Chapter 56 Reading SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee READ HAUSA Novels

SO NE DALILIN HAWAYENAH by Khadija bee bee

Author :  Khadija bee bee Category :  African Stories & Novels

Chapter   56 / 58

165K to 168K   out of 173.5K words

dole yanzu ta dinga tsayawa tana gani, tun da bata iya dogon tsayi.

Cikin farha yayi girma, wanda sai dai ta d'inka dogayen riguna ba dai zane ba, domin cikin nata kowa kira mata twins yake saboda wani girma da yayi.

Tunda Abdul-jabbar yaga yadda farha ta zama, komai sai da kyar, sai ya rage nuna nacinshi akanta, domin yasan idan yace yana so, zata aminta ta bashi, amma kuma zata wahala sosai.don haka sai ya daina zak'ewa sosai, sai dai wasannin da ya saba yi da ita, idan zai fita, ko idan ya dawo kafin yayi wanka, wanda suma yasan k'arfin hali ne kawai take yi, domin bata son barinshi da k'ishirwarta ko kad'an.

Bayan farha ta daina zuwa gurin aiki, sai dai bata daina yin waya da k'awayen aikin ta ba,kuma sun shaida mata, da taji alamar na k'uda, basai ta je asibiti ba, zasu zo su kar'bi haihuwar da kansu gida, ako yaushe haka suke fad'amata.

Tunda watan haihuwar ya shigo, sai cikin gabad'aya yayi dawo k'an mararta ya tsaya, hakan yasa ko tashi bata son yi, domin ita kad'ai tasan me take ji.

Tunda cikin ya shigo month nashi, ko yaushe Abdul-jabbar cikin yima farha waya yake yi idan ya fita office, burinshi yaji komai normal. Wanda har dariya farha ke yimai, tare da ce mashi ta haifi twinx, sai daga baya yake gane cewa wasa ne.

Kamar kullum yau haka yau farha ta tashi, domin gyara Ikram da kuma duba yadda aikin ke gudana. Tunda farha ta tashi, sai take jin ba a yadda tasan kanta ba, yau take jin kanta ba, bata fad'ama kowa، sai wata nurse yar uwarta, itama don taji abun ya wuce gurine, gata ita kad'ai cikin gida babu kowa, hakan yasa ta nemi taimako, domin abun ya fara wuce guri.

Sistr farida, ita ta kasance da farha tun da ta kirata, sai dai har yanzu haihuwa shiru, kusan 3hour farha na abu guda.

Farha ta hana a sanar da Abdul-jabbar domin tasan zai rud'e sosai.sister farida tace..

"Sistr idan abun nan yak'iya fa, wajibi a fad'amasa mu wuce asibiti, domin kusan 2 hour fa amma har yanzu 2 c.m kike fa, kuma idan baki kai 4 c.m ko 5 c.m ba, wallahi haihuwa bata iso ba "
Farha da ko magana a halin yanzu ta kasa, ta nuna mata hannu da ta kirashi, domin ko c.s ne ta yadda ayi mata, domin wahalar ta yi mata yawa, tana iya mutuwa take gani.

Farha d'in ta nuna mata wayar, tare da ambaton sunan da ta rubuta mashi, nan take ta kirashi.
Tunda yaga kira ya san cèwa da matsala.hakan yasa bai tsaya komai ba, ya kamo hanyar gida aguje kamar wanda bai san akwai hatsari a hanya ba, sai sauri yake yi, amma gani d'ewar tafiyar yake yi.

Da wannan gudun ya iso gida ko rufe motar bai yi ba ya fad'o gidan.......




*Bee Been masoya*💞
[4/22, 4:22 PM] 💖HASKEN MASOYA💞: 💧💧💧💧💞💧💧💧💧
*SO NE......*
*DALILIN HAWAYENAH😭😭*
💧💧💧💧💞💧💧💧💧

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

©®
Khadija bee bee
Khadijabeebee@gmail.com

My wattpad user name.... *khadijabeebee......*
My Facebook page....
*beebeenmasoya*

*I LUV YOU ALL MY FANS*
💋💋💋💋💋

★TRUE LYF STORY★
★★★★★★★★★

*ALLAHUMMA IHDINAS SIRA'DAL MUSTAQEEM*
ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘ðŸ»ðŸ‘

Page..79


Da gudu Abdul-jabbar ya shigo gidan.Dai-dai da fitowar sister farida tana k'walawa sadiya kira domin kawo ma farha ruwan Lipton domin k'ara samun kuzari, da alama lavour ya iso kusa yanzu, tunda har farha ta kai 4c.m.
Karo sukayi da juna, sannan wanda sai da sistr farida taji tsoro. A rud'e yake shi yasa bazai gane hakan ba. Kallonta yayi sannan ya tambaya cikin rud'u.

"Yaya take ne?"
Sistr farida tace "to da sauk'i, insha'allah nan da 30mnt, ina saran zata haihu,domin yanzu ta kai c.m d'inda baby zai fito, amma yanzu akwai saura, domin an sanya mata drip, insha'allah komai normal zai je. Yanzu ma lipton nake so a kawo mata domin ta samu k'arfin yin nishi"

Abdul-jabbar da sauri ya nufi k'ofar shiga d'akin. Sistr farida tace "ah ah! Da ka bari ta haihu sannan ka shiga, domin yanzu kaima ba zaka ji dad'in ganinta a hakan ba "

"Haba sister! Ai samun natsuwata shine; naga halin da take ciki, kada ki manta, matata ce fa, don haka zan shiga muyi wahalar tare, burina taimakon ki akan mu, naga ta fita lafiya "

Murmushi sistr farida tayi, sannan ta matsa ya shiga ciki.hango farha yayi kwance da ruwan nak'ud'ar a hannunta sai matsar fuska take yi, tana juyar da kai alamar azaba da rad'ad'i.
Da sauri ya isa gurin ya rik'o hannunta, sannan yace....

"Farin ciki na sannu! Allah ya rabaku lafiya "

Shi kad'ai ke zancen shi, domin farha bata san yanayi ba, domin bata shaida wanda ke kanta iya lokacin.
Sistr farida ta shigo da cup d'in lipton a hannunta.Abdul-jabbar ya d'ago kan farha, sistr farida ta bata ruwan lipton d'in da ke da d'an zafi, domin samun kuzari.
Ba'a fi 10mnt ba, nak'uda ta taso, wanda banda zufa da juyar da kai babu abun da farha ke aikatawa, domin abun ba na wasa bane. Hakan yasa farida yunk'urin taimaka mata, duk da Abdul-jabbar ya k'i fita daga d'akin, k'arshe ma kan na farha a saman jikinshi ya dawo, hannunta d'aya cikin nasa ya dumk'esu, sai zufa su ke yi, ita gumin azaba ke fita, shi kuma gumin azabar tausayin sahibar shi dake sha, wanda bata gane komai.

Lokacin da wani mugun nishi ya taso mata, sai da tayi k'ara mai k'arfi, tare da sakin dukkan hannayenta daga jikin Abdul-jabbar, tayi wani nishi mai k'ara, wanda sai da taji mutuwarta tafi mata wannan azaba.

"Alhmdllh!" Abun da sistr farida ce kenan, fara 'bullowar kan baby. da kanta ta taimaka ma farha,gurin k'arasa ciro babyn k'ato guda,wanda batayi mamakin ganinshi a hakan ba, domin farha ta sha wuya sosai, hour 8 tana abu d'aya.

Fitowar baby, sai farha itama tayi k'arfin halin cewa "Alhamdulillh"
Sannan taji wani barci mai dad'i ya d'auketa, hakan yasa Abdul-jabbar gyara ma farha kwanciyarta, sannan ya juya karbar new baby nashi mai shegen kyau da girma.

Bayan sister farida tayi duk wani taimako da nurse ko likita ke bama duk wani wanda yayi labour.haka tayima farha, Abdul-jabbar ke rik'a mata har suka tsaftace gurin da ya lalace, sannan ta d'auki new born babyn nasu tana gyarawa, anan itama ta tabbatar da cewa; baby boy ne aka samu.

Farha banda barci babu abun da take yi, domin ba zata shaida Abun da ta samu ba, saboda ta dad'e tana neman barci, amma bata samu ba, sai yanzu da suka rabu lafiya.

Bayan natsar da komai, sannan Abdul-jabbar sai kiran waya ya tashi, duk inda ya kamata ace sunsan sun samu k'atuwa, sai da Abdul-jabbar ya fad'i.Rungume yake da baby nashi, sai murna yake yi yak'ara zama babba, uban 'ya'ya biyu, wanda ko wannensu k'aunarsu yake yi.

Hafsart matar hafiz, tunda akayi waya aka sanar dasu, ta kwaso mayafinta da sauri ta fad'o gidan da murnarta. Sai ta rik'a aka k'arasa gyara abun da ba a k'arasa gyarawa ba, ita ta aza ruwan zafin da za'ayi ma baby wanka, sannan itama farha aka d'aura nata, duk da barci take yi har yanzu.

Komai ya lafa, gidan ya dawo tamkar ba anan akayi labour d'inba, sannan farha na tashi abinci ta fara kiran a kawo mata, sannan taci ta iya takawa toilet gurin wanka.
Alhmdllh! Domin haihuwar ta zo da sauk'i sosai. Saboda farha ta haihu ko k'arin da ake yima mata, ita ba'a yi mata shi ba, duk da zamowar babyn k'ato guda barakallah, amma ita komai normal, sai wahalar labour da tasha, wanda kuma dole ne, tunda ba'a haihuwa banza.

Sister farida ta k'arasa yima farha Alluran da ya kamata tayi mata, domin ta k'ara samun k'arfin jiki, sannan ta rubuta maganin da ya kamata, a siyo mata da baby shima kanshi, domin dukan su sunsha wuya, sannan tayi sallama da su, don komawa gidan ta itama.

Sistr farida, ta sha mamakin irin k'aunar da Abdul-jabbar ke yima family d'in nashi, ta dad'e a rayuwarta, tana mamakin irin wannan kulawa da yake yi da matarshi, babu kamar gurin labour d'in, wanda duk lokacin da azabar ta murd'a ma farha, har wani rik'eta yake yi, shima kamar yayi kuka. Bai samu natsuwa ba, har sai da farha ta sauka lafiya, sannan ya samu relief, kuma k'aunar ta juya a babyn sak.

Abdul-jabbar Alkhairi ya k'unsa ma sister farida, mai yawa, amma tace bazata kar'ba ba.Abdul-jabbar ko sauraronta bai yi ba, har ya kaita k'ofar gidan nasu, ta shiga ya samu yara ya turasu da kayan da aka bata.Turamen atafa ne manya guda ukku, da turare guda biyu manya, da set d'in man shafawa da sabulu, sannan da kud'i I5k a wata farar takarda a nad'e, wannan duk tukuycin k'ok'arinta ne da ta yi.

Bayan ya dawo gida, sai ya tare a d'akin farha, wanda kowa ya watse, ita kad'aice zaune a gado, tana kallon babyn da ke ta famar tsutsar hannunshi, alamar yunwa ya ke ji. Ikram duk ta wani tattare ko ina kada a ta'ba masu babyn su, wanda hakan ba k'aramar dariya ya bama Abdul-jabbar ba. Babu yadda bai yi ba, taje gurin aunty sadiya ba, ya gana da farha, amma yarinyar nan tak'i tafiya. Juyawa yayi yace ma farha....
"Zanzane d'iyarki fa, ko ki ce mata ta tafi"
Kallon Abdul-jabbar farha tayi, sannan ta zaro ido duka waje, alamar jin tsoron zancen da ya fad'a. hakan yasa ko kallon gurin da yake batayi ba, ta k'ara gyara kwanciyarta a filo tana kallon Ikram da baby, wanda shi kawai take kallo tana dariya.

Abdul-jabbar dubara ta fad'o mashi yace...

"Ikram ki kira aunty sadiya,sai ta d'aukar maki babynki ku tafi dashi d'akin ku ko?"

Da sauri Ikram taje tana murna, dama sadiya ita take jira, ta fito ta bata abinci kuma tayi mata wanka ta kwanta, domin dare ya fara yi, gashi gobe akwai school. Wanka tayi mata, sannan ta bata abinci, sai tace su je su kwanta. Ikram tace ai bata san hakan ba, domin cewa akayi gurinsu baby zai kwana, don haka Aunty sadiya taje ta d'auko mata babyn ta.kuka take yi sosai, har farha najiyo kukanta, kuma sai taji shiru alamar tayi barci.

Fitar Ikram, Abdul-jabbar ya d'auki babyn ya matsa kusa da farha yana cewa....

"Ki shayar damu, wallahi yunwa muke ji, duba kiga yadda yake shan hannu"

Farha kallonsu tayi, sannan ta juyar da fuskarta gefe, alamar babu. Abdul-jabbar ajiye babyn yayi, sannan ya jawota da kanshi, ya matse jikinshi, ya bud'e rigar tata da ya zamo ba wuyar bud'ewa zasuyi ba, domin rigar kawai ce jikinta, sannan ya d'auko babyn yace....

"Akan me bazaki bashi abincinmu ba, idan bakiyi hankali ba, har ni zaki shayar ba shi kad'ai ba, don haka ki kar'beshi ki bashi "

Farha yamutsa fuska tayi tace...
"Babu komai a cikinshi fa, har yanzu abincin bai zo ba, kuma wallahi zafi nake ji, ka barshi har zuwa gobe"

Bai ko saurareta ba, ya jawo babyn ya kara a bakin nonon nata, yark'e da kanshi, nan take babyn ya kama yana ja, kamar an koya mashi. Farha sai cije baki take yi, saboda babu komai a nonon kuma ja babyn yake yi da zafi, Abdul-jabbar saboda k'eta har wani k'ara matsawa yake yi, wai babyn yasha. Farha ta gano k'eta kawai yake yimata, don haka sai ta yi sauri cije mashi hannu tace ya barta ta bashi da kanta, sannan ta kar'ba tana bama babyn nono tana kallonsa. Abdul-jabbar ya rufe mata ido, yace...
"Ki daina kallar man yaro, saboda naga ba ki damu dashi ba, muma kuma a daina kallon mu "

"Eh waya ce ku wahalar dani to?"

"Kwad'ayi ne ya kaiki wahala, wanda gashi inata murna kin bani beautiful boy mai kama da ke"
Fad'in Abdul-jabbar kenan tare da dariyar k'etar maganar da yayi, sannan ya juyo yana kallonta, ita kuma jaye babyn tayi wanda barci yake yi, sannan ta juyar da fuskarta gefe, tana turo baki. Abdul-jabbar na ganin hakan da sauri ya kar'bi babyn ya ajiyeshi gefen su, sannan ya rungumo farha da sauri, tare da saka bakinshi kunnenta yana cewa....

"Wasa fa nake yi maki, ai dole na biya wannan k'ok'arin da kikayi, dama jira nake yi ki k'arasa bashi abincin, nima sai kiji dani, nayi maki sannu da abun alkhairin da kika sama mana, kin bamu baba Aliyu, kincika burina na samun baba na, ko nace; Allah ya cika burina da yabani baba a tsak'en jikin masoyiyata. My farha ina godiya fa, kinata cika buri na, gashi a k'ark'ashin soyayyar mu da k'aunar mu, mun samu beautiful boy, nayi mashi hud'uba da sunan baba, na saka mashi; *ALIYU (HAIDAR)* ina fatan hakan zai yi maki dad'i?"

Tureshi tayi jikinta, domin har wani shafe-shafe yake shirin yi a saman rigarta ta kalleshi yana wani lumshe ido tace....

"Anya kuwa, Aba Ikram lafiya kake? Duka ko 24hour banyi ba, da fitowa tsaka mai wuya, amma sai wani shafa ta kake yi, kamar wata mage, ko tausayina ma baka ji, kuma yanzu wani sanyin kake nema again "

"Kin ta'ba ganin wanda ya k'oshi da dad'i? Ai banda ma nasan halin da kike ciki, kuma bazan iya zuwa gurin ba, da sai nace a koma ruwa tun yanzu "


Yana fad'in hakan yana dariya tare da shirin k'ara rungumota yace "baki fad'aman taki shawar ba, akan sunan baby na ba?"

"To me zan ce, bayan yanzu ka kira shi da babyn ka, duk yadda kayi dashi ai naka ne.amma da shawara ce akan my Ikey; wannan nice gaba, don mugun son da nake yi mata ko......!
" ko meye? K'arasa mana naji "

"Ni dai barci nake ji, wallahi ka barni na huta hakan, Allah yasa umma ma tace na shirya mu koma gida, ko zan dinga barci "

"Wallahi ki jaye wannan zancen, domin babu inda zaki je, saboda idan na yarda, aikin da nake yi a yanzu zai samu matsala, saboda idan dai nayi winning gareshi, to na samu girma babba, wanda nake burin nakai gareshi, don haka ki daina cewa hakan, kinsan umma na iya yadda, kuma tace sai kin je, wanda ni kuma za'a cutar dani "

"To ka barni nayi barci na"
"Ban gama ganin ku ba"
"Sai ka d'auki babyn kuje kuyi fira, ni kuma sai na huta ko?"

Dariya yayi, sannan ya matso da babyn kusa da ita, ya mik'e zuwa toilet don yin wanka da alwallah ya fito, ya yi nafilar godiya ga Allah, sannan yayi shirin barci da farin ciki, yaje ya rufe ko ina ya dawo ya rungumesu suka kwanta.

★★★★

Kwana hud'u da haihuwa, su umma suka kamo hanya don zuwa ganin baby, tare da matan kawu.baba shi yayo driving nasu daga kaduna zuwa abuja.
Gidan cike da jama'ar arzik'i, wa'yanda suka zo gurin barka, wasu kuma sai anyi suna zasu koma.

Umma tace zata zauna, har sai anyi buki sannan zata koma gida,tunda an hanata d'aukar d'iyarta. Haka 'yan uwa na nesa da na kusa suma sun halarci garin abuja.

Umma dad'i soyayyar muji, wai ai haidar nata ne, don haka babu mai rabasu.
Part d'aya aka ware ma umma da jama'arta, don haka sai taron ya koma acen.

Mai jego da babyn ta sun sha kaya, domin set biyu yayi masu ko wannen su na kayan sakawa, wanda ikram ma da nata kayan na daban, haka sadiya ma sai da yayi mata kayan suna.

Rasheeda itama tazo ana gobe suna, haka k'annen mahaifiyar farha, suma sun zo Abujar gurin buki, wanda da gidan ya cika, wasu gidan Abdul-hafiz gurin hafsart suka sauka.

Daren sunan Aliyu haidar, komai an gabatar dashi, ta yadda ake sonshi, domin an shirya gagarumar walima wadda za'ayi gobe, a harabar gidan nasu.

Ranar sunan mai jego tayi kyau,ita da yaranta, domin idan ba ka sani ba, bazaka ce, itace ta 'bullo haidar ba, a satin da ya wuce, sunsha photo, tun a wayoyi, har a camera iri-iri, wanda duk pic d'in ko wanne Abdul-jabbar na ciki, sai da aka fara walima, sannan shima ya tafi yin tasu walimar da aka had'a gidan su hafiz da abokan shi.

Walima har walima, domin matan manya ne suka had'u, manyan k'usoshin garin abuja masu fad'a aji, domin yawan kwangilar aiki da suke bawa Abdul-jabbar, hakan yasa matan su, suka san farha sosai.

A gurin walimar anci an sha, sannan a raba kyaututtuka naji da fad'i, wanda itama mai jego da yaronta, sunga alkhairai masu yawa. Akayi buki aka k'are lafiya sai kuma huce gajiyar hakan.

Bayan ank'arasa komai, kowa ya koma masaukinshi, farha kawai ta rage, sai sadiya da ke ta hidimar gyara gida,domin Ikram tana cen part d'in su umma da suka sauka, ko nace part d'in umma, domin don iyayenshi yayi gurin idan sunzo. Farha wanka ta fito bayan ta gyara haidar sai ta bama sadiya ta goyashi kafin ta fito. Tasaye take tana shirya kanta, domin barcin da take ji, ba na wasa bane, hakan yasa take shirin Sharp-sharp, jin an rungumota ta baya yasata yin saurin rik'e towel d'in jikinta, kafin tayi wani yunk'uri, ya rungumeta baki d'aya jikinshi, sai k'amshi yake zubawa

56 / 58