyalleta anma wannan karan yayi fushi sosai.

Wuraren k'arfe Tara da rabi na dare ya dawo daga yawo yaga wad'an nan manyan mutanen masu sanye da bak'aken kaya a k'ofar gidan, parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga motan suka fita da gudu daga layin sauran mutanen na mara masa baya a wata hilux.

Ummy Abduol✍🏻
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
*JAMALUDEEN*
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

By *Ummy Abduol*


Dedicated to My *Late Siblings*

*Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/


Page 93

🔚

Parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga Motan suka fita da dugu daga layin sauran mutanen na mara masa naya a wata helux.

Shiru yayi yana tunanin Abinda ke fita da Abba da daddare, ya kunna motan yayi horn mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga. Ammi ya samu a falo itada Mama dasu Ummy suna hira, a hankali ya k'arasa ya zauna tare da gaidasu suka amsa da fara'a. Su Ummy suka mai sannu da zuwa ya amsa yana satan kallan Ummyn. Ammi tace

"Yauwa Jamaludeen dama Maman Jaleelah ce tace mai zai hana Umman Bilal ta dawo gidan da take su zauna tare"

Mama tace

"Gidan ne yamin k'ato kaga idan muna jin motsin juna yafi dad'i tunda itama ba miji gareta ba kuma Bilal d'in na nan"

Ya d'ago fuskansa d'auke da murmushi yace

"Babu damuwa Mama wannan shawaran yayi"

Mama ta sake masa godiya ya mik'e ya shiga d'akinsa.
Gaba d'aya jikinsa ne yayi sanyi ala ala yake su dawo dan yau ya k'uduri niyan tambayan Abban inda suke zuwa.

Kwanciya yayi kan gado a rigingine yana kallan ceiling ya dad'e a haka yaji knocking a k'ofar d'akin, bada izini yayi a shigo, Da sallama Ummyn ta shigo hannunta d'auke da k'aton tray ta k'araso ta aje k'asa sai binta da ido yake. Tad'an kalleshi tace

"Yau naganka wani iri lafiya kuwa"

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Lafiya lau kawai dai na gaji neh"

Ta duk'a ta soma zuba masa abincin, tana cikin zubawa yace

"Barshi haka"

Ta d'an d'ago ta zuba masa narkakun idanunta

"D'an kad'an fa na zuba ai bazai isheka bah"

Ya gyad'a mata kai kawai batare da yace komai bah. Ganin yanayin sa yasa ta mik'e ta xauna kusa dashi tare da kamo hannunsa

"Ya Jamal ko bakada Lafiya neh"

Yad'anyi dariyan k'arfin hali

"Lafiya na lau Wife kawai gajiya neh"

Plate d'in ta d'auka ta diba a spoon takai bakinsa, ya kauda kai tare da yatsine fuska

"Plsss Ya Jamal"

Yanda tayi maganan a shagwab'e yasa ya juyo ya d'an bude baki tasa masa. Da kanta ta basa yanata mata shagwab'a tana dariya har yad'anci dayawa. Yana gamawa ta tattara kayan ta aje gefe ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka. Nan ma saida sukasha daru dan tsayawa yayi kai da fata dole ita zatai masa. Guduwa tayi niyan yi yayi saurin janyota ta fad'a jikinsa ya sakar musu shower.

Soyaiya mai tsafta ya nuna mata wajan wankan sai susune kai take kamar *Ummu Manal* har suka fito. Da kansa ya shafa mata mai tanata turjewa idanunta a lumshe. Wajan shafa man ne kid'a ya soma chanzawa ina ganin haka nayi waje abuna.

Su Abba basu dawo gidan ba sai k'arfe shabiyu da rabi, lokacin gidan tsit da alama duk mutanen gidan sunyi bacci banda Jamal dake kwance rungume da Ummynsa dake bacci hankali kwance. Jin k'aran gate yasa ya zame daga jikinta ya d'an d'aga labule yana lek'awa. Bilal ne ya bud'e ma Abban mota ya fito sannan ya wuce side d'insa shi kuma Abban ya shigo cikin Falon gidan.

Jiki na rawa yad'au jallabiya yasa ya fito daga d'akin, ga mamakinsa Ammi ya gani a falon tana karb'an babban rigan daya cire, Yana juyowa suka had'a ido da Abban, Ammi itama ta juyo suna kallan kallo, Kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya k'arasa indasu Abban suke ya sadda kai yace

"Sannu da zuwa Abba, Ab..."

Yayi saurin d'aga masa hannu yace

"Nasan me zaka tambayeni"

Ya kama hannunsa suka zauna a falon, itama Ammi ta zauna. Abba ya sauke ajiyar zuciya yace

"Kamar yanda na baka labarin abinda ya faru damu shekarun baya har hakan yayi sanadiyar b'atanka. A lokacin da Mahaifiyarka ta tafi dakai ni kuma suka b'alle k'ofan suka kamani sukamin duka a nan suke shaida min wani Alhaji Dauda ne ya aikosu su kasheni. Alhaji Dauda Abokin kasuwanci na neh, tare muka shiga harkan kasuwanci dashi, sanda muka fara Allah ya soma bud'amin sosai sai ya soma min zagon k'asa dajin haushina. Shima a lokacin yana samu saidai ba kamar ni bah.. Tun sanda na bud'e shagon zinari tsanar dayake min ya yawaita, har takaiga ko na gaishe shi baya amsawa."

"Tun a wannan lokacin na gane ba masoyina baneh. Mutanen daya aiko suka harbeni na suma, sai sukayi tunanin na mutu ne suka tafi. Alumma annabi suka taimakeni aka kaini asibiti. Kwana hud'u da faruwan hakan mahaifiyarka ta dawo, babu wanda na fad'ama abinda suka shaida min sai matata. Ita ta cigaba da kula dani a asibiti saida na shafe wata hud'u sannan aka sallameni"

"Kwana na Uku a gida a ranar na hud'u na fita kasuwa, abin mamaki duk shagunana wasu sabbin ma'aikata na samu nan na soma fad'a akan waya basu izinin shiga shagona, a nan sukama Alhaji Dauda waya sai gashi yazo yake shaida min Shaguna mallakinsa ne ba nawaba. Nayi mamaki sosai na dangana ga Office d'in 'yan sanda, bayan nakai k'ara aka umarci wasu 'yan sanda su taho dashi. Ina nan zaune suka zo dashi aka d'au statement d'inmu akace naje sai gobe na dawo. Washe gari dana koma abin mamaki 'yan sandan suka nuna basu sanni bah haka zalika basu san zancen bah har suna k'okarin kulleni"

Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa

"370million shine darajan kayan shagona, Ba takaicin rashin kud'in nake bah, takaici na d'aya yanda ya hak'ikance akan rashin gaskiya. A lokacin babu Ofishin 'yan sandan da banje bah anma duk magana d'aya ce. Haka na had'a sauran kud'in danake dashi muka haura k'asar Masar da Mahaifiyarka, a chan na cigaba da kasuwanci cikin ikon Allah abubuwa nata hab'aka"

"Bayan dawowa na naji labarin ta dalilin dukiyata Alhaji Dauda ya zama babban d'an siyasa wanda a halin yanzu yake da babban matsayi a siyasar da muke ciki yanzu, shine nad'au alwashin saina d'au fansan abinda yayi min. Anma kash babu wani jami'in tsaron daya mara mani baya sai wani guda d'aya dake cikin garin kaduna, shi kuma bana samunshi sai dare lokacin ya dawo aiki. Duk sanda kaga nayi fitar dare Kaduna nake zuwa duba D'an sandan sannan kuma mu tattauna akan abinyi, ta bakinsa na samu labarin har yanzu Alhaji Dauda bai daddara ba yana cigaba da kwacen dukiyar mutane batare da ance uffan ba saboda d'aurin gindin dayake dashi a gwamnati"

Jamal ya sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa da maganganun Abban nasa, yace

"Abba mai zai hana nayi ma Mifzal magana, nasan insha Allahu za'a dace, kuma kaga IG k'anin Abbansa neh"

Ammi tace

"Jamaludeen kenan babu wani babban d'an sandan da ba'ayi masa magana bah"

Abba yace

"No ki barsa ya jaraba wata k'ila a dace"

Ran Jamal ya sosu sosai da jin labarin da Abban ya bayar

"Insha Allahu Ammi za'a dace, In Allah ya yarda K'arshen Alhaji Dauda yazo kuma wallahi bai isa yaci kud'in Abba bah sai ya amayo su"

Abba ya mik'e yana bubbuga kafad'ar Jamal

"Allah ya bada sa'a my Son, go and have some rest"

Saida safe ya musu ya koma d'akinsa cike da tunani kala kala. Washe gari da asubah Ummy ta sulale ta koma d'akinta, Shima bai tashi da wuri bah sai k'arfe goma, Koda ya fito Ya samu su Ammi da Mama zasu Kasuwa siyaiyar kayan da Maman zata buk'ata a sabon gidan nata. Gaidasu yayi tare da musu sallama suka fita.

A ranar ya nemi izinin Abba na zuwa Zaria don su gama da Mifzal, ba musu Abba ya amince masa da Bilal suka tafi, sun samesa sun masa bayani, ba tare da b'ata lokaci bah ya kira k'anin Abbansa ya masa bayanin abinda ke faruwa. Nan ya shaida musu su had'u a Abuja ranar Sati, sunmasa godiya sosai basu dawowa ba sai washe gari, a ranar suka d'auko Umman Bilal basu d'auko Bahar ba dan yana karatu a ABU kuma yana tsaka da karatu.

Ranar da suka iso Mama da Umman suka tare a sabon gidansu, Godiya wajan Umma da Bilal ba'a magana dan sunyi matuk'ar farinciki sosai.

Kwana biyu tsakani Mifzal ya iso a ranar suka samu ganawa da IG gaba d'ayansu harda Abba, ba'a dau lokaci ba aka fara Bincike kan maganan. Cikin satin Ummy ta tare a nata gidan Bakin Jamal har kunne.

Soyayya Jamal ke nunama Ummy nasa kamar ba gobe, yana tattalin abinsa sam bayansan abinda zai tab'a matar tasa. Kyautatawa babu irin wanda Jamal bayama Sarakan masa.

*Bayan Wata Biyar*

Cikin Ummy yayi girma sosai yakai watan haihuwa, kulawa babu irin wanda bata samu daga wajan Mijinta da surukan nata harda su Mama. Dole Ammi tasa Jamal ya d'aukota ta dawo kusada Ita, cikin yayi nauyi sosai har anata tsammanin ko 'yan biyu ne anma duk scanning d'in da'akai d'aya yake nunawa. Hakan yasa kullum da yanma Jamal ke sata gaba sai sun fita road work duk bayan la'asar.

Yauma kamar kullum sun fito suna tafiya a hankali sai sannu yake mata tanata tura baki, kamar daga sama taji an kira sunanta

"Ummy!"

Juyawa tayi dasauri wa zata gani in ba Laurat bah, da mamaki Ummy tace

"Laurat kece"

Da murmushi ta k'araso inda suke tace

"Ni ce Ummy ashe da rabon zamu sake had'uwa"

Ta gaida Jamal ya amsa fuska a sake dan ya ganeta, tace

"Ina aiki ne a nan bayan layin, Allah sarki tun bayan barina Gidan Mami bamu sake had'uwa bah"

Jamal yace

"Yanzu ku muje mu k'arasa gida sai kuyi Hiran dakyau"

Ba musu Laurat tabisu har gida, Ammi ta amsheta dakyau suka k'ulle a d'aki sunata hira. A nan Laurat ke shaida mata tasan duk abinda ke faruwa a gidan ta bakin wani Mai gadi dake unguwar d'an anguwansu ne dake chan kaduna. Ta sauke ajiyar zuciya tace

"Gaskiya Mami batada imani, zataga K'arshenta insha Allahu"

Ummy tayi murmushi dai batace komai bah, Laurat tace

"Wai meya faru da Mabrookah dan kwanaki na ganta a wani guest house a nan garin, nifah yanda na ganta kamar karuwanci take"

"Karuwanci?" Cewar Ummy tana zare ido

"Wallahi kuwa, bakiga ma kayan jikinta bah"

"Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun" cewar Ummy tana dafe da goshinta, ta cigaba da cewa

"Gaskiya Mabrookah ta b'ata wayonta, Allah ya kyauta"

Laurat ta amsa da Ameen suka chanza hira, tad'an dad'e a gidan sannan ta tafi bayan tama Ummy kwatancen Gidan da take.

Bayan kwanaki Akayi shar'iar Alhaji Dauda da Abba kuma Alhamdulillahi shari'a ta tafi yanda akeso dan su Abba sunyi nasara. Bayan fitowa daga shar'iar wanda Ram ya kasance Lawyern Abba, nan suka samu chinchirindon mutane masu son abi musu hak'insu wajan Alhajin Daudan, nan aka sanar dasu kowa za'a bashi hak'insa sukayi ta godiya.

Kwana biyu tsakani Akama Mifzal k'arin girma tare da transfer ya koma Abuja, Ram shima ya samu wani contract da wani Company inda ya kasance Lawyern Companyn duk dai a nan Abujan.

Ranar wata talata Ummy ta tashi da ciwon nak'uda, cikin ikon Allah ana isa asibiti ta sub'uto santalelen d'a namiji mai kamada Jamal sak. Murna wajan Jamal ba'a magana, su Abba sunyi Farinciki sosai Bakuna yak'i rufuwa.

Ranar suna Yaro yaci sunan Abba Mijin Mami wato *Suraj* anma ana kiransa da *Alwaz* anyi bidiri sosai ranar suna harda su Laurat duk sun zo a nan Ram ya ganta ba wani b'ata lokaci ya nuna mata buk'atarsa bata tsaya wani jan aji ba ta amince masa.


```Bayan shekara D'aya abubuwan cigaba da alheri dayawa sun faru, Alwaz yayi wayo sosai har ya soma tafiya, Ummy tana shekarantanta na farko a Turkish Nile University, Ta k'ara murjewa tayi kyau kamar ba itaba. Kallo d'aya zaka mata ka gane tanada shigan ciki saboda yanda tayi fari da ta cicciko. A cikin watan Jamal ya samu aiki a k'asar Germany tare da sabon Companyn Versace. Murna wajan Ummy ba'a magana su Abba sunyi farinciki tare da sa Albarka.```

A cikin watan akasa Ranar Mifzal da Areefah wata Uku, Lokacin saura Wata biyu bikin Ramadhan da Laurat wanda za'ayi a tudun wadan kaduna.

Tun a makaranta take ta jin kamar zazzab'i zai rufeta, dakyar ta iya attending lectures d'in ranar, tana fitowa ta kira Jamal a waya, ba'adau lokaci bah ya iso makarantar duk hankalinsa a tashe, hand bag d'inta ya amsa tare da rik'o hannunta ya sakata a motan yanata mata sannu.

Sun d'au hanya suka hango chinchirindon jama'a a tsakiyar titi, parking yayi ya fito wani mutumi ya gani yana baro wajan, ya masa sallama tare da tambayansa abinda ke faruwa, mutumin yace

"Wata 'yar shaye shaye ce ta shigo hanya mota ta bigeta wallahi, tama mutu. Kai irin wannan rayuwa ta 'yayan yanzu Allah ya sawake"

Jamal ya masa godiya harya bud'e kofan mota ya hango ambulance d'in road safety sun k'araso wajan, nan aka mutane suka mamatsa aka basu waje, kamar a mafarki ya Hango Mabrookah kwance a wajan, sake mutsutsuke idanunsa yayi dan ya tabbatar da abinda ya gani, bai san sanda ya saki k'ofan motan ya k'arasa wajan bah, har an d'auketa an sakata a mota. Sai bin motan yake da kallo gabansa na fad'uwa. Yana nan tsaye aka wuce da gawanta, hawaye suka gangaro masa yayi maza yasa hannu ya share. Koda ya shiga motan bai fad'ama Ummyn wacece bah, yadai ce wata aka bige. Da damuwa suka isa gida har lokacin yana tausayawa Mabrookahn da tunanin Makomanta.

Bayan wata d'aya Jamal yayi reporting a wajan aikinsa achan Germany, ba b'ata lokaci ya soma aiki dasu kuma yana jin dad'in aikin saidai abu d'aya dake damunsa rashin iyalinsa kusa dashi.

Haka itama Ummy tun bayan tafiyarsa ta dawo gidan Ammi da zama saboda kewar mijinta, tare suke zuwa makaranta da Areefah, Alwaz shekaransa d'aya da wata d'aya yayi wayo sosai kamar d'an shekara d'aya da rabi. Lokaci guda yak'i nono ya yaye kansa, gashi bashi da k'iuya hakan yasa ya koma Wajan Ammi tana kula da jikan nata.

_A nan sai ince Allah ya k'arama wannan Family zaman lafiya da san juna Ameen_

*ALHAMDULILLAH*

A nan na kawo k'arshen Littafina mai suna _JAMALUDEEN_
Kurakuren danayi Allah ya yafeni, abinda na fad'a daidai Allah ya bamu ladan gaba d'aya. Darusan dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka Ameen.

```Na yanke labarin neh saboda Zuwan watan Ramadhan, dan banaso mukai har bayan sallah bamu gama bah. Ina fatan zakumin Afuwa```

Ina godiya ga Masoyana gaba d'aya, Allah ya barmu tare. Ina sanku kamar yanda kuke sona.

Sai kunjini a cigaban littafina mai suna *GA ZARAH GA WATA* bayan sallah insha Allah.

Inayi ma kowa fatan alheri, Allah yasa muyi azumi Lafiya ya kuma bamu lada da falallan dake cikinta Ameen.

RAMADHAN KAREEM
In
Advance

Ummy Abduol✍🏻

32 / 32